Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din da duk kudure-kuduren sa. Ganin sun hango shi sun ya saka shi katse wayar da suke da Ya Nabila ya nufe su cikin tafiyar sa. Idanu duk suka zuba masa har Adam din hakan ya sakashi jin ya takura sosai, ya dan rissina kad'an ya gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa, hakan ya dan bata ran daddy ganin irin tarbar da sukayi wa Adam ba irin ta Aryan din ya samu ba, hakan kuma baya rasa nasaba da shi yadda Adam din yazo musu fuskar sa a sake cikin iya mu'amula da mutane.
A wajen shiga mota Daddy suka rabu da sauran, Adam ya karbi key din driver da ya kawo su ya shiga wajen tukawa yana jaddada shine zai kai Daddy gida, dariya sukayi shi da Daddyn dan shi komai Adam din yayi yana burge shi sosai yasan duk abinda zai ya faraanta ran Daddyn, a dole ba dan Aryan yaso ba, ya shiga gaba gefen sa ya zauna shi kuma Daddy ya hakimce a baya yana cigaba da nazarin halayen Aryan din duk da ba wai yau ne karo na farko da ya fara fuskantar hakan daga gare shi ba, amma kuma a yau sai yaga ya sauya masa sosai ya nuna matukar yanayin damuwa a tattare dashi, yasan damuwar sa bata raba dayan biyu akan abinda ya kwallafa rai ne yake ganin idan be cimma ba tamkar bashi da wani amfani a duniyar ma baki daya, dalilin sa kenan na sake komawa karatu a karo na uku yayi karatun da yake da yakinin samun cikar burin sa ta wannan hanyar, sai dai katse shi da Daddyn yayi ya kuma gindaya masa sharuda masu yawan gaske ciki har da dawowa yayi aiki a karkashin company sa wanda hakan yayi matukar takure shi, sai dai a duk wani abu da Daddyn zai saka shi ko ya gindaya masa baya taba iya ketare shi, shi din me matukar biyayya ne a gareshi ko da kuwa babu wata alama da take nuna soyayyar sa ga mahaifin nasa dan har kwanan gobe yana cikin mutanen da yake zargi wajen salwantar da rayuwar mahaifiyar sa, me tsananin so da kaunar sa. Shiyasa komai ya tsaya masa chak dan yana rayuwa ne kawai a karkashin ikon sa ba wai dan yana so ba, sai dan cika umarnin Allah da Yace lallai ya zama wajibi 'yaya su yiwa iyayen su biyayya akan duk abinda be sabawa Allah ba.
Hirar dake wakana tsakanin Daddyn da Adam din yake sauraro cike da kulawa Daddyn yake saurare shi yana kuma amsa masa daidai kamar yana hira da abokan sa makusanta. Aryan ya kan yi mamaki idan yaga yadda Daddyn ya sake da Adam ya bashi dukkan yarda fiye da kowa a duniyar nan, yayi matukar yarda dashi har ta kai baya ganin iyawar kowa sai ta Adam din. Duk da dai shi Aryan zai iya rantsewa da wayon sa ba zai iya tuna wata hira doguwa da ta hada shi da Daddyn ba, dan baya jin akwai wani abu da zasu iya tattaunawa akai idan har ba maganar mahaifiyar sa bace ba, tun da kuma yaki zancen yace masa baya so, tun daga sannan ya bar shi, be kuma sake tada masa maganar ba ko da wasa, shiyasa duk abinda yazo masa dashi toh kawai yake cewa ya aiwatar ba tare da wani dogon nazari ba, shiyasa magana a tsananin su bata tsawo kwata-kwata.

"Muhammad." Dan waigo da kansa yayi bayan motar hade da amsawa a lokaci guda

"Na'am?"

"Akwai wata matsala ne?"

_"matsala?"_ ya tambayi kan sa, dan ya manta rabon da yaji irin wannan tambayar daga bakin Daddyn, ai shi a kullum a cikin matsala yake sai dai babu wanda ya damu ya fuskance shi ciki kuwa hadda Ya Nabila da yake ganin kamar tafi yarda da uzurin da Daddyn ya bayar shi yasa a kullum take dakushe shi a duk yunkurin da zai yi. Duk a zuci yake wannan tunanin a cikin yan dakikun da basu gaza sha biyar ba, a fili sai ya hau girgiza kansa kafin ya ce

"Babu wata matsala."

"Ka gane kuwa abinda nake nufi? Maganar company nake yi, ina fatan daga bangaren ka babu wata matsala dan shi Adam yana bani details da duk abinda ya faru a rana which I'm very impressed."

_ohh."_ Ya raya a ransa, ashe ba tasa matsalar yake nufi ba, ta aikin da ya saka shi ce._

Dan murmushi yayi kad'an me ciwo wanda ya tsaya iyakar leben sa sannan yace;

"Alhamdulillah,babu wata matsala."

"Good, sai ku cigaba da kulawa da komai,dan zan kwana biyu gaskiya ban shigo company ba, domin Dr. Mubarak yace ina bukatar hutu dan haka zan huta sosai."

"Allah ya kara sauki Daddy, babu wata matsala ni da Aryan zamu tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata."

"Bana jin ka Adam, nasan zaka iya."

"Shima zai iya Daddy, duk da dai sabo ne a system din amma naga kwazon sa,gaba daya da baka nan din nan yayi dedicating dukkan energy dinsa wajen aiki."

"Ok." Daddy yace a gajarce ya daga wayar sa da take kara.

Kallon Aryan din Adam yayi a fakaice yayi dariya kad'an, ko dagowa Aryan be ba bare ya kalli bangaren da Adam din yake tunda ya fara maganar har ya dire ta. Shi da ya riga yasan duk wani motives din Adam din babu wani abu da zai yi ko ya yabe shi har yayi masa dadi tunda ya riga yasan karya yake yi, ba kuma wai har zuciyar sa yake ba, tsabar makirci ne. Yana jin Daddyn na jinjina masa bayan ya gama wayar amma yayi kum yaki cewa komai, shi dai burin sa kawai a isa gida ya samu ya zame dan ko cikin gidan baya son shiga musamman da yasan dukkan su zasu hadu waje daya dole Hajiya Zeenat zatayi wani abun da Daddyn zai iya ganin bakin sa, shiyasa baya taba yarda zama inuwa daya ta hadasu tun bayan da yayi wayo ya kara sanin ciwon kansa, ya gano irin bakin fentin da take goga masa a duk sanda ta ganshi tare da Daddyn.
Daga baya ya tsaya Adam ya dauki suitcase din Daddy yayi gaba, juyowa daddy yayi ganin yana tsaye yace

"Muje ciki." Babu yadda ya iya, haka yabi shi a baya har suka dangana da cikin gidan. Hajiya Zeenat na tsaye a falon cikin matukar ado ta sha kwalliya irin wadda take ciki a kowanne lokaci musamman idan Daddyn yana gari, da sauri ta karaso ta tare shi, ta jingina kad'an da jikin sa jikin farin ciki da murnar ganin sa.

"Sannu da hanya Your excellency."

"Sannun mu Hajiya, kuna lafiya?" Yace yana zama, tayi saurin zama a kubin sa ta lankwashe murya cikin kissa da kisisina ta shiga gaishe shi, hannun ta, ta kai saman kansa ta zare masa hular kansa.

"Wanka ko abinci Alhaji?"

Waigowa yayi yaga Aryan din a tsaye amma ya basu baya

"Muhammad."

"Na'am." Ya juyo suka hada ido da Hajiya Zeenat yayi saurin dauke kansa daga gallon ta, ya bawa daddy dukka attention dinsa

"Kaje kawai zan neme ka da daddare."

Da sauri yayi gaba dan dama jira yake yayi saurin hanyar fita, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, ta cigaba da shafa kan Daddyn zuwa gemun sa tana lankwasa jikinta cikin salon ta da tasan yana tafiya da Daddyn sosai.
Shi kadai yake ta jan tsaki har ya fice daga gidan a kafa dan be dauko mota ba, kuma baya bukatar daukar motar kowa a gidan duk da ga motocin nan amma shi a komai yafi son nasa, gidan sa ya nufa wanda ya kasance mallakin mahaifiyar sa, shine asalin gidan su da suka fara zama anan ne kuma duk wani tarihin rayuwar sa yake, anan yake samun nutsuwa sannan anan ne hankalin sa ya kan tashi idan har memory din abinda ya faru a baya zai dawo masa. Babu kowa a gidan dan ko haya be yarda ya saka ba, sai Baba Me gadi da iyalinsa da suke zaune a bq suna kuma kula da gidan har yanzu sosai. Baya kwana biyu be ziyarci gidan ba, anan yake duk wani shiri da tanadin sa anan kuma yake ajiye duk wani abu me muhimmanci a wajen sa. Knocking yayi a gate din sanda me napep ya sauke shi, Baba me gadi ya leko ganin shine yayi saurin bud'e masa kofar ya shigo.

"Sannu da zuwa."

"Sannu da aiki Baba."

"Yawwa, ban tsammaci zuwan ka a wannan lokacin ba, Allah yasa ba wani abu ne ya faru ba naganka a kafa."

"A ah ba komai, motar na office zan dan huta ne anjima sai na fita, Malam Rabi'u zai kawo motar anjima kad'an idan yazo ya ajiye ta kawai inaga zan dan samu bacci."

"Ok a fito lafiya." Yace masa, gaba yayi shi kuma ya koma bakin aikin sa cike da tausayin Aryan din.

A falon ya yada zango ya kwanta rigingine yana kallon saman pop din falon, shi kadai yasan abinda yake ji a zuciya da gangar jikin sa, da abinda yake masa yawo a cikin kwakwalwar sa, baya iya controlling fushin sa wanda yana cikin abubuwan da ke matukar takura shi, abu kad'an sai ya hau yayi ta kunci wanda yake sake kashe masa kwarin guiwar sa, sai dai a duk fushin da zai yi baya taba nadamar fushi akan cin amanar sa, baya kaunar cin amana haka kuma baya yafewa duk wanda yaci amanarsa, shiyasa har gobe ya kasa hakura da abinda sukayi masa, yake kuma kaffa kaffa da duk wanda yasan zai iya cutar dashi.

_Me Adam yake nema a wajen yarinyar nan?_

Abinda ya faru dazun ya fado masa, yayi tsai yana tunani ko zai iya gano wani abu,duk da yasan maitar Adam din akan mata amma kuma wannan karon yaga abu mabanbanci a tattare da kallon da Adam din yake mata. Toh amma menene nasa? Me yasa zai shiga tsakani?

_Saboda a karkashin office dinka take, shiyasa kayi hakan._

Zuciyar sa ta tuna masa dalilin sa

_Toh amma kuma idan itama ta amince da Adam din fa?_

Wata zuciyar daban ta sake tunasar dashi, tsaki yaja ya mike yana wurgi da pillow da yake kan kujerar yayi hanyar bedroom, ba zai taba yarda har wata shakuwa ta shiga tsakanin ta da Adam ba, idan kuma haka ne sai dai ta koma aiki a karkashin office din Adam din dan shi ba zai iya zama da duk wanda yake zaune inuwa daya da Adam din ba. Wannan dalilin shi ya bar wa kansa, da hakan ya samu bacci ya dauke shi, wanda be farka ba sai kusan karfe uku, a kasalance ya watsa ruwa hade da alwala yazo yayi sallah sannan ya dora kansa a gefen gadon cikin yanayin rashin karfin jiki. Ya dau kusan minti talatin a haka yana jin wayar sa tana neman agaji sai da ya ji tana neman takura shi sannan ya mike ya dauke ta a gefen bedside, ya duba call log din yaga kiran Ya Nabila ne sai Kamal wanda dama yasan a cikin su ne duk kiran da ake masan, be bi kiran ba sai da ya fara zuwa kitchen ya samar wa kansa shayi ya hado a cup ya dawo dakin ya zauna sannan ya bi kiran nasu.
Tare sukayi sallar la'asar da Baba maigadi sannan ya dawo ciki ya bud'e safe dinsa, in da yake ajiye duk wani muhimmin abun sa ya jawo takardun da ya saka a karshe ya sake duba su, suna dauke da sa hannun mutane hudu ne Wanda yake dauke da yarjejeniya da aka kulla ta cikin aminci da yarda da juna, wajen da Ammin sa ta saka hannu ya kurawa ido, a hankali kwalla ta biyo gefen idon sa, yayi saurin saka hannu ya share, sannan ya cigaba da nakaltar saka hannun da yake kusa da na Daddy.

*_Nasir Matawalle._*

Ya furta a chan kasan makoshin, yana nan yana jiran fitowar sa, duk da rashin bashi dama da yayi akan duk abubuwan da yaje masa da su amma ba zai taba gajiya ko karaya ba, zai jira shi har zuwa lokacin da zai gaji da nacin sa, ya bashi abinda ya dade yana jira. Sannan ya kai shi yaga mutane mafi soyuwa a gareshi idan ka cire Ammin sa da Ya Nabila.
Ajiye komai yayi ya rufe ya maida key din inda yake, sannan ya sauya shigar sa zuwa kananan kaya, ya bar gidan zuwa wajen Kamal da yake jiran sa a shoprite tun dazu.



*RUMBUN K'AYA*๐Ÿ”ฅ

*DAUDAR GORA*๐Ÿ”ฅ

*IDON NERA*๐Ÿ”ฅ

*A RUBUCE TAKE*๐Ÿ”ฅ

*KI KULANI*๐Ÿ”ฅ

*_uhmmmm_*๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š๐Ÿ˜Š

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*โ˜บ๏ธโ˜บ๏ธ

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

0022419171
Maryam sani
Access bank.

Shaidar biya tanan๐Ÿ‘‡๐Ÿป
09033181070

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*๐Ÿ”ฅ



RUMBUN QAYA*


Page 7

ยฉยฎ *_Hafsat Rano_*

ZAFAFA 2023๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ

____________

Tunda ta koma gida take tunanin abinda ya faru tsakanin Adam din da Oga Aryan, bata san dalilin sa na yi mata hakan ba, sai taga rashin dacewar abinda ya aikatawa Adam din, ita a ko da yaushe a mai zafin gaske take kallon sa, dan yanayin sa baki daya ya gama nuna hakan, bata son mutum da ya cika zafi sosai a koman sa, dan ita bata ga abinda akayi da har zai yi irin wannan acting din ba. Muskutawa tayi daga kwanciyar da tayi,kamshin turaren sa na cigaba da shigar mata hanci sosai, bata san yadda akayi kamshin ya manne mata haka ba, tashi tayi ta cire kayan ta watsa su laundry basket ta zura boubou, ta koma ta sake lafewa a gadon. Gida take son komawa, tana so ta ji ta jikin Dadan ta dan ita din me masifar son jiki ce, ko zama kayi kusa da ita sai ta ra'bi jikin ka tamkar mage. Har la'asar likis tana ta juye-juye kasancewar bata sallah, ga Amina bata gidan bata dawo daga school ba balle ta rage mata zaman kadaitar.
Bayan la'asar ta mike da k'yar, ta shiga toilet ta chanja pad ta gyara kanta sannan ta fito, tazo ta dau wayarta a saman mirror ta zauna kiran Babbo Sadeeq, shi kadai ne basu fiya waya sosai ba saboda duk ciki ya fisu commitment saboda yanayin aikin sa da baya bashi cikakken time, dama Hamma Hydar ne best friend dinta sannan Lamido. Tana fara ringing yayi rejecting tasan dama ba zai daga ba, haka suke mata basa taba daga wayarta sai dai su kirata, kiran ne ya shigo ta d'aga da yar murnar ta

"Babbo nah."

"Na'am, kanwata kina lafiya?"

"Lafiya Lou, sai missing dinku da nake Babbo."

"Shiyasa naji muryar ki haka?"

"A ah bana dan jin dadi ne."

"Me yake damun ki? Kinje asibiti? Kin sha magani?"

Duk a jere yayi mata tambayar cike da kilawa

"A ah, stress ne kawai kaina ne yake dan ciwo kad'an amma nasha magani ma."

"Ciwon kan nan wai ba zai hakura bane ba ya kyale ki? Ko dai zuwa zamuyi ayi scan din?"

"A ah da sauki, kwana biyu baya damuna sosai ma, ina shan magunguna na dukka, kawai ni gida nake son dawowa."

Murmushi yayi me sauti, kafin yace

"Ke fa kika dinga murna zaki tafi ki barmu, yanzu kuma?"

"Allah na gaji, boss din wajen aikin namu bashi da kirki ko kad'an, yayi ta shan kunu."

"Duk rashin kirkin sa dai kar ya yarda ya batawa kanwata, dan wallahi ranar Kano ba zata dauke mu ba, ki fada musu yayyanki maza ne kuma ke yar gwal ce baa taba ki, ba'a bata miki rai."

"Kaiii Babbo."

"I'm serious fa, gwara su sani, ba bautar k'asa ba ko bautar duniya ce ba zamu bari wani kato chan ya bata mana ran Princess ba."

"Su ma ba zasu fara ba ai."

"Yawwa better, yanzu dai nasan maganin boredom din nan da yake damun ki, zan sa miki wani abu kije ki dan yi shopping abinda kike bukata kinji?"

"Yaayy, you are the best Babbo, nagode Allah ya kara budi, ya kawo mata ta kari."

"Amin Amin, very soon in sha Allah, bari na koma aiki, sai anjima ki kula da kanki."

"In sha Allah, bye."

Da karfin ta, ta mike dan tuni karsashin ta ya dawo, duk halin da take ciki in dai tayi magana da daya daga cikin su toh in sha Allah sai sun san yadda zasuyi su faran ta mata, bata san yawan son da suke mata ba, dan tunda tayi wayo ta gane zasu iya komai da taba kowa akanta, ko dan ita kadai ce mace? Kuma karamar su? Kuma yanayin rayuwar da suke shiga? Ta fada mahaifiyar ta da karacin shekaru amma basu taba barin ta, tayi kukan rashi ba. Dadah kakarta ce wadda ta haifi mahaifiyar ta, amma ita take mata role din uwa da kuma role din kaka a lokaci daya,tana matukar kaunar su da dukkan rayuwar ta, domin sune Raihana, sune gatan ta, sune koman ta, zata bar duk wani abun da basa so bari na har abada, zata kuma so abinda suke so ko d hakan na nufin ajalinta.
Dawowar Amina ya kara sata warewa ta manta da komai, suka shiga hirar su irin ta daidai da shekarun su, har zuwa sanda kowa ya aje hakarkarin sa domin samun hutu daga kwarafniyar da aka sha na ranar.
Fresh ta tashi ta shirya a tsanake bayan sun gama ayyukan gidan, ba ta zuwa aiki yau dan haka ma tana yin breakfast ta koma gado ta kwanta Amina kuma ta tafi school, sai kusan sha biyu ta tashi shima kiran wayarta akayi ya sakata tashin ba wai dan taso ba. Miss called din Hajiya ZEENAT ta gani sai wata bakuwar special number da bata san ta waye ba, rabon da sukayi magana da Hajiya Zeenat din tun ranar da taje gidan karbar posting letter. Mikewa tayi da nufin zuwa toilet ta wanko fuskarta ta bi kiran sai ga kiran ya sake shigowa da wannan special number din, dagowa tayi dan duk a tunanin ta Hajiya Zeenatun ce, sai taji muryar wanda bata yi zato ko tsammani ba.

"Ina kika ajiye paper din da na baki jiya?"

Kawai abinda ya fara fada kenan ba gaisuwa ko sallama, yanayin yadda yayi maganar kamar wanda akayi wa dole yayi kiran, kafin ma ta bashi amsa ya sake watso mata tambayar cikin muryar sa da ta shiga ciki sosai ta shake.

"Nasa ta akan table sir, good afternoon."

"Ban ganta ba, dole ki dinga summiting komai idan kin san zaki yi fashi." Ya fada a hasale

"Ba fashi nayi ba sir, yau Thursday dama Sir Kamal yace Monday - Wednesday zan dinga zuwa."

"I'm waiting for you, kizo ki bani ita."

Ya kashe wayar, tsaye tayi da waya a hannu kamar wadda aka dasa, sha biyu har da yan mintuna be tashi cewa tazo ba sai yanzu? Wanne irin abu me wannan? Ranta ya sosu sosai, tayi kamar kar taje dan tafi minti goma a tsaye tana tunanin kin zuwa din kuma ta kashe wayar tunda abin nasa kamar hadda rainin wayo, da tasan ma irin sa zata samu a wajen da ta gwammace ta karbi teaching dinta ko a kauyan ne yafi mata sau dubu.
Tana shiryawa tana tsaki haka ta shirya ta fito ta samu Addah Maimuna a falo ta fada mata yadda sukayi, ta tayata jajantawa sosai dan yau ba karamar rana ake a gari ba, kuma sha biyu ranar ta kwalle sosai ace ka fito haka kawai ba tare da ka shiryi hakan ba. Ta dan sha wahalar samun napep dan suma idan azahar tayi sai kaga duk sun rage zirga-zirga, da k'yar ta samu wani shima a hanya ya sauke ta, ta taka a kafa har zuwa office din. A galabaice ta shiga ga yunwar da take ji a ranar da ta dake ta. Kai tsaye office din su ta fara zuwa ta dudduba ko ina bata ga takardar ba, ta tambayi Abdulhakeem shima ya tayata dubawa babu. Sai ta fito ta nufi office dinsa dan tasan dama ta kai masa dan tayi mamakin ma rashin ganin da yace be yi ba. Knocking tayi a kofar ta dan tsaya jim shiru, ta sake kwankwasawa sai ga Zainab ta taso, dama tana kallon ta tun shigowar ta

"Oga ya fita fa."

"Ya fita? Yanzu fa ya kirani yace nazo."

"Toh ya fita dai, sai ki jirashi."

Ta juya ta koma wajen zaman ta, ranta idan yayi dubu ya gama baci, bata san wulakanci a rayuwar ta wallahi, shi kuma taga alamun haka yake, kamar ma abinda yafi enjoying kenan a rayuwar sa, lallai dole Hajiya Zeenat ta shiga damuwa, dan zama da mutum da irin halin sa sai me tsananin hakuri. Office din su ta koma tana ta kunci, ta zauna bata sake kula kowa ba, ta ciro wayarta tana dannawa sai ga Oga Kamal ya shigo. Da mamaki yake kallon ta dan yasan yau ba ranar zuwan ta bace ba, zai yi magana ta riga shi

"Oga ne ya kira ni yace nazo wai be ga takardar da ya bani jiya ba."

"Aryan din?" Yace cike da tsananin mamaki

"Eh." Ta gid'a kanta

"Abun da mamaki, takardar fa tana wajena na bashi dazu, sai dai ko kafin na bashi ya kira kin kenan, maimakon kuma ya sake kira yace ki zauna ya ganta."

"Hmm." Tace kawai

"Shikenan tunda kinzo ma, zo na nuna miki wani waje"

Tashi tayi tabi bayan shi, zuwa wata kofa da take kallon office dinsu, bud'e kofar yayi da key suka shiga ciki, ga mamakin ta sai taga kitchen din madaidaici, dauke da coffee machine, microwave da sauran kayan kitchen dangin su cups da spoon, yar madaidaiciyar kettle me dauke da kananan cups irin ta su Hamman ta ce ta ja hankalin ta, ta matsa wajen ta dauka tana kallo

"Waye yake shan irin shayin nan."

"Mune nan, ni da Aryan, dalilin ma dai samar da kitchen din kenan, dan gwara ni ma, Aryan baya wasa da shayin nan, ya zamar masa addiction wallahi."

"Kamar su Hamma na,suma kullum cikin sha suke, tun ban iya ba har na koya dafa musu, nima kuma na koyi sha."

"Kin iya dagawa?" Yace cike da murna dan dama suna tunanin yadda za'a yi

"Na iya sosai, har majlisa suke kaiwa ayi tasha wallahi."

"Shikenan wallahi, dama muna neman me dafa mana yadda aikin zai dinga tafiya sosai, ta kwana gidan sauki."

"Amma sai dai na dafa maka kai kadai, banda shi."

Ta bata fuska kad'an ita a lallai haushin Aryan take ji, dama kuma ita bata iya rufa rufa ba, idan ka bata mata sai ta nuna amma bata da riko ko tsananin fushi

"Tuba muke, ai yanzu dole muyi miki biyayya, shima ba zai kara ba."

"Allah ko abinci banci ba, daga bacci na tashi kawai naga kira wai nazo, dama ya fada min da ya ganta, amma haka na dauko kafa ga rana wallahi kamar zan narke."

"It's not hygienic ko zauna a kitchen kuna gulmata."

Kofar dama a bud'e take shiyasa ma basu ji shigowar sa ba sam, kusan subucewa kofin yayi daga hannun ta dan bata zata zai shigo a time din ba, kuma bata ma san dalilin da yasa ta ke fadawa Kamal din ba, ko dan taga kamar ya sake da ita kuma yana kokarin jan ta jiki? Ji tayi kamar Hamma Haydar take fadawa wallahi shaf ta manta ma da waye shi da alakar sa da wanda take masa maganar tasa.

"Ba gulma bace ba, gaskiya ce ai Aryan, da sai ka kira kace ta zauna kawai."

"Menene yayi saura da ba'a saka ba?"

Ya share maganar ya sako tambayar,

"Komai an saka, har kuma an samu wadda zata kula da bangaren."

"Wace? Kasan dai i don't trust anyone."

"Raihana ce."

"Who?" Yace kamar be gane wacce yake nufi ba

"Gata nan a gaban ka."

"No, a samu wata dai.."

"Why?"

"We will talk about that later."

"Raihana please ki jirani a office ina zuwa."

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment