Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aranta da sauri ta kutsa kai tafito daga dance floor din tabi hanyar dataga Hamidan tabi tana kalle kalle har itama takai gaban jirgin amma bata ganta ba, babu ma alamunta awajen da sauri tace "to ina taje" sosai taji tanajin wani iri a zuciyarta tashiga wani irin damuwa hakan yasa ta juyo ahankali tana tafiya tana tunani, yar budurwa da saurayinta data gani a wajen takarasa wajensu tana murmushi kafin ma tai magana saurayin yace "cute girl wakike nema anan ki koma ciki karki fada ruwa, small girl doesn't suppose to be here" murmushi tamai tace "please Uncle have you seen my sister Anty Hamida anan?" da sauri dagashi har budurwanshi sukace no, hakan yasa tajuya tana magana ita kadai tace "to a ina kikaje kika boye Anty Hamida?" komawa hall din tayi but still she's not herself karasawa wajen Zainab dake rawa abinta tayi tarike hanun Zainab da sauri Zainab ta kalleta, ganin idanunta sun cika da kwalla yasa ta duko dakai cikin daga murya dan karan waka yay yawa tace "Ihsan leave me alone, if you are hungry dau plate ga wajen abinci chan serve ur self ne babu mai hanaki, kici duk abinda kikeso, am having fun please karki daman da rigiman ki auta pls" sakinta Ihsan tayi cikin fushi tai gaban hall din chan inda Ayush ke zaune da handsome mijinta agefenta sunyi kyau sosai, tana ganin Ihsan suka mata murmushi da sauri ta karasa wajen kaman zata fashe da sauri Ayush tarike mata hannu tace "menene auta?" hawaye ne ya gangaro daga idanunta tace "banga Anty Hamida ba nabi inda tayi banganta ba" dan shiru Ayush tayi tana kallonta hakan yasa mijin Ayush yadan duko dakanshi yace "menene Baby" ahankali tace "wai bataga Hamida ba" shiru yayi saikuma yace "bari nasa a bincikata" ya kalli Ihsan din dake share hawaye yay murmushi yace "cry cry Auta, bari nasa anemo miki ita tunda you are missing her dama gashi kunfi kama" yana maganan ya juyar dakai yama wani abokinshi dake sanye da kayan security alamu da hannu yazo yana zuwa yace "Man please ga Ihsan anemo mata Hamida duk inda, am sure ta buya a jirgin nan ne somewhere just help her find her" ya kalli Ihsan yace "follow him kinuna mai Hamidan inkin ganta" washemai baki tayi tabishi da sauri suka fita daga wurin tanamai surutu tace "Uncle dukna duba saman nan bata, muje kasane" murmushi yamata dan d girl is so cute yace "okay fine girl muje" kasa sukayi dan duba dakunan dake kasan.....



Wani irin tumble tayi ta shige chan cikin ruwan takai kafin wani wave mai karfi na ruwa yay sweeping dinta with force gaba dawani irin mugun gudu, sanan ruwan yawani irin wuntsulota sama kanta yafito space wani irin nishi tayi tana daga wuya. "iy..yyuuu" tabude baki tana wuntsila kafa da hannu sama tana juye juye tana kokarin bude idanuwanta da ruwa duk suka shiga, da kyar ta bude idanun tana juye juye amma bata hango jirgingu ba tadai ganta a tsakiyan ruwa, gaba ruwa baya ruwa, gefe ruwa ko ina ruwa, gashi sai kasa kasa take kaman ruwan najanta ciki ta nitse, ruwan har habanta, da kyar cikin tsananin tashin hankali gwanin ban tausayi tace "Ma...m" wani irin wave na ruwa yakara zuwa kaman ana aikoshi yahau kanta yay sweeping nata away with force fiye da nada gabaki daya kawai tasadakar ta mutu dan tama kasa bude ido tana kokarin bude baki danta iya numfashi ruwa na shigan bakinta ga ruwan so salty, gawani irin ruwa dake shiga hancinta da kunnuwanta taji kanta yay dumm, yanda take kasa kasa kasa tana bubbuga kafa tana fighting da ruwan dataji gabaki daya yawani irin matseta ya shaketa ya murdeta sosai kaman an kulleta da chain yasa fishes din ruwan duk suka rude suna neman wurin guduwa......



_Elagushi Beach Lagos_

Zaune yake agaban Beach yana kallon ruwa, he's d sunset type, there's something about sunset that gives him goosebumps, tun yana yaro when ever he's outside d yamma he always stare at the sun idan yana faduwa, saisa yau ya shigo beach da yamma just to have fun and watch the sun set.
Sanye yake da summer beach pant dayadan wucemai cinya kadan ya dameshi yabi kakkauran cinyarshi, jikinshi ba riga sai fadaddan huge full kirjinshi irin na maza masu work out, idanunshi sanye da ocean cabaretti sunglasses daya wani irin fitar da dogon hancinshi kaman karas, ga wani round black tabon salla agoshin shi daya karama fuskarshi kyau sosai, gashin kanshi dakeda dan yawa jike yake da ruwa dan ruwan ma diddiga yake yanabin gefen fuskarshi alamun daga cikin ruwan yake hanunshi rike da abinda akafi sani a beach da Aqua de coco (danyen kwakwa da aka fere saman akasa straw aciki) ahankali yake sipping coconut water har lokacin yana kallon beach din cool breeze da feshin ruwa na fesomai.

Ahankali take tafiya sanye da bikini pink tadaura beach hat akan long kitson attachment din dake kanta, tana tafiya ahankali cike da rangwada babu takalmi akafa kafafunta na nitsewa cikin lallausar kasar Beach din, hanunta tana rike da nata Aqua de coco tana sipping kadan kadan ta karaso inda guy din yake zaune, fadawa kanshi tayi ta daura kan akan kafadarshi kaman zatai kuka cikin harshen turenci tace "auch Aabid my feets are aching" shiru yayi kaman baijitaba ya cigaba da sipping aqua de coco shi yana kallon ruwan, ahankali ta sakeshi ta tankwashe kafa ta cigaba da sipping nata saikuma ta ajiye ta sake kallonshi tana turo baki takai yatsanta dake sanye da dogon kumba irin na arna tace "talk to me love, I have a shoot today but I abondon it just for you Aabid" ganin ko kallonta baiyiba yasa ta ijiye kwakwan nata a gefe ta tashi ta zagayo ta gabanshi ta shiga ruwan bayanta yabi da kallo tsugunnawa tayi ta dibi ruwan ta watsamai tana murmushi tace "you must talk, say something Aabid, say something, you must talk" takara watsamai ruwan a kirji, dan murmushi yayi daya bayyanar da cute one sided dimple dinshi daidai lokacin wani ma'aikacin beach din yazo yadan dukkar dakai alamun respect yace "sir your sport water bike is ready" dawani irin murya chan kasan makoshi kaman anyi forcing dinshi yay magana yace "okay u can go" ya juyar dakai yana kallon bike din dake cikin ruwan da aka daure igiya a jikin wani karfe awater front din gudun karya gudu, ajiye aqua de coco yayi yamike tsaye da sauri tafito daga ruwan tabiyoshi da gudu takama hanunshi tace "am going too Aabid let's water dive together since d bike has two seat" dan juyo dakai yayi ya kalleta da baki yanuna mata yaron beach din akasalance yace "then get a life vest jacket, I don't want you to die before your time" dariya tayi tamai kiss a hanunshi tana wani irin kallon shi cike da so tace "so you care for me" tai maganan tana kallon fuskarshi ganin bai kalleta ba yasa tasaki hanunshi ahankali tajuya da sauri taje wajen yaron beach din karban jacket shikuma yay wurin bike din, there's nothing dat gives him more fun koyana nigeria koyana outside inhar yana beach shine riding bike a ruwa, dan tsaki yayi dan beach din Lagos dinma is not as blue as he wants it to be, is too local for his liking, shiga ruwan yayi harya kaima gwuiwa kana ganinshi kaga wanda ya kware da ruwa sanna yahau kan bike din yajuyo yana kallon Vanessa that's coming towards him tanasa life jacket din data karbo akan dan pininin pant da bra na beach dake jikinta bikini, tana gyara beach hat dake kanta, ruwan itama ta shiga tace "yayy am so excited Aabid this ride is gonna be mad fun right baby" gyada mata kai yayi da sauri ta dane ta rungumeshi ta baya ta daura hanunta akan cikinshi tanaji kaman ta cinyeshi dan so, dan yatsine fuska yayi yadan duko yamika hannu yacire igiyan daga bike din ya kunna bike din dawani irin jarababben gudu yana awizo yaja bike din sukai cikin ruwan wave yawani irin dagasu ihu tayi sosai tana kara kankameshi tace "please Aabid we shouldn't go far okay, am a lil bit scared" cikin husky voice yace "and you shouldn't have followed me, just keep quiet and enjoy d free ride am giving you" kiss tamai abaya cike da murna takara kankameshi tace "I feel honored Mr Cute, sharing a ride with you is a privilege, no is an achievement" kara lankwashe murya tayi breeze din ruwan na neman fadin da hat din kanta tace "am so happy you choose me acikin all d hot hot celebrities damukeda shi a nigeria, thank you handsome" lashe pink lips dinshi yayi yawani irin yin awizo da machine din ruwa ya feso musu a fuska ihu tayi ta kankameshi tace "am having maddd fun, I love you Aabid" tai maganan tana juyawa daidai lokaci ta hango kafar mutum da sauri ta bubbuga bayanshi tana pointing da hannu tace "Aabid look is that a marmaid leg? A think is a marmaid Aabid let's leave here" batare daya kalleta ba yadanyi murmushin iskanci yace "they're no marmaid in Nigeria gurl" ahankali ruwan yadan wurgota sama kadan hakan yasa ta hango fuskan mace, ihu tayi sosai tace "Jesus christ Aabid look is human being, look I think is a girl, Jesus I hope she's not dead ewooo olorun!" da sauri yadan juyo da kanshi yace "stop enchanting rubbish on my ear" ya yatsine fuska, da sauri ta rikemai kafada tace "look Aabid am serious" ahankali cikin tsananin gajiya da ita ya kalli inda take nunamai fuskan mutum ya hango kadan saikuma wave din ruwa yazo yahau kanta hakan yasa ta niste cikin ruwan, ihu Vanessa takara yi tace "how are we going to save her now Aabid, am not with my phone we suppose to alert the beach authority, are you with your phone Aabi...?" bata gama kiran sunanshi ba ya kashe bike din yawani irin mikar da hanunshi up ya hadasu yay wani irin jumping daga bike din yafada cikin ruwan straight takai ya shige chan kasan ruwan shima hangota yayi ta bude hannu sideways jelan gashin kanta sun mike sun kwanta a ruwan suma tana kasa, kasa, kasa, idanunta a kulle bata numfashi ko kadan, wani irin sauri yayi yana numfashi da baki yana fito da ruwan waje yana swimming kaman fish kafin yakaraso wajen, ahankali ya tsaya ya bude hannayenshi yana wani irin kallon fuskarta tacikin glasses din dake kan idanunshi yanajin wani irin abu da tunda yake in his life betaba jiba, ahankali ya jata da hanun damanshi yahadata da jikinshi ya daura fuskarta akan kirjinshi ya kife fuskar yay sama ya mikar da hanunshi daya sama yana yin kafarshi kaman kifi yay saman ruwan kanshi yafara fitowa kadan saman ruwan, Vanessa dake kan machine gabanta na faduwa sosai sabida tsoro tana hango kanshi nesa da bike dinsu sosai tai ihu tace "thank you Jesus" da sauri ta kwalamai kira. "Aabiddd am right here love" wani irin ciro Hamidan yayi daga cikin ruwan ya daurata akan kafadarshi yana komar da ruwan baya da hannunshi daya yana yin wajen bike din da sauri, tashi yayi daga ruwan yahayo kan bike din da ita Vanessa na kallon fuskarta, zaro ido tayi tace "Jesus she's beautiful Aabid are you sure she's not a marmaid?" kunna bike din yayi yana gyaramata zama a kirjinshi yaja bike din dawani irin fitinannen gudu kirjinshi na bugawa fast fast, ko 1min bai daukesu ba tsabagen shegen gudun dayake yi yakaisu gaban ruwan da sauri ya kashe bike din baima damu da kar ruwa yatafi da bike dinba ya diro daga kai rike da ita da sauri Vanessa ta sauko itama ta biyo bayanshi ahankali ya shimfideta akasa yana kallon fuskarta daidai lokacin Vanessa ta karaso dan dago kai yayi ya kalleta tareda jan glasses din idanunshi sama cikin husky voice dinshi yace "get d medic" da sauri tace "o..okay handsome" tabar wajen dagudu, ahankali ya juyo da kanshi ya daura cool brown eyes dinshi akanta, ahankali yay placing hanunshi akan cikinta dayay dan kato sabida ruwa yay pressing gently yana kallon fuskarta, sau uku yana pressing cikinta ganin ba response yasa ya bude bakinta yanadan kallon fuskarta, ahankali yana kallon fuskarta ya daura bakinshi akan nata da sauri ya lumshe ido, ahankali ya hura mata iskan bakinshi cikin nata bakin kafin yadago kanshi ya maida hanun kan cikinta yy pressing but no response, hanunta ya kama yana murza palm dinta sosai sabida yay warming nata yana kallon fuskarta feeling somewhat awkward ahankali yace "hey Jewel, stay with me okay" da sauri ya saki hanun nata yakara dukawa ya daura bakinshi kan nata yasa mata iska sosai this time kafin yakoma adan rude yafara danna cikinta yana kallon fuskarta yace "fight, Jewel don't go just like that precious, stay with me okay".
_🌹IN BANI 🌹_





_M. Shakur_


6......

Sake danna cikinta yayi da karfi da duka hannayenshi yana kallon fuskarta cikeda damuwa yace "please Jewel" yay maganan yana sake pressing cikin wani irin nishi tayi tawani bangaro jikinta na rawa sosai ruwa na fitowa ta bakinta da hancinta da sauri ya dagata ya daura kanta kan kafadarshi yana bubbuga bayanta yana kallon yanda ruwa ke fita ta bakinta da hancinta ahankali yace "sorry" sosai take aman ruwa tana wani irin mikewa ahankali yake bubbuga bayanta yadaga kai da sauri yaga Vanessa na karasowa wajen da sauri ita kadai hakan yasa yaja gajeren tsaki ya mayar da kanshi ya kalle fuskarta jintai shiru kuma, ganin ta kara suma yasa da sauri ya dagata kaman wata yar baby yafara tafiya da sauri, adan rude Vanessa tabishi da sauri itama tace "Aabid where are you taking her?" batare daya kalleta still idanunshi akanta yana kallon fuskarta yace "hospital" da sauri tana kokarin cimmishi kafafunta na shigewa kasan Beach din tace "but d medic are coming, they're looking for first aid box" batare daya kalleta ba yana kara saurin tafiyanshi yace "I can't wait for them" daidai lokacin yafito parking lot, bude babban jeep dinshi yayi Brabus da hannu daya ahankali ya kwantar da ita a back sit yaja jacket dinshi black na Gucci ya rufamata in order to keep her warm, sanan yaja dayan plain white shirt dinshi dake jikin hanger anan bayan motan ya saka baimabi takan rufe boturan riganba ya rufe kofan yabude gaba ya shiga ya zauna a mazaunin driver, da sauri Vanessa data karasa saka dan half kimono ta tana daure igiyan gaban ta zagayo ta shiga dayan bangaren tana rufo kofar tana gyara zama tana kallonshi dan cije lips dinshi yayi ya waigo yasake kallonta sanan ya maida kanshi kan wajen key yatada motar, da gudu yabar wajen, da sauri tace "handsome where are we taking her to? Where are we going with her? We don't know her, don't you see she don't look like a human, she looks like a marmaid u know that's how they use to be very fine and beautiful" wani matsiyacin kallo ya watsa mata kafin yamika hannu ya kunna waka a motan na drake yanabi yana wani irin dan iskan gudu harsuka kai wani private hospital mai suna safeguard hospital, parking yayi yafito yabude baya da sauri ya yaye jacket din daya rufamata ya dauketa ya shiga ciki da ita da sauri aka karbeta daga hanunshi a reception din aka kwantar da ita akan gado, bin fuskarta yay da kallo ya tsaya awurin yana kulle boturan riganshi, daidai lokacin Vanessa ta karaso tazo inda yake ta tsaya kaman zata shige jikinshi hanunshi ta rike tashafa soft kumatun shi ahankali tana kallon fuskarshi tace "let's go home baby since we've brought her to the hospital" kallonta yayi kafin ya janye hanunta daga fuskarshi yabi bayan Dr din dayaga suna shigar da ita wani daki, binsu yay cikin dakin yana kallon oxygen din dayaga ana kokarin yimata fixing a hanci da sauri Dr yajuyo ya kalleshi yay dan murmushi yace "don't worry young man, she will be fine, she need oxygen ne sabida state of her lungs right now but for now excuse us let do our work please Sir" fuskarta yakara kallo kafin ahankali ya juyo yafito daga dakin, wata nurse ne tabiyoshi da folder da kuma takardan bill, bill din tafara mikamai ya karba sanan tace "Sir wats her name? And how old is she?" kallon nurse din yayi da shanyayyun idanunshi masu kama dana mijin bacci ahankali yace "name Jewel, age 19 or 20" da sauri tace "okay okay, is all we need for now, then the bill sir, we need to get the things now" tashi yayi yace "1min" fita yayi danba kudi ajikinshi mota yaje ya bude yadau wallet dinshi ya bude most of kudin dake cikima are US dollars Nigeria naira daya gareshi which is a 1000 note, tsaki yayi dan bai chanza kudin ba tunda ya shigo ba, hakan yasa yaciro ATM card dinshi na first bank ya rufe motan ya shiga cikin hospital din da POS yabiya kudin sanan ya kalli nurse din daketa kallonshi yace "take care of her please, zanje gida I wanna shower and change, will be right back" murmushi tamai tana washemai baki dan guy din can speak, his accent kaman nadan amurka tace "okay Sir I will do dat for you" dauke kai yayi yana kallon Vanessa yace "gud" dagama Vanessa data cika tai fam da gira yayi yace "are we safe gurl?" yay maganan yana hanyar fita daga reception din yana taku daidai, binshi tayi da kallo in life halin Aabid na kasheta, tana bala'in son this his C² character, the guy's coded and classic hali na bala'in burgeta, baka taba gane halinshi komin dadewan dakayi dashi, dan juyowa yayi ya kalleta hakan yasa ta tashi da sauri ta biyoshi tana murmushi tana turomai baki.

Koda tafita wajen harya shiga mota yatada ahankali tabude dayan side din itama ta shiga itama ta zauna yadan juyo ya kalleta murmushi yay kadan yana kallon fuskarta yace "cool down" da sauri ta kama dayan hanunshi tamai kiss tana murmushi tace "I love you Aabid please stop ignoring me okay" dan murmushi yamata yana kallon kwayar idanunta kafin yamata alamu da ido data sakeshi, murmushi tasake yi tasakemai kiss a hanun sanan ta sakeshi ahankali tana murmushi, kunna motar yayi yanadan fuzar da iska yaja motar sukabar asibitin, Victoria garden city VGC yawuce, gaban wani babban hadadden gida yay horn gateman yabudemai ya shiga yay parking motar, hadadden compound ne mai fadi sosai flowers ko ina, fitowa yayi yay ciki batare daya jirataba ya bude kofa ya shiga, falone babba da akai komi off white, dakin yahadu sosai da sauri yakarasa wajen fridge ya bude yadau bottle water na Eva, budewa yayi yasha yana kallonta daidai lokacin ta shigo sai kumbure kumbure take, shareta yayi ya ijiye goran ruwan kan saman fridge yahau stairs yy sama yabude wani daki ya shiga, shima dakin komi off white da akamai sirki da sky blue, dakin yay kyau fiye da misali kaman aturai, jefa wayarshi kirar iPhone 11 yay kan makeken gadon dayaci farin duvet, ahankali yakai hanunshi yanadan lumshe ido alamun gajiya kan boturin rigan shi yay unbutton shirt nashi ya cire yayar nan kasa, yaja summer beach pant din shima kasa sanan ya tsallake kayan ya wuce yana tafiya ahankali yabude bathroom ya shiga.
_🌹IN BANI🌹_



_M. Shakur_

7....

Ruwa yahada mai dan zafi a bathtub da kyar sabida gajiya ya zuba shower gel nanda nan bayin ya cika dawani irin mugun kamshi ya shiga ciki ruwan ya lumshe ido yanadan tunani, yakai kusan 5min ahaka Vanessa tai knocking kofar rike da wayarshi dake ta haske murya chan kasa tace "handsome your phone is ringing" dan yatsine fuska yayi cikin kasalalliyar murya yace "who is calling?" kallon screen din tayi ganin Dil❤ da emoji heart yasa tace "is Dil" wani irin murmushi yayi daya bayyana set din white hakoran shi yace "rascal keep d phone, I will call him back" murmushi tayi tace "okay love" maida wayar tayi ta ijiye kan bed din, fita tayi daga dakin ta shiga d next room inda yar akwatin LV dinta yake, wanka tayi itama tasa wani hadadden red lingerie tafesa turare tafito daga dakin sanye da white bathroom slippers tabude kofan dakinshi ta shigo tana kallonshi yana tsaye gaban mirror sanye da bathrobe yana kokarin shafa cream, kallo daya yamata ta mirror ya dauke kai, ahankali ta maida kofan tarufe tana wani irin cat working takaraso gaban mirror ta baya ta rungumeshi dudda yafita tsawo sosai abayanshi ta daura kanta tana shafa kirjinshi da hands dinta asaman kirjinshi dakeda gashi ta saukar da hannun dawani irin bedroom voice tace "Handsome lemme help u with the cream, why am I here if am gonna let you do things yourself" tai maganan tanajan hannayen daga chest dinshi zuwa kan navel dinshi, wani irin ajiyan zuciya ya sauke yana kallon kanshi ta mirror, dan murmushi tayi tawani irin zagayo ta gabanshi tahau gaban mirror ta zagaye kafafunta ta bayanshi tana murmushi tana kallon fuskarshi, shima kallonta yake da idanunshi dasuka chanza kala, ahankali takai hanunta kan pink lips dinshi tana shafawa gently tana wani irin kallonshi tace "you are so cute Aabid, I love your skin, your skin is so soft, I love your ebony skin is so sexy" ahankali ta janye hanun nata daga kan lips dinshi ta janyo cream din ta debo a hanunta tana mutsitsikawa tana kallon fuskarshi, gently ta daura hannayen nata akan kirjinshi tafara shafamai mai tana sauka kasa kasa har ta sauka kan V-lines dinshi dan lumshe ido yayi yana cije lips, yanda taga yayi yabata more access na fadin abinda takeso tace, fuskarta takai saitin kumatunshi tana shafawa, cikin low voice tace "Handsome I wanna feel you, am tired of romance, romance romance, let's have s*x, make me pregnant plss, I wanna be pregnant for a handsome young milloniare like you Aabid, make me your baby mama plss" tai maganan while grabbing his thing gently, da sauri yabude ido yatureta tai baya, dawani irin sauri ya shiga bayi, yakai kusan 10min kafin yafito yana goge jiki ko kallon inda take baiyiba ya shirya cikin wasu hadadun Jean da riga black and white ya feshe jikinshi da hadadun turare, bakaramin kyau yayiba yadau key mota daga gaban mirror yawuce yafita ya sauka kasa, wajen mota ya karasa ya bude motan ya shiga yaja motar yafita, masallaci yafara shiga yay salla sanan ya fito ya shiga KFC take away yay sanan yafito ya shiga mota yaja motar zuwa asibitin, parking yayi a haraban asibitin yafito yana kallon ko'ina yadau take away yarufe motar ya juya ya shiga cikin asibitin yana taku dai dai yakarasa ciki, da sauri nurse din dazu dake zaune kan kujera ta taso tana washemai baki tace "welcome Sir lemme take you to her room, amma gaskiya Sir your patient tasha ruwa sosai, kaga ruwan da aka cire daga jikinta kuwa" tsayawa yayi chak ya kalleta, murmushi tasake mai tace "don't worry she's fine, we manage to save her, mun fitar da duka ruwan datasha, yanzu bacci takeyi bama ta tashiba har yanzu but am sure any moment from now zata tashi" cigaba da tafiya sukayi tabude mai kofan dakin da aka kwantar da ita ta shiga ciki bayanta yabi yana kallon gadon tana kwance kan gado ansa mata kayan asibiti an kunna warmer adakin, dakin yay dumi sosai, maida kofar yayi yarufe har lokacin idanunshi akanta ya tsaya awurin tare da folding hanunshi a kirji yana kallonta, dauko wani magani nurse din tayi tazo inda yake tsaye tace "Sir maganin nan once ta tashi kabata 5ml" gyada mata kai yayi takoma ta ijiye maganin tadawo tace "if you need anything from me Sir just ring that alarm" ta nunamai wani jan button, gyadamata kai yayi batare dayay magana ba ya matsa gefe tabude kofa tafice, ahankali ya tsaya a wurin yana kallon fuskarta, tai wani irin haske looking innocent, gashin gaban goshinta ya kwanta sosai tana fitar da

Please Login or Register in order to submit comment