Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauri ya kalleta cikin fushi yace "auch waike old lady nan me haka kike dukana agaban yara" kaman Kaka zatai kuka ta nuna kanta tace "kafara kirana da wanan yaren yahudancin ko Faruku, to wlh bari ubanku yadawo saina fadamai cin mutunci dakuke shigowa har Sasa na kukemin, ku tashi kufita, kutashi kufita nace, kuma bani ruwan gorana saurayin Zainaba ya kawomin su kusan katan biyar, bani" tafada bacin rai tana mika hannu zata karbi ruwan, tsaki yayi yadaura kafa daya kan daya yanashan ruwan shi ahankali Kaka tasaki baki tana kallonshi tace "ai shikenan kasha wuta shege dan buhun uba" fashewa da dariya Hamida tayi dayasa Faruk saukar da ruwan daga bakinshi ya watsa mata wani mugun kallo da sauri ta tashi tafita daga dakin da gudunta yabita da kallo, hararan kofan Kaka tayi tace "ja'irar yarinya, ai wlh Faruk banso kaje ka daukota ba, so nayi jiya da Sama'ila nama maganan kace aiki zaka, baga tanan ba rass bataima kama da wacce tafada ruwaba" juyowa Kaka tayi ta kalleshi daidai ya ijiye ruwan akasa tace "kaje wurin Maman kane yau?" girgiza mata kai yayi yana yatsine fuska, yace "sai anjima da yamma yanzu aiki zan tafi" washemai baki tayi tana kara matsowa kusa dashi tana murmushi tace "Faruku na wai har yanzu ba'ayi albashin bane, kamin alkawarin dubu ashirin fa" hararanta yayi yace "jiya agabana Abba yabaki dubu talatin wai mekike yi da kudi ne haka?" sake matsowa kusada shi tayi kaman zatai gulma tace "na rantse maka Faruku adashi nakeyi, tara kudin bikin Hamida nake" wani irin kallo yamata yace "wace Hamidan?" baki tabude tace "kagamin iskanci munada wata Hamida agidan nanne bayan wanan hamidan data fita daga dakina yanzu?" cikin daure fuska yace "yaushe tai saurayi?" sake matsowa tayi kusa dashi kaman wacce ke shirin yin gulma tace "a'a kaima dai kasan ko mashinshini Hamida batadashi ko, amma so nake kabani kudin dukna hada naita zubin adashi ina tari, inama bikin ta tari, kasan Hamida yar wajena ce, itace mai sunana fa, kaga shegen fadan nan danake mata wlh sonake ta chanza ne dan batayi gadon halina ba, bataci sunana da aka bataba, amma dazaran ta chanza zamu zo mu fara shiri sosai, nama tuna bari naje sasan su hado kayanta zatayi tadawo shashin nan ma yau dinan" shiru tayi tana nazarin yanayin fuskanshi yanda yay kini kini darai, tace "kaikuma lafiyan ka naga kai wani iri" yatsine fuska yayi yace "am fine" ya mike tsaye yana gyara kayan jikinshi yace "natafi aiki" tashi tayi tace "muje na rakaka, kadan tahomin dayar bakan leda kaji inzaka dawo, tunda su Zainaba da Ayush sukabar gidan da yunwa nake kwana Faruku" hararanta yayi yanaji kaman ya bugeta kiri Kiri sai Kaka tabude ido tana karya, dariya tayi sosai ganin yanda yake kallonta tace "bawai yunwan abinci ba na kayan kwadayi, idan kadawo kaza bani kudin aiko? Bazanyi barci ba zan jiraka" hararanta yayi yajuya zai fita hanunshi da damke tace "dan ubanka saika bani danma ina lallabaka" kaman zaiyi kuka ya kalli yanda ta damke well ironed uniform dinshi yace "naji inna dawo zanbaki, ki saken to" sakinshi tayi tana dariya ta dungure mai kai tace "ja'iri barima ubanku yadawo yau zan mishi maganan aurenka ne, wlh koka fito da mata kona je kauye nahadaka dayar aminiyata Iyami" tsaki yayi tsabagen takaici baima tsaya yabata amsaba yawuce yafita daga sasan da sauri tabi bayanshi amma har yay wajen gate hakan yasa tai tsaki ta wuce part din su Hamida.

Da sallama ta shiga falon su Hamida tagani zaune a falon tanacin indomie data dafa da boiled egg tana kallon zee world tana ganin Kaka tai murmushi tana sunnar dakai, hararanta Kaka tayi tace "aikin kenan ki zauna ke kadai awuri babu kowa shine burinki a duniya miskilan banza, ni ina mamarki?" daidai lokacin Mama tafito daga kitchen rike da tray data debo wake dan gyarawa zatayi tana ganin Kaka tai murmushi tace "yau Umma a shashin mu" da sauri Kaka tace "eh nazo ne, kihada ma yarki kaya sasana zata dawo" turo baki Hamida tayi tana tauna abincin dake bakinta ahankali Kaka ta kalleta tace "ahap ai saidai ki mutu ingayamiki yarinya, yaushe zasu koma ma makarantan yama sunan hutun da sukaje?" murmushi Mama tayi tana karasa shigowa cikin falon tace "mid semester break" da sauri Kaka tace "yauwa shi yaushe zaku koma ke?" tai maganan tana kallon Hamidan dakecin abincinta, dan turo baki tayi tace "ranan Monday" kwafa Kaka tayi tace "saura wanan karan ma ki kwaso zero zero a makarantan kaman na wanchan karan, wlh cema Sama'ila zanyi bazai kara kashemiki koda sule biyar a makarantan ba, aure zamu miki, inyaki kuma nida kaina zan aurar dake" da sauri ta kalli Kaka, gyada mata kai tayi tace "eh kinjini da kyau, wlh aure zansa amiki inhar wanan karan ma kin fadi kaman wanchan tunda kedai bazaki saki ranki ki jona mutane kikoyi abuba, ba nannan zainaba ke zuwa makaranta karatu ba banda ke, malami na koya muku abu kina kakkare fuska kikasa kallon allo, yoto menene amfani Sama'ila yay ta bata kudi akanki har shekara hudu? Kema kinsan naso keda Zainab da Ayush dakuna gama sakandire a aurar daku amma kuma sainazo na hakura da Sama'ila ya nunamin yanaso kuyi karatu amma kam wanan karan bala'i zanyi dashi dan wlh bazan bari dan kudin dayake samu a saida kaji, saida kajifa jama'a yazo yana batasu akanki ba, dan asarace, da'ace nine yabama uban kudaden danasan menayi dashi kuma Allah kaimu mondan, ni nan dakaina zan kaiki har Bayeron incema malamin ku wlh yazane min ke tunda dai kinki maida hankali kiyi karatu" tai shiru tana kallon Hamidan data daura hannu a fuska tana share hawaye, tsaki tayi ta kalli Mama data zauna kan kujera tafara gyaran wakenta ita yanzu bala'in Kaka baya damunta dan tsufa ce yamata yawa, cikin masifa tace "ai cewa nayi kibar gyaran waken nan kitasa keyanta taje dakinsu ta ciro kayanta daga sip dinsu, na Zainab da Ihsan kawai zaku bari a sip din ta tattaro tadawo Sasa na, nariga na share dakin dazan bata tastas, Allah kuma yakaimu Monday zakiga nizan kaiki makarantan na rantse miki saina sa malamin ajinku yamiki bulala goma hala hakan zaisa kifara karatu, kici jarabawa da kyau, kigafa tunda sukai hutun nan banga tabude littafiba fa, kullum tana nanike adakin su daga taci saita bacci sai shegen bacci kaman kaza, ki ajiye kwanon wanan tsutsan kampanin duksu kesaki bakida kyan gani, yarinya taci tuwon dawa da miyan kalkashi abinci mai Gina jiki bazata ciba sai tsutsan kampani" murmushi Mama tayi tace "Kaka indomie ce ba tsutsan kampani ba" cikin daga murya kaman zata fasa gidan tace "injiwa Haleematu" ta nuna plate din tace "ke bakiga yanda abin take a lankwashe ba, wani irin ziza ziza da ita, tsutsa ce saisu busar saisu barbadeta da fulawa fa asaka a leda a sayar" ta kalli Hamida dake share kwalla tana tauna indomie bakinta ahankali tace "ba dake nakeba dan gidanku, tashi kije mamar ki ta tayaki hada tulin kayan ki, dama gobe su Zainaba zasu dawo sa sami sarari adakin suma" tashi tayi ahankali tai hanyar corridor inda dakinsu yake, ajiye waken Mama tayi ta tashi tabita tana murmushi kasa kasa Kaka tabisu da harara kafin takarasa tadau plate din indomie tafice dashi tana hararan abincin takarasa wajen bolansu zubar da indomie tayi sanan ta wuce chan pampo ta ijiye kwanon ta wuce Sasan ta.
_🌹IN BANI 🌹_




_Maman Abd Shakur_

12....

Tashi Abie yayi yadauko maganin shi da yawancin inya fara surutai haka shi ake bashi ya dauko da sauri yadawo kan gadon ya dagoshi yana mikama Mami maganin yace "tashi kasha to saimuje wajen She" gyadama Abie kai yayi yana kuka ahankali yana yatsine fuska, zuba maganin Mami tayi ta mikamai ahankali yabude baki ya shanye maganin da kyar kullum yake yarda yasha amma yau yasha da kanshi, yanasha ko two minutes baiyiba bacci yay gaba dashi, gyaramai kwanciya Abie yay da kyar yaja bargo ya lullubeshi ya tofamai addu'a yajuyo ya kalli Mami dake share kwallan dake xubo mata, tasowa yayi ahankali yadawo bakin gadon kusada ita hanunshi yasa ya rungumota batare dayay magana ba, ahankali ta saukar da kanta kan kafadarshi wasu sababbin hawayen na gangaro mata kumatu tace "Abie why this? Why we? Why our Son? Shekaru talatin da biyu kenan muke fama, Abie please kafadamin what else dazanyi da yaronmu zai sami lafiya, banda burin daya wuce nabude idanuna naga Aadil kaman kowani namiji aduniyan nan, kaman dan uwanshi, Abieee" taja sunanshi cikin kuka, kiss yama forehead dinta yanadan shafa bayanta shima idanunshi sunyi ja, zaiyi magana wayarshi dake aljihun jallabiyar shi ta shiga ringing, riketa yay da hannu daya yasa hannunshi a aljihu ya ciro wayar yana kallon screen din, dan juyowa yayi ya kalleta yace "Baba ne" da sauri ta share hawayen datake yi tana mishi alamu daya dauka, daukan wayar yayi cikeda girmamawa harda dan dukar dakai yace "barka da safiya Baba" daga tachan bangaren tsohon da akalla xaikai shekara 80 yace "da Abdullahi nake magana ko?" yay maganan a natse kuma dadaddaya kaman yanda tsofaffi ke magana, cikeda girmamawa yace "eh Baba nine" a natse yace "to, to, to Masha Allah, ya kuke? Ya sana'ar taka tachan?" murmushi yayi yace "Alhamdulillah Baba, sana'ar munakan yi kuma ana samun riba daidai gwargwado" ahankali yace "masha Allah, Allah ya taimaka, Maryama fa?" murmushi yayi yace "gatanan Baba bari nabata wayan" ahankali yace "tsaya tukunna" cikeda girmamawa yace "to Baba" dan shiru yayi kafin ahankali yace "ina Hassan da Hussain?" kallon Mami yayi suka hada ido sanan ya maida hankalinshi kan wayan yace "Alhamdulillah suna lpy, Hussain na Nigeria yanzu haka yana Lagos ya...." cike da fada yace "Hussain na Nigeria shine baizo gidaba? Abdullahi dagakai har Maryama inda kusan bazaku iya bama jikokina yan biyuna tarbiya mai kyau ba dakun banisu na rainesu sun girma sun taso anan wurina, amma yaro ace yana kasar iyayenshi munan bamamu da labari yana gari, kenan inda ban kirakaba da bazaka fadi mini ba" cikin kwantar da murya yace "kayakuri Bab..." da sauri yace "bannemi wanan daga gareku ba, yau kwanan shi nawa?" ahankali yace "kwanan shi tara Baba, wani assignment yajeyi a Lagos amma dama..." katseshi yayi ta hanyar kiran sunanshi. "Abdullahi" da sauri cikeda girmamawa yace "na'am Babana" ahankali yace "kafadama Hussain yakamo hanya yazo kano yauyau dinan gidan kakanin shi banason naji wata magana, sai magana nabiyu dayasa na kira" yadanyi shiru yana hutawa, a natse yace "ina Hassan, yaya jikin nashi?" dan juyawa yayi ya kalli Aadil dake bacci har lokacin yace "Alhamdulillah Baba, jikin nashi da sauki" cikin dan kakkausar murya tsohon yakira sunanshi. "Abdullahi" ahankali yace "na'am Baba" shiru yayi nawurin minti biyu kafin yace "kaima kasan nabaku lokaci mai tsawo, na tsaya sanan na zuba muku ido ina kallon ku dakai da Maryama, nasan ku nasan halinku na yaran zamani, sanan bankuma tauye muku hakkin ku ba a matsayin ku na iyayen yaraba, na barku babu kasashen duniyan nan dabaku zaga da Hassan ba tun yana dan mininin shi neman mishi magani, to kanajina?" da sauri yace" eh Baba ina jinka" cikin yar shakakkiyar muryanshi ta tsofaffi yace "masha Allah, abinda nakeso daku shine, ka tattaro yinaku yinaku ka kawomin jikana nan kano, ku kawomin shi nan kano afara mishi maganin gargajiya, zamu jaraba mugani abinda Allah zaiyi, bazan zuba muku ido ku karar min da rayuwan jikana a hanyar asibiti ba, burina shine ya warke namai aure naga tattaba kunnena kafin mai afkuwa ta afku wato mutuwa, ku kawomin jikokina Kano zan nema mishi magani da kaina, ku kawomin su, ku zaku iya komawa indanta Hassan ne zan daukomai babban nurse ko Nani dazai dinga kulanmin dashi" yay dan shiru yana Tari da sauri yace "sannu Baba" saida tarin ya lafa sanan yace "kuyi shirye shiryen dazakuyi, ku kwasan mai duk wani abu dayake so gudun karya muku kuka a jirgi inya gaji da zama, ku hada komi kutaho Nigeria gobe, kufadima Hussain ina jiranshi shikuma yauyau dinan" ahankali yace "to Baba" "yauwa ka gaidamin da Maryama" "to Baba zataji" ahankali yace "Allah yamuku albarka dukan ku, Allah yabama Hassan lafiya, Allah ya kiyaye hanya yakawoku lafiya" da sauri yace "Ameen Baba" "yauwa to, nabarku lafiya" ya katse wayan. Ahankali ya zare wayan daga kunenshi ya juyo ya kalli Mami data gamajin komi, ahankali yace "anjima kihada mai kayanshi komi da komi, I will sort out d booking" gyadamai kai tayi tace "to Alhaji Allah yabada sa'a" juyowa sukayi dukansu suna kallon Aadil din dake bacci ahankali Mum tasa hannu tana shafamai kai kafin tadan kwanta a gefenshi tana shafamai kai tana kallon fuskarshi, Allah kadai yasan yanda takeson Aadil dinan, zata iya bada duka abinda ta mallaka a duniya inhar zai warke, shafa fuskarshi tayi tana kallonshi hawaye ya gangaro mata daga ido ahaka bacci yay gaba da ita hanunta akan fuskarshi, kafesu da ido Abie yayi feeling guilty, babu irin tunane tunanen da baiyi ba, blanket din gadon yaja ya lullubesu dashi yatashi yafita daga dakin yarufo musu kofa yafita, dakinshi ya shiga ya zauna gaban study dinshi ya kunna laptop dinshi yaje sight din emirate airlines, booking yamusu yay making payment aka turamai booking reference din ta email dinshi sanan ya rufe laptop din yay shiru yana kallon wani babban zoben dake kan yatsarshi yakai kusan 10min yana kallon zoben sanan yasake daukan wayarshi, dailing number Aadil yayi amma baishiga ba hakan yasa yatashi ya kwanta akan gado.



***
Shafashi dayaji anayi yasa yabude ido daga wani irin nauyayyan bacci daya samu ya kwasheshi around 4 nadare tunda jiya dayadawo daga asibitin da aka kwantar da Hamida yakejin wani irin kunci, sosai zazzabi yarufe shi jiyan nan, ahankali ya daura idanun akan fuskar Vanessa dataci gayu sosai tai makeup a fuskar tana daure dadan white towel, kwanciya tayi akan kirjinshi tanama kirjinshi kiss murya chan kasa tace "handsome baccin ya isa haka okay, your temperature is normal yanzu, am so lonely Aabid how are you feeling now?" lumshe ido yayi yanadan cije lips yakira sunanta achan kasan makoshi yace "Vanes...sa" dago kanta tayi tace "yes Handsome menene? something seems off about you tun jiya dakadawo, kodai yarinyar nan is a witch ne dama she's too fine" bude idanunshi yayi duka yadaura akanta yana mata wani irin kallo da idanunshi dasuke cike da bacci a gajiye yace "watch your tongue" yay maganan yana kara lumshe idonshi danko kadan baison hayaniya ko motsi zaiyi sai Hamida tafado mai arai, anytime daya kulle idanunshi ita yake gani, ta tsayamai arai, ta tsayamai a thought, ta tsayamai akomi ma, baitabajin yanda yakejin nanba akan any girl, pink lips dinshi Vanessa takafe da ido kafin ahankali ta daura fuskarta kan nashi tana kallon lips din tana breathing heavenly takira sunanshi dawani irin low sweet voice. "Aabid, talk to me handsome, what's the matter uhm?" tai shiru tana kallon fuskarshi amma baiyi magana ba, kiss tamai akan fine soft lips dinshi light one, bude ido yayi kadan ya kalleta batare daya cemata komiba, murmushi tayi tai cupping face dinshi tace "lemme make you feel better" zaiyi magana ta daura yatsar ta akan lips dinshi tana wani irin mai sexy kallo tasanya dayan hanunta ta warware towel din jikinta tai flinging dinshi, lumshe ido yayi da sauri dan she's so tempting, yasan dayana school he and Vanessa dated for a very long time, but yanzu ya girma he really wants to change, baya sonta but she's just a girl a d tun yana school ta makale mai dudda ba same course suka karantawa ba, kuma ba same school sukayi ba, lokacin dasuka haduma masters yakeyi ita tana degree dinta a New York film academy, another thing dayasa yake kara kulata is because bata kula any guy bandashi dan yanada mugun kishi, yarinyar na sonshi sosai bana wasaba, they had sex couple of time dan akwai wasu abubuwa datake mai da koyaya yaso karyayi saiyayi but yanzu he really wants to change, yasan a Islam abin is a sin haramun ne saisa yaketa son yay aure but baitaba ganin wacce yakeso ba, wacce tamai ta kwantamai arai baitaba ganiba, yaje kano sau da dama all his cousins, duk yanmatan garin dayake gani ko sha'awa basu bashi balle yamaji yana sonsu, sai akan Hamida dayaji he loves every single thing akan yarinyar, yaji his whole world is revolving akanta.

Grabbing dinshi dayaji tayi down there yasa ya saukar dawani irin ajiyan zuciya ya ware Ido ya kalleta, da kyar ya iya yay fighting yanda yakeji dan he so want it shima bana wasaba, hanunta yarike cikin rashin karfi ya girgiza mata kai yace "stop it" fashemai tai da kuka ahankali tace "please Aabid, I want you badly handsome, nakasa saurayi Aabid, nobody can f*ck as good as you, please my love, okay I understand you said having sex without marriage in your religion is a sin right" tai maganan tana share fuskarta da bayan hannu ta kalleshi, gyadamata kai yayi yana mika mata bargo danta rufe kirjinta dake dancing a face dinshi, karban bargon tayi tarike tareda hanunshi tace "okay let's get married handsome" lumshe ido yayi ya girgiza mata kai yace "I cannot get married to you" da sauri tace "why?" bude idanunshi yayi ya kalleta ahankali yace "because I don't have feelings for you" fashemai tayi da kuka tafada jikinshi tana girgiza mai kai tace "please love dont say that kaji My Aabid, am begging you" zaiyi magana wayarshi tai kara alamun shigowan message ahankali yamika hannu yadau wayar da sauri yabude sakon ganin daga Abie ne, yana gama karantawa ya ijiye wayan wani irin murmushi yayi yace "Kano!" tashi yayi daga kan gadon, drawer gefen gadon yajawo, bundle din kudi yaciro nayan dubu daidai guda biyar ya ijiye mata yana kallon yanda take goge idanunta da hannu yace "get ready and leave, am going to my grandparents house, my parents are coming to Nigeria tomorrow, take care okay will call you" juyawa yayi ya shiga bayi tabi bayanshi da kallo kafin ta kalli kudin daya ajiyemata tafashe da wani kukan sanan ta tashi ta kwashi kudin ta wuce tafita ta shiga next room ta shirya tsaf tsabagen yanda takeji haushin shi ko jiranshi tamai bye batayiba tadau jakanta tafita tana kumbura kumbure.

Yana fitowa shafe shafenshi yayi yana murmushi, yasan halin kakan shi hakan yasa ya shirya cikin wani white soft yard da akamai dinki jumper, bakaramin kyau kayan sukamai ba, kallon wardrobe din yayi yana kallon kayanshi he's so lazy, baida karfin dazai wani hada kayanshi a akwati banda hakama yanada kaya achan kano, hakan yasa yaje gaban madubi turaruruka ya fesa yana kallon kanshi a gaban mirror yanda farin kayan yawani irin haska shi ya shiga kayan dam yay wani irin shegen kyau, ahankali yana murmushi yace "am coming Jewel saina nemoki koma a ina kike agarin kano, ur husband is coming Mrs Aabid" murmushi yasakeyi ya zira takalmin shi na Gucci yadau wrist watch dinshi ya daura, wayarshi ya dauka yafita daga dakin yafara sauka kasa yana danna waya yana order Uber, ya sauka kasa yana wani irin kamshi dukya cika gidan da kamshin turaren shi, kitchen ya shiga yahada coffee a mug yafito zama yayi kan kujera yanashan coffee kafin Uber yazo yana cikin sha mai Uber yazo, tashi yayi yaje ya ijiye mug din a kitchen yafito ya kulle gidan, mai gadin yabama key yamai sallama tareda mai kyauta sanan yawuce yafita gate ya shiga motar Uber yajashi har airport yana zuwa yay komi Azman airline zaibi to Kano, ya karbi boarding pass dinshi yawuce upstairs ya shiga departure lounge bai wani dadeba akai announcing boarding dinsu, tashi yayi yawuce yaje yay boarding jirginsu yadaga, 1: 25 jirgin su ya sauka a Airport din kano, wani irin murmushi yayi yafito yana kallon ko ina rabonshi da kano almost a year kenan, yasan inda yafadama grandpa yana hanya da yanzu airport dinan yacika da motoci anzo daukan shi, he's so eager yaga Aadil gobe, karasawa yayi yashiga taxi yacema mai taxi din "New GRA zaka kaini".
_🌹IN BANI 🌹_


Maman Abd Shakur


13....

_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting_





Agaban wani babban gida yasa akai parking, gidan babban gaske ne dan yay girman wani anguwan, fitowa yayi daga mota yabama mai taxi kudi, masu gadin gidan dake sanye da kayan security ne suna ganinshi suka washe baki. "laaaa jikokin Alhaji ne, barka da zuwa oga" murmushi yamusu ya gyadamusu kai dan baijin yin magana suka budemai gate ya shiga, babban gidane dakeda fadi sosai gawani hadadden water treatment plant a tsakiyan compound din dayay kaman round about ta gefe kuma wajejen parking cars ne inda cars sunfi kala goma apake awurin, gawasu irin hadaddun design din flower dayabi ko ina na tsakar gidan babu kowa atsakar gidan kasancewa babu kananun yara a gidan inbadai jikoki sun zo kokuma anyi hutun school shine zakaga yara cike a gidan, da saurin shi yakarasa shiga ciki yay shashin kakanshi bude kofan part dinshi yayi babban falone dayasha hadaddun manyan kujeru sai carpet mai bala'in kyau da taushi dake shimfide akasa, wani tsohone azaune yasha manyan kaya dadan rawani akanshi idanunshi sanye da glasses nakara karfin ido, yana zaune akan wata lumstatsiyan kujera hanunshi rike da jarida yana dubawa gefen kujeran dayake zaune kuma yar sanda ce ajingine awajen wanda daga gani kasa ita ke taimakamai ya tsaya yay tafiya, manyan mazane guda uku a falon zaune akasa wanda suke yaranshi Uncle Suleman, Uncle Muhammad, sai last namijin shi Uncle Mustapha, sai mace guda daya wacce take yayar Mami tana sanye da hadadun kayan kamansu daya da Mami mai suna Asma'u, sunfi kiranta da Big Mum, itama tana zaune a falon suna hira suna shan slice fruits dake wadace agaban su, ahankali yay sallama ya shiga falon yana dan sosa keya dan yasan shima laifine, dukansu dagokai sukayi suna kallonshi cikeda mamaki Uncle Suleman wanda yake babban yayan su yace "kaga daman zuwa yanzu Hussain aika kyauta" kaman zaiyi kuka yakaraso cikin dakin yace "sorry Uncle" cikeda masifa Uncle Muhammad yace "bazaai sorry ba, shine baka fada ka shigo hanya ba kadauko taxi daga Airport kataho wat if something happen akai kidnapping dinka ahanya eh?" sake dan turo baki yayi yana kallon Baffan daya janye jaridan daga fuskarshi yana kallonshi yanamai wani irin calm love look irin na kakanni da jikoki, a sanyaye yay murmushi yanadan sosa keya ya ware hanunshi yatafi wajen tsohon. "oyoyo Grandfather oyoyo Oldman dina" karasawa yayi zai rungumeshi tsohon yadau sandar gefenshi yana nunashi dashi cikeda masifa yace "ka zonan kaga yanda zan kwaleka da sandar nan" da sauri yakoma baya ya zauna kusa da Anty Asma'u dasuke kira da big Mum kaman zaiyi kuka yace "Big Mum kinga grandfather zai bugamin wanchan ugly sandan nashi ko" dariya duka yaran sukayi tsohon yanunamai sandar cikin jin haushinshi yace "kana Nigeria kusan sati biyu saiyau zakazo dan baka da mutunci bakasam mahimmmancin yan uwanka bako, kullum da tunanin ku nake kwana nake tashi aika kyau" kallon Uncles dinshi yayi dake kallonshi cike da so yace "Uncles am sorry kunji, Big Mum am sorry wani assignment fa nazo yi dama nace saina gama zanzo, kema kinsan bazan iya zuwa Nigeria banzo wajenki ba, please Uncles kucema grandfather am sorry" duk dariya sukayi gabadayan su, Big Mum ta shafa kanshi tana kallon mahaifin nata tace "amai afuwa Baba bazai karaba" baban yayansu Suleman yace "Baba amai afuwa ai gashinan yazo, muma madan huta da maganan yan biyun ka dakake ta mana" kallonshi tsohon yayi yanajin wani irin sonshi aranshi tun yana saurayi yaso yan biyu yakeson yan biyu amma Allah baitaba bashi ba sai akan jikokin shi akuma kansu saisa yake mugun sonsu, ahankali yamai alamu da hannu. "yaka" da sauri yatashi yaje yana murmushi rungumeshi

Please Login or Register in order to submit comment