Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

numfashi ahankali ahankali an mata fixing drip a left hand dinta, ahankali yadaga kafa kaman bayaso ya taka kasa yana kallon fuskarta kaman wani magnet na pulling dinshi towards her harya karasa jikin gadon ya tsaya akanta yana kallon fuskarta, sai lokacin ya lura da bandejin da akasa a saman goshinta alamun tanada injury a wurin, kujeran gaban gadon yaja ya zauna yana kallonta still ko kyafta ido bayayi shi kanshi baisan mesa yake kallonta hakaba, kawai yasami kanshi da kallonta ne nonstop, saukar da idanunshi yayi kan hanunta da aka makala mata ruwa ahankali ya mika hanunshi ya dauki hanun nata yarike yana yana kallon hanun yanda gashi suka kwanta lub lub ajikinta kafin ya saukar da idanunshi kan fuskarta yanda take baccinta innocently kaman ka kirata tai magana, cikin wani irin cool free voice yace "Jewel" shiru yayi yana kallon fuskarta kafin ya lumshe ido yana kara holding hand nata tight, yadan fuzar da iska yana ganin d first time he saw her face daya shiga cikin ruwan, how he felt dakuma yanda yaga fuskarta tamai wani irin haske sosai acikin ruwan, motsin dayaji a hanunta dake cikin hanunshi yasa yabude idanunshi dahar sun soma chanxa kala sun kankance ya daurasu akanta, motsi yaga tanayi sosai tana yatsine fuska kadan kadan idanunta alumshe tana motsi da hannayenta da kafafunta, da sauri yatashi daga kan kujeran dayake yakai fuskarshi gab da fuskarta yana wani irin kallonta, cikin wani irin murya mai cike da natsuwa da dadin ji yakirata. "Jewel" dan shiru yayi yana kallon yanda idanunta ke rawa tana kokarin budesu, ahankali ya hura mata iska asaman idon kafin ahankali kaman mai whispering yay magana asaitin kunenta yace "open your eyes Jewel" bude idanunta tayi gabaki daya a lokaci daya dasuka mata wani iri sabida ruwan dasuka shiga cikinsu ta daurasu akanshi, dishi dishi take gani danjin idanun tayi kaman an zuba mata oil acikinsu, ahankali murya chan kasa yace "Jewel can you see me" hanunta ta daga dakeda lafiya ahankali ta daura kan idanunta ta shiga sosawa non stop dan murmushi yayi yakai hanunshi yakama hanunta datake sosa idanun nata dashi ya janye hanun daga idanun nata yana kallon kwayar idanunta, ware idanunta tayi da kyau tana kallon mutumin datagani akanta cike da mamaki yana mata wani irin cool smile yana bata wani irin warm look, da sauri ta runtse idanunta cike da tsoro kirjinta na bugawa sosai dan d last abu data tuna was lokacin data bude ido ta ganta acikin ruwa, where is she yanzu and who's this man dayake mata murmus.... Bata karasa maganan zucin ba taji sauka iska akan idanunta ba shiri tabude idanun a mugun rude tana kallonshi, shima kallonta yake ahankali yadan matsa hanunta dayake rike dashi har lokacin yana kallon kwayar idanunta yace "how are you feeling now Jewel?" zaro ido tayi arude tana wani irin kallon shi kafin tafashe dawani irin kuka ta fizge hanunta daga nashi da sauri arude ta yunkuro zata tashi kanta da nashi suka gware, wani irin ihu tasaki da saida ya mike tsaye da sauri yana shafa gaban goshinshi yana kallonta yanda take kuka tarike gaban goshinta tana shafa inda ta bugen yasa da sauri ta dira daga gadon batare data lura da drip din hanunta ba dudda batajin karfi sosai saida tai gaba zata gudu tai wurin kofa, wani irin jiri ne ya debeta tai baya zata fadi da sauri yatareta hakan yasa tafado jikinshi, wani irin ajiyan zuciya yayi yana kallon fuskarta yariketa gam gam, zaro ido tayi hawaye na zuba daga idanunta tana kallonshi bakinta na rawa sosai shima kallonta yake calmly da lumtsatsun idanunshi, saukar da idanunta tayi tana kokarin fizge jikinta daga nashi amma takasa sabida yanda yariketa, sake dago ido tayi dasuka cika da hawaye sosai ta kalleshi koina na jikinta rawa tama kasa magana, ahankali yadan sauke ajiyan zuciya kafin ya dagata ya zaunar da ita akan gadon da sauri ta dau filo tana kare fuskarta dashi jikinta na rawa sosai, dan matsowa yayi kusa da gadon ganin yanda ta rude saukar da muryanshi yayi sosai yace "Hey Jewel calm down, am not gonna hurt you, you are safe okay" kare fuskarta tai da filon sosai hannayenta na rawa daidai lokacin nurse tabude kofan ta shigo sabida ihun dataji, arude Hamida tasaki wani irin kuka tana kara rufe fuskarta da filon tana neman inda zata shige bakinta har rawa yake ta damke filon sosai tace "Ma...ma, Mama, wayyo Allah na Mama!" ta kwalama Maman su kira, ahankali nurse din takaraso gaban gadon ta kalli Aabid dayay folding hannu yana kallonta tace "Sir your patient ta tashi, hello Jewel stop crying, am your nurse, nurse Kuburat, how are you feeling now, meke miki ciwo?" tai maganan tana fizge filon hanunta cikin dabara, fashewa tayi da kuka sosai tana komawa karshen gadon tasa hannu ta daura akan fuskarta tana kuka sosai tana kakkare fuskarta arude tace "pls Mama, ina Mama na?" cikin rarrashi nurse din tace "don't worry Mama zatazo yanzun nan, but for now ga maganin ki kisha, inhar kinsha kinji sauki gobe da safe zamu sallameki, saikije kiga Mama, you drown a ruwa and Sir brought you here" tai maganan tana nuna mata Aabid, ahankali tana hawaye sosai tadan juyoda kai ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta sake dukar dakai tana kakkare fuskarta da hannu daya tana share hawayen datakeyi da bayan dayan hanun, maganin nurse din tazuba a marfi 5ml takai saitin bakinta tana murmushi tace "yauwa to open your mouth kisha ba daci" ahankali tadan juyo dakanta jikinta na rawa har lokacin tadan bude bakinta da sauri nurse din ta zuba mata maganin, hadiye maganin tayi hawaye na gangarowa, murmushi nurse din tace "good" ta kalleshi tace "Sir taci abinci please, I will come back anjima nai checking vitals dinta" tajuya tafita daga dakin, saukar da kanta tayi kasa tana kuka sosai tana gogewa da bayan hannu, kara jan kujeran yayi ya zauna tareda daukan takeaway dayayo mata yabude fried rice din yasa spoon aciki ya mika mata yana kallon fuskarta, kawad dakai tayi chan gefe tana kare fuskarta da kyau, dan murmushi yayi yace "take d food and eat kona duramiki, kinsan menene force feed?" yay maganan yana dage mata gira daya, adan rude tafashe dawani kukan tadan juyo ta kalleshi, hada ido suka sakeyi da sauri takara juyar dakan tana goge fuskarta da hannu, dan matsar da kujeran baya yayi zai tashi hakan yasa tadanyi ihu ta yar da filon ta mikamai hannunta dake bari da sauri, bata abincin yayi yana murmushi takarba da sauri tana goge fuskarta da bayan hannu, murmushi yasakeyi dan hakanan yaji yarinyar na burgeshi, abincin ya kalla ya kalli yanda takeyi da hannu taki diba taci, murya chan kasa yace "nabaki dakaina?" da sauri ta girgiza mai kai batare da ta kalleshi ba tadebo kadan takai bakinta taci, hanunta dake rawa sosai yabi da kallo yace "what's your name Jewel?" dan dago kai tayi ta kalleshi da sauri ta janye idonta dan kasa jure kallonshi tayi saima kirjinta data fara bugawa danji tayi zata kware abincin ya tsaya mata a kirji da sauri yadau bottle water ya bude marfin yamika mata, karba tayi da sauri tasha kadan hakan yasa ya mika hannu ya karba yana kallon fuskarta tareda karban takeaway from her ahankali yace "ya sunanki" yay maganan yana debo fried rice din a spoon yakai bakinta.
_🌹IN BANI🌹_



_M. Shakur_

8....

Kara zaro idanunta tayi duka tana kallonshi tana wani irin kallon abincin daya kawo bakinta yanajira tabude yasamata aciki, dan lumshe ido yayi yabudesu ahankali ya sake daurasu akan white oily eyes dinta, cikin wani irin dense voice yace "open your mouth Jewel" ja baya tafarayi akan gadon arude yana binta rike da spoon din harsaida takai bangon gadon tafashe da kuka tana kare fuskarta da hannu, ahankali ya zauna kusa da ita ya mika hanunshi yakama hanun datake kare fuskan dashi yakai spoon din mouth dinta yana wani irin kallonta batare dayay magana ba, da sauri ta bude bakin yasaka mata rice din ta karba zata fizge hanunta yakara rikewa gam gam, ahaka yacigaba da bata abincin hartaci kusan 5 spoons sanan ta kauda kai tace "na..na koshi" rufe abincin yayi ya ijiye a inda yake yadau bottle water yabata, ahankali ta karba tasha kadan tabashi ya karba ya ijiye yana kallon yanda gefen bakinta ya baci da oil din food din, hanunshi ya zira a aljihu yaciro clean white handkerchief dinshi mai taushi da kamshi yakai saitin bakinta yana wani irin kallonta, arude ta yunkura zata koma baya da sauri yasa hanunshi yakama waist dinta yana wani irin kallonta, kwalalo ido tayi tana wani irin kallonshi adaburce kaman wacce ke shirin suma, ahankali batare daya yanke eye contact dinsu ba ya daura handkerchief din gefen bakinta yana share mata ahankali harya gama yana kallon kwayar idanunta, zare handkerchief din yayi batare daya saketa ba yana rike da ita har lokacin yace "what's your name Jewel?" kulle idanuwanta tayi da sauri dan bazata iya jure kallon dayake mataba, ita tunda take bata taba ganin namiji mai eyes irin nashiba, yatsarshi yadaura kan nose dinta yana kallon long eyelash dinta yace "what's your name Jewel?" wani irin nishi tayi dan sosai yatsarshi ke mata wani irin sanyi a hanci hakan yasa tasaki wani irin ajiyan zuciya tace "Amatullah" murmushi yayi sosai dayawani irin karamai kyau maidan sauti hakan yasa ta bude idanunta, kallonta yasakeyi yace "your name is very cute just like you Ama" sake ware idanunta tayi ta kalleshi adan tsorace, gyadamata kai yayi yace "yes, you're beautiful Jewel" saukar da idanunta tayi kasa da sauri hakan yasa ya sanya hannu yakama habarta ya daga fuskarta ta fuskance shi, sosai zuciyarta ke neman dena aiki sabida yanda yake kallonta, da sauri ta sanya hanunta tana tura nashi daya rike mata habanta dashi muryanta na rawa sosai tace "s...stop touching me" da sauri yace "why?" tabe baki yayi yace "ba kyau ko? In UK is a normal thing" shiru yayi yana kallon yanda har lokacin hawaye ke fita daga idanunta and he could feel yanda jikinta ko'ina yake rawa sabida riketan dayayi ahankali yace "kinaso na sakeki?" da sauri ta dagamai kai batare data kalleshi ba, dan murmushi yayi yace "okay to stop crying and listen to me, I wanna talk to you, inba hakaba I will hold and touch you again" da sauri ta sanya hannu ta share hawayen nata tass tadan kalleshi irin kallon nan na antursasani ne, ahankali yajanye hanunshi daga waist dinta ya saki habarta yadan koma baya da ita kadan dan yasan inhar yana kusa da ita he will touch her again and yanaso he wants her to be comfortable, gyara zama yayi ya kalleta murya chan kasa yace "Amatullah" da sauri ta dago kai ta kalleshi dan sosai yanda ta kira sunan ya daki ranta danko kadan a gida ba'a saba kiranta da Amatullah a gidaba dan sunan Kaka ne, babu wanda ya isa yakirata da sunan. "where are you coming from, tayaya kikai drowning? Kinje Beach ne?" shiru tayi tana kallonshi kafin cikin siriruwar muryanta tace "bikin Anty Ayush" da sauri yace "who's Anty Ayush?" ahankali batare data kalleshi tace "My sister" "aruwa kuke bikin?" gyadamai kai tayi tace "yes d husband is navy a jirgin ruwa suke party" da sauri yace "to tayaya kika fada ruwa basu ciroki ba?" cikin wani irin muryan kuka tace "jiri" da sauri yace "jiri kika dinga gani?" gyadamai kai tayi batare datai magana ba, shima shiru yayi yana kallonta, dan dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido da sauri ta saukar da kanta tana share hawayen daya zubomata tace "I thought na mutu ma" murmushi yayi yace "no, I was the hero, I saved u Jewel, am your superman Jewel" batare data kalleshi ba tace "my name is not Jewel stop calling me that" murmushi yayi maidan sauri yakamo hanunta yace "you're my Jewel, I found you a water, and bazan barki ba Jewel, I just li..." hawayen dayaga tana sharewa yasa yadanyi shiru yana kallonta, dago kai tayi ta kalleshi adan tsorace ahankali tace "zan kira Mama na" dan yatsine fuska yayi kaman wani karamin yaro yace "I don't want them to come and carry you now Jewel" duka hannayenta tadaura kan fuskarta tana share hawayen dake zubo mata sosai wanan wani irin mutum ne haka, wani asibiti ne wanan, tasan su Anty Lami da Ayush kowama ana chan ana neman ta, tasan hala yanzu ma har an kira su Baba da Mama harma Kaka duk an sanar dasu ta bace, hanunta taji yakamo ya matsa. "Jewel stop crying pls, zakiyi magana da Mum dinki?" gyadamai kai tayi hakan yasa yaciro wayarshi daga aljihu ya mika mata dan dago kai tayi suka sake hada ido, karban wayan tayi tasaka number Mama tai dailing, harya katse mama bata dauka ba, ana biyu ne ta dauka muryanta yadan shake alamun taci kuka tace "Assalamu Alaykum, waye?" jin muryan Mama yasa taji hawaye yazubo mata da sauri tace "Mamaa" tashi Mama tayi daga kan gado datake kusa da Abba dake lallashinta, dafe kirjinta tace "Hamida, Hamida kene?" gyadamata kai tayi ahankali tace "uhm nine Mama" kaman Mama zatai kuka tace "Hamida ina kike? Ina kikaje su Ayush hankalin su dukya tashi anata neman ki, Hamida I promise bazan kara turaki kije wani waje idan bazakije ba kinji, fadamin inda kikaje, inkika boye? Anbicika jirgin kakap ba'a gankiba, ina kika boye Hamidana nakira su Ayush nafada musu suzo su daukeki ki koma gida gobe sudawo min dake nan kano tunda bakison chan, kina ina Baby na? and wanan wani number ne kika kirani dashi naga banaki bane, da number wa kika kirani, ina kika boye eh Hamida na fadamin?" Mama tai maganan muryanta narawa sosai hankalin ta atashe, dama ance yaro mai matsala yafi shiga rai, bala'in son Hamida take bana wasaba, ko Ihsan auta tabiyo bayan son datake ma Hamida, ahankali Hamida tace "ruwa nafada Mama" "innalillahi wa innailaihi raji'un ruwa Hamida? Wanan babban rafi da manya manyan jirgin chaina kebi kika fada? Ru kika fada Hamida? Are you fine? Kina ina yanzu?" ganin yanda tabi ta rude ko'ina najikinta na rawa yasa Abba karban wayan daga hanunta yakara a kunne yace "Mamana kinajina" gyadamai kai tayi tana kuka murya chan kasa tace "eh" anatse yace "yanzu kina ina?" ahankali tajuya ta kakkali dakin cikin kuka tana lankwashe kai kaman tana gabansu tace "asibiti" da sauri yace "subhannallah asibiti? Garin yaya? Waya kawoki asibiti?" fashewa tai da kuka tace "nima ban sanshiba Abba" da sauri Abba yace "da wayanshi kika kiramu to" gyadamai kai tasake yi cikin kuka tace "eh shiya bani wayan" da sauri Abba yace "bashi wayan nai magana dashi" ahankali ta dago idanunta dake cike da hawaye ta kalleshi hada ido sukayi ya rungume hanunshi yamata kuri da ido yana kallonta kaman zai cinyeta, mikamai wayan tayi tace "Abba na zaima magana" kallonta yayi kafin ya kalli wayan yasake kallonta, sanan ya karbi wayan yakara a kunne a natse yay sallama kaman bashiba sanan yajuya yafita daga dakin tabi bayanshi da kallo, yakai kusan 10min awaje sanan yadawo dakin, gyangyadi yaga tanayi a zaune, kujera yaja ya zauna hakan yasa tabude ido da sauri ta kalleshi da idanunta dasuka dan kankance sabida bacci tace "za'azo a daukeni?" gyadamata kai yayi yace "amma saida safe za'azo nafada musu sunan asibitin" wani irin bakin ciki taji ya tsaya mata a wuya dan bataso kara koda minti daya da wanan mai shegen kallon ba, ahankali ta kwanta kaman marainiya ta juyar da kanta dayan side din tana danne kukan daya wani irin taushe mata makoshi.
_🌹 IN BANI 🌹_




_M. Shakur_

9....

Magana zai mata wayarshi ya shiga ringing da sauri ya kalli wayar ganin number dazune Dil❤ yasa yay wani irin cute smile yay picking call din cikeda murmushi yace "I know you're missing me Dil just admit" daga tachan bangaren cikin wani irin cool voice dayamafi na Aabid din dadi gata yar karama yace "when are you coming back Bid?" dariya Aabid yadanyi yace "me nawani cin magani? Saikace kayi missing dina sanan zan fadama ranan dazan dawo Dil" shiru wanda aka kira da Dil yayi baice komiba hakan yasa da sauri Aabid yace "kaifa kacika zuciya matsalana dakai kenan Dil" cikin fushi sosai ya daga murya cikeda fada yace "I said when are you coming back?" dariya sosai Aabid yasakeyi yace "say u miss me first" katse wayar yayi dip hakan yasa Aabid ya kalli fuskar wayan da sauri ganin ya katse yasa ya ware manyan idanunshi, dailing number yayi back da sauri wayar yay ringing harya gama ba'a daukaba hakan yasa yasake dailing number akaro nabiyu.

Da sauri fine dattijuwan matar data shiga babban hadadden kitchen dinsu hadamai hotchocholate tafito daga kitchen din, hadadden dining din takaraso tadau wayar tai picking, murmushi tayi cikin muryanta mai dadi tace "hello Son" wani irin murmushi Aabid yayi yace "Mami na, I miss you so much, ina Dil Mami?" dan murmushi matar tayi mai sauti tana kallon tilin brunch dake kan dining tace "mekama dan uwanka Son? Yay fushi yabar phone din da abincin duka a dining, dama kasan da kyar na lallabashi yazo yaci dan rabonshi da abinci tun jiya" dan murmushi yayi yana karajin son dan uwan nashi aranshi yace "Mami I told him yazo muje tare yaki zuwa wai bazai iya zaman flight ba he's scared, and Nigeria weather is harsh sabida nataba cemai garin dazafi, sai yanzu dana zo shine zai wani dameni nadawo yanamin fushi to baza'a dawon ba" yay maganan yana daure fuska shima alamun ranshi yabaci, hadadden kujeran dining matar taja tazauna tana saukar da ajiyan zuciya kafin ahankali takira sunanshi. "Aabid" da wuya Mami ke kiran sunan su hakan yasa yasake natsuwa yace "na'am Mami na" dan ajiyan zuciya ta saukar tace "you know your brother's condition, you know how your twin brother is so attach to you, kasan baida lafiya sosai, please kadawo kaji and be with him am sure yanzu yanadaki he's crying" sosai maganan Mami yatabamai zuciya hakan yasa yaji hawaye sun taru a idanunshi da sauri ya hadiye su murya chan kasa yana kallon Hamida data dade dayin bacci yace "please Mami kaimai wayan lemme speak to him" tashi Mami tayi daga dining tai sama, wani babban hadadden daki ta shiga da akai komi blue, gadaje biyune adakin hadaddun gaske komi iri daya, hangoshi tayi akan gadon yana kwance yaja bargo yarufe jikinshi yajuyama kofa baya, shiga ciki tayi ta maida kofar ta rufe takarasa jikin gadon, ahankali ta zauna abakin gadon ta daura hannu akanshi tana shafawa cike da lallashi ta mikamai wayan tace "gashi Aadil dina, Aabid zaima magana" ture hanunta yayi cikin fushi yana juyo da kanshi dan bayason ya karbi wayan. Hadadden saurayi ne kyaykyawan gaske ebony, kamanninshi daya da Aabid banbancin shine kana ganin wanan kasan baida cikakaken lafiya, dan sosai bakinshi ke dilalar da miyau kanshi na wani irin rawa kaman kan karamin jariri, yana sanye da plain white t-shirt na givency, yasanya 3quater black iya guwiwa, bakaramin kyau yakeda shiba saidai shi yafi Aabid jan lebe, dakuma sleepy eyes.
Cikin wata irin raunanniyar murya Aabid yace "yaki karban wayan ko Mami?" ahankali tace "eh yaki Son" dan murmushi yayi yana share hawayen daya zubomai da sauri yace "sani a speaker Mami and keep the phone close to him" saka wayan Mami tayi a speaker ta ajiye wurin kanshi ta tashi tafita daga dakin ta rufo mai kofa, karan rufe kofan Mami dayaji yasa yace "I know you can hear me u dis rascal, rascal boy meyimin wayau in muna buga kwallo kawai, little rascal me boyemin car keys idan zan fita, u better talk ko I will come out through that phone and pinch your cheeks so hard kasan u hate that ko? Now say something to your twin brother please my Aadil, kaji D...il" yay maganan bakinshi narawa sosai hakan yasa yatashi da sauri yafita daga dakin yarufo mata kofa, waje yafita ya shiga cikin mota ya rufo yana gyara zama yace "kamin magana please" ahankali yamika hannu yaja wayan kanshi narawa sosai ya kara wayan a kunenshi yatashi ya zauna bakinshi na zubar da miyau kaman karamin yaro yafashe da kuka sosai yana shesheka yana murza ido, arude muryan Aabid narawa sosai yakira shi da karfi arude "Aadil! Aadil! please stop crying, tell me yaushe kakeson nadawo koma yaushe ne i will come back I promise you, stop crying dan Allah kaji" sosai yake kukan miyau na zuba daga bakinshi yana wani irin nishi kaman wanda aka zane yace "now, kadawo yanzu, I want to see you now" runtse ido Aabid yay ahankali ya sassauta muryanshi yace "Aadil" cikin kuka sosai yana turo mai baki yace "uhm" murya chan kasa yace "kasan I don't lie ko, banama karya, am sorry Dil but I can't come back right now, Please stop crying I promise you I will come back soon okay" turomai baki yayi yana share hawayen kaman small yaro yace "w...wat..wat is keeping you there then?" dan lumshe ido yayi yabude ahankali dan muryanshi ayanda yakejinshi yanzu is really breaking his heart, yasan he's brother is missing him, murya chan kasa yace "she" da sauri cikin kuka yace "she??" gyadamai kai yayi yace "yes twin I saw my Jewel yau, and is love at first sight" da sauri yace "love? Bid we found our Jewel, I love her too, love at first sight ko" gyadamai kai yayi yana share hawayen dayake yi yace "yes, love at first sight my Dil" da sauri yana share kukan dayake yi yace "to when are we going to get married to her?" murmushi yayi sosai jin yasoma dawowa daidai yace "I don't know Dil, she don't like me" da sauri yace "give her roses, plenty plenty rose like kaman a movie" murmushi yayi yace "okay Dil, yanzu kaci abincin da Mami tabaka, go and eat your food and take your drugs okay, anjima your Dr will come" gyadamai kai yayi kaman karamin yaro yace "okay, tell her I love her" dariya yayi sosai yace "rascal okay" dariya shima yayi yatashi yana tsalle akan gado yace "I will tell Mami na kacemin rascal again batahanaka ba yaro kawai" da sauri yana murmushi yace "wayace ma ni yarone zan haihu innai aure dankaji" da sauri shima yana share miyan daya zubanmai awuya yace "me to, nima zan haihu dan kaji, plenty plenty babies" dariya yayi sosai yace "okay naji go and eat your food to" turomai baki yayi yace "the food is peprish Bid" shima turo baki yayi kaman yanda yayi yace "eat small okay and be taking water d pepper will go" dariya yayi yace "Bid I've gotten two friends on my messenger, Anty Hamida and Ihsan, can I be their friend Bid?" yay maganan yana lankwasa kai yana turamai baki, dan dariya Aabid yayi yace "yes chat with them but don't tell them who you are okay" da sauri yace "okay I will not, and...and..and" da sauri Aabid yace "and wat" da sauri yace "my Skype is not working kuma" dan shiru yayi kaman mai tunani yace "I will check it for you inna dawo" da sauri yace "okay, tell her I love her, bye am hungry" da sauri yace "okay I will, oya run, run jekaci abincin ka, finish everything okay" da sauri ya gyadamai kai yana katse wayan, yay tsalle ya dira daga gadon yafita daga dakin yana tsalle sosai yana sauka daga stairs din, da sauri Mami ta tashi daga kan kujera tace "stop jumping Son karka fadi" washe mata baki yayi yataho dawani irin shegen gudu yafada jikinta yace "oyoyo Mami na" yamata kiss a kumatu kafin yatashi da gudu daga jikinta yay dining yaje ya zauna ya bude abincin ya cillar da marfin kasa yadau spoon yafara ci rabi na zuba cikin plate din da dining rabi na shiga bakinshi, sosai Mum ta kafeshi da ido taji hawaye zai zubo mata da sauri ta hadiye kukan ta taso ahankali tazo

Please Login or Register in order to submit comment