Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[4/10, 7:57 PM] โ€ช+234 803 509 6818โ€ฌ: *๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ'DAN GARGAJIYA๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ*
*(gargajiya ba addini bane)*



*Na*
*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป




*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*



*1โšœ5*



*BIRNIN KAHUTU*



Kwance bahijja take cikin tsananin ciwo na nak'uda gashi babu kowa a tare ita, sai addu'o'i takeyi ga mahaliccinta na samun sassauci, can wani kuxari yazo mata ta ja jiki ixuwa kan mudubin ta ta dauko wayar ta ta danna lambar mahaifiyarta, bugu biyu ta dauka tare da karawa a kunnen ta, nan taji muryar 'diyar tata tasan ba kalau ba.

"Umma ki yafe ni mutuwa zanyi ki rokar min Baba ya yafe min shima" Bahijja ke fadin haka inda hankalin mahaifiyar yayi mutuqar tashi domin tasan diyar tata na tare da tsohon ciki ga ta kuma a gidan gargajiya, tana tsaka da tunani saiga Alhaji Mahmud ya fito daga wanka.

Nan ta sanar dashi abinda me faruwa aikuwa ya zura kayan sa yace suje su ga halin da take cinki. Ya dauko motar sa suka tafi, da Isar su yace Umma ta shiga ta gano halin da take ciki, shigar ta da kamar minti biyu sai ga ta dawo a guje tana fadin Alhaji shigo mu kamo ta zuwa asibiti kan 'da ya fito gashi ko motsin kirki bata iyawa.

Tun kan ta karasa Alhaji Mahmud yayi ciki a guje ya dauko ta suka nufi asibiti, isar su ke da wuya nurses suka kawo musu agajin gaggawa inda aka dauke ta zuwa dakin haihuwa Dan ceto ranta dana yaron.




A bangaren Badaru (mijin bahijja) kuma yana dawowa gida ya kutsa kai cikin gida yana muzurai shi a dole baya son raini, yana shiga yaga bata nan, nan ya fito ya shiga wurin mahaifiyar shi yake tambayarta ko ta shigo gidan, kada baki tayi tace yoo ni ina na ganta.


Suna cikin haka saiga k'anwar Badaru nan ta dawo daga aiken da aka mata, nan ta Sanar dasu cewa ai taga Umman ta sunzo sun dauketa zuwa asibiti, nan ya mulmulo wani uban zagi yace "mu za ai wa birnanci a karya mana tsarin iyaye da kakanni alhalin ni *'Dan Gargajiya* ne gaba da baya" fuuuu ya fice sai asibitin da yake tunanin nan zai samesu, aikuwa yayi Sa'a nan din sukaje danya hango surukar tasa a zaune, nanfa ya shiga cikin inda nurses suke da masu kawo yan haihuwa, nan fa Badaru ya fara tijara yana bubbuga kirji yana fadin "mu 'yan gargajiya ne ba'a mana iskanci, kawai an dauko min mata ba tare da an sanar da ko mahaifiyata ba an kawo ta nan, wannan ai reni ace mahaifiyata tana raye ace ba'a sanar da itaba saidai taji daga baya".



Umman bahijja tace kayi hakuri mun same ta ne cikin wani hal... bata qarasa ya katse ta yana zuba rashin arxikin sa son ransa, duk abinnan dake wakana kowa ya kasa cewa Badaru komai har ma'aikatan jinyar, nan wata jajirtacciya ta taso adaidai lokacin dayake cewa uban wa yasa a kawo mishi mata asibiti, a zuciye ta dira gabansa tace ubanka ne......



Wai shin wacece wannan, kuma ya zasu kare da badaru?


Amsoshinku na shafi na gaba.



Kuyi hakuri bana iya yin dogon shafi.




*Ummu Rahma ce*โœ๐Ÿป
[4/10, 7:57 PM] โ€ช+234 803 509 6818โ€ฌ: *๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ'DAN GARGAJIYA๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ*


*(gargajiya ba addini bane)*



*Na*


*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป



*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*


*5โšœ10*


Kai wane irin mara tausayi ne, wane irin mutum ne kai mai butulcewa rahamar mahalicci, ka ko san a halin da aka kawo ta nan zaka zo kana wa mutane rashin arziki.


Badaru yace mata " ba ruwanki hajiya" yana muzurai kamar ya tik'i gudu a filin tsare.

Malama Ramatu tace da ruwa na mana saboda 'ya mace ka tab'a, kai zakaso ayiwa k'anwar ka haka ko 'yarka ko mahaifiyar ka.


A a hajiya banda Babata wlh. Mal Ramatu tace harda ita, ita wannan da make ciwa mutunci ba uwar wata bace, duk wannan maganganun suna yin shine a hasale, Mal Ramatu kuwa kamar ta rufe shi da duka.

Ta dora da cewa yanzu kai saboda Allah kayi daidai kenan wannan 'dabi'ar da kazo ka nuna har kana wani ikirarin kai Dan gargajiyane, to ka fada min inda ya samo asali a addini.



Shiru Badaru yayi yana tunanin k'arfin hali irin na wanna mata, bai gama tunanin sa ba yaji ta jefo masa wani tambaya da cewa, 'yayanka nawa, Badaru kamar bazai amsa ba yace 'yata daya na biyu za a Haifa.


Malama Ramatu tace Alhamdulillahi ka rubuta ka ajiye watarana zaizo kanka.



Badaru zaiyi magana kenan wata nurse ta fito daga dakin karbar haihuwa dan kiran Malama Ramatu domin patient dinta ta sauka, dama ita ma mai haihuwa ta kawo, har tayi gaba ta juyo tace kuma zan dawo gareka.....



**** **** ****


*'KAUYEN BANDAAS*




Hinde! Hinde! Hinde! Wai ina kika shiga ne ga awakai can zasu cinye ya'diyar dana zo da ita ki dafa min, jin shiru wacce aka kira da Hinde bata fito ba yasa shi 'dage labulan 'dakin nata Dan yaga ko tana ciki.



Turus yayi ganinta tana sallah, nanfa ya hau sababi ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.



Yanzu Hinde saboda taurin kai irin naki sallar ma baza ki bari ta nuna ba sai kinyi ta yanzu, dama nasan za a rina, shiyasa liman yana sallame wa na taho gida dan in ganewa idanuwa, ke kullum bakya bin abinda iyayen mu suka bari saboda kinje birni kin koyo rashin biyayya, ace Juma'ar ma bazaki bari sai an dade da dawowa ba sannan kiyi taki saboda taurin kai.



Duk wannan fadan da yake yi Hinde tana sauraran sa kuma tana jin takaicin halinsa da a komai saiya sako batun *Gargajiya*.



Malam Maude kenan mijin Hinde daya gaji al'adu tun iyaye da kakanninsa, dan kuwa da ana sayar da al'adu wurinsa za aje, mutum ne shi mai tsattsauran ra'ayi, gashi kuma ba shi da ilimin addini mai zurfi.



Bayan ya gama fadan sa yayi daidai da idar da addu'o'i da Hinde take yi nan ta fara bashi amsa cikin hikima da wayewa irin ta addini....




Haba Malam bai kamata ace har yanzu ka kasa sakin wannan ra'ayin naka ba na kimai kace iyaye da kakanni, shifa addinin Allah ba ruwan sa da wani gargajiya ko rashin ta, amma har yanzu ka kasa fahimta ta.



Ke rufa min baki, nawa kike da har kika San me duniyar ta 'kunsa, ku da baku riski al'adun mu ba masu daraja, yana fadi yana huci.



Hinde ce ta katse shi da cewa " yi hakuri Malam, ba wai ina nufin al'adun Ku basu da kyau ba a a kawai dai akwai inda ya dace ace basuyi tasiri ba musanman akan addini.


Ka Sani cewa acikin hadisan Manzon Allah akwai wanda yai mana nuni da zuwa masallaci amma mu suturce jikin mu kar muyi fita irin ta jahilci


Kuma ita sallah da kake fadin in barta ta nuna idan kuma na mutu kuma kafin lokacin fa.



Nan fa yay karaf yana fadin haba Hinde ke kullum baki da magana saita mutuwa, bari inje wurin ja'e in dawo kafin maraice, kiyi maza ki kwa'da min ya'diyar ina nan dawowa, ya shuri takalmansa yai gaba.


Dariya Hinde tasa Dan tasan cewa Malam Maude baya son zancen mutuwa.

Nan ta tashi ta fara kokarin hada masa ya'diyar sa kafin ya dawo.




Shin ya Malama Ramatu zasu k'are da Badaru a asibiti?



*Ummu Rahma ce โœ๐Ÿป*
[4/10, 7:57 PM] โ€ช+234 803 509 6818โ€ฌ: *๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ'DAN GARGAJIYA๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ*


*(gargajiya ba addini bane)*



*Na*


*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป



*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*



*10โšœ15*




Tsaye Badaru yake yana nazarin kalaman Malama Ramatu tare da jiran ta ta fito dan su 'karkare.



Yana cikin tunanin yaji muryar ta ta dawo tana masa sallama, yayi mamakin haka duba da yanda suka rabu, abinda bai sani ba shine shi Malama Ramatu tana da saukin hali ga fahimta mai zurfi irin ta addini domin ya cancanci ayi masa sallama kasancewarsa musulmi.



Amma a wannan karon bata dawo a hasale ba, nan ta fara masa da nasiha tana cewa " baka kyauta ba bawan Allah, ya sunan naka" jikinsa ne yayi sanyi yace sunana Badaru.



Haba Badaru gaka a haka dai anga kamili mai nutsuwa amma kuma ka dauki wata dabi'a ka sawa kanka, duba ka gani nan duk mutane ne kowa da abinda yake fadi a kanka na rashin tausayi, shin Kasan bakin wani kuwa.



Badaru yace kinsani ne Babata kawo ta fa sukayi basu sanar da Inna ta ba shine na fusata sos.....


Malama Ramatu ta katse shi da cewa to da kuma ta mutu fa ga kan 'da ya fito ita kuma bata da karfi, in ba a taimaka mata ba Kasan abin da zai biyo baya?.



Nan dai tayi masa nasiha ta nuna masa kuskurensa tare da mata al'kawarin zai daina, tayi murna da jin haka, Matan wurin kuwa sai kallon su ake wasu na dariya suna cewa gaskiya kin samu 'da, shidai zuwa yanxu yayi sanyi dan ya ji nasihar da aka masa.




Suna zaune tana fada masa yadda zaiyi bayan anyi haihuwa yana amsa mata da to.



A wannan yanayi wata nurse ta fito tana fadin " ina Wanda suka kawo Bahijja Mahmud" nan fa badaru yayi kicin kicin yana fadin "kinji ko Babata anma cire sunan ta daga Bahijja Badar...... bai 'karasa ba tace wato dai bazaka bar batun *gargajiya* ba kenan, ai a addinance mutum da suna Ubansa ake kiransa koda kuwa ya kasance ba musulmi ba, sannan yayi shiru, suna haka ne Umman bahijja ta nufo su tana fadin ta sauka an sanu 'da na miji.



Badaru bakinsa kamar ya yage sai zabga murmushi yake.



Bayan ta koma ciki Badaru yace Babata ya za ayi, nan ta fada masa ya samo wa mai jego abinda zataci sannan inda hali ya siyo wa jaririn kaya ko kala uku ne, nan badaru ya fiddo kudi ya miko mata, tace masa a'a muje dai in raka ka ka siyo (๐Ÿคฃ).



Malama Ramatu kenan mace ce mai gudun duniya, nan suka rankaya zuwa bakin 'kofar asibitin inda masu sayar da kayayyaki suke zauna, anan aka zabo kaya daidai da kudin Badaru domin tace kar ya matsa ma kanshi, a kullum.kayi amfani da abinda kake dashi yafi alkhairi, anan ma Badaru ya siyo musu abinci harda madara Wanda hakan ya faranta ran Mal Ramatu ganin ya dauki maganar ta.




Nan suka dawo cikin asibitin kowa na kallon su cikin sha'awa da burgewa.



Malama Ramatu ce ta mika wa Umman Bahijja kayan Wanda itama tayi farin ciki tayi mata godiya sannan ta wuce ciki.




Malama Ramatu ta fito waje dan har yanzu ba a gama da patient dinta ba, tana zaman jira ta hango 'dan nata (Badaru) ya nufo ta......



**** **** ****



Malam jauro yana zuwa ya iske Ja'e 'karkashin wata bishiya yana ta gyaran tsohon keken sa, nan suka gaisa tare da yiwa juna barkwanci dan babu laifi akwai ban dariya ga wadannan abokai, suna tsaka da hira saiga 'dan gidan Malam Ila ya nufo su yana kuka sosai, duk suka zuba masa ido jin dalilin kukansa, nan ya sanar dasu baban shi ne ya rasu, nan fa cikin malam Maude yace 'kuuuuuuuu saboda tsoro, gashi an manyanta ga kuma tsoron mutuwa, dadin da'dawa kuma ma'kocinsa mai rasuwar.



Nan ya daidaita nutsuwar shi suka rankaya zuwa gidan malam Ila.




Isar su keda wuya mata suka dinga bullowa ta ko ina kafin kuce me gida ya cika dankam da mata said koke koke akeyi.....




To wai shin a wannan garin me wadannan Matan zasu aika ne?




Malama dai da Badaru fa har yanzu suna asibiti,wai shin ya zata kaya ne?.



Ku biyo bi a shafi na gaba.



*Ummu Rahma ce* โœ๐Ÿป
[4/10, 7:57 PM] โ€ช+234 803 509 6818โ€ฌ: *๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ'DAN GARGAJIYA๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ*


*(gargajiya ba addini bane)*


*Na*

*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*


*15 โšœ20*


*Gidan makokin Malam Ila*


Mata ne dan'kam a gidan banda koke koke babu abinda kake jiyowa wasu harda birgima ana fadan kalmomin da basu dace ba.


Ita kuwa matar malam Ila tayi 'kuri a gefe tun tana hawaye har ta kai ga hawayen baya iya fita saidai ajiyar zuciya.


Ana zaune cikin jimami da kuma dakon gama ha'da malam Ila dan mik'a shi gidansa na gaskiya, wata tsohuwa ce tayi sallama tare da shigowa tayi wa kanta mazauni, 'dauke take da 'kullin kayanta.


Wannan tsohuwa dai ba wata bace illa malamar 'kauyen bandass a cewar su, sunanta malama Hakama, amma asalin sunanan Iya Dije, ana kiran ta da *Hakama* ne saboda duk kalma 'daya a zancen ta saita sa *Hakama* ita ce mai shigar da matar mamaci takaba.

*_Niko nace yau naga ikon Allah, shin takaba ma sai an shigar da mutum_* ๐Ÿค”


Ana zazzaune sai ga gawar malam Ila an fito da ita nan fa mata suka rude da wani gigitaccen kuka, haka aka fita dashi zuwa kushewar sa, malam Maude yaso ya zille dan baya 'kaunar mutuwa ko kadan balle zuwa ma'kabarta, da 'kyar malam Ja'e ya ja shi suka tafi.


Anje ma'kabarta za a sanya shi a rami kenan saiga wani tsoho ya gabata yana mai cewa, ai ba ai masa addu'a ba irin wacce iyaye suke yi kafin binne mamaci, nan fa kowa yayi tsit yana sauraren shi. Tsoho kuwa ya ta'kar'kare yace su maimata abinda zai fa'di, suka ce to.

Yace Abuna Rabbi, Abuna Rabbuka, Hasken madina walaii, ( ๐Ÿค”) kowa dai ya zuba masa idanu kasancewar lokacin ilimi ya fara wadatar su ba kamar kakanninsu ba, nan dai aka matsar dashi gefe akayi yadda musulunci ya tanadar.

Bayan sun dawo kuma aka dasa wata sabuwar al'ada.


Acikin gida kuwa Malama Hakama tana jiran a dawo daga kai malam Ila ta shigar da matar sa takaba.


**** ****

*ASIBITI*


Badaru ne ya zo wurin Malama Ramatu ya samu wuri ya zauna ya fara cewa " Ha'ki'ka Babah ta da ace za a samu iyaye irinki da anyi farin ciki, (a lokacin yasa hannu ya goge kwallar da ta zubo masa) ya cigaba da cewa da ma mahaifiya ta tana nuna min daidai da rashinsa da abubuwa basu lalace min ba Amman inaaa bana samun haka.

Malama Ramatu ce ta juyo Dan sauraren abunda yake fadi.......


*WANENE BADARU*


Badaru dai matashi ne 'Dan kimanin shekaru 32.....

Ku biyoni......


Wai ya zata kaya ne a 'kauyen *Bandass* wurin shigar da matar mamaci takaba? ๐Ÿค”

Ya rayuwar Badaru take kasancewa ne?

Mu hadu a shafi na gaba.


*_Congratulations Nigeria_*



*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป
[4/10, 7:57 PM] โ€ช+234 803 509 6818โ€ฌ: *๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ'DAN GARGAJIYA๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ*

*(gargajiya ba addini bane)*



*Na*

*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*


*20โšœ25*


Badaru matashi ne 'dan kimanin shekara 32, an haife shine a can birnin kahutu, 'kannen sa hudu, uku maza 'daya mace, Allah ya wa mahaifin su Malam Datti rasuwa tun suna yara, kafin rasuwar sa ya ba wa yaran sa tarbiya daidai gwargwado.


Mahaifiyar Badaru mace ce mai tsaurin ra'ayi kuma ga ta da a'kida irin ta mutan Da.

Badaru ya taso mai biyayya ga ilimi mai zurfi musamman na addini, yana da shekara 18 ya sauke Al'kur'ani mai girma. Tun bayan kammala karatunsa na gaba da primary bai samu ya cigaba da karatu ba kasancewar mahaifiyar sa ta 'ki amincewa ya cigaba da karatu wai a cewar ta yahudanci ne, Dan ita mace ce mai akidar *Gargajiya*.


Haka rayuwar sa ta cigaba da wakana, Idan yayi abin bajinta sai ta kushe, idan ya yi wa dangin mahaifinsa alkhairi sai ta 'dau fushi da shi, ga ta da saurin fushi haka yasa Badaru yake gujin 'bacin ranta, tun ba ya bin abin da ta ke so har ya fara ganin daidai ne.


A haka ya dauki 'dabi'ar ta, amma wani lokacin yana kokarin gujewa hakan.

*_kalubalen mu iyaye, mu Sani cewa duk yanda muka bi da 'diyan mu to a haka za su taso, mu tuna cewa fa amana Allah ya bamu akwai ranar kar'ba, mu guji San zuciya saboda wata akida ta daban wanda ba fa'din Allah ba_*


A haka har Allah ya sa suka hadu da Bahijja 'yar gidan Malam Mahmud suka fara soyayya, nan ma an yi dauki ba dad'i kafin ta bari ayi auren.

Bayan auren nasu ta hana Bahijja sakat a cewar ta ba ta biyayya saboda ba ta da irin halayyar gidan, musgunawar yau daban na gobe daban. Wannan kenan......


Malama Ramatu tace Badaru ina jinka ya kayi shiru, nan ya 'dora da cewa " mahaifiya ta ba ta nuna min abin da ya kamata in yi, idan na yiwa iyali na hidima takan nuna min cewar ba dai dai ba ne, ga yawan korafi da shiga hakki, idan na yi magana ta ce ba ni da biyayya, a dalilinta ne na fara kora 'kwaya amma ba ta ta'ba nuna damuwar ta ba, wannan rashin arzikin da nazo nayi anan ma 'bacin rai ne ganin an ta'ba min ita, ina ma..... bai 'karasa ba Malama Ramatu ta dakatar da shi.




**** ****

*GIDAN MAKOKI*

Malama Hakama ce a na'de akan wata tsohuwar tabarma inda ta fara jawabi kamar haka......

Murya a sha'ke ta fara da cewa " Allah ya jikan Ila hakika babban bango ya rushe *_(mata mu kiyaye idan an yi mutuwa, wannan kalmar ba ta dace ba a musulunci)_* yau zaki fara takaba dan haka matso nan ki ji dokokin ta


Inna Habi ce ta matso, nan take tsohuwa ta janyo ta ta zaunar akan wata tabarmar kaba ta na cewa yauwa Habi sai hakuri yanzu dai ki maimaita duk abin da na fadi ta ce to, nan dai ta karanto mata wasu siddabaru da ban samu jiyo wa ba saboda koke-koken mata.

Da farko dai zaki dinga yin sallah kafin lokaci ya yi (๐Ÿค”), na biyu kullum ya kasance akwai tsintsiya a kusa da ke, na uku duk sanda lokacin sallah yayi butar da yake alwala a zuba ruwa aciki, na hudu duk sanda aka gama abinci a zuba a kwanon sa a bayar sadaka, ki dinga cin abinci sosai da man shanu domin takaba ta na cin 'bargo, wanka kuwa sai bayan sati 'daya kuma banda magana da karfi ra'da-rada za a dinga yin ta, kuma kar a bari gashin kanta ya fadi 'kasa ko 'daya.........

*(ikon Allah๐Ÿค”, Alhamdulillahi ala Ni'imatil Islam)*


Ku biyo ni dan jin ya za a 'kar'kare a wannan 'kauyen.


Malama fa da 'Dan nata Badaru har yanzu suna asibiti

Mu ha'du a shafi na gaba




*Ummu Rahma* โœ๐Ÿป
[4/10, 7:57 PM] โ€ช+234 803 509 6818โ€ฌ: *๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ'DAN GARGAJIYA๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ๐Ÿ‘ณ๐Ÿผ*

*(gargajiya ba addini bane)*



*Na*

*Ummu Rahma*
โœ๐Ÿป


*Gajeren labari mai dauke da nishadi, gidadanci da rashin wayewa ta addini*



*25โšœ30*


*_Afuwan masu bin lbrn Dan Gargajiya na jin shiru kwana 2_*


*_JINJINA GAREKI NABILA ZANGO ( MAI NASARA) AM PROUD OF YOU_*



*GIDAN MAKOKI*



..... Malama Hakama ta 'dora da cewa, kuma kitson ma idan za ayi guda uku kawai za a ayi.



Sannan bayan kin gama takaba za ki yi sadaka da abubuwa masu yawa dan murnar fita daga takaba.



Duk wadannan bayanai da ake yi Hinde matar malam Maude tana jin su, takaicin rashin Neman ilimin su yana damun ta kwarai da gaske, duk da cewa Inna Dije (Hakama) ta girme masu sosai hakan bai hana Hinde yi mata gyara ba.



_Tabbas addinin musulunci sauki ne da shi kuma maslaha ce Babba, duk wanda ka ga ya aikata abu ba daidai ba to ka dawo da shi bisa turba mai kyau_



Hinde ce ta fara bayani kamar haka....


.
Ita takaba ba'a shigar da matar mamaci kamar yadda Inna Dije ta gabatar, da zarar an kau da mamaci ita matar tasan da cewa ibada ta hau kanta, domin shima ibada ne, za tayi takaba na watanni hudu da kwana goma, yin hakan zai bada dama a San ko tana tare da rabo (wato juna biyu) wasu malaman kuma sun hadu akan cewa za ayi amfani da zuwan jinin ta na al'ada idan mai yi sau biyu a wata ne, da zarar tayi jini uku to ta gama takaba.



Sannan batun shafa man shanu da cin sa kuma wannan zance ne na mutan Dรก, ita takaba bata cin 'bargo, sallah kuwa akan lokacin ta za ta dinga yi ba kafin lokacin ta ba, akwai wani hadith da yake magana akan cewa *_Duk wanda ya aikata wani aiki ba daga cikin abin da aka umurta ba, za a mayar masa_* sannan idan anti kwana arba'in za ta iya zuwa gaida mara lafiya ko wurin ta'aziyar rasuwa amma banda zuwa gidan biki ko suna, wanka kuma kullum za ta dinga yin abin ta amma ba da sabulu mai kamshi ba, wadannan su ne

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment