Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amintaccen likitan me girma governor yasaka aka masa Alluran b'atar da mutum hayyacinsa"sbd yana so ya haye kan kujerarsa ta mulki.... Abubuwa sosai naban mamaki suka gani"wanda mus'ab ne kawai ke mamakin Amma uban gayyar wato miskilin namiji ko Ajikinsa"bayan sun gama ganin komai "mus'ab yace"yanzun dole yaka mata ka zauna ka nutsu ka had'a duk wasu baya nai da vedios ka tura can sama"nasan ta hakane iyalan governor zasuyi k'ararsa"Shariff beyi mgn sbd kiran fareedah daya gani"rejecting d'in kiran yayi ya zare layin ya karya" dama sbd ita yasaka shi"sai wajen 6 pm yatashi daga office "har zai bar laptop d'insa Anan sai yayi wani tunani yafasa"Ahanya suka tsaya wata super market shariff ya shiga da kansa yazab'oma Amaan wata jibgegiyar teddy"bayan yabiya kud'in sannan yafito driver yakawosa gida"yana rik'e da ledar da teddy d'in keciki ya wuce cikin gidan Anutse....hango Amaan yayi itada Abdallah sunata guje guje yabiyota"kanta bbu ko d'an kwali gaba d'aya jikinta bbu inda baya juyawa"sbd gwont d'in jikinta ta kamata kuma robber ce.....✍️

Adinga sharhiπŸ₯Ή

wannan book d'in na kudine ! idan kina buk'atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❀‍πŸ”₯ *MISKILI NE*❀‍πŸ”₯

*19&20*




.........tsintar kansa shariff yayi dajin fad'uwar gaba had'e da bugawar zuciya"wanda shima besan dalilin jin hakan ba" lokaci guda ya had'e girar sama data k'asa ya tamke fuska bbu Annuri ko kad'an"hakan kuma be hana kyawunsa matuk'ar bayyanah ba"rungume hannayensa Aki'rji yayi ,ya jingina bayansa Ajikin bango yana jifarsu da wani irin mugun kallo....sam Amaan bata lura da shiba sai Abdallah ne ya Ankara dashi"da sauri yatsaya da dariyarsa jikinsa na b'ari"Amaan ta matso tana mik'o masa hannunta tana fad'in kabani Alawana Abdallah kona had'aka da Ammi....lura datayi yayi shiru yasha jinin jikinsa yana kallon wani waje"hakan yasa ta kalli gefen daya ke kallo.....saida taji k'irjinta yabuga! sakamon hango shariff datayi,yayi wata iriyar tsayuwa irin ta zaratan jaruman mazaje" fuskarsa bbu Annuri yana kallon Abdallah.... Atake itama jikinta yayi la'asar dukda Azatonta Abinda sukayi ba laifi bane"saidai yadda taga hamman nata yayi ta tabbatar da laifi sukayi kenan"da sauri Abdallah yaduk'a yana fad'in dan Allah yaya na tuba ka yafemun"wlh laifina ne bbu ruwan Amaan Aciki"uffan sharif bece masaba yana dai duk'e"yayinda Amaan idanuwanta sun ciko da k'wallah"tana tsaye gefe, shariff Azuciye yanufosu ,sbd gaba d'aya Abdallah yafi bashi haushi sbd yasan shi meya keyi"saidai dukda haka itama bata tab'a bashi haushi irin yauba...cike da izzah ya iso wajensu fuskarsa tamkar hadarin gabas"yana isowa ya finciko Abdallah yabashi maruka zafafa guda biyu"Amaan tasaki k'ara tana zaro Ido ta juya zata gudu"tak'i biyu kika komayi ranki ne zai b'aci.... yafad'a cike da gadara yana huci"Amaan bata saurareshiba tayi gaba da sauri"sanin idan ta gudu shikenan bazai hukunta taba yasaka yacika Abdallah yabita"ita kuwa tana juyowa taga ya biyota aguje ta wuce cikin parlourn tana k'walama Ammi kira"jikinta na b'ari"Ammin na fitowa daga kitchen shariff na shigowa cikin parlourn afusace, yanufi Amaan gadan gadan.....ta saki k'ara ta b'uya bayan Ammin tana rirrik'eta"shariff yayi jifa da ledar teddy d'in hannunsa yana fad'in ba cewa nayi kizoba?"yafad'a yana zaro mata idanuwansa da har sun fara jaa sbd bacin rai"wai shariff meke damunka ne?"kabi komai Ahankali mana"menene tayi maka?"shiru yayi yanufi bayan Ammin"Amaan ta koma sakin k'ara tana rirrik'eta....karka tab'amun yarinya nadai gaya maka ko?"yana b'ata rai yace"Ammi kinsan meye sukayi ne idata Abdallah?"shariff fita nace kabani waje"beyi mgn ba yana huci yabar wajen Azuciye batare da yabi takan k'atuwar teddy d'in dake yashe a tsakkiyar parlourn ba"yana haye upstairs Amaan ta sauke Ajiyar zuciya tana saka kuka"Ammi ta jinjina kai tana fad'in jeki d'aki kiyi sallah gani nan zuwa nima"ta fad'a jikinta a sanyaye"hakan yayi daidai da shigowar Abdallah idanuwansa jajir da Alama kuka yayi"kai zonan"cewar Ammi tana nufar kujerah ta zauna"fuskarta Ad'aure tace"meye kukayi kaida Amaan?idan kamun k'arya saina saka sheriff yamaka shegen duka....abu k'arami Ammi Amma yaya ya maidashi me girma "ko itama Amaan d'in yadaketa ne?"ah ah be daketaba ,maza kamun bayani"dama kinsan d'azun na shigo da big boom"saina bata guda nasha guda"ita kuma saita rage"wlh ni wasama nake mata Ammi saina d'auka Ina ce mata yazama nawa"shine tadinga dire dire inata dariya na fita"saita biyoni da gudu saina bata shine yaya yasamemu"wlh saida yamun marukan da jina na wucin gadi ya d'auke.... d'an jim Ammi tayi kafin ta girgiza kanta Afili tace"dama bakada hankali Abdallah?"kanada 18 yrs kake guje guje da mace"muharramarka ce ita?"nan Ibtihal meke be sanar makaba ka kiyaye kanta?" tsakaninka da ita sai gaisuwa" to wlh ka kiyayeni daga yau iya karka da ita gaisuwa kaji Abinda nagaya maka?"uhmm"idan Allah yakaimu da safe ka bashi hak'uri "kasan idan kaje yanzun k'arama kanka laifi ne Awajensa zakayi, tunda ya rigada ya hau kan dokin zuciya! dato Abdallah ya Amsa "maza ka wuce katafi masallaci"yana k'ok'arin mgn Alh yahaya yashigo cikin parlourn da ledoji Ahannunsa"Ammi ta tarbesa da fara'a had'e da yimasa sannu da zuwa"Abdallah kuwa da k'yar ya gaishesa yafita"Alh yahaya Aransa yace"duk na kusan maganinku harda ishashshen d'an zafin kan yayan naku... Amsar kayansa tayi suka wuce d'akinsa....bayan sallar isha'i Amaan na zaune kan Abin salla tayi tagumi hawaye kwance cikin idonta"sbd laifin datayiwa hammanta"Ammi ta shigo d'akin da teddy d'in ta saka cikin ward rope"kafin ta zauna gefen bed tana kallon Amaan had'e da nazarinta"Ahankali tace"Amaan ki tashi kije kici Abinci Azo Ayi shirin kwanciya bacci ko?"na k'oshi Ammi"banganeba?"akan me zakice kin k'oshi?"k'asa tayi dakai tana hawaye"subahanallahi meya faru kuma?"dan Allah kiba hamma hak'uri nadena koma miye karya dakeni"bazai dakekiba Amaan"nima rabona dashi tunda yabiyoki ,zuwa da safe kin bashi hak'uri sannan ya huce"Abinda nakeso dake"daga yanzun karki koma wasa irin haka da Abdallah dama kowane namiji"sannan idan hammanki yace"kidena koma miye, toki dena kinjiko? dato ta Amsa tana tunanin wasan da sukayi itada Abdallah shine laifi"gaba d'aya wani irin mugun tsoron had'uwa da shariff d'in taji tanaji...fargaba da tsoro ya hanata taci Abinci"Ammi dai najin tausayinta tabar d'akin"itama jikinta Asanyaye ta dawo parlourn ta sami Ibtihal zaune tana kallo"sai Alh yahaya da Ammi na dining area yana cin Abinci"tunda yaga Amaan yaketa kallonta"dama y'arsa tasanar masa da labarin zuwanta ta waya"ya kalli Ammi yace"Hjy bak'uwa mukayi ne Agidan?"Eh Alh"da Alama hutu tazo mana ko?"Eh zata d'an jima kafin ta tafi"Allah sarki"ga wannan maganin miyagune da shaid'anu idan zakiyi girki ki zuba duk kowa yaci"yafad'a yana d'an murmushi "haka nan Ammi taji fad'uwar gaba"ta Amshi maganin tana tuna kalaman shariff na kwanaki *nan gaba zaki gane wanene mijinki* Ajiyar zuciya ta sauke ab'oye tana fad'in to shikenan za'a zuba d'in "ya Amsa dato"sai bayan yagama cin Abincin suka bar wajen......Ab'angaren shariff,ransa Ab'ace ya haye upstairs "Aciki yayi sallar magrib da isha'i"ko masjeed be fita, be Amsa wayar kowaba dan sbd a bad mood yake"zai iya samun matsala da kowa idan yace zai Amsa wayar mutane"ko coffee d'in dayake sha be shaba yayi wanka ya kwanta ransa ab'ace yasha Alwashin gobe zai tarkata Amaan ya maida ita gidan mlm da sharad'in yafita daga rayuwarta"da wannan tunanin bacci ya d'aukesa"yayi mafarkin gata nan tanata gudu cikin daji wasu mutane masu bakak'en kaya sun biyota zasu kamata"tanata ihu da kiran sunansa.... adaidai nan yafarka"lokacin karfe 2:17 am"yayi Addua yana tashi zaune yana jin kansa na sarawa kamar zai rabe gida biyu"Amma dayake namijin duniyane haka ya daure ya shiga bath room ya d'auro Alwallah yafito"jallabiya ya d'akko gogaggiya yasaka yafara jero nafilfili"bayan yagama yayi karatun Alkur'ani me girma "sai yaji zuciyarsa tayi wasai dayin sanyi"saidai k'asan zuciyar mafarkin dayayi akan Amaan ne"tunawa yayi da yau Alh yahaya yadawo"hakan yasa ya Isa wajen laptop d'insa ya d'auka yanufi parlourn sa"bayan yagama saita komai ya kunnah yafara kallo"Anan yaga shigowarsa da fitowar Amaan da firansa da Ammi har zuwa maganin daya bata"Anan ya fahimci Alh yahaya yaso yabigi cikin Ammi yaji wata mgn game da Amaan"Amma Bai samu nassara ba"sai kawai yabari da safe zai Amshi maganin"zai kuma bar Amaan Agidan"dan idan tabar gidan to Alh yahaya zai d'auka Asirin yafara Aiki"da wannan tunanin yakoma bed room d'in yad'an kwanta,be jima ba da kwanciya Aka kira sallar Asuba"hakan yasaka yatashi badan baccin ya isheshiba yayi Alwallah ya fita masjeed"yana sakkowa down stairs ya hango Alh yahaya tsaye yana mgn k'asa k'asa kamar haka"ni kuma yallab'ai?"Allah yasa ba laifi nayiba kake kirana da gaggawa haka?....jin motsin takun mutum yasaka yadena mgn yana kallon sharif daya had'e rai kallo be isheshiba"saidai yasha Alwashin idan yadawo Anjima zai duba ta CTV camera yaga da uban waye yake mgn ?"dake nuna Alamar babu Alkhairi Acikin maganar....bayan sallar Asuba shariff ya shigo cikin gidan sbd ya gaida Ammi"fuskarsa Ad'aure ya murd'a handle d'in k'ofar bed room d'in ya shigo.....saida Amaan taji fad'uwar gaba daya shigo taji Amon jarumar muryansa me ban sha'awa"kallon gefen datake beyiba yaduk'a ya gaida mahaifiyarsa"da sauri Amman murya na rawa tace"hamma Ina kwana?"doguwar tsuka yaja ya mik'e tsaye yana yatsina fuska zai fita," Ammi tayi saurin dakatar dashi da cewa....ka jirani a parlour zamuyi mgn yanxun "tamkar ya musa mata ya Amsa dato kawai yafita"Ammi ta kalli Amaan data sunkuyar da kanta ak'asa batace komai ba saidai taji tausayinta"ta rasa shariff wane irin murd'add'en mutum ne?"mik'ewa tsaye tayi ta fice daga cikin d'akin Amaan tasaki kuka me ban tausayi"tama rasa wane irin kalar tunani zatayi"sai tambayar kanta takeyi to ita suwaye iyayenta??"itadai kawai hammanta ta sani Arayuwarta.... sheriff yana zaune a parlourn kan kujerah yayi bala'in had'e rai saicin magani yakeyi"yana ganin Ammi ya kauda kai"gefensa ta zauna tana fad'in sannu ishashshe me walkin sa! toko ubangiji muna masa laifi mu tuba ya yafe mana, balle kai d'an Adam dazaka k'ullaci k'aramar yarinya irin haka"bayan kasan halin data tsintsi kanta"koma dalilin hakan bazaka mata uzuriba?"yaron nan Abdallah tunda dare beda walwala sbd fushin dakakeyi dashi"da ita dashi na musu fad'a, musammun Abdallah dashi yafita hankali"bana zaton idan Amaan a hayyacinta take zata iya Aikata wannan shirmen"sbd haka kayi hak'uri kamanta"duk Abinda bakaso zata dena....Toni Ammi Ina ruwana da koma miye zatayi?"kawai na gama mgn zan mayar da ita wajen mlm taje can su k'arata tunda bata jin mgn kuma batada kunya....oh kuma kace babu ruwanka?"yanzun kuma kace batajin mgn batada kunya"to bari kaji! zaman Amaan Agidan daram babu wanda zai rabamu sai Allah da iyayenta"na rasa meyasa bazaka dena wannan zafin zuciyar nakaba?"tun jiya yarinyar nan batada walwala sbd ta fahimci kana fushi da ita ko Abinci bata ciba"sbd haka yanzun zan turota tabaka hak'uri kanuna ka hak'ura ko ranka yab'aci....pls Ammi basai tazoba kawai ya wuce"banza Ammin ta masa ta mik'e tsaye ta wuce d'aki"babu jumawa yaji y'ar siririyar muryar Amaan na masa sallama"tana sanye da hijab iya gwiwa da doguwar riga ta kanti Ajikinta"saida ya gama shan k'amshinsa sannan ya Amsa fuska a had'e "ita dai tana duk'e gabansa kan carpet cikin rawar murya tace"hamma Ina kwana?"lafiya qlau"ya Amsa da k'yar cikin basarwa"dan Allah kayi hak'uri Akan laifin danayi ,bazan koma ba"banza ya mata ya mik'e tsaye "dan Allah hamma ka hak'ura? miskilin beyi mgn ba sai kallonta yayi yanuna mata k'ofar bed room d'in Ammi"shi kuma ya haye upstairs.....babu wanda yasan fitarsa dan ta baya yabi yafita daya shirya....driver na jansa yana zaune a back sit yana karatun wata jarida"yana sanye da suit red colour sunyi bala'in haskashi"fuskarsa Ad'aure yarasa meye yasaka yaketa jin fad'uwar gaba tunda yatashi??....can kiran mus'ab ya shigo cikin wayarsa"batare daya damuba ya share"dan beson takura"suna isowa office nasu dake cikin gari"tun kafin driver yayi parking sukaga police dasu mus'ab tsaitsaye charko charko"ga uban hayak'i yana tashi Acikin wajen da Alama gobara ta tashi jiya"saidai miskilin bbu wata damuwa Asaman kyakykyawar fuskarsa yafito cikin Isa had'e da shan k'amshi"mus'ab da wani bellow na hangosa suka nufi wajensa"kallo d'aya zakayiwa mus'ab kasan yana cikin tashin hankali"da dara daran Idanuwansa shariff yatsare mus'ab yana nazarinsa"gefen zuciyarsa na harbawa"sharif muje can muyi mgn"shine Abinda mus'ab yafad'a idanuwansa jajir"babu musu sheriff ya bisa abaya suka zauna kan wasu kujeru"ka kalli labarai na k'arfe 7 na safiyar yau?"girgiza kansa sheriff yayi"mus'ab yace Anshiga har cell Ajiya Ankashe Alh tanimu sbd gudun yatona Asirin sauransu"kuma Ina zaton Alh isah ne yasaka Ayi hakan"jiya ta CTV camera na gidansa yaganku kaida y'arsa kuna mgn ,yakuma ga zobban data mik'a maka "hankalinsa yakasa kwanciya sbd yana zargin dama can kai d'an CID ne"Acikin daren sukayi binciken gano number motata dana d'aukeka Aciki"sannan suka gano cewa kayi bincike Agidansa ta hanyar y'arsa"shine yaturo y'an daba sukazo suka yi bincike nan sbd su d'auki vedio ko wani abu damuka samu game da sirrinsu"sukaga bbu shine suka kunnah gobara"shiyasa tun jiya nasanar maka shariff karkayi kuskuran zuwa gidan su fareedah Amma kafiyarka ta hana"yanzun zancen danake maka da Asuba yaturomun y'an daba munyi Artabu dasu"nayi iya bakin kok'arina ganin na kare kaina da iyalaina Abin yaci tura"su biyar suka rik'eni sauran suka d'aurema noory fuska da Ahmed suka tafi dasu"Akan cewar saina kamusu vedio sannan su kyalesu "wlh ko sallar Asuba banyiba tsabar tashin hankalin Dana tsintsi kaina Aciki "bayan fitarsu na shiga mota naje gida na sanar musu "motar yaya na d'auka nazo nan natura Amintattunmu sukaje har k'ofar gidan kamar masu maula"suka d'akko y'an vedios da pics na wad'anda ke shiga da fita cikin gidan "Abin mamaki wlh Akwai Alh yahaya cikin wad'anda suka fito daga cikin get d'in gidan suka shiga mota"yanzun Abin tashin hankali tayaya zan iya Amso matata da d'ana a hannun wa'annan Azzaliman shariff? kuma kasan koda munyi report baza'a yardaba sbd bbu shedar cewar Alh isah ne yaturo.... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! shine Abinda sheriff ya furta yana furzan da wani irin zazzafan huci daga bakinsa "zuciyarsa na tunano masa wayar dayaji Alh yahaya nayi da Asuba"sannan ya lura daya dawo daga masallaci bbu motarsa haraban gidan"ya kalli mus'ab da idanuwansa ke jajir yace"zo muje"Ina zamuje? gidan mu"muyi me a can kuma?"shiru yayi yak'i mgn"pls sheriff bafa lokacin k'yaliya bane yanzun kamun bayani mana...zan binciki CTV camera d'in dake gidan, sbd d'azun naji Alh yahaya yana wata waya"kaga idan Akwai saka hannunsa shine kawai zan kama da hannuna zan masa azabar da bbu shiri zai sanar mana inda bilkisu da Ahmed suke.... mus'ab na kok'arin mgn kiran Ammi ya shigo cikin wayar sheriff "wanda bugawar zuciyarsa tayi daidai da shigowar kiran"mus'ab yace"pls ka d'auka kaji waye"yafad'a sbd ganin sheriff ya tsare wayar da Ido yana kallo"beyi musuba yad'aga"tun kafin yayi mgn yaji muryar Abdallah yana fad'in yaya koka fita kaida Amaan ne munata nemanta bamu gantaba?"shine Ammi tace"na kiraka naji ko kuna tare ne??.....✍️

❀‍πŸ”₯ *MISKILI NE*❀‍πŸ”₯

*21&22*




.......what?? shariff yafad'a da k'arfi yana jin zuciyarsa na wani irin tsinkewa! fuskarsa da muryarsa bbu alamar rahama acikin su da wani irin tone yace"da gaske kakeyi abdallah?"daga d'ayan bangaren abdallah yace"wlh da gaske ne yaya....d'it! sheriff ya yanke wayar yana furzan da wani irin mugun huci me matuk'ar zafi daga bakinsa"meke faruwa kuma?"cewar mus'ab yana binsa da kallo"atak'aice shariff yasanar masa abinda ke faruwa"kafin yace"ayau zan kawo k'arshe alh yahaya da auresa da mahaifiyata, bayan na nunawa duniya da ammi wanene shi"yafad'a ahassale....cikin k'ank'anin lokaci shariff ya juye yakoma tamkar wani jan zaki"idanuwansa suka juye sukayi jajir"abinka game zafin zuciya"be tsaya sauraren driver yajasuba yafad'a cikin motar shida mus'ab "a haukace yaja motar cikin k'ank'anin lokaci suka iso gidan su"horn kawai shariff yaketa dannawa babu k'ak'k'atawa "tuni yakoma hassala"ana bud'e get d'in ya zuro kansa ta glass ya kalli get man agadarance yace"kaje na sallameka tunda baka san aikinka ba"yafad'a yana danna hancin motar cikin gidan"mus'ab kasa mgn yayi"tambayar kansa yakeyi shin duk sbd akan amaan d'in ne shariff ya canza haka ko kuwa?? be gama wannan tunanin ba sukaji k'arar shigowar text message acikin wayar shariff babba"lokacin kuma k'arfe 10:37 am"da sauri shariff daya gama parking zai fito yazaro wayar yafara dubawa kamar haka.... *kai d'an zafin kai! abinda mukeso dakai shine kayi gaggawar kamana duk wasu vedios dakasan kasamu game damu"basai mun maka dogon bayaniba"idan baka kawoba zamu kashe yarinyar nan bayan mutum 10 sunyi raping d'inta "bayan haka kuma zamu d'auki mahaifiyarka da k'aninka*.....k'aryane wlh! in har ban amso amaan ayau ba bancika d'an halak ba"cewar shariff cikin dakakkiyar muryarsa yana yin wurgi da wayar batare daya ida karanta text d'in ba har k'arshe"atake wayar taci screen "kallonsa kawai mus'ab keyi yanata huci"kafin ya d'auki wayar yaduba yagani"ya girgiza kansa yace"matsalar private number ce ,ba zamu iya kira ko tracking ba"tabbas duk sune suka sacesu"shariff beyi mgn ba yabud'e k'ofar yafito"shima mus'ab yafito rik'e da wayar yabi bayan shariff suka wuce interest d'in shiga cikin gidan.....tsaye carko carko yasami ammi da abdallah da jummai da laure masu aiki"suna ganin sheriff kowace tabar parlourn jiki na kirma"dan sun tabbatar da azuciye yake,ya koresu k'aramin aikinsa ne"kallonsa kawai ammi keyi aranta tana furta innalillahi wa inna ilaihir raju'un"sbd yadda taga fuskarsa ta tabbatar yana kan dokin zuciya"abdallah yayi saurin cewa yaya koka san inda taje ne?"banza shariff yamasa"ammi ta amsa gaisuwar mus'ab"duk suka zauna kan kujerah mus'ab yashiga yima ammi bayanin komai harda tashi matsalar"saidai besanar mata ga wand'anda suke zargi ba"kuma be fad'i turo text message ba"ammi! ibtihal na nan?"cewar shariff da k'yar yana kallonta da jajen idanuwansa "ah ah ta tafi skul"mahaifinta fa?"shima benan, dan tun asuba yafita be dawo ba har yanzun...sharif ya kalli mus'ab ya gyad'a masa kai kafin yace"pls ammi ki kira alh yahaya ki nuna damuwar kinga baya nan "daga nan zakiji zai dawo nan ko kuwa?"akan me zaka saka na masa hakan?"pls ammi zan miki bayani bayan kin kira d'in"batace komai ba ta d'auki waya ta nufi d'aki"shariff da mus'ab suka wuce upstairs"komai shariff ya had'a ahanzarce kafin ya kunnah laptop d'in"sai ga alh yahaya yana waya bayan fitar shariff d'azun da asuba.... yallab'ai mun rabu jiya kuma yau kana son ganina kuma?"sai kuma yayi shiru"can yace"tabbas mahaifiyarsa nake aure sbd dukiyarsa da wacce suka gada wajen ubansu"dama na jima ina zaton kamar police ne, shine zai shiga gonarka?to karka damu zanzo muyi mgn yanzun"amma bana zaton zai saki vedio d'in dan yanzun"akwai wata yarinya danake zaton uwar zata had'ashi aure da ita "ita yaka mata asato atsoratar dashi koya kawo vedio d'in koku kasheta"kuma ko bayan yakawo vedio d'in zaku bibiyesa sbd zai iya seving d'inta ya ajiye"bara dai nazo yanzun.....kashe laptop d'in shariff yayi ya zaro k'aramar wayarsa yana huci yasaka kiran me gadi"bugu ukku ya d'auka yana magiyar ayi hak'uri bisaga laifin dayayi...tambayarka zanyi! kalmr da shariff yafad'a kenan atak'aice "to inaji yallab'ai "da asuba waye ya fita ,kuma waye yadawo?"to gaskiya alh yafita yadawo kuma"sannan bayan fitarka da safen nan yakoma fita"kashe wayar shariff yayi yabi mus'ab da kallo yana fad'in yadawo ammi bata saniba, anan kuma yayi dubarun yadda yayi yasace amaan"damuwata mus'ab kar y'ar mutane ta salwanta ko wani abu marar kyau yafaru da ita"bansan yazanyi ba idan hakan yafaru?"ban tab'a dana sanin shigowar ta rayuwataba sai yau....ya isa shariff karka zobe ladanka "karka manta haka allah yatsara tun kafin zuwan gudanmu duniya! shariff ya mik'e tsaye yana fad'in ina zuwa"fita yayi daga cikin parlourn ya sakko down stairs"ammi da abdallah na zaune da sauri tace"na kirashi yacemun yana kasuwa amma yanzun zai dawo yayi wanka" to shikenan ammi taso muje ciki kiga wani abu"kai kuma ka zauna anan koda ya shigo ka kirani"yafad'a yana kallon abdallah "dato ya amsa "ammi da shariff suka wuce upstairs......komai ammi ta gani da idanuwanta"salati kawai takeyi tana dafe da k'irjin ta"cikin wani yanayi tace"allah ya isa tsakanina da alh yahaya "dama abinda yake k'ullamun kenan batare dana saniba?"kinyi amfani da maganin ammi?"ah ah sbd ban yarda da maganin ba"yanzun damuwar, wane hali amaan take ciki....kiran abdallah daya shigo wayar shariff yasaka ammi tayi shiru"d'auka shariff yayi batare dayayi mgn ba"abdallah yace"yaya yadawo yana d'akinsa"kashe wayar shariff yayi yana kallon ammi yace"ammi muje"batace komaiba ta tashi ta fita cikin tausayin d'an nata"sai yanzun ta fahimci dalilinsa nak'in amincewa da aurenta da alh yahaya"shariff kuwa bed room d'in sa yakoma ya d'akko bindigogi guda biyu yasaka cikin aljihun wondonsa"sannan ya d'akko ankwa yafito"mik'ama mus'ab ankwa d'in yayi suka fito"abdallah dai na zaune yanata kallonsu"ammi kuma tayi tagumi"ammi kije kice yafito ina son mgn dashi"daga haka shariff yanufi bakin k'ofar fita shida mus'ab suka tsaya..... ammi na shigowa cikin bed room d'in ta samesa zaune da jallabiya ajikinsa da alama wanka zai shiga"yanayin yadda yaga fuskarta saida gabansa yafad'i"hjy lafiya dai ko?"yafad'a batare daya amsa sallamar taba"da sauk'i dai"amaan ce ta b'ata bamusan inda takeba"to shine shariff dukya tashi hankalinsa yana parlour muje kad'an taushesa dan allah"subahanallahi! ko wani wajen ta tafi ne? yafad'a hankalinsa nad'an kwanciya"ammi batayi mgn ba, ta masa wannan dubaran sbd ba gaskiya ce da shiba zai iya kiran miyagun yasanar musu ga shariff nan nason mgn dashi..."atare ita dashi suka shigo cikin parlourn......wani irin mummunan fad'uwa gaban alh yahaya yayi dayaga shariff tsaye da mus'ab suna jifarsa da mugun kallon da yasaka y'an hanjin cikinsa hautsinawa"shariff na huci yanufi gabansa"yaja baya da sauri yana fad'in lafiya dai?"shariff beyi mgn ba ya fincikosa yana bashi wasu punchers guda biyu gefen fuska"atake bakinsa yafashe! cikin azaba yace"hjy agabanki d'anki zai dakeni kina kallo?......da k'arfi shariff ke taune lip nasa na k'asa da yayi jajir "zuciyarsa takai mak'ura wajen fusata yace"gidan ubanwa kakaimun amaan?"da kuma matar mus'ab?"karma kanuna wani abu ko ki fad'in gaskiya" duk naji wayarku gara tun da sauk'i kasanar kona datse y'an yatsun hannunka yafad'a yana turashi da k'arfi, yafad'i kansa yabigi tayis"yazaro bindiga yadaki gefen kansa cikin karaji yace"baza kayi mgn ba?"suna get house d'in alh isah tafashiya dake can g r a layi na karshe"daga hannun haggu gida me red d'in get"idan kayi k'arya bazaka tsiraba"kuma haka idan gaskiya ka fad'a"inaso yanzun kasaki mahaifiyata kona harbe maka k'afa..... ammi na kuka ta karb'e zancen da cewa allah ya isa tsakanina dakai"kaci amana ta"da k'yar bakinsa na jini yace na sakeki saki biyu"mus'ab ya matso ya d'aura masa ankwa"shariff kuwa dr mansoor yafita yakira, yasanar masa yazo da wata allura.......(bazan fad'i sunan taba)bayan sun gama wayar yadawo yana bin alh yahaya da mugun kallo yace nafiku iya mugunta"muddin kamun k'aryar inda suke naga ba nan sukeba saina yanke maka harshe"ya kalli ammi yace"ammi kamun wayarsa"dato ta amsa taje ta d'akko"shariff yashiga phone"yaga number d'in da alh yahaya yayi waya da ita da k'arfe 5:48 am"d'aukar number d'in yayi awayarsa ,kafin yasaka wayar alh yahaya cikin aljihu"hakan yayi daidai da shigowar dr mansoor cikin parlourn "bayan sun gaisa da ammi shariff ya amshi alluran"bbu tausayi ya matsa ya dakama alh yahaya ita gefen kafad'arsa"yasaki k'arar azaba....cikin second 50 yakoma kamar gawa"mus'ab da shariff suka d'aukesa suka kaisa wani d'aki suka rufe da key"kafin su nufi side d'in shariff ta computer sukayi tracking number d'in da alh yahaya yayi waya da ita"sai gashi sunga inda daidai yafad'a musu me number yake... bayan sun fito ammin na tsaye tace"shariff miye amfanin yimasa haka kuma?kaida yaka mata ku makashi cell "karki damu ammi, ammasa hakane kafin muje mudawo"barinsa yana numfashi koda yana a cell akwai had'ari"wannan alluran zatayi kusan awa 6 zuwa 7 ajikinsa kafin yadawo hayyacinsa"to ina zakuje?"police station! (yamata k'arya)"mus'ab kuzo muje"abdallah ka zauna tare da ammi ko ina kasan akwai security bbu abinda zai faru"yafad'a yana k'arema parlourn kallo "be tab'a zaton yadamu da amaan ba sai yanzun"dan gaba d'aya wani iri yakeji,dabai gantaba ko yaji motsinta agidan ba "fatansa allah yasa basuyi mata komai ba"suna fitowa shariff ya kalli mus'ab yace"nifa can zanje yanzun komai zai faru saidai yafaru!ya fad'a yana huci" wai kai kad'ai shariff? ka bari musanar office aturo mana wasu police ko?"girgiza kansa sheriff yayi cikin wani yanayi yace"fad'uwar gaba asaran namiji! kuma har abada matsoraci bai tab'a zama gwani"bazan dogara da kowaba sai allah da kuma kaina"sbd haka bbu shegen danake shakka koda ta sanadin hakan zan rasa rayuwata bazan damuba"yafad'a batare daya jira cewar mus'ab ko dr mansoor ba yayi gaba kamar zai tashi sama"dr mansoor yayi mamaki"mus'ab kuwa beyiba sbd yasan fahad shariff kaifi d'aya ne"baya tsoro balle shakka"dukda shima ba tsoronsu yakeyiba,beso garin ceto ran iyalansu su duka su rasa nasu rayukan gaba

Please Login or Register in order to submit comment