Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai shariff daya lumshe idanuwansa yana jin rad'ad'in ciwon ya ganta gabansa tana hawaye tana fad'in" hamma nah! meye yaji maka ciwo ?"sannu! bara na dafe maka wajen kar jininka yak'are"ta fad'a tana kuka had'e da kok'arin dafe masa gefen yatsan"shariff dake kallonta da tsantsar mamaki ya janye k'afar tasa gefe da sauri, yana girgiza mata kansa beyi mgn ba "hakan yayi daidai da isowar Ammi"bayan ta mik'a masa ta kalli Amaan tana fad'in kukan meye kikeyi?"ba hamma bane yaji ciwo"Ammi na murmushi tace"bansan zaki damuba daban sanar miki ba Amaan"ta fad'a tana tsintse glass cup d'in daya mutu tabar parlourn "shariff kuwa Anutse yazuba hydrogen d'in jikin cotton yashafa Asaman ciwon"sai gashi ya tsane jinin kuma yatsaya"Amaan dai na duk'e gabansa tana kallon yatsar"Ahaka yaji sallamar Abdallah"yabi gashin Amaan da yaji gyara da kallo"kafin ya zare pasincap d'in dake saman kansa ya aza mata saman kanta da sauri yana fad'in taso kidawo nan ki zauna"to hamma kadena jin zafin ?"kansa kawai ya gyad'a mata "yah Allah kabama hamma nah lafiya! ta fad'a tana d'aga hannu sama"shi mamakinta kawai yakeyi"be tab'a zaton zata iya kuka sbd shiba"saiya kalleta murya can k'asa yace"keda kike fushi dani shine harda yin wani kuka sbd naji ciwo?"toba na hak'ura bako?"kumafa lafiyarka ta fimun komai mahinmanci hamma"sosai yaji kalamanta na dukan zuciyarsa yana kallon ta babu ko k'iftawa"dan wannan kalmar tata ta wuce ace yarone yayita....yaya shariff kanada bak'i suna a parlourn bak'i "okay yafad'a yana kallon Amaan"kamar bazaiyi mgn ba can yace"tashi kije ki kwanta"ki kuma saka hula ko d'an kwali"to hamma ka bani wannan hular?",kansa yagyada mata"sai kuma tace"to yajikin naka?"nifa Amaan lafiyata qlau"yafad'a yana kallon gefen da Abdallah yake"yaga su yake kallo"harara ya watso masa yana mik'ewa tsaye "itama Amaan saita tashi tsaye ta nufi d'aki"shariff kuma yafita waje"sai wajen k'arfe 10:11 pm yadawo ciki"bbu kowa a parlourn"matsawa yayi yafara knocking Abakin k'ofar bed room d'in Ammi"jin shiru ba'a yi mgn ba yasaka ya murd'a handle d'in k'ofar ya shigo"d'akin da haske"Amaan na kwance gefenta na dama"ta saka hula ga wacce yabata rik'e A hannunta da Alama wasa takeyi da ita bacci ya kwasheta "tsaye yayi yanata kallonta can ya matsa yatofeta da addua,kafin yaja devut yarufe mata jikinta.....yana d'ago kansa Ammi na fitowa daga bath room"sosai yaji nauyin ganinsa d'akin datayi"saiya basar yana shafa kansa yace"Ammi zanje Abuja da safe insha Allah "Akwai Abinda zanyi ne Acan"Amma ta jirgi zan tafi da k'arfe 8 na safe zan wuce"wani abu zakayi Acan?"gidan mai na dake a can Ake kok'arin rufewa"subahanallahi! to Allah yakare"ya Amsa da Ameen yafita....washe gari da Asuba daya dawo daga masallaci ya shigo gidan"Abin mamaki Amaan na zaune parlourn da dogon hijab Ajikinta "tana ganinsa ta mik'e tsaye tana fad'in hamma ya jikin?"shifa harga Allah yama manta da wani ciwo da yaji saida yaji tayi maganar....hamma dan Allah kamun mgn kodai Asibiti zakaje??"girgiza kansa yayi cikin sanyayyar muryarsa yace"Amaan bakya gajiya da shirme ko?"nifa daga masallaci nake"karki damu tuni na warke"to Ina kwana?"lafiya qlau "kije ki koma kwanciya kiyi bacci....kafin tayi mgn Ammi ta shigo cikin parlourn"shariff yaduk'a ya gaisheta"ta Amsa da kulawa tana kallon Amaan tace"dama nace miki kidena damuwa shida ciwon ke jikinsa kilanma ya manta"ka ganta nan tunda na tasheta taketa faman tambayar ka warke ciwon?"shinefa muna gama sallah tace mun zataje ta gaisheka"shariff dai na duk'e yana sauraren kalaman Ammi"wanda Azahiri zaka d'auka bema damuba"Amma Abad'ini mamakin yadda yarinyar ta damu dashi har haka yakeyi.....tashi muje ki d'an kwanta ko?"muryar ammi ta katse masa tunani"Amaan batayi mgn ba tadai kalli shariff da shima ita yake kallo"saidai shi suna had'a Ido ya d'auke kansa ....shima be zauna a parlourn ba "side nasa ya wuce yafara shiri"sai wajen k'arfe 8:5 am ya sakko down stairs d'in"yana ta zabga daddad'an k'amshin sa me kashe jiki"kallon second 3 yayima parlourn ya lura bbu Amaan Aciki "wanda saida yaji fad'uwar gaba daya tunata"kuma shi kansa besan meyasa yatunata d'in ba"yana sanye da k'ananun kayan da sukayi matuk'ar dacewa da kalar fatar jikinsa "yayi kyau harya gaji"dukda fuskar tasa kamar koda yaushe d'aure take"Ammi dai na kallonsa Aranta tace"mutum har mutum Amma yak'i Ajiye iyali"ita yanzun rashin k'inyin Auren nasa harya fara bata tsoro"koda sadeeq be sanar mata yana soyayya ba ta fahimci shi yafishi kula mata da sunan soyayya....ganin yazo ya zauna yanata danne danne Awaya yak'i yin mgn yasaka ta girgiza kanta kawai tace"kaje kayi break fast mana"No Ammi zanyi Acikin jirgi ne"iya Abinda yafad'a kenan Atak'aice"tasan ba mgn zai komayi ba hakan yasaka tace"Acan zaka kwana ko yau zaka dawo??"idan matsalar batayi yawa ba yau zan dawo"idan kuma da matsala sosai Acan zan kwana"to shikenan Allah ya tsare hanya yabada nassara Ai bama fatan matsala shariff"koda kadawo bamunan muna wajen suna na hafsat(y'ar k'anwarta) kamar bazai tanka ba sai kuma yace" keda waye zakuje?"da Amaan mana"tunda kasan ba skul ko islamiya take zuwa ba"haka nan yaji beson Ammin taje tare da ita"sannan kuma zuciyarsa nason jin Ina Amaan d'in take?Amma miskilancin sa yahanashi ya tambayata"mik'ewa tsaye kawai yayi fuska bbu walwala yace"pls Ammi ki barta gida"zuwanku da ita wasu zasuyita tambayar ita d'in wacece?"daga haka yayi shiru ya nufi k'ofa"kamar tace" ya jira Amaan tazo suyi sallama Amma sanin halinsa tana iya masa mgn yace A k'yale Amaan d'in yasaka ta barsa......lokacin daya iso parking lot harma body quards nasa da driver nasa sun zama on ready"cikin girmamawa Aka bud'e masa back sit yashiga"yana zama kiran mus'ab na shigowa cikin wayarsa"ya d'auka da sallama"Ina tayaka murna Abokinah bisaga nassarar dakayi wajen bincike"kaji dai Alh Isa yau Anyanke masa hukuncin kisa ko?"d'an tab'e baki yayi yace"ban saniba! Okay Ai yau Aka sanar A news d'in safe"okay"pls sheriff dan Allah kaduba lamarin da Dr Mansoor yake ciki game da Amaan ka tausaya masa"wlh yana cikin wani hali game da soyayyar yarinyar nan"sannan bana so na sanar masa ta yadda kasameta sbd idan nayi hakan sai naga kamar na tona Asirin kane......✍️


wannan book d'in na kudine ! idan kina buk'atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

❤‍🔥 *MISKILI NE*❤‍🔥

*27&28*





..........So what idan kafad'a masa wacece ita?"nace sai me?yafad'a Aharzuk'e yana jan doguwar tsuka, ya yanke wayar cikin zafin rai tun kafin mus'ab yasami damar furta masa wani abu"sai huci yakeyi yana jin ko Dr mansoor zai iya rasa ransa sbd Amaan bazai tab'a taimaka masaba dan ta soshi balle harya mallaketa"sbd Aganinsa wannan Ai cin Amana wa matarsa ne Dr Mansoor yayi! duk yadda yaso ta sukayi Aure shine yanzun harya hararo wata"idan taji maganar Ai bbu dad'i"shiyasa da yawan mata ke cewa wa" mazan basuda tabbas ,kuma maciyan Amana ne mayaudara"da wannan yanayin suka iso Airport"ko a be cewa body quards nasaba da PA d'insa da driver, yayi gaba ya shige jirgi sbd ransa Ab'ace yake"ko break fast d'in da yayi tunanin zaiyi a cikin jirgin k'inyi yayi"sai wajen 11 am ya sauka....saida yafara zuwa masaukinsa yayi wanka ya huta,yyi waya da Ammi"yasanar mata sun sauka lfy"yanaso ya tambayeta ina Amaan? Amma yakasa"sai bayan sallar Azahar sannan yafito yatafi yayi Abinda yakawosa garin"be samu Aka gama solving problem d'in ba saida yamma hakan yasa dole Anan zai kwana"yana ganin kiran Dr Mansoor dana mus'ab duk ya musu banza yak'i d'agawa"yakuma sha Alwashin muddin Dr mansoor zai damesa game da zancen Amaan zai rufe Ido yamasa Abinda zaiyi matuk'ar mamakinsa.....bayan sallar isha'i yana kwance saman wani luntsumemen bed da yaji shimfid'u na Alfarma "yana sanye da wondo 3 quarter da t shirt me gajeran hannu"kasancewar sucan garin ba'a musu sanyi"pillows guda biyu na rungume Atsakkiyar k'irjinsa"yayinda kyawawan idanuwansa ke A lumshe yana sauke Ajiyar zuciya Anutse "wayoyinsa guda 3 na zube saman bed side drower sai ringing sukeyi yamusu banza"gaba d'aya kewar Amaan ce Aransa "duk yadda yaso yabasar ya manta da ita Amma zuciyarsa tak'i yarda hakan"sai koma bujuro masa da tunaninta takeyi"kunnuwansa na juyo masa sautin siririyar muryarta datake masa surutu"gaba d'aya Abinda yafaru daren jiya game da ciwon da yaji shine ke yawo a k'wanyarsa"sai yaji kamar yakira Ammi yace Abama Amaan"sai kuma yaji bazai iyaba....can yaja tsaki Akaro na bbu Adadi yana mik'a dogon hannunsa me cike da zara zaran gashi bak'i ya d'auki baby nokia d'insa"contact d'in Abdallah ya lalibo...k'arfe 8:47pm kiran shariff yashigo cikin wayar Abdallah dake zaune a parlourn yana kallo"sai Amaan dake zaune can gefe"Ammi kuwa tana d'akin ta"bugu biyu Abdallah ya d'auka yana fad'in yaya d'azun na kiraka dan naji lafiyanka shine kak'i d'auka ko?"shariff ya yamutsa fuska yana fad'in kasan bana son yawan k'orafi ko?"hakane Ina wuni?"lafiya qlau "Ina Ammi?"tana d'akinta"d'an jim yayi sai kuma yace" "Amaan fa?"gata nan zaune tanata fushi sbd taga baka dawoba"shine ta tambayi Ammi kana Ina? Akace mata tafiya kayi"shine tasha kuka kamar wata yarinya, sannan tanata fushi ko Abinci bata ciba..... Ayya maza bata wayar"yafad'a batare daya san yama furta d'in ba"Abdallah ya kalleta yaga hankalinta bama wajensa da wajen TV yake ba"Anty Amaan!yakira sunanta" d'ago kanta tayi ta kallesa batayi mgn ba"ya mik'e tsaye yana fad'in ga yaya yace abaki kuyi mgn"wai hamma nah?"shariff dake sauraran y'ar muryarta yasaki d'an murmushin gefen baki yana jiran yaji meye zatace idan Ance shine"Abdallah yace Eh shine"kukan shagwab'a tasaka tana Amsar wayar"Abdallah dai na kallonta yana tunanin to ita meyasa batada waya?....Amaan kuwa k'in mgn tayi sai k'ananun kuka irin na zallar shagwab'a takeyi"can shariff dake sauraronta ya gyara zamansa yana fad'in ya Isa haka sarkin rigima! ko wani abun kikeso ne?"cikin yarinta tace"hamma bakai bane katafi kabarni ko?"karki damu gobe fa zan dawo"shine kuma ni baka sanar mun zakayi tafiya ba?"Amaan dama haka kike da k'orafi?"yanzun fad'amun me kikeso gobe na siyo miki tsaraba?"komai dai inaso hamma nah"Amma ka siyamun kayan wasana kaji?"murya can k'asa yace" duk zan siyo miki"to harda irin turarenka nakeso"zan siyo miki Amma da sharad'in kije yanzun kici Abinci saiki kwanta ko?"to hamma kai yanzun kana Ina?"shiru yayi yak'i mgn "Abdallah ga wayarka tunda bazaiyi mun mgn ba"duk shariff najinta kafin yayi wani abu Akai ta mik'ama Abdallah wayar tanufi dining area "jin Abdallah na fad'in hellow yaya! yasaka shariff ya yanke wayar "gaba d'aya jin zuciyarsa yakeyi tana son cigaba da jin muryar Amaan....da wannan tunanin yayi bacci"washe gari kuwa yana gama kimtsawa ya wuce yima Amaan shopping "kaya yashiga jidar mata na ban mamaki"harda kayan kwalliya da irin turarukan dayake Amfani dasu"ya zab'armata wata teddy me kyau"koda yaje sashen da y'an kunne da sark'a suke haka yadinga jidar mata da set d'in kayan gyaran gashi...... k'arfe 2:45 pm shariff ya iso katafaren gidansu"yaransa na rik'e da ledojin kayan Amaan da tsarabar kayan fruits dayayima Ammi Ahanya"yaran suka fara shiga da kayan shi kuma ya shigo yana waya....jummai me Aiki ce da Amaan zaune Acikin parlourn suna kallo"ihun murna Amaan tasaki tana tasowa ta nufesa tanata dariya had'e da murmushi"saida ya rintse Ido sbd jin ihun nata"ta k'araso gefensa kamar zata shige jikinsa tana fad'in oyoyo hamma nah! Allah har na d'auka sai wata goben zaka dawo"ta k'are maganar tana bin kyakykyawar fuskarsa da kallo"shima ita kawai yake kallo"k'asan zuciyarsa yana jin dad'in yadda take shiga ta mutunci tana rufe jikinta"dan Ayanzun ma mini hijab ce Ajikinta da sabuwar doguwar riga ta Atamfa"ganin yak'i yimata mgn saidai yayi tsaye kawai yanata kallonta yasa ta kwashi fili zata kama dire dire gashi yana lura jummai me Aiki nata kallonsu"hakan yasaka ya d'aure fuska tamau yana fad'in koki nutsu ko kuma Allah na b'ata miki"wuce ki d'auki ledojin can farare"nawane hamma?"kansa ya gyad'a mata "jummai ta matso ta duk'a tana gaidasa had'e dayimasa sannu da zuwa"ya Amsa Atak'aice,Amaan dai ta matsa wajen ledojin tana d'auka da k'yar sbd sun mata nauyi "hakan kuma yayi daidai da fitowar Ammi daga cikin kitchen"tana sanye da kaya na Alfarma Ajikinta"fuskarta d'auke da murmushi tace "koda naji nasan kaine kadawo tunda naji murnan Amaan"Shariff na d'an murmushi yakarso yaduk'a yana fad'in Ammi Ina wuni?"nasameku lafiya? Alhmdllh shariff"tafada tana zama yafara yimata bayanin yadda yashawo kan matsalar"yana satar kallon Amaan da farin ciki yak'i b'oyuwa saman fuskarta"tana d'auke da leda guda"da nufin taje takai tadawo takoma d'auka"Ahaka Abdallah yashigo dawowarsa kenan daga skul"bayan yayima shariff sannu da zuwa yanufi dining area da nufin zaiyi lunch"Ammi ta kallesa tana fad'in Akwai dambun nama da Amaan ta Ajiye karka tab'a mata"to Ammi meyasa bata ciba ta Ajiye?"nidai gaskiya idan yamun zan d'iba.....meye zaka d'iba?"yaji muryar Amaan data fito daga cikin d'aki ta tsintsi maganar"dambun nama mana"b'ata fuska tayi ta kalli shariff da ita yake kallo yana ganin zata kallesa ya janye idanuwansa Akanta "hamma ka ganshi ko?"jeki kwashe tsarabarki yaje yad'iba idan zai iya"cewar shariff fuska a gimtse"to dama hamma kaina Ajiye mawa danaga Ammi bata Ajiye maka ba saina hak'ura na Ajiye maka ko?"kasa mgn shariff yayi dukda k'asan zuciyarsa mamakin yadda yarinyar kullum ke k'ara damuwa dashi yakeyi"ita kuwa jin beyi mgn ba saita wuce ta d'auki gudar ledar ta koma d'aki "Abdallah kuwa yanata d'acin rai yaje yazuba Abinci yadawo cikin parlourn ya zauna"yayinda uban gayyar ya mik'e tsaye ya d'auki tarkacensa ya haye samansa.....Amaan na zaune tsakkiyar carpet ta baza kayan shopping d'in tanata dubawa"teddy d'in na rungume Ajikinta tana fad'in nasamu y'a! sai kuma ta d'auki turarukan tanata faffesawa Ajikinta "Ahaka Ammi ta shigo tana kallon ta tana kallon kayan tayi shiru kawai"saidai tasha Alwashin yimasa mgn yarage wannan facakar dayake mata da kud'i "bayan bata hayyacinta ,wasu Abubuwan ma batasan yadda ake Amfani dasuba.... Ammi kinga hamma ya siya mun?"nagani Amaan"kingode sosai"yanzun ki tashi kimayar a wardrobe duk idan zakiyi Amfani dasu saiki d'auka ko?"Amma ki cire kayan kwalliyar ki Aza kan mirror da socks d'in idan zaki saka saiki d'auka "dato ta Amsa komai ta fidda sannan ta mayar dasu cikin ward rope"Anan taga teddy d'in da shariff yatab'a siya mata a kwanaki"Ammi dake lura da ita tana kallon teddy d'in sai cewa tayi"ki had'a da ita duk nakine"sosai Amaan farin cikinta yak'i b'oyuwa "bayan tagama Adana komai ta d'auki teddy d'in guda ta fito main parlour ta zauna ta azata saman cinyarta tana mata wasa harda surutu......Anutse yake sakkowa down stairs d'in"yana sanye da bakar shadda wacce akayima Aiki da golden d'in zare"ya Aza golden d'in hula me zanan bak'i saman kansa"yayi wani irin kyau kamar Ango"hannunsa guda na zube cikin Aljihun rigarsa"tunda yafara doso parlourn yalura da Amaan da Abinda takeyi"ita kuma daddad'an k'amshin turarensa ne yakaima hancinta ziyara"ta juyo da sauri idanuwanta danashi na sark'ewa"hamma! Uhmm"kaci Abinci?"kansa ya girgiza mata"to meyasa?"wanka naje nayi sarkin tambaya"yafad'a yana zama kan 2 seeter "Amaan ta taso ta zauna gefen sa har saida yad'an matsa sbd kusancinsu yayi yawa"hamma kayi kyau sosai"shiru yayi yana dai sauraron ta"kaji?"kema kinyi kyau *Amaan shariff* Amaan Shariff?"ta tambaya"kansa ya gyad'a mata yana tab'e baki yace"koba ita bace?"uhmm! To shikenan thank you! daga haka be koma mgn ba yana maida hankalinsa a waya yana kallon yadda mutane keta post d'in Alh yahaya da Alh Isa a face book"Anata kace nace game da hukuncin da aka yanke musu"Ibtihal da fareedah nata zage zage....hamma ! tashi muje kaci Abinci na baka dambun naman"kansa yad'ago ya kalleta yace"bazan ciba"meyasa hamma?"sbd k'azama ceke bakya wanka sosai"saufa 3 nakeyi kullum"tab'e baki yayi yak'i mgn saiya mik'e tsaye yanufi wajen dining table"ita ma saita biyosa taja kujera ta zauna"kinci Abinci?"uhmm uhmm! be tambayeta dalili ba yazuba mata plate guda yatura mata gabanta yana fad'in oya kici Abinci"to hamma zakaci dambun naman?"oh my God! zanci Amaan dan Allah"yafad'a yana d'aukar spoon yayi bissimillah yafaraci"itama Abincin takeci Amma jikinta Asanyaye yake"shine yarigata gamawa yaci dambun naman rabin bowl d'in ya Ajiye mata sauran sbd zai tafi yayi sallar la'asar....itama Amaan data gama sallar tayi"bayan ta idar ta kwanta saman bed itada teddy d'inta..…. Ammi ce zaune kad'ai cikin parlourn"shariff ya shigo ya zauna beyi mgn ba"dama inaso muyi mgn dakai game da Amaan! saida yaji fad'uwar gaba Amma saiya dake yana fad'in to Ammi"Abinda nakeso dakai shine karage wannan siye siyen dakake yawan yimata"wasu Abubuwan batasan yaya Akeyin Amfani dasuba"bawai na hanaka kamata Alkhairi bane koka k'i kyautata matane bane"shikenan Ammi zan kiyaye"ya jikin naki?"Alhmdllh da sauk'i"bece komai ba yamik'e tsaye yafita....

*Bayan kwana 2*
tun bayan shariff yadawo daga Abuja shak'uwa me k'arfi ta koma k'aruwa tsakaninsa da Amaan"dukda yana d'an dojewa had'e da basarwa"Amaan kuwa ta maida hankali wajen wasa da teddy d'inta"ta gogeta ta goyata....mus'ab kuwa yakasa gane kan shariff tunda sukayi wannan wayar" dan yanzun iyakarsa dashi gaisuwa idan sun had'u office"Ayau yakama week end"kuma masu Aikin Ammi duk suna ganin gida"itace ta had'a break fast yau"tun bayan ta gama ta d'an kwanta Amaan ce ta gyara d'akin da main parlour "sannan kuma tace itace zatayi wanke wanke "tana tsaye gaban sink tana sanye da dubai abaya light green me zanen bak'i da Adon stones"ta yane kanta da mayafin tamkar wacce ta saka Acuci ,haka gashinta yayi Atsakkiyar kanta"yau harda red d'in lip stick ta shafa"teddy d'in ta na zaune saman dining table d'in dake cikin kitchen d'in ita kuma tana wanke wanke "Ahaka shariff ya shigo da nufin zai d'auki ruwa"wanda a bad'ini bbu wasu ruwan dazai d'auka "kawai tunda yashigo yaga began taba yanaso yace tana Ina Amma zafin kansa ya hanashi"can yaji Ammi dake kwance a parlour tana cewa Abdallah Amaan na kitchen tana wanke wanke shine yafake da zaisha ruwa yashigo"yana sanye da farar shadda kansa bbu hula"Ammasa Aski da gyaran fuska"Anutse yayi sallama be Ida shigowaba yana kallonta k'irjinsa na bugawa"sai yaga tamasa kamar Aljannah sbd irin kyan datayi yau"juyowa tayi ta kallesa tasakar masa murmushi tana dariya har wushiryar dake a tsakkiyar hak'oranta ta bayyanah"hamma nah baka fita ba?"uhmm"dama kin iya Aiki?"na iya mana kawai Ammi ce bata son sakani nayi ne"ta fad'a tana dauraye hannunta sbd ta gama"gefenta shariff ya matso yana fad'in yau bakyajin sanyi ko?"yak'are maganar yana deb'o ruwa yawatsa mata gefen fuska murmushi me ban sha'awa na sub'uce masa"wanda tunda take dashi bata tab'a ganin yayiba ko kuma ta tab'a zaton ya iyaba"shine zaka jik'ani hamma?"nima saina rama Allah"ta fad'a cikin shagwab'a itama tana deb'o ruwan da hannayenta guda biyu yana k'ok'arin tsaida ita ta watso masa gaban rigarsa da saman fuskarsa "nidai ko Amaan?"gwalo ta masa ta koma deb'o wasu ruwan ta watsa masa tana dariya"tsaye kawai yayi yana kallon ta tanata murmushi cikeda burgewa ta matso gab dashi tana fad'in kaga nasaka saika canza kaya gashi zakaji sanyi ko?"tafad'a tana masa gwalo"shidai ya kalleta ya kalli jikinsa yana kuma tunanin idan yafito Ammi ta gansa da kaya Ajik'e yace mata me?be gama wannan tunanin ba Amaan ta d'akko teddy d'in ta tana fad'in hamma muje ka canza kaya saina zab'ar maka masu kyau irin kalar kayana ka canza ko?"kuma Allah ni yau sai nashiga d'akinka"kullum sai kace karna biyoka...shiru dai yayi yak'i mgn"nifa hamma kaine kake ja Ina fushi dakai sbd sai nayi mgn kamun shiru"beyi maganarba sai matsowa yayi by surprise taji ya d'alli pink lips nata......✍️

wannan book d'in na kudine ! idan kina buk'atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment