Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin ta yake mata azabar ciwo ta bugi bakin meenah tace dallah can kimn shiru nima na sani ne?.



Sosai Ashna ta shaƙe securityn yana ihu, ihun da yake yi ne ya jawo hankalin ragowar securities ɗn har oga Jibo.
suna ƙarasowa suka ga abnda ke faruwa take ƴafafuwan su suka fara rawa, ba shiri suka juya da niyyar guduwa, saidai me? suna juyawa wasu ƙattin macizai suka zagaye su.

Ashna ta saki securityn ta wurgar dashi gefe ta haɗe hannayen ta a kirjin ta.

Kallon oga Jibo tayi aiko kmar daga sama yaji an finciko shi ya watsar da gun ɗn dake hannun sa ya fasa ihu, ba a ajiye shi ko ina ba sai gaban Ashna aka tsaida shi kan ƙafafun sa.


Kallon rigar sa Ashna tayi sai gata ancire ta anyar a ƙasa, wandon ma tana kallon sa aka cire shi saiga oga Jibo daga shi sai ɗn ƙaramin pant, hannun sa yasa ya kare dick dnshi da ya fito sosai ta cikin wandon, ganin abnda yake yi yasa Ashna ta kalli pant aiko a ka shiga Jan wandon jibo na riƙewa ana ja ba shiri ya tsuguna ya fara kuka.

suma ragowar securities ɗn suka tsuguna suka fara kuka, hanci shaɓe shaɓe da majina jibo ya dubi Ashna yace dn Allah kiyi hakuri wllh mn tuba ki tafi mn sallame ki har ragowar ma dn Allah badon ni ba"" sheƙewa da dariya Ashna tayi, ta yi tsalle ta zauna ta tankwashe ƙafa bata sama bata ƙasa tace "" ba ku kuka kawo ni ba nice na kawo kaina Kuma ban shirya tafiya ba.

Samari ne wanda zasu iya kaiwa shekara ashrin da shida ko da bakwai suke sakkowa daga upstairs, anda ya fara sakko wa da gudu ya ƙarasa kusa da wata farar dattijuwa dake zaune a palour ya ɗora kansa kan kafaɗar ta yace ""Ammi kinga Sadiq ko? Ɗaga kanta Ammin tayi ta kalli wanda aka Kira da Sadiq Yana tsaye Yana huci tace ""haba Abubakar wai kai meyasa baka da haƙuri ne? kuma ma gaba ɗaya wata uku fa ka bashi amma ka matsa masa kai ga babba".

rRan Abubakar a ɓace ya dubi Ammi yace dama kece kike sawa yana ƙara raina ni , yanzu saboda tsabar iskanci kaya na fa yake sawa, kuma ai dama kinsan ƙazami ne kayan sa ma inda ya cire ana yake bari saidai ni na kwashe masa shine yanzu ya koma kan kayana"".

murmushi Ammi tayi ta dube shi to ayi hakuri Garba, idan Umar baisa kayan ka ba nawa zai sa haba babban yaya"" ƙarasowa yayi ya zauna yana ta kumbura Ammi ta kallesu gaba ɗayan su tace "" to nifa bama wannan ba ni na gaji da ganin ku kuna yi mn tsere a gida kunƙi aurwekodai bakwa so naga ƴaƴan ku ne?

Umar ne ya dubi Abubakar yana ƙunshe dariyar sa yace ""Ammi nidai zakiga ƴaƴa na Amma dai nasan boss bamai son shi da wannan miskilancin, da sauri Abubakar yayo kan Umar, da gudu Umar ya miƙe suka shiga zakage palourn yana yiwa Abubakar dry

More comment more typing.
Oum sharifat ce.
ASHPA KO ASHNA
7-8
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI+GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽
بسم الله الرحمن الرحيم


Bugun da momy tayiwa bakin meena ne yasa taja baki tayi shiru bata sake magana ba, su kuwa su Bash komawa gefe sukayi sukayi tsit kamar ba su ba, palourn yayi shiru tamkar babu kowa a ciki komai ya dena girgiza, a hankali suka shiga sauke ajiyar zuciya suna nishin wahala.

Wani zazzafan mari aka watsawa Kb da sauri ya juyo a fusace ya kalli bash hannun sa riƙe da kumatun sa yace"" wannan wane irin iskanci ne? me nayi maka? wllh sai na rama"" bash da baisan komai ba yaji Kb ya kamashi da kokuwa shima ko ya shiga ramawa, momy na musu magana amma kowa zuciyar sa tazo yuwa.


suna cikin kokuwar ne aka haɗa kawunan su aka gwara su da ƙarfi babu shiri kowanne yaja baya yana sosa goshin sa wanda a take ya kumbura yayi suntum, sun kai minti goma a haka, ganin babu abnda ya sake faruwa ne yasa bash saurin miƙewa ya kalli k Kb yace"" nidai bazan zauna agidan nan ba zan koma inda na fito, sannan ya kalli momy yace to ""momcy Allah ya ƙaddara saduwar mu.

kb da tyake jin wani mugun zafi a goshin yayi saurin miƙewa ya ja trolyn sa ya fara yin gaba ba tare da ya yi wa kowa sallama ba, shima Bash rufa masa baya yayi suka fara tafiya, saida suka kai bakin ƴofar palourn suka ji wani ƙaƙƙarfan hannu ya daki ƙirjin su, a take aka watso su cikin palourn, momy dake zaune tayi saurin mirginawa ganin an watso su Bash kar su faɗo kanta, cike da rashin sa a Bb ya faɗo kan ƴafarta a tare suka ƙwalla wata uwar ƙara suna kuka mai ban tausayi.


A daddafe Kb ya tashi ya tsuguna ya sunkuyar da kansa ƙasa ya fara magana yana kuka yace """" dn Allah dn Annanbi kiyi mana rai ki yafe mana wllh".

bai ƙarasa faɗin wllh ba aka kaiwa bakin sa bugu tsananin zafin da ya ziyarci kwanyar sa yasa yaja bakin sa yayi shiru.

Kukan jarira suka fara ji daga bakin ƙofa suka kasa kunne suna sauraron daga inda kukan yake, a hankali kuwa kukan ya dinga tahowa basu ankara ba sai ganin jarirai sukayi au goma sha biyu cikin palourn suna ga kuka, idanuwan su na zubar da jini suka yo kan Bash, da gudu Bash ya tashi yayi bayan momy ya cukuikuye ta yana tsalle yana kuka yace "" na shiga uku momy shikenan na mutu na lalace wayyo Allah momy na dn Allah ki bata haƙuri na shiga uku momy ki kaini kotu a yanke mn hukun ci momy, nayi wa wata yarinya fyade momy har ta samu ciki na kaita a zubar da cikin ta mutu, momy dn Allah ki kaini a kashe ni a kotu wayyo ni na shiga uku ki taimaka mn momy na dn Allah, karasowa jariran suka dnga yi suka zagaye momy da Bash suna buɗe baki.

wani tsalle bash yayi ya ɗane bayan momy yana ihu ""dn Allah momy kar ki bari su kashe ni ki kaini kotu ayi mn hukuncin musulunci.

momy da nauyin Bash ya fara damun ta ta tankaɗo shi tana kuka tace ""haba Bash ka rabu dani haka mana ai na fika buƴatar hukuncin addinin ma abnda nayi bash yafi naka muni"".

tana faɗa tana kuka, kamar an jeho ta kuwa sai gata ita da Bash sun faɗo kan jariran, aiko nan jariran suka shiga fincikar rigar momy saida suka yagata sannan suka shiga shan nonon momy, zuƙa ɗaya sukayi momy ta kurma uban ihu ta sume a wajan.


Jin kalaman Ashna ba ƙaramin tada hankalin kidnapers ɗn yayi ba, hanjin cikin su ya fara kaɗawa, dk irin magiyar da zasuyi mata sunyi amma taƙi tafiya, saida suka jigata sun sha kuka shaɓe ahaɓe da majina sannan Ashna ta dubi oga Jibo tace ""miƙe!!" da sauri oga Jibo ya miƙe kansa a ƙasa yana sauraron Ashna.

"" daga yau babu kidnapping ɗn talaka, sannan nice zan dnga sanar da ku wanda zaku kama, daga nan kuma idan kun kama kuɗin ba namu bane ni da ku ba ".

da sauri jibo ya ɗago ya kalli Ashna suka haɗa ido yayi saurin sunkuyar da kansa saboda ganin blue ƙwayar idon ta ba karamin tayar masa da hankali yake ba..

OUM SHARIFAT CE..
WANNAN LITTAFIN GABA DAYAN SA SADAUKAR WA NE GA MY TRIPLES MAMAN NUSAIBA, MAMAN AMATULLAH DA AUNTY NA KYAUTA DAGA ALLAH INA ALFAHARI DAKU ALLAH YA KARA TSARE MN KU.

JINJINA GA DUKKAN JARUMAI KUNGIYA TA ABAR ALFAHARI NA ALLAH YA KARA HADA KAN MU.


INA MATUKAR GODIYA A GARE KU MASOYA DA ƘARFAFA MN GUIWA WAJAN YIN COMMENT INA ALFAHARI DAKU LOVE YOU ALL.


ASHPA KO ASHNA

9-10

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI.

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)

بسم الله الرحمن الرحيم

Gaba ɗaya ihu suka saka ganin momy kwance bata numfashi, kuma aka rasa wanda zaiyi yi wani abu daga cikin su kowa yana tsoron tashi daga inda ya ke.
Bash ne ya kalli meerah dake kuka tna jijjiga momy yace"" jeki samo ruwa mna kin tsaya kuka"" wani kallon banza meerah ta watsa masa cike da rashin kunya tace bazan tashi ɗn ba kai namiji ka kasa sai ni"? koda ke ai ba zaka iya ba da fyaɗe ne nasan nan kafi ƙwarewa dn iska kawai mai cinye ƴaƴan mutane".

A fusace Bash ya tashi yayo kan Meerah ta tashi da gudu tayi sama, haka Bash ya bita tana shiga ɗakin ta ta turo ƙofa, kafin ta gama rufewa Bash ya danna ƙofar, aiko yana dannawa ta buɗe.

gaba ɗaya tsayawa sukayi turus ganin Ashpa tayi ɗai ɗai akan gadon meerah, da sauri sukayi hanyar fita waje, nanfa suka fara kokawa da ƙofa, gam suka ji ta babu alamun zata buɗe.

cikin su ne ya fara ƙullewa tsoro ya cika zuciyoyin su.

Ganin Ashpa ta miƙe tsaye bata sama bata kasa tana tunkaro su yasa meerah faɗawa jikin bash ta cukuikuye shi tana kuka, shima bash kukan yake yi ƙafafuwan sa suna rawa yake ja da baya, dariya aka farayi wacce tasa gaba ɗaya ɗakin amsa wa, ganin haka yasa Bash zubewa a ƙasa yana kuka ya fara mgana""" bansan ko ke wacece ba bansan me muka yi miki ba dn Allah ki yafe mana ki fita daga rayuwar mu bai gama magiyar ba aka ɗauke shi can aka buga shi da bango sannan ya faɗo kasa ji kake Tim ya ƙwalla wata uwar ƙara ya dena motsi.

ganin haka yasa meerah fara j da baya ganin Ashpa nayin kan ta, saidai ta kai ƙarshen bango sannan ta tsaya zuciyar ta na lugude.

daga inda Ashpa take ta miƙo hannun ta ta shaƙe wuyan meerah ta ɗaga ta sama a haka, sai ga ƙafafuwan meerah na rawa, mgana take so tayi amma ta kasa idanuwan ta sun firfito snyi ja sosai, saida ta tabbatar ta fita daga hayyacin ta sannan ta sake ta ta jefa ta kan bash.

kallan su tayu da idon ta nan take wani hayaƙi ya fito daga idon ta ya shiga jikin su a tare suka bace ita da su, a palour ta sauke su kusa da su momy ta fice daga gidan.

Sai Bayan minti goma sannan momy ta farfaɗo tare da kb da meenah wanda aka sa su baccin dole, mamaki ne ya kamasu ganin su a plourn babu Ashpa, kuma dk abnda aka ɓata cikin palourn komai ya koma daidai, har jinin da idon jariran ya dnga zubar wa babu kamar wani abu bai faru ba, gefe guda wata ƙawar momy ce zaune kan kujera tana latsa waya.

A Hnkali momy ta ƙarasa kusa da ita tana murmushi wanda bai kai zuci ba tace "" aa hajiya Maryam saukar yause? wacce aka kira da hajiya maryar ta dubi momy fuskar ta da murmushi tace """ nayi wajan minti talatin da zuwa dk kuna bacci shiyasa nace bari in barku ku huta.

Sauke ajiyar zuciya momy tace ta kalli hajiya maryam tace "" bari kedai hajiya bamu nan mnyi baccin ba "" .

""kmr ya ? hajiya Maryam ta tambaya tana ƙara gyara zama mamaki ƙarara ya bayyana a fuskar ta, itama momy gyara zama tayi ta kwashe komai ta sanar wa hajiya maryam.

Dariya sosai hajiya Maryam ta dnga yi har da riƙe ciki sannan ta dubi momy tace ""haba ƙawata kina da ni har wani aljani zai dame ki to bari kiga.

Waya hajiya maryam ta ɗakki ta fara kiran wata number ba jimawa kuwa aka ɗauka da sallama hajiya Maryam ta fara mgana da cewa "" yawwa malam wllh dama aljanu ne suka damu ƙawata gata nan malam wuni daya dk ta rame idan babu damuwa ko za a taimaka mata ",da to ta dnga amsawa har suka gama wayar sannan ta dubi momy tace an gama ƙawata malam zai zo idan anjima kadan.

A tare suka dnga sauke aiyar zuciya ita da ƴaƴan ta, ranar dai sai hajiya maryam ce ta shga kitchen dan kowa na gidan tsoron matsawa yake yi musamma Bash da meerah da suka San abnda suka ji.


Sai wajan yamma malam yazo ya kira hajiya Maryam ya sanar da ita tayi masa iso ya shigo.


Jinjina kai oga Jibo yayi sannan Ashpa ta maida masa kayan sa da idon ta tmkar ma baa cire su ba, izinin zama ta basu a hanzar ce kowa ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa suna jiran umar ni.

Rintse idon ta tayi tayi shiru wajan minti biyu kafin ta bude ta saki murmushi ta dubi Jibo tace"" daga nan zuwa titin Allu evenue zai ɗauke ku mnti hamsin idan kuka yi sauri, Alh jibril Mato zai ƙaraso wajan a lokacin zai ci abinci a seven therty restaurant, ku shiga cikin gurds ɗn sa ku ɗakko shi babu wanda zai ganku "".

jinjina kai sukayi babu ɓata lokaci suka tashi suka bar wajan suka dauki motoci suka hau titi.

Kmr ana tura su haka suka dnga gudu a titi har suka iso wajan, kmr yanda ta faɗa kuwa haka abn yake dk yanda tace suyi haka sukayi har Alh ya gama cin abnci ya tashi ya nufi wajan mota.

jibo ne ya buɗe masa ya shiga gurds ɗn suna tsaye sun ƙame basu san meke faruwa ba, sai PA ɗn sa wanda yake tare da alh koda yaushe aiko suka taso su gaba ɗaya.

A cikin dajin Ashpa ta tashi wasu securities ɗn suka fitar da waɗanda aka kama.


Tana nan zaune tana saƙawa da warware wa motar su Jibo ta dawo, tn daga bakin hanya ta hango su ta ƙara gyara zamn ta tana sakin wani killer smile.

Alh bai fahimci komai ba saida aka zo bakin dajin sannan ya gane batare da gurds ɗnsa yake ba.

juye juye ta fara yi yana shirin magana ya ji an ɗaga shi sama.

Ja da baya PA ya fara ganin oga a sama ba a hannun ko wa ba, wata irin damƙa jibo yayi masa ya ja baki yayi shiru yana wurga Ido.



Jinsa a sama ya sa ya waiga don ganin wanda ya ɗaga shi, saidai ba kowa shi kaɗai yake tafiya cikin iska, wani uban ihu ya kurma da ƙarfi yana wurgar Ido yace "" wayyo Allah na wayyo na ga ta kaina haba boka ya zaka mn haka ka rufa mn asiri ta kara ta ban yanka jariran ba saura kaɗan ka rufa mn a siri kar ka kashe ni ban cika buri na ba innahumin sulaimanu wa innahu wainnahu "".

wainnahu yake ta maimaitawa ya kasa kamo ƙarshen har aka sauke shi gaban Ashna, ya bude baki zaiyi mgana a ka daki bakin yaja yayi shiru, kallon kowa na wajan Ashna tayi suka watse aka barta daga ita sai Alh, kallon sa Ashna tayi fuskar ta babu annuri tace """ Faɗi abnda zaka fada"" jikin sa na rawa yake kallon fuskar ta yace "' babu abnda zance nidai kimn rai karki kashe ni takara ta dn Allah ki barni ban gama cika buri ka na ba.

da karfi Ashna ta kaiwa bakin sa bugu ya sake kurma ihu ganin haƙorin sa guda ɗaya a hannun sa, kafin yayi magana dajin ya fara rawa wasu ƴananun yara suka zagaye shi suna tsalle suna rawa, babu abnda suke furtawa face"" jini"".

wani irin numfashi alh ya fara ja mai cike da wàhala da tashin hankali.

yana cikin hakan ya sake ji anyi sama dashi ana jujjuya shi, zuwa yanzu muryar sa ta fara dashewa, banda gunji babu abnda yakeyi idon sa a rufe yake fadin"" wayyo ni wayyo rayuwa na shiga uku dn Allah ki yi haƙuri ki yafe mn kaico kan mu kaico abnda zai ƙarar damu, kaico na na shi ga uku na lalace innahu"" bai ƙarasa faɗar innahu ɗn ba aka sake kaiwa bakin sa bugu yayi shiru wani gurnani yake kmr zaki yace"" nayi shiru nayu shiru madam bazan sake ba wllh na tuba kimn rai nayi shiru "".


nayi shiru yake ta maimaitawa yana gunji yana tuba sannan Ashna ta kalle shi ya sakko ƙasa

harisu (PA) dake gefe ya ƙunshe dariya ganin wandon oga jiƙe kashi.

bai yi aune ba yaji an ɗaga shi sama kansa a ƙasa ƙafar sa a sama yana lilo, nan fa ido ya raina fata ya fasa ihu yana cewa""" na tuba anty na wllh bazan sake dariya har abada nida dariya bazan sake ba dn Allah kar ki bari na mutu wllh ni kaɗai iyaye na suka haifa kuma tnda na samu aiki suna ƙauye banje wajan su ba dn Allah ki bari naje su ganni ko sau ɗaya ne, dn Allah ki mn rai ko auren farin banyi ba na shiga uku na, dn Allah ki yafe mn oga ka yafe mn na cuce ka abubuwa da yawa dn Allah kowa ya yafe mn niko tawa ta ƙare



Hajiya maryam ce tace wa malam ya shigo, ga mamaki na wani baƙin mutum ba gani jikin sanye da rigar fatar kura hannayen sa ɗaure da guraye ya ɗaura wata fatar a ƙugun sa, hannun da rike da wani gashi irin na inyamurai da ƙoƙo a ɗaya hannun nasa.


Babu ko sallama ya shigo cikin falon yana raba idanu, ya kalli hajiya maryam yace"" daga ina ne shaiɗanun suke? hajiya maryam ta kalli momy tace"" to ƙawata faɗa masa"" nan da nan jikin momy na rawa ta kwashe dk abnda y faru ta faɗawa malam.

Yana gama ji ya fara zuwa kusurwa kusurwa na palourn yana tsoma wannan gashin cikin ƙoƙon hannun sa sai ya yarfa ruwan dake ciki a jikin bangon kusurwar.

saida yayi dka kusurwar sannan ya dawo tsakiyar palourn ya tsaya cak ya ɗaga ƙoƙon sama ya fara magana da wata irin murya mara daɗin ji yace """ Kuna ina ! Kuna ina kananun marasa kunya!! kuzo ku shiga nan ya faɗa yana nuna ƙoƙon dake hannun sa, shiru babu wanda ya amsa haka yayi ta kururuwa shiru.

wata yar dariya yayi ya dubi hajiya Maryam yace "" an gama sunji tsoro ba zasu iya komai ba ƙananun ƙwari ne"" bai ƙarasa faɗa ba aka zabga masa wani gigitaccen mari saida yayi tagaltangal saboda tsabar zafi amma haka ya dake ya tsaya ya cigaba ya murmushin yaƙe.

wani marin aka sake zabga masa ya sa hannu ya sosa kumatun sa yayi shiru.

zuwa yanzu jikin sa ya fara rawa wani gumi ne yake karyo masa gashi baya so a gane, can dai aka sake zabga wani marin ai da ƙarfi ya buɗe baki yace ""kaaaaaiiiiiiiiiiiiii"" yana faɗa ya yadda ƙoƙon da gashin yayi hanyar ƙofa a guje, ai kafin yaje aka rufe ƙofar ji kake garam, nan take kuma wani duhu ya mamaye Palourn Wanda ko tafin hannu baa iya gani...


Oum sharifat ce.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LWo0GX36DMiJAdHiIcVwrl



ASHPA KO ASHNA

11-12
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI)GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽
بسم الله الرحمن الرحيم



Momy da ƴaƴan ta suka ƙanƙame jikin junan su suna wani kuka mai tsuma zuciya, ita kam hajiya maryam bayan kujera ta samu ta laɓe, shi kansa malam neman wajan laɓewar yakeyi amma ya rasa.

Yana nan tsaye ya ƙanƙame jikin sa yaji an ɗauke shi cak aka ɗaga shi sama ka buga shi da ƙasa wai uban ihu ya kurma cike da nadamar zuwa gidan, wutar ɗakin ce ta fara kawowa tana ɗauke wa aka dnga jijjiga dakin, wasu muryoyi mara sa daɗin ji suka fara dariya suna jan ɗafar malam.
zuwa yanzu malam yayi suman wucin gadi saida aka zabga masa mari sannan ya farfaɗo, wata doguwar mace ya gani tsaye a gaban sa fuskar ta na kallon bayan ta tana zaro harshen ta gajin kanta ya rufe idon ta ta na yo kansa da wata sharbebiyar wuƙa, ja da baya malam ya fara yi tana ƙara biyo shi.

saida ya kai ƙarshen bango sannan ta tsaya.
ya rintse idon sa gaba ɗaya ya gama sallama rayuwar sa yaji an ja ƙafar sa kmar ana jan kayan wanki aka kaishi tsakiyar palourn, a lokacin kuma hasken palourn ya dawo.

ganin wannan matar ba ƙaramin tada hankalin su Bash yayi ba haka suka sake maƴale juna shida kb, cikin rashin saa Bash ya kai idon sa jikin tv da sauri ya rintse idon sa sakamakon matar da ya gani cikin tvn tana zaro masa ido, ta cikin tvn ya ga ta miƙo hannu yayi saurin ɓoye kansa jikin momy Amma saida hannun yazo inda yake ya shaƙe shi ya ɗaga shi sama aka haɗa shi da bango.

cikin wata kakkausar murya aka daka masa tsawar da saida jikin sa ya fara karkarwa aka ce ""malami kuka samo ko? wanda zai cire mu ko""?

Jiki na ɓari Bash ya ce ""wllh anty ba ni bane nifa banma san inda malamai suke ba wllh momy ce da ƴawar ta dn Allah kiyi hakuri ni wllh ma ƙasar zan bari"""

"" kaje ka cigaba da lala ta ƴaƴan mutane ko ?ido wuri wuri bash yace ""ni?!! aa wllh ni ko aure ma bazanyi ba babu abnda zan ƙara nida mata har a bada"" wani zazzafan mari aka zabga masa aka ce"" sunnar manzon Allah (saw) ce ba zakayi ba? wato ka fi son na yan iska ko? .

bash ya fashe da kuka yace. Aa wllh zanyi a satin nan ma zan yi anty wllh zanyi aure da kanki ma kinemo min matar ko kuturwa ce wllh Ina so dariya ta sake kecewa da ita sannan ta watsar da bash gefe

Yanda ta juyo kan malam tana wata irin tafiya yasa gaban malam ya cigaba da bugu kmr gangar coci , ƙura idon ta tayi a kan malam kmr daga sama malam ya fara jin duka ta ko ina kafin ya sosa wannan an sake zabga masa wani tsuguna wa malam yayi a gaban ta yace "" kiyi mn rai dan gausin dan giyasin"" ƙafa ta sa hankaɗa shi baya.

cikin wata karairaya da yauƙi ta ƙarasa gaban sa tace ""kai fa malami ne kuma kace mnji tsoro kai kukan me kake yanzu? kawai ka fitar da mu daga gidan nan.

tana faɗa gabaaya palourn ya lauka da hayaniya wasu muryoyi mara sa daɗi suna sudai a fitar da su daga gidan.

idon malam pa sunyi wuƙi wuƙi kamar shege a rabon gado yace ""wayyo ni ni na isa na kore ku bazan iya ba wllh ba aiki na bane ni ɗin banza ai nan gidan ku ne dole a tafi a barku"".

"" zaka iya" yaji wata murya mai kama da ta ƙaton gardi ya faɗa, ja da baya malama ya farayi yana kuka yace ""wllh bazan iya ba ki rufa mn asiri wllh ban iya ba bansan komai ba kawai damfara ce irin tamu ta ƴan bariki "" zafafan maruka aka shiga zabga masa cikin muryar jarirai aka ce da gaske kai ɗan bariki ne "?
jikin malam na rawa yana jijjiga kai ya ce"" ƙwarai kuwa tantirin ɗn iska ne ni bansan komai ba jahili ne ni wllh kina saki na islamiyya zan koma, na rantse da Allah na dena duba.

wata dariyar aka sake sheƙewa da ita sannan aka shiga dukan gaba ɗaya mutanen palourn tako ina ba ji ba gani.

momy da ta gama jin duka tayi lilis ta ce"" Allah ya isa hajiya Maryam babu ni babu ke Allah ya tsine miki""

hajiya Maryam dake sosa jikin ta dk inda aka daka tana jin kamr ranta zai fita cikin kuka tace ""saima kin faɗa? aini yakamata in faɗa babu ni babu ke har abada gayyar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment