Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gano yan Oum sharifat novel pans ansha ashoke ana ta diban shoki mrs Ashwal ana ta rabon kaji .

Umar ko banda gumi babu abnda yakeyi Ashpa na zaune hankalin ta kwance tana kallon masu casu tana murmushi.

Ashna da Abubakar lokaci lokaci suke kallon juna suna murmushi kafin a gama dinner kafar Umar ta kumbura saida aka tashi Abubakar ya kula ya dingisawar da Umar yakeyi sannan ya matso kusa da shi yace "" yane Dude naga kana dingishi nothing kawai Umar yace yacigaba da tafiya saida suka koma gida sannan Abubakar ya matsawa Umar aka dingishin da yakeyi cike da bakar zuciya Umar yace kafa ta ce kawai take ciwo yanda ya Fadi maganar idon sa yayi jazur ga wasu jijiyoyi sunyi radarada akan sa yasa hankalin Abubakar ya ya tashi ya Kira likita ba jimawa Kuma likita yazo ya fara duba kafar Umar dn yatsan sane ya karye Kuma ya danyi tsami se an gyara Amma zesha wahala a gyara kawai cewar Abubakar yana kallon doc .

Kafar Umar aka ja aka fara gyarawa tn Yana cije lips har ya fara hawaye abnka da ajeboter dakyar Abubakar ya rike shi aka gyara aka yi masa allurar bacci ya samu relief cikin zuciyar Umar kuwa tnanin abnda ke kafar Ashpa yakeyi zan duba na gani sai na ga uban menene a kafar tata shine abnda ya dnga maimaitawa a hankali har bacci ya dauke shi.


SU WAYE ASHPA DA ASHNA ? WAYE DADDY ? ME SUKA AIKATA? DK ZAKU JI SU A NEXT PAGE.

Oum sharifat ce..

*ASHPA KO ASHNA*

19_20

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽

بسم الله الرحمن الرحيم
Kamar yadda kuka sani suna na balarabe nima Muhammad mn taso.cikin soyayyar juna tn muna kanana abotar mu tasa iyayen mu zama abokai dk da mutanen da dama can su sun dauki makoci tamkar dan uwa, gidan su Muhammad babu laifi suna da rufin asiri domin ko baban su ke fitowa da abnci kofar gida da yawa nan mutanen unguwa suke taruwa suke ci sannan matan gida ma matar sa na taimaka musu baban su Muhammad wato Alh jibril ya kasance mutumin kirki wanda abnda baya hadashi da kowa yana zaune da kowa lafiya haka matar sa hajiya Aisha nida Muhammad Alh jibril ya hada mu ya kaimu makarantar allo ya dauki komai na rayuwa ta dk abnda yayi wa Muhammad haka zaiyi mnshi lokacin sallah kuwa komai iri daya yake mana a kwana a tashi har kwana nakeyi a gidan baba na wato mal mudi yana matukar ganin mutuncin Alh Muhammad saboda yadda ya nuna soyayyar a gare ni dk da kuwa yayan unguwa ma yana kyautata musu amma dai ba kamar ni ba da komai yake Mana daya da Muhammad.


Muhammad yana son karatu sabanin ni da bana so guduwa nake yi ba yadda baba na baiyi dani akan nayi karatu ba amma naki haka ake ta hakuri dani wata rana naje wata rana naki zuwa .


A kwana a tashi muka fara zama samari baban su Muhammad ya dauke mu ya mai mu kasuwa abnda nake so kenan inga Ina samun kudi domin sune buri na na duniya ai ko mun samu a lokacin babu wasu saannin mu da suke samun kudi kamar mu nan pa muka fara neman aure Muhammad ya nuna yana son wata yar fulani fateema nima kuma Ina son ta Amma ban fada mata ba da Naga sun fara soyayya da Muhammad sai na janye Amma fa zuciya ta fal take da soyayyar ta daga baya ne na nemi auren mahaifiyar ku .


Baban su Muhammad ya bamu gida muka zauna muda Muhammad komai na aure shine yayi mana sannan ya bamu jari muka fara kasuwancin kanmu.

muka fara zama cikin kwanciyar hankali a gidan zuwa wannan lokacin babu komai cikin zuciya ta face kiyayyar Muhammad domin ko kasuwancin sa kullum habaka yakeyi Amma nawa bayayin gaba dk da rage cutar da nakeyi wa mutane don na kara kudi amma basa karuwa kllm cikin asara nake sannan ga shi kullum Ina ganin Fateema tare da Muhammad Ina ji kamar na shake shi ya mutu nabi hanyoyi da yawa wajan ganin na gurgunta Muhammad Amma kllm gaba yakeyi Nasha sakawa shagon sa wuta Amma daga sai komai ya dawo daidai Kuma ya samu cigaba.

A wannan lokacin aka haifeka Bashir dk wani daya shafi haihuwa Muhammad ne yayi hadda ragon sunan ka shine yayi murna sosai yakeyi ya samu da haka muka cigaba da zama dashi har aka haifi su Ameena da Ameera Allah bai nawa Muhammad haihuwa ba wannan Kuma bai hana shi cigana da daukar nauyin ku ba shine yake muku komai har hidimar makarantar shine nasan ba zaku mnta da shi ba .


Zuwa wannan lokacin na dena damuwa akan sa saboda naga komai nasa yana karar da shine akan ku , saida aka haifi Aliyu da shekara uku sannan matar Muhammad ta samu ciki tnda na fahimta hankali na ya tashi nabi dk wasu hanyoyi domin zubar da cikin amma yaki fita dk wannan abn ban sanar da mahaifiyar ku ba saboda yadda suke shiri sosai bana tnanin zata bani hadin kai saboda ance mai da wawa tana jin dadin yadda Fateema take kula da ku kmar yayan ta.

Ina cikin wannan halin Fateema ta haifi yayan ta guda biyu mata kyawawa abn shaawa ranar suna yara suka ci sunan mahaifiyar sa wato Aisha inda ake Kiran daya da Ashpa daya kuma Ashna.

hankali na ya kara tashi nasan dole yanzu hankalin sa ya koma kan yayan sa nan fa na fara kokarin raba shi da yayan sa a nan ne wani aboki na ya bani shawarar zuwa wajan wani boka banyi wani dogon tnani ba ba amince bayan munje wajan bokan ne take sanar dani ba yadda zaayi da yayan saidai shi Muhammad dn a raba shi da rayuwar sa.

Nayi shiru zanyi tnani aboki na ya tnatar Dani irin son da nake wa Fateema nan da nan na amince.

Wasu yan surutai bokan yayi yace na kalli kwaryar dake gaban sa Ina kalla kuwa Naga Muhammad yana zaune shida fateema rike da yayan su nan fa zuciya ta ta kara fusata na ce ayi dk abnda zaayi boka.

Wata kwalba ya dakko ya yi wani ihu ya bude kwalbar saiga wani hayaki ya bayyana ya shige cikin kwalbar boka ya mayar ya rufe nan yake sanar Dani wannan shine rayuwar Muhammad Kuma ze fara ciwo bazai wuce kwana uku ba zai mutu ya bani kwalbar tare da sharadin dk ranar da ta fashe komai ze iya faruwa dani.

Kamar yadda boka ya fada hakan akayi tndaga ranar Muhammad ya fara lalura aka rasa magani ciwo ba sauki bayn kwana uku ya bar duniya

*ASHPA KO ASHNA*

21-22

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE) 💪🏽

SAMFOTI
( DANDANO)

Cikin office dn likita mutane guda biyu a ciki, mace da namiji ke zaune suna jiran bayanin doctor.
doctor keta yan rubuce rubucen ta akan wani file, daga can da ta dago kai ta kalle su fuskar ta dauke da fara'a ta mike tsaye ta ce "" congratulations " shiru sukayi suna raba Ido suna kallon ta suna kallon juna, fahimtar basu gane mai take nufi ba yasa tayi ta yar dariya tace "" Ina nufin albishirin ku " a tare suka hada baki wajan cewa goro, gyara babbar rigar dake jikin sa namijin yayi yana washe hakoran sa yace "" goro fari soll bamu musha "" matar ka na dauke da juna biyu na wata biyu cewar doctor fuskar ta dauke da murmushi
kallon doctor yayi sannan ya kalli matar tasa kamar wani dolo daga can kuma ya mike da sauri gadan gadan yayi kan doctor kafin ta ankara ya daga ta sama cak ya fara juyi da ita, wani ihu doctor ta sa tana daga hannu tana neman dauki ,dk ihun da take yi baisa ya sauke ta ba, zagaye kawai yake da ita a cikin office dn.
matar sa dake zaune gefe ta kwalla wata uwar kara ji kake timm ya yarda doctor a kasa da gudu ya karasa kusa da matar tasa ya tsuguna yace "" Bilkisu mai gadon zinare Bilkisu tawa me yafaru? tabe baki Bilkisu tayi cike da shawagaba tace "magana yakeyi" da sauri ya tsuguna ya daga rigar ta yasa kunnen sa kan cikin nata jin shiru yasa ya dago ya kalle ta ce banji komai ba cike da shwaba tace "" ai ni take fadawa "to "mai tace fada mn dk abnda yar baba tace daga nan har birnin sin zaa yi shi ke incewa tayi in kona asibin nan takwarankwatsa dubu sai na Kona shi ke nifa akan me sunan Inna wllh se in Kona gari... ✍🏽
*Kadan kenan daga cikin littafin CIKI DA RAINO na khadija Umar Abdullahi garkuwar jarumai ce*



بسم الله الرحمن الرحيم


Sorry not edited

Lokacin da daddy yazo daidai nan a lbrn sa sai yayi shru zuciyar sa na kuna gaba daya dakin kuka suke ba suyi tnanin rashin imanin daddy yakai haka ba ita kanta momy mamaki takeyi lokaci daya taji tsanar Daddy ta mamaye zuciyar ta gaba dayan su babu Wanda bayajin haushin abnda daddy ya aikata Meenah ta goge hawayen ta cikin rawar murya tace "" no wonder dole ai dole ma musha wahala wllh nayi nadamar kasance wa ta yar ka daddy nayi nadama ta sake fashe wa da kuka cikin shashsheka bash yace ashe wannan shine halin ka tabbas mn aikata laifi kusan daya da kai dk da ni banyi cin Amana irin taka ba Amma nayi silar rayukan yammata da yawa indai haka ne to bamu fara ganin komai ba.

Shima daddy kuka yakeyi Yana Shirin yin mganar a ka fara feso masa wai ruwa mai mugun zafi ihu daddy yakeyi Yana son cewa wani abu Amma ina an rufe bakin saida yayi likis dk jikin sa ya kone sannan aka jefar dashi gefe a sume aka shiga feso.masa ruwan sanyi cike da tsananin azaba daddy ya fardado jikin sa na karkarwa gaba dayan su kasa sukayi da kansu dk da suna jin haushin daddy Amma ba sazu iya jurar ganin halin da yake ciki ba "" karasa labarin ka mushriki aka fada da wata kakkausar murya "" cikin rashin nustuwa da tsoron azaba daddy ya dora da cewe .


Lokacin da aka ce Muhammad ya rasu haka na fto Ina kuka Ina rike gawar sa ba Wanda bai tausaya mn ba aka dnga rirrike ni da kyar aka iya tsaida ni a ka fta dashi ganin kamar bana cikin hayyaci.na yasa aka rufe ni cikin daki aka hana ni zuwa makabar ta Niko Ina shiga cikin dakin na shiga murna Ina ganin nayi maganin matsala ta.

A kwana a tashi har Fateema ta gama takaba Ina daukar nauyin komai nata ita da yayan ta lkcn ba a ajiyar kudi a banki se dai a gida a cikin buhu .


Bayan fateema ta gama takaba na nemi auren ta Amma fur tace ba zata yi aure ba nayi iya kokari na Amma taki haka nakoma.wajan boka amma sai yake sanar da ni fateema ba matata bace haka na taho Ina wasiwasi dama zuwa lokacin ba wai soyayyar fateema ce zata sa na aure ta saidan kudin Muhammad dake dakin ta gashi iyayen Muhammad sn ce sun barwa yayan gadon gaba daya dama shi kadai suka haifa ganin dk wasu dabaru sun kare mn hat Fateema ta saka ranar komawa gidan su dk da Ina hana ta .

Ina cikin wannan halin ne dabara ta fado mn naje na hadu da wasu yan Saba suka zo sukayi fashi cikin dare a dakin fateema dk abnda ke cikin dakin saida suka kwaso mn shi nu Kuma na sallame su to daga nan ne fa na hada da tawa dukiyar cikin kankanin lokaci na zama mai kudi kmar yadda nake so saboda dk.wasu kasuwanci na Muhammad nine nake yin sa na siya gida mai kyau muka tashi muka kowa daga nan kuma na raba mahaifiyar ku da yan uwan ta hadda mahaifiyar ta nace ta zaba ko ni ko su kuma ta zabe ni muka cigaba da rayuwa muka.juyawa talauci da talaka baya dani da mahaifiyar ku bamu Kara neman iyayen mu da yan uwan mu ba har yanzu da kwalbar ruhin Muhammad ta fashe ni yanzu nasan tawa ta kare sannan ban ta inda zan nemi yafiya ba sbd nasan ba me yafewa laifi na wannan shine lbr na.

Sunkuyar da kai momy tayi cike da nadamar juya wa iyaye da yan uwan ta baya tace "" hakika na tafka babban kuskure da na zabi duniya fiye da iyaye na nayi nadamar zuwan wannan ranar ynzu bansan a wane hali suke ciki ba.

Jigum jigum sukayi kowa da abnda yake sakawa cikin ransa daddy kuwa wani azababben zafi yake ji a dukkan jikin sa zuciyar sa nazafi zuwa yanzu babu abnda yake bukata kmr ya mutu ya huta.



Kaduna
Kashe gari da yamma aka.kai amare gidajensi Wanda ke makotaka da juna manyan gidaje me hadaddu na daidai masu rufin asiri komai na cikin gidan iri daya ne bayan an kai amare akawa watse aka.bar kowaccen su ita kadai a gidan ta .

Da sallama Abubakar ya shigo dakin da Ashna ke zaune fuskar ta a rufe da mayafi kusa da ita yaje ya zauna aya hannu ya daga mayafin daidai nan itama ta dago.idon ta suka hada ido a tare suka sauke ajiyar zuciya .

Murmushi mai tsada Abubakar ya sakar mata ya gyaran mata mayafin ya kalle ta cikin so da kauna yace godiya ta tabbata ga ubangijin daya halicci wannan tauraruwar kuma ya bani ita Ina rokon sa ya bani ikon yi mata adalci cike da kunya Ashna tace Amin nima.ina rokon sa da ya bani ikon yo maka biyayya Amin yace yana shagala da kallon kyakykyawar fuskar ta wayar sa ce ta fara kara ya na dakko wa ya duba secren dn ya sauke ajiyar zuciya yace ana jiran mu a palour sai sannan ya tna da abokan sa da suka zo tare .

Mikewa tayi ya maida mata mayafin ta ya rufe Maya fuskar ta sannan ya rike mata hannu suka fito palourn tare tnda suka fto abokan Abubakar suke tsokanar shidai baice komai ba se washe baki kawai yakeyi .

Bayan yan wasanni da raha suka yi musu nasiha sannan suka cika da addua suka tashi iya bakin palour Abubakar ya raka su suna yi masa tsotya haka ya ki raka su waje ya ja kofar ya rufe ya dawo ciki cak ya dauke Ashna Tana jin kunya tana rufe Ido Amma bai sauke ta ba saida ya kaita toilet sannan ya ajiye ta yace "" oya ayi alwala muyi sallah habeebty murmushi Ashna tayi tana sunkuyar da kanta kasa shiko dry yake ya fice yaja Maya kofar ya nufi dakin sa.



Yan kawo amarya suna tafiya Ashpa ta cire mayafin ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito tayi addua ta rufe kofar ta haye bed tinanin mama ne fal aranta har bacci ya dauke ta.

Umar shi kadai ya shigo direct dakin sa ya nufa ya watsa ruwa ya haye bed yana saka irin hanyar da zai bi ya kori wannan aljanar yarinyar.

Da asba Ashna ya farka tayi sallah ta koma bacci misalin karfe takwas ta farka da wata azababbiyar yunwa da sauri ta sakko daga ita se rigar bacci kanta ba dankwali dogon gashin ta ya zubo har bayan ta leke leke ta fara yi a palour har ta gano kitchen kanta tsaye ta shige turus tayi ganin Umar tsaye wajan gas da alamun girki yakeyi ita shigewa tayi ta bude fridge tana duba abnda ke cikin.


Wani irin cafka taji anyiwa gashin kanta da karfi a fusace ta dago Umar ta gani ransa a hade ya kalle ta yace "" ke wace irin Mara hankali ce zaki shigo ba sallama.bare gaisuwa bacin ranta ne ya karu jin ya ambaci gaisuwa wani yawu mai daci ta hadiya ta daga kanta sama tace "" kwarai banida hankali yanzu ma zakaga sample tana gama fada ta dagaa hannun ta sama saiga hannun Yana kara tsawo saida ya kai daidai wuyar Umar ta shakeshi ta daga shi masa har wajan pop yawo kafafun Umar suka fara yana kakari idon sa sun firfito sunyi ja ya kasa magana saida idon Umar ya fara lumshewa sannan Ashpa ta yadda shi gefe yana yan kananun tari lemo da meet fie ta dauke ta tsallake shi ta fice daga kitchen dn...

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment