Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsiya kawai"" a tare aka zabga musu mari suka ja baki sukayi tsit sai gurnani suke kamer zaku na

KADUNA

Gyaran murya akayi tare da sallama , Abubakar da Umar suka juya suka kalli ƙofa, wani dattijo ne ya shigo wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka ga tsananin kamar sake tsakanin sa da su.
da sauri kuwa Umar yayi bayan sa ya tsaya yana dariya, jawo shi mtmn yayi kmr wani ƙaramin yaro yace"" aa ni fa Umar bana goyon bayan wannan halin naka nasan dai tsokana ce kayi dama Ammin ku ce ke goyin bayan ka Amma banda ni""
turo baki Umar yayi kamr zaiyi kuka ya koma kusa da Ammi ya zauna Yana kumbura, murmushi Ammi tayi tana shafa kansa tace"" ka rabu dasu kaji ni Ina bayan ka ai " ɗn murmushi yayi yana yiwa Abubakar gwalo .

Zama dattijon yayi suka fara yi masa sannu da zuwa yana amsawa.

Ammi ce ta dube shi cike da kulawa tace "" to Alh muje kayi wanka ko? sai ka ci abnci ""

aa ba yan zu ba sai na huta cewar daddy yana gyara zamn sa kan sopa.

sannan ya dubi Abubakar da Umar yace"" dama Ina so muyi wata magana da ku in sha Allah ranar week end zamuje daku Kano zaku ga ƴaƴan gwaggon ku Ashpa da Ashna kowa zai auri ɗaya.

Wani kallo Umar ya yi wa daddyn cike da damuwa yace ""wai daddy kana nufin wannan yaran masu kama da aljanu?
fuskar Daddy ta zanja zuwa b
ɓacin rai yace"" Umar ƴannen naka ne masu kama da aljanu? ashe ba zaka iya tsayawa kan rayuwar su ba? ashe ba zaka iya yin yaƙi da dk wanda zai aibata su ba? to su nake nufi kuma su zaku aura idan har na isa

Kayi haƴuri daddy Allah yasa haka shi yafi alkairi cewar Abubakar yana zabgawa Umar harara.

haƙuri shima Umar ɗn ya bawa daddy a ransa kuwa yana lissafa irin azabar sa zai yiwa dk wacce aka aura masa a cikin su ( nidai nace Anya kuwa? Readers kowa ta zaɓi team ɗn ta nidai ina bayan Umar yanzu za a fara wasan).


Bayan sun gama shan dukan palourn yayi tsit matar ta ɓace komai ya dawo yanda yake kamr ba ayi komai ba.

malam da bai san inda kayan sa suke ba daga shi sai gajeren wando ya tashi a guje ya fice daga palourn yana tsinewa hajiya maryam.

mai gadi na banɗaki malam yana ta kira azo a buɗe masa amma shiru ganin bazai iya jira ba ya daka wani wawan tsalle ya haura katanga ya dira ta baya ya zuba a guje

Ranar dai Babu wanda ya haura upstairs anan palourn suka kwana baccin dai ba wani isasshe ba, kashe gari da safe daƙyar suka yi wanka ranar dai da kansu suka shiga kitchen suka dafa shayi suka sha

Suna cikin yin breakfast suka jiyo wata murya daga bakin ƙofa wacce na kasa banbance macece ko namiji ne.

nidai naji ance ""Salam wa'alam"" gaba ɗaya suka juyo dn ganin mai wannan sallamar sn San dai mtm ɗaya ne mai yi wato sai autan momy .

Wani matashi ne wanda bazai wuce shekara ashirin da biyu ba sanye da farar jallabiyya ya ɗaura zanin atamfa a ƙugun sa sannan ya ɗaura wani ɗankwalin atamfar a kansa.

a haka ya karaso cikin palourn yana karairaya shi a dole ga mace, girgiza kai meerah tayi ta dube shi tace"" yanzu kai Aliyu ba zaka dawowa daidai ba kai fa .. Bata ƙarasa ba wanda aka kira da Aliyu yaja da baya ya taɓe baki cike da yauƙi yace ""keee dakata ƙaramar yar iska Aliya nake kar ki sake jefa ni cikin ƙattai ni jinsin ki ce ehe "" ya ƙarasa faɗa yana buga cinya. Kb da zuwa yanzu ya fara sabawa da masifa yayi wata ƴar dariya yana hango irin masifar da Aliyu zai jefa kansa cikin gidan.

Oum sharifat ce..


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LWo0GX36DMiJAdHiIcVwrl



ASHPA KO ASHNA


13-14

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI

NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI (GARKUWAR JARUMAI CE)

بسم الله الرحمن الرحيم

Kowa komawa yayi ya jingina da kujerar zuciyoyin su Banda lugude babu abnda sukeyi, tnani fal ransu yadda Aliyu ke Shirin jefa su cikin masifa.

Kb ne ya taso yazo kusa da Aliyu ya kai hannu da nufin taɓa shi, da sauri Aliyu yaja baya yana gyara ɗaurin ƙirjin sa yanatafa hannu "" yace na shiga uku an fasa aure na, kai yanzu saboda ka cika ƙaton gardi ɗn iska ni zaka taɓa me kake son ji a jiki na? shege kwarto, to wllh a hir ɗn ka ƙwalelen kare da hantar kura ya ƙarasa faɗa yana murguda baki kmr karuwar ƙauye.


Tsananin mamaki ya hana Kb magana haka ya koma gefe ya zauna ba tare da yace komai ba.

cike da rangwaɗa Aliyu ya fara taku cikin palourn ya ƙaraso gaban momy ya kai hannu ya rike ƙafar ta, yana shirin yin mgna da sauri momy ta ɗaga masa hannu tace "haba Aliyu menene yake burgeka a cikin wannan rayuwar ? Me kake nema wanda Allah bai maka ba ? Baka ga kowa na gidan nan alamun yana cikin damuwa ba? haba Aliyu ka dawo yadda kake kaji Aliyu na.

Maimakon Aliyu ya canja sai ma ƙara miƙewa yayi yana yarfa hannu yana kashe ido yace ""yo ni fa momy nasan dama ba ƙaunata ake a gidan nan ba, dk yadda nake taka tsantsan da rayuwa ta nake jan jiki saboda gudun raini amma bakwa gani, kuma ma idan naƙi shiga a gidan aure ai ba zan ƙi shiga a tasha ba a hayyye ya kara fada yana bugun cinya tare da cewa sawaaaa.

Bai kai ga gama faɗar sawaa ɗn ba yaji saukar zazzafan mari a fuskar sa, a hasale ya ɗago kai ya kalli Kb wanda ke kusa da shi ya buɗe baki da shirin magana aka kaiwa bakin sa bugu, zaro Ido Aliyu ya fara yi yana kallon gabas da yamma kamar daga sama yaji an finciki zanin sa anyi wurgi da shi gefe, rintse Ido Aliyu yayi ya buɗe yana buɗewa ya ga wasu yan daudu guda uku kamar su sak dashi cikin shiga irin tasa suna tahowa kowanne yana wurga hannu.

Ja da baya Aliyu ya fara yi yana riƙe da bakinsa yna girgiza kai zuwa yanzu banda kaɗawa babu abnda cikin Aliyu yakeyi a haka suka ƙaraso inda yake.
suka fara jansa suna shashshafa jikin sa suna yanga, wani ihu Aliyu ya kurma ya kalli Kb ya ware murya kmar ba shi ba yace"" wayyo Allah na yaya Kb kana gani zasu kashe dn Allah ka riƙe ni
, ya fada yana miƙowa kb hannun.
da sauri kb ya girgiza kai yana juya fuska shima zuciyar sa Banda lugude babu abnda yakeyi.

Dukan Aliyu sosai aka shiga yi babu ji babu gani, tini mganar Aliyu ta canja zuwa ta maza sak saida suka masa lilis sannan sannu suka yadda shi a palourn suka bace.


Saida suka bace sannan su momy suka yo kan Aliyu, Bash ya ɗauke shi suka fice daga palourn suka nufi compound.

suna shirin shiga mota wata motar ta shigo cikin gidan, ko gama perking na cikin motar baiyi ba ya fito da sauri ya nufi cikin gidan, da kallo suka bishi suna kiran daddy Amma ina tini daddy ya shige ciki ba tare da ya juyo ba.

mntawa sukayi da Aliyu suna rigawa daddy baya Yana shiga direct upstairs ya nufa ya shige dakin sa a palour suka tsaya momy ta bishi sama wata uwar kara momy ta kwalla ganin daddy a tsaye jikin wata wardd robe wacce baya bari kowa yaje inda take wata katuwar kwalbace a hannun sa a cikin kwalbar kurwar mutumce a ciki kwance da alama ma dattijo ne dk.da kwalbar ba babba bace Amma hakan bai Hana momy ganin suffar mutumin dake cikin kwalbar ba gificewa daddy yayi ya saki kwalbar a kasa ta fashe wani bakin hayaki ya fara ftowa.daga cikin.kwalbar kafin cikar wasu mintoci gidan ya fara girgiza Yana zubewa da sauri daddy ya ciccibi momy ya fara sakkowa daga saman dk inda ya taka sai wajan ya zube.

Su Bash dake palourn ganin abnda ke faruwa yasa su ficeqa da gudu suka dauki Aliyu sukayi waje suka kallon.yadda gidan ke zubewa kamae daga sama aka jeho su momy daidai lkcn Kuma gidan ya karasa zubewa sannan ya kama da wuta .


Hankalin daddy bai dawo jikin sa saida Ashpa da Ashna suka bayyana a gaban sa suna kyalkyala dariya sai.kuma suka hade rai suka dubi daddy cikin hadin baki suka ce guje gujen ka ya kare yau ce ranar gudun ka na karshe daga yau ka fara lissafin munanan ranakun ka suka karasa maganar suna shekewa da wata mahaukaciyar dariya sannan suka bace ba momy ba hatta su Bash Kb Meerah Meenah da Aliyu da ya farka yanzu tsirawa daddy Ido sukayi suna jiran karin bayani




Oum sharifat ce
ASHPA KO ASHNA
15-16

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA

KHADIJA UMAR ABDULLAHI)GARKUWAR JARUMAI) CE

بسم الله الرحمن الرحيم

Da kallo daddy ya bi inda suka wuce zuciyar na masa zullo kamar zata fasa ƙirjin sa ta fto, ganin zaman bazai masa ba yasa ya miƴe tare da karkaɗe jikin sa ya kalle su ba tare da yayi magana ba suma suka miƴe jikin su dk a sanyaye suka yi cirko cirko a tsaye suna kallon gidan.

yadda komai ya lelece hatta motocin gidan sun ƙone cike da ƙunar zuciya daddy yayi gaba a ƙafa suka rufa masa baya, saida sukayi tafiya mai nisa sannan suka ƙaraso wajan mai pos, daddy ya zura hannun sa cikin aljihun wandon sa cikin saa kuwa ta ciro atm ɗn sa ya miƙawa mai pos.

karɓa mtmn yayi ya zura cikin pos dn yayi ƴan danne danne sannan ya ɗago ya kalli daddy ba tare da ya ce komai ba.

"" dubu ɗari zaka bani"" cewar daddy yana gyara tsayuwar sa. ba a ɗauki mintoci sosai ba mai pos ɗn ya miƙawa daddy atm ɗn sa ya cigaba da harkokin sa.

ran daddy ya fara ɓaci a zafafe ya kalli mai pos dn da nufin yin ƙorafi saidai me? Damm ƙirjin sa ya buga ganin fuskar Ashpa ajikin mai pos ɗn haƙoranta sun yo waje ƙawayr idon ta ta firfito jini na zuba ta cikin idon.

zabura sukayi gaba ɗayan su sukayi baya daddy ya fara tangal tangal zai faɗi mai pos ɗn ya zuro hannu daga cikin shagon, hannun yayi tsaho sosai yazo har wajan daddy ya riƙe shi gam ya tsaida shi sannan ya maida hannun sa ya kalli daddy da murmushi a fuskar sa yace "" Kar kayi saurin faɗuwa ba yanzu ba"" yana faɗa ya ɓace daga shagon sannan a lkcn suka gane ma shagon provision ne kuma a kulle yake.

cike da yanke tsammani suka fara tafiya har suka ƙarasa bakin titi, daddy ya ɗakko wayar sa ya fara duba account.
zero shine abnda daddy ya gani a take ya kurma uban ihu ya zube a bakin titi, momy da ƴaƴan ta sukayi kansa suna kuka amma Daddy banda sambatu babu abnda yakeyi, dk da momy na rufe masa baki Amma hakan bai hana shi ihu yana kururuwa ba .

""Asamau ki barni nayi ihu na shiga uku na gama lalacewa kinsan lokcin da na ɗauka Ina tara kuɗi na? kinsan rai nawa na kashe ?sai kuma ya tashi a fusace ya shaƙe momy yana kururuwa yace ""kece" kece kika sa kwalbar ta fashe ke ce zaki kashe ni"" daidai nan wani mai napep yayi perking ya kalli su bash yace "" subhnllh lafiya kuwa ku shigo dashi mubar nan kafin mutane su taru ""to suka ce tare da yi masa godiya, daƙyar suka tura daddy cikin napep ɗn momy ta shiga Bash ya zuna kusa da ita.

Meerah da meenah suka hau sama Aliyu da Kb suka shiga gefen mai napep ɗn suna gama shiga ya ja suka hau titi.


Alh da Pa ɗn sa saida suka sha baƴar wahala a hannun Ashna sannan ta tabbatar ta karɓe dk wasu kuɗaɗe dake account dn su sannan ta sake su daga nan ta sallami su oga jibo bayan tayi musu warning akan kidnapping daga nan gidan marayu ta wuce ta saka kudin cikin poundation nasu.

Ashpa na zuwa ƙofar gida ta tsaya turus ganin ƙatuwar mota a ƙofar gidan, tafin hannun ta ta duba ta jijjiga kai tana murmushi sannan ta fara murza zoben hannun ta tana kiran Ashna ba jimawa sai ga Ashna ta bayyana suka kalli juna suka.sakar wa juna murmushi sannan suka shiga gidan da sallama.


Mamace ta amsa tana kallon su fuskar ta fal farin ciki ciki suka karasa suka tsuguna suka gaida Ammi da daddy da su Yaya Abubakar yaya Abubakar ne kawai ya amsa Banda Umar wanda fuskar sa a tamke take Yana latsa wayar sa.


Daddy ne yayi gyaran murya sannan ya sanar da su Ashpa dalilin zuwan su da maganar auren su gaba dayan su ba wacce ta dago kai sosai daddy da Ammi suka ji dadin tarbiyyar su inda aka.tsaida gobe a matsayin ranar da zasu je sokoto wajan yayan baban su a nemo auren .

Misalin karfe takwas da rabi Ashpa da Ashna suka fito soro suna tattauna wa akan maganar Yaya Abubakar ne ya shigo soron ya kalle su fuska cike da annuri yace "" to wai ni ina amaryar tawa Ashpa taji dadin yadda Yaya Abubakar bai nuna kyama a gare su ba tace gata nan ta fada tana nuna Ashna ita ma Ashna nuna Ashpa tayi tace ita ce fa yadda tayi maganar a shagwabe saida Yaya Abubakar yaji wani abu tndaga kan sa har dan yatsan kafaraa lokaci daya soyayyar Ashna ta samu gurbi a zuciyar sa yana son mace mai nustuwa mai kunya sannan kuma silent .

Ashpa ta barsu a wajan da nufi cikin gidan a soro na biyu taji an jawo mata hijan cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba tace kai dalla sake ni kana wani yamutsa fuska kmr kaga wani abn kyankyami kifta idi Umar ya shiga yi yana mamakin yadda akai taga fuskar sa ba tare da ta juyo muryar ta ya tsinkayo tana cewa"" ai dole ka kifta ido kmr mara gaskiya ta kasara fada tana fizge hijab dn ta daga hannun sa jikin Umar yayi sanyi zuciyar sa ta fara wasiwasi akan yarinyar.

Ganin zata shige ciki yasa shi saurin shan gaban ta ya tsaya ya hade rai yace "" ke dalla ki nan bana son ki kuma bazan taba son ki ba idan kina son zaman lafiya kicewa daddy bakya so na dn idan kika sake kika aure ni wllh I will teach you a lesson ya karasa maganar tare da yin tsaki kmar daga sama yaji an daki bakin sa da sauri ya rike bakin yana waige waige babu kowa daga shi sai ita .

Murmushi Ashpa tayi sannan ta matso kusa da shi tace "" sai kuma gashi ni naji ina son ka kuma aure babu fashi sannan kmar yadda ka shirya koya mn darasi karka fasa ka Kara daura ramara ta fada tana sakin wata yar siririyar dariya sannan tayi gaba tana shiga tsakar gidan taja wani dogon tsaki tace dn wahala kawai.

Sharara gudu kawai mai napep dn yakeyi tn suna gane hanya har kansu ya kulle bash magana yakeyi Amma mai napep dn yayi shiru kame baya ji saida momy ta gaji ta ce haba bawan Allah Ina zaka kaimu ne ka ji tausayin bata karasa ba kan mai napep dn ya juyo keyarsa wata kara suka saka gaba dayan su Banda daddy Wanda zuwa yanzu baya cikin mutane nasu hankali a haka ya cigaba da tuka napep dn fuskar sa tana bayan sa sun suna ganin hanya har hankalin su ya bar jikin su sai farkawa sukayi suka sami kansu cikin.wani daki an daddaure su day sarka .


Kmar yadda daddy yace haka akayi kashe gari da sassafe suka dau hanyar sokoto cikin ikon Allah suka sauka lafiya inda suka iske yayan baban su Ashpa a kofar gida tarba ta mutunci akayi musu sai bayan sun huta sannan daddy ya kebe da malam ya sanar dashi abnda ke tafe da su.


Farin ciki wajan malam.baa magana ya dubi daddy cike da farin ciki yace "" hakika naji dadin abnda kazo da shi saboda haka nidai na bada su Ashpa ga reku in sha Allah give idan anyi sallar jumaa zaa daura bama bukatar komai daga gare ka sai sadaki shima Kuma mafi kankan ta daddy yaji Dadi sosai haka Ammi saida daga amare har angwayen babu Wanda yasan halin da ake ciki.

Kashe gari ana idar da sallah liman ya daura auren Aysha Muhammad (Ashna ) da angon ta Abubakar Sulaiman )
Sannan Humaira Muhammad ( Ashpa) da angon ta Umar sulaiman)
Akan sadaki naira dubu dari.


Nan fa aka shiga murna Abubakar baki har kunne har ga Allah yanason Ashna a bangaren Umar kuwa zuciyar sa kamar ta fashe saboda takaici amma yaci alwashin sai ya nuna mata bambamci dake tsakanin su .

Kashe gari su daddy suka koma kaduna inda aka tsaida nan da sati daya zaa kai amare ciki sokoto kuwa dangin mahaifin su suka shiga gyara amare da kayan daa irin nan sokkotawa...

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LWo0GX36DMiJAdHiIcVwrl

ASHPA KO ASHNA

17-18
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
NA
KHADIJA UMAR ABDULLAHI ( GARKUWAR JARUMAI) CE 💪🏽

بسم الله الرحمن الرحيم

Aliyu cikin tashin hankali ya dubi Ragowar yan uwansa hawaye na zuba daga fuskar sa yace "" na zata zuwa na gida hutu ne ga rayuwa ta nazata agida ne kawai nake da ikon yin abnda Naga dama na zata iyayen mu zasu cigaba da nuna Mana komai daidaine kamar yadda suka Saba mana a da can saidai Naga sabanin hakan a yanzu ne muke bukatar tallafin ku Amma kun kasa bayan komai muka nema wajan ku bamusan kalmar ba zata yiyu ba meyasa yanzu muke shan wahala kuka kasa yin komai ya karasa fada yana kallon momy da daddy sunkuyar da kansa daddy yayi ya kasa dago kai gaba daya zuciyar sa Banda radadi babu abnda takeyi hankalin sa yana kasan sharudan da aka gindaya masa shekara goma sha biyar da suka wuce .

Ajiyar zuciya meerah tayi ta kalli Aliyu tace "' wannan ba shine abn damuwa ba Aliyu sun koya Mana samun komai sun koya mana taka wanda muka so Amma basu koya mana yanda zamuyi maganin matsala idan ta taso ba sun barmu cikin jahilci mk fifita ilimin boko fiye da na addini gaba dayan mu babu Wanda yakeyin sallah complete a rana na samu damar da zan canja na samu damar da zan zama cikakkiyar musulma Amma momy ta hana dk wanda zai fada mn gaskiya momy cemn take bakin ciki yake mn tn bana yadda har na yadda cewa idan kana da kudi kana da komai yanzu babu kudin babu komai sannan koda adduar da zamu fita daga wannan masifar bamu sani ba wllh nayi nadamar kasance wa ta daga cikin wannan ahalin kuka ne ya kwacewa meerah tayi shiru tana shashsheka .

Gaba dayan su kuka sukeyi da kyar Bash ya bude baki zuciyar sa na masa daci yace "" na sani kuskuren iyayen mu ne basu barmu mnyi abnda kowane Yaya sukeyi ba na tafka kuskure kala kala gara ma ku kunyi karatn bokon niko dk zama na a London banyi komai ba face shaye shaye da fyade wa yaran mutane nayiwa da yawa ciki na zubar da shi wasu sun rayu wasu sun mutu ina yin iya kokari na wajan ganin ban bar wata alama ba dn ko bana taba tnkarar yayan kasar sai namu wannan abubuwan na san ba zasu barni na zauna lafiya ba nagama saduda da wannan azabobin mutuwa ta kawai nake jira share hawaye bash yayi ya kalli daddy da momy yace kafin nan dole ku fada mana menene yasa kuka tarbiyyan tar damu a haka me kuka aikata yake bibiyar mu?.

Kan daddy har yanzu a sunkuye ya kasa dakowa wata irin zungureriyar bulala ce ta bayyana a bayan daddy aka shiga zabga masa baka ganin mai dukan saidai bulalar kawai ihu daddy ya shiga yi kafin ya sosa can sai yaji an sake zabga masa gaba daya dakin yayi shiru bakajin sautin komai sai dukan da akewa daddy da kuma kukan su gaba daya saida daddy ya fita daga hayyacin sa sannan aka tsaya da duka aka shiga zuba masa wasu kananun kankara a jikin sa nan da nan ya fardado Yana rawar sanyi ya bude baki da niyyar magana aka daka masa wata razananniyar tsawa wacce tasa gaba daya dakin ya fara girgiza cikin wata murya mai kama da ta katon gardi aka ce fada musu mai ka aikata jikin dady na rawa ya fara daga kai hawaye na zuba a fuskar sa ya ce"".


Gyara sosai aka yiwa Ashpa da Ashna ciki da waje sunyi kyau fatar su kamar ta jarirai cikin sati dayan nan kuwa soyayya sosai ake zubawa tsakanin Ashna da Abubakar ta wayar daya bata lkcn da zai tafi .

Ashpa ko gaba daya ma ta mnta da wani Umar bata tnawa da shi sai sanda akayi maganar bikin .

Yaune satin ya cika Kuma yaune dangin baban su Ashpa suka dauke su day wasu daga cikin dangin mama suka wuce da su kaduna ba tare da wata bidi'a ba .

Lokaicin da suka sauka kaduna gidan Ammi ana ta shagali cikin karamci Ammi da yan uwanta suka karbi amare aka basu part guda daga cikin gidan sabon kamu Ammi tasa aka yiwa amaren sun sha kyau cikin wani pink dn material Wanda akayi masa ado da stone dack blue abnka da farar fata gashi ansha kunshi abn kamar ka sace su ka gudu kashe gari akayi dinner misalin karfe takwas na dare aka kwashi yan biki amota zuwa wajan event.

Amare cikin gown milk colour mai adon golden stone yayin da angwaye ke sanye da dakakkiyar shadda milk colour sunyi kyau sosai idan ka gansu kmar ba yayan hausawa ba .

Motar da Abubakar yake ciki aka budewa Ashna ta shiga ta zauna a tare suka sauke ajiyar zuciya ita da Abubakar dake cikin motar jingina bayan sa yayi da jikin kujera motar ya shaki daddan kamshin dake jikin ta ya lumshe idon sa ya bude a hankali ya dago ya kama hannun ta ya rike dago kan ta tayi suka hada ido yayi saurin yin kasa da kanta cike da kunyar murza dn yatsan hannun ta Abubakar ya fara yi can kasan makoshi ya fura gogiya ta tabbata ga ubangijin da ya haliccin wannan baiwar tasa kuma ya mallaka mn ita Ina rokon sa da ya bani damar kyau tata mata da bata kulawa cike da jin kunya Ashna tace ''" nima Ina rokon sa ya bani ikon yi maka biyayya Amin hayateee Abubakar ya fada yana janyo ta jikin sa ya zagaye ta da hannun sa wani yarrr suka ji a jiki su gaba daya Ashna tayi lamo a jikin Abubakar tana shakar kamshin jikin sa wanda ya saukar mata da kasala lokaci guda.


Lokacin da aka budewa Ashpa motar da Umar yake ciki tana shiga ta zauna ta jingina da jikin kujera hankalin ta na wajan daddy wanda suka baro yanzu shida yayan sa wani zafi taji a kafar ta ba tare da ta bude ido ba ta ga kafar Umar akan tata Yana murzawa da karfi cike da mugun ta dn guntum murmushi Ashpa tayi still idon ta a rufe ganin bata motsa ta nuna alamun damuwa ba yasa Umar Kara saka kafarsa ya murza da karfi wata yar Kara yayi jin an ja masa dn yatsan kafar sa da karfi har saida yace kasss ha sauri ya dago kafar jin yanda take masa wani azababben zafi sannan ya maida kallon sa ga Ashpa wacce yanayin ta ya nuna kamar Bata san abnda ke faruwa ba .


Haka suka karasa cikin holl dn aka shiga shagali nan dai na

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment