Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


‘YAR NAJERIYA
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



LITTAFIN




SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]





SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga dukkan ALBINOS din Najeriya….You are special a yadda Allah ke son ganin ku.




“YAR NAJERIYA
FARKON FARI (HASNA 'YAR INNAR TA)
Na taso cike da dokin ranar zuwan ziyarar ‘yan makaranta, ba don komai ba sai don na san Inna zata kawo min kanzo, kuli da kwaki, wadanda su ne abinda nake samu a kowanne visiting, sabanin sauran dalibai masu uba a raye, idan aljihun Inna da dan nauyi (in ta samu surfe mai yawa) kafin zuwan ranar ziyarar mu to tana hadomin da mankuli wani lokacin har da busashishiyar yakuwa (rama) wadda zan dade ina jikawa ina kwadantawa.
Makarantar mu makaranta ce ta hadakar ‘yan Najeriya (UNITY COLLEGE) wadda nayi nasarar samu sabida hazakata ba don ina da gatan zuwan ta ba. Duk fadin kauyen mu na fi kowa kwazo a karatun boko da na muhammadiyya har wani suna ake kira na da shi (Huda-Huda ‘yar Inna) wasu su ce (Mungu Park ‘yar Inna) sabida tsabar son karatu na da son Inna ta.
Bayan son karatu Allah yayi ni da tsafta, wadda aka ce it ace cikon addini, duk da irin halittar da yayi min wadda ta banbanta data sauran al’umma, kai bazaka ce girman kauye bace kuma tashin kauye sabida yadda nake kula da tsaftar jiki na. Tsaftar da Inna ke kan ce aljanu ke sani yin ta, domin ta wuce misali. Na taso ban san kowa ba sai Inna ta ban kuma shaqu da kowa ba sai ita, mahaifi na tun ina ciki ya rasu, kuma nice kadai diya ga iyaye na. Sannan ba kowa ke son mu’amala da iri na ba (da mutum mai irin halitta ta).
Mahaifi na Mal. Dabo dan asalin karamar hukumar Kabo ne ta jihar Kano, wanda sana’ar sa ta iyaye da kakanni itace ‘jimar fatu’. Da wannan sana’a yayi aure ya kuma rike Inna ta da mahaifiyar sa Kaka A’I. kakata A’I bata tare da mu yanzu haka tana can garin Kabo.
Mahaifiya ta ‘yar asalin garin Kachako ce inda ci-rani ya kai mahaifi na ya auro ta, bayan auren su ya taho da ita garin su wato Kabo suka zauna gida daya da mahaifiyar sa A’I. duka-duka auren bai rufa shekara biyu ba ciwon ajali ya kama mahaifi na Malam Dabo, kuma bai dade yana jinya ba ya amsa kiran mahaliccin sa.
Mahaifiya ta Inna Zulai ta cigaba da rainon ciki na a gidan mahaifi na har ta haife ni. Na zo da halittar data barranta data kowa a gidan mu, ga dai kyau har kyau amma zabiya ce, don haka ni ban gado fatar jiki na ba a wajen iyaye na kudurar Ubangiji kadai ta sa aka haife ni haka.
A lokacin ne manema suka fara kawo mata caffa, don haka A’I tace ta yaye ni ta bata ni ta samu ta yi aure, amma Inna ta kafe kan cewa ita ba auren da zata yi raino na kawai zata yi har karshen rayuwar ta, sabida irin halittar da Allah yai min, da ba kowa ke son raba ta ba, sannan bata son tayi wani aure da zai sa a kira ni AGOLA.
Zaman mahaifiya ta da kakata A’I sai ya canza salo bayan rasuwar mahaifi na, sabida A’I ta dage sai ta yi aure shine mutuncin ta kuma ta gaji da dawainiya da mu, ta kan ce da wannan zabiyar ‘yar taki wadda ba miji zata samu ba. A karshe ba tare da shawara da ita ba ta amsawa wani malamin makarantar sakandire Malam Saminu da ya nace yana son auren Inna ta.
Rannan A’I ta fita makota sai dawowa tayi ta tarar babu mu babu alamun mu a gidan, Inna ta goye ni mun bar Kabo cikin bacin rai don har ta fara gayyatar daurin auren Inna ta, muka koma garin Kachako gidan su mahaifiya ta, iyayen ta duka sun kwanta dama gidan na gadon su ne ita da Yayan ta Sama’ila.
Yaya Sama’ila na zaune a gidan da matar sa Hajjo, sai mahaifiya ta ta share daya bangaren na iyayen su muka yi zaman mu. Nan Inna ta fara tunanin sana’ar da ya kamata mu fara don mu dinga samun na cin abinci kasancewar Yaya Sama’ila shima fama yake da kan sa ga nauyin iyali duk da haka yana da matukar zumunci akan Inna ta duk abinda ya samu daidai karfin sa yana bata, sana’ar sa itace noman Rake.
Garin Kachako na nan a karamar hukumar Albasu ta jihar Kano. Gari ne ni’imtacce da al’ummar garin duka masu zuciyar nema ne, kusan babu wanda bai da kwakkwarar sana’ar da yake cin abinci da ita, tashin farko muka soma sana’ar danwake da wake da shinkafa a tashar Kachako. Kuma babu laifi muna samun rufin asiri, ni nake wanke kwanuka tare da mikawa masu bukata in an saya. Da muka dan yi karfi muka buga rumfar kwano anan cikin tasha muka saka dogayen bencina guda biyu suna kallon juna.
A wani marece Yaya Sama’ila ya shigo yana ta fada kamar zai ari baki wai akan Dagaci yace ya kai su Hassan makaranta su daina sayar da Rake, cikin fushi yace “in sun daina sana’ar Rake shi Dagacin ne zai ciyar damu? Karatun nan da aka ce yana maida ‘ya’ya kafurai su kuma fi karfin iyayen su zan dauki Hassan da Hussaini in kaisu? Mu da bamu yi karatun ba me ya same mu? Hajjo na kara zuga shi da cewa “ah to dai, ka biyewa Dagaci ya lalata maka ‘ya’ya su zama ‘yan daba in bazasu saida rake ba”.
Innata na jin su haka kawai sai taji tana min sha’awar ni in yi karatun ni da banida future, ‘ya’ya iri na dole su nemi madogara a rayuwa ko su kare a bara bisa titi, madadin bin ta tasha dana ke yi muna sayar da danwake. Sanin halin YaYa Samaila yasa bata yi shawara da shi ba ta wanke hannu tayi lullubi ta kama hannu na muka tafi gidan Dagacin garin Kachako.
“Allah ya taimaki Dagaci ga ‘ya ta HASNA’U marainiya ce, ina so a sata makaranta, daga nan har zuwa lokacin da zata isa aure, duk da bana jin zata iya samun mijin aure”.
Dagaci ya sanyawa Inna albarka yafi cikin Kwando tare da cewa “‘yar ki mutum ce lafiyayya kamar dan kowa, ki daina maida ita koma baya sabida Allah yayi mata halittar zabiya, inama sauran jama’ar gari zasu yi koyi da Innata, da mun fita daga duhun jahilci mun shiga sahun ilmin zamani da ke kara karfi a kauyuka a wancan lokacin.
Daga wannan lokacin na fara karatun firamare tare da ‘ya’yan Dagaci da wasu tsirarun ‘ya’ya da ga al’ummar kauyen mu duk da karatun ba wani mai inganci bane amma mun koyi Huruful Hija’iyyah da rubutu da karatun haruffan boko dana Hausa.
Sanda na gama karatun firamare ba da jimawa ba gwamnatin Tarayya ta kafa UNITY COLLEGE KACHAKO, a matsayin mu na wadanda suka samu alfarmar yin firamare mune dalibai na sahun farko (pioneers) a Kachako wadda ta hada dalibai daga kowanne yanki na Najeriya ciki har da ‘yan kudu da yammacin Najeriya.
Na fara Unity Kachako da kafar dama domin babu jimawa kwakwalwata ta dinga budewa karatu yana shiga, sai a lokacin nasan a firamare ba karatu muke ba, ga islamiyya muna yi da yamma a renakun mako, ga abinci wadatacce gwamnati na bamu a wancan lokacin makarantu sun fi samun gatan gwamnati sabida neman masu yin karatun ake yi ruwa a jallo.
Ubangijin da ya halicce ni sai ya halicce ni ba kala daya da sauran mutane ba, bansan cewa halitta ta abin kyama bace kuma abin gudu sai da na fara sakandire, inda ya kasance makarantar kwana, na gane ba kowa ke son mu’amala da ni ba haka ba kowa ke cin abinci dani ba, ke ko kayana babu mai tabawa sabida Allah ya halicce ni ZABIYA.
“Albinism” halittar Allah ce ga daidaikun bayin sa, yadda yake halittar kowa haka yake halittar zabiya, yawanci gado ne amma ni ba gado bane, farin mu ya wuce misali sannan bama jure zafin rana, gashin kanmu ba baki bane kamar na kowa, sannan masu halittar “albino” na fama da raunin gani (short-sightedness).
Duka ban gane haka ba sai da na fara shiga shekarun balaga, a baya na dauka fari na is normal sabida babu mai goranta min ko kira na ‘zabiya’. Sai zuwana Kachako da naji ana kira na ‘Hasna-Zabiya’. Sai na gane ni ba fara bace mara lafiya ce, abin kyama ga wasu daidaikun al’umma.
Amma hakan bai sagar min da gwiwa ga neman ilmi ba, na saka a raina bazan taba aure ba, zan yi ilmi har sai naga karshen sa. Wanda zai sa in samu abin yi da zan kula da kai na da Innata.
Yau ta kasance ranar ziyarar dalibai, tun safe mun sha wanka mun zuba wankakken uniform muna jiran iyaye da ‘yan uwan mu. Ta fanni na nasan babu wanda zai zo min sai Inna, don haka ina daga layin farko na masu rarraba ido don jiran nasu amma har kusan azahar babu Inna ta.
Sai na koma gindin wata bishiyar darbejiya na zauna abin duniya ya ishe ni, na hada kai gwiwa amma ba kuka nake ba, tunanin halin da Inna take shi ke damu na, don bata taba tsallake rana bata zo min visiting ba. Ga yunwa da ta fara galabaitar da ni. Sai nasa kai na a tsakanin gwiwoyi na, ni kadai nasan irin damuwar dake cunkushe a rai na. Bazan manta ba shekaru na goma sha shidda a lokacin.
Kamshin masculine turare na ji a hancina mai karfi sannan naji ana Magana a kai na.
“Are you alright?”
Da farko ban zaci da ni ake ba sai da aka kara maimaitawa tare da sunana “Hasna’u are you okey?”,
Da sauri na dago ido na dubi mai Magana; he’s tall and slim, shi ba fari ba shi ba baki ba, gashi nan dai wankan tarwada mai kyawun siga kuma ma’abocin tsaftar jiki wanda kallo daya zaka yi masa ka fahimci ilmi ya wadata a tare da shi. Sannan bai nemi komai ya rasa a rayuwa ba.
Kusan zan iya cewa na taba ganin sa sau daya ko biyu, a rashin sani na shine wanda zai juya duniya ta daga yadda take zuwa ga inda ban taba mafarki ba, zuwa ga inda bana fatan kai kai na, shine wanda zai juya kaddarori na daga yadda nake fatan su. Sannan shine tsanin da zan taka ya ruguzo da ni daga kan kyakkyawar turbar dana ke kai.
Da bai shigo rayuwata ba da watakila komai ya cigaba da tafiya min normal a yadda Allah ya halicce ni na kuma mallaki ‘mental well-being’ dina dai-dai. Kada ki ce ko kyawun sa da tsaftar sa ne ya rude ni a’a, wata irin ‘kamala’ ke gare shi da kwarjini mai daukar hankali da ba duk ‘yan adam suka mallaka ba.
A cikin muryar sa akwai ‘maturity’ da ‘tone’ mai nuna sanin ciwon kai, yana daga cikin masu kula da asibitin makaranta, ko likita ne ko ma’aikacin jinya shine abinda ban sani ba, sau biyu na je clinic da bani da lafiya kuma shine ya bani magani ya kuma sa nurse ta yi min allura.
“I’m alright Sir”, na bashi amsa a lokacin da na dago idanuna masu rauni da suka kada suka yi jawur, na dube shi, haduwar idanun da ya janyo rushewar duk wani tubali da na aza harsashin rayuwa ta a kai. Na cewa har abada bazan yi aure ba….tunda ni ZABIYA ce…..
*****









SAHEEB DAN MAMAN SA!!! (IN WANI YA KI KA DA WUNI...)
Tun gani na da shi na farko, zuciya ta bata kara zama lafiya ba, rayuwa ta bata kara komawa daidai ba har yau shekaru talatin a gaba. Ya jirkita rayuwa ta upside-down ta duk yadda yake so, ya hargitsa tunani na ya mayar da shi yadda yaga dama, ya zamo silar da na san cewa ZABIYA ma mutum ne kuma mai 'yanci, amma kuma shigowar sa cikin rayuwar tawa ba farin-ciki ta haifar ba sai akasin sa. In ma da farin-cikin to takaitace ne na wani dan kayyadadden lokaci. He gave me love but the people around him gave me hatred.
“What are you crying for Hasna’u?”
Ya tambaya cikin kulawa. Ban yi niyyar Magana ba amma sai naji bazan iya share shi ba, duk da na san ba abinda zai iya akan kawo min Inna ta. Ko gano min dalilin rashin zuwan ta.
“’Yan gidan ku basu zo bane?” Ya sake tambaya kafin in bashi waccan amsar. Ganewa da yayi cewa hankali na ba ya jikina sabida yunwar da ke sakadata. Ban san san da nace masa.
“Ai ni bani da ‘yan gida, Innace kawai take zuwa min kuma bata zo ba. Ba kuka nake yi ba hutawa nake yi Sir”
“baki da Wa ko Ya, kuma baki da kanne? You have no relatives? Baban ki fa?”
Muryarsa is husky mai zurfi da kauri ta 'yan boko mai ratsawa har cikin zuciyar mutum. Murya raunane nace, “tun ina ciki Babana ya rasu, ni kadai ce a wurin Inna ta”.
Sai ya ce “to dan jira ni ina zuwa ko?”
Kafin in ce komai ya juya cikin takun sassarfa ya bar wajen. Bai jima ba ya dawo da farar leda a hannun sa ya mika min, sannan yace.
"Zan turo kanwata Nusaiba ta kawo miki abinci, ita muka zo wa visiting. Though i'm working here. Na hango ki anan na dauka kuka kike yi, don na san ki tun da jimawa a clinic”. Hannu biyu na sa na karba, tare da cewa.
“Thank you so much Sir”.
Ya taka a sannu ya bar wajen, amma kamshin kakkarfan masculine turaren sa bai bar shiga hanci na ba. Na bishi da kallo ina kiyasi, a very soft-hearted gentleman indeed! Har sunana ya sani, to ta ina? Sai na tuna da sanda na je clinic an tambayi sunana kuma an rubuta a folder.
Na maida duba na ga ledar da ya bani, wadda sanyin abinda ke ciki ke ta taba cinya ta, na fiddo gorar dake ciki yoghurt ne mai sanyi kuma mai girma, sai ruwan FARO mara san yi. Har karkashin zuciyata nagode masa, na kuma yi masa addu’ar alkhairi. Ashe har yanzu akwai sauran mutane masu son taimako saboda Allah?
“Nusaiba zuba abinci ki kaima waccan yarinyar ta karkashin bishiya?”
Kyakkyawar budurwar 'yar hutu wadda aka kira Nusaiba, da ganin ta ka san she's born from a silver spoon, ta juya tana kallon inda Yayan nata ya nuna mata, da sauri ta juyo ta dube shi cikin mamaki. “Waccan zabiyar?” Har tana kwalalo ido waje. Ya kalle ta da mamaki “ZABIYA ba mutum bane?” Sai Maman su ta dago daga kan waya da take dannawa ta dube su tana tambaya.
“Menene wai? Ya kamata ku tashi mu tafi rana ta yi” tace da ‘dan nata dake tsaye, amma duk hankalin sa yana kan Hasna’u. Nusaiba ta ce “Mama wai Yaya ne yace in kaiwa zabiyar can abinci” Mama ta ce “Zabiya kuma? A kwanon wa za’a kaiwa zabiyar abinci ba dai nawa ba?” Nusaiba ta yi dariya amma suna hada ido da Yayan nata ba shiri ta hadiye dariyar ta. Sabida mugun kallon da ya wurga mata.
Kawai sai gani suka yi ya sunkuya ya dauki plate yana zuba abincin da kan sa, ya loda soyayyen naman kaza da salad ya rufe yayi gaba abin sa.
Nusaiba ta ce “oh ni ‘ya su Yaya SAHEEB akwai jaye-jaye”. Mama tace “in ya dawo da plates din ki zubar, dan kankanbar tsiya kawai da fin kowa iyawa.”
“Take this food Hasna’u”.
Da farko ban yi niyyar karba ba, amma intonation din cikin muryar sa ya nuna how much he cares ga son na ci abincin, da yadda ya damu da kadaicin da ya riske ni a ciki. Sannan Inna ta sha ce da ni ba’a maida hannun kyauta baya.
Hannu biyu na san a karba, a karo na biyu, tare da cewa “nagode Sir”
“Sunana Saheeb”.
“nagode Uncle, ni kuma sunana Hasna’u Dabo. Zan iya cewa kana da kirki Uncle?” Murmushi yayi yace “maza ki ci ki kai musu plate din ki koma hostel, saura kadan lokaci ya cika, tunda Mamanki ta kai har yanzu bata zo ba to bazata zo ba, khair insha Allah”.
Daga haka ya bar wajen, ni kuma har ya kule na kasa dauke ido a kan sa. Ina mamakin kyakkyawar zuciya irin tasa.
Tunda nake ban taba cin abinci mai dadin wannan ba, kunne na har wani irin kaikayi yake yi, sannan ga nama zuqu-zuqu dana kasa tantance na kaza ne, ko na zabo ne ko na dawisu ne don dadin sa, nayi masa cin hani’an na dau plate din zuwa inda suke, har sun fara haramar tafiya. Suna nannade katon kilishin da suka zauna a kai.
“Kin gama Hasna’u?” Ya fada tun kafin na karaso gare su.
“Na gama Uncle kuma nagode sosai”. Na fada ina mika masa farantin, tare da kokarin russunawa don gaida Maman na su, sai ji nayi an tankwabar da shi ya fadi kasa.
“Me zamuyi farantin da zabiya ta ci abinci? Allah kayi mana tsari da mummunar haihuwa”.
Ban taba jin kalaman da suka doke ni irin wadannan ba, duk da ba yau aka fara goranta min halitta ba. Amma wannan matar babba ce ban zaci irin wadannan kalaman na rashin darajta dan adam daga bakin ta ba. Yawanci duk masu yi min gorin zabiya tsaarrraki na ne sai ko Hassan da Hussaini 'ya'yan Kawu na. A nan makarantar dai dalibai 'yan uwa na basa mu'amala da ni amma ba'a faya goranta min da kakkausan harshe irin haka ba, sai da ace "Hasna - Zabiya".
Sai na juya sannu a likkafa hawaye cike da ido na na bar wurin. Ina jin shi yana “haba Mama! Haba don Allah Mama! Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi……”. Sauran maganganun ban bari sun shiga kunnuwa na ba domin takawa na yi da gudu na karasa hostel ina mai nadamar karbar abincin su. Saidai wannan karamci na wanda ya kira kan sa SAHEEB ya kasa dakushewa daga zuciya ta.
To haka 'yan adam muke dama kowa da halin sa, sai ka ga da ya fi uwa hankali, kuma a hakan dai ita ce mahaifiyar sa.
Tun daga wannan ranar na soma daurawa kaina damuwa wadda a baya bana damun kai na. Ganewa da nayi cewa halitta ta abin kyama ne ga wasu bangaren al’umma. Damuwar da ba ni kadai ta soma yi wa illah ba, har da karatu na.
Performance dina yayi kasa sosai lokacin da aka hada continuous assessment, ni da nake daukar na daya sai gani kowa ya doke ni. Mr Samson shine class master din mu kuma shi ya fara noticing something is wrong a tare da ni, duk da cewa dama can ni din ba ma’abociyar walwala bace amma bana wasa da karatu. Ganin wannan fadowa kasa da nayi warwas, yasa Mr. Samson kira na staff-room.
“Hasna do you know that your marks are poor? ( Hasna kin san cewa makin ki bai yi kyau ba?) Kina da damuwa ne ko baki da lafiya ne?”
Idanuwa na sukayi rau-rau suna shirin zubar da hawaye. Mr. Samson ya dage sai ya ji abinda ke damu na, ni kuma na rasa me zan ce masa. Da zan iya, da na ce masa so nake ya samo min mai, wanda in na shafa zan koma baka (kirin). Ko mutane sa daina kyama ta da goranta min. The stigma attach to my disability is tormenting my heart.
To amma bazan iya gaya masa hakan ba kada ya ga rashin hankali na, (canza halittar Allah) sannan sauran malaman duka sun bada hankalin su a kan mu. Kowa so yake ya ji dalili na na komawa ba fuss a karatu. Sabida kowa da ya sanni ya san mai kokari ce kuma zaqaqura. Daga dalibai har malamai.
Sai kawai na samu baki na da cewa “bani da lafiya ne”. Don dai na samu Mr. Samson ya kyale ni. Domin kuwa bai da maganin abinda ke damu na.
Mr. Samson ya ce “Oh my

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment