Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kullum.

Rungumar da Josphe yai wa Meenat bai Ankara ba ya zurma a shaukin so yaji anyi kutuball dashi har sai da ya kife k'asa a fusace ya juyo Don ganin Wanda yai masa wannaan aika aikar
Damko wuyan rigar Josphen yai a fusace yace,

The man education Muslim is like car without tayer "Kadube ka k'aton Arne ka zo kana taba wacce ba muharramrka ba
Koda ganin haka Meenat ba tayi wata wata ba tazo ta d'aga hannu ta sharara wa Hafiz mari.
Cikin huci take cewa nace bana sanka bana sanka saime?

Kafita daga Rayuwa ta.

Abin haushe taba jikinsa da tayi sai yaji wani irin nishad'i yana fisgarsa.

A hankali ya furta Ilove you Meenat.

A fusace ta juyo ta Kuma wanka mishi wani Marin murmushi ya ciga ba dayi cikin sauk'in so.

Josphen yai tsaye yana duban Meenat cikin mamaki da al-ajabi ransa a b'ace na ganin wanna n sakaran zai zo har gaban a bar kaunarsa yaci mutuncinsa,
Kallon Meenat yai tare da cewa,"Golden girl "Waye wanna?

Tab'e baki tayi kafin tace "I have never seem
him
A kufulu Hafix ya juyo "Meenat Ni ke baki saniba?
Akan wanna k'aton Arnen Ni ke baki tab'a gani ba? Yanxu kin zab'i K'aton Arne a kaina? Makiyin Manzon Allah (S.A.W.),





*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

💖💘💘

*SO KO HAUKA?......*

💘💘💖


(Daga Marubuciyar ISHARA.)

Ayshatour Abdul-falalu.

Mommy n Yusif


16-20.


K'auye.



Shatu ta ciga ba da kuka tana cewa Baba don Allah ka sanar min da gaske ne ni Ƴar inna ce?

Idan ni ba ƴar ta bace ka gaya min gaskiya
Baba a kullum kai ke sanar min mutum baya zama cikakken Musulmi face sai an jarrabeshi da ƙaddarori ''Ni musulma ce ka sanar min hatta annabawan Allah 25 da aka
ambata da alq'urani dukkaninsu sai da Allah
Swa ya jarrabasu kamar ANNABI ISAH AS)DA KIRISTA. ANNABI MUSA AS) DA FIR'AUNA. ANNABI YUNUSA (AS)DA ALLAH YASA KIFI YA HAƊEYESHI. ANNABI LUƊ (AS)BABBAN ƊANSA DA MATARSA. ANNABI IBRAHIM BABANSA BA MUSULMI BA, ANNABI YUSIF DA 'YAN UBA.. . . . . Da sauransu duk da nasan cewa imanimmu bai kai na annabawa ba amma duk kaine ka sanar dani kissoshinsu. Don haka don soyayyar ka da manxon Allah ka sanar min din waccece, ta zuba mishi ido tare da share hawaye.

tausayinta ya kama Mal. Bello ya zuba mata ido ya share hawaye ba tare da ya bare ta gani ba , tabbas Shatu na cikin ukuba ya zama dole ya sanar da ita ko ita ɗin waccece ,
yace zan sanar dake kaɗan daga abin da baki sani ba Shatu.

Bai jira cewar ta ba ya soma da faɗar-

WATA RANA ta kasance Lahdi ina zowa kasuwar charanchi siyar da ruwan alwala da nakeyi a duk ranar lahdi.

A dai dai mararrbar ƙauyen nan namu nayi kiciɓis da kwali yashe a ƙasa, ga kukan jariri a ciki gabana naji ya yanke ya faɗi da sauri na ƙarasa na buḍa abin mamakin kuwa jariri
ne na gani ciki yana ta kuka.

Kamar kadda na ɗauka sai kuma na daure nayi Bissimillah na ɗauka.
Ko da isa ta gida Hansai ta ganni da jaririya bata tsaya wata-wata ba ta ɗaga hannu a ka ta soma kururuwa wai Mal. Ya sake hali yaje yayo ma wata cikin shege ta bashi ƴar.

Kankace me sai ga mutan ƙauye maza da mata har da mai mai gari kowa ya firfito.

na zauna tsaf na kora wa mutanen ƙauye labari, kowa ya yaba da ni a ka dinga tur' da hali irin na hansai domin kuwa kowa yasan niɗin ba mutumin banza bane.

Shatu sai dai fa kiyi haƙuri da abinda zan gaya miki domin kuwa nasan keɗin mai karɓar ƙaddara ce,

Bayan mun buɗe kwalin da aka tsinceki akwai takar da a ciki wacce aka yi rubutu gwaɗo-gwaɗo.

Rubutun ya kunshi haka ,

WANNAN ƳAR SUNANTA AISHATU, KUMA ƘADDARA CE TA FAƊA MIN NA HAIFETA SHEGIYA CE BATA DA UBA. DON ALLAH DUK WANDA YA TSINCE TA YA RIƘE MIN ITA TSAKANI DA ALLAH SUNANTA AISHATU.

Shatu ƙanwata Rahmatu ita ta shayar da ke kafin Allah ya amshi abarsa.
Kuma a cikin kayanki akwai sarƙar goal. ɗaure a wuyanki.

Wannan shine Shatu.
Shatu ta ƙanƙame Mal. Bello.
Kuka take wiwi duk mai imani idan yaga shstu a wan an hali dole ne ya tausaya mata.
Mal. Bello ba rarrasheta ba ƙyaleta yai taci kukanta ta gode Allah

Mal. Bello ya ɗago ta tare da bubbuga bayanta alamar rarrshi.


Bammm suka ji an bugo ƙyare da ƙarfi

kururuwar Inna Hansai ta ankarar da su.

"Ye eee kuwa jama'a ƙwartaye abinda na daɗe ina sanar daku yau gashi ya tabbata.
Inna Hansai ta jawo aci bal-bal ɗin ɗakin ta kashe.
Ihu take tana ƙarawa iya ƙarfinta ,

Mutane suka taru fululu wani yasa touchlat ya dallaro Shatu da Mal. Bello.


KATSINAN DIKKO

Hafeez yace yanxu kin zaɓe ƙaton Arne a kaina Meenat?
Meenat ta mayar da dubanta a kan Josphen tare da ruqu hannunsa tace, tana nuna Hafeez,
Man that is mental. Gyaɗa kai Josphen yai yana murmushi, Mota suka ƙarasa suka shiga da gudu Josphen yaja motar tare da ɓula ma Hafeez ƙura , shaddarsa tayi jawur da ƙasa.
Dafe kai yai, ''Yaushe Meenat ta zama haka?
Yaya zaiyi da ƙaunar Meenat da ke kwance a ransa?
"Uhum yanxu mafita ɗaya ta rage min bara naje ƙauye wajen kakata watakil na samu sauƙin raɗaɗin da nake ji akan san Meenat
dolene na ziyarci ƙauye Hafeez ya faɗa dafe da kai.


Ko ta halin k'ak'a sai na AUREKI MEENAT.



**********


Akan hanya Josphen ke dubanta tare da cewa Goldyn ctgirl ,"Wai yaushi zamu yi Aure?


Das!das!
Gabanta ya faɗi
''Josphen ina jin tsoron tinkarar Daddy da wannan maganar Amma kai me zai hana muje a wajen Mom dinka a ɗaura mana aure a ɓoye kaga ita kaɗai tayi Amanna da soyayyar mu koko yaya kagani?

Rungumota yai tare da shafa face ɗi ta yace
thankyou my Goaldyn giril mu ƙarasa gidan

Da murna Mom Josphen ta tarbesu cikin farin ciki, Josphen yace Mommy mun yanke hukuncin Aure ni da My goldyn giril
Mommy auren ya kasance secret marrage. (auren sirri)
Batare da sanin iyayenta ba nima Ba tare da sanin Dad va.
Murmushi Mommy tayi tare da cewa gaskiya lokaci yayi da ya kamata a ce kunyi aure amma jus calm down i a aready had a plan.
Murmushi sukayi gaba ɗayansu cikin farin ciki.
Yanxu abinda ya kamata bana san abin ya ɗau dogon lokaci gobe zan tara ƙawayena ayi baiko na biya ko, daga Meenat har Josphen rungumeta suka yi suna masu farin ciki.

lallai Chakwakiya ta fara dannowa
ku ci gaba da kasancewa dani Ayshatou Momyn yusif don jin ci gaban labarin.




*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

💖💘💘

*SO KO HAUKA?......*

💘💘💖


(Daga Marubuciyar ISHARA.)

Ayshatour Abdul-falalu.

Mommy n Yusif




(Labarin Meenat 'yargata da Shatun K'auye)
By









Ayshatour Abdul-falalu
Mommy Yusif.


(Marubuciyar ISHARA)



̄21-25.

(K'auyen k'ereriya)

Mal.Jabiru ya haska da touchlat dinsa Mal.Bello ne rike da hannun Shatu tana kuka shima yana hawayen takaicin mugun hali irin na Hansai.

Salati suka d'auka Mal.sale yace, yana duban Hansai "Kekam Hansai kinji kunya wallahi kuwa ace ki rasa wanda zaki k'ullah wa sharri sai mijinki uban 'ya'yanki.
Mu bamu ga abinda kika fad'a ba illah kuka da muka tarar sunayi wanda baya rasa nasaba da kukan bak'in cikin Halinda kika jefa su na bak'in sharri.
Don haka matsayina na mai gari kina da bulala d'@ri tayi wa mutanen da basuji ba basu gani ba sharri.

Hansai ta aza hannu aka tana kururuwa
Mal.Bello ya dubi Shatu yace kiyi Hakuri kiyi Hakuri Aishatu.

Kowa yai caaa ana tambayarsa dalilin kukansa , ya kwashe labari tas ya sanar musu, kowa Allah wadai yake da halin Inna Hansai,
Jama'a da dama sun vukaci Mal.Bello da ya basu ruk'on Shatu ko don ta Huta da azabar Hansai, Amma ta turje tace bazata tab'a rabuwa da wanda take jin shine uwa da ubanta ba.

Tunda daga lokacin kowa ke san Shatu a k'auye mai gari ya hana a d'ora mata tallah , haka zaliqa kullum sai tayi wanka da wanki saigata tayi shar abinta ashi kyakkwace sosai , kankace me samarin k'auye sunyo mata caba😭😭

a Shatu kowa Shatu ashe ita d'in kyakkyawace.

Daga ciki harda d'an gidan mai gari ga kuma samarin Asabe so na gaskiya da gaskiya sukeyi mata sab'anin Asabe da sai dai abi yarima a sha kid@.

Aikam wannan sabon Al, , amari da ya faru wa Shatu sai taji ina ma inama inama hakan bai faru gare ta ba😭😭
Hansai taci gaba da cewa indai na tsotsi nonon Talatuwa wallahi shatu sai kin gane kurenki, gidan malamai gidan bokaye chan Inna Hansai tayi wa mafak'a sai da duk wani abu da Hansai ta mallaka ya kare kaf Asiri kuwa gaskiyar mai shi.

Idan kuka ga Rayuwar shatu sai kun zubar mata da hawaye 🕵🕵🤦🤦🤦 sai da takai hatta shi kansa Mal.Bello a yanxu baya bata kulawa kwata-kwata a rayuwarsa.

Mai gari k'iri-k'iri yaji ya tsani yarinyar baya san ganinta sam.
Mamuda d'an gidan mai gari da ya soma sauya mata rayuwa da d'inkuna masu kyau tune lamarin ya juye ga Asabe.

Tallah kuwa da inna Hansai ke d'orawa shatu bata k'irguwa da safe tallar kunu da rana taliya da manja da yamma suyar Awara a k'ofar gida.
Idan dare yayi kuwa a kuma d'ora mata kunun dare.

:-*:-*:-*:-*:-*:-*:-*:-*:-*:-*:-*:-*

Da safe Shatu na duk'e tana ixan wutar kunu,
Yaran Inna Hansai kuwa na daga gefe kowacce tana ta cika tana batsewa, Shatu tace, "Inna ta tafasa fa tukunyar kunun.
" Cewa nayi ki dubamin Shegiyar gari?

"Ke zonan Asabe ta fad'@, ta isowarta Asabe vatayi wata-wata ba ta sa k'afa ta tad'e ta kicaaa ta fad'i baki ta ya dafji k'asa.
Gaba daya suka kyal-kyale da dariya.

Mal.Bello yana kallo Uffan bai ceba Shatu ta fashe da kuka " Ko shi ma ya daina sona ne?

Zo ki janye min kunun nan, dukawar da shatu zatayi wajen janye bokitin kunu.
Inna hansai sauran ruwan xafi da ta rage

Batai wata wata ba ta kwarara wa Shatu su a jiki wayyo Allah!
Rad'ad'in ya sata sakin razananniyar k'ara.

Duk suka shek'e da dariya.wajen ya gwalje ga mugun rad'ad'i."Zaki zo ki dauka ki tafi tallar koko sai nayi k'asa dake?

Tana kuka ta d'auki bokitin k'osain tatafi. Jikinta ko ina rad'ad'i yake bata tav'a ganin marar imani ba irin inna Hansai.

Ya dage iya k'arfinsa sai Hon yake azab'a tayi wa Shatu yawa sam bataji ba sabo da tuyar ta fito rad'au.
Takaici ya ishi Hafix A fusace ya fito ya sha gabanta "ke bakyaji koko kurmace ke?

Shiru yaji tayi fuskanta yasa ya dago " Ke ya fad'a da k'arfi sai a sannan ta d'ago fararen idanunta da sukayi jajir ta zuba mushi ido.

A uziyya ya ja tare da jan ayatul-kursiyyu ko gamo yayi koko ya fara hauka tunda gashi duk inda yaje ita yake gani da k'arfi ya kirayi sunanta "Meenat " Yar gata?
Jin ya kirata da wani suna yasa ta tunanin ko dai irin yan yankan kannanne?

Ta kamce kafa me naci Wayyo Allah gudun da zatayi yayi daidai da lokacin da tana d'ga kafa tayj karo da katon dutsin dake wajen.
Da sauri ya isa wajen"Meenat meya kawo ki nan? yaya naganki a k'azamar shiga irin wannnan me kika zo yi?
"Ba ita bace! " Ba ita bace furucin da Shatu ke furtawa kenan Hafiz ya dafe kai ya na jan dogon salati wannnan wacce irin muguwar kama ce hatta murya irin ta Meenat (Yar gata)
Shin meke faruwane??.........




Ku ci gaba da kasance wa ni mommyn Yusif A domin nishad'@n tuwa da wannan zazzakan labari me cike da sarkakiya cin Amana ban tausayi al-@jabi.


So ko hauka?.


by


Ayshatour Abdul-falalu

Mommyn Yusif.





*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

💖💘💘

*SO KO HAUKA?......*

💘💘💖


(Daga Marubuciyar ISHARA.)

Ayshatour Abdul-falalu.

Mommy n Yusif




(Labarin Meenat 'yargata da Shatun K'auye)
By









Ayshatour Abdul-falalu
Mommy Yusif.


(Marubuciyar ISHARA)







📄 page -26 -30.
Wai meke faruwa kama ita da Meenat kamar an tsaga kara sannan muryar su iri daya banbanci fa?
Abu daya ya banbanta su Meenat wayayyiar yarinya yar birni wacce ta tashi cikin kudi sabanin wannan da ta kasance bak'auya wacce ke rayuwa cikin wahala.

Hafez bai k'ara rud'ewa ba sai da yai tozali da yatsar k'afar ta da hannunta sannan yaja dogon salati.
"Anya ba Meenat ce keyi min gizau ba?
" Anan garin kike?
E"
Ta fad'a a tsorace.
"Meye sunanki?
"Shatu"
Jawo wayarsa yai I phone 11ya shiga Gallary tare da zak'ud'o photon Meenat duk inda ya duba ba ban-banci tsakanin su da Shatun k'auye.

Lallai Allah mai iko.
Abu mafi d'aure kai hatta da tsayin su iri d'aya da Meenat din tirk'ashi!

Shatu ta mik'e tana karkad'e jikinta ko da ta duba bokitin tallar ta ta ganshi a fashe ta kuma tuna da mummunar a zabar da zata fuskanta a wajen Inna Hansai tuni hankalinta ya tashi a razane ta aza hannu aka🙆🙆🙆 ta fashe da kuka.
Hafiz ya juyo izuwa gareta " lafiya Shatu "Meke faruwa?
Bokitin tallah ta ta fad'a cikin kuka.
Dai-dai lokacin Zulai ta doso layin." Shatu lahiya?
Ganin bokitin Shatun a fashe yasa Zulai cewa,
"Shatu kin hi gan ga d'a uku! " waya hasa miki bokiti?

Hafeez ya juyo da tambayar sa ga Zulai yana cewa, "Shiga uku fa ki kace? a kan bokitin?.
Zulai tace da kwaran-kwatsa sai Innah Hansai ta kusa kasheta yau sabo da wannan bokitin." Waccece Inna Hansai ?
"Matar Baban ta ce.
Koda naji ya fad'a Zulai ta ciga ba da fayyace mishi irin uk'ubar da Shatu ke fustanta a wajen Innah Hansai.
Tausayin ta ya kama shi lallai sai yanxu ya dad'a tabbatar da cewa bafa tare da Meenat yake ba to yaya akayi su kayi kama tamkar an tsaga kara?

Gudar naira dubu sabuwa dal ya fito da ita a aljihu ya dube ta." Karbi ki siyi wani bokitin wannnan kuma kud'in kayan tallar ne ya kuma zaro wata naira dubun.

Zaro ido tayi duk da cewa hankalinta ya kwanta ta amshi guda ta ce wannan ma tayi yawa domin bokitin bazai wuce dari uku ba a yayin da kayan tallar duka na d'ari hudu ne.

"A'a sai fa kin karb'a ya fad'a cikin d'aure fuska.
Ai nine na baki ko?
Kin ga bara na k'arasa inda zani cikin sauri yabar wajen.

Zulai ta dube Shatu kana tace kawai ki ajiye ki dinga kashewa.
Shatu ta girgiza kai. " Aa Baba ya hanani kinga idan kina so karb'i guda sai na kai mata d'ayar Zulai tace, "Wallahi bani ina so.

***************



SO KO HAUKA
Complete HAUSA NOVELS Document
Shigar Shatu gida keda wuya ta zaro naira dubu tare da mik'a wa Innah Hansai tace, " Innah gashi, Innah Hansai ta a za hannu a ka " nashiga uku yarinya ta gama lalacewa kenan iskanci kika fara?
Maza taho na duba ki, jawota tayi tayi band'aki da ita ta kwaye mata zani ta d'auki sauran barkonon k'osai ta raraka mata wayyo Allah!
Duk mai tausayi sai ya tausaya wa Shatu,
Karon farko Jimmala ta mik'e tsaye.

"Haba Inna wannan wanne irin rashin tausayi ne duk fa cikin yaran ki babu wacce ke mike abinda shatu keyi miki amma don me zaki dinga Azabatar da ita irin 💁 haka?
Inna ki sani da d'a da dukiya ba'ai musu mugunta domin kuwa ba@ san mai morarsu ,
Inna Hansai ta juyo ga Jimmala." To uwata sai ki taso ki dake ni."Anya kuwa ni na haife ki Jimmala duk cikin yara na babu wanda ya tab'a yi min katsalanda sai ke don haka muddin ki na san zama lpy ja bakin ki kiyi min shiru.

Jimmala bata saurari Hansai ba ta jawo Shatu tasa savulu ta wanke mata tare da shafa mata vasilin a ranar yini tayi xungur tana kuka sabo da a zaba ga tuya ta fito tulu-tulu.Jimmala ta kai ta gidan mai maganin gargajiya a ka saka mata magani iya azabar duniya Shatu ta ganta...

KU DANNA HOTON KASANNAN DON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN
https://t.co/0NiWvztyxk

****************
Asu bar fari taji saukar ruwan sanyi wai ta tashi ta d'obo ruwan sanwar kunu.Jimmala tai tsallen albarka tace, "Gaskiya Innah ba inda Shatu xata, daga yau a dinga raba d'ibar ruwan idan wannan ya d'ibo yau gobe wannan ya d'ibo bara na fara daga yanxu ni naje na d'ebo gobe Asabe jibi Abu.
"To bazaki ba " Kafira 'yar iska.
"Wallahi ita ma Shatun ba zata ba wannan
Ai rashin imani ne ta d'evo ruwa sannan kunun ma ita zaki d'ora mata tallah kuma taje duk wa'innan hird'a hird'an dake zaune.
'Daukar ruwa kuwa matsayi na na 'yarki bara na je, bata jira cewar su ba tayi gaba .

Aikam Innah Hansai tace dawa Allah ya had'a ba da Shatu ba ta jawo ta dinga nark'a har shigowar jimmala da kyar ta k'wace ta.
Fitar Jimmala Innah Hansai ta jawo ni ta matse min baki sai na fad'a mata wajen bokan da naje ya asirce jimmala rantsuwa nake ina k'ara ban san wani boka ba , amma ina sai da tayi ma baki na jina -jina.

****************Kammala shiqa kunun keda wuya.
Na zo na dauqa bakin soro ta biyo ni.
" Shatu.
A mamakance na juyo na dubi Innah Hansai domin ban tab'a jin tayi min maganar nutsuwa irin haka ba.

"Yawwa Shatu abinda nake so kije wajen mutumin jiya wanda yai miki irin abin nan na jiya?
Ya baki kud'i wallah bazan dake ki ba kinji?
" Inna Ni ba abinda yai min illah kad'e ni da mota da yayi kuma a gaban Zulai akayi kuma a yanxu bansan inda zan ganshi ba.
Rank'washi ta zuba min "Shigiya tsintacciyar mage komai akai da jaki sai yaci kara.

Shiru nayi na wuce, Isowata kenan inda nake siyar da kunun k'amshi ya ziyar ci hanci na.

" Meenat 'YAR GATA naji an fad'a na d'ago na dube shi mutumin jiya ne , wato wanda Inna Hansai ke zaton iskanci nayi ya bani kud'i kamar wannan me k'amshin me zaiyi da k'azama irina?.............
Katse ni yai.
"Meenat 'yar gata tunanin me kike haka?

" Don Allah ka daina kira na haka "Sunana Shatu.
" Saboda ke d'in bakya da ban-banci da ita kuma ki ajiye a ranki cewa wannan sunan specie name ne da na zab'ar miki a karan kaina..
Ya jawo kwanon k'osan yana cewa." Na nawa ne?
"Kaga don Allah da zaka tausaya min da ka kyaleni kodon bala'in da ka jazamin jiya a wajen Inna Hansai.

Shiru yayi bayan yayi nazari akan labarin da Zulai ta bashi a jiya.
Tausayinta k'arara ya bayyana a gare shi.

" Yaya batun karatu fa?
"Izif d'ina Arba'in. " wow ki ce ked'en malama ce ko? ta boko fa?
" Au ka manta nan bamu da pramary sai anje charanchi akwai (payelat)
"To yaya akayi bakya zuwa?
" A da ina zuwa tallah ta hanani yanxu.
"A halin yanxu ki na san koma wa.
" E, sosai kuwa domi n nayi pramary dakyar shima a lokacin governort ta aiko da jami'ai.tsaro domin iyayen da ke hana yara zuwa.
Muddin kina san karatu to da yamma zanzo in gana da babanki.
Shiru nayi domin ina jin tsoron Inna Hansai matuk'a.
A gaba na ya rabar wa almajirar k'osan kamar kullum gudar naira dubu ya bani.
Wajen k'arbar kud'in mukayi ta jayayya a dole na amsa.
Shago naje na chanxa domin kuwa ko na kai wa inna bina zata yi da sharrin zina kai tsaye gidan su Zulai na wuce na sanar mata duk abin da ke faruwa Zulai ta amshi kud'in ta a jiye min.
Hafeez yana jin dad'in zama da Shatu har ya fara manta wacce ce "Meenat 'Yar gata tunda ga mamadinta ya samu.


Ku ci gaba da kasance wa dani domin jin jumurd'ar da ke cikin wannan kayataccen labari kar ku manta Meenat na fa chan zata yi aure da Josphen kirista batare da sanin iyayenta ba.

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ


💘💘💖
SO KO HAUKA?
(Labarin Meenat ƴar gata da Shatun ƙauye)
💘💘💖
By Ayshatour Abdul-falalu
(Mommy'n Yusif)

*_From the writer of ISHARA_*




📄 page 31-35.

Da sanyi safiya an tashi da muk'u-muk'un sanyi Shatu na kwance dai dai lokacin da take tsaka da jin dad'in barcinta.
Innah Hansai da yaranta sun jawo kyare sun gark'ame d'aki.A yayin da Baiwar Allah Shatu ke takure a madafi.
Tsakiyar Barcin taji an watso mata ruwa masu sanyi a jiki.
Firgice ta mik'e sai'ilin da ta saki wata razananniyar k'ara numfashin ta ya d'auke na wucin gadi.
Hak'oranta na karo da juna suna karkarwa.
Kuka ta saki da k'arfi, ita yaushe zata fita daga wannan uk'ubar ne ?

A yau taji ta samu jarumta da k'arfi nayin gaba da gaba da Innah Hansai, bakinta na karkarwa tace, " Innah duk zaluncin da kike min sai Allah ya saka min Abinda nake miki kaf 'ya'yanki babu mai miki ko da rabinsa amma ni kike zalunta sabo da son zuciya nayi miki tallah na dibo miki ruwa amma yadda ake sanyin nan ko Alwala da kyar mutum ke yinta saboda sanyin da ake yi amma kin d'ibi ruwa mai sanyi kin kwaranya min a jiki kuma nan..................fau fau taji an shillah mata maruka kyawawa kuma tagwaye.
Asabe ce tsaye tana huci.
"Ke Don " Ubanki uwar tawa zaki yi wa rashin kunya?

Innah Hansai ta kyal-kyale da dariya 😀 tace.
"Dakyau kare da yaga rawar kura.yanxu nasan Asabe kin haifu.
Jawota Asabe tayi ta ci gaba da kirb'a kamar ta samu jaka Kana daga bisani Innah Hansai tajata keeeeeyyy tayi k'ofar gida da ita ta bud'e k'yare tare da jillota da k'arfi bakinta ya gwaro da bango Asume ta xube k'asa.

Hakan yai dai-dai da lokacin da ya doso hanyar.me idonsa ke gane masa?
Abinda bai tav'a tunani ba da shi yai tozali.
Hango wata ballagazar k'auye yai bakikkirin tasha d'aurin gaba da zanin kamar mai tuyar k'uli tsaye take sai surfa ruwan ashar take abin bako kyan gani.

D'ago Shatu yai yaji sam bata numfashi.
Mayar da dubansa yai ixuwa ga Innah Hansai yace ." Ki sani 🔫 🚶 hukumace zata yi maganinki "Me tayi miki?zalunci ko?
Jin zancen 'yan sanda yasa Innah Hansai aza hannu aka ta soma k'wantsama makoki.
Gaba d'aya yaranta suka fito.
👯
Jimmala tace.Innah kinga abinda nake jiye miki nan gashi da tsufanki za'a gark'ame ki tunda da alama d'an sanda ne.
Sautin kukan Innah Hansai ya kuma fitowa.
Bakinta na kef.kef tace." Jimmala "Don Allah ki saka baki kadda a kamani don Allah?
Mal.Bello yace." Jummala d'auko kayanta mu tafi asssbiti.

Cikin motar Hafiz a ka saka ta suka nufo charanchi (lafiya tafi kud'i )sunan Assibitin.
Hafiz ya zuba mata ido tausayin ta fal ransa ashe kalar azabar da take fuskanta kenan wajen matar babanta.
Kud'in komai shi ya biya.
Mal.Bello Godiya kawai da saka albarka yake wa Hafiz.

*****
Wajen k'arfe biyar ta farka.
Jimmala tace.
"Shatu sannu?
" Ya jikin?
Mal Bello da Hafiz suka matso suna tambayar ta "Ina ke miki ciwo?
Shiru tayi idonta d'auke da hawaye tana tambayar kanta " Inane nan?
Wa kuma ya kawota?
Hafiz yace bara na fita na samo miki abinda zaki ci kinji?
Fitar sa ba jimawa Jimmala ta dubeta.
"A gaskiya Shatu mutumumin nan yana da kirki sosai. Duk wannan hidimar fa shi yayi ta.
Shatu tace." Tun a k'auye yake hidima dani......Amma Jimmala nan d'akin waye?

"Ke ba d'aki bane Assibiti ce ta masu kud'i.
Ji wani ruwa mai zak'i Shatu d'an Sha kiji.
Ta bud'e murfin lemon ta kafa kai.
" Kai jimmala Ashe akwai ruwa me zaki haka?..
Kila irin na 'yan makkane.Uhum da gani dai na 'yan gayu ne.

Kwananta d'aya a ka bata sallama.
Kwanan 2 ya d'an shak'u da ita matuk'a ya fahinci komai ita d'in yarinya ce me hak'uri.

Matuk'ar tsorata Innah Hansai ta tsorata da lamarin Shatu yarinyar ta zame mata ciwon ido me wuyar magani.


KATSINAN DIKKO.
Zaune suke suna( break fast)
Alh.Kabir ya dubeta "Yar gata?"
Ta tsare shi da ido tare da murmushi.
"Kinga zab'e nata tunkarowa ko?
Mak'iya sun taso mu gaba." Don Allah ki kula da kanki kar ki ja min abin yad'awa kinji?

Dar! Dar!
Gabanta ya yanke ya fad'i.to yanxu idan Dad
d'inta yaji tsakaninta da Josphen "Me zata ce mishi?"
Daddy sai dai fa kayi hak'uri nayi nisa akan son Josphen bazan iya rabuwa dashi ba Daddy.

Misalin K'arfe takwas na dare suna Viodio call.
A nan yake k'ara sanar mata irin d'inbin son da yake mata.
Tace.Daddy yasa min matakan tsaro kasan zab'e ya matso "Ni kuma da na rasa ka gara shi ya rasa takarar My Josphen.
Yace." Goaldyn girl kenan Ni kuma ina nan ina fama da matsalar grass ita a dole ni take so. Ayau Mom d'inta tazo da kuka wai sai na auri grass kinsan Sister d'in .
Mommy nace .
Kin san me?
"Aa sai ka fad'a Idan kin taso daga school tomorrow za 'a saka mana zoben bai ko da ranar ta zagayo a d'aura aure mu dage k'@sar da ba mai iya gane mu.
Tsalle tayi tare da cewa kace gobe i

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment