Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

war haka mun zama 'yan promise.
" Yesss!
Tsalle tayi tare da buga k'afa tana mai farin ciki.


*************Washe gari ta yi shirin tafiya School.
Ta kuma gargad'i direva kar yazo d'aukar ta sai shidda tayi sabo da tana da lakca.
Yana ajiye ta ta kira number Josphen bai dire ta ako ina ba sai k'ofar gidan da Mommynsa ta tanada a domin shagalin baikon su..

Abokan Madan Gloria ne Amintattu kowacce ta ci gayu cikin koren Ashobi sun sha attachemen mai kalar black and coffee
Dogayin rigunan kowacce iya gwaiwa sunsha air line gazar -gazar.
Ga fararin kujerun roba.
Bangare daya kuwa naui'in abinciccika ne dangin Amala kuskus algaragi sinasir kai da dai sauransu.
Kujerun da aka ware don Ango da amarya k'ayatattu ne shigar ta ita da josphen kala d'aya suka yi rungume yake da ita haka suka doso wajen tayi kyau matuqa. isowar su wajen aka hau tafi tare da yin wani irin yare da bansan me suke cewa ba๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž
Cimak wata daga cikin su ta d'auketa aka yi ciki da ita.wanka aka yi mata tare da saka mata wasu kaya riga da zane mai ruwan qoal.rigar daga sama ayayin da zanin ya fito saman rigar sai sark'ar duwatsu da 'yan kunne dogaye.

Bangare daya kuwa grass ce da mamanta cikin bakin ciki na ganin yadda Madan Gloria ta wulaqanta su ta fifita bare akansu.
Koda aka fito da Meenat Josphen ne saman kyayatacciyar kujera yayi kyau matuk'a An lilliqa balam- balam. โš– โš–
Gefe d'aya kuwa ga abin bautar su nan
Bayan sun gama bautar aka zo wajen cashewa.
๐Ÿฅ ๐Ÿฅ cake ya yanko ya saka mata a baki aka hau tafi ita ma ta yanko ta saka mishi wajen ya hautsine da tafi.
Wani zobe Madan gloria ta mik'o wa babbar k'awarta ta ba Josphen ya saka mata ita ma ta saka mishi nata wayyo kar kaso kaga.
Kammala saka Zoben keda wuya ya jawota ya rungume cikin kunne ta rad'a mishi.
"Na fa ce maka Addinimu yai hani da Aikata hakan My Josphen.
Yace " So kike K'awayen Mom suyi miki kallon logal giril? A fa jami'a ki ke ba pramary ba.


Ku ci gaba da kasance wa dani domin jin jumurd'ar da ke cikin wannan kayataccen labari kar ku manta Meenat na fa chan zata yi aure da Josphen kirista batare da sanin iyayenta ba.

*SO KO HAUKA?*

Daga marubuciyar (Ishara)
Ayshatour.
Abdul-falalu.

Mommyn Yusif.


*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ


๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’–
SO KO HAUKA?
(Labarin Meenat ฦดar gata da Shatun ฦ™auye)
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’–
By Ayshatour Abdul-falalu
(Mommy'n Yusif)

*_From the writer of ISHARA_*

๐Ÿ“„ page 36-40.

Josphen yace "Ai kin dai kusa zama mallakina ko?
To ai sai ka jirayi lokaci"
K'awar Mommy Mrs. Bikola ta zo ta ruqo Meenat aka shiga filin rawa.
Cikin K'awayen Mommy har da masu liqa Dollars.
Daga bisani Mommy ta shiga ita ma aka fara da ita. Grass da Mamanta an yi an yi dasu su shiga amma sun nuna tsantsar Hassadar su a fili.
Babbar k'awa ga Mommy Madan Elena kyautar mota sabuwa dal ta baiwa Meenat a yayin da Mommyn ta bada kyautar sarqar goal wacce zata kai kimanin milyan goma.

Grace ta ida fashewa da kuka Mommynta ta jawota tana rarrashi tace muddin tana raye babu wanda ya isa ya d'aura auren.
A madadin kanwar mahaifiya Mommyn Josphen ita ta bayar da kyautar k'anwar Mahaifiya.
Bak'in ciki ya dad'a cika Mommyn Grass.

Wajen k'arfe hudu kowa ya watse daga Mommy sai Josphen sai kuma Meenat.
Mommy ta kira sunayen su baki d'aya.
"A rayuwata ba abinda nake so irin naga na faranta ran My son Josphen don haka nake sanar muku rana irin ta yau kamar yanxu kun zama mallakin juna.
Don haka duk irin hukuncin da General Eberi zai d'auka a shirye nake tsaf domin bana jin dad'i komai irin inga na faranta ran My son ta fad'a had'e da shafa kansa.
Sai dai kuwa matsala d'aya " Meenat kece abin ji shin kina ganin babu takura a auren ku da Josphen?

Meenat ta girgiza kai.
"Mommy kar ki damu dani kamar yadda ki kai Amanna akan duk hukuncin da Daddy zai d'auka to nima ina tare dake na shiryawa bin Masoyi na Josphen duk inda ๐ŸŽญ Masoyi na zashi ina tare dashi zamu bar k'asar ke kad'ai zaki san addres d'in inda zamu Don haka ina fatan nan da rana ita yau da gaske ne za'a d'aura mana aure da Josphen?
Murmushi tayi tare da shafa kanta.
"To kyautittikan ki fa?"
"Am wannan ki ajiye a wajenki bana buk'atar komai sai josphen, Domin kuwa a bankunan nigeria kaf ban san iya adadin kud'ad'en da na mallaka ba.



*K'AUYE.*
Yammacin ranar Hafiz yai sallama a domin ganawa da Mal.Bello.
Hafeez ya soma da fad'ar " Sunana Hafiz isma 'il sale jika a wajen mai gari.
Mal.Bello ya fad'ad'@ fara'arsa yace kana nufin Marigayi Alh.isma'il.
"Eh nine babban d'ansa.
" ko da naji Mal.Bello ya fad'a.
"Ai Mahaifinka mutumin kirki ne a garin nan kowa ya san sa.

Dad'i Hafiz yaji na yadda duk wanda ya bud'i baki yabon Daddynsa yake.
Babah Alfarmar da nake nema ina son zan dinga koyawa Aishatu karatu kafin na tashi tafiya!
Mal.Bello bai yi gardama ba ya Amince domin yabawa da hankalin Hafeez da yayi.

A ranar Hafiz ya shiga garin Charanchi ya siyo mata kayan sawa tare da umartar ta da ta zubar da tsummokaran.
Cikin kwana 2 kar kaso kaga yadda rayuwar Shatu ta koma ta koma baturiya ashe Shatun kyakkwace sai yaga basu da ban-banci da Meenat.Illah rawar kai kurum da Meenat tafi ta.
Asabe da Abu Sun saka Innah Hansai a gaba suna kuka." Innah Hansai tace ku sha kurumin ku duk wannan rawar kan badon komai yake yinta ba Illah don ya yaudareta ya d'irqa mata ciki ku zuba ido kuyi kallo.

***********Shatu nada fahinta sosai cikin satinnan biyu da yai yana koya mata ta soma iya wasu abubuwan da dama.
Daga Shatu har Hafix shaquwar su ta kai idan d'aya bai ga d'aya ba zai shiga damuwa.
Ga wani irin mugun kyau da tayi sosai.
I yanxu ya tabbatar da cewa ya kamu da son Shatu dumu dumu.Meenat kuwa ta fice a ransa sam to meye ma banbancin Shatun da Meenat d'in banbanci dai daya ne *Birni *KAUYE.*
Musamman idan ya tuna irin wulaqncin da meenat tayi masa a kan wani banxan kirista.
Gashi ya sauya mata *Ak'ida*

******Da sanyin safiya Shatu ta had'a tea suna karyawa ita da Jimmala Ayayin da ta zubawa Mal.Bello.Innah Hansai a gefe sai zafaga Habaici take wai an ga inda tusa zata kure wa buddari yarinya tayo lalata yazo an bashi yana sha
(**domin a yanxu hafiz yai mata baraza na muddin ta kuma cutar da shatu to a binni zai kaita ai mata hukunci shiya sa sai dai ta yada habaici**)
In ba ta girka basa ci sai dai taci ita da jimmala a yayin da ake cewa jimmala mak'wadaiciya.
Abu ce ta fito da gudu jin k'arnin kwai.
Ta na kelaya amai.yi take ba k'ak'k'autawa Innah Hansai tace."Abuy Ko jante (zazzab'e) kike?
Abuy ta girgiza kai dak'yar tana nishi.
"Aa Innah haka nan naji zuciyata ta hautsina.
(*abinka da k'uruciya*)
Innah Hansai ta zubawa Abuy ido ta k'are mata kallon tsaf.
Kawai gani mu kayi ta a za hannu aka tana kururuwa.
Ta zage iya k'arfinta tana kirb'ar Abuy.
" Ni zaki tonawa Asiri?
"Uban waye yai miki ciki?
" Ciki kuma duk muka waro ido ni da su Jimmala.
Innah Hansai ta ci gaba da kirb'ar Abu.Mal.Bello sai da ya kammala karin kumallonsa tsaf kana yazo ceto.
Ya dube ta yace."Shi yasa a kullum ake son ka kyautatawa d'an uwanka musulmi zato gashi fatar da kike akan Shatu ya juye wa 'yarki.

"Kenan farin ciki kake tsintacciyya tafi 'yarka.
Tunda ana baka ruwan bunu da burodi.
"Hansai kenan ke kanki shaida ne kan ni ba mak'wadaici bane abin wani bai dame ni ba.
" Wallhi wannan Abun sakayyar shatu ne idan da rabon ya zame wa masu irin halinki *ISHARA*

Abu fa ya game k'auye kowa yana cewa Alhaqin Shatu ne.
Har waqa aka yi dandali.

(*Wata mata tayi abin kunya.*
*Wata 'Yama tayi abin kunya*
*Sun so sharri ga wata baiwar Allah*
*Sharrin ya bisu har tsakar d'aki*)



**********
Ni kan Shatu a yanxu na samu yanci ga dai tallah na dai nayi .
A yanxu soyayyar tsantsa muke zubawa ni da Hafiz.
Mal.Bello ya dubi Hafiz tare da cewa,
"Hafiz baka tafi bane?"
"Eh Babah na jinkirta tafiyar saboda wasu dalilai ina so zamu tattauna wata magana da kai.
"Ina jinka Hafixx.
"Yawwa dama idan ba damuwa Baba na yaba da tarbiyyar Aishatu ina so zan Aureta.

Daram!dam!
Gaban Mal.Bello ya yanke ya fad'e.
Shikenan sirrin Aishatu ya kusa tonuwa shikenan da yaji wannan sirrin bashi ba sake zama da Shatu.........." Lafiya Babah.
"Meke faruwa ne koko nid'in ban chanchanta da zama mijin Aishatu ba?.

M.Bello yai ajiyar zuciya kana yace.
" Ba haka bane.

"Illah kai d'in dai ne nake gudun samun matsala daga gareka.
Saboda a kwai wani babban sirr ne damu
da Shatu wanda ba kowa yasan dashi ba.
" Wanne sirrine wannan Babah?"

"Uhum Hafiz na yarda da nagartar ka da dattakonka shi yasa zan sanar ma wacce ce Shatu.
Amma don Allah nasan idan na sanar maka zaka guje wa Aurenta to alfatma d'aya zan nema a wajenka ita cr don Allah kadda ka yanke zumunci damu๐Ÿ‘‹๐Ÿ‘‹๐Ÿ‘‹

" Ina jinka baba"
"Malan Hafiz Shatu ba 'yar ciki na bace.
" *What*?
"To 'Yar d'an uwanka ce?"
A, a Tsintar ta nayi tun tana jinjira.
"Innalillahi wai'inna ilaihirraji'una.
Kuma ma abin tausayi akwai takardar da akayi rubutu cikin kayanta inada aka saka.
(*Cikin shege nayi na haifeta*)
Hafiz ya share k'wallar fuskarsa kana yace.
" Tabbas Aishatu abin tausayi ce Baba a "zatonka wannan ne zai sa na guji Aisahtu?
"Ina wannan ma shi ya k'ara min karsashe na k'ara yin Amanna da zama mijin Aishatu Insha Allah.
" Gobe na ke so zan tafi yanxu zanje na sanarwa mai gari abinda ke wakana.
"Shikenan yanxu bara na turo maka da Shatun.

Zaune take tana rubutu M.Bello yace " kije zakuyi sallama da Hafiz.
Inna Hansai tai wuff! Ta amshe.
"Andai ji kunya Namiji da suna Hajara.
Hijab d'in ta ta jawo a goge tasaka.

Jingine jikin mota ta tarar dashi tayi mishi sallama tare da gayar dashi.
Aishatu na zo nayi miki sallama a Gobe zan tafi na zo na sanar miki wani babvan sak'o wanda zai girgizaki.
Kallonsa tayi tai jim kafin tace, " Ina jinka Uncle wanne sak'o ne ?insha Allah zan masa kyakkyawan fahinta.

Murmushi yayi tare da cewa.
*Aishatu zaki iya aurena ina sonki so ba na wasa ba*

Runtse ido tayi tare da cizon yatsanta amma koda ta bud'e Hafix ta gani tsaye.a gabanta da gudu ta bar k'ofar gidan fuska a rufe Hafiz ya girgiza kai yana murmushi tare da cewa *Aishatu kunya adon 'ya mace*

Koma wa tayi gida a gaggauce ta rubuta mishi takarda.
*A gaskiya uncle hafiz bani da bakin godiya* a gareka duk wani 'yanci na rayiwa a* wajenka na sameshi wacce mace ce zata* tozali da kai tak'i ka?*
Sai dai kai kuma anya matsayin da ka bani* na kai nan?a gani na ban chanchanta da* zamowa mallakin ka ba na ganin ajina da* naka ba d'aya yake ba ina son ka uncle Hafiz* so marar misaltuwa*

Saman dakali k'ofar gidan ta ajiye tare da tsillawa da gudu.
Hafiz yai wa Allah godiya domin kuwa zuwansa k'ereriya ya zame masa silar warakar sa daga cutar son *Meenat 'yar gata*
Wacce tafi tasa nutsuwa kamun kai ayanxu ko yaya rayuwar Meenat da Josphen?

***Washe gari ya shurya da nufin tafiya wani iriin bak'in ciki ya ziyarci Shatu sai take jin kamar an d'auke mata duk wani farin ciki fa wal-walar ta.
Shi ya dinga rarrashinta duk da shima din d'auriya ce kawai.
Allah sarki sabo tirken wawa kuka riris Shatu ta saki lokacin da Hafiz ke d'aga mata hannu yana mata bai bai.

A haka har ya juya ya tafi.


***********
"Innah na'am.

" Na'am.
"Yanzu kina kallo ace Shatu tafi mu komai?"
"Tayi fari kamar baturiya mu kuma kullum jiya i yau.
" ni wallhi Inna abinda nake gudu karfa d'an birninnan yace ita yake so kinga yadda ta koma 'yar birnin ita
"Banda abinki taya zai auri wata Shatu *Shegiya* wacce akai cikin *Shege*aka haifa?
" Yo ko yace yana san ta yaji labarin tsintar ta akai tuni zai fece.
"Ni fa sonsa nake Innah"
Don wannan kar ki damu ki bar komai a wajena zan ziyarci Boka mai ta tsine.
"Meke bazan iya yi miki ba Asabe ta tunda kin fi shasha me yawon ta zubar.

Abu tai karaf tace " Naji ai dai kice Ummul-aba i'sin lalacewar tarbiyyata.
Kin manta sadda nake kawo miki kifi da tsire kina cinyewa?
"Don ubank don nace ki kawo min tsiri sai nace kiyo cikin shege.

Abuy tace wallhi duk alhakin Shatu ne ki bibiyarki amma hat yau baki sadudaba kina ce mata Shegiya to gashi kema a d'akinki sai ki dafa ki sha.
" Rufe min baki kafurar banxa.
Asabe tai ta guna-gunai Innah Hansai ta k'wafd'e mata baki sai ga jini Bull! abinka da bakin da bai saba da ganin burush ba.
Mal. Bello ya shigo ya dubeta, "Hansai ina san magana dake"
Ta auna mishi harara tana fad'ar
"In ce ba wata manaqisar aka qullaminba?Shatu dai ce na fita safgar ta to sai me? " Kai kuma sahorahi an ga malasa an liqe "Wai gyartai ya sami sarauta yace banda tuna baya.
" Kinga Hansai ba wannnan ya kawo ni ba dama ince Shatu ce ta sami mijin aure.
"Au Mato d'in na gidan Delu mai gwanjo ta sami dai dai ita dama ance jiya ya dawo daga folish (๐Ÿ‘ฎ Folice station) ai dama tsohon k'wartonta ne domin tuni ya gama lalubeta..........Katseta yai.
" Hansai kenan me kuma Shatu zatayi da wani Mato wanda ko ada bata aureshi ba bare yanxu da ta zama 'yantacciya.
Yaron nan dai jikan gidan mai gari wato Hafixu yaron arziqi shike santa da Aure.

"Aume?
" Aure!
Kukan da Asabe ta aza hannu aka ta soma rerawa game da sabvatu "Shikenan Baba dama baya sammu ya fi san Shatu gashi ya zab'ar mata d'an birni mu ya barmu k'auye.

Innah Hansai ta dubeshi.
" Kace Mutuwa kazo sanar min?
"yanzu kai Mal.fisabillahi ga baka 'ya'yan sai ka d'auki tsintacciya ka bashi?
" kinsan tarbiyya ita ce mutum tarbiyyar ta ya yaba shiya sa.

To naga ubanda ya isa ya d'aura auren ko dai ya nemi Asbae ko a fasa duka , ko zanyi yawo tsirara sai naga an fasa aurennan.

******Afujajan Innah Hansai ta jawo tsumman gyalenta wanda in banda k'arnin d'auda ba abinda yake yi. Tayi waje.
Lungu da sak'on gidajen 'yan bori tai ta zarya.
Boka mai gaba d'aya ya tabvatar mata tunda yaron nan ya tafi ya tafi kenan ba zai kuma dawowa ba.
Bunsurunta da shikenan ya rage mata ta jawo ta d'amqa masa.



Mommyn Yusif.


*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ


๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’–
SO KO HAUKA?
(Labarin Meenat ฦดar gata da Shatun ฦ™auye)
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’–
By Ayshatour Abdul-falalu
(Mommy'n Yusif)

*_From the writer of ISHARA_*



๐Ÿ“„ page.41-45.

Isar Hafiz gida ba tare da b'ata lokaci ba ya ke sanar wa da Maman sa ya samu matar Aure. a k'auyen su Daddynsa.kuma abin mamaki mai kama da Meenat sak!
Haj.Usaina tayi murmushi tace, Hafiz kenan "Meenat ta zauta ka har ka fara ganin me kama da ita kenan?
Jawo wayarsa yai ya nuna mata poton " Kai Hafiz wannnan ai Meenat ce "Meke damunka? Kar fa Soyayyar " Meenat ta zauta ka.
"Uhum Mama kenan bake ba Ina zaton ko Alh.Kabir d'an takatar deputy Governor yaga Shatu bazai tab'a cewa ba 'yarsa Meenat bace ni na rasa irin wannnan kama.Mama inda zan tabbatar miki da cewa ba Meenat bace kinsan dai Meenat bata tab'@ zuwa K'auye ba ko duba runbun nan ki gani kuma meenat bata sa ka kaya irn wai'innan ki yarda da hankali na mama.
Haj.Usaina tayi shiru daga bisani tace." Allah ya sa Alkhari.
Hafiz yace gashi tafiyar gaggawa ta kama ni zuwa k'asar germany.
Dole ne na ziyarta Haj.Usaina tace kadda kayi gaggawa Allah keda komai.
Hafiz ya gwad'a kai.



*K'AUYE*
Wata 2 ciff! Ba labarin Hafiz Innah Hansai sai yada Habaici take.
Shatu da Mal.Bello sun shiga damuwa matuqa.
Sai a yanxu Shatu ke nadamar fad'awa TARKON SON! 'Dan birni me kud'e mema zaiyi da 'yar k'auye irinta?
Tabbas Hafiz ya yaudareta
Duk wasu kayan dad'e da ya siya mata sun k'are duk da Innah Hansai ke bin dare ta sace ta kad'ar wajen bin bokaye.
Ta ba zaune ta zabga tagumi Asbe sai yada Habaici take "Dan birni yazo yayi yaudara ya lalubeta a banxa kila ma ya d'irqa mata ciki.
Ita dai tasan Hafiz mutumin kirkine domin ko yatsar ta bai tab'a riqewa ba..........sallamar da akayi ce ta dakatar dasu.
Wasu mata ne Hajiyoyi wayayyun 'yan boko sukayi sallama su biyar. innah Hansai tace, " Kunyi batan kai ince gidan mai gari kuke nema ko?
"Aa banan bane gidan Mal.Bello?
Malan Bello da ya fito daga bayi yai saurin fad'ar " Nan ne.
"To Masu neman Auren Shatu ne.
Munzo da lefe da sadaki domin kuwa sati 2muke so a saka a shirye muke.

Mal.Bello ya fad'ad'a fara'arsa tare da cewa " "Sannunku "Sannuku.
Kan kace me?
Mata sun cika gidan.
Rahane ta rangwad'@ bud'a."Ayyiriri Shatu ki n dangwalo, Allah ya sa mu a damshinki.

A kwati set biyu kowa a k'auyen mamaki yake akwati 24 ko yaran mai gari dai uku ake kawo musu.

Innah Hansai kasa cewa uffan tayi Wato Boka yaudarar ta yai kenan.
Dubu d'ari biyar sadaki d'ari biyar kud'in neman aure sai key din mota da kujerun makka 2 Shatu da Babanta.
Daga tsaye cikin Innah Hansai ya bada k'uuuuuuuu!
Da gudu ta Arta bayi amma kafin ta dafa gora tune sarkin rashin haquri ya wanke zaninta tass.
Allah yasa ba wanda ya lura da ita.
Fitowarta bayi keda wuya.
"Yanzu ina gida Shatu zata makka?
Da gudu ta k'araso bainar jama'a tana kuka tana cewa, " Shegiya face.Tsintar ta yayi bata da asali.ku zo ku zab'a cikin 'ya'yana kyauta zan baku.

Mal.Bello yace kar su damu bata da hankali.
Gaba d'aya ba wanda ya kulata.

Shatu kuwa wacce zuwan farko ta gudu ta b'oye.
Matan sun buqaci da san ganinta.dakyar aka nemota, tabvas sun yaba da kyawonta da tarbiyyarta
Sai dai duk wNda yai mata kallo d'aya sai yace Meenat to me zai kawo Meenat anan.

Sunce ana saura sati zasu zo tafiya da ita a domin gyaran jiki.


******Tsakar dare Mal.Bello ya mayar da kansa gabas yana sallah kamar yadda ya saba.
Sadaq! Sadaq! Innah Hansai ta lallab'a ta watsa kalanxir a d'aqin tare da kyasta ashana.
Sallame warsa kenan yaga haske ya yawai ta a d'akin da sauri ya qaraso izuwa wajen sai me?ganin wuta wanda da alama gobara ce yasa sa neman taimako tare da furta kalmar Innalllahi wai'innah ilahirraji'una.

A hankali jama'ar k'auye su ka yi cincirendo.
Wanda hakan ya faranta ran Innah Hansai ta shige d'aki tana ta faman k'yak'yatar dariyar mugunta shi kenan kayan Auren Shatu da a ke musu kan-kan ba yau dai taga bayan su.



*KATSINAN DIKKO*

Hannunta sargafe da na Josphen. ๐Ÿฆ icecream ce take d'iba tana basa a baki.
A yayin da shima yake bata tasa.
Hafiz ya k'araso dai dai wajen don ta bashi haushi sai ta dad'a k'aime wajen rungumar Josphen.
Ga mamakinta murmushi ta gani d'auke a fuskar Hafiz.
K'araso wa yai izuwa gareta.
"Meenat kenan, " Duk abinda zaki yi wa 'Katon Arne ba damuwata ba ne domin kuwa , ki sani na samu matar aure wacce ta fiki nutsuwa da tarbiyya. wacce bata wulaqanta kanta ba wajen rungumar arne.
Cimak ta miqe da nufin bal-bala mishi musifa.
Invitation d'in d'aurin Aurensa ya cilla mata tare da bin titi da k'arfi ya cillah motar.
Abinda ta gani yayi matuqar razanata.

*The family of**Late Alh.Ismai'il( K'ereriya)*
*And Thet of*
*Mal Bello (Kerereya*
*Cordely invite*to*The wedding fatiha*
*Of the son &together*................

Hafiz Ismai'il

&
Aishatu Bello.

Duk iya hasashenta ta kasa gano wacce ce Aishatun nan.
Jawota Josphen yai.
" Golden giril "What happen?
" Uhum wannan guy fa wai yazo ne yana sanar min aurensa.
Gaskiya bana san ya rigamu aure
"Kar ki damu My GoIdeyn.



*******
" Meenat naga kina cikin nishad'i "Meke faruwa?
Cikin ranta kuwa cewa tayi.

*Mommy sai dai fa kuyi hak'uri dole na bi masoyina duk inda za shi*

" Fine Mum.
'Ni zan shiga na kwanta kai na ne yake d'an sara min.
"Ok baki da matsala.



Meenat ta miqe tare da had'a duk wasu gwala-gwalai nata masu mihimmanci.
Shigar Mommy bedroom ya ba Meenat damar miqewa ta bi ta k'ofar baya K'ofa ce da ba kowa ya san da ita ba daga ita sai Daddyn ta sai Mommynta anyi ta ne sabo da fataken dare .bata buk'atar komai a haka ta tafi ta bar gidan bata re da kowa ya ganta ba Napep ta tara sai unguwar su Josphene.

Isarta gidan. kamar daren (Kirsimate)
Haka ta tarar da gidan. A na ta aiki ka'in da nai'in. aikin dare biki.
Domin da an d'aura aure a ke son tafiyar ta su ta kasance saboda k'aurace ma fushin General Eberi. Zuwa kasar America domin har an riga da anyi musu buking d'in jirgi.

Ta na isa cimak aka d'auketa zuwa wani katafaren d'aki.

Daga Mommy sai Josphene.
Mommy tace, ta na duban Meeneer.
Listes to me carefully.Gashi lokacin Aurenku da Josphene yayi.
Na sadaukar da farin ciki na gare ku ba gudu ba ja da baya.

Mum ta ju yo ta na duban Josphen kana ta ce, My son I wont you know Meerneer will be your wife *Meeneer ta zama matar ka*)

I will get you marrigeid before the eyes of Eberi willy nilly *Ko Ebiri yana so ko ba ya so a i donsa yana kallo za'a d'aura auren.*)

I will shew him my power and mightness that he is jus A dog before my feel

*zan nuna mishi k'arfin iko na zan tabbatar mishi cewa wallahi nafi shi*)

Meerner cikin matuqar farin ciki tace." By God, I am ready to sacrifice any thing for he r seke muddin akan soyayyar Josphen.
Tafi su kayi daga Mommy, har Josphen d'in.
Kana Mommy ta ruqo hannun Meerneet domin tafiya a yi mata gyaran jiki.

Da farko gyaran gashi aka fara mata sannan akayi mata wankin qafa.sannan aka jera mata Flour me kyau hannu da qafa na jan lallai.
Sannan aka zuba mata kitson Attach. Me kala uku kana aka bishi da k'arfuna.
Sannan aka yi mata dilka har wayewar gari Misalin k'arfe 8:0am.pestor da zai d'aura aure ya k'araso.

Domin kuwa Secret Marrgeid ne duk wasu mata kai da ake bi a auren Kirista dole ne a dakatar da su sabo da ba'a san ko wa ya san a na wani biki.
Ko da kuwa Whate Weddy ne ba zai yuwu a gabatar ba sabo da Mussamman ita Meerner ko d'an 'Yan jaridu masu son jin k'waf da irin su Mommy's Yusif๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ.




Meenat tayi kyau sosai kai kace Sarauniya ce duk da ba shigar hausawa tayi ba.


Grace tace.Mama har yanzu ba ga kin d'au matakin komai ba ga shi har aure ya kusa kammaluwa.

Murmushi tayi.tare da shafa kan Grace.
"My Baby, This meeting has come to an end as far as I am concerned.
Don haka baki san waye Eberi ba. I know what to tell him. And I know what to do.
Grace tace.Thank you Ma!.

*****Maman Grace ta danna number General Eberi Cikin kuka tace."Yanxu har 'Yar musulmai tafi yata? "Kamar yaya, "Wacce irin magana ce haka, "But why do you sey that? "Uhum!
Mr.Eberi You do not understand.

Yarinyar da tace tazo shiga addinimu to k'arya take yi Budurwar Josphen ce. A halin yanxu ma an d'aura musu aure.bud'e Datar ka na turo maka vidoin bikin. Kuma ita ma yarinyar ko mahaifanta basu sani ba.
Wata irin razananniyar k'ara ya saki da k'arfi.
Wanda har kunnuwan Maman Grace suka dumm! Na d'an lokaci.

Wajen buki kuwa an fasa kwalaben barasa ana ta zagaye.Zoben da aka ba shi ya saka mata yafi na promise kyau da tsada.
Bangare d'aya kuwa Grace da mamanta keta tiqar rawa suna dariyar k'eta wanda sun ba kowa mamaki.

Daurin Aure ya kammalu.
Gefe guda kuwa me photuna ne keta haska su.
Duk photon da za'ayi rungume suke da juna ita da Josphen. Cikin tsananin farin ciki.
Me kid'a ya daddage yana ta d'aga sauti ganin dalar America da Mommy keta liqawa.
Meenat taji ina ma Hafiz
Zai zo ya ganta da abin k'aunarta Josphen.
Lallai da idonsa ya tsiyaye tsabar bak'in ciki. Da kishi.

Darammm! Suka ji an saki harsashi a jikin bango.
Gabjejen 'Kato baqi Wuluq!
Rik'e da zabgegiyar bindigarsa.
Daram! Ya daki deburin da ke girgirke da giya.
Kowa sai da ya firgita harda Meenat.amma abin mamaki banda Josphen da Madan Gloria.
Gaban Josphene ya matso ya dinga sharara masa maruka.
Madan Gloria tace "Me zan gani.......
Cikin tsawa me qarfi yace.
"You keep quiet.

I well not allow musulum.

Madan Gloria tace."Tun yaushe?
Bayan aure ya riga da ya kammalu.


Ganin haka ya ba duk matan dake wajen sararin darewa.suka gudu.
Maman Grace taja yarta tace tazo su bar garin.
Cikin murd'd'd'iyar murya ya soma magana.
"Gloria Ashe ke " Muna fukace?
"Maqaryaciya Kin " Cuceni da kika had'a min zuri'a da 'Diyan Musulmai.
"kin sani cewa babu abinda na tsana sama da musulmai shine

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment