Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels

*WAKE ƊAYA💍*

MomIslam



🆓Page1



Ɗanɗano





A gigice ta durƙusa a gaban, Inna Meramu. tana cewa "dan Allah Inna kiyi haƙuri ki taimakamin karki jefani cikin wannan ruwan wlhi zan iya mutuwa"

Hawaye nabin kumatunta kamar an buɗe famfo.



Cikin rashin tausayi da sanin darajar ran ɗan adam, Inna Meramu ta dagata sama ta waiga taga babu mai kallonta ta wurga Hanan cikin tafkeken kogi.



Inna meramu ta juya a guje tana darara ihun neman agaji, tana isowa ƙofar gida ta zube a gaban malam Junaidu tace "rabona da ganin Hanan tun safe nayi yawo har nagaji, yanzu nan daka ganni daga Kadage nake"

Malam Junaidu ya miƙe tsaye tare da rafka salati yace "nima zama bai ganni ba dole ina shiga gari nemanta"

Sai kuma ya tsaya ya kalli Inna meramu yace "ammafa sai naji kamar Halliru mai shago yace "yaganta da tiran tallar shinkafa?"



Inna meramu ta fara ƙirƙiro kalaman kare kanta kafin tace "uhm malam me kake nufi?"

Bai tsaya jin abinda zatace ba ya bazama gari neman Hanan.



Kowa yagani a hanya sai ya tambayesa yaga Hanan, suce basu ganta ba.



Yayi tafiyar datakai ta d'ari biyar amma bai ko ga d'ankwalin Hanan ɗin ba, zama yayi gindin wata bishiya ya yakice zufar data karyo masa kafin yace "ina yarinyar nan ta shiga?, a iya sanina bata saba yin nisa da gida ba, Allah ka nunamin ta inda zan ganta"



Ya miƙe yaci gaba da tafiya a gajiye.

Yamma liss ya dawo gida ya samu Inna meramu tana alwalar magriba, shima butar ya ɗauka tare da nufar bayi, yana shiga aka kwashe shi aka watsar gefe kamar kayan wanki, ya rafka salati yana cewa "nashiga uku meramu kinajin halin da nake ciki?"

Tana daga bakin murhu tayo kansa da gudu har tana kujewa a jikin bango tace "malam koda ka taka musu ƴaƴan ne?"

Ta fita waje da gudu tana ihun neman agaji,

Cikin sa'a Halliru mai shago ya jiyo kururuwarta ya taho da gudu yana cewa "Inna meramu meke faruwa?"

Tasa hannu akai ta rusa ihu tace "malam ne ya faɗi a banɗaki ka taimaka ka fito dashi"

Halliru ya shiga gidan da sallama ya shiga banɗaki yaga malam a yashe sai wani irin numfarfashi yake,

Cikin azama ya fito dashi, Inna meramu ta shimfiɗa tabarma ta fara yi masa fifita,

"Akira malam mai karatu?"

Halliru ya faɗa yana kallon Inna meramu,

"A'a barshi muga abinda Allah zeyi dan wlhi sisi bana magani bare ince ka kira shi"

Halliru yace "inhar befi ƙarfina ba zan taimaka"

Inna meramu tace "to tunda ka kafe kamar ƙanin ubanka"

Halliru baice mata komai ba ya fice yana jajanta rashin mutunci na matarnan,

Cikin natsuwa ya isa gurin malam mai karatu yace "malam Junaidu ne ya faɗi a banɗaki shine nazo dan Allah ka taimaka masa"

Jinjina kai malam mai karatu yayi kafin yace "bana son shiga gidan nan saboda niƙanmu baya laushi da Meramu"

Halliru ya haɗe hannayensa biyu kamar zeyi kuka yace "dan Allah kai taimaka masa malam ka duba halin da yake ciki"

Malam mai karatu yace " to Allah yasa mu dace, muje yanzu na dawo daga sallahar magriba zan shiga gida"

Suna shigowa suka samu tanata adu'a tana tofa masa, malam mai karatu yace "kull karki sake ta6ashi bare tofa masa gubar bakinki"

Cikin rashin fahimta da dama ba shiri take yi dashi ɗin ba tace "ban gane ba?, ko dole sai kaine idan kayi masa magani zai warke babu wanda Allah yaba sa ni?"

Malam ya girgiza kai tare da fara karantowa malam Junaidu karatun Alkur'ani mai girma, yana yi yana tofa masa, tashi ɗaya ya fara ɗaga hannu amma babu bakin magana,zatayi magana malam mai karatu ya dakatar da ita cikin fushi yace "idan na kaiki Shari'a wlhi bazamu dawo tare ba acan zan barki?"

Inna meramu ta miƙe tsaye tana nuna malam da hannu tace "ƙarya kakeyi wallahi ko an gaya maka niɗin lafiya ce?"

Cikin rashin fahimta Halliru yace "malam wai meke faruwa ne?"

Malam yace "kambun baka ne da ita, sarai tasani inada yaƙinin wlhi akwai kalmar data furta masa muguwa"

Inna meramu ta miƙe rai a 6ace tana share hawayen da suka fara sintiri a fuskarta tace "wlhi yau sai na kaika gidan mai gari"

Malam mai karatu yace "ki kaini gaba da nan ma"

Ta fice.

Wasu irin yaruka malam Junaidu yakeyi wanda babu wanda yasan abinda yake faɗa dagashi sai Allah.



A gajiye suke tafiya ɗaya na goye da jaka a bayansa ɗayan kuma yana riƙe da waya, samari ne kyawawa daka gansu zaka tabbatar da hutu ya zauna a jikinsu ba wasu farare bane sai dai akirasu da chocolate color sbda kalar fatarsu,

Mai goye da jaka a baya yace "Hamud kana ganin gobe zamu sami mashin ɗin da zeyi sammako a ƙauyennan kuwa?"

Hamud yace "kaifa Lirwan ɗan iska ne, cemaka akayi basu da mashina ko yaya?"

Wanda Hamud ɗin ya kira da Lirwan yace "kanaji ɗazu da mukayi tambaya cewa akayi sai dai idan sun kawo goyo daga nan cikin garin Saminaka"

Suna cikin magana suka iso bakin kogi, Hamud ya ware idanuwansa sakamakon ganin mutum da yayi yana tasowa yana komawa,

Yaja da baya yana cewa "Lirwan tayani gani kamar mutum?"

Lirwan yace "yarinyar ce wlhi zatayi shekara sha uku"

Hamud yace "bashi na tambayeka ba"

Yana rufe baki Hamud ɗin ya faɗa cikin ruwan, sosai yake kaiwa da komowa a ciki dan ganin ya dawo da Hanan bakin kogi, amma abin yana neman gagararsa dan sai yayi kamar ya dawo da ita sai a kuma yin gaba da ita, lokaci ɗaya Hamud ya sauya yanayi, gashi da naci yaƙi fitowa, Lirwan yace "dalla malam ka fito tamutu sai kaje ka kashe kanka a banza akan wata ƴar ƙauye"

Hamud ɗin yana jinsa amma babu halin ya bashi amsa.

Cikin sa'a ya turota gaban kogin tare da fitowa shima, kana ganinsa zakasan ya mugun walaha gashi itama ɗin daya ciro ko numfashi batayi,

Hamud ɗin na fitar da wani irin numfashi yace "Lirwab Please taimakon gaggawa"

"Ban gane ba, kana nufin bayan na daddana mata ciki in sanya bakina a nata impossible, kama godewa Allah dana dinga haska maka"

A zuciye Hamud yayi kanta ya fara yi mata taimako yana danna ruwan cikinta yana karanto adu'i duk wace tazo bakinsa.

Da sauri yasa bakinsa a nata yana hurawa a hankali, ƙirjinta ya fara bugawa yace "problem ɗin basu da hospital anan kusa gashi mukuma bamu zoda mota ba"

Lirwan yace "malam kaje gurin me gari ayi cigiyar iyayenta Dan wannan aikin ba naka bane"

Hamud yace "meyasa zuciyarka babu tausayi a cikinta?"

Zai sake magana sukaga ta buɗe ido tana kallonsu, duk da hakan bawai ta gama warwarewa bane, Hamud yaje gurinta da sauri ya kamo hannunta cikin siririyar murya yace "zaki iya tafiya?"

"A'a" tace masa tana daɗa ƙare musu kallo,

Hamud ya ratayata a kafaɗarsa ya shiga gari da ita, duk wanda ya gani ya tambayesa shin yasan wannan yarinyar?,

Yawancin yara sunƙi cewa eh saboda tsoron Inna meramu da masifarta, cikin sa'a sai gashi a ƙofar gidansu, malam mai karatu ya fito zai koma gida sukayi ido biyu, Hamud ya ɗan sadda kansa ƙasa yace "malam wannan yarinyar a kogi muka cirota dan Allah ko zaka taimaka mana da cigiyarta inason ganin iyayenta?"

Malam mai karatu yace "inda nake a tsayen nan ne gidansu zomuje mahaifinta ma babu lafiya"

Lokacin Lirwan ya ƙaraso suka shiga gidan.

Suka sami malam Junaidu a kwance, Lirwan ya haska fitilar wayarsa yace "sannu baba"

Malam Junaidu yace "yauwa a ruwa kuka ciro min Rashidan?"

Hamud yace "eh baba, ya jikin naka?"

Malam Junaidu yace "Alhmdulilah"

Inna meramu dake shigowa yanzu ta hango Hanan kwance tana ta rarraba idanu, da sauri ta ƙaraso kana tace "mezan gani kamar Hanan?"

Malam mai karatu yace "itace uwar ƴan tsibbu"

Ta nuna shi da yatsanta tace "gobe mai gari yana nemanka a fada dole ayimin iyaka da rashin mutuncin da kakeyimin wlhi"

Malam mai karatu yayi murmishi.

Sai kuma yace "wayasani ko kece kika Kaita can ɗin?"

Cikin masifa tace "innalilahi wa inna liaihir raji'un sharrin harda na hallaka yarinyata, malam kana jinmu fa?"

Malam Junaidu daya samo kansa yace "bazan iya ba"

"A yau da zan sami mai auran Hanan wlhi da babu abinda zai hana ban badata ba"

Hamud yace "inhar zaka bani ita baba wlhi Allah ina sonta kaje kaga dangina dan Allah"

Malam mai karatu yace "ba ɓoyayyu bane fa na ganesu gidan hakimi sukazo yau kwanansu huɗu"

Karaf Inna meramu tace "an yi baikonta dan haka sai abarta tasha ruwa"

Malam Junaidu yace "nidai a iya sanina banyiwa ƴata miji ba, saboda ban taɓa ganin wani yazo da niyar zance ba"

Inna meramu tace "malam kadai tuna dan wlhi munci dubu arba'in na Usaini mai gidan duhu"

Malam Junaidu ya zato ido ya kalli Inna meramu cike da mamaki kafin yace "toki tattara ki maida masa da kayansa dan bana fatan musiba a rayuwata"

Malam mai karatu yace "wannan wane irin dabbanci ne? ke zaki aurar da ita kenan ba mahaifinta ba, kowa dai a garinnan yasan irin ginin Gidan duhu, matan gidan basa fita ko zaure kullum gidan a kulle yake da kwaɗo kinsan bayan haka ko fitowa basayi gaisuwar marar lafiya sai cikin dare kamar munafukai"

Inna meramu tace "kai kaga haka, kuɗinsa kawai ya isa yasa a aureshi ni nan daka ganni badan na rigada na auri malam ba yace yana sona wlhi auransa zanyi"

Malam mai karatu yace "Ashsha budurwar zuciya Allah wadaran naka ya lalace wannan wane irin san zuciya ne?"

Malam Junaidu yace "oho nidai babu zancen aure a wannan lokacin Ni da kaina zan nema mata miji"

Inna meramu tace "kuma sai kayi wlhi inhar kaga Hanan bata auri Usaini mai gidan duhu ba, to bani da numfashi ne"

Malam mai karatu ya fice ransa a ɓace.

Hamud da Lirwan da suke durƙushe sun gama gano matsalolin da yarinyar take fuskanta daga ɓangaren uwar goyonta, Hamud ya mike kafin yace "baba gobe zamu tafi, yakamata kuyi shawara a tsakaninku domin duba dacewar irin mijin daya kamata Ku aurawa y'arku"

Baba yace "to"

Har suka fita baice musu komai ba, ya kasa furta koda kalma ɗaya ne tsabar baƙincikin dake ci masa rai,

Inna meramu ta shiga ɗakinta, ɗakin daya kasance duk abubuwan tsibbace tsibbace, dalilin da yasa suke yawan faɗa da malam mai karatu kenan,

Ta kalli gaban ta ɗibi wani baƙin abu ta watsa tana cewa "Juuunaiiiiiduuu,"

Sai data kira sunan sau uku sannan ta kunce ɗaurin wani lanƙwasashen ice tana dariya marar sauti,

Malam Junaidu na zaune a tsakar gida har akayi sallar isha'i, Hanan ɗin tana gefensa bacci ya ɗauke ta dan batasan wainar da ake toyawa ba,

So yakeyi ya mike sam ya kasa ƙafafunsa babu ƙwari sai ƙyarma suke, a hankali ya kama bango yana cewa "meramu zoki ɗaga Hanan taje ɗaki"

Inna meramu tace "meyasa kai baka ɗagata ba tunda ka nunamin rashin mutunci ƙarara a idon jama'a to ka rubuta ka ajiye wannan aure anyishi an gama, kuma zai kawo sadaki dubu ɗari uku kaga ya isheka siyan iri da takin noma"

Malam Junaidu nadaga tsaye ya zube a gurin yana salati yace....







*WAKE ƊAYA💍*

MomIslam



🆓Page2



"Meramu zaki ƙarasani"

Inna meramu na dariya tace "yo kuɗi ma sun hallaka kaga kawai mujira turo iyayensa da yace zeyi"

Malam Junaidu na daga zaune ya rarrafa ya shige ɗaki, yana shiga ya fashe da kuka, sai da yayi mai isarsa harda majina kafin yace "Allah Sarki hanne tunda kika mutu na shiga wani hali"



A yanayin inda malam Junaidu yake maganar sai ya baka tausayi,



Tunowa da yayi Hanan na kwance a tsakar gida, yasa ya rarrafo ya fito jikinsa na rawa, bazai iya d'agata ba sai dai ya tasheta, yace "Hanan tashi kizo ki kwanta"

Da sauri ta miƙe ta shiga ɗakin ta kwanta a katifar yayin da ta kasance makwancinta,

Shima ya rarrafo ya shigo ya kwanta, tare da kwararo adu'oi.

Acan 6angaren Inna meramu, tana zaune sai lissafin kuɗaɗen da Usaini mai gidan duhu ya bada take, a lissafin nata ne naji tana cewa "saura dubu biyu su zama dubu hamsin in siyo saniya, taci gaba da cewa yawancin matan garinan kowacce ta ɗaure saniya amma ni mazauna sanya, badan Allah ya haɗani da wannan mai jinin takaicin ba da tuni inada kiwo"

Ta ƙarashe maganar tana 6oye kuɗin nata, tare da hayewa gadonta me rumfa, tsayawa yin adu'ar kwanciya baci a gurinta ɓata lokaci ne dan haka ta cigaba da hamma,

Sha ɗayan dare malam Junaidu ya farka, ya tashi zaune gabansa na tsananta faɗuwa, a fili ya furta "innalilahi wa inna ilaihir raji'un"

Sai kuma yace "gaskiya ina tantamar aurannan na Usaini mai gidan duhu, idan na bashi Hanan zai cutar da ita, dan haka inaga asubar fari zan riƙe hannunta in kaita gidan Hajiya Indo"

Har aka kira assalatu idonsa biyu, a hankali ya tashi Hanan yace "ki tattara kayanki a buhu zan kaiki gidan Hajiya Indo ta sama miki aiki a Kaduna"

Hanan na miƙe da sauri tana mutsuke ido tace "baba ka mance ance a binni akwai ƴan yankan kai?"

Malam Junaidu yace "ban mance ba Allah zai kareki nidai fatana kiyi nesa da wannan azzalumin mutumin ko zanji sassauci a zuciyata"

Hanan tace "to"

Ko ɗaurayo baki batayi ba suka fice cikin sanɗa,

Kasancewar hanyar tasu uku ce, koma ince ko ina hanya ne a gidan yasa sukabi wacce babu yawaitar mutane, suna isa gidan Hajiya Indo, malam Junaidu ya bubbuga k'ofar, kasancewar ita ɗaya ce a gidan mijinta Allah yayi masa rasuwa ta fito tana cewa "waye nawa"

Ganin malam Junaidu riƙe da hannun Hanan ya sata cewa "lafiya?"

"Lafiya lau"

Malam Junaidu yace "kafin ya nuna Hanan yace "kin ganeta?"

"Ah haba malam Hanan ai ƴar gudana ce"

Malam Junaidu yace "dan Allah Inba damuwa ko zamu shiga daga ciki? dan naga mutane sun fara wucewa"

Hajiya Indo tace "to muje"

Kasancewar garin da hasken farin wata yasa suka zauna a tsakar gida ta miƙa musu kujera ƴar tsuguno tace "to ina jika"

Malam Junaidu yace "basai na faɗa miki ba, kinsan halin da Hanan take ciki a gidan nan, dalilina na kawota gurinki kuwa shine ki tafi da ita binni ki nema mata aiki, saboda Meramu naso ta haɗata da Usaini mai gidan duhu"

Da sauri Hajiya Indo tace "innalilahi wato wannan mata ta iya cin zali, dama yau nake san zuwa can ɗin, dan dakunkai anjima bakuzo ba wlhi da bazaku sameni ba"

Malam Junaidu yace "Alhmdulilah naji daɗi, dan Allah idan ta tara kuɗin a dinga yi mata siyayyar kayan ɗaki wanda suka kamata"

Hajiya Indo tace "insha Allah, ai naga kamar kanada waya ko?"

"Eh inada"

"To ungo wannan itace lambata ka ɗauka yanzu, naji an shiga Sallah"

Malam Junaidu ya ɗauki lambar kasancewar yaɗan iya haɗa hausar boko amma bawai sosai ba,

Yayi musu fatan isa lafiya yayiwa Hanan faɗa tare da ce mata tayi abinda ya kaita karta tsaya shirme da surutu tunda ita Allah ya hore mata ɗan banzan magana kamar taci bakin Aku,

Yana tafiya, Hajiya Indo tace "jeki ɗaƙi ki cire kaya kiyi wanka tunda akwai kayanki sai ki zaɓi mai kyau kisa, ni narigada nayi wanka sallah kawai zanyi mu tafi, tunda yaron talle ne zai kaimu basai munsha wahalar mai mashin ba"

Kamar inda Hajiya Indo ta umarci Hanan hakan tayi, tana fitowa daga wanka ta shige ɗakin Hajiya Indo tana tambayar ta man shafawa,

"Gashi nan kina gamawa kisa kaya amman dai kinyi alwalah ko?"

Hanan tace "eh nayi"

Ƙararrawar mai mashin sukaji, cikin sauri Hanan tasa kaya tare da ɗaukar hijabinta dafaffe sbda ya gaji da datti, Hajiya Indo tace "bakida wani hijabin ne?"

"Eh shikenan min na sallar Bara"

Hajiya Indo ta kama hannunta suka fito, Hanan na riƙe da buhun kayanta itakuma Hajiya Indo na riƙe da hand bag tasha koren janbaki saboda a ƙauyen itace wayayya me fita birni.

Bayan sun gaisa da me mashin ɗin ta fara hawa da Hanan kafin itama tahau suka wuce tashar Kaduna,

Suna cikin tafiya Hanan tace "dan Allah ka tsaya in tsinko yalo wlhi wacce na samo shekaran jiya ban ganshi ba"

Hajiya Indo tace "sedai ki koma gida"

Hanan tayi tsit

Har suka iso mangwarori, Hanan bata sake magana ba, wato tashar mota.

Godiya tayiwa yaron talle kafin ta miƙa masa ɗari tace sun gode, suna isa gurin motocin dake pake dama saura mutum ɗaya ake jira, Hajiya Indo na shiga mota ta cika sai tafiya,

Inna Meramu

Fitowa tayi tana miƙa tana hamma lokacin gari yayi haske wai zatayi alwalar asbha, taja ruwa a rijiya ta shiga banɗaki ta fito tayi alwalah ta koma ɗaki tayi sallah, shiko malam Junaidu yanata tararradin kalmomin da zai gaya mata saboda tsoronta yakeji kamar ta shanyeshi,

Kamar an jefota ta faɗo ɗakinsa tana bambamin masifa, "wato barinta kayi tana bacci har yanzu ko?, to wlhi sai dai kaci tuwon da sanyi dan bazan taɓa ɗumamawa dakai ba, niba asararriya bace"

Tayi kiɗanta tayi rawarta ta fice baice mata ƙala ba.

Kamar inda ta faɗa bazata ɗumama tuwon dashi ba haka tayi, iya nata, tana gamawa ta shige ɗaki tanaci tana fifitawa.

Malam Junaidu yayi murmishi a zuciyarsa yace "duk abinda zai faru yanzu bazai sosamin raina ba, abinda zai tayarmin da hankali shine, inji ance Hanan ta dawo garinnan wlhi sai nakusa sheƙawa"

Yana faɗar haka ya fice ƙofar gida.

Kai tsaye ya wuce gurin Halliru mai shago, yasiyi biskit da ruwa,



GIDAN DUHU••

Gidane babba bazaka tabbatar da girmansa ba har sai ka shiga ciki, wani irin gini akayi mai matuƙar tsayin gaske, babu wanda ka isa ka hango to katangar ma takai tsayin gidan ina batun ganin wani abu, daga cikin gidan akwai ɗakuna goma, ɗaya na Usaini shine a farko, ƙofar shigowa gidan tana cikin ɗakinsa, dan haka idan zai fita koda yaushe gidan da ƙwaɗo yake wuni har kwana ma,

Daga can cikin gidan kuwa ɗakuna tara ne, uku a gabas uku a kudu uku a yamma nashi kuma a arewa, ɗakin dake gabas shine na Ladidi, tana riƙe da ɗakuna biyu ɗaya na yara, ita kuma wacce ɗakinta ke kudu tana riƙe da ɗaki ɗaya sunanta Iyami, saboda bata aihuwa yasa aka bata ɗaki ɗaya mai ciki da parlo, ragowar ana saka kayan abinci, mai ɗakin dake arewa shikuma Hauwa ce a ciki ragowar ɗakunan yaranta maza suna kwana a ciki ɗaya kuma yara mata,

Usaini yanada yara goma sha biyar, goma mata biyar maza ya tura su almajiranci, saboda shige da fice, inda ya tura shi ba'a dawowa Sai anyi sauka ko shekara hamsin zakayi inhar baka sauke ba bazaka dawo ba, a cikinsu babu wanda ya dawo shekararsu goma kenan, kuma shi Usanin bai damu da yagansu ba, idan yaji iyayen sun matsa sai yayi musu asiri sudena maganar yaran kwata-kwata,

Ladidi itace uwar gida, tanada yara bakwai, mata biyar maza biyu, matan nata akwai mai shekara goma sha biyar, akwai mai shekara goma, akwai mai shekara takwas akwai mai shekara biyar Sannan akwai mai shekara uku Sannan akwai mai shekara ɗaya wato yarinyar ta da take goyo,

Mai shekara sha biyar ɗin sunanta Sahura, mai shekara goma ita kuma Habiba, mai shekara biyar Lawisa, mai shekara ɗaya kuma Sa'ade, mazan da Muhammadu zangina shekarar sa Ashirin Fatihu kuma goma sha biyu duk basa gida.

Ita kuma Hauwa tanada yara takwas maza biyar mata uku, ta farkon mai shekara goma sunanta Hinde ta biyun kuma Barira, mazan da Saminu shekararsa goma sai Tanimu shekarasa bakwai sai Zubairu shekarar biyar sai Ashiru shekararsa uku sai Ashahabu mai wata shida a duniya,

Kaf yaran gidan maza basa gidan matan kuma haka suke rayuwa a cikin gidan da kansa yake biya musu karatun allo boko ko oho, tunda suke Babu wacce ta taɓa fita ko nan da ƙofar gida, haka suma iyayen tunda ya aurosu basa fita sai cikin dare,

Al'adar gidance kullum da safe da safe sai an surfa gero anyi dakan kunu, idan markaɗe ne da kansu suke yi a turmi ko a dutsen miƙa,

Duk yawansu magin talatin suke sawa a abincinsu farin magi guda ɗaya, ɗakunan biyu dake gidan duk kayan abinci da kayan miya ne, kama daga kabewa yakuwa tayin fate daddawa da sauransu.

Duk ranar juma'a sunayin tuwon shinkafa miyar kabewa babu alaiyyahu,

Da Sallah kuwa yana yiwa duka yaran ɗinki da iyayen amma babu mai gigin fita ko nanda ɗakinsa bare yakai ga ƙofa, babu kuma mai kawo musu abinci, matan basa zuwa gidan iyayensu sai ƙarfe takwas fuskarsu sanye da niqab, idan lokacin sallah ne kenan, idan kuma gaisuwar mara lafiya ne, sai ƙarfe shaɗaya na dare suke fita, shizai kaisu a mashin ɗinsa kana ya dawo dasu.

Wani abin mamaki idan matan suka aihu shi da kansa yake unguwar zoma, kuma ba'a suna, idan iyaye suka aiko da gudunmawa shi ake bawa ya basu,

Haka rayuwarsu take tafiya cikin matsatsi da tashin hankali, suke rayuwa, bayajin maganar iyayensa sam.

Hamud Lirwan••

Tunda suka koma gida Hamud ya kasa samun sukuni saboda har mafarkin Hanan takeyi, yau kwanansu uku da dawowa amman sai yakejin kamar yayi sati ne, tunanin Hanan ya hanashi sukuni idan yazowa Lirwan da zancen sai ya fara yi masa faɗa yana cewa, yayi asara duk yawan ƴan matan dake binsa amma zai ƙare a ƴar ƙauye wacce iyayenta ba sonta sukeyi ba, wata ƙila ma a waje aka samo cikinta,

Morning "Hamud an kammala breakfast tun ƙarfe bakwai 7:am kace yau zaka fita aiki da wuri amma naga baka shirya ba?"

Mom ta faɗa tana kallon Hamud dake dafe da kansa yana zaune akan kujerar parlon,

"Nafasa fita mom"

"Akan me?"

Yayi shiru bai ce komai ba, Lirwan dake fitowa yana sanye da lallausan yadin boyel me ruwan toka, yace "mom kibar Hamud kawai, ya kamu da ciwon so"

Mom ta zaro ido kafin tace "ai da nafi kowa farinciki inhar hakan ta kasance"

Hamud yace "wlhi momy ƙarya yake yimin kawai banajin ɗaɗin jikina ne"

Badan Mom ɗin ta yarda ba tace "to shikenan tasan Lirwan bazai yi mata ƙarya ba...

Banyi editing ba, littafin Falak sai ƙarfe takwas insha Allako tara ma'ana 9:pm ko 8:pm



Gaskiya bakwa comments

Mom Islam ce



08141799224















*WAKE ƊAYA💍*

MomIslam



_True life story_





*Arewabook@momislam11*





🆓page3





A hankali Lirwan ya isa dinning room ya buɗe warmers ɗin dake jere da abinci ya ɗauki plet yasa abincin, girgiza kai yayi yana murmishi sakamakon kai lomat abincin da yayi bakinsa, taliya ce jollof ta mangyaɗa , cikin d'aga
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment