Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dadi neh ya lullubeshi amma kuma wani sashi na zuciyarshi bugawa yakeyi da dan sauri cos baisan irin tarban da zatayi mishi bah.....

    Haka tadinga takowa ahankali, saikuma tafara sauri sauri daga baya taji she can't wait to be cuddled in his arms , kawai saitasa gudu kafinta isa shikuma ya bude arms nashi, without a waste of time ta rungume shi shikuwa dagata yayi daidai face nashi haka yadinga juyawa daita itakuwa miye zatayi inba dariya bah, ajiyeta yayi akan mota while tayi crossing legs dinta a waist nashi

"Only God knows how much av  missed you" yafada mata in whisper, pecking nashi tayi sannan tace

"Same here"

"Oh really?" Yatambayeta

"Ofcourse" tabashi amsa, daganan kuma tasa head nata akan chest dinshi  cikin sanyin murya tace

"My Nafhi and Momma are gone, i will never see them again"

"It's okay, may their souls rest in perfect and everlasting peace" yafada

"Ameen" tafada tareda dagowa, rolling din eyes nata tayi sannan tace

"So tell me are you married or still single?wani mumunar faduwar gaba yaji sannan yadaure yace

"why are you asking?" Gyara wuyar top nashi tayi then tace

"Just want to know how many kids you got" yanda tayi magana neh yabashi dariya aikuwa yahau darawa

"Kafara koh" tafada tana pouting din small mouth nata, lips dinta yadan ciza

"Ouch banson mugunta fah" tafada tana ware legs dinta daga waist dinshi domin sauka

"Am sorry ABAR SO karkiyi fushi dani please" yafada tareda kama kunnenshi cos yaga tadauka da serious

"It's okay and let me down" tafada mai tana mai yin murmushi

"Kinzamo big girl fah"Amin yafada

" hmm, you know as times goes on cos kaima ba kaman da bah" tafada tareda kama hand nashi bayan yasaukar da ita , kuma saiyanxu suka lurada yadda aketa kallonsu

"Wai nikam sadaka ake rabawa neh kokuma shooting din film akeyi  naga kun tsaya mana aka tareda zuba mana na mujiya" tafada cike da tsiwa da gadara

"It's okay babe mushiga ciki" yafada hade da matse hannunta dake cikin nashi, akasar zuciyar shi kuwa farinciki neh fal aciki cos baitaba kawowa zata mishi irin wannan tarban bah, suna shiga ya gaisar da Antyn itama da murmushi afuskarta ta amsa mai

"Wato Babynmu shine kikaje kika dade koh, bakisan dare natayi bah" Antyn tafada tana juyawa wajen Nadhira

"Oh Antymu i was so happy shiyasa" Nadhira tafada lokacin  tana rolling eyes nata wanda hakan yazame mata body

"Oya jeki" antyn tafada lokacinda take bata juice baaket din

"Antymu yanxu korata kikeyi koh?, kenan harkin gaji da ganina koh, babu damuwa" tafada hade da ficewa azuciye .

"Babynmu wlhy kitsaya bakorar ki nakeyi bah" antyn tafada tana mai bin bayanta , itakam ko sauraron antyn batayi bah  tatari keke napeep, shikuma Amin ganin ta tare napeep yasashi komawa cikin gidan dasauri domin dauko car key dinshi, haka yagama duba gurinda ya dan zauna  amma babu key babu alamunshi , zuwa lokacin kuma yasan sunyi nisa, sai asannan yatina ashe key din na kan car dinshi yamanta......(lol.....😆)

"Yanzu yazamuyi" Hasana ta tambaye antyn cikeda damuwa

"Karki damu daman haka take da saurin fushi ko da abin baikai ayi fushi bah.

"Toh ki gwada kiran numbern ta mana" inji Amin da fada

"Ai kona kira badagawa zatayi bah" Antyn tabashi amsa

"Toh kiban numbern nayi trying luck" yakara fada, haka antyn ta karanto mai numbern, kira yayi amma har yatsinke batayi receiving bah, sallama yayi musu   akan zai cigaba dakira , cike da damuwa yakoma gida ranar. Su antyn kuwa jigum suka zauna har Hasana takoma gida, tana isa kofar gidansu tasami Husain wajan

"Ya dai twinee?" Yatambayeta

"Wlhy wai Nadhira neh ta tafi cikin fushi" tabashi amsa

"Miye akamata haka?"yakara tambaya......nan dai ta labarta mai abinda yafaru

" kut.. Wannan wace irin zuciya ce daita , gaskiya za'asha fama"yafada

"Gaskiya kam cos ko yafiya batadashi" Hasana tafada

"Hmmm,  ya akayi kika sani madam Hasana?"zama tayi na musamman ta bashj labarinsu wanda tasani gabadaya , wani tausayinsu yaji shima

" shiyasa ai yanayinsu baiyi kamada na talakawa bah"haka dai suka dinga hira har aka tada sallah sannan Hasana tashige cikin gida.

    Abangaren Nadhira kuwa  tinani takeyi akan abinda yasata fushi kuma bayan tayi alkawarin bazata sake bah gabadaya saiyaji bata kyauta bah. Gaishe da baba maigadi tayi sannan ta ajiye basket din akofar side dinsu kafin tashiga side dinsu mumy tana shiga tasame su harda wani bakon fuskanda bata sani bah amma kamanninshi yanuna cewan shi dan gidan neh

"Sannu da gida" tagaishesu hadeda risinawa cikeda girmamawa

"Saiyanxu  baby"

"Eh"

"Yamutanen gida?, hope suna lfy" Abba yatambayeta

"Alhmdllh , wai inji Antynmu tana gaishe ku" ta bada amsa

"Muna amsawa" mumy tafada

"Toh saida safe " tafada musu

"Bazakizo muyi dinner bah?" Mumy ta tambaya

"A'a wlhy cikina a koshe nake " tafada murmushi kwance akan face dinta....

"Waini mumy miye kike gayyatar wannan kazamar kan dining dinmu, ko sokike Love dina yaganta yakasa cin food neh cos kinsan ba kowace cleaner yake kulawa bah balle kuma tazauna a inda yake for the matter of fact cleanern wannan kazami gurgun !!!" Afirgice suke kallonta , kaman wata walkiya ta iso gabanta

"One more bad word from you and i promise to keep you mute"Nadhira tafada cikeda bacin rai cos har jah idonta yayi

"Miye kike nufinda zaki keeping dinna mute, yar yarinya ma dake yar matsiyata , doluwa mah irinki, tukunna mah wai kare wannan gurgun zakiyi don rashin hankali , wanda ko gata baida akanshi zaki nema gayamin magana tukunna mah waye ubanki a fadin Nigerian nan miye kika taka arayuwa nasan familyn ki dake suka dogara soboda ke ne mai nema musu na daily bread kuma a haka kike neman wasting opportunityn ki"

"Kursum" Abba yakirata cikin kausashiyar murya

"Karka kirani mijin mumy kayi shiru cos bada kai nake yi bah, ka adana duk abinda xlzai fito daga wannan mushen bakin..." Ai bata karasa bah taji saukar mari a kumatunta..........tirkash

Guess waye mareta?

💋💋wurarh💋💋


💝💝💝💝💝💝  
                       *ABAR SO*
                                    💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN by: NAFISAT  MA'ARUF  SHEHU*
                      *💋💋wurarh💋💋*
Wattpad:Nafisatma'arufshehu

🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

               🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 75-76

Ai bata karasa maganan bah taji mari a kumatunta

"Ke wace irin mara hankali ceh, kinfini sanin abinda wannan bawan Allahn yamiki arayuwa amma tsantsan rashin hankali irin naki kike zaginsa kuma fah dukda hakan yana suriki awajenki, wai tsaya mah tukunna  harke dinnan kin isa ki zageni , kinsan wace ni kuwa, kinsan waye mah ubana kuwa, babu shakka kinsanshi bama ke kadai bah dukkanku kunsanshi , muba matsiyata bane cos daga kaina har 7th generation dinmu masu zuwa bazasu taba sanin miye talauci bah, kuma mijinki dakike ikrarin baisom kaza da kaza toh i bet you ni zan aureshi kuma kindai ganni babu namijin daya isa yayin resisting dina cos ni ABAR SO ceh!!!, babu magani babu tsafi zan siye zuciyar mijinki dukda nima inada wanda nake so amma haka zan hakura na aure mijinki, zan nuna mai tsantsan soyayyar da babu algus acikinta , sannan abinda zan gargadi ki guda daya neh kawai shine ki boye mijinki cos haduwata dashi will be the beginning of your downfall, lastly wanda kike kira da kazami gurgu shin kinada masaniya akan abinda ya mayardashi hakane?, ko kuma kina da masaniyar akan matsayinda yakedashi kafin yadawo wannan  condition din?, ko kinada masaniya akan asalinshi, kokuma abinda yakeda kafin yadawo haka?  ko kuma kina nufin Allah baya jarabtan bawanshi?, bakya tunanin shidin mah yanada gata kaman yadda kowa yakeda?"numfasa tayi sannan tajuya wajen wannan saurayin

"Kaikuma  kawani tsaya sokoko ka wangale baki hangam kaman wani maloho , shasha kawai agaban idonka wata kanwar bayanka take zagin babanka wanda inada yakinin cewan bazaka wuce 28 bah itakuma nasan babu tantama 25 amma shine bazaka dauko tsumagiya ka chachauda mata bah, wlhy you are a disgrace to manhood"tana gama fadin hakan ta fice daga palourn hartana bangaje a bakin kofa shigowa.

     Shikuwa dawowarshi kenan daga gidansu Nadhira , mamaki neh yakamashi jin yadda aka bangaje shi amma ko arzikin sannu baisamu bah, girgiza kai yayi hade da kutsawa ciki , abinda ya tarar neh yasashi jan birki yana dada bin gidan da kallo cos tunaninshi shine gidan wasu yashiga  soboda ganin da yayi an tsatsaya  while Kursum na durkushe tana kuka ga idon yakumbura , shahada yayi sannan ya matsa kusa dasu

" lafiya naganku haka?, miye faru?"ya jera musu questions trying to figure out what the problem is. Mumyne tafara haurawa sama, cike da rashin nutsuwa ta mike tabi mumyn tana fadin

"Wlhy bazan yadda bah , i swear to make the hell out of that small girl , tinda nake ba'a taba cimin mutunci irin na yau bah , look at my face i can feel how it got swollen" tafada daidai lokacinda tarike hannun mumy dayan hannun kuma akan cheek dinta. Mumy kam babu baki  magana cos bazata taji dadin marin da aka mawa daughtern ta bah kuma bazata ceh ta ji dadin zaginda Kursum tamawa mijinta bah amma kuma yazatayi, batareda tace komai bah ta zame hannu Kursum sannan takarasa hayewa, cikin kuka Kursum tamara mata baya

"My son inkagama kasameni a room dina" Abba yafada tareda barin palourn

"Kai miye faru?" Amin yatambaye kaninshi

"Infada maka yau ankoyawa Kursum hankali " nan dai yakwashe komai yafada mishi, shikuwa abangaren shi haka kawai yaji yarinya ta burgeshi kuma zaiso ganinta

"Barinaje wajen Abba " yafada hade da barin wajen. Da sallama yashiga cikin bedroom din Abbanshi , amsawa yayi hade da nuna mai gefenshi alaman yazauna batareda ya musa bah yaneme mazauni agefen nashi

"Ka kalle ikon Allah koh abinda baby tayi naji dadinshi sosai cos taburge ni bakadan bah she's indeed a very good girl and i like her confidence and am very surw if you marry her you will definately be happy foe for life, Dan Allah ka aureta" tinda Abbanshi yafara magana yake jin wani iri gameda yarinyan, wani abu na bashi shawarar da ya aureta kodan takoyawa Kursum hankali kafin ya aure ABAR SOnshi cos baison takara shan wani wahalan

"Toh Abba , amma inada wani urgent emergency wanda gobe karfe 10 nasafe zai iso, insha Allah idan nadawo zanje mugana da ita yarinyar" Amin yafada

"Toh dan Albarka,yadda kake shirin faranta min rai haka Allah zai faranta maka naka " Abba yafada cikeda jindadi

"Ameen Abbana" yafada yana murmushi sakamakon tinawa dayayi da moment dinshi da ABARN SOnshi dazu

"Jeka" inji Abba

"Toh Abbana" yafada tareda ficewa zuwa part dinshi

    Abangaren Nadhira tana shiga tanufi wajen Dadynsu lokacin kuma idonshi biyu da alama mah yunwa yakeji batareda bata lokaci bah ta debi juice din a cup sannan tafara bashi shikuwa karba yakeyi sosai kuma alamu sun nuna yana jin dadinshi sosai. Tana gamawa takimtsa shi sannan tashiga watsa ruwa tareda dauro alwala, tana idar da sallah da sallah tasa kayan baccinta kafin tafara tinani  abinda yawakana tsakaninta da Kursum

"Zakisan dani kikeyi" tafada tareda da lumshe ido. Sallaman datajine yasata gyara hulan net din kanta sannan ta amsa shikuma yashigo wani irin bugawa kirjin tayi cos batayi zaton zata ganshi bah

"Who are you?" Shine tambayar daya mata, abazata tambayar tazo mata

"Na rokeki da sunan Allah da  karkimin karya kuma akwai abubuwan da nayi noticing gameda ke shiyasa nake son sanin more about you" Abba yafada mata

"Bazaniya baka amsa dakaina bah amma ina iya baka address din wanda zata iya baka kyakyawan labarina " tafada mai cikin sanyin murya

"Okay if that's fine with you" Abba yafada

"Tnx for understanding" tafada sannan tadauko paper tarubuta mai address dinsu then tamika mai

"Gud night baby" yafada da murmushi a face dinshi

"Good night Abba" itama tafada tana miyar mai da martanin murmushin.

       Bangaren Kursum kuwa tana hawa upstairs direct room nata tawuce , travelling bag dinta tadauko tadinga zuba kayayyakin ta aciki

"Wlhy yarinyan nan tadebo ruwan dafa kanta , harni zata mara , harni takecewa zata auramin miji if am not mistaken  kwacemin miji fah take nufi, this can't be Amin must leave this house first thing tomorrow morning , i won't bear to loose my love to another woman wait mah is she a woman?no she's a girl" haka tadinga magana itakadai kaman wanda maganin ta yakare(loh....hhhh).

      Tana gama parking din kayanta tafice zuwa part din Amin, ko kwankwasa kofa bata yi bah takutsa ciki , hangoshi tayi asaman bed yana danna laptop yana ganinta amma yayi biris kaman babu abinda ya gani kuma sarai tasan yaganta zama tayi awajen dressing mirror  tana kallon swollen face nata wanda haryanxu shatin hannun yarinyar bai bace bah, tsakin dataja neh yasashi kallonta

"Kai yarinya nan badai zafin hannu bah, mtsww shegiyar yarinya kawai dangin mayu wlhy sai tayi dana sanin marina, kazama mah daita,  Love you need to see that small insect wlhy yarinyan bata da sense wai kai zata aura wai saita sace zuciyar ka hhh, stupid slot kawai cos daga ganinta mah zakasan da yi PHD a karuwaci tana magana tana rolling din ido" kallonta yakeyi ko kiftawa baiyi cos wlhy maganan ta mah zainuna yadda takejin haushin yarinyan,   shafa kanshi yayi sannan yace.........

Comment,
Vote &
Share
💋💋wurarh💋💋


💝💝💝💝💝💝  
                       *ABAR SO*
                                    💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN by: NAFISAT  MA'ARUF  SHEHU*
                      *💋💋wurarh💋💋*

*Wattpad:Nafisatma'arufshehu*

🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

               🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 79-80

.....Ga Wanda tafiki nan ta iso,sanye take cikin wata doguwar rigan kanti amma da kadan yawuce gwiwa dakuma hula colourn kayan,cos yawancin kayayyakin ta basu cika tsayi bah,gaishe da mumy tayi hade da durkusawa har kasa as usual while mumy ta amsa da fara'a cos yarinyar na burgeta

"Kanin mu yanaga tarike kaman kayo mata sata"tafada mai cikeda son gano abinda ke dariya

"Gwanda dakika Zo Matar yaya cos Allah yagani bazan iya dukar Matar yayana bah,kuma gaskiya bazan iya zaginta bah"yafada hade da shafa Kai

"Gaskiya kayo tunani mai kyau ,and ke Anty Kursum wannan dakika rike haka kinsan kanin mijinki neh Kuma yakamata kidinga girmamashi "tafada

"Ke fah nalura kinada shishigi,tukunna mah yaushe nadawo Antynki?yaushe Abdulkadir yadawo kanin mijinki?yaushe Amin yadawo mijinki?,toh wlhy ki kiyaye ni,karkiga jiya kin mareni banrama bah wlhy bashi Kika dauka Kuma ni ba'acin bashina batareda an biya bah"tafada tana zazzare eyes

"Wai ni bashin miye naci miki neh?kodai marinki danayi miki jiya?hala kinmanta ke Kika fara mareni nah rannan?toh bari in fada miki an eye for an eye,blood for blood and life for life,ma'ana shi kuwa shine  ni Nadhira bana yafiya duk abinda akamin bana mantawa  cos there's a blood of vengeance running in my veins,ba'a shiga sabga ta akwana lafiya"tafada looking so serious hade da Jan kujerar dining,while itakuwa Kursum tafara tsorata da lamarin Nadhira cos taga yarinyar hayakin kanta yafi Wanda yake nata kan,cikin sanyin jiki tahaura sama. Mumy mah taji dadin yadda Nadhira ke magana Kuma alamun yarinyar yanuna cewan there's something burning in her ,itama haurawa tayi Sai yasauran daga Nadhira Sai Abdul  Wanda ahalin yanxu sun fara cin abinci.

    Can ba da dadewa bah saiga Kursum tasauko da traveling bag a hannunta,tana hango su taja tsaki

"Allah yaraka taki gona"Nadhira tafada hade da siping din tea,dariya Abdul yayi tareda fadin

"Wlhy matar yaya bakida  dama"itama dariyar tayi while Kursum takara sauri  acikin tafiya ta

"Mutum dai yafadi nikuma nasha dariya"tafada yadda Kursum din zataji........

       "Matar yaya!!"Abdul yakirata cikin serious tune bayan sun kammala cin abinci,dagowa tayi  tareda kura mishi ido

"Hmm... Daman so nake kinema min budurwa,kinga Sai tsufa nakeyi,inkina da kawa saiki hada mu in yaso Sai asa ranar aurena da Dana yayana rana daya "yafada tareda Sosa Kai

"Amma fah ka kawo point ashe kwakwalwar ka naja"tafada cikin sigar tsokana

"Waye zaki bani?"yatambaye ta

"Zan baka tsalelliyar budurwa wacce itama kwakwalwar ta yana jah,amma fah sorry to say tafika Jah,kuma sunan ta Hasana idan kun daidai ta toh Falillahilhmd,amma fah saika yi dagaske cos Zuma ce,ita Zuma Kuma Saida  Wuta" tafada mai

"Kai amma nagode sosai,amma inbazaki damu bah ina son in miki tambaya"yafada mata

"Am all hears"tafada

"Wani school kikayi attending?"yatambaye ta

"Nayi NTIC na Abuja"ta bashi amsa,sanda yakaremata kallo kafin yakara fadin

"Amma scholarship board neh suka dauki nauyinki koh?".... Yafada while itakuma tayi dariya

"Dadynmu neh ya samu"tabashi amsa

"Yasaku Kuma?keda waye?ya jera mata tambaya

"Eh mana ai bani kadai bane nida twin sis dinna neh"

"Wow kardai itace Hasana? Amma Kuma intake?"yatambaye ta cikeda zumudi

"Ba ita bace wannan din kawata ce,ita sis dinna tarasu last year"tafada looking so sad

"Sai gobe"tayi adding cos bazata so yaga tears dinta bah cos she believes that babbar rashin hankali shine kabari nakusa dakai yasan wickness dinka

"But bamu gama bah"yafada mata cos bayason discussion dinsu yayi ending this way,juyowan datayi neh yasashi yin Shirin daga maganan dayake son yakara fadi ,ga eyes nata yayi mugun ja,kuma daman haka take in tahana kanta kuka lokacin da take da bukatan yin hakan,jah idon sukeyi daganan kuma tafara Head migraine dinta.


     Barin wajen tayi hade da komawa side dinsu,tana shiga kuwa ciwon Kai yamata sallama ,fadawa tayi toilet don watsa ruwa ,tana gama wa tafito sannan tasa short nickern ta na mata da vest ,ga gashin kanta ajike cos tasawa kan ruwa ko zataji  saukin ciwon amma ina!!!!.

Dakyar takarasa kan bed ga gashin yamannu mata,jitayi she can't hold it anymore daman Kuma in tana ciwon kan kama mata akeyi Sai amata Addua,dakyar tajanyo wayanta sannan tabugawa Hasana Kira ,bugu biyu yayi aka sauke

"Sai yanxu aka gama fushi damu?"Hasana tafada cos tinda tadawo bata kirasu bah amma tamawa Antyn text amma Kuma idan Antyn takira bata dauka

"Kina gida neh?"ta tambayeta cikin dauriya don bayason Hasana tasani

"Eh... Amma yanaji voice dinki haka ko dai Baki jin dadi neh"tafada cikeda damuwa
      
"Not at all,lafiyata lau kawai dai ina son kizo neh"tafada wa Hasanan

"InshaAllah zaki hannu In the next 20 minutes"

"Pls kiyi sauri"

"OK"sannan takatse Kiran while ita Nadhira tagyara kwanciyarta

"Allah kabani lafiya"tafada hawaye na gangaro mata(it's said that in mutum baida lfy,yayi Addua cos Adduan majinyaci nasaurin karbuwa,bawai mutum yace am sick,need your prayers bah)

    Sallama Hasana tamawa Umminta tafito har zata shiga tafada wa antyn,kawai saita bari sanadiyar ganin wani Lexus Jeep Parke akofar gidan cos ita atunaninta big dadynsu neh.

Adaidaita ta tsara sannan suka wuce GRA,tana sauka ta gaishe da Baba maigadi  sannan tamai bayanin wajen Wanda tazo gani batareda bata lokaci bah yafada mata inda zatashiga.......

Fitowanshi kenan dinshi kenan zaije wajen car park cos yake yazaga gari ,itakuwa ta taho tana cire phone nata daga side bag nata domin shaidawa Nadhira ta iso,gware taji tayi da mutum har sanda wayarta yafadi kadai

"Buuu....wlhy saika biyani phone dina ,taab saikace baka gani,kana tafiya kaman Wanda yasha abu,karma kafara bani hakuri cos saika siyamin wani, sabon phone neh fah ko sati banyi da fara amfani dashi bah,kaii banma bukatan wani, nawa nakeso"tafada cikeda masifa(daman Kuma hasynah akwai masifa🤣🤣..lol) galala yayi yana kallonta cos babu karya tamai Dari bisa Dari amma da itace

"Gaskiya kinma raina nih kidubi tsabaragen eyes dina kice nina bugeki , karki manta fah kece bakya kallon gabanki"yafada mata while eyes nata nayawo ajikinta

"Kaikuma dakake kallon gabanka miyesa baka kauce bah?nikam duk wannan maganan ba problem dina bane problem dina shine phone dinda kafada"tafada tana mainuna phone dinda ke hannunshi

"Alhmdllh tinda fashewan kadan ne,saikije kiyi manage kafin natambaye matar yayana duk hukuncinda tayanke shi za'ayi"yafada tareda Mika mata phone dinta

"No gaskiya ban yadda bah,daman Zan Kira besty na ne yanxu Kuma gaskiya bazan iya amfani da wannan bah"tafada haryanzu bata karba bah

"Toh ganawa ki kirata dashi "yafada yana mai mika mata nashi wayan

"What kana nufin da wannan abin xanyi waya"tafada tana mai nuna Samsung Galaxy S6 din hannunshi sannan tacigaba

"Inama kace muje wajen matar yayan naka tayanke whatsoever hukuncinda xatayanke tinda nalura maybe ita judge ce "yafada tana mai murguda mai Baki

"Muje"yafada tareda yin gaba cos idan yacigaba da tsayuwa da ita baisan miye zai faru bah. Suna Isa bakin kofa yadan bude sannan yace tayi sallama....

"mushiga kawai"yafada mata suna shiga suka hangota ta akan bed bed

"Matar yaya yadai? yafada while ita Hasana tayi wajen bed din cos daga ganin yana yin ta zaka San something is wrong

"Babynmu!!!"tafada dakarfi SAKAMAKOn........



Vote,
Comment&
Share

💋💋wurarh💋💋


💝💝💝💝💝💝  
                       *ABAR SO*
                                    💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN by: NAFISAT  MA'ARUF  SHEHU*
                      *💋💋wurarh💋💋*

*Wattpad:Nafisatma'arufshehu*

🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

               🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 83-84

"Ok please babu ruwanki dazuwa da phone"Nadhira tafada

"Confirm"Hasana tabada amsa

"Miye kuke kullawa neh wai?"Abdul yatambaya

"Kai ina ruwanka,amebo kawai"Hasana tabashi amsa tareda murguda mai baki....

"Kanin mijina!!!" Nadhira takira shi.....

"Ke wai ni fah bangane bah haka kawai saiku dinga Kiran kanku da names"Hasana tayi interrupting

"Calm down my Hasy,i will gist you after you complete your mission"tafada hade da kashe mata ido

"There's something fishy between you guys" yafada yana girgiza Kai

"And it's none of your business"Hasana tafada

"Silly girl.."yafada

"It's okay guys,kanin mijina kadan sauke min ita agida mana"Nadhira tafada tana mai kashe mai ido

"Taab nikam zantafi dakaina,basaiya kaini bah"tafada tana tura baki

"No Hasana kije yakaiki, please do it for me"tafada

"Okay,for you besty"tafada

"Thanks dear,kaikuma nasan bazaka ki kaifa bah kodan yayanka"tafada

"Ke nifa kin ishe ni, tukunna mah waye yayanshi?"Hasana yatambaya tana mai zaro big  eyes nata

"Soboda shi Zan aura"ta bata amsa atakaice hade da kanne mata ido,dariya kurun Hasana tayi hade da daukan side bag dinta

"Ke kisameni amota,kuma kiyi sauri"yafada cikeda neman tsokana

" Baza'ayin bah"tafada tana murguda baki,kwafa yayi tareda ficewa itakuwa Nadhira dariya tadinga musu

"Dariya mah zaki min koh? shikenan natafi"tafada tareda ficewa wai tayi fushi,itakuma ganin tafice cikin jin haushi,yasata bin bayanta

"Haba besty kiyi hakuri mana, am so sorry"tafada tana mai kama kunne....

"It's okay dear,saikin jini"Hasana tafada

"Thanks dear and remember no mistake"

"Trust me"Hasana tafada daidai motan yafara tafiya kuma yayi daidai da fitowan mumy, mumy kuwa ganin mutum kamar yar India yasata gyara zaman medicated glass din eyes dinta,juyawa tayi daniyar komawa cikin gida ya hange mumy, karasawa tayi tareda gaishe ta

"Ashe kece,nadau bakuwa mukayi"Mumy tafada tana murmushi

"Ammafa Dana baya son masu Karin gashi fah cos naga har lashes kike karawa"mumy tayi adding,saiyanzu  tatina ashe ko dankawali babu akanta,wani irin kunya taji ya lullube ta,wanda tinda bata taba jin irin shi bah

"It's okay,ki gyara kinji"mumy tafada,gyada kanta tayi tareda shigewa while mumy tabita da kallo  tareda sa shakku acikin ranta gameda yarinyar

"Dole nasa abincika minke cos ba yadda dake bah"mumy tafada lokacin tana komawa cikin gida.

     Abangaren su Hasana kuwa yana zuwa daidai gidansu ta tsayar dashi,fita tazoyi ya danna lock din motan

"Malam yadai?"tafada frowning her face

"Hmm..... Shadayan ki zaki bani"yafada yana Sosa keyarshi

"Miye shadaya  kuma?ta tambayeshi looking so serious,ganin dagaske takeyi batasan abinda yake nufi yasa yayi dariya daidai lokacin da dabara tafado mai, jefa wayarshi yayi tagefen seat dinshi

"Ok barina tambaya miki matar yaya"yafada yana lalube

"Miye kake nema  ne wai?"tafada cikeda kosawa da zaman

"Wayata fah nake nema,oh gosh kardai na batareda"yafada kaman dagaske,haka suka dinga neman abinda bai bata bah

"Toh kiban aron wayarki nayi flashing din nawa"yayi requesting,batareda tayi musu bah tabashi wayarta cos itafa ta kosa taji miye shadaya,karbar yayi tareda dannawa nashi Kira kawai saiga waya na ringing agefen seat dinshi

"Oh ashe mah faduwa tayi"Hasana tafada,shikuwa dariyar dayake dannewa ne ya kusan kufcewa , daukar wayan yayi sannan yaduba screen din wayanshi, special numbern ta ne ya bayyana

"Miye wannan?"yatambaya tareda nuna mata screen din wayanshi

"Special number naneh"ta bashi amsa

"Toh ki kirga kigani"yafada yana tabe baki

"Toh miye amfanin kirgawa?"ta tambayeshi

"Just to prove something"yabata amsa,kirgawa tayi dukda tasan amount dinshi

"Shadaya neh"tabashi amsa

"Yauwa toh wannan shine shadayan danace kibani,kinga  yanzu basaina tambaya miki matar yaya bah"yafada hade da kanne mata ido daya,tsaki taja tareda fadin

"Budemin kofa nafita"murmushi mara sauti yayi cos  dariya tabashi yanda take ta  faman hada rai

"Ko baki fada bah daman zanbude  tinda motan banaki bane"yafada cikin son

Please Login or Register in order to submit comment