Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi magana tareda bude mata kofa

"Sai munyi waya"yafada daidai tafita daga motan,sanda yashige gida kafin yafadi......

     A week later......

Acikin sati dayan dasuka wuce abubuwa dayawa sun faru irin shakuwan da Amin da Nadhira sukayi dukda awaya neh, amma har Amin ya gayawa Nadhira sirrin azuciyar shi,itakuwa cemai tayi zatayi tunani akai......

    Ga kuma Abdul yayi nisa akogin son Hasana batareda yashirya bah ,gashi kullum saiya mata 100 missed calls amma bata taba dauka bah abin sosai yake mishi ciwo,harya kaiga zuwa gidansu,anan aka fada mai tayi tafiya,daganan yanemi ganin Babanta  sannan ya fadamai bukatunshi,Babanta kuwa cewa yayi idan yashirya yaturo iyayen shi,sosai Abdul yaji dadi  while dayan bangaren azuciyar shi kuwa cike yake da fargaban kallan masifan da zaisha Hasana  yakeyi.

Akwana nabiyu akaje tambaya mishi aurenta kuma anbayar,dayake tinda yatafi akayi bincike akansu kuma aka samu basuda wani aibu.

  Su Abba sunso abasu auren Nadhira ma aranar ,amma gudun magana yasa tace zataje tafada wa big Dady cos bazaiyiyu tayanke hukunci dakanta bah,kuma su Abba sunyi na'am da barin .

   Hasana kuwa gadan gadan tafara aikin da yakaita ,inda masu gidan kuma suka amince da ita ,duk movement din mutanen gidan babu na wanda ba tayi monitoring bah,atakaice dai aikinta yana tafiya smooth

Back to labari....

"Baby".....

"Na'am Abba"....

"Why not ki fito da dadynki yasha iska"Abba yafada wa Nadhira dayake yaje wajen Antynsu kuma ta bashi LABARINSU kuma har mumy yafada wa  kuma itama ta tausayi musu kuma tabada goyon bayan a aurawa Amin Nadhiran

"Gaskiya Kam baby yakamata kifito dashi"inji mumy dafada

"Toh"ta amsa cikeda jin dadi cos itama taso ace yana fitowa shan iska amma Kuma babu yanda zatayi....

  Shiga tayi tareda fitowa dashi akan wheelchair dinshi daidai bakin kofa ta tsayar dashi  tareda komawa cikin gida dan dauka ruwa,dadynsu kuwa sake hannunshi yayi daga kan handle din wheelchair din SAKAMAKOn gyangyadin dayafara,aikuwa nan  wheelchair yafara tafiya dakanshi,kuma daman gangare ne, wheelchair Kam Sai tafiya yakeyi abinshi,daidai kuma lokacin Nadhira tafito dauke da goran ruwa a hannunta,mamakine yakamata ganin bata ganshi bah, jefar da goran hannunta tayi SAKAMAKOn ihun da taji anyi,aguje tayi inda taji ihun

"Innalillahi.....


Vote
Comment&
Share

💋💋wurarh💋💋



💝💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN by: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
*💋💋wurarh💋💋*

*Wattpad: mhizzphydo

🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page 85-86

Barkanmu da sallah,Allah ya maimaita mana. Ameen

"Innalillahi"shine abinda su mumy da Abba ke furtawa sanda suka karasa inda dadynsu yafadi

"Dadynmu kabude idonka babynku ce,wayyo Allah kuyi wani abu mana ga kanshi yafashe "haka tadinga magana ita kadai lokacin da ta isa awajenshi,Abba kuwa phone yadauka yakira doctor,kamin yakira Amin akan yayi gaggawan dawowa gida, baima jira jin abinda Amin ke Shirin fada bah ya yanke wayan.

Bada dadewa bah doctor ya iso ko gama parking baigama yi bah Keke napep yashigo da Amin cos daman alokacin da aka kirashi yana cikin Keke napep din dasauri yakarasa wajen, Abba yasha mamakin ganinshi amma yanzu ba lokacin magana bane

"Akawo ruwa" shine abinda doctor yace,dasauri mumy tadauko bottle water, yayyafa mai akayi inda shikuma ya sauke nauyayiyar ajiyar zuciya

"Yaya kataimake ni kabarni,karka cutar da families dina yanda kake ikrarin cewa,duk abinda kakeso Zan baka"Shine sambatun da yakeyi ,dasuka ga sambatun bamai karewa bane yasa su danna mai Allura,nan da nan bacci yakwashe shi.

Carpet aka shimfida daidai wajen da yake sannan suka mirgina shi. Alokacin kuma Baby na rungume ajikin mumy tana sharban kuka.

"Abbana garin yaya akan tafaru??" Amin ya tambaya yana mai miye da kallonshi wajen Abba, muryan dataji ne yasata dago kanta domin ganin mai magana amma Kuma bayanshi tagani, sake sunkuryar da kanta tayi yayinda Abba yabashi rahoton abinda yafaru......

Sallaman da akayi neh yasa su miyar da dubansu inda suka jiyo sallaman

"Antynmu!!!" Tafada cikin kuka tareda barin jikin mumy, dagudu takarasa wajen Antynsu tareda rungumeta ta kuka, itama Antyn kuka takeyi sosai.....

Mamaki ne yakama Amin dalilin ganin wanda baiyi expecting ba

"Miye sukeyi anan??"Amin yatambaya

"Kasansu neh??" Mumy ta tambayeshi batareda ta amsa mishi bah

" Erh mana ABAR SO na da Antynsu" yabawa mumy amsa

"Allahu Akbar, daman itace ABAR SO din?? ai itace mukace zamu aura maka"mumy tafada mai

"Tsuntsu daga sama gashasshe"yafada azuciyar shi amma afili cewa yayi

" Amma kince bazan kara aure bah??"

" Yanzu ba lokacin magana bane" tabashi amsa

Some hours later...

Ahankali yake bude idonshi ,dishi dishi yafara gani kafin idon yabudu tas... Nadhira neh tafara lura dashi ,aikuwa dasauri suka matsa wajenshi

" Dadynmu!!!" Tafada cikeda jindadi, muryan wanda yajine yasashi runtsa idonshi abubuwan da suka faru yafara dawowa mai.....

" Nakashe duka iyalanka , kaida su kuma yanxu Sai amafarki kokuma a lahira" yayanshi yafada

" Innalillahi wa'inna illahir rajioun....." Dadynsu yafada dakarfi hade da bude idanunshi,still bata bace ba juyar da kanshi yayi wajensu Abba yana sake fadin

" Ya kashe su, he killed those innocent souls , he killed all of my happiness , why didn't he killed me too?? He knows that I lived for them, they are my second half.....

"Dadynmu!!!" Nadhira ta Katse shi cikin cracking voice, dasauri ya juya jin ankira shi tareda taba shi

" DanAllah ku mintsi ne ni ko zantashi da mafarkin danake yi " yafada yana me kallon kwayar idonta

"Dadynsu!!! Antyn takira shi tana me taba fuskarshi ( cos haka take kiranshi)

Ahankali yake juya fuskanshi gabadaya awajenta sannan ya sauke ajiyar zuciya mai karfin

" Daman nasan yayana bazai iya kashe min iyali bah , nasan wasa yakeyi amma those jokes where so expensive, amaryata ina habibity na take sannan kuma ina Nafhira dakuma cikin jikinki??" Yafada yana mai taba cikin ta

" Dadynmu!!!" Nadhira takira shi , miyarda duban shi yayi wajen ta

" Babynmu!!! Ina yar uwarki dakuma Mommanku ??" Yatambaye ta tareda riko hannunta

" That monster killed them, he gave them the worst death ever" ba bata lokaci ta zayyano mishi abinda yamusu saidai abu daya bata fada mishi ba shine alluran da aka mata

" Ya Salam!!!" Dadynsu yafada hawaye na zuba daga idonshi likewise kowa na wajen

" How could he be so cruel?? Hmmm Nayafe mishi duniya da lahira!!!" Arazane Nadhira tadago ga eyes nata sun gama rinewa tsantsan tashin hankali, su Abba kuwa mamaki ne Yakama su

" Bangane ka yafe mishi bah??" Abba yatambaya

" In ban yafe mishi bah kuma miye zanyi mishi?? Ku Tina fah sakkayya a wajen Allah yake,kuma Allah yanason masu yafiya muma fah muna mawa Allah laifi kuma yana yafe mana nikuma asuwaye da bazan yafe wa wanda ya mana laifi bah?karku manta fah ciki daya muka fito dashi dan'uwa na ne najini in shi ya kini wlhy ni haryanzu inason shi , tinkan ayi daran akayi kwandi, kunga babu abinda Zan iyayi akai" Dadynsu yafada cikeda da kwarin gwiwa

" Tabbas haka yake, Allah ya yafe mana gabadaya" Abba yafada

"Ameen" aka amsa in chorus amma banda Nadhira cos ance na ciki na ciki

" Nagode sosai Allah yabiya ku" dadynsu yafada wa su Abba cikin hawaye

" Babu komai ai yiwa kaine" Abba yafada

" Zaku iya dawowa nan da zama tinda akwai parts dayawa cos nasan zai iya zamowa matsala idan yaganka da rai" Abba yafada

" Gaskiya neh wannan shawaran yayi" mumy tayi adding

" Bazamu daina yimuku godiya bah" Antynsu tafada

" Ai babu komai yar uwa mugode wa Allah " mumy tafada da murmushi asaman fuskarta ,while Nadhira tana zaune kaman an dasata ga tunani kala kala kai kawo sukeyi azuciyar ta shikuwa Amin banda nazarinta babu abinda yakeyi ga wani dadin da yaji Yana huda kahon azuciyar shi.

" Ina Saleem din??" Dadynsu yatambaya

"Yana school amma sun kusa tashi" Antynsu tabashi amsa

"Baby, kishirya muje dauko shi cos bansan makarantan bah" Amin yafada cikin nutsuwa yana mai kallon Nadhira

"Yauwa ka kyauta "inji Antynsu dafada , murmushi kawai dadynsu yayi yana mai raya wani abu azuciyar shi gameda Amin din.

Itakuwa tashi tayi cikin sanyin jiki sannan tawuce cikin gida while kowa ya bita da kallo....

"Ina... Taab wlhy bazanyi hakuri bah bayan Alkawarin dana dauka wa Yar uwata..." Haka Nadhira tadinga magana kaman wata sabuwar Kamu , toilet tashiga tasan watsa ruwa , tana fitowa wayar ta yafara ringing karasawa tayi tadauka , tana ganin sunanda ya bayyana acikin screen din tayi wata sanyayar murmushi sannan tayi receiving

"Am done besty" Hasana tafada daga dayan bangaren

" You're so sweet dear, nagode sosai"

"Mention not besty, yaushe Zan shigo??" Hasana ta tambaya

"No Zan shigo and kuma dadynmu yafarka" tafada tana mai murmushi

"Wow Alhmdllh, naji dadi wlhy" Hasana tafada har anajin sautin dariyar ta

" Kuma yace shi ya yafe shiyasa banason muyi maganan awajen mu cos nasan maybe Antynmu tayi hearing conservation dinmu and I won't want that to happen" tafada cikin sanyin murya

" Ayyerh amma why not mubari tinda yace ya yafe??" Hasana ta tambaya

"I can't let it go wlhy" itama tafada

"It's okay, yanxu yaushe zakizo??

"Inaga zuwa da yamma zanzo kokuma gobe "

"Okay Allah yakaimu"

"Ameen" tafada sannan tayi dropping, shap shap tashirya cikin wata armless short ready-made white gown as usual cos tafi ganewa da irinsu, agaban mirror tatsaya kafin taja tsaki sannan tabude wardrobe tadauko black American jacket mara nauyi tadaura akai, kamar kullum ta shafa Kohl , sannan tadauki nude lipstick tashafa wanda ba karamin kyau ya mata bah, katuwar black khimar ta dauko sannan ta sanya shi, flat black cover shoe tadauko sannan tafita haryanzu suna nan ainda tabarsu

" Masha Allah" Kalmar dayafurta neh yasa dukkansu suka juyawa saitin inda yake kallo, dukkansu sakin baki sukayi suna kallonta kaman sunga sabuwar hallita cos bakinta bakaramin karawa fuskanta kyau yayi bah

"Sai mun dawo" tafada batareda ta Lura da kallon da suke mata bah,tashi yayi Shima yamusu sai sun dawo

" Sunshine!!!" Yakira sunan ta bayan yatada mota

" Moonlight" itama tafada

" Ya akayi kina gidanmu kuma bamu taba haduwa bah??"

"Nima dai bansanibah"

"Miracle"yafada underneath his breath

"Indeed" tayi adding, daga nan kuma babu wanda yasake yin magana acikin su har suka isa makarantan su Saleem din

" Why are mute??" Yatambaye ta

" Kaima haka" tabashi amsa

" Daman kana da aure shine baka taba fadamin bah??" Tafada cikin sanyin murya

" Am so sorry , bana son Kiji babu dadi ne shiyasa banfada miki bah" yabata amsa

" But At least you should have told me koda zanji babu dadi, akan miye zanji babu dadi don kayi aure ?? You need it shiyasa kayi auren and I can't question you for that" tafada hawaye nasintiri a idonta cos ita kadai tasan irin zafin da zuciyarta yakeyi

"Stop crying sunshine am really sorry for keeping the truth away from you ki gafarce ni" yafada tareda rungumo ta , dukan shi tafara yi at the same time tana tureshi daga jikinta, ahankali yashiga Jan jikinshi daga nata cos yasan kishi ne kawai yake cinta, tana ganin yasake ta ta rungumeshi gam gam kaman za'a kwace mata shi , ajiyar zuciya yasauke sannan ya saka hannunshi tabayanta yana shafawa a hankali daga bisani kuma suka breaking hug din

" Kalli yanda kikayi zufa" yana magana yana mai cire mata khimar dinta

" Kicire khimar din kisha iska, kin wani zumbula khimar kaman wata MATAR MALAM " yafada daidai yagama cire khimar din , dariya kawai tayi shikuma yajefa khimar din back seat

"Masha Allah"shine abinda yakefadi azuciyar shi

"An tashia su " yatsinkayo muryar ta

"Muje toh" shine abinda yafada, sauka sukayi daga motar suka karasa cikin makarantan, Yan Maza da Matan makarantan Sai kallonsu sukeyi barin ma Nadhira, ga fresh legs dinta awaje Sai shining sukeyi donma Allah yasota tadaura dankawali da kallon yafi haka

"Babynmu!!!" Shine abinda Saleem yafada da karfi lokacin dayayi harba da fuskanta dagudu yaje ya rungumeta

" You look so Gorgeous sis" yafada yana pecking lips and cheeks dinta

"Thank you bro, I miss you like crazy dear" tafada mai

" Same here baby" Shima yafada, gyaran muryan da Amin yayi ne yasa su dakatawa

"It's like kinmanta bake kadai Kika Zo bah" Amin yafada

" Lahh... Ai duk lokacin da muka hadu mantawa dakowa mukayi"Saleem yabashi amsa

"Like really??" Amin yafada yana mai zaro ido alaman mamaki

"Of course yes" Saleem yabashi amsa again harda mai gwalo, dariya dukkansu suka yi sannan suka hantaya wajen mota. Suna shiga wayar Nadhira yafara ringing dagawa tayi hade da yin sallama

"Babynmu , kubiye gidan su Hasana kifadawa umminsu dadynku yatashi" Antynsu tafada

"Okay" tafada hade da hanging up din wayan

"Muje anguwanmu Zan shiga gidansu Hasana " tafada wa Amin

"Ok dear"

Suna Isa anguwansu ido yadawo Kan dallaliyar motarsu, kowa soyake yaga wanda yake cikin mota cos tinted neh. White legs dinta ne yafara musu sallama

"Bari na maka iso zuwa ciki " tafada mai hade da fita daga motan , everybody was like wow cos bakaramin tafiyada imanin su tayi bah ,Sai asannan ma sukaga face nata, budewa Salim kofa tayi Shima yafito

"Salim Antynmu bata nan , so gidansu Hasana zamuuje kafinnan zankaika wajen Antynmu kuma akwai surprise dinda nakeson na nuna maka " tafada tana fadada murmushi face dinta

" I can't wait wlhy,muyi sauri cos am nervous" yafada hade da kama hannunta ,rufe marfin motan tayi sannan suka bar wajen. Suna shiga tagaisar da ummi hade da fada mata aikin anty sannan tamawa Amin iso zuwa main palour while Salim yafara cin abinci itakuma tashige dakin Hasana batareda bata lokaci ba Hasana tafada mata anzo neman aurenta wa Abdul ,sosai Nadhira tamata murna , kafinnan suka gangaro kan plan nasu....

"Muje zanga dadynku din yau"Hasana tafada

"Yauwa da kin kyauta" fita sukayi daga dakin ,Hasana tamawa ummi sallama kafin suka fito cos basu same su Amin a palour bah. Awaje suka hangosu zaune akan mota

"Daman tare kuka zo??" Hasana ta tambaya

"Oops... Wlhy namanta ban fada miki bah" tabata amsa hade da fada mata ashe a gidansu take bata sani bah kuma shine yayan Abdul. Suna Isa wajen Hasana tagaishe shi cikeda ladabi, kafin suka shiga cikin mota daganan kuma Sai gida.

Yadawo kenan daga office ya hango motar yayanshi na shigowa, gyara tsayuwa yayi ajikin motan yana mai jiran fitowanshi , wacce yagani tafito daga cikin motan yasashi hade rai kaman bai taba dariya bah.

Wanda tagani ne yasata fitowa daga motan dasauri cikeda fara'a, amma gani irin disgusting look dinda yake bata yasata shan jinin jikinta, ahankali yake takawa har ya isa gurin ta alokacin kuma kuwa ya fito daga cikin motan Salim kan dagudu yayi inda yaga Antyn tashiga cos kwata kwata bata Lura dasu bah

" Nagode sosai Allah yasaka" yafada yana mai kawar da kanshi daga gareta...

"Miye faru ne kanin mijina??" Nadhira ta tambaye shi

" Tsantsan ranin hankali da rashin sanin darajar dan Adam harni zanmawa wannan 100 missed calls amma tarasa miye zatamin Sai........

*Rashin jina dawuri dakukayi yasamu nasaba ne da rashin yin comment, agaskiya banjin dadin wannan abun haba!! Ace kuna son abu amma bazakuyi comment ba,, haka akeyi neh?? To yanzu in ba'ayi comment bah toh babu posting har sainaga comments dinku. In akwai wanda nabatawa acikin ku toh yamin afuwa.....

Comment,
Vote&
Share

💋💋Wurarh💋💋



💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Page 87-88*

"Tsantsan ranin hankali da rashin sanin darajar dan Adam harni zanmawa wannan 100 missed calls amma tarasa miye zatamin Sai flashing 1 tak" yafara yana mai nuna Hasana da bacin rai kwance asamar fuskarshi

"Wlhy bangani bane shiyasa ban dauka bah kuma lokacin dana kiraka network ne yasa ya katse amma ba dagangan naki dauka bah" Hasana tafada cikin sanyin murya, har lokacin bai sake look din face dinshi bah

" Dallah Malama kirufe mana baki don kinga inasonki ne shiyasa zaki walakanta ni ba damuwa ai naga bake kadai ce mace bah kuma aurenkin ma na fa..."

"What da hell!!!" Ta katse shi

"Nace maka ban gani bane ai dana gani dana dauka and ka tsaya kana fadamin magana, and kuma inka fasa aurena din so fucking what,ko cemaka nayi na rasa mashinshine wlhy ko ranar aurena kace kafasa I can assure that bazan rasa wanda zai aureni aranan bah, ina ma maka magana cikin sanyi Sai botsarewa kake ai......"

"Calm down guys" Nadhira ta Katse ta, shikuwa ido yazuba wa Hasana cos azatonshi zata bashi hakuri ne komai yawuce amma Sai yaga sabanin hakan, shikam Amin banda mamaki babu abinda yakeyi

"Wato har Abdul yasaba dasu haka harda cewan zai fasa aurenta, lallai abin nasu azimun neh" ya raya azuciyar shi, itakam Hasana tuni hawaye yafara sauka a idonta, dagudu tabar wajen tana mai fashewa da kuka duk Sai jikinsu yayi sanyi

"Hey bestie!!!" Nadhira takira ta tareda binta da gudu zuwa cikin gidan, taba kafadar Abdul Amin yataba tareda sakar mishi da murmushi shikuwa da yake yamiyar mai, cikin part dinsu Abdul zaishiga Amin ya dakatar dashi yana mai janshi zuwa nasu part din...

"They need some space" shine abinda Amin yafada bayan sun zauna

"You guys love each other fah!!!, Yaushe kuka hadu" Amin yasake fada,nan kuwa Abdul ya zayyana mishi haduwarsu

" It's prayer time, in munyi sallah muje ka gaisar da Dadyn Nadhira"

"Ya dawo hayyacin shine?" Yafada cikin mamaki

"Wlhy you need to meet that great man with the big heart" yafada yana murmushi, Shima dai murmushi yayi batareda yasan inda maganar ya dosa bah.....

"Besty!!!kukan kuma na miye??" Nadhira ta tambaye ta

" Miyesa zai karyata ni ?? Wlhy bakarya nake mishi bah" Tafada cikin sanyi murya

"Do you love him??"

" Yanzu kuma dayace yafasa aurena miye zanyi?" Tafada cikeda damuwa

" Ana so ana kaiwa kasuwa ,wayace miki dagaske yakeyi?"

" Eh mana he looks so serious"dariya Nadhira tasake hade da tashi daga zaunen da take, cire dankawali kanta tayi ta'ajiye shi gefe

" I'm very sure he was pulling your legs and nothing more" tafada tana shigewa bedroom dinsu cos bataji muryan su anty bah

" I pray so" shine abinda Hasana tafada cikeda farin ciki

"Ina Dadyn yake ??" Hasana ta tambaya cikin daga murya ,chan saiga Nadhira tafito

"Shiga kiyi Alwala muyi sallah"

"Am pointing red fah" Hasana tafada

"Ohk" tana idar da sallah tacire zanin da ta daura

"Muje"tafada wa Hasanan dake game awayarta....

"Babynmu!!!" Taji ankirata kuma tasan bazai wuce Salim bah

"Naga surprise din da kikace zaki nuna min"yafada yana murmushi

"Oops!!!"tafada tana shafa gashin kanta ga ta yamutsa fuskanta, dariya yake mata harda gwalo cos ba haka taso bah

"Catch me if you can baby" yafada yana girgiza mata bumbum dinshi tareda guduwa aiko cikin zafin nama tafara binshi dagudu ,Sai tazo dab dashi zai sulale , Hasana kuwa Sai dariya takeyi harda zama akan daya daga cikin chairs din wajen,nan kuwa ashe su Amin mah suna kallonsu,itakuwa ta dage Sai binshi take yi cos girgiza bum bum din dayayi neh ya tunzirata ga gashin ta Sai tsale yakeyi ta bayanta harta mai gadi kallon baturiya yakeyi sbd alokacin tacire jacket dinta hango maigadi da yake kallonta Amin yayi ai kuwa wani abu yasoki zuciyar shi...

Tsawan da aka dakamata yasasu tsayawa cak nan da nan kuma hawaye yafara sintiri afuskarta...

"Ke jakar ina ce??" Yatambaye ta cikeda bacin rai daidai lokacin da ya isa wajenta

"Baki da hankali ne?" Yasake jefo mata tambaya, juyawa takeyi don tabbatar da muryan wanda yake zaginta ai kuwa taga babu kowa Sai masoyinta

"Ke!!!" Yakara daka mata tsawa, wani kuka mai tsinka zuciyar mai sauraro tasake cos zagin yashigeta amma ainihin bazallan zagin yasata kuka bah,magana take sonyi amma kuka ya hanata nan da nan jikinshi yayi sanyi.

Kukan da Salim yashiga dashi ne yafito dasu daga cikin gida harda Dady acikin wheel chair dinshi cos suna ta tambayanshi amma bai amsa bah Sai nuna musu waje dayake yi azatonsu wani mumunar abu yafaru shiyasa suka garzayo,abinda suka ganin ne yasasu yin turus, ido Hudu dasukayi da Antynsu neh yasata ruguwa wajenta

"Kya uwah?? Anty ta tambaye ta hade da bin jikinta da kallo

"Tell him abinda banaso" tafada tana nuna shi da yatsa

"Nace miki miye faru?" Anty tafada hade da rike ta cos she's so scared kwata kwata bata son ganin abinda zai bata musu rai balle azo ga zubar hawayen su

"Tsawa yamin Antynmu, kifada mai tinda nake arayuwata ba'a taba min tsawa bah , kifada mai natsani tsawa balle wanda yake yinta ,Zan iya mai rashin mutunci ba bu ruwana da inasonshi ajiye soyayyar zanyi agefe na mishi rashin mutunci which bazaiji dadin shi bah kuma Allah yagani that will be the least thing din da zanyi, gwanda yakiyaye cos bana barin bashi kema kinsani" tafada hade da barin wajen

"Babynmu kiyi hakuri bazan kara bah" Salim yafada ganin wajenshi ta nufo, amma still bata daina nufanshi bah while shikuma naja da baya,hawayen da tagani a idonshi yasata tsayawa cak,aiko yana ganin ta tsaya ya ruga ya rungumeta

"I hate that Salimu nah" tafada hade da goge mishi hawaye

"Am so sorry Babynmu I don't that it will hurt you"

"Don't do that again okay?" Gyada kanshi yayi

"Good boy" tafada hade da tashi ta wuce cikin part dinsu, banda na mujiya ba abinda suke dinsu dashi while kowa na mamakin abinda yafaru atsakanin su, Hasana ne kawai tasan abinda yafaru

"Allah sarki" shine abinda tafada azuciyar ta ,shi kam Amin gabadaya ya damu da cos shi baisan bata fushi bah

"AL-AMIN!!"Dadyn su yakira shi bayan sun gama gaisawa da Hasana harma tashige abinta cos kowa yabar wajen Dady ne yace abarshi cos ya Lura da yanayin Amin din. Karasowa cikin sanyin jiki

"Ya akayi baka san abinda bataso bah??" Cikin sanyin murya yake fadin

"Bata taba fadamin bah" murmusa Dadyn yayi

"Tin yanxu jikinka yayi sanyi??, Amma kasan tanada riko??"

"A'a Dady"

"Yadda ta tafinnan yatabbatar bazata sake maka magana ba Sai after a month" arazane yadago yana kallon Dady

" DanAllah Dady katayani rokonta kozatayi hakuri, in tadaina min magana bansan yazanyi da arayuwa na bah" yafada cikin rawar murya

"Ai haka halinta yake, ko kasan yar'uwarta?? Dady yatambaya

" Kaga duk son da take mawa yar'uwarta toh koya suka samu sabani toh ta daina mata magana kenan!!, Soboda haka just let her be for now cos duk abinda zaka fadamata bazai yi tasiri akanta bah soboda bata barin bashi"

"Au daman abinda take nufi da bata barin bashi kenan??"

"Kwarai dagaske"

"Hmmm"

"Ka kwantar da hankalin ka soboda kasan ance mai Hali bai fasa halinshi"

"Ok Dady amma tasani wannan hukunci nata yayi tsauri dayawa"dariya kurun Dady yayi.......

"Besty!!"

"Miye"

"Akan kawai yamiki tsawa kikayi wannan kukan ko kuma there's more to it??"

"Idan natina da babu hanyan dazanbi inbar gidan nan zuciyata kuna yakeyi sosai amma Kuma kinsan abinda yayi is not fair,miye na mishi daxaimin irin wannan tsawa? " Ta tambaya cikin sanyin murya

"Nima gaskiya abinda ban gano ba kenan"

"It's okay"

"Does that means kin hakura??"

"I don't know cos nasan in yayi gigin min magana I may disgrace him soboda har yanxu inajin karar tsawan dayamin"

"Allah yakawo mana da sauki"

"Ameen"

"Barina mawa Antynmu sallama"tafada hade ficewa....

"Miye zai mata dazaice tazo??"shine abinda Anty ke tambayan Dady cikin sanyin murya ga idonta harya kawo ruwa...

"Toh miye don ya bukaci tazo?? Shima fah amatsayin uba yake awajenta karki manta" Dady yafada

"Yadda Nadhira bata kaunar shi anya zataje kuwa kasanta da taurin kai" antyn tafada tana share hawayen ta

"Why not aji ta bakinta tukunna"mumy tafada

"Hakane kuma fah" Abba yafada,ganin Hasana yasa Dady aikanta Kiran Nadhira,cikeda sanyin jiki takirawo Nadhira....

Ganin su atsatsaye yasata yin turus

"Karaso baby" jin muryar Antyn yasata karasawa wajen ta dasauri , face dinta ta rike

"Miye sameki Antynmu??" Ta tambaye ta cikeda da damuwa soboda itama bakaramin so takewa antyn nasu bah

"Big Dady neh yace yakamata kizo" wani irin dadi taji tindaga tsakiyar kanta amma Sai ta daura fuska tareda fadin maganar dayasa kowa yin tsit awajen....

*Naji wasu nacewa miyesa

Please Login or Register in order to submit comment