Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da Aunty Farah. Yana basu labarin rikicin da akeyi a gidan suna kwasar dariya. Sai dai ko sau ɗaya Zinneerah bata saka baki a hirar tasuba. Murmushi kawai takeyi tana dai saurarensu da kallon hanya, zuciyarta na yaba ƙyawun ƙasar burtaniya da tsarinta. Tare da godiya ga UBANGIJI da ya bata damar ƙetare ƙasarta zuwa wata ƙasa batare da ko a mafarkinta hakan ya taɓa zuwa mata a cikin ranta ba.
        Sai da suka iso inda ya dace ta kawo numfashi, waje ne daya samu tsararrun gine-gine da burgewa ga mai kallo. Babu wani hayaniya a wajen dan saima ka ɗauka ba gidaje baneba wata ma'aikatace. Su kansu sai bayan shigarsu ainahin cikin estate ɗin suka fahimci nannefa inda gidan Yayan nasu yake kenan. Sun haɗu da mutane ɗai-ɗai dake kai kawo, kamar masu fita da masu shigowa. Duk da kasancewar ginin estate ɗin a dunƙule yake waje ɗaya idan ka shiga baka da alaƙa dana kowanne, abinda kawai zakai nufar hanyar da zata kaika ainahin number naka building ɗin. Abinda kuma zai birgeka a rayuwar wajen babu ruwan wani da wani. Iyakarka da kowa hello hii idan an gamu.
        Zinneerah daketa tunani a ranta taketa ayyana dolene turawannan su dinga ganinmu a banza. Dan duk wani jin daɗin duniya tamkar an tattarashine garesu. Basusan wani tashin hankalin rayuwaba sukam sam. A African kashe-kashen nan kawai ya ishi bawa da yunwa. Mu baga neman lahirarba duniyar da mukeso kuma kullum cikin wahal damu take. Gamu nan dai babu fasali ko wasu abubuwan birgewa duk mun fita a hayyacinmu.....
    Nannauyan numfashi ta sauke saboda taɓatan da Bahijja tayi, “Haba Baby ina kika tafi haka ne?”.
     Ɗan murmushi Zinneerah tayi da duƙar da kanta saboda kallon da Khalipha ya kafeta da shi. A hankali tajawo trolly ɗinta ta fito a cikin taxi ɗin tana gyara bag ɗinta. Jamal sarkin tsokana yace, “Ashe ni ƙauyancina ma kaɗanne ga wadda ta fini”.
     Harara ta zuba masa da kai masa duka ya goce yana dariya. Khalipha ya girgiza kansa yana nufar ƙofar da zata sadasu da gidan na yayansu yana faɗin, “Uhm kudai tuna a ina kuke yanzun, kokuma ku koma Nigeria ba'a yanda kuka zo Burtaniya ba”.
        Dukansu sun fahimci inda zancen nasa ya dosa. Dan haka duk sukai ƙaramar dariya kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
         Tunda suka shigo man kan kowa ya tsiyaye tas suka koma santin zuciya, sunaji a ransu dolene Aunty Farah da take hura musu hanci ashe tasan abinda ta taka. A ɗan corridor ɗin kafin ka shiga ainahin falon duk suka cire takalmansu suka saka cikin drawer dake a wajen alamar ba'a buƙatar ganinsu a waje. Sabbin Slippers na zaman gida Khalipha ya ciro daga cikin drawer ɗin ya miƙa musu. Kowa cira yay ya saka sannan suka shigo ainahin falon daya tsaru harya gaji. Sai ka rantse ma ba'a amfani dashi tsabar yanda yake fes. Tozali da Hajiya iya dake hakimce zaune ta ƙara ƙyau ya mantar dasu a ina suke da kuma santin. Tuni suka yadda bags suka nufeda da gudu cike da ihun farin ciki duk suka ɗaneta.
    Itama dai cike da farin cikin ta tarbesu tana dariya dajin ƙaunar ƴan jikokin nata da kewarsu.

        Cikin ɓacin rai Farah ta fito daga wani lungu danjin hayaniya na neman halaka mata kunnuwa, sanye take cikin wando dogo da riga da sukai mata ƙyau ainun, taku take cike da isa da ƙasaita fuska a yatsine. Taja ta tsaya turus tana dubansu alamar batama san da zuwansuba, dan sosai mamakin ganin nasu ke bayyana mata kan fuska ƙuru-ƙuru. Gashi kuma babu damar magana saboda hajiya iya. Sai dai wani kallon tsantsar takaici takema Khalipha da shima kai tsaye ita ɗin yake duba.
     Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta janye idanunta daga kansa ta maida kansu Meenal da sai a yanzu nasu idanun suka ganta. Duk da sunsan halinta na wulaƙanci sai sukai ƙoƙarin nuna murnar ganinta suna gaisheta cike da girmamawa kodan darajar wanda ya ajiyeta a gidan. A yatsine ta amsa musu ɓacin ranta na kasa ɓoyuwa, ta kafe Zinneerah da ko kallon inda take bataiba balle gaisheta da ido.
Zinneerah da batasan tanaiba gaba ɗayama hankalinta nakan Hajiya iya batasan da zuwanta wajenba. Lura da kallon da Farah kema Zinneerah ɗinne yasa Khalipha kiran sunanta.
    Ta juyo fuskarta ɗauke da murmushin da takema Hajiya iya ta dubesa. batare da yayi maganaba ya nuna mata Farah.
     Da iya gaskiyarta tace, “Ayyah Aunty kiyi haƙuri bansan kin fito bane. Mun sameku lafiya? Yaya jikin Granny”.
      (Buhun bura uban nan kayyasa) Farah ta ambata a zuciyarta tana kafe Zinneerah da wani shegen kallo, dan babu abinda ta hango a zancenta sai tsantsar rainin wayo a gareta. Batare data amsama Zinneerah ɗimba tabar wajen cike da takunta na ƙasaita da izza kai kace wata sarauniya ce.
     Gaba ɗayansu da kallo suka bita. Hajiya iya ta girgiza kanta kawai tana mai nema mata shiriyar UBANGIJI a ranta. Yayinda su Jamal duk jikinsu yayi sanyi. Zinneerah kam ko'a jikinta, dan itako a masu mugun hali taga waɗanda suka taka Farah suka shanye mizaisa na Farah ya dameta. A bazata dariya ta siɓicema Khalipha ya kauda kansa gefe yanayi. Dan haka kawai ta bashi dariyar. Ita dake takaicin zamansa shi kaɗai ga wasu huɗun nan an kuma kwaso mata bayan Hajiya Iya. Sai dai kuma shi duk zatonsa tasan da zuwan nasune tun farko, amma a yanda tayi yanzu kam ya tabbatar Yayansu ya ɓallo ruwa yau.
       Hajiya iya ce tai masa daƙƙuwa, ya ɗauke kansa yana haɗiye dariyar badan yaso ba. Itama maida hankalinta ta sakeyi gasu Bahijja dake gaisheta da tambayar lafiyarta, itama tana tambayarsu mutanen gida da hanya. 
       Sai da Khalipha yace, “Ashe ƙaryar gajiya kukeyi daman”.
        “Yah Khalipha ganin Granny yasa gajiyarma ta gudu ALLAH”. Bahijja ta faɗa tana dariya. Murmushi yayi da kallon Granny dake magana da Zinneerah fuskarta a washe itama alamar tana cikin farin ciki yau fiye da kullum, sai yaji daɗi a ransa. Koba komai sa huta da mitarta na a maidata gida ita ta gaji da zaman kurkuku.
      “Assalamu alaikum”.
   Suka tsinkayi muryar Yayansu dake ƙoƙarin shigowa a bazata. A take duk sukai tsit da maida dubansu ga ƙofar. Khalipha ya miƙe ya nufesa ganinsa ɗauke da ledoji a hannu. Suma ɗin duk tsaye suka miƙe domin bashi girmamawa. Ledojin ya miƙama Khaliphan yana faɗin, “Thanks besty” ba tare dasu sunji miya faɗa ɗinba. Sai motsawar laɓɓansa kawai suka hanga.
      Cikin haɗa baki sukace “Barka da dawowa yayanmu;
      Sai yanzune ya kallesu fuskarsa da ɗan sakewa amma ba murmushi yakeba. Ya zame rigar sanyin saman suit ɗinsa yana hanging ɗinta a hanger ɗin dake gefensa, sannan ya ƙaraso cikin falon. Gaba ɗayansu gani sukai ya ƙara musu ƙyau da cikar haiba a idanu, kamar yanda Hajiya Iya da Yah Khalipha suka ƙara musu. Sai da yakai zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan yay magana.
“Kun iso kenan?”.
     Nanma a tare sukace, “Eh Yayanmu”.
Batare daya kalli kowansuba ya jinjina kansa yana musu nuni dasu zauna. Babu musu suka zauna suna gaisheshi da tambayar jikin Granny.
       “Ta warke ai, tunda gashi tana mana boren sai kunzo”.
      Duk da ba cikin raha yay maganarba sai da sukai ƴan ƙananun dariya suna gumtse bakuna. banda Zinneerah da tun shigowarsa kanta ke a ƙasa murmushi yanzunma kawai tayi.
    Granny dake hararsa tace, “Ai ni ba irin wasu bane da basa son mutane. Na saba jina cikin hayaniya da karaɗin ƴan jikokina ina jin daɗi”.
     Karan farko ya saki lallausan murmushi yana miƙewa da ɗan taɓe baki, duban Khalipha daya kai ledojin abincin kitchen ya dawo yayi. “Besty ina zuwa”. Ya faɗa yana nufar hanyar da Farah ta fito ɗazun.
       “A fito lafiya Yayanmu” Khalipha ya faɗa yana wata shaƙiyyar dariyar tsokana ƙasa-ƙasa da kaiwa zaune. Hajiya Iya data fahimci mi yakema dariyar tace, “Halan zargina ya zama gaskiya akan ƴar tutsun tasa? Tunda yanzu dai ba lokacin dawowarsa gida bane ba”.
        “Ai da alama itace tai kiransa a waya ko kuma ta kira Mammah ita kuma ta kirashi, dan a yanda ta nuna mamakin ganin su Jamal na tabbata bai sanar mata zuwan nasuba. Kinsan wannan jikan naki shine dai-dai dasu ai, ya manna musu rashin m ya noƙe da barinsu suyita masifa”. Khalipha ya bata amsa magana ƙasa-ƙasa kamar wani munafiki yana ɗan dariyar ƙeta.
       Dariya Hajiya iya tayi itama, “Kaɗanma ta gani indai nice Amina, ita Hindatun idan ta isa tazo gidan mana ta sameni ja'ira kawai. Nima nan saina saitasu a layi da ƙyau ai kafin nabar wannan garin da ba daɗin zamane da shiba”.
      Sudai su Zinneerah da ba sanin ina zancen ya dosaba saurarensu kawai sukeyi, ita babban burintama azo a basu masauki ta kwanta dan kanta ciwo yake mata.
       Shiko Khalipha dariyarsa ya cigaba da sha dan show ɗin na Granny na birgesa. Sosai a zaman nan nata take ƙara cusama Yayansu son ƴan uwansa a ransa da sanin muhimmancin su da girman zuminci. Shiko da alama yana haddace karatunta tsaf kuma yana aiki dashi. Dan rana ɗaya babu zato ya sanar masa ya kira cikinsu Haneef akan tahowarsu Meenal nan ɗin. Bashi ba hatta Granny tayi mamaki dan duk tsogumin da take masa nason zuwan su Zinneerah ɗin batai zaton zai saka suzo ɗinba. Aiko ranar yasha addu'a a wajenta da albarka.
    To yanzu dai gasu sunzo, shi dai yasan akwai ƙura akan wannan zuwa nasu gidan, musamman daya kasance uwargida gimbiya Farah batasan da maganar zuwan ba, amma bara su zuba ido suga yanda wasan zai kasance dai, tunda shima yayan nasu ba kanwar lasa baneba.............✍

      

*_Masha ALLAH Guys, ina fatan asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._*



*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*

*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


*Page 30*


________________________


*MG’s SKIN CARE*
(With us, your skin is elegant..)

Are you guys  looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k

Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Nd guess wht🦻
Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis  30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is  the time to glow🧖‍♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘

Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️

KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU, INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE.

__________________________


*Page 30*

............Tunda ya turo ƙofar tsararren bedroom ɗin ya shigo da shashshekar kukanta ya faracin karo cikin kunnuwansa. Batare da damuwa da rashin amsa sallamarsa ba ya ƙaraso cikin ɗakin yana kallonta.
      Zama yay a kujerar dake ɗakin tamkar bai damu da kukan nataba, a dakile yace, “Kinsa an tasoni daga office, gani to, mike faruwa?”.
     A fusace Farah da ke a kwance tana kukan ta tashi duk da tun farko tasan da shigowar tasa dama. Hawayenta ta share tana kallonsa, sai dai yanda ya tsatstsare ta da idanunsa dake rikitata yasa ta janye nata danta samu damar faɗar abinda ke a bakinta.
     “Babu abindama bai faruba. Ni wlhy bazan iyaba, tayaya wannan gidan zai ɗauki wannan gayyar dan ALLAH? Hidimar nawa zasuci ta kuɗaɗe tun daga kan abinci, ruwa da wasu wahalhalunsu?. Kawai sai dai muga yara batare da an sanar mana ba daga ni har kai. Ita bata tunani zamanta ma a takure muke bare tasa an ƙaro mana wannan yaran harda mara kunyar yarinyarnan data kusa min sanadin karayar ƙugu. Ko an faɗa musu rayuwar Nigeria da babu tsari da tanan iri ɗaya ce? Nasan duk Khalipha ne munafukin nan dan dashi zata haɗa bak......”
        “K ya isa haka malama!!”.
Ya faɗa a kausashe cike da nutsuwarsa. Dan inma baka saniba sai kace ba shine yay maganarba. Babu shiri Farah tai baya dan firgita tana kallonsa dan ya fito mata a zakinsa. Ya tsatstsare ta da birkitattun idanunsa yana nunata da ɗan yatsa. “Farah! Farah! Wlhy daga yau, daga yanzu, bakinki ya ƙara kuskure akan Granny saina zubar miki da haƙora a wannan gidan. Da kike cewa ta takura miki, mizai hana bazaki tafi inda zaki shaƙata ɗinba ke?. Ki kiyayeni Farah, ina ɗaga miki ƙafane kawai saboda ra'ayina badan kai ƙarata da kikeyi wajen mahaifiyata ba. Yara kuma nine na kawosu, idan kin isa dan ALLAH ki maidasu Nigeria yau ɗin nan stupid kawai”. Ya ƙare maganar yana karkaɗa mata yatsansa alamar gargaɗi na ƙarshe ya mike ya shiga toilet.
       Da wani banzan kallo ta bisa, ji take tamkar ƙirjinta zai buɗe dan tsananin zafin da takeji na cika mata gida da akayi. Ta tsani takura a rayuwarta. Dama Mammah ta faɗa, zuwan Khalipha tamkar buɗe hanyar banbarowar danginsa ne garesa, dan sun sami ƙofar da suka kasa samu tuni. To ita kam sai dai ayi duk ma abinda za'ai waɗanan yaran bazasu zauna a gidan nanba, kai itama makirar tsohuwarnan mai ƙulla komai saita tafi.........
         Fitowarsa ta katse tunaninta. Tasa hannu ta share hawayenta tana dubansa duk da kallon fuskar tasa kawai tsoro take bata ma. Zatai magana ya katseta dan yasanta da shegen naci da mita akan abu,  “Ki kwaso duk kayanki na ɗakincan tunda ba amfani kike da shi ba su zauna. Jamal ya zauna wajen Khalipha”.
      A zabure ta miƙe tsaye tana dubansa hawaye na rige-rigen sakko mata. “Haba Yah Abdul-Mutallab, ɗakin nawa zan basu?”.
      “Zama ɗakin kikeyi ne?”.
“To amma dan ALLAH kodai bana zama a ciki ai dai sunansa ɗakina.  Suje ɗakin Granny su zauna mana”.
     Wani banzan kallo ya mata idanunsa na sake canja kala. “Wlhy Farah idan kikace zaki bani ciwon kai akan zuwan yarannan tabbas zan baki ciwon zuciya ni kuma. Garama tun muna mu biyu kije ki kwaso abinda yake naki a can ki basu ɗakin, idan kuma kinƙi zakisha mamakina dan ina nan Abdul-Mutallab ɗin ɗin da kika sani”. Yana gama faɗa ya fice abinsa.
         Khalipha kawai ya samu a falon, Granny taja su Zinneerah zuwa ɗakinta. Jamal kuma Khalipha ya kaisa nasa ɗakin. Duk ƙoƙarin ɓoye fushinsa da yake sai da Khalipha ya gane. Har cikin ransa baiji daɗiba. Shiyyasa yaso Yayan nasu ya haƙura da batun zuwan yaran tunda ba dole bane. Dan yasan Farah ba zataso suzo ɗinba. Tunda shima a yaya yake zaune gidan ma. Ita kanta Granny ɗan hali Farah ke nuna mata duk da tsufanta.....
       “Ina suke?”.
Ya katse Khalipha muryarsa cike da ɗaci. Cike da son kauda masa damuwarsa Khalipha ya miƙe yana dariya. “Ai Yayanmu kasan waɗanan yaran ƴan gatan Granny ne. Ta jasu ɗaki wai suyi wanka da barci. Shima Jamal yana wajena”.
     Goshinsa yaɗan murza da furzar da huci yana lumshe ido. Batare da ya samu yanda yake so na daidaiton muryar tasaba ya nufi ɗakin yana cewa, “Taya zasu zauna a wannan ɗakin harsu huɗu zasu takura mata ai”.       
       Bin bayansa Khalipha yay yana magana cike da lallashi. “Yayanmu daka barsu isarsu zaiyi ALLAH, kaga munma huta da mitar Granny akan kaɗaici ko”.
        “Bazai yuwuba Khalipha ɗakin Farah zasu koma”.
     Dama abinda Khalipha kema gudun kenan. Ya ƙara buɗe baki zaiyi magana a dai-dai isowarsu ƙofar ɗakin AK ya ɗaga masa hannu alamar ya isa. Kai Khalipha ya dafe dan harga ALLAH baya buƙatar wata fitina akan zuwan yaran nan tsakanin yayan nasu da matarsa. Idan ta gaskiya za'abi sune da laifi, gashi kuma dama ba'a sanar mata ba tun farko. To amma yasan halin Yayan nasu tunda yace haka za'ayi dole a yarda ayi hakan”.
           Daga can Granny tace, “Khalipha shigo mana”. Dan batai zaton AK ɗin baneba. Batare daya nuna shi ɗin baneba kuma ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama ciki-ciki. Akan Zinneerah data fara wanka harta kwanta ya fara sauke idanunsa. Ya janye yana maidawa ga Granny dake gyarama Meenal kwalar riga. Bahijja kuma na toilet tana wanka.
      “A'a wai dama baka komaba?”.
Hajiya iya ta faɗa idanunta akan AK. Kansa kawai ya kaɗa mata yana kaiwa zaune. “Yanzu zan koma Granny, akan waɗannan dama na shigo, su koma can ɗakin ba'anan zasu zauna ba”.
       Shiru tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma ta saki murmushi tana girgiza kanta. “Moddibo bazai yuwuba. Ka barsu anan muyi zamanmu zai ishemu”.
       A karon farko ya kalleta shima. Ta kaɗa masa kanta da iya gaskiyarta tace, “Idan akai hakan ba'a ƙyautaba Moddibo. Inda itace taso su zauna mata a ɗaki dan kanta hakan ba damuwa bane. Amma ko nice miji yayma ƙarfa-ƙarfa akan danginsa su zauna min ɗaki zanga kamar an ƙasƙantar da nine. Ka barsu kawai suyi zamansu nan zai ishemu duka zaman kwana nawane ma”.
      Bai iya yace mata komaiba, sai idanunsa dake ƙara canja launi ɓacin ransa na bayyana a fili, miƙewa yay a hankali batare da ya sake kallon kowansuba yace, “Saina dawo”. Daga haka ya fice yabar ɗakin..  
      Da ga hajiya iya har Khalipha da su Meenal da kallo suka bisa suma damuwa fal ransu. Suna son Yayansu dan shima yana son su. Ko rashin sakewarsa a garesu kowa yasan wannan halinsane da kuma yanayin rayuwar daya tashi a hannun Mahaifiyarsa. Amma sunsan badan ƙuntatawa a garesu yake musu hakaba.
        Afusace Meenal tace, “Wlhy na tsani matarnan, danma taga ta samu Yayanmu mai haƙuri dajin maganar iyayensa shiyyasa takema mutane wani iskancin”.
      “Barta hankali zamu koyama shegiya ai a wannan karon, tunda ta yarda mukazo gidan nan wlhy tayi gamo da gamonta kuwa”. Cewar Bahijja itama muryarta har zuga take.
     Rai ɓace Hajiya iya ta kallesu tana musu daƙƙuwa. “Duk kunci iyayenku, ina ruwanku a cikin wannan zancen? Kunsan ALLAH duk wanda ya aikata wani abu a gidannan saina ɓata masa rai kuma ya koma gida. Ina kuma sake gargaɗinku shiga abinda ba'a sakakuba. Wannan ma ai rainine. Koyaya take ai matar Yayankuce taci albarkacinsa a wajenku marasa kunya”.
      Duk ƙasa sukai da kawunansu alamar nadama. Dan dama sunsan wannan ba tarbiyyarsu bace. Hasalima Hajiya iya bata yarda da irin wannan maganar a gabansu, yau ma dai akasi aka samu. Haƙuri suka bata. Shima Khalipha ya ƙara musu faɗa sannan yace suzo suci abinci shima zai wuce school ne.
     Duk wannan abin da sukeyi Zinneerah najinsu sarai, amma tai shiru kamar barci takeyi. da Khalipha ma yace a tadata taje cin abincin Hajiya iya hanawa tai. Catai su barta idan ta tashi sai taci nata tunda ta riga tayi barci.

      A ɓangaren AK kuwa koda ya fito daga ɗakin hajiya iya ɗakinsa ya sake komawa. Zaune ya tarar da Farah da waya a hannu kamar ba ita ta gama kukaba yanzun. Ko'a jikinsa dan ya shirya mata tsaf, ya kuma san Mammah bazatazo gidanba dan yunda Hajiya Iya ta dawo daga asibiti taƙi zuwa, dama kuma ko asibitin bataje ta dubataba. Yanzu hakama tana China batare da sanin Farah ɗin ba, dan shekaran jiya ta wuce da daddare.
        “Ki tashi ki tattara komanki dake a ɗakin nan ki maidashi ɗakinki. Karna dawo na taddaki anan ko wani abu naki”. Daga haka ya juya ya fice abinsa bai jira cewartaba.
       Fuskarta bayyane da tsantsar mamakinsa ta bisa da kallo. Yana fita ta miƙe a fusace dayin wurgi da wayar hannunta. ‘Ni zaka wulaƙanta akan waɗanan banzayen ƴan uwan naka Abdul-Mutallab? Saboda nace bazasu zaunamin ɗakiba kaima zakace na bar maka ɗakinka bayan kasan nafi son zama a cikinsa. Na rantse da ALLAH sai yaran nan da tsohuwarnan sunbar gidannan zan baka mamaki kai dasu. Bazan sake zubar da hawayena akansu a banzaba mu zuba mu gani’.
     Yanda take surutai ita kaɗai a kuma matuƙar fusace sai ta baka dariya. Ta koma tamkar wata zararriya. Sanin halinsa yasa bata ƙetare maganarsaba ta shiga tattare duk wani abu nata tana saka mai aikinta tana kaiwa ɗakinta. Sai dai kuma alwashin ƙuntata su Hajiya iya a gidan tacisa yafi sau shurin masaƙi.
         Bayan ta gama tattare komai nata tsaf ta saka mai aikin nata sake gyara masa sannan ta jawo masa ɗakin ta rufo harda saka key.

Su dai duk wannan abu dake faruwa su Hajiya iya basu saniba suna ɗaki abinsu tana hira da jikokinta. Abincin ma anan sukaci kusa da ita har Jamal da yana gama kimtsawa ya tafi can. Shiko Khalipha ya wuce school kamar yanda ya faɗa.

________________★

         *_DANYA_*

   Su inna sun kai Karima asibitin kusada. Likitocin nata faɗa ganin yanda jikinta ko ina sayin duka ga tsohon ciki da a yau ma yaketa nuna alamun zai fito duniya. Dan tunkan su wuce ashe naƙuda take shiyyasa jikin nata ya nema rikicewa.
       Ɗakin haihuwa suka kaita dan shine yafi cancanta da ita a wannan halin. Daga haka suka shiga bata taimakon gaggawa. Suka bar su Inna a waje da zaman jigum-jigum. Tun suna zuba idanun jiran kukan jariri da wuri har al'amarin ya fara fin ƙarfinsu. Dan ihun Karima kawai suke jiyowa babu na jariri. A haka suka cinye wannan yinin suka shiga marece. mahaifiyar Babawo sai kiransa take a waya yaƙi ɗauka. dan tunda ta sanar masa abinda ke faruwa kafin su baro Danya bai sake yarda ya ɗaga mata wayaba. Dole sai ƙaninsa keta kaiwa da kawo akan komai har ALLAH ya sauki Karima wajen ƙarfe goma na dare.
     Tsabar wahalar data sha daga ita har jaririyar sun fita hayyacinsu ko kukan kirki batayiba. Koda aka buƙaci kayan haihuwa babu abinda sukazo dashi asibitin. Aiko Nurse ta balbalesu da masifa dan haushi. Inna ta miƙe itama a fusace tana danƙarama Nurse zagi abu ya nema zame musu faɗa sai da aka lallashi Nurse ɗin da ƙyar. Dan sun fahimci Inna ma ba kanwar lasa baceba.
      Wannan abin daya faru yasa gari na wayewa aka basu sallama suka dawo gida duk
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On MAKAUNIYAR KADDARA
avatar
aisha-4-4-6

9 months ago

Reply

I want to download the book

avatar
maimuna-2-6

7 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment