Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ambaton Alhmdllh tare da mata fatan samun lafiya. daga haka suka fita domin biyan kuɗi suma suɗanje gida kuma.

*BAYAN KWANA UKU*

         Kwana uku Zinneerah na samun kulawa a asibitin da taimakon Khalipha dake tsaye akan komai. Dan koda direba Naziru ya bada iya kuɗin da ALLAH ya hore masa Khalipha ɗinne ya ƙara wasu aka biya kuɗin gado harna kwana goma, yace idan da buƙatar tafi waɗanan kwanakin sai asan abinyi. Alhmdllh jikin nata da sauƙi, dan ƙananun ciwukan harsun fara nuna alamar warkewa saboda bata da ƙan jiki, sai dai hannun natane take kuka da shi dan ta samu tsagewar ƙashi ne. Amma shima Alhmdllh yau ta tashi da sauƙi.
       Abu ɗaya ke tadama su Khalipha hankali, shine da zaran dare yayi babu zaman lafiya. Tata zabura kenan akan saita fita a asibitin. A daren farko sun ɗaukama tanada taɓin hankaline, hakan yasa suka danna mata allurar barci mai ƙarfi sosai, wadda ta jata har washe gari da rana tana barci. Sai da likita yay bincike kamar yanda Khalipha ya buƙata sannan suka fahimci lafiyar ƙwaƙwalwarta ƙalau sai dai kuma wani abu daban da basu saniba.
      A dare na biyu kam tana farawa wani tunani yazoma Khalipha. Kafin azo ai mata allura ya shiga tofa mata addu'oi, tun tana ɗan fisge-fisgen kaɗan da faɗin ita a barta ta tafi har ta fara lafawa, sai kuma gashi kafinma ayi allurar barci mai nauyi yay gaba da ita. A ranar haka Khalipha ya kwana da abin nan a rai, dan ji yake a ransa tamkar ya santa ko yanada alaƙa da ita. Dare na uku ma tana farawa ya fara mata addu'oin nanma sai gashi ta lafa. To a yau Alhmdllh bayan an cire mata ruwan da aka saka mata Khalipha ya saka wata Nurse ta taimaka mata aka goge mata jiki da duk abinda zai taimaka mata.
     Kusan ƙarfe bakwai sai ga Naziru direba da abincin karyawa kamar yanda ya jura kawowa kullum, da rana kuma almajiri yake kawo mata. Idan kuma ya dawo aiki yakan zo asibiti yay kamar awa guda sanann ya wuce gida. Hakan da yake yi nama Khalipha daɗi, shiyyasa baijin ƙyashin taimaka masa akan jinyar yarinyar dako sunanta har yanzun basu sani ba.
        Sai da aka gama kimtsata sannan suka shigo ɗakin. Fuskar Naziru washe da fara'ar jin daɗin ganin jikin nata yaketa ambaton, “Alhmdllhi, Alhmdllhi. Kai naji daɗin ganinta haka Malam Khalipha, ALLAH ya saka maka da alkairi, nagode-nagode”.
      Murmushi Khalipha yayi idanunsa akan Zinneerah shima yace, “Ai ƙoƙarin ka ne da adalcinka ya kaimu ga wannan nasarar Malam Naziru. Da ace guduwa kayi bayan kawota nan muma bazamu sami ƙwarin gwiwar taimakonta ba, dan direbobi da yawa idan irin haka ta faru guduwa suke subar majinyaci a asibiti koda kuwa ya zama gawa. Yanzu inaga jikin nata Alhmdllh gaskiya, ya kamata musan sunanta da inda ta fito dan mu nema iyayenta da mijinta kodan abinda ke a cikinta”.
     Cikin washe haƙora Naziru yace, “Wannan gaskiya ne Malam Khalipha”.
       Duk wannan magana dake fita tsakanin Khalipha da Naziru Zinneerah na zaune ne a gadon kanta a ƙasa tana saurarensu. amma ko sau ɗaya bata ɗago ta kallesu ba tanata faman wasa da yatsun hannunta ne kawai kamar bata a wajen ma.
       Nurse ɗin dake a gefenta ta ƙarasa gyara mata abinda ya rage ta fice ta barsu. Sai a lokacin su Khalipha suka ƙarasa inda take suna mata sannu. Yanzunma bata ɗago ta kallesu ba. Sai dai cikin rawar murya tace, “Ina yini”. Daga haka tai tsit.
     Wannan shine karon farko da sukaji muryarta tana cikin hayyacinta, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu. Khalipha yace, “Masha ALLAH, yau dai naji muryar ƙanwata”.
       Batace komaiba, kamar yanda bata ɗagoba. Bai damuba, dan ya fahimci akwai damuwa tattare da ita. Zama yay a bakin gadon daga can ƙarshe, dan haka tai saurin janye ƙafafunta data miƙe ta naɗesu. Baice komaiba, sai ma Naziru ne yaja kujerar roba shima ya zauna a kusa da shi. Su dukansu idanunsu a kanta suna kallonta cike da tausayi, dan shekarunta sunyi ƙanƙanta da fuskantar lalurar ciki irin haka a ganinsu.
      “Ƙanwata!”.
Khalipha ya kirata cike da kulawa..
      A karon farko ta ɗago taɗan kallesu, sai kuma tai azamar maida kanta ta duƙar batare data amsa masaba. Ya ɗan murmusa da sake faɗin, “Ki saki jikinki munan duk yayunkine kinji, munason miki wasu tambayoyine, ko zaki taimakemu da amsa?”.
      Kanta a ƙasa har yanzu ta gyaɗa masa kanta. Shima kan nasa ya gyaɗa cike dajin daɗin tana fahimtarsu. Ya cigaba da faɗin, “Minene sunanki?”. Shiru bata amsaba. Fahimtar bazata faɗaba ya sashi sake cewa, “A wane anguwa kike anan kano?”. Yanzu kam kanta ta girgiza masa.
      Cikin rashin fahimta yace, “baki san anguwarba ko ba'a nan kikeba?”.
    Kanta ta ɗaga masa.
Naziru ya amshe da sake faɗin, “Ba'a nan kike ba?”.
      Kanta yanzu ma ta kaɗa musu.
Kallon junansu sukai da mamaki, kafin Khalipha yace, “A wane gari kike to?”.
       “Nima ban saniba, na manta komai”.
    Ta basu amsa a fisge tana ƙara ƙasa da kanta alamar gajiyawa. Nanma kallon juna sukai cike da mamaki da fargaba. Naziru zai sake magana Khalipha ya girgiza masa kai alamar su barta kawai.
      Badan Naziru yasoba yay shiru, Khalipha ya miƙe yana faɗin, “Yauwa to bara na turo sister Salima ta baki abincin kici, dan nasan kina bukatarsa”. Daga haka ya kama hannun Naziru suka fice batare da ya jira amsawarta ba.
         Bayansu tabi da kallo har suka fice, ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tana lumshe ido. haka kawai take shiga takura da shiga wani yanayin da batasan dalilinsa ba a duk sanda Khalipha ya kasance a ɗakin.

        “Malam Khalipha akwai matsala kenanfa idan yarinyarnan batasan wacece ita ba, gata da ciki”  Naziru ya faɗa cike da damuwa sanda suke fitowa.
     Ajiyar zuciya Khalipha ya sauke yana furzar da iska. Yace, “Tabbas akwai matsala, amma ni tun daren farko da aka kawota na fahimci akwai wani ɓoyayyen al'amari tattare da ita. Dan yanda take zabura cikin dare da faɗin abarta ta tafi, da safe kuma taita barci yasa nake ganin kamar tana a wani hali. So yanzu dai sai munyi haƙuri munbi a hankali zamu kamo bakin zaren insha ALLAH”.
        Numfashi Naziru ya sauke shima. ransa da damuwa yace, “Ni kuma yarinyar kama ma takemin da amaryar Yayana wlhy, sannan maganar ɗawainiyar asibin wani abune mai zaman kansa Khalipha, badan ka taimaka min ba ai bansan yaya zanyiba nikam”.
     Murmushi kawai Khalipha yayi, cikin kauda maganar ƙarshe yace, “Kana nufin tana kamani da wadda kasani?”.
     “Sosaima kuwa, tun jiya da aka ɗan goge mata jiki naga kamaninta da Maman Sadiq sosai wlhy. Amma dai yau zan kawo matata da yamma dan ina komawa gida da wuri irin yau ɗin, kasan mata sun fimu lura. Kaga sai muji abinda zatace itama”.
      “Wannan shawaran yayi Malam Naziru, ALLAH ya jishemu alkairi”.
     “Amin ya rabbi, bara nazo na wuce dan na samu damar dawowa da wuri, yau katsina zan nufa insha ALLAH. Kuma sahu ɗaya zanyi na dawo gida”.
     “ALLAH ya bada nasara. Ya kuma maido mana daku lafiya”.
    Godiya Naziru yayma Khalipha ya wuce. Shima Khalipha sai ya wuce nasa uzirin acikin asibitin.

★★★

       Misalin ƙarfe huɗu na yamma Zinneerah na zaune a gadon jinyarta, idanunta tsaye ƙyam akan matashin cikinta, wanda yau ne karan farko data iya zaman masa wannan kallon. A duba guda da zakai mata zaka iya fahimtar ta lula duniyar tunanine. Dan har Naziru direba da matarsa sukai sallama biyu a ɗakin babu amsa.
      Kallon juna sukai shi da matarsa, kafin su sake maida idanunsu ga Zinneerah wadda da'alama har yanzu batasan da shigowar tasu ba. Takowa matar Naziru tayi har inda take, ta kai hannu akan kafaɗarta tana sake rangaɗa wata sallamar. Zabura Zinneerah tayi dan kamar daga sama taji sallamar tata. Ganin Naziru tsaye a ƙofa ya saka sauke ajiyar zuciya. Ta janye hanunta data ɗora saman cikin nata tana maida dubanta ga matar Nazirun da tai tsaye ƙyam tana duban Zinneerah ɗin da alamun mamaki a fuskarta.
      Kafin Zinneerah tai magana tai saurin faɗin, “Ikon ALLAH, Abban Nasiba kaga kuwa abinda nake gani?”.
     Cikin nuna tamkar bai fahimceta ba yace, “Mi kika gani?”.
     Ganin kallon da Zinneerah ke musu ne na alamar tsoro ya sakata wayancewa ta zauna kusa da Zinneerah ɗin tana faɗin, “Gani nai ƙanwar tawa ta lula tunani batama san da zuwan namu ba”.
     A hankali Zinneerah ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da sake maida kanta ta duƙar a ƙasa.
    Yayinda shi kuma Nasiru ya kasa ko motsi dan yayi zaton abinda ransa ke raya masa na kamannin yarinyar da Maman Sadiq matar tasa zata faɗa. Sai kuma yaji saɓanin hakan. Jin Zinneerah da matar tasa na gaisawa ne ya sakashi shima ƙarasowa gaban gadon ya ajiye ledan hannunsa yana dubanta da kulawa.
        Itama batare data sake ɗagowa ta kallesaba ta shiga gaishesa kamar yanda ta saba. Da kulawa ya amsa mata da sake tambayarta ƙarfin jikinta. Tace taji sauƙi.
     Sun jima a ɗakin tare da ita, sai dai su kaɗai suke ƴar hirarsu jefi-jefi. Zinneerah na zaune shiru tana saurarensu kanta a ƙasa. Sai da Naziru ya tambayeta ko Khalipha ya shigo? Ne ta girgiza masa akai alamar a'a kawai batare da tayi magana ba.
      Fara kiraye-kirayen sallar magriba da akai ne yasa sukai mata sallama suka fito.
      Suna fita ta sauke ajiyar zuciya, tare da zamewa a gadon ta kwanta ta lumshe idanunta da sake maida hannunta akan cikinta kamar ɗazun. Batasan wane tunani zatai akan wannan cikinba a rayuwarta. Dan yazo mata a yanayin MAKAUNIYAR ƘADDARA. shin tayaya wai aka samar da shi ne? Wanene ubansa? Kodai dama cikin basai mutum yayi aure ko ya aikata iskanci ba yake samunsa?.
      Wannan tunanin shine a ranta. Dan harga ALLAH ita dai tasan duk masu haihuwar garinsu sai sunyi aure. sannan idan akaga wadda batai aureba da ciki akance mata ƴar iskace mai bin maza. A yanda kuma takejin ma'anar kalmar mai-bin maza a abaki manya shine mace mai zuwa ta aikata abu mara ƙyau da namiji. To amma ita yau gashi bata a cikin duk waɗancan kason mutanen amma gata da ciki. Bata taɓa aure ba. Bakuma ta taɓa iskanci irin na waɗancan matanba. To kenan bayan waɗanan dalilan mace zata iya samun ciki ta wata sigar kenan kamar yanda itama a yanzu take tsamanin ta hakan ta sameshi?.

        Lokacin da Zinneerah ke wancan tunani a waje tsakanin Naziru da natarsa kam tattaunawa sukeyi suma akan abin al'ajabin da suka gani. Dan suna fitowa Matar tasa ke faɗin, “Abban Nasiba wlhy ɗazunfa waskewa nayi dan naga yarinyar nan ta tsorata. Kasan kuwa mina gani tattare da yarinyar nan?”.
       Kansa ya girgiza mata kawai batare da yace komaiba. Itama batare data damu da hakan da yayinba tace, “Wai shin kai bakaga kamarta da Maman Sadiq ɗin gidan babban yaya bane?”.
        A yanzu kam gaba ɗaya ya tattara hankakinsa gareta. Cike da zumuɗi yace, “Wannan dalilin yasa na kawoki nan Faɗima. Dan inata kokwanto, kinsan akan hakan jiya har gidan Yaya naje na sake ganin Maman Sadiq kuwa?”.
       “Ikon ALLAH, to amma ita yanzu ai kaga yan uwanta ko?”.
       “Inafa, bata iya faɗa mana komai akantaba wlhy, da alama akwai saka hannu a al'amarinta gaskiya, dan kamar bata da isashshiyar kafiya, kamar kuma mai tare da sammu ko jinnu. Amma ni yanzu kinsan wane tunani nayi?”.
     Kanta ta girgiza masa.
Ya sauke numfashi yana bin Khalipha dake fitowa daga wata baƙar mota data faka a kusa dasu da ido. Tinted glass ɗin motar yasa basuga wanda ke zaune matsayin driver ba. Sai Khalipha ɗin daketa faman ɗaga masa hannu yana murmushi har motar ta sake ficewa a harabar asibitin.
      Inda su Nazirun suke ya ƙaraso yana faɗin, “A'a malam Naziru kune anan haka?”.
         Cike da kallon alamar tambaya da Nazirun ke masa ya gyaɗa kansa. Dan mamakin wannan babbar motar da aka saukesa a ciki yakeyi. fahimtar hakan da Khalipha yasoyi ya sakashi yin murmushi da juyawa yana kallon motar da har ta gama ficewa a gate ɗin asibitin ta hau titi. Sake maido dubansa yay ga Naziru da shima motar ya koma kallo yanzun cike da basarwa.
         “Yaya dai malam Nazir?”.
Murmushi Naziru yayi a karon farko ƙasan zuciyarsa fal saƙe-sake akan tunanin da alama Khalipha ɗan masu da shi ne. Dan shi tunma randa suka ɗakkosa a Jigawa yaso fahimtar hakan. Amma shi Khalipha kamar bayason nuna shiɗin wanine.......
       Gyaran muryar da Khalipha yayine ya katse tunaninsa. Shi kuma Khalipha ya maida dubansa ga matar Nazirun suka fara gaisawa. Bayan sun gama gaisawarne Naziru yay masa bayanin itama abinda matar tasa ta faɗa game da kamannin yarinyar da matar yayan nasa.
       Khalipha yace, “To inaga mafita ɗayace damu kamar akan wannan tunain naku, mizai hana kubi hanyar data dace ita matar yayan naka tazo asibitin nan ko zamu sami wani bakin zaren, idan kuma babu damar yin hakan mu haƙura har yarinyar ta samu sauƙi sosai sai mu kaita gidan yayan naka mu da kanmu”.
        “Lallai wannan shawaran taka yayi Khalipha, kuma na gamsu da shi. Insha ALLAH zanyi iya duk ƙoƙarina zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu Maman Sadiq tazo asibitin nan kafin yarinyar nan ta kammala kwanakinta inaga kamar zaifi sauƙi”.
       Daga Khalipha har matarsa sun gamsu da hakan, dan haka sukai sallama yay cikin asibitin su kuma suka fito don tafiya gida.

__________________★

         A haka kwanaki suka cigaba da tafiya, Zinneerah na cigaba da jiyya da samun kulawa ga Khalipha, Naziru ma yana iya bakin ƙoƙarinsa ganin yazo dubata koda hidimar Khalipha ɗin da baya gajiyawa.
     Sosai ta samu sauƙi, dan yanzu Alhmdllh ko zaburan daren nan nason a barta ta fita batayi saboda Khalipha bai barin asibitin da wuri saboda ita kawai. Kasancewar suna sakata barci da wuri dan ta sami hutu sosai yakan zauna yayta mata addu'oi yana tofa mata, itako bama tasan yanayiba dan tuni tayi barcinta.
     Yawan kulawa da samun abinci mai inganci da takeyi yanzu ya sakata canjawa a zaman asibitin tamkar bamai zaman jinyaba. Tayi wani fresh da ita ga cikin nata nata sake nuna kansa. A duk sanda ta dubi cikin takan zauna taita kuka maiban tausayi. Dan takan rasa wane irin kalar tunani zatayi akan wannan MAKAUNIYAR ƘADDARA data riski rayuwarta?. Gaka da ciki amma bakasan ta hanyar daka samosaba balle ai tunanin wanene ubansa kuma. Ita yanzu ma da'an sallameta daga asibitin nan batasan indama ta dosaba kuma. Dan koda sha'awa bata son tunawa da Danya a ranta ma balle ai tunanin komawarta can.
     Har yanzu su Khalipha basusan sunantaba, tun kuma waccan ranar basu sake neman jin wacece itaba. Tamaƙi yarda ta saki jiki dasu gaba ɗaya.

       Yauma kamar kullum tana zaune a ɗakin da tab ɗin Khalipha dakan bata wai tayi game ko kallo haka danta rage kaɗaici. Game ɗin takeyi fuskarta na fidda murmushi mai ƙayatarwa, a kallo ɗaya zaka fahimci tana cikin nishaɗi, shiyyasa shi kansa Khaliphan yake ɗaukar Tab ɗin ya bata dazaran ya shigo cikin asibitin. Shekaran jiyama a wajenta ta kwana.
      Ɗan harbawar da zuciyarta yayi yasata dakatawa dayin game ɗin, haka yau ta tashi da wannan tsinkewar zuciya da batasan dalili ba, jin abin na ƙara ƙarfi ne ya sakata ajiye tab ɗin ta Khalipha gefe ta zame ta kwanta tana ambaton ‘hazbunallahu wani'imal wakil’ a ranta ko zataji ɗan daɗi............✍


*_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.

*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_TYPING📲_*


*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*


*Page 9*
________________________

*_Hummmmm!!. Wai wai wai, wani aiki sai: GIDAN ƘAMSHI💃🏻💃🏻💃🏻🥺_*

*_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON ƘAMSHIN GIDA DANA JIKI?_*

*_INA MATAN DAKAN SO DUK INDA SUKA DOSA KO SUKA BARI SAI SUN BAR MUSU TARIHIN ƘAMSHINSU_*


*_TO MATAN ƘWARAI KUZO GA WANI SIRRI DAZAN BAKU DAGA FITACCEN GIDAN ƘAMSHIN NAN DA BAIDA NA BIYU A KANON DABO😁_*

_Ina magana ne akan GIDAN ƘAMSHI da ke a Jihar KANON DABO MAIDUGURI ROAD MARIRI_.

*MUNA SIYAR DA TURARURRUKAN WUTA SET NA AMARE, MUNA KUMA BADA SARI.*

*AKWAI KUMA SABULUN GYARAN JIKI MAIDA TSOHUWA YARINYA, BUDURWA TAURARUWA, MATAN ƘWARAI ANNURIN HASKAKA GIDA. SHIMA DAI AKAN SARI, DOZIN KO KATON*

*AKWAI KUMA ZUMAR ƘARA ƘIBA GA MATAN DA KESON SU GANSU DUMURMUR SUNA JUYAMA OGA KAYAN...😉🙈💃🏻 kundai gane*.

*_Mata ku garzaya GIDAN ƘAMSHI domin ƙamsasa kanku kuma kar aci kasuwar sama babu ku😁_*

*ZAKU IYA SAMUN MU TA WANNAN LAMBAR WAYAR: 07033778564 DOMIN JIN ƘARIN BAYANI*.

*KO A KANO MAIDUGIRI ROAD MARIRI*.💃🏻💃🏻👍🏻


_______________________


*Page 9*

..........Jin kamar ana nufo ɗakin ya sata miƙewa zumbur taja hijjab ɗinta da Khaliphan ya kawo mata saboda salla ta saka da sauri. Ƙirjinta ne ya sake ƙarfin bugawa fiye da ko yaushe lokacin da Khalipha yay sallama a ƙofar ɗakin. Haka yakeyi mata a duk sanda zai shigo sai yayi sallama ta amsa sannan yake shigowa.
     Yanzu ma bai shigo ɗinba sai da ta amsa ya turo ƙofar ya shigo. Kallo guda tai masa tai saurin maida idanunta ƙasa saboda kwarjinin da yake mata da cika ido. Sai dai kuma luguden dakan da ƙirjinta ke mata ne ya tilastata sake ɗago kanta badan ta shirya ba. Naziru ne biye da bayansa. Sai matarsa. Sai wasu mata biyu da batasan daga inaba. Sai dai shigowar ta ƙarshen ya sakata wani irin zabura tana binta da kallon ƙurilla maiban mamaki.
       Yanda take kallon matar da yanda itama matar take kallonta tana tafiya da ƴar sassarfa ne yaja hankalin su Khalipha garesu baki ɗaya. Kusan mini ɗaya matarnan da Zinneerah na kallon juna batare da sun saniba, sai can Zinneerah ta fara janye nata tana sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya a ɓoye. Kanta ta maida ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika mata ido da batasan na minene ba.
         Jin yanda ɗakin yay shiru ɗayar matar da suke tare da itama al'ajabi ke neman halakawa ta katse shirun da faɗin, “Baiwar ALLAH sannu kinji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya ƙara lafiya”.
        Kusan a tare duk sukace amin, banda matarnan mai kama da Zinneerah da gaba ɗaya hankalinta bayama tare da ita. har yanzu kuma idonta nakan Zinneerahn. Sun ƙara jajanta mata da mata addu'ar samun lafiya mai ɗorewa sukai musu sallama suka fita bayan matan nan biyu sun ajema Zinneerah kuɗi. Koda zasu fitanma matarnan tana tafiya tana waigen Zinneerah har suka fice. Shi dai Khalipha yana tsayene yana kallonsu da nazari tun shigowarsu har suka fice.
        Wayarsa da ke ring a aljihu ta sashi sauke numfashi da warware hannayensa daya harɗe a ƙirji ya cirota a aljihu. Wani lallausan murmushi ya saki wanda yay dai-dai da ɗagowar Zinneerah. Sai ko ga idanunsu cikin na juna. Tai azamar maida kanta ƙasa ƙirjinta na wani irin harbawa, dan ba ƙaramin dukan zuciyarta wannan murmushi nashi yayiba.
        Shikam wayar ya kai a kunne yana ɗan lumshe idonu, cikin wata murya mai ɗunbin ladabi da girmamawa yace, “Assalamu alaika Yayanmu”.
     Batajin mi ake faɗa acan ɗin, sai Khalipha ne taji ya wani sake narke murya da shagwaɓa yana faɗin, “Oh Yayanmu Please ka jirani gani nan zuwa, nifa nace zan kaika da kaina yau, nanda mintuna goma insha ALLAH ina gida”.
         Bataji mi nacan ya sake cewaba. Sai Khalipha ne ya matso gaban gadon yaɗan bubbuga yana cigaba da sauraren abinda ake faɗa ɗin daga can. Ɗago kanta tayi ta kallesa dai-dai ya sake narke fuskar tamkar wani yaro ƙarami, kokuma yana a gaban wanda yake wayar. “ALLAH Yayanmu bazanyi gudu ba, kasan mashin bakamar motaba ai, kuma zanbi ta hanyan dazan samu sauƙine fa Please ”.
        Ita dai Zinneerah ganin yana neman zauta mata kwanya taso sake maida kanta ƙasa sai yay saurin mata alama da hannu wai yana zuwa. Bai jira cewartaba ya fice da hanzari. Bin bayansa tai da kallo harya fice, tsigar jikinta na wani tashi batare da tasan daliliba. Sai kawai ta fashe da kuka.
       Kuka sosai Zinneerah taci wanda yana alaƙa da wasu baƙin al'amura a gareta, sai dai ƙuruciya ta hanata fahimtar komai. Ta zame a hankali ta kwanta tana lumshe idanunta badan barciba, sai don son samun damar tunani da wassafo matar ɗazun da takesonyi harma da tuno halin data shiga a dalilin ganin nata da wanda ta lura itama matar ta shiga saboda ganinta.

     A ɓangaren Maman Sadiq kam itama tunda suka fito daga asibitin tafiya kawai take tamkar bata cikin hayyacinta, jitake kamar ta dawo ta sake ganin Zinneerah ɗin saboda abinda takeji a ranta da dukkan magudanar jinin jikinta a dalilin tozali da yarinyar. Duk da wani ɓangare na zuciyarta na ƙwaɓarta da cewar ba haka bane ta kasa yarda sam.
       Daga Naziru har matarsa hankulansu nakanta ne suna nazarin halin da take a ciki, sai dai basuce komaiba har ya maidasu gida shima ya wuce nasa gidan da matarsa. Inda sai anan suka sami damar tattaunawa akan yanayin maman Sadiq ɗin.

        Tunda suka shiga cikin gida ta buɗe ɗakinta ta shige saita kasa zaune ta kasa tsaye, kaikawo taketa famanyi a ciki, duk da masifar kishiyarsu Saude da take jiyowa akan taƙi fita ta ɗora girkin rana ga lokacin kaima yara abincin rana makaranta ya kusa bata fito ɗinba. Sai Uwargidansu da sukaje asibiti tare ce ta jiyo tana bama Sauden amsa da “Haba dai Maman Sakina, kodan himma irinta Maman Sadiq ai yakamata ki fara tunanin anya lafiya kuwa? Amma sai ki ɓige da neman fitina daga shigowarmu gidan dai”.
         A harzuƙe da masifar da dama Sauden jira take ta hayayyaƙoma Uwargidan nasu.....
       “Yaya! Yaya! Ƴar ayi jikan nasaba”.
Muryar mai-gidan dake shigowa ta katse masifar Sauden ta koma ƙunƙuni ciki-ciki. Baibi takantaba sai uwargidan tashi dake masa sannu ya duba. “Mike faruwa kuma daga dawowarku Binta?”.
      “Babufa komai Alhaji, fitinace irin ta Saude da baƙarewa take a gidan nan ba. Kawai dan Maman Sadiq bata fito ba shine take tsogumin batazo ta ɗora abinciba wai lokacin kaima yara makaranta ya kusa”.
       Ɗan tsaki yayi yana girgiza kansa. Yace, “Ina ita Hauwa'un take?”.
      “Tana ɗakinta, inaga dai akwai abinda ke damuntane, dan tunda muka baro asibitin naga yanayinta ya canja, na bartane muzo gida taɗan huta dama ko wani abune ya tada hankalinta acan ɗin tunda wajene bana daɗin rai ba”.
     Baice komaiba ya nufi ɗakin Maman Sadiq ɗin, wadda duk tanajin mi'ake a tsakar gidan amma taƙi yin ko tari dan abinda ya isheta ya girmi fitinar Saude. Labulen ya ɗaga yana dubanta daga bakin ƙofar, yitai kamar bata gansaba, hakanne yasa ya shigo ciki yana faɗin, “Hauwa'u lafiyarki kuwa”.
       Juyowa tai ta kallesa tamkar yanzune tasan da zuwansa. Tace, “Ashe ka shigo? ALLAH yasa dai lafiya?”.
        “Ai ke za'a tambaya ko
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On MAKAUNIYAR KADDARA
avatar
aisha-4-4-6

9 months ago

Reply

I want to download the book

avatar
maimuna-2-6

7 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment