Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[04/08, 21:52] Hubbey Frd Ameena Kn: [4:40AM, 7/15/2018] hubbeey: *🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀



*Sat/july/14/2018.*




*STORY*
*By*
*_AISHA MODIBO_*
*_(Aindo k'afar yawo)._*




*_WRITTEEN & EDITING_*
*BY*
*_HABEEBA IDREES(Hubbeey)._*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*



*_ALLAHUMMA LAASAHLA ILLAMAJA'ALTAHU SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZ'NA IZA SHI'ITA SAHLAH._*




*💠SMASHER & HUBBEEY🌺 FANS GROUP 1&2.*

*WAN NAN PAGE 'DIN NA FARKO NAKUNE KUYI YADDA KUKE SO DASHI.*



*GARGA'DI*

*BAN YARDA WANI/WATA SU JUYAMIN WAN NAN LABARINBA TA KOWACCE SIGA, HAK'IK'A YIN HAKAN ZAISA IN 'DAUKI BABBAN MATAKI GA DUK WANDA YA AIKATA HAKAN.*
*IDAN KUNNE👂🏻👂🏻 YAJI..........*


*HAK'IK'A WAN NAN LABARIN BA K'IRK'IRARSA NAYI BA, HAKAN YAFARU DAGASKE KUMA ZANFARA RUBUTA WAN NAN LABARINE DA YARDAR WACCE ABIN YAFARU AKA*





*_PAGE1⃣_.*



Yarinya ce 'yar kimanin shekaru goma sha uku,
Gudu takeyi iya k'arfin a dai² lokacin da AUDU mak'ocinsu ke k'wala mata kira..
"Indoooo! Indoooo!!
Inaaaa aituni indo tasha kwanar dazata sadata da gidan sabuwar Amaryar da aka kawo kwanaki uku dasuka wuce..
Tsaki AUDU yayi yanacewa "kai jama'a wan nan yarinya indo akwai k'afar yawo duba yadda BAFFAN ta yake kiranta nima na mai² ta mata amma saida takai ga inda take son zuwa ALLAH yashirya...





Ko sallama babu indo ta tura kai cikin d'akin Amaryar, a jikin k'aramin gadon Amaryar ta jingina, itakuwa Amaryar ido kawai tazuba wa indo, ganin yadda Amaryar take kallonta ne yasa INDO ta matsa daga jikin gadon...
"Ke mene haka zakishigomin d'aki ko sallama babu?"
Washe baki INDO tayi tana faman dariya kamar bada ita Amaryar take maganba........
Daga bakin k'ofa taji sallama, aikuwa suna had'a ido da INDO ya d'aure fuska, gaban INDO ne yafad'i saboda arayuwar ta bata k'aunar taga mutum ya 'bata rai saboda ita, baiyi mata maganaba sai wata muguwar harara dayake watsa mata, sum sum sum takama hanya tayo waje bata tsaya ko inaba sai bakin k'aramar kasuwar dake cikin garinna su.....
Tun daga nesa suke mata dariyar yadda suka hango k'afarta ko takalmi babu, haushine yaka mata ranta A 'bace ta k'araso inda suke...
"Amina nagaya miki banason abinda kukeyi min amma kullum bakuji ko?"
kallon k'afar INDOn Amina takeyi ta kuma kwashewa da dariya.......
Sosai INDO taji haushi ganin zasu maida ita mahaukaciya ne yasa tayi saurin barin wajen......
Chaaaan gefe tasamu tazauna tana ta kallon sauran mutanen dake kai komo acikin kasuwar....
Kamar antsikara mata wani abu haka ta mik'e ta kyalla da gudu gida tanufa bata zarce ko inaba sai d'akin BAFFAN ta babu kowa ad'akin bincike tashiga yi duk inda tasan BAFFA yana ajiya saida ta duba amma sam bata samu abinda take nema ba.......
A tsakar gidansu ta tsaya tana tunanin ina zataje, jitayi an damk'e hannunta tabaya da sauri INDO ta juyo ganin wadda ta rik'eta d'in yasatayi shiruuu takasa cewa komai........
"INDO wato ke bazaki iya zaman cikin gidanku bako?"

"GOGGO naga sai na gama miki komai san nan nake fita"

INDO tabata amsa tana turo baki gaba.....

"Ehhh amma dai kinsan wan nan fita yawon da kikeyi yana 'batawa BAFFAN ki rai ko?"

A dai² lokacin ne BAFFA yashigo gidan, da sauri GOGGO tasaki hannun INDO......

K'afar indo kawai BAFFA yakalla ya girgiza kai da alamun damuwa sosai akan fuskarsa, baice komai ba yashige d'akin yabarsu anan, aikuwa tana ganin BAFFA yashiga d'aki da gudu INDO tayi waje........
jiyo muryar GOGGO yayi tana salati da sauri BAFFA yafito yana tambayarta mene yafaru?
Nan ta shaida masa cewar ai INDO ce tasake ficewa daga gidan,
'Daga kansa yayi sama kamar mai duba wani abu............

"Kai jama'a YA ALLAH kaine kabani AISHA ALLAH kaine zaka shirya min ita, YA ALLAH ka karemin ita aduk inda take"

GOGGO dake gefe ta amsa da "AMEEN"






Ta cikin wata k'atuwar gona tabiyo tafiyar ta take hankalinta kwance duk da duhun maghreb dayafara amma ko kad'an INDO batajin tsoro haka take taka k'afar wadda ko arzik'in takalmi bata samuba, itayi kamar ana binta abaya ahankali ta juya babu alamun tsoro atareda ita.....
AUDU tagani ya d'akko ice mai makon INDO tabashi hanya kawai saita juwa tacigaba fa tafiyarta....

"INDO kauce mana kina ganin kaya akaina ko tsoro bakiyi ga Almoru ta kawo kai"


Kamar bada ita yake maganaba haka taci gaba da tafiyarta san nan ta tage saurin da takeyi....,

Haushine yakama AUDU haka ya hak'ura ya kaucewa INDO yashiga cikin gonar mutane yana sauri² baifi taku biyar AUDU yayi ba ji kake yiiippp AUDU ya fad'i shida itacen da yad'akko.....

Da gudu INDO tak'araso inda AUDU yake kwance, a gabanshi ta tsuguna wata irin muguwar dariya INDO taleyiwa AUDU, shikuwa sai salati yake yi yana neman ataiaka masa....

"INDO nakarye wllh INDO nakarye"

Fad'a yake yana mai² tawa amma duk da haka INDO bata dena dariyar datakeyi ba......
Saida taji dai yayi shiru san nan itama ta dena dariyar.....

"ALLAH sarki AUDU sannu bara inkai maka itacen gida sai ingayawa INNA LAMI ka karye a gonar MALAM TANIMU"
Da kyar ta iya d'ora itacen akanta san nan ta d'auki hanyar gida......,

Tundaga jikin dangar gidan AUDU INDO tafara kwalawa INNA LAMI kira tareda sanar da ita cewar AUDU yafad'i yakaye, kamar daga sama INNA LAMIn take jiyo mufyar INDO d'in.....
A dai² k'oafar dazata shiga gidan AUDU ne taci karo da d'angidan AUDU agabansa ta saki itace saura kad'an yasauka akan k'afarsa....

"Ga itacen kunan kuma babanka yana chan kwance a gonar malam tanimu ya fad'i yakarye inkun gadama kuje ku d'akko shi"

Tana gama fad'ar haka ta juya takama hanyar gidansu.





*_FANS DAN ALLAH KUMIN AFUWA NARASHIN YIN TYPING EN NOVEL EN SAMEERA, JIYA DA YAU DABANYI BA AMMA INSHA ALLAHU GOBE ZANYI DA YARDAR ALLAH._*









*_Ur's Hubbeey._*
[4:41AM, 7/15/2018] HASSN ATK: Hmmm kingama wachanna
[4:41AM, 7/15/2018] hubbeey: Gobe zan gamashi
[4:43AM, 7/15/2018] HASSN ATK: Hmmm lallai km
[4:49AM, 7/15/2018] hubbeey: 😏😏😏😏
[4:50AM, 7/15/2018] hubbeey: *Falyaqul khairan auliyasmuut*🤫🤫
[4:52AM, 7/15/2018] MEINAH LTTL: 😂😂😂
[4:52AM, 7/15/2018] MEINAH LTTL: Bafa abinda nace
[4:52AM, 7/15/2018] MEINAH LTTL: Ba tsiya nafa ba
[04/08, 21:52] Hubbey Frd Ameena Kn: *🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀




*sun,july,15,2018.*



*_STORY_*
*BY*

*_AISHA MODIBO_*
*_(indo k'afar yawo)._*


*_WRITTEN_*
*BY*

*_HABEEBA IDREE(hubbeey)._*




*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*


*ALLAHUMMA LAASAHLAH ILLA MAJA'AL TAHU SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZ'NAH IZA SHI'ITA SAHLAH.*






*S.H.D.G NOVELS GROUP*

*S.H.D.G COMMENTS GROUP*

*S.H.D.G KITCHEN GROUP*

*MIJIN AURENA FANS GROUP*
*&*
*GAMU GA ALLAH FANS GROUP*


*DUK NAZO GAREKU*

*_WAN NAN PAGE 2 'DIN NAKUNE_*
*_KUMA KARKU MANTA DA SAKA INDO CIKIN ADDU'O'INKU._*





*_page2⃣._*



A k'ofar gida INDO tagamu da BAFFAN ta bashiri ta sunkuyar da kanta k'asa tabi ta gefensa ta shige cikin gida, Abakin murhu ta samu GOGGO tana kwashe dasauri INDO tafara d'aukan tuwon da GOGGO ta kwashe tana kaiwa cikin d'akin girkin su, itakam GOGGO da ido kawai tabita a zuciyarta kuwa tanayi mata addu'ar ALLAH YASHIRYE TA da wan nan yawon datakeyi, bayan tagama kaiwa tanufi bakin rijiyar su ruwa ta jawo tazubawa GOGGO a buta itama ta zuba tayi alwala.....
Tunda tashiga d'aki take jero sallolin dabatayiba wanda suka wuce ta tana chaaan wajen yawo, har GOGGO ta idar tayi addu'o'in ta amma INDO bata idarba.........
Bayan ta idarne tafara jero addu'oi afili takeyin addu'ar yadda duk wanda yake cikin d'akin zai iyajin abinda take fad'a cikin addu'ar.....
"YA ALLAH KASA INADA RABON ZUWA BIRNI KODA AK'AFANE, KUMA ALLAH KASA INNAJE BIRNI INSAMU MIJI MAI KU'DI WANDA ZAI BARNI INTAYAWO NA INA GANIN GARI"......
GOGGO kuwa dake gefe guda cikin d'akin tana jan charbi da sauri ta juyo saboda jin wanan Addu'a da INDO tayi, ba shiri GOGGO ta shafa addu'ar datakeyi ta fice daga d'akin GOGGO tana fita tanufi soro ta rufe k'ofar gidan da kuuba, abakin k'ofar soron sukayi karo da INDO zata fice wata harara GOGGO ta watsawa INDO ta wuce tabarta awajen...

'Dakin BAFFA GOGGO tashiga a zaune tasameshi sallama take tayi amma sam BAFFA baisan ma tanayi ba yayi nisa sosai cikin tunanin "yarsa INDO, harsaida GOGGO ta zauna kusa dashi ta kama hannusa tasauke daga kan kuncinsa wanda ya zabga tagumi dashi.
"haba MODIBO saunawa Zan gaya maka kadena yawan tunanin nan addu'a ya kamata muyi tayi mata bawai musaka damuwa aranmuba"


" kayya BINTA bakisan yadda nakeji ba wllh saboda yawan yawon da INDO takeyi, indama nake godewa Allah bata jawo min magana barta dai tashiga nan tashiga chaan amma hakan ko kad'an bashida wani amfani musamma ga ita mace, gaskiya BINTA bazan 'boye mikiba wan nan abu yana matuk'ar damuna wllh"
Ya k'arashe maganar yana kamo charbinsa...

"to yaya zamuyi MODIBO addu'a babu abinda ta bari ita zamuci gaba dayi mata har muga k'arshen lamarin"...

GOGGO tayi tunanin fad'awa BAFFA irin addu'ar dataji INDO nayi d'azu da ta idar da sallah, amma ganin yadda tasamu BAFFA ne yasata fasa gaya masa....
mik'a masa kuubar data rufe gidan dashi tayi...

"Gashi inzaka fita sallah Isha sai ka bud'e"

"Hmmm yanzu ma fita zatayi ko?"

BAFFA yatambaya fuskarsa cike da damuwa...

" a'a kawai dai na rufene, bara inkawo maka abincin ko?"

" a'a kibari saina dawo daga sallah tukunna"

Yana fad'ar haka GOGGO ta mik'e tabar d'akin.......






Alokacin da iyalan AUDU suka isa gonar malam tanimu sosai garin yayi duhu dan Alokacin ma anashirin yin sallar ISHA, akwance suka sameshi ga k'afarsa d'aya akarye, nan suka shiga tunanin yadda zasu d'aukeshi, halliru wanda qanin ga AUDU shine yaba shawarar akoma ad'akko kura sai asakashi aciki atafi gidan dori, aikuwa haka akayi halliru da Aminu d'angidan AUDU sune suka komo gidan dan d'aukar kurar dazau sako AUDU aciki, basu wani jima sosai ba suka dawo suka d'aukeshi suka sakashi aciki, haka sukayi ta turashi har suka shigo cikin garin, kai tsaye gidan. Sarkin 'Dori suka nufa dashi.....

Bayan BAFFA yadawo daga sallah isha ne ya rufe gidan tareda yin addu'a, d'akin GOGGO ya lek'a ya kirawo INDO cewar taje tasameshi a d'akinsa....

Saida tagama nuk'u-nuk'un ta kafin ta tashi ta tafi...,
Daga bakin k'ofar ta tsaya tace

"BAFFA gani"

" haba AISHA shigo daga ciki mana"

"Wllh BAFFA nasan fad'a zakayi min innashigo gara kawai intsaya daga nan idan naji ba fad'an bane sai in k'araso ciki"
Tayi maganar tana kunbura baki irin na shahararrun shagwa'ba'b'bun yara.....

Wani murmushin takaici BAFFA yayi san nan yace..
"Ba fad'a zan miki ba aikenki zanyi"

Aifa tanajin kalmar aike da sauri tashige cikin d'akin....

"yawwa ko kefa AISHA ta, amma kafin in aike ki bari in tambaye ki nasan bakyayin k'arya dan Allah AISHA ki fad'amin gaskiya kminji"


"To BAFFA na zangaya maka"


"yawwa AISHA jiya dana fita kinsan na jima bandawo ba ko?"
Bai jira ta amsaba yacigaba da maganar sa..
"To dan Allah wakika gani yashigomin d'aki?, da na dawo natarar anyimin bincike kuma ni nasan ba GOGGON ki bace, AISHA ko kinsan wanda yashigo min?"

Batare da wani jin tsoro ba INDO ta kalli BABBAFAN ta tafara magana..

"BAFFA wllh nice nan nashigo inaneman kud'ina dana baka ajiya zan sayo takalmi akasuwa kuma nayita dubawa baganiba na hak'ura, amma yanzu tunda ka tinamin saila d'akko min kud'ina ko?"
Dariya sosai BAFFA yayi

"Yanzu AISHA daman haka akeyi idan anbawa mutum ajiya sai naya nan azo ayi masa bincike? ashe tba banzaba BINTA tace tadena karban ajiyar ki kota meye, to nigashi tunjiyan banga kud'ina ba dana ajiye kinga kenan kin d'auki kud'in takalmin ki ko?"

Nanfa idanun INDO suka ciko da hawaye tashiga rantsuwa..

"Wllh BAFFA saidai inwani ne ya shigi ya d'aukar maka amma wllh Allah niban d'aukar maka kud'I ba"


"To shikenan naji yanzu koibari kinga gobe LARABA innaje kasuwar LARABAR ZANGO sai in sayo maki takalmin ko"?


" BAFFA nidai dakabani kud'in sai insayo da kaina"


"haba AISHA tunda nace zan sayo naki aikinsan zansayo maki ko?"

Itakam abun bai mata dad'i ba kawai ta hak'ura ne saboda tafiso taje kasuwar dakanta....

"BAFFA to kabani aiken mana intafi"
INDO ta tunawa BAFFAN maganar aiken dazai mata.....


"Kibarshi ma naga dare yayi da safe in Allah yakaimu saiki sayomin"

Bakinta tura gaba ta mik'e zata bar d'akin, da sauri BAFFA yakamo hannunta "AISHA fushi kikayi dani"?
Hannu tasaka ta rufe fuskarta saboda taji kunyar tambayar da ABBAFA yayi mata...
"A'a ba fushi nayiba"

"Yawwa AISHA ta jeki to ALLAH yayi miki albarka, ALLAH yashirya minke, inkije kice ina kiran GOGGON ki"
Da to ta amsa masa, harta kai bakin k'ofa ta juyo..
"Au BAFFA bangaya makaba wllh d'azu ina tafiya akusa da gonar malam tanimu saiga AUDU ya d'akko itace daga gonarsa wai a lallai sai ta inda nakebi shima zaibi nikiwa nak'I kaucewa, shine yabi ta cikin gonar aikuwa ya fad'i yaketa salati BAFFA ingaya maka harji nayi yanacewa wai yakarye, saboda zabar dayaji"
Ta k'ashe maganar tana dariyar ta alamun babu abinda yadameta.

Dasauri BAFFA ya mik'e yana fad'in "SUBHANALLAHI"
Amma shine AISHA baki gayamin ba sai yanzu da daddare?"

"To BAFFFA mai zakayi masa innagaya maka, tunda naje gudansa nafad'a aishikenan ko"
Tana fad'ar haka tayi tafiyarta, shikuwa BAFFA k'am yak'ame awajen.








*_Ur's Hubbeeey._*
[04/08, 21:53] Hubbey Frd Ameena Kn: *🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀



©®.
*21/7/2018.*


*_STORY BY_*

*_AISHA MODIBO_*
*_(Indo k'afar yawo)._*


*_WRITTEN BY✍🏻_*

*_HABEEBA IDREES_*
*_(Hubbeey)._*



*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*




*ALLAHUMMA LAA SAHLAH ILLA MAJA'ALTAHU SAHLAH, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZ'NA IZA SHI'ITA SAHLAH.*



*_KARKU MANTA DAI INDO K'AFAR YAWO🚶🏻‍♀ZAI DINGA ZUWA MUKUNE ARANEKUN ASABAR DA LAHADI INSHA ALLAH._*



*SAK'ON INDO ZUWA GAREKU*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*DOMIN FITAR DA KAUSHIN K'AFA KO FASO:-*

*KISAMU RUWAN ZAFI KIZUBA A BAHO SAI ZUBA BAKING POWDER COKALI 2 SAIKI SAKA K'AFARKI ACIKI TASAMU KAMAR MINTI 15 SAN NAN KI FARA GOGE TA DA ABIN GOGE KAUSHI IDAN KIN GAMA SAIKI SHAFA MAN KA'DANYA.*







*_page 3⃣._*




Tunda gari ya waye BAFFA yagama shirinsa don zuwa duba AUDU a gidan sa, INDO ce ta tareshi a k'ofar soro bayan ta gaida shi.....
"BAFFA zaka fita baka bani kud'in takalmin ba"

"Haba AISHATU yanzu harkin manta yadda mukayi dake jiya, yanzu hakafa gidan AUDU zanje indubashi sai kuma inwuce kasuwa kuma ina shiga kasuwar takalmin zanfara saya miki kafin ink'ara rumfa ta karki damu insha Allahu yau zan sayo miki kinji"?

"To shikenan BAFFA Allah ya kiyaye hanya"


"Yawwa AISHATU maza jeki kirawo min GOGGOn ki"

Da gudu tanufi d'akin GOGGO amma koda tashiga tsalle tayi ta haye gado abinta ta kwanta bata sanarwa da GOGGOn sak'on BAFFAn ba, itakam GOGGO kawai kallon INDO takeyi tana jiran taji tasanar mata da sak'on BAFFA saboda duk tana jin yadda sukayi amma ta ji shiru, ganin bata da niyyar gaya matane kuma tasan BAFFAN yana chaan yana jiranta yasata mik'e ta je wajenshi......
"Ahh modibo harka fito?"
GOGGO ta tambayi BAFFA wanda ke tsaye yana jiranta..

"Ehhh na fito zanje gidan AUDU ne induba shi daga nan kuma sai inwuce kasuwa"


"Allah sarki bashida lafiya ne?"

"Ehh jiyane yadawo daga gona ya d'akko itace sai yafad'i yasamu karyewa a k'afa"

"subhanallahi Allah yabashi lafiya amma bansaniba"

"Ehh nima sai da daddare indo take gayamin da yake wai agabanta yafad'i ita tazo gidansa ma tafad'a, kema inkin gama abinda kike sai kuje da INDO kudubashi, to nizan tafi Ga INDO nan dan Allah Kici gaba da hak'uri da halayen ta Insha Allahu wata rana sai labari kinji?"
Tuni idon GOGGO ya ciko da hawaye lokuta da dama haka modibo yake cemata wataran sai labari amma itakam takasa ganin wan nan lokacin da za'ayi labarin saboda gashidai INDO kullum girma take kuma YAWON ta k'aruwa yakeyi....
Ganin tayi nisa cikin tunanintane yasa BAFFA yayi ficewar sa yabarta anan tsaye saboda inda sabo yasaba da halin GOGGO na tunanin, kamar yadda itama ta saba danasa halin, Kuma duk tunanin nasu akan INDO ne.......


A soro yasamu AUDU inda aka kwantar dashi, bayan sun gaisane BAFFFA yake tambayar AUDU yadda tsautsayin yasameshi, murmushi kawai AUDU yayi yace "abar maganar kawai Allah yakiyaye gaba kuma ALLAH yashirya mana zuri'a"
BAFFA kam yakasa gane wan nan kalma ta AUDU....
Amin kad'ai BAFFA ya iya furtawa san nan sukayi sallama akan zaije kasuwa amma inyadawo da yamma zai dawo yasake dubashi....

Malam AUDU mutum ne mai matuk'ar hak'uri, dan ko natar shi yak'i gayawa yadda akayi yafad'i har yasamu karaya, yaranshi kuwa duk sunyi iya tambayarsu amma furr yak'i gaya masu kawai sai yace "DAGA ALLAH NE" saboda yasan idan yagaya masu abin bazaiyi kyauba.........


Rana tayi jama'a duk suntafi kasuwa garin yayi shiruuuu, GOGGO ta shirya zata shiga gidan AUDU domin ta duba shi, A soro taci karo da INDO anan tasanar mata da cewar BAFFA yace suje su duba AUDU...
"Kije GOGGO gani nan yanzu zanbiyoki"
GOGGO kuwa bata amsa mataba haka ta fice tayi tafiyarta ita kad'ai, fitar GOGGO kedawuya
wani yaron mak'otansu yashigo an aikoshi wajen BAFFA...
"INDO BAFFAn ki yanan"?
Inji yaron da yashigo gidan wanda ko sallama baiyiba......

"Kai wanne irin gidahumine?, zaka shigo gida ko sallama babu, kuma mai zakayiwa BAFFA na da kake nemansa?"
INDO ta fad'a tana masifa tareda matsowa kusa da yaron kamar zata dakeshi, shikuwa sai jaaaa dabaya yakeyi saboda yasan halinta yanzu saitayi masa duuuka, cikin in'ina yaron yafara magana...

"Innnn innnnn daman innar muce tace idan BAFFAN ki zaije kasuwa ga kud'i yasayo mata gero kwano uku"
Ya fad'a yana mik'owa INDO kud'in, aikuwa da sauri ta karba...
"Kaje kace BAFFA yatafi kasuwa amma nizanje kasuwar anjima zan siyo mata, maza kayi sauri katafi gida kace zankawo mata innadawo"
Badan ransa yaso ba haka yaron yabata kud'in saboda innar shi ta.gargad'eshi da cewar in har BAFFA baya nan to yadawo mata da kud'inta, yaron yana fita INDO ta wanke fuskarta ta lafka mai a k'afarta tazari takalmin GOGGO ta nufi kasuwa..........

Tafiya ce mai tsayi tsakanin garin tsiiko da kasuwar larabar zango dake k'aramar hukumar ajingi cikin garin kano, amma hakan bai hana INDO mik'a k'afafunta tayi wan nan tafiyarba dan ganin taje wan nan BABBAR KASUWA dan cika burinta, duk da dai akwai masu tafiya a k'afarsu amma duk cikinsu Babu mai k'ank'anta kamar INDO, dan haka duk duk inda tabi kawai kallonta akeyi musamman takalmin dake k'afarta yafi komai jaan hankalin jama'a, itakam ko ajikin ta tafiyar ta take abinta lokaci² kuma tana duba kud'in da taci d'amara dasu a k'ugunta..........
Layi² takebi cikin kasuwar idan taga d'an garinsu saita yashe baki alamar taganeshi haka tayi taci gaba da kutsakai cikin kasuwar har Allah yakaita layin 'yan takalma duk takalman wajen na roba ne akwai silifas akwai sau ciki, babu magana kawai INDO ta fara iban takalmi nan fa tashiga gwada takalma tasaka wan nan ta cire wanchen, shikuwa mai takalmi ya zuba mata ido shi duk atunanin shi bata da hankali saboda sunsaba had'uwa da yara masu tabin hankali suna yawo a kasuwar, duk takalimin da INDO ta gwada baiyi mataba saita mayar ta ajiye shikuwa mai sayar da takalmin sai ya d'akko ya goge saboda duk wanda ta gwada saita shafa masa k'asa da maik'on mai wanda ta lafkowa k'afarta, hakadai tayi ta gwadawa harta samu wanda sukayi mata guda hud'u ta d'iba, biyu sau ciki(fillo toms) biyu kuma silipas nan tashiga k'ok'arin kunto kud'in da ta d'aure a k'ugunta gaba d'aya ta mik' masa kud'in bayan yaduba ne yaga tana da ragowar chanji ya bata chanjinta yasaka mata takalman aleda, anan tabaro takalmin GOGGO wanda tasako, ta d'auki d'aya daga cikin sabon da ta saya tasa ka ak'afar ta, daga wajen mai takalma INDO ba ta sake zuwa ko inaba saita nufi hanyar gida itakam buk'atar ta tagama biya burinta yacika..........
Sai bayan ta 'bace daga wajen san nan mai takalmin ya lura da ta bar takalmin datazo dashi ak'afarta sai ya d'iba ya ajiye mata wai kozata tuna ta dawo.........



Tunda GOGGO tadawo take neman INDO amma shiruu babu labarin inda ta tafi, abinda yafi Tsorata GOGGO shine tadda taga babu takalman ta dake k'ofar d'aki lallai hakan yanuna mata cewar INDO nisa tayi dan indai harba cikin gari INDO zata bariba babu abinda zaisa ta tasaka yakalmi a k'afarta, fatan GOGGO dai shine Allah yasa kar BAFFA yariga INDO dawowa saboda tasan lallai zaifita shiga damuwa......



Sai bayan da aka idar da sallah la'asar san nan INDO tashigo gidan su koda tashi bata samu kowaba, dan haka ta nufi d'akin BAFFA anan ta 'boye takalman da ta sayo san nan ta rufo masa d'akin tashiga gari....

Tuni GOGGO tashiga neman INDO gida-gida duk inda GOGGO taje sai ace INDO batazo ba harta gaji ga yamma tayi ko tuwo bata d'ora ba haka ta hak'ura ta dawo gida.




*_Ur's Hubbeey._*
[04/08, 21:53] Hubbey Frd Ameena Kn: *🚶🏻‍♀INDO K'AFAR YAWO*🚶🏻‍♀




*22/7/2018.*





*_STORY BY_*

*_AISHA MODIBO_*
*_(Indo k'afar yawo)._*



*_WRITTEN BY_*

*_HABEEBA IDREES_*
*_(Hubbeey)._*





*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.*




*ALLAHUMMA LAA SAHLAH ILLA MAJA'AL TAHU
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

1 Comments On INDO KAFAR YAWO
avatar
jamila-3-9

6 months ago

Reply

Lovely

Please Login or Register in order to submit comment