Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[09/02 12:01 pm] Sis Ummu Bashir: 🌹 *BA MU DACE DA JUNA BA*🌹

🌹

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader's📚)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *1~5*





*Cike* da tafiyar k'asaita ta fito daga cikin mota, tafiya take tamkar baza ta taka k'asa ba,Sanye take cikin English wears na riga da skirt,tayi rolling d'in k'aramin veil a kanta, ga Kuma sunglass da tasa. Fuskar ta a d'aure yake babu alamun dariya, yayin da driver yayi saurin bin ta a baya d'auke da briefcase d'in ta. Cike da tafiyar k'asaita ta Shiga parlour'n gidan Wanda ya tsaru ta ko'ina, Driver dake Bayan ta ya ajiye mata briefcase akan kujera, tare da cewa"Madam a huta lafiya"

Ko kallon shi ba tayi ba bare ta amsa mai, dama already ya Riga ya Saba da halin ta, kawai sai ya fita.


Wata Mata ce Tana da kyau,tana sanye da kayan alfarma ga gold a wuyan ta da hannayen ta, murmushi ta saki ganin y'ar nata tare da cewa"Lovely Daughter welcome back"

Zama tayi a kujera ba tare da tace komai ba, Matar k'arasawa tayi gurin ta idan da sabo to ta saba da Miskilancin y'ar nata, K'wala ma house maid Kira tayi, ko 5 minutes ba'a d'auka ba sai ga House maid d'in cikin rawar jiki tayi kneeling a k'asa,

Matar tace"hurry up and prepare my daughter's favourite food"

Cikin rawar jiki tace"ok ma" ta nufa wani Had'ad'en kitchen.


Kyakyawar budurwan ko ta kwantar da kanta kan kujera tare da lumshe idanun ta, Matar ta kalle ta tace" My daughter *NIHLA* hope you're okay?"

Wacce aka Kira da NIHLA cikin sweet voice tace"yeah Mom, I'm just tired" ta k'are cikin shagwab'a.


Shafa kanta tayi Mom tace" Sorry Daughter NIHLA, have your lunch first sai kije ki huta"


House maid ce ta shigo tare da sanarwa ta gama prepared d'in komai, mik'ewa tsaye NIHLA tayi ta Isa dining area kamar baza ta taka k'asa ba,



Fried rice ne with coslow sai ferfesun D'awisu, tare da juices kala-kala, house maid ce tayi serving d'in ta, NIHLA tana Fara cin abinci ta fito da shi tare da d'aukar plate d'in abincin gaba d'aya ta juyema house maid d'in a jikin ta.


A fusace tace"you are fired from this house, idiot do you want to kill me?"


Mom ce ta k'araso gurin tana cewa"what happened NIHLA?"

Tace"Mom gaba d'aya abincin yayi gishiri"

Cikin massifa Mom ta fara ma house maid fad'a tana cewa zata kashe mata 'Ya, house maid ko ta kasa motsi daga inda take tsabar ta tsorata.



NIHLA ko barin gurin tayi Cox ita bata jure hayaniya, wani bedroom ta Shiga Wanda ya tafi da tunani na tsabar kyau, komai na bedroom d'in orange and lemon green colour ne, tana Shiga ta cire kayan jikin ta tasa bathrobe tare da Shiga toilet, wow toilet d'in ma ya had'u, shi Kuma lemon green and white colour ne, cika bathtub tayi da ruwa tasa different performs na wanka, sannan ta Shiga, ta jima sosai tana wanka sannan ta fito inda ta nufa dressing mirror Wanda cike yake da kayan shafe-shafe da make-up, lotion ta shafa sannan ta nufa wardrobe inda Kaya suke a jere ta d'auko wani silk d'in doguwar riga white tasa, gashin ta Yana da tsawo sosai ga santsi, da k'yar ta iya d'aure shi da ribbon white colour, lipstick sai eyeliner kawai tasa sannan ta d'auko wayan ta Wanda tunda ta shigo bedroom d'in yake ringing.


Ganin number'n dake Kiran ta yasa ta jefar da wayar tare da kwanciya akan bed, wayar ko sai ringing yake,daga k'arshe offing d'in wayan tayi, sannan ta samu barci ya d'auke ta.



Around 8:00 pm


NIHLA na Danna system da alama wani aiki take, knocking taji inda aka bud'e k'ofar, Mom ce ta shigo tace" NIHLA your Dad he's back, ki fito"


D'aga kai kawai tayi, Mom ko fita tayi, sai Bayan 5 minutes ta tashi ta nufa parlour'n Dad d'in ta.



Babban mutum ne Yana sanye da medical glass, Yana duba wasu files, shigowa tayi ta zauna a kusa da kujeran da Mom take tare da gaishe shi, sai da ya ajiye files d'in tare da cire medical glass sannan ya amsa tare da cewa"Ya Maganar mu dake akan kawo min mijin da kike so?"



Shiru tayi tana kallon k'asa Dan tana bala'in tsoron mahaifin ta domin baya d'aukar Wasa da raini.

Ganin tayi shiru sai ya daka mata tsawa yace"are you deaf? Kar ki maida ni k'aramin mutum, lokaci yayi da zakiyi aure domin kinyi karatu har kin gama kin Fara aiki, to meye yayi saura Kuma bayan aure, na Baki 2 months ki kawo Wanda kike so but you refused to, me kike nufi ne?"


Cikin rawar murya tace"Dad please ka sake bani lokaci, zanyi k'okari"

Tsaki yayi yace"wannan shine last time da Zan baki chance, Nan da one week na Baki if not Zan had'a ki da wani"

A rikice ta d'ago kai ta kalle shi, daka mata tsawa yayi yace ta fita, ai ba shiri ta fita da sauri.


Bayan fitar tane Mom ta kalle Dad tace" please ka dinga yin Mata a hankali..."

D'aga mata hannu yayi alamun baya son jin komai.shiru tayi Dan tasan shi baya son maimaita magana.




NIHLA ko na Shiga bedroom ta fad'a kan bed tare da fashewa da kuka mai k'arfi, wayar ta ne yayi ringing ganin aminiyar tace ke Kira yasa ta d'auka, cikin tashin hankali aminiyar ta ke tambayar meke faruwa?


Tsayar da kukan tayi amma hawaye na zuba tace" *HUDA* what's should I do? I'm totally speechless"

HUDA tace"calm down NIHLA, fad'a min is everything okay?"

Tace" Akan lokacin da Daddy ya d'iban min ne, gashi time yayi, yanzu one week kawai ya k'ara min if not yace zai had'a ni da wani"hawaye ya zubo mata.


HUDA tace"oh come-on NIHLA, I've already told you that ki amince da *SABIR*, Kinga Yana son ki"

Cikin fushi tace"please ki daina min maganar wannan d'an iskan, how many times could I told you that I hated him, please kawai ki k'yale ni"



HUDA shiru tayi Cox tasan idan friend d'in ta tak'i abu to tak'i shi kenan har abada Haka Kuma idan tana son Abu to zata so shi har abada, Haka dai tayi ta bata hak'uri daga k'arshe sukayi sallama.




The following day


Yau NIHLA ta tashi da ciwon Kai ne, Cox jiya da daddare batayi barci ba sai tunanin maganar Dad take domin tasan shi kaifi d'aya ne, baya maimaita magana Kuma idan ya kafe kan Abu to ya kafe kenan.



Da k'yar tayi wanka ta shirya cikin wani Riga navy blue da black skirt but Yana da fad'i, sai veil black, da tasa Akan ta, handbag ta d'auka sai black hill shoe da tasa, ko make-up Ba tayi ba, Cox she's not in the mood.



Fitowa parlour tayi.................













*I'm back again my fan's*🤸🏻‍♀







*TAKU CE UMMU BASHEER*
[10/02 11:48 am] Sis Ummu Bashir: 🌹 *BA MU DACE DA JUNA BA*🌹

🌹

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader's📚)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *5~10*



*DEDICATED TO RAHMAT NALELE*



*Have this page is yours my lovely Aunty Rahmat, Allah ya kare ki daga sharin mak'iyya da mahassada Ameen, Allah ya k'ara basira da hazak'a k'warin ido tare da laushin hannu Ameen, keep the 🔥 fire burning, and more grace to your shining elbows, Ina yin ki, Ina jinki, Ina tare da ke 4ever, one love UMRAH,(UMMU BASHEER & RAHMAT).*

❤ heart you dear❤







*Fitowa* parlour tayi inda ta tarar da Mom and Dad suna breakfast, k'arasawa tayi ta gaishe su, Wata house maid ce daban tazo tayi serving d'in NIHLA, Dan an kora na jiya akan tayi abinci gishiri yayi yawa, pepper soup ne da chips with plantain, sai tea mai kauri Wanda yaji Ovaltine, sharp-sharp tayi breakfast sannan tayi musu sallama ta fito waje.



Driver na ganin ta yayi saurin taren ta ya karb'a briefcase tare da gaishe ta, as usual Bata answer ba, bud'e mata back seat yayi ta Shiga sannan ya rufe,tare da bud'e front seat ya ajiye briefcase d'in, suka d'auki hanyar office.




Lokacin da ta shigo office gaba d'aya mutanen gurin suka mik'e tsaye suna gaishe ta, d'aga musu hannu kawai tayi ta wuce, sectary d'in tace ta shigo ta ajiye Mata wasu files sannan suka yi magana ta fita, ba tare da wasting of times ba NIHLA ta fara aikin gaban ta.






Around 2:00pm in the office


NIHLA sai aiki take a system time to time tana duba wasu files, knocking akayi inda ta Danna wani abu alamar mai knocking ya shigo Cox ita bata jure magana.



Kyakyawan saurayi ne black handsome guy, ya shigo cikin kayan police, sai murmushi yake yin Mata, d'ago Kai tayi Dan ganin Wanda ya shigo ganin *SABIR* ne yasa ta cigaba da aikin ta Bayan taja tsaki.


K'arasawa yayi gaban ta ya zauna a kujeran da ke facing d'in ta yace"my pretty da alama aiki yayi Miki yawa, should I help you?"


Ko kallon shi ba tayi ba bare yasa ran answer, an d'auki tsawon 5 minutes kafin tayi magana da k'yar tace" idan ka gama magana zaka iya tafiya"


Gyara zama yayi yace"I'm not done yet, Pretty please you know I loved you, why can't you accept my love for you, ki amince muyi aure kinji mu haifa Kyakyawan Yara" ya k'are da murmushi.


A fusace tace"how many times Ina ce maka bana son ka, why can't you understand ne, duk matan garin Kaduna ka rasa wacce zaka ce kana so sai ni da ka Raina, kaje ko y'an matan ka, ka aura wata a cikin su but not me"


Murmushi yayi yace"pretty yanzu dai fad'a min why do you hated me?"


Mik'ewa tsaye tayi ta nuna hanyar fita tace" look SABIR just go"

Murmushi yayi yace"I'm going love but Zan zo gida later" ya fita.

Dafe kai tayi ta nufa fridge ta d'auko coke Mai sanyi ta zuba a glass cup tasha, sannan taji ta samu relief.







In the night


Kwance take kawai tana tunani, Mom ce ta shigo bedroom d'in, ganin halin da y'ar ta ke ciki yasa taji tausayin ta, k'arasawa gurin ta tayi tace"daughter ki dinga rage tunani Kar wani ciwon ya same ki"

Zama NIHLA tayi tace"Mom ya za'ayi in rage tunani Bayan kinsan one week kawai Dad ya bani, I'm confused" ta k'are kamar zatayi kuka.

Mom tace" I know what you're going through my daughter, kiyi hak'uri ko SABIR ne ki fitar a matsayin miji"

Tace"I don't loved him Mom"

Tace"nasan ni daughter but da ace Dad d'in ki ya had'a ki da wani fa, ai gara shi Kinga SABIR d'an aminin mahaifin ki ne, gashi can yanzu SABIR d'in a guest room Yana jiran ki"


Turo baki tayi tace" ni bana son ganin shi kice I'm sleeping"

Mik'ewa Mom tayi tace"no ba za'ayi Haka ba, ki shirya yanzu kizo ki same shi" ta bar bedroom d'in.





Da k'yar ta shirya cikin wani doguwar riga maroon colour na Swiss lace, wayyo fan's tayi kyau sosai, veil white ta yi rolling a kanta sannan ta fita.


Lokacin da yaga shigowan pretty d'in shi suman zaune yayi Cox ta had'u over, fuskar ta a d'aure ta zauna a kujera, yayin da House maid ta kawo juices and cupcakes.



An d'auki tsawon 10 minutes ba abin da sukace sai sannan SABIR yayi magana but ko kula shi batayi ba har ya gaji da surutun shi ya tafi, sannan ta Shiga bedroom ta d'auki phone d'in ta tana charting da HUDA, inda take sanar da ita abin dake faruwa ita Kuma tana Bata hak'uri.









*KANO STATE*





Wani Kyakyawan saurayi ne Wanda ba zai wuce shekaru ashirin da hud'u ba, sanye yake cikin riga red da jeans black, fari ne mai kyaun jiki irin mazan Nan ne k'arfafa, Yana da tsawo dai-dai, hancin shi siriri, fuskar shi d'auke da saje, Wanda ya fito da ainihin kyaun shi, Kyakyawan saurayi ne Wanda ke tashi yanzu, wani gidan k'asa ya Shiga tare da sallama.



Wata mata dake zaune akan kujera tana tuk'a tuwo,ta amsa,

Da Sauri ya k'arasa gurin ya karb'a mujiyan Yana cewa cikin murya mai dad'i" Umma na, ki Bari inyi" ya karb'a ya fara t'ukawa, yayin da tace" *JAMAAL* baka gajiya ne Kai da ka fito daga makaranta"


Murmushi yayi Wanda yayi bala'in kyau yace"Meyasa Zan gaji da aikin Umma na? In dai kece Umma na to bazan tab'a gajiya ba"

Murmushi tayi tana sa mai albarka.


Wata budurwa ce ta shigo gidan chocolate colour ce tana da kyau dai-dai gwargwado, tana shigowa ta tuntsire da dariya tace"Umma'n mu, kina kallon Ya JAMAAL sai fasa Miki tukunya? Waya yaga namiji da tuk'a tuwo" ta tuntsire da dariya.


Umma tace" neman albarka yake ai"

JAMAAL ko dariya yayi yace"yauwa Umma na ni kad'ai, " kinji kunya *RAUDAH* Umma ta fad'i gaskiya"


Wacce aka Kira da RAUDAH d'aure fuska tayi tace"Umma kin gan shi ko"

Umma dariya tayi tace"Kai idan ka gama bamu guri nida y'a ta"

Ai ko RAUDAH dariya tayi sosai, shi Kuma ya d'aure fuska ya mik'e tsaye yace"to ai sai ki k'arasa t'ukawa"

Zaro ido tayi dan ba abin da RAUDAH ta tsana irin aiki,bare kuma tuk'a tuwo, D'akin shi ya nufa, inda Umma ke dariya wato shima ya Rama kenan.


RAUDAH ko da sauri ta shararo k'arya Wai dama Aiken ta Maman ta tayi sai ta shigo gidan.


Umma ko ta gano ta dariya tayi tace ta tafi, sannan ta k'arasa tuk'a tuwon ta kwashe.




*TAKU CE UMMU BASHEER (UMRAH)*
[26/02 12:27 pm] Sis Ummu Bashir: 🌹 *BA MU DACE DA JUNA BA*🌹

🌹

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader's📚)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE* *10~15*




*DEDICATED TO AISHA ALI GARKUWA*


*Aunty Garkuwa wannan shafin naki ne, Ina yinki kamar yanda kikeyi na, Ina tare da ke a Koda yaushe tare da Miki fatan alkhairi, Allah ya raya su Basheer da Aysha mu ga Auren su,😍 Allah ya k'ara zumunci da k'aunar juna, ke d'in ta daban ce, ni UMMU BASHEER Ina yin ki sosai, Love you🍇 Allah ya k'ara basira da hazak'a Ameen*

*Karki damu ana mugun tare irin sosai d'in nan*🍇








*NIHLA* zaune take a office aiki yayi Mata yawa sai danne-danne take a system, sectary d'in tace ta shigo tana sanar Mata an taru ana jiran ta domin fara meeting.

Hannu ta d'aga alamar taji kawai, sai after 5 minutes ta Isa gurin meeting d'in, tana Shiga duk suka mik'e tsaye, sai da ta zauna sannan suka zauna inda suka fara gudanar da meeting d'in.


Bayan sun tashi meeting ne ta Shiga office take ganin 5 missed call, duk SABIR ne ya Kira ta, haushi duk ya cikata, ta zauna kenan ya k'ara Kiran ta, a fusace ta d'auki phone d'in.

Da sauri yace"luv hope you're okay? I called you but you didn't answer"

A fusace tace"wai Mai yasa ka cika takura ne? Please leave me alone, I've already told you bana son ka, then ka rabu da ni"

Jikin SABIR yayi sanyi yace"I'm sorry luv, I don't meant to hurt you"

Tsaki tayi tare da offing d'in wayan, SABIR ko bai ji dad'i ba.




Da missalin k'arfe 5:00 pm

NIHLA ce a kitchen sai shirya dinner suke ita da Mom domin ba kowani times ne house maid ke musu ba, Yam balls and chicken souce sukayi with Pineapple juice, daga Nan sukayi fruit salad,Dan kullum sai sunci fruit salad sannan suke cin abinci, domin hakan nada kyau Yana k'ara lafiya.


Bayan sun gama ne house maid ta shirya komai a dining table Sannan NIHLA ta wuce bedroom d'in ta, inda tayi wanka ta shirya cikin riga da wando pink and blue na Pakistan ko veil d'in Bata d'aura ba sai parking gashin ta tayi kawai, earpiece tasa a kunnen ta inda take sauraren music.


Garden ta nufa tare da kwanciya akan grass carpet ta lumshe idanun ta, ba ita tabar gurin ba sai da aka Kira sallan magriba, toilet ta shiga tayi alwala sannan ta fito ta d'aura veil d'in kayan dake jikin ta tayi sallah, a cewar ta baza ta iya saka hijab ba Yana sata Jin zufa.


Bayan Dad ya dawo aiki ne suka had'u sukayi dinner sannan NIHLA tayi musu sallama ta wuce bedroom d'in ta, sai Bayan tayi aiki a system sai ta kashe wuta tare da barin bedside lamp, tayi barci.








SABIR Koda yaushe Yana cikin Kiran NIHLA da zuwa gidan su Amma hakan bai sa ta bashi fuska ba sai ma ta gaya Mai bak'aken maganganu, yanzu lokacin da Dad ya bata ya cika gashi Kuma bata samu Wanda take so ba, ita Bata son yin auren ma at all. Lokacin da Mom ta Kira ta cewa mahaifin ta na Kiran ta sai da cikin ta ya murd'a tsabar tsoro, daurewa kawai tayi ta nufa parlour'n shi.



Tana Shiga ta gaishe shi, sannan ya gyara medical glass d'in shi yace"kinsan dai lokacin da na d'iban miki yayi ko?"

Cikin rawar murya tace"ehm..yayi ....lokacin Dad"


Yace"then ya maganar mu?" Akwai wani da Kika tsayar a matsayin miji?"


Tasan mahaifin ta kaifi d'aya ne shiyasa gaban ta ya fad'i tace"Dad kayi min hak'uri Dan Allah wallahi banda Wanda zan tsayar,Amma ka bani lokaci dan Allah"

A fusace ya mik'e ya mik'e tsaye yace"ni zaki maida k'aramin mutum? Ke har kin Isa tsabar rashin kunyar ki kice in baki time, are you out of your sense?"


Mom ce tace"Kayi hak'uri amma ni Ina......."

Katse mata maganar ta yayi ta hanyar d'aga hannu yace"this is stupidity, duk kece Kika b'ata yarinyan nan, komai take yi da sanin ki, dan haka bazan yi tolerating ba" ya bar parlour'n cikin fushi.


NIHLA fashewa tayi da kuka yayin da Mom ta rungume ta tana rarrashin ta.



Cikin kwana biyu hankalin NIHLA a tashe yake domin bata san wani irin hukunci Dad zai yanke mata ba, HUDA ce mai Mata nasiha da ban hak'uri, gashi SABIR ya nace Mata kamar maye a cewar ta.


Sanye take da English wears na gown maroon colour, tayi rolling d'in veil a kanta ga sunglass da tasa duk ya rufe rabin fuskar ta, light make-up kawai tayi, dawowan ta kenan daga aiki ta shigo gidan.




Tana Shiga parlour taji muryan mutane a parlour'n Dad, d'aga kafad'un ta tayi irin she don't care, Mom na ganin ta tace tayi lunch Dad nason ganin ta kafin Nan guests d'in shi sun tafi.



Bayan tayi lunch ne ta nufa parlour'n, ba kowa a parlour'n sai Dad, abin da ya bata mamaki shine ganin su goro da sweety, dayawa, gaishe shi tayi sannan tayi shiru.


Parlour'n ya d'auki shiru tsawon 5 minutes sannan Dad yayi gyaran murya yace"I know you'll be surprised, tunda na baki time ki fito da miji amma kin kasa to shine ni na zab'a Miki miji, D'an Aminina ALHAJI MUSTAPHA, wato SABIR, a yau ne aka sa ranar d'aurin auren ku Nan da 2 months!"



Tunda ya fara magana take zufa duk da sanyin A.C dake parlour'n, gaba d'aya ta rikice ta rasa mai za tace, she's totally out of her sense, da k'yar cikin rud'ewa tace"Dad kayi min Rai ka taimake ni, wallahi bana son SABIR"

Daka mata tsawa yayi yace"shut up, ni zaki fad'a ma Haka, in baki miji kice wai baki so, kina hauka ne after na baki chance but kin k'i kawo miji Kuma inyi Miki miji yanzu and you're telling me nonsense, tashi ki bani guri idiot kawai"


Da sauri ta bar parlour'n tana kuka, straight bedroom d'in ta, ta shiga ta rufe tare da fashewa da kuka kamar ranta zai fita.







*ASALIN NIHLA*


*NIHLA TAHIR* shine cikaken sunan ta, Kyakyawar budurwa ce y'ar kimanin shekaru ashirin da shida, 26yrs, Fara ce doguwa, tana da eyebrows masu kyau ga pink lips d'in ta gwanin ban sha'awa d'an k'arami, idanun ta farare tas.

Mahaifin ta cikaken d'an kasuwa ne, Yana zuwa k'asa-k'asa yin business, wani zuwa da yayi k'asar Misra anan ne ya had'u da RUKAYYA, mahaifiyar NIHLA, larabawa ne su, inda suka fara soyayya mai k'arfin gaske, iyayen RUKAYYA da k'yar suka yarda akayi auren da sharad'in zai dinga kawo ta, Haka Koh akayi Bayan Auren suka koma Nigeria, lokaci zuwa lokaci Yana Kai ta, sai Bayan sunyi aure da shekaru had'u Allah ya basu haihuwar y'a mace inda taci sunan NIHLA.



Kasancewar ta y'a d'aya gurin iyayen ta hakan yasa take zuba shagwab'a duk da mahaifin ta baya son yanda Mom ta shagwab'a ta, NIHLA Kyakyawar budurwa ce tayi primary and secondary School d'in ta anan Kaduna, sannan tayi University ta karanci business, Bayan ta gama Dad d'in ta ya malaka Mata d'aya daga cikin company d'in shi, ta fara aiki.



HUDA aminiyar tace tun suna secondary School har zuwa University sannan HUDA tayi aure, yanzu Haka tana da ciki, HUDA tana da kirki sosai,ita ma y'ar masu kud'i ce.



NIHLA ta d'auko wasu halayen mahaifiyar ta na k'in talaka, Bata son talakawa ga ta miskila

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment