Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son baby'n Nan"

"Ni ma Ina son ku duka"๐Ÿ’‹

Suman zaune yayi Jin furucin ta, "Wow my wifey dagaske kikeyi kina k'aunar mu"๐Ÿ˜

"I mean what I said, I loved the baby"๐Ÿ˜˜

Rungume ta yayi very tight cikin farin ciki.


Ni ummu basheer Ina ganin luv lokaci d'aya๐Ÿ˜‚.




Cikin sati d'aya sosai yake kula da ita da ririta ta ya shagwab'a ta sosai fa, Dan komai take so sai ya samo Mata, sunje hospital an tabattar musu da ciki 2 months take d'auke dashi, sunyi farin ciki ba k'adan ba.


RAUDAH da taji NIHLA nada ciki kamar zata mutu take ji, Nan ta yanke shawaran had'uwa da JAMAAL ta fad'a mai sirrin zuciyar ta.



"Ni gaskiya pounded yam nake son ci" NIHLA ta fad'a Haka cikin shagwab'a da k'ara kwanciya kan jikin JAMAAL.

"Duk abin da baby na ke so shi Zaki ci,oya Bari in je gurin Aunty Jameela in samo miki"

Kissing d'in forehead d'in ta yayi, ya Mata bye.

Fitowa yayi k'ofar gida kawai sai yaci karo da RAUDAH da zata shigo.

"Yauwa Yaya na dama Kai nazo nema"

"Ok ya akayi,Ina sauri ne Aunty'n ki na jira na"

Wani irin bak'in ciki taji,sai ta daure tace"dama ...Ina...son in ... fad'a ma.."

Katse ta yayi ta hanyar cewa"come-on ki fad'a min mene ne kin tsaya kina in Ina"


Daurewa kawai tayi tace"Yaya na jima da birne wani sirri a cikin zuciya na, nayi k'okarin ganin cire abin a raina Amma hakan yak'i yuwuwa, Na jima da kamuwa da ciwon so, Yaya ko kasan wa nake so?"

"A'a, wane ne?"

"Kai ne nake so"

A firgice ya kalle ta, "kin San me kike cewa?"

"Eh Kai ne nake so, Yaya Ina k'aunar ka, wallahi Zan iya mutuwa idan baka aure ni ba, Na jima Ina jinyar son ka, ka taimake ni ka so ni"

Gaba d'aya ya rasa Mai zaice Dan baiyi tunanin abin da zata fad'a kenan ba, gaskiya shi ya d'auke ta ne a matsayin K'anwar shi ba zai iya auren ta ba, kuma idan yace Yana son ta yayi k'arya.

"RAUDAH da farko dai Zan Baki hak'uri gaskiya na d'auke ki ne a matsayin K'anwa na, idan naje Zan aure ki to tabbas na Yaudare ki Dan ko k'adan bana k'aunar ki a zuciya na sai dai Ina Miki son y'ar uwa ta, kiyi hak'uri ki samu wani mijin kiyi aure, Kinga Ina son NIHLA Mata ta, bani da sha'awan k'ara aure, Mata d'aya ta ishe ni a rayuwa Dan Allah kiyi hak'uri Kuma zanyi Miki addu'a Allah ya Baki miji na gari"

Wani irin kuka ne ya taho Mata da k'yar ta iya dannewa, tace"ba komai Yaya, tunda har baka so na,to wallahi na hak'ura domin Ina son auren namijin da yake so na, nagode sosai" Nan ta shige gidan su, shi Kuma ya nufa gidan Aunty Jameela Yana mamakin RAUDAH, shi a gaskiya ma RAUDAH Bata cikin irin matan da yake so, Bata da shape Mai kyau gashi Bata son aiki, tana da k'azanta, gaskiya ba zai iya auren ta ba, bare yanzu NIHLA ita ce farin cikin shi.



Har ta fara barci taji dawowan shi, A hankali ya k'arasa gurin ta "baby I'm sorry har kin Fara barci Koh?"

"Uhm nidai please ka bani sakwaran Nan in ci har mafarkin shi nake"๐Ÿ˜‹

"Hoo baby har dreaming kike,oya zo inyi feeding d'in ki"

A kan cinyar shi ta zauna ya dinga Bata har ta k'oshi Tasha ruwa sannan ya rufe ta da blanket sukayi barci.





Saura sati d'aya JAMAAL ya tafi Canada, sosai yake mak'ale Mata Dan baya son rabuwa da ita, Kullum cikin kula da ita yake,yayin da take Jin wani irin mugun son shi a zuciyar ta, har mamaki take yanda take k'aunar shi.


Tana kwance kan kujera dake parlour'n Umma taji wata murya Wanda har abada baza ta manta ba, Muryan Mom take ji.


Mom ce ta shigo gidan cikin yatsina fuska take k'are ma gidan kallo, Umma ganin Babbar mace yasa tayi tunanin ko Y'ar uwa'n NIHLA ne Dan sune masu kud'i, cewa tayi"Hajiya barka da zuwa ga guri ki zauna"

Tsaki mom tayi "ke yanzu nayi Miki kama da wacce zata zauna anan?, Ina y'a ta take?"

A wannan lokacin ne NIHLA taji muryan Mom da gudu ta fito.

Umma tace"wace ce y'ar ki baiwar Allah?"

NIHLA na ganin Mom ta rungume ta cikin wani irin tsananin farin ciki, hawaye Mom tayi tana cewa"My daughter I can't believe you're leaving here"

Cikin hawaye tace"I really missed you Mom"

Umma tace"NIHLA mahaifiyar ki ce?"

"Eh Umma itace,Mom ga mahaifiyar JAMAAL"

Umma tace"Ah maraba lale bissmillah shigo daga ciki"

Tab'e baki mom tayi tace"ban zo Dan in zauna ba nazo d'aukar y'a ta ce"

Gaba d'ayan su a rikice suka kalle ta, lokacin Kuma yayi dai-dai da shigowan JAMAAL gidan yaji wannan kalmar daya firgita shi.

Umma tace"A'a Hajiya ba za'ayi Haka ba"

A fusace Mom tace"Dole ne in d'auki y'a ta yau Dan wallahi baza tayi irin wannan rayuwar na talauci ba, y'a ta tafi k'arfin ku"

Da sauri NIHLA ta rik'e hannun ta taja ta zuwa d'akin ta.


JAMAAL ne ya k'araso gurin Umma "Umma na ki taimake ni kar ki Bari a raba ni da Mata ta, wallahi Ina k'aunar ta"

Cikin kwantar Mai da hankali tace"karka damu ba abin da zai faru sai alkhairi"

Daga inda suke suna jiyo maganar su Mom, inda NIHLA ke cewa"Mom ya akayi Kika san Nan?"

"Daughter dole in bincike inda kike, tabbas mahaifin ki baiyi Mana adalci ba da har ya raba mu, ya hana in zo inda kike, da k'yar na samu Aunty Shuwerh ta bani address d'in inda kike,Dan kullum cikin yin mata waya nake Ina rok'on ta har taji tausayi na, Dan Haka dama nace Zan shirya plan, yanzu Zan tafi dake Misra Dan har nayi Mana visa, kije ki zauna gurin Ummie na, har sai nasa ya Baki takardan sakin ki"


Gaba d'aya ta tsorata da Jin furucin Mom, Haka ma su JAMAAL.

"A'a Mom kiyi hak'uri bazan iya binki ba, Ina son yin ma Dad biyayya a karo na biyu"

"What do you mean NIHLA,nazo ne fa Dan tafiya dake"

"Kiyi hak'uri Ina son Zama, Ina son miji na"

A rud'e tace"are you out of your sense NIHLA,do you know what you're saying?, Ko kin manta ke wace ce?,kece fa NIHLA TAHIR , kyakyawa Mai ji da kanta, kud'i da dukiya kina dashi, kina da company inda kike aiki, driver ke kaiki duk inda zaki, Shin duk kin manta ko ke wace ce a lokacin but look at you now, duk kin rame kinyi duhu, kalla kayan jikin ki, kalla fuskar ki, NIHLA what's wrong with you, kefa Kika ce Baki son auren, what happened?"


Cikin hawaye tace"mom I knew all that, na tuna ko ni wace ce Earlier,but now everything has changed, Mom yanzu ba nice NIHLA da Kika sani ada ba, Ni yanzu Mai kud'i da talaka basu ne a gaba na ba, duk Allah ne yayi su, tabbas Ada nayi kuskure da nake nuna jiji da Kai da nuna Isa, Mom ni yanzu Ina k'aunar miji na bazan iya rabuwa da shi ba, kiyi hak'uri kawai ki tafi"

"Anya ba suyi Miki asiri ba kuwa, Anya kece y'a ta NIHLA da na sani kuwa?I don't think so, NIHLA ki dawo cikin sense d'in ki, kisan me kikeyi"


"Mom Ina cikin hayyaci na nasan me nakeyi, Ina son miji na bazan iya rayuwa Babu shi ba, Kuma Ina d'auke da ciki"

A firgice tace"Ciki? Kina nufin ciki kike da shi NIHLA, da wannan yaron d'an talakawa?"


Cikin kuka tace"Mom please I'm sorry but just go, bazan iya binki ba"

A fusace tace"Yau nasan matsayina a gunki, daga yau Ina son ki d'auka na mutu, Baki da iyaye a duniya kiyi rayuwar ki keda talakawan da Kika zab'a" tana fad'in haka tayi waje.


Da sauri NIHLA tabi bayan ta tana cewa"Mom please wait, karki ce Haka"


Mom ko kallon su Umma batayi ba ta fita waje inda driver ke jiran ta, NIHLA ce ta bita da sauri Nan JAMAAL yabi Bayan ta Yana Kiran ta.


Shiga mota tayi yayin da NIHLA ke knocking d'in glass d'in window tana Kiran sunan Mom, ita Koh kawar da Kai tayi yayin da driver ya ja motar a guje, da gudu JAMAAL yayi saurin rungumar NIHLA saura k'adan motar ta ja da ita.


Kuka ta fashe mai da shi, Shiga da ita cikin gida yayi Yana rarrashin ta.


Haka Kaka wacce dawowan ta d'aga unguwa kenan, da Umma sai Bata hak'uri suke, Kuma yanzu JAMAAL ya tabatta da NIHLA tana k'aunar shi.





Har dare tana kuka shi Kuma Yana aikin rarrashin ta har ta hak'ura.




Cikin sati d'ayan Nan suna wani irin soyayya ne Mai zafin gaske domin wani irin shak'uwa sukayi da junan su. A yau ne JAMAAL zai tafi, NIHLA sai kuka take, Har airport driver ya Kai JAMAAL inda su NIHLA,Umma,Kaka da Abba suka raka shi.


Jirgin su ya tashi zuwa k'asar Canadaโœˆ

Yayin da ya tafi cike da k'aunar matar shi NIHLA,Haka ita ma suka juya gida cike da k'aunar mijin ta da kewar shi.







******************************



NIHLA cikin ta ya tsufa, haihuwa yau ko gobe, sosai Umma ke kula da ita, Haka Kaka ma, kullum cikin waya suke da JAMAAL, Yana Jin lafiyan baby'n shi. Ta b'angaren JAMAAL ma ya maida hankali sosai kan karatu ya gama ya dawo Dan ganin matar shi, y'an Mata dayawa na son shi amma basa samun ko kallon kirki, Dan Burin shi karatu. Yayi watsi dasu.




Ranar wata Friday ne NIHLA ta tashi da nak'uda tun abun Yana Mata k'adan-kad'an har yayi yawa, Umma ta Gane, ba tare da b'ata lokaci ba aka nufa hospital da ita, Dan dama JAMAAL Yana karatu Yana wani aikin ne acan Kuma Yana turo musu da kud'i, duk siyayan kayan baby ma shi yayi acan sai ya turo musu.


Cikin awa d'aya Allah ya sauke ta lafiya inda ta haifa yaro namiji Mai kama da mahaifin shi JAMAAL sak, carbon copy kenan inji ni Ummu Basheer.


Anyi taron suna inda yaro yaci sunan mahaifin NIHLA,suna Kiran shi da HANIF, yaro ne Kyakyawa, Haka NIHLA tayi wankan jego Mai kyau domin sosai Umma ta tsaya Mata, ta Zama kamar mahaifiyar ta, Haka HUDA na yawon zuwa. RAUDAH ko ta gaji ta hak'ura ta fito da miji tayi aure.



NIHLA ta cigaba da zuwa makarantar islamiyya sosai ta dage har ta sauke Al-QUR'AN, gashi ta k'ara kyau sosai, Dan ko suna cin abinci Mai kyau sannan Kuma ga tsafta, Koda yaushe JAMAAL cikin turo musu kaya yake har iyayen nashi ma, yanzu suna rayuwa cike da ban sha'awa.











"""""""""'''''''""""""""""""""""'''''''''''"""""""""""""""""





*Bayan shekaru Uku*

*After three years*


A yau ne ake ta Shirin dawowan JAMAAL daga Abroad, NIHLA ce na gani, Masha Allah nace, domin ba k'aramin kyau tayi ba gashi ta dawo yarinya k'arama baza ku tab'a Gane Tana da shekaru ba, wani Kyakyawan yaro ne d'an kimanin shekaru biyu yaje gurin Umma.


Dariya Umma tayi tace"Wato HANIF baka son wanka Koh"

Cikin maganar shi da Bai iya ba yace"Ci b'oye ni, ka Mommy ci gani"

NIHLA ce ta k'araso gurin "Let's go and bath,ai na gan ka"

Mak'e kafad'a yayi yace"A'a ban sho"

"Daddy'n ka zai dawo kazo ayi wanka kaji miji na Mai kawo cefane"cewar Umma cikin Wasa.


Da k'yar dai NIHLA ta d'auke shi tayi mai wanka, ta shirya shi cikin riga blue Mai check da ratsin white,sai white jeans, ta gyara Mai gashin shi Wanda yake kwance kamar na larabawa.



Abinci kala-kala ta shirya ma mijin nata, ga natural drink na fruit da ta had'a, gashi dama a shirye take domin ta gyara kanta sosai gurin Aunty Jameela. Fatar ta yayi smooth ga wani irin sihirtacen k'amshi Mai dad'in gaske da takeyi. Ko'ina na gidan kamar Koda yaushe k'al-k'al yake.








KANO STATE AIRPORT


Sanu a hankali yake saukowa daga stairs na jirgin, Kyakyawan saurayi ne kamar bature Haka yake cikin suit black,ga sunglass da yasa, a hankali ya shak'i k'amshin k'asar shi Nigeria, JAMAAL kenan Wanda dawowan shi kenan daga k'asar waje, Yana cike da Burin had'uwa da Matar shi da yaron shi tare da Family'n shi.



Wani driver ne yazo ya d'auke shi tare da mutumin Nan da yayi Mai komai na tafiya, inda suka gaisa, sannan suka nufa unguwar su JAMAAL.
















*Janih one love*๐Ÿ’˜







*UMMU BASHEER CE*




๐ŸŒน *BA MU DACE DA JUNA BA*๐ŸŒน

๐ŸŒน

{ *Short and interesting story* }



*NA*

*UMMU BASHEER*


ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_


#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



*PAGE 50~55*




*THE END*





*Happy Married Anniversary FATY AXLAND Allah ya k'ara dank'on so, Allah ya raya yaran ku, Ameen*๐ŸŽ‚


*UMMIE GARKUWA BOMB*๐Ÿ’‹






*JAMAAL* ne ya fito daga cikin motar tare da Shiga gida, Abba ne da Umma suka taro shi suna welcoming d'in shi, wani Kyakyawan yaro ya gani ya nufo shi, da sauri ya d'aga shi sama ya rungume shi Yana mamakin yanda yaron nashi yayi girma da wayau,Dan dama NIHLA na tura mai picture d'in shi, kissing d'in forehead d'in shi yayi, HANIF ko sai dariya yake, Shiga parlour'n Umma yayi inda suka k'ara gaisawa sai Abba yace ya tafi d'aki tukuna ya huta, Dan yasan Yana buk'atar ganin matar shi, NIHLA ko tana d'aki Kuma taji lokacin da ya shigo sai dai kunya ya hana ta fita.


Shigowa yayi da sallama da sauri da d'an gudu ta rungume shi da k'arfi har sai da jakan shi ya fad'i, hannun shi yasa ya rungume ta da kyau cikin missing d'in ta, gaba d'aya ya kasa hak'uri sai da ya had'a bakin su, sun Kai kusan ten minutes suna kissing d'in juna, sannan da k'yar suka dakata.


"I really missed you my baby"๐Ÿ˜˜

"Missed you too my Lion King"๐Ÿ‘„

Murmushi suka sakar ma juna sannan ta had'a Mai ruwa yayi wanka ya shirya,da kanta tayi feeding d'in shi har ya k'oshi.


A ranar mutane sai shigowa suke suna Mai barka da dawowa, RAUDAH ma tazo da mijin ta, tsohon ciki take dashi. Nan akayi Hira har suka tafi. Ita dai RAUDAH tasan tayi rashin JAMAAL namiji kyakyawa mai kyaun hali, Allah ya k'adara ba mijin ta bane.




A Daren ranar ansha amarci domin kamar first night d'in su, Haka JAMAAL yaji NIHLA kamar budurwa wacce bata haihu ba, sun nuna ma junan su zallan so da k'auna.



Washegari kayan shi suka iso inda ya ba kowa tsarabar shi hard dasu yaran Aunty Jameela. NIHLA ko saitin Akwati biyu yayi Mata, yace shine lefen ta da baiyi ba.




Cikin sati biyu sun shak'u sosai ga soyayyan da suke Sha, hmm ba'a magana Ga yaron su HANIF suna son shi.



*BAYAN SHEKARU BIYU*

JAMAAL ya samu aikin yi Kuma suna biyan shi albashi Mai tsoka, Dan sosai yake samun kud'i har yayi gini a Hotoro, ya gina gida mai shegen kyau flat ne babba da boys quarters, parlour'n su babba ne ga dining area, ga d'akin Yara da d'akin NIHLA sai wani parlour a gefe da bedroom shine na JAMAAL, sannan yasa an rushe gidan su anyi ginin zamani mai kyau, har gate ne a gidan da mai gadi.



NIHLA na d'auke da tsohon ciki yanzu, yayin da JAMAAL ke kula da ita sosai, tayi kyau tayi haske, Haka Kuma HUDA aminiyar ta, suna zumunci sosai.



"I'm back Honey, where are you?" JAMAAL ke fad'in haka lokacin da ya shigo cikin parkour.

Direct Kitchen ya nufa sai dai Bai ganta ba, bedroom d'in ta da toilet duk ya duba but she's not where to be found, da sauri ya nufa bedroom d'in shi inda yake tunanin she must be there.


Tana zaune kan bed ta had'a kanta da gwiwa sai kuka take. cike da rud'ani ya k'arasa gurin Yana cewa"Honey what's happening with you?"

A rud'e take sosai tana ganin shi ta rungume shi tare da fashewa da kuka.

"Oh Honey mene ne?, Koh labour kikeyi, mu tafi hospital" ya fara Shirin d'aukar ta.

Rik'e shi tayi cikin kuka tace"Dan Allah ka Kai ni gurin iyaye na, Ina son in gansu Ina son neman gafarar su, Ina matuk'ar k'aunar iyaye na Dan Allah ka Kai ni" ta fashe da kuka mai tsananin gaske.


Sosai ya tausaya mata, a hankali ya fara shafa bayan ta Yana rarrashin ta cikin kulawa da soyayya"baby karki damu Inshallah Zaki gansu, karki sa komai a ran ki, Idan kin haihu zan Kai ki"

Ture shi tayi a rud'e tace"A'a yanzu nake son ganin su, idan ba zaka Kai ni ba Zan tafi" d'aukar hijab tayi tasa zata fita.

Da sauri ya rik'o ta"calm down baby, Zan Kai ki, kinsan condition d'in ki yanzu, I'm sorry please just calm down"

"A'a ka barni Ina son ganin su, nayi mafarki ina binsu suna tafiya har sunyi min nisa, sai Kuma suka dawo kusa dani suna min murmushi kawai sai na farka, Ina son ganin su"ta k'are cikin hawaye.

Rungume ta yayi"It's nothing baby you'll meet again, kiyi shiru bana son kina min asaran hawayen ki"


A ranar da k'yar ta hak'ura zuwa gobe ya su tafi Kaduna, saboda yamma tayi lokacin.




Washegari da asubah ta gama shirin ta, kasancewar weekend ne sai barci JAMAAL yake.

Zama tayi kusa dashi tare da hura mai iska a kunne.

K'ara shigewa blanket yayi, "please baby I'm feeling sleepy"

"Please wake-up Sweet heart, have you forgotten that we're going to Kaduna?"

"I knew it baby but please let me sleep okay"

K'ara hura mai iska tayi a kunne ba shiri ya rungume ta ta fad'o jikin shi, lips d'in shi ya Kai kan nata tare da sucking d'in lips d'in ta, cikin Wasa ta ture shi"Sweetheart please wake-up"

Tashi yayi domin yasan idan Bai tashi ba sai ta fashe mai da kuka.


Bayan yayi wanka ya shirya sannan suka shiga had'adiyar motar shi, ya jasu zuwa Kaduna.



*KADUNA STATE*




Duniya kenan yau ga NIHLA a gidan su bayan shekaru kusan biyar da barin ta gidan kenan, ko'ina sai yayi Mata wani iri kamar ba gidan su ba yayi kyau sosai.

A parking lot yayi parking suka fito, d'aukar HANIF JAMAAL yayi tare da rik'e hannun ta suka nufa parlour'n gidan.


Zaune Dad and Mom suke suna hira cikin nishad'i, shigowan su JAMAAL ne yasa suka mik'e tsaye, Da sauri HANIF ya sauka daga gurin Baban shi ya nufa gurin Dad Yana cewa"Oyoyo Grandpa I miss you"

D'aukar shi Dad yayi tare da hugging d'in shi.


NIHLA ba k'aramin mamaki tayi ba, bare da taga JAMAAL na gaishe su da alama sun Saba da juna.


NIHLA durk'usawa tayi a k'asa tare da wani fashewa da kuka "Dan Allah Iyaye na ku yafemin"

Da sauri Mom ta d'ago ta tare da share Mata hawaye, "Dad d'in ki ya jima da yafe Miki, Haka Kuma har yau har gobe kina ran mu, nice Zan rok'i gafarar ki abin da nace Miki a baya ki yafemin daughter na, naji dad'i sosai daga baya lokacin da nayi nadama Ashe gara da Baki biyo ni ba" ta k'are cikin hawaye.

Rungume juna sukayi cikin farin ciki sannan ta k'arasa gurin Dad, shima rungume ta yayi Yana fad'in komai ya wuce.


Nan sukayi ta hira cikin nishad'i da anashuwa, har Dad na fad'in cewa ai JAMAAL tun bayan ya dawo Nigeria yake zuwa gurin su, Kuma har HANIF Yana kawo musu, har sun Saba dashi.

Tayi mamaki sosai Dan Bata tab'a sani ba.



Abin da bata sani ba komai na tafiyan JAMAAL zuwa k'asar waje da komai da akayi Mai, duk Dad ne yayi Mai wannan hanyar Kuma Abba ya sani shine ma ya fad'a ma JAMAAL har yazo yayi ma Dad godiya sosai.





Ai NIHLA tak'i yarda su koma KANO a ranar dole dai JAMAAL ya koma shi kad'ai๐Ÿ˜‚




Satin ta d'aya a gidan su inda JAMAAL yazo ya d'auke ta suka koma gida, Bayan dawowan ta da sati d'aya ta haifa yaro namiji Mai kama da JAMAAL, ranar suna yaro yaci sunan Abba IBRAHIM suna kiran shi da Abba k'arami. Mom da kanta ta zauna ma NIHLA har tayi 40 days sannan ta tafi,Bayan ta gyara Yar ta sosai.


Daren ranar ko JAMAAL ya dirje ta kamar kayan wanki๐Ÿ˜‚














*BAYAN SHEKARU BIYAR*



NIHLA ce na gani ta fito cikin wata had'adiyar mota Bayan driver yayi parking, d'auke take da wata Kyakyawan yarinya y'ar shekara d'aya.


Shiga gidan tayi tare da kwantar da yarinya wace take Shan barci,cire nik'ab da hijab tayi ta Shiga Kitchen. Bud'e fridge tayi ta Ciro nama Wanda yayi k'ankara ta d'auraye tare da Kuna Electric cooker ta d'aura, sannan ta Ciro vegetables Wanda already ta gyara duk ta yanka, ajiyewa tayi a gefe, sannan ta gyara kayan Miya tayi blending, ta d'aura Miya, sannan tayi white rice.


Vegetables soup with white rice tayi Bayan ta had'a ferfesun D'awisu tare da had'a juice na fruits, sannan ta shirya komai a dining table tayi wanka. Ta shirya cikin riga da skirt na English wears, Bayan tayi make-up.



Around 7:00pm


JAMAAL ne ya shigo gidan cikin black suit Yana rik'e da briefcase, da sauri NIHLA ta fita tare da hugging d'in shi then ta karb'a briefcase d'in.

Suna Shiga parlour yaji wani k'amshin turaren wuta mai dad'in gaske, K'aramar yarinyan nan Mai suna Ummul-kursum ya d'auka tare da kissing d'in ta Yana Mata Wasa, NIHLA tasan idan ta biye mishi sai ya kwana Yana Wasa da Ummul-kursum shiyasa ta karb'e ta yaje yayi wanka shima sai da ta Taya shi, sannan suka zauna a dining table Dan yin dinner, ciyar da junan su sukayi har suka k'oshi.


Around 8 :00 pm Yara suka dawo Islamiyyan dare Dan duk every Thursday and Friday suna tafiya islamiyya tun 3:00pm sai 8:00pm, driver ke Kai su Yana dawo dasu.


Kyakyawan Yara ne su hud'u dukan su maza suka shigo gidan suna sanye da Uniforms, gaishe da Iyayen nasu sukayi sannan suka nufa bedroom d'in su suka cire Kaya suka canza sai suka fito sukayi Dinner sannan NIHLA tace su d'auko Al-QUR'AN su karanta Mata Haddar su Dan ta k'ara biya musu. Bayan sun gama tasa duk su nufa bedroom suyi barci lokacin 9:00pm ne.


Sannan ta shirya cikin wasu nighties masu shegen kyau, ta feshe jikin ta da turare, tare da nufan bedroom d'in JAMAAL Bayan ta shirya Ummul-kursum cikin kayan barci sai k'amshi suke.


Tana shigowa yayi saurin rungumar su Baki d'aya tare da karb'an Ummul-kursum ya kwantar da ita, Cox tayi barci.

Rik'o hannun NIHLA yayi zuwa kan bed tare da rungume ta very tight Yana cewa"Ina ma Allah godiya da ya bani Mata ta gari, Ina matuk'ar son ki my lovely wife"๐Ÿ˜˜

Kissing d'in lips d'in shi tayi tace"Nima ina ma Allah godiya da ya bani Kai a matsayin miji, Ada nayi kuskure gurin cewa *BAMU DACE DA JUNA BA*, sai dai yanzu zance *MUN DACE DA JUNA* I love you sweetheart"๐Ÿ’‹




Cire mata riga yayi inda yayi arba da breast d'in ta a tsaye suke ba alamar kwanciya kamar Bata shayar da Yara biyar ba, cafko su yayi da bak'in shi ya fara Mata wani irin tsotso๐Ÿ™ˆ. Yayin da suka fad'a duniyar ma'aurata.









*Alhamdulillah*

*JANIH ONE LOVE ke muku fatan alkhairi*๐Ÿ’˜


*Anan na kawo k'arshen litafina Mai suna BAMU DACE DA JUNA BA Ina ma Allah godiya da na Fara lafiya na gama lafiya, Allah ya yafemin kuskuren da na aikata a wannan litafin, Allah yasa mutane su amfana da darasin dake cikin litafin Nan*





*Kamar yanda nace muku idan na gama wannan Zan cigaba da yin muku DANA SANI..... Inshallah Yana kan hanyar zuwa*


*Massoya litafai na Ina muku godiya sosai Ina sonku ina k'aunar ku a Koda yaushe, ku biyo idan Kun shirya*๐Ÿ’‹




*UMMU BASHEER CE KE MUKU FATAN AlKHAIRI*



*For comments only 07030865952*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment