Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan uwansa..
January mar Abdulhadi Mati ▶ DANDALIN LITTATTAFAN YAKI AND HAUSA NOVEL BY (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 12:
Yayin da sadauki dalƙus da jarumi saljam suka karewa kansu kallo tsaf kowanne na tunanin yadda zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa ba'a jima ba suka fara zagaya juna yaddakasan an tsikare su a tare suka ɗaga makamansu suka afkawa juna suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin baki zafinnama yadda kasan jikinsu ba na jini da tsoka bane wohoho!! Hakika wanda ya iya ya huta, babban goro sai magogin karfe gani yadda suke safkewa junansu azabar yaki ce tasa filin gaba daya ya dau shewa da tafi kowanne yana kiran sunan gwaninsa yana kodashi hakika su sadauki dalƙus da jarumi saljam sun cika jarumai wanda suka tumbatsa a fagen fama domin kowanne daga cikinsu ya himma tu da safkewa abokin karawarsa masifar yaki haka suka wanzu har tsawon sa'a hudu amma ga yan kallo kamar yanzu ma aka fara domin su wanan yakin yana nishadantar dasu sosai domin jarumtace ta hadu da sadaukantaka abinda ya ba jama'a mamaki shine ganin salon yakinsu da zafinnamansu yaxo daya yadda kasan malami daya ya koya musu yaki a haka suka wanzu har saida makamansu suka lalace ganin haka yasa suka rabu kowanne daga cikinsu yaja da baya yana mai maida numfashi saljam ne ya fara watsar da takobinsa da garkuwarsa domin sun jima da lalacewa sana ya fuskanci dalƙus yana mai dunƙule hannunsa hade da yin murmushin mugunta sana ya bude baki karo na farko yace da dalƙus tunda salon yakinmu yazo daya kuma makaman yakinmu sun lalace me zai hana mugwada "yar ƙashi nan take dalƙus shima yayi jifa da tagwayen addunan dake hannunsa hade da yin murmushi na yadda da kai "hm inda ba kasa ai nan ake gardamar kokowa cewar dalƙus nan take shima ya fuskanci saljam yana mai duƙule hannunsa lokaci daya sukayi kururuwa suka afakawa junansu suka wanxu suna mai kaiwa juna duka kafa da hannu lokacinne fa hankalin "yan kallo ya tashi domin ganin yadda suke jibgar junansu yadda kasan jikinsu ba na jini da tsoka bane babu alamun sassauci a tare dasu kowanne burinsa ya lahanta dan'uwansa kafin kace mai tuni sun hadawa junansu jini da majina da wuya tayi wuya gumu yayi gumu da kansu suka rabu suka ja da baya suna mai kallon juna kowanne daga cikinsu yana mai tunanin yadda zai illata dan uwansa kamar an tsikaresu suka fallo da gudu saida ya rage baifi taku ukku su haduba sai dalƙus ya daka tsalle ya tsallake saljam duk tsawonsa kafin ya juyone yaji...
INA YIWA KOWA BARKA DA JUMA'A ALLAH HADAMU DA ALKAIRAN DAKE CIKIN WANAN RANA
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 13:
Kafin jarumi saljam ya juyo ne yaji hucin tahowar wani abu a bayansa juyowar da zaiyi yayi dai-dai da saukar wani abu a mukamikinsa yadda kasan an janyeshi haka yayi "yar dungure har sau biyu sana ya baje a gasa ba kowane yayi masa wanan kyakyawan naushin ba face sadauki dalkus wanan bajinta da dalkus yayi ba karamin burge "yan kallo tayi ba nan take filin ya dau ihu, jarumi saljam ya shafa bakinsa ya ga yana yoyon jini hakan ce tasa ya fusata ya bugi kasa da hannunsa kafin sadauki dalƙus ya ankara sai gani saljam yayi a sama daidai kansa kafin yayi wani yunkuri tuni saljam ya sanya kafafunsa biyu ya bugi kirjin dalƙus yadda kasan an janyeshi haka yayi sama sai da yayi tafiya mai nisa sana ya fado kasa hakika dalkus yaji wanan dukan domin yana tari jini ya biyo baya nan take masoyan saljam suka dau ihu hade da tafi nan take saljam ya nufi dalƙus yana mai dariyar mugunta yana isa wajan da dalƙus yake kwance kamar gawa ya sukuya ya kamo kafar dalƙus ya jawo shi kasa ya kawoshi tsakiyar wanan filin sana ya kamo kafar dalƙus ta hagun ya sanya a tsakiyar ƙafafunsa yana yunkurin karyawa hakan tasa hankalin dalƙus ya tashi cikin karfin hali ya sanya kafarsa ta dama ya daki bayan saljam ya fadi can gefe yaje da fuska hakan taba dalƙus damar miƙewa cikin zafin nama kafin saljam yayi yunƙurin mike tuni dalƙus ya karaso yayi tsalle sama tun a sama ya rike kafarsa ta dama ya saita kafar saljam ya diro kanta jikake kats kashin ƙafar saljam ya karye saljam yayi wani irin ruri yana mai rike kafarsa data karye ya yunkura domin ya mike amma ya kasa nan take ya baje kasa hakan tasa filin ya dau shewa da ihun "yan kallo nan take wasu mutane su hudu sanye da fararen kaya suka shigo wanan filin suna rike da wani karamin gado suka sunkuci saljam suka dora a gadonan sana sukayi waje dashi hakan shike nuni da cewa dalƙus ne yayi nasara nan take dalƙus ya ɗaga hannun sa sama yana mai kwarara ihu nan take filin ya ƙara kaurewa da ihu da tafi masoyan dalƙus na kiran sunansa dalƙus, dalƙus.. nan take ƙofar wani daki ta bude dalƙus ya fada ciki yana dafe da ƙirjinsa.
Shigar dalƙus ke da wuya wanan dakin sai wanan alƙalin gasa mai kiran suna ya ƙara tashi yana mai cewa dalƙus ya haye zagaye na farko na wanan gasa, jaruman da zasu kara yanzu sune dodo zalƙim babban jika ga dodo kiryanu da dodo kalkus jika ga dodanniya afjagata uwar dodannin duniya take wata katuwarkofa ta bude abinda "yan kallo suka gani ba karamin firgitasu yayib

(IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 14.
Ba komai ne ya firgita "yan kalloba kuma ya dugunxuma hankalinsu ba face tozali da sukayi da mummunar jibgegiyar halittar da aka kira da dodo kalkus jika ga dodanniya abjagata uwar dodannin duniya tozali da dodo kalkus da "yan kallo sukayi ne yasa dayawa daga cikinsu musamman ma yara tsulewa da gudawa tsaffi kuwa fitsarine ya kuɓuce musu masu karfin haline daga cikinsu suka yunkura zasu gudu amma hakan bata samuba sakamakon tozali da dodo zalƙim da sukayi nan take suka ƙame waja daya razanar da sukayi ta farko ta daɗu hakan tasa wasu suka fara sumewa ganin haka yasa sarki nawwar saurin nuna wanan filin da yatsarsa hakan tasa wata ƙawanya ta haske ta bayyana wadda ta zagaye dilin gaba daya kamar gilashi hakan tasa "yan kallo fara dawowa cikin hayyacinsu tabba dodo kalkus da dodo zalƙim munana ne ajin farko girmansu ya wuce misali sanan ga tsawo da suke dashi dake barazanar kere doguwar katangar da ta zagaye wanan fili yadda kasan "yan biyu tsawonsu da girman jikinsu daya abin da kawai ya banbantasu shine shi dodo zalƙim yana da fiffike a bayansa sanan yatsunsa sogayene manne a jikinsu dogayan farata ne kamar takobi sai walkiya suke da alama wasasu yakeyi domin suna da kaifi da tsini matuka sabanin dodo kalkus wanda hannayensa hudu masu kama da na bil'adam a komani hannu yana rike da wasu miyagun tsafaffun takubba bakake bayyanarsu ce tasa jinsin dodanni ihu da kururuwa wanda hakan yasa filin yayi wata karamar girgiza lokacinne su dodo kalkus suka fuskanci juna hakika daga ganin yadda suke kallon juna karce tasan kar saida suka jima suna kallon juna kowanne daga cikinsu alamun shakku sun bayyana a fuskarsa karara domin wanan haduwace ta tantiran hatsabiban da suka buwayi duniya ma'ana dai babu wanda sunan sa bai shaharaba a duniyar mutane data aljannu kafin daga bisanni kamar an umarce su sukayi girgiza nan take mutane suka sha mamaki domin tsawonsune da fadinsu ya fara raguwa har saida tsawonsu da fadinsu ya komo kamar na bil'adam sana suka kwantsama wata uwar kururuwa sukayi tsalle suka afkawa juna...

BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 15.
Kururuwar da su dodo kalkus sukayi da takun sawayensu ne yasa kasar wajan ta fara girgiza da raurawa kamar zata tsage sai da ya rage baifi taku biyar ba su hadu sai suka daka wani wawan tsalle sukayi sama a samar suka ruguntsume da azababan yaki suka wanzu suna masu kaiwa juna sara da suka yawan kaikawo da suke a sama ne ya haifar da wata bakar guguwa badan wanan kawanyar haske da sarki nawwar ya samar ta tsafi mai kamar gilashiba da tuni wanan guguwa ta tada hankalin wanan fili yayin da gumurxu yayi gumurxu, naci da taurin kai da juriya ta hadu da kishiyarta sai abin ya kara muni domin kowanne daga cikinsu yaki yake iyakar karfin babu alamun saussauci a tare dasu kowa budewa abokin gwaminsa kofofin masifa yake idan faratan dodo Zalƙim suka hadu da tsafaffun takubban dodo kalkus sai kaga wani tartsatsin wata bakar wuta ya tashi tare da wani dunkulallen bakin hayaki wanda shikansa hayakin idan mutum ya shaƙeshi zai iya zama guba a gareshi yayin da masifa tayi yawa da kansu suka rabu dole kanwar naƙi domin kowa a cikinsu babu abinda yake sai maida nufashi hade da hucin fusata kafin su ja da baya suka ƙara kwarara wani sakaran ihu suka afkawa junansu saidai wanan karon fadan nasu ya sha banban da na baya domin wanan karon ruƙunƙume juna sukayi a sama sana sukayo kasa inda suka dira a tsakiyar filin gasar suka ruguntsume da wani azababban yaki mai taken ayita ta kare domin wanan karon kowa iyakar karfinsa yake yaƙar dan uwansa kowanne daga cikinsu ya wanxu yana juyewa dan uwansa dabaru da tsantsar muguta da masifar da suka jima ahlinsu na koyar dasu tabbas su dodo zalƙim yau sun nunawa duniya cewa su jinin dodanni ne domin kowanne daga cikinsu ya samu nasarar sarin ɗan uwansa amma abin mamaki maimakon jini ya biyo baya sai tartsatsin wutane ya tashi kamar sun sari mulmulallen bakin ƙarfe hakan tasa kowanne daga cikin su ya daka tsalle yayi baya yana mai kallon makaminsa da kuma abokin gwaminsa cikin tsabar mamaki da kaduwa domin dukkansu babu wanda bai yi imani da makaminsa ba sudai takubban da suke hannun dodo kalkus a wajan kakarsa dodanniya abjagata uwar dodannin duniya ya gajesu kuma tsafaffune wanda duk abinda ka sara dasu sai ya tarwatse ya ragargaje, su kuma faratan dodo zalƙim suma haka ahlinsu sunyi imani da cewa duk abinda suka sara da wanan farce nasu sai sun rabasa biyu, hakan ce tasa wanan dodanni ƙara fusata nan take kowanne daga cikinsu ya mayar da makaminsa hade da dunƙule hannu kamar an tsikaresu a tare....BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 16.
Idan ka kalli fuskar kowa dake kallon wanan bakin gumurxu musamman ma bangaren dodanni zakaga tsabar tsoro ne da fargaba ya mamayesu kowanne yana ganin idan akayi wanan haduwa za'a iya yin galaba a kan gwaninsa yayin da su dodo zalƙim suka kusan haduwa sai suka yi tsalle sama kowanne daga cikinsu ya ware hannayensa iya ƙarfinsa suka gabzawa juna naushi shi dodo zalƙim ya samu nasarar gabzawa dodo kalkus naushi a baki wanda hakan yasa hakoransa na gaba futar burgu daga bakinsa hade da wani dunkulalle jin shi kuwa dodo kalkus a ƙirjine ya samu damar gabzawa dodo zalƙim naushi wanda hakan tasa numfashinsa ya sarƙe yayi wani sarƙaƙƙen tari yayo kakin wani bakin jini hakan tasa wanan dodanni silmiyowa ƙasa kowanne daga cikinsu ya baje a ƙasa a galabaice suna masu maida lumfashi sama-sama hakika wanan duka da suka yiwa junansu ya galabaitar dasu matuƙa kamar an tsikaresu kowanne daga cikinsu ya doki ƙasa da hannunsa nan take suka taso sama suka dire da ƙafafuwansu hakan ne ya haifar da wata ƙaramar guguwa kamar ba su baneba dazu suke a galabaice ba suka ƙara runguntsumewa da azababen yaki suka rinƙa jibgar junansu kamar babu jini da tsoka a jikinsu sukarinƙawa junansu luguden duka hannu da ƙafa hakan tasa suka hadawa junansu jini da majina tun suna gumurxun a tsaye har suka durƙushe ƙasa suna mai turmusuwa a ƙasa haka sukayi ta juyi a ƙasa wanan ya danne wancan wancan ya danne wanan..BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 17.
Halin da su dodo zalƙim da kalkus suke cikine ya tada hankalin "yan kallo musamman ma bangaren dodanni domin dayawa daga cikin makusantan wanan dodanni sun fara zubar da hawaye domin sun sadaƙar cewa dolene a rasa ɗaya daga cikin wanan dodanni kokuwa ma a rasa su gaba daya a baɗini kuwa sarki nawwar yafi kowa razana da shiga tashin hankali domin idan har haka ta kasance tamkar an tarwatsa masa babban burinsane na duniya wanda ya shafe shekaru da dama yana tanadinsa amma duk wanan tashin hankali a zuciyarsa kaɗai yake idan kayi duba ga fuskarsa ma saidai kaga yana murmushi mai kama da na yaƙe.
Ɓangaren dodo kalkus da zalƙim kuwa abin yayi muni matuka domin ruƙunƙume suke da juna sun shaƙe wuyan junansu numfashinsu na ƙoƙarin ɗaukewa amma saboda tsananin baƙin naci da tsabar taurin zuciya babu alamun sassauci a tattare dasu domin kuwa kowanne daga cikinsu ya gwammace ya rasa rayuwarsa akan ya faɗi wanan gasa saboda tsabar gaba da cakwakiya tsamar dake tsakaninsu kai hadama ahlinsu domin kowa yana ji kuma yana ganin ahlinsu ne mafi ƙarfi da buwaya da maita haɗe da tsabar hatsabibanci da mugunta a jinsin dodanni hakance tasa kowanne ya zage dantse iyakar ƙarfinsa domin ya rinjayi abokin gwaminsa domi faɗuwarsu dai-dai yake da jawa ƙabilarsu abin kunya da gorantawa a cikin jinsinsu na dodanni .
Bangaren su dodo zalƙim da kalkus kuwa abin ƙara muni yake domin kowanne daga cikinsu ya fara jiyo ƙamshin mutuwa domin kuwa jajayen idanuwansu sun ƙara ja kuma sun fito fili yadda kasan zasu faɗo kasa hancinsu ya ƙara fadi sai wani baƙin hayaƙi ne ke fita fuskarsu ta ƙara baƙi da muni wanda da ace mace mai ciki zatayi arba dasu a wanan halin da suke ciki zata iya yin ɓarin ɗan dake cikinta saboda tsabar razana hakan tasa makusantan wanan dodanni fara yin magiya ga alkalan wanan gasa da su tsaida wanan gasa amma kash!! babu dama domin ƙaidar wanan gasa kenan duk tsanani idan aka farata babu zance a dakata sai wani ya samu nasara.
Shure-shuren da su dodo kalkus suka fara ne yasa "yan kallo fara ihu nan take sarki nawwar ya nuna su dodo kalkus da yatsa wata guguwar tayi futar burtu daga hannunsa ta fincike su dodo zalƙim tayi jifa dasu kowanne daga cikinsu aka watsar dashi gefe a sume tabbas badan wanan guguwa ba ta sarki nawwar da tuni sun jima da sheƙawa barzahu.
Ganin cillin da akayi da sune yasa ni fecewa domin kada a dawo kaina dan haka masu karatu saidai kuyi hakuri nima nayi takaina amma idan da masu rakiya sai suzo mu koma BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 18.
Yayinda wanan guhuwa tayi watsi dasu dodo kalkus a sume nan take wasu likitoci daga jinsin dodanni suka shigo da wani katon gado na ƙarfe suka sunkuci su dodo zalƙim suka yi wajen fili dasu sai lokacin ne jama'a suka lura da cewa dare ya fara domin rana tuni ta jima da faɗuwa hakance tasa wanan alƙali mai kiran sunaye ya tashi tsaye ya kafa abin magana a bakinsa sana ya fara jawabi kamar haka"A ƙa'idar wanan gasa ba'ayinta da daddare don haka duba da yadda dare ya fara zamu tsaida wanan gasa sai gobe amma bayan haka a gaban idanuwanku kunga yadda wanan karawa ta wakana tsakanin dodo kalkus da zalƙim dan haka a daren yau alƙalan wanan gasa zasu zauna su yanke hukuncin da samun matsaya akan wanan fafatawa nan take aka buga wani kuge wanda ke nuni akan dakatar da wanan gasa inda sarakuna da manya-manyan hatsabiban bokaye da attajirai na duniya suka fara mikewa tare nan take dakaru sauka zagayesu domin tabbatar da tsaro, tawagar sarki nawwar ce akan gaba sana sarki hammad, sai sarki laffaru da sarki alkasim sana gimbiya aryala sai sarki dujalu da mahraz da sauran alƙalan gasa da manyan attajirai, matsafa sai mutanen gari wanda kowanne daga cikinsu sai ya nuna wata alama wadda take nuni da cewa shi haifaffen garinne sana za'a barshi ya shiga wanan dokace wadda sarki nawwar ya sanya duk baƙon da yazo saidai ya yada zango a wajan gari akwai rumfuna marassa adadi da aka tanada saboda baƙin da sukazo wanan gasa a jikin katangar wanan tamkeken fili kuwa wani ƙatan babban gidane mai cike da kayan ƙawa da kayayyakin alatu na more rayuwa wanan ƙaton gida an tanadeshi don jaruman gasa indai mutum bai kasance wani hamshaƙin attajiri ko sarki shine kaɗai aka yadda ya shiga cikin gari.
Alamarin sarki nawwar kuwa yayi da ya shiga cikin garin ruma nan take sauran jama'ar da basu samu damar ziyartar wajan gasa ba suka rinƙa fitowa suna masu zubewa a ƙasa suna kwasar gaisuwa kowanne daga cikinsu fuskarsa cike da annuri domin suna matuƙar ƙaunar sarkinsu haɗe da matuƙar girmamashi saboda adalcin da yake nuna musu hade da matuƙar ƙaunarsu da yakeyi da nuna kishi a garesu wanan ce tasa suma suke ƙaunarsa da kishinsa. BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 19(BIRNIN RUMA)
Tabbas samun birni mai kyawu, tsari kamar birnin ruma sai an tona idan ka shigo garin babban abinda zai fara ɗaukar maka hankali shine babban hanyar da idan ka bita ɗoɗar zata kaika har fadar sarki nawwar gefen wanan hanya cike yake da filawowi koraye firensu mai ƙamshi da ɗaukar ido, babu abin birgewa da ban sha'awa sama da gineginen wanan birni wanda dukkansu iri dayane banbanci kawai shine iyakar wadatarka da dukiyarka iyakar benayen da zaka ɗora a gidanka wanan shine dalilin da yasa dogayen gine-gine suka yawaita a wanan birni babban abin burgewa kiwa shine kowata unguwa da kalar fentin da gidajen unguwar suke dashi wanda hakan ce ma tasa kowace unguwa ake kiranta da sunan fentin da gidajen unguwar ke dashi misali unguwar ja, unguwar fara, unguwar ɗorawa, unguwar da gidan sarautar wanan birni yake kuwa sune suke da gine-gine ruwan zinare wanda kuwa duk gidan da kagani a wanan unguwa to gidane na sarauta wanda wanan unguwa kaf birnin ruma babu unguwar da ta kaita tsari, kyawu da tsaro a gefen unguwar kuwa wani tafkeken shimfiɗeɗen filine wanda yake cike da shaguna kowani shago kuwa cike yake da kayayyaki na amfanin yau da kullun, kallo ɗaya zaka yiwa wanan ƙaton filin kasan shine kasuwar wanan birni wanda take ci kullum wanan ne dalilin da yasa mafi yawancin mutanen wanan birni "yan kasuwa ne wananne salilin da yasa kusan mafi yawancin mutanen dake wanan birni attajiraine, ɓangaren sadaukantaka da jarumta a kaf wanna daula ta rumawa babu garin da ya tara jajurtattun sadaukai, hatsabibai kamar birnin ruma hakama a duniyar tsafi sun yiwa sauran birane fintinkau wanan nema dalilin da yasa sauran daulolin dake maƙwabtaka dasu ke masifar tsoronsu kuma suke binsu sau da ƙafa.
Sarki nawwar ne a ƙuryar turakarsa tsaye yake yana ta kaikawo tun lokacin da sukayi ban kwana da su sarki alkasim kowa ya nufi masaukinsa dake cikin wanan gida shima ya nufi turakarsa yana zuwa alkyabbarsa kawai ya fidda yayi tilli da ita ya kama jiran bokansa amma har yanzu bai zoba wanan ne dalilin da yasa fuskarsa ta ƙara canzawa tsananin damuwane bayyane a fuskarsa ƙarara gyaran muryar da yaji ne yasa shi saurin juyowa bayan sa nan take yayi arba da boka nazara ne tsaye yana riƙe da wata sanda ta tsafi fuskarsa babu alamun annuri ko kaɗan wananne dalilin da yasa gaban sarki nawwar faduwa kenan tabbas abin da yake zato da tsammani na gab da faruwa.. KANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 20.(burin sarki nawwar)
Tabbas sarki nawwar ya girgiza da yanayin da yagani a fuskar boka nazara kafin ya fara magana ne ya ya tafa hannuwansa biyu nan take yanayin ɗakin ya canza iskar dake kaikawo ta canza ta koma wata tsaya cak komai na ɗakin ya koma kore cikin fargaba sarki nawwar ya tambayi boka nazara "ina fatan dai shirinmu bai tarwatse ba " sai lokacin boka nazara ya ya risina yana mai sakin fu skarsa ya mai duniya hakika shirin mu bai tarwatseba har yanzu yana kan hanya amma daga yanzu har zuwa gobe komai na iya faru ma'ana kowanne daga cikin wanan dodanni zaibiya rasa ransa yanzu na baro likitoci na jinsin dodanni sun duƙufa wajan ceto rayuwarsu don haka ba zamu ɗau wani mataki ba har sai munga mai gobe zatayi nan take boka nazara ya ɓace bat kamar bai taba wanzuwa ba shikuwa sarki nawwar futa yayi daga cikin turakarsa ya nufi turakar matarsa gimbiya shamila, shigarsa ɗakinnke da wuya ya isketa a zaune ta caɓa ado sanye take da kaya na alfarma wanda kallo daya zakayi wanan riga dake jikinta kasan ta isa jarin wani hamshaƙin attajiri kunnuwanta da wuyanta, hannayenta sanye suke da dankunnaye, awarwaro, sarƙa ta zinare tabbas shamila kyakyawa ce ajin farko domin samun mace mai kyawunta sai an tona wanan shiga da tayi shine ya ƙara fiddo tsantsar kyawunta jin shigowar sarki nawwar ce tasa gimbiya shamila ɗago kanta nan take ta tashi tana mai yiwa sarki nawwar murmushi nan take duk wata damu dake ran sarki nawwar ta yaye haka ake son duk wace mace wadda ta amsa sunanta ta kasance ga mijinta hakan na faru a duk lokacin da sarki nawwar ya shiga cikin bakin ciki da damu itace mai kwantar masa da hankali.
A can ɓangare guda kuwa alƙalan gasane suka haɗu dukkansu idan kayi duba sosai zakaga shaharu, sarki mahraz, sarki alƙasim, sarauniya aryala ne a manya-manyan kujeru sana sauran alƙalan wanda suke zaune akan ƙananun kujeru ana tattaunawa akan wanan fafatawa ta dodo kalkus da dodo zalƙim inda sarki alkasim ya tashi ya fara magana cikin girman kai da taƙama ba komai ne ya haɗamu anan ba face dan mu tattauna akan wanan fafatawa da akayi tsakanin dodo kalkus da dodo zalƙim dan misamu cimma matsaya kuma mu yanke hukunci akan abinda ya dace......

Wannan ebook din yazo muku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Domin jin karashen labarin sai ku cigaba day bibiyar shafinmu www.hausaebooks.com.ng


BAKANDAMIYAR GUMURZU
Kashi na Uku 3
Na Umar Abdulhadi Math
Ebook created by Shuraih Usman
Published at www.hausaebooks.com.ng







AKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 21.
Sarki alƙasim ya caba da bayani kamar haka dan haka yanzu idan da mai shawara a kan wanan zaman da zamuyi to muna jira sarauniya aryala ce ta tashi ta fara bayani dukkan mu mun jima da sanin cewa tun farkon duniya har zuwa yanzu idan har akayi ragas a tsakanin runduna ko jarumai biyu to wanan yana nuna ƙarfi yazo daya dan haka babu wani ɓangare da yayi nasara ko ya faɗi dan haka wanan hukuncin mai sauƙine dole cikin ɗaya ayi biyu imma dai a ƙara basu dama idan sun warke su ƙara fafatawa domin a samu wanda zaiyi rinjaye kokuma a idan sui
kowanne daga cikinsu a sauya masa sabon abokin gwami yayin da sarauniya aryala tazo nan a zancenta nan take ta koma mazauninta ta zauna.
Bayan "yar tattaunawa da alƙalan gasa sukayi ne suka yanke hukuncin za'a ƙara haɗa dodo kalkus da dodo zalƙim fada bayan sun gama jiyan raunukansu a haka wanan taro ya watse kowa ya koma masaukinsa.
Tun da asubahi filin gasa ya cika da mutane aljannu, dodanni ayau mafi yawancin "yan birnin ruma kowa ya halarci wanan gasa domin kuwa waɗanda basu samu damar zuwa wanan gasaba jiya yau sune gaba-gaba domin kuwa sunji labarin irin baƙin gumurxun da akayi jiya kowanne daga cikinsu ya ƙagu gari ya ida waye a fara wanan gasa gari na ida wayewa ne aka fara jin ƙaran tambura da algaitu wanda ke nuni da cewa sarki nawwar ne da jama'arsa ke tafe hakan tasa "yan kallo fara nutsuwa.
Shigowar su sarki nawwar ce tasa filin gabaki ɗaya yahau ihu haɗe da tafi domin kuwa shigar da su sarki nawwar sukayi tayi matuƙar burge ''yan kalla domin kuwa dukkan sarakunan wanan karon hadewa sukayi a tawaga guda dukkansu suna sanye da wasu irin riguna na alharini wanda akayi musu cin baki da ruwan zinare sanan suka ɗora alkyabbu farare hakan tasa ƙwar jinisu ya ƙaru ta yadda kallo daya mutum zaiyi masu ya gane cewa suncika hamshaƙan sarakuna wanda suka tumbatsa wajan tattalin arziƙi da girman masarauta har su sarki nawwar suka zauna a karagunsu "yan kallo basu daina taɓi ba zamansu ke da wuya sai wanan alƙalin mai kiran suna ya miƙe domin kiran waɗan da zasu fafata hakan tasa "yan kallo nutsuwa yadda kasan mutuwa ta gitta hakan kowa ya nutsu yana mai kashe kunne da sauraran sunan da za'a kira ba tare da ɓata lokaciba wanan alƙali mai kiran suna ya kafa abin magana a bakinsa sana ya fara magana yanzu ba tare da ɓata lokaci

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment