Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa wanan jarumai biyu ƙara fusata haɗe da tunxura, fusatarsu da tunzurarsu ce tasa wanan yaƙi ya ƙara caɓewa haɗe da cukurkuɗewa kowanne daga cikinsu ya ƙara zage dantse haɗe da buɗewa abokin karwar sa salo-salo na ƙofofin masifar yaƙi cikin baƙin zafin nama da juriya ta ban mamaki suke kaiwa junansu sara da suka haɗe da dukan junansu hannu da ƙafa duk wanda aka kaiwa sarako suka yana kaucewa ko ya kare kafin ya maido martani sai kaga an kaimasa duka da hannu ko da ƙafa amma saikaga kamar walƙiya ya kare ko ya kauce cikin ƙwarewa da bajinta saikaga shima ya maida raddi da masifa tayi masifa wanan jarumai sukaga iya yaƙi yana neman zuwa ɗaya sai kowa ya fara tunanin canza salon yaƙi domin ya samu damar lahanta ɗan uwansa ba tare da an kai ruwa rana ba hakance tasa kowanne daga cikinsu himmatuwa haɗe da ƙara zage dantse wajan safkewa dan uwansa salo-salo na masifar yaƙi ana cikin wanan turmutsutsu ne sai Basadaukiya ta shammaci sadauki salka ta daka wani uban tsalle haɗe da juyawa a sama sau ukku sana ta dire nesa kaɗan da inda sadauki salka yaja tunga sana ta gyara tsayuwarta jaɗe da yin murmushin mugunta hade da raini wanda yake nuni da cewa wuyar aiki ai bama 'a faraba domin wanan yaƙi da sukayi kamar sharar fagene, shi kuwa sadauki salka wani irin kallo yayiwa Basadaukiya wanda ke nuni da cewa "wai wanan yarinyar dame take taƙamane" ba'ayi auneba sai ganin Basadaukiya akayi tayi shiga tsalle sama haɗe da ware hannayeta kamar mai fukafiki haka ta sulmiyo ƙasa tayi di dirar mikiya akan sadauki salka, baiyi aune ba sai ganinta yayi a samar kansa kafin yayi wani kyakyawan yunƙuri tuni ta kawo masa wani bahagumen sara cikin baƙin zafinnama ya kare amma kafin ya ankara tuni ta sanya gwiwar ƙafarta ta masa wani wawan duka a fuska duk da yayi ƙoƙarin kaucewa amma sai da tayi nasarar samu gefen fuskarsa wananne yasa sadauki salka yaji wani azababben raɗaɗi ya ratsa masa ƙwaƙwalwarsa duk da haka abin bai tsaya nanba domin kuwa Basadaukiya wulƙila jikinta tayi haɗe da juyowa ta ƙara kawo masa walfta kamar shaho... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 34.
Kamar shaho haka Basadaukiya takaiwa sadauki salka safta duk da yayi saurin duƙewa haɗe da juyo hakan bai hana Basadaukiya samun damar yankanshi a kafaɗa ba kafin ta dire da ƙafafuwanta nesa kaɗan da inda sadauki salka yake, wanan tsananin jarumta da bajintar Basadaukiya ce tayi yasa "yan kallo wanda suka haɗa da alummar aljannu dodanni da mutane ihu haɗe da tafi su kansu hamshaƙan sarakunan da suke zaune a wanan fili saida sukayo mata jinjina domin ya burgesu matuƙa, shi kuwa gogannaka wato sadauki salka fusata yayi zuciyarshi ta ƙufulo gashin jikinsa ya mimmiƙe idanuwansa suka ƙara ja jijiyoyin jikinsa suka futo sukayi burɗa-burɗa idan ka ganshi a wanan hali da yake ciki zaka iya cewa yana ɗaya daga jikin manyan dodannin da suka halarci wanan gasa saboda gaba ɗaya ya rikiɗa cikin tsananin fusata da ƙunar rai ya shafa kafaɗarsa yaga jini cikin ransa yace tabbas ko yanzu aka raba wanan faɗa wanan tarin ar ta mani abinda babu wani sadauki da ya taɓa mani dan haka idan har ban mata kisan wulaƙanciba to bazan taɓa hucewa ba nan take ya gyara tsayuwarsa haɗe da wurgi da takobinsa yana mai yafito Basadaukiya alamun su gwada "yar ƙashi hakan tasa Basadaukiya ta fallo da gudu tana mai soke takobinta a jikin kubenta tana zuwa gab da sadauki salka ta daka tsalle da niyyar tayi masa ɓarin makauniya shikuwa sadauki salka tsawa yayi kyam yana kallonta sai ƙafarta tazo gab da sukarsa cikin baƙin zafinnama ya cafketa ya wulwulata sau ukku a sama sana ya fyɗata da ƙasa ya ɗaga ƙafarsa ya baketa saida tayi sama sana ta faɗo ƙasa cikin galabaita hannuta na dafe da ƙugunta ta yunƙura zata tashi amma ta kasa saboda tsanani buguwa da tayi nan take hankalin kowa dake wanan fili ya tashi murna ta koma ciki, sadauki salka ya nufi Basadaukiya yana tafiya cikin taƙama da fusata yana mai ɗaukar takobinsa haɗe da yi mata murmushin mugunta ganin irin murmushin da sadauki salka ke mata ne yasa ba shiri ta miƙe haɗe da ƙara zare takobinta domin ta tabbata in har ta bari sadauki salka ya isketa a wanan hali da take ciki kashinta ya bushe domin ranta kawai zai nema nan take ta ɗaga takobin ta ta buga wata uwar kururwa haɗe da fallowa da gudu hakan ce tasa shi (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 34.
Kamar shaho haka Basadaukiya takaiwa sadauki salka safta duk da yayi saurin duƙewa haɗe da juyo hakan bai hana Basadaukiya samun damar yankanshi a kafaɗa ba kafin ta dire da ƙafafuwanta nesa kaɗan da inda sadauki salka yake, wanan tsananin jarumta da bajintar Basadaukiya ce tayi yasa "yan kallo wanda suka haɗa da alummar aljannu dodanni da mutane ihu haɗe da tafi su kansu hamshaƙan sarakunan da suke zaune a wanan fili saida sukayo mata jinjina domin ya burgesu matuƙa, shi kuwa gogannaka wato sadauki salka fusata yayi zuciyarshi ta ƙufulo gashin jikinsa ya mimmiƙe idanuwansa suka ƙara ja jijiyoyin jikinsa suka futo sukayi burɗa-burɗa idan ka ganshi a wanan hali da yake ciki zaka iya cewa yana ɗaya daga jikin manyan dodannin da suka halarci wanan gasa saboda gaba ɗaya ya rikiɗa cikin tsananin fusata da ƙunar rai ya shafa kafaɗarsa yaga jini cikin ransa yace tabbas ko yanzu aka raba wanan faɗa wanan tarin ar ta mani abinda babu wani sadauki da ya taɓa mani dan haka idan har ban mata kisan wulaƙanciba to bazan taɓa hucewa ba nan take ya gyara tsayuwarsa haɗe da wurgi da takobinsa yana mai yafito Basadaukiya alamun su gwada "yar ƙashi hakan tasa Basadaukiya ta fallo da gudu tana mai soke takobinta a jikin kubenta tana zuwa gab da sadauki salka ta daka tsalle da niyyar tayi masa ɓarin makauniya shikuwa sadauki salka tsawa yayi kyam yana kallonta sai ƙafarta tazo gab da sukarsa cikin baƙin zafinnama ya cafketa ya wulwulata sau ukku a sama sana ya fyɗata da ƙasa ya ɗaga ƙafarsa ya baketa saida tayi sama sana ta faɗo ƙasa cikin galabaita hannuta na dafe da ƙugunta ta yunƙura zata tashi amma ta kasa saboda tsanani buguwa da tayi nan take hankalin kowa dake wanan fili ya tashi murna ta koma ciki, sadauki salka ya nufi Basadaukiya yana tafiya cikin taƙama da fusata yana mai ɗaukar takobinsa haɗe da yi mata murmushin mugunta ganin irin murmushin da sadauki salka ke mata ne yasa ba shiri ta miƙe haɗe da ƙara zare takobinta domin ta tabbata in har ta bari sadauki salka ya isketa a wanan hali da take ciki kashinta ya bushe domin ranta kawai zai nema nan take ta ɗaga takobin ta ta buga wata uwar kururwa haɗe da fallowa da gudu hakan ce tasa shi sadauki salka ɗaga addunansa biyu ya fallo da gudu yana mai ruri mai tsorata ƙanan sadaukai tabbas du wanda ke wanan fili ya tsorata da wanan haɗiwa da za'ayi saboda sunsan cewa idan har akayi wanan haɗuwa dolene a samu matsala.....
February 24 at 1:03 PM · Facebsadauki salka ɗaga addunansa biyu ya fallo da gudu yana mai ruri mai tsorata ƙanan sadaukai tabbas du wanda ke wanan fili ya tsorata da wanan haɗiwa da za'ayi saboda sunsan cewa idan har akayi wanan haɗuwa dolene a samu matsala.....
February 24 at 1:03 PM ·
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 36:
Haƙiƙa ba ƙaramin tashi hankalin waɗanan jarumai ba yayi ba komai yasa hakan ba face ganin wankin hula na ƙoƙarin kaisu dare hakance tasa kowanne daga cikinsu ya ƙara fusata kamar hadin baki nan take kowanne daga cikinsu yayi watsi da makamin dake hannunsa hakanna faruwa basadaukiya ta dunƙuƙe hannunta haɗe da kwantsama wata uwar kururuwa ta falfalo da azababban gudu tana mai tunkarar sadauki salka cikin mugunnufin ayita ta ƙare saboda tsananin ƙarfin gudu da take ne yasa har wani tashi sama take, ganin hakance tasa sadauki salka shima ya dunƙuƙe hannunsa haɗe da kwarara wata uwar kururuwa yana mai dukan ƙirjinsa da hannuwa biyu kafin ya fallo da gudu shima zuciyarsa cike take da mugunnufi suna kusan haɗuwa sai kowanne daga cikinsu ya dako uban tsalle yana mai kaiwa ɗan uwansa mugun naushi kowanne cikin zafinnama ya kare kafin su silmiyo ƙasa suna dira suka kacame da wani azababben yaƙi "mai taken ƙarshe tika tik" haka suka dunga jibgar junansu kamar jikinsu ba na jini da tsoka bane ana cikin wanan baƙin gumurzu ne sadauki salka ya shammaci badaukiya ya gabza masa wani mummunan nashi a ciki kamar a janyeta haka tayi tsalle ta tumu da ƙsa a can gefe tana mai dafe cikinta cikin galabaita domin ko numgashinta ma da kyar yake fita kafi ta dawo cikin hayyacinta ne sadauki salka ya ƙara dako tsalle daga inda yake ya ƙara shaƙar wuyanta yana mai ɗagata sama nan take ta fara wutsul-wutsul tana mai kakarin mutuwa tabbas wanan shaƙa da sadauki salka yayiwa basadaukiya bata wasa bace ya kalleta yana mai mata wani murmushi mai ɗauke da tsabar xunxurutun mugunta ya fara maga cikin izza ''hm haba yarinya waya faɗa maki ana zama wani a banza, azatonki a banza na buwayi sarskuna,matsafa,sadaukai da jarumai na wanan nahiyar tabbas a yaune zan zare maki numfashinki sai na miki kisa mafi muni wanda a tarihin duniya ba'a taɓa yiwa wani irinshiba yana zuwa nan a maganarsa ya ƙara shaƙeta nan take idanuwanta suks fito numfashinta ya sarƙe ta fara jiyo ƙamshin mutuwa ganin haka yasa alƙalan gasasuka fara shirin kaɗa ƙaraurawar da ke nuni da tsayawar wanan gasa sadai kash! Adaidai lokacinne sadauki salka ya jimƙe hannuwansa na hagu nan take wata koriyar wuta bayyana, bayyanar wanan koriyar wuta ce yasa kowa dake wanan fili ya tsorata yana mai dafe ƙirji domin duk wanda yasan labarin sadauki salka to yasan bala'in wanan wuta tasa domin da wanan sirri na koriyar wutane ya fitini sadaukan jinsin mutum, aljan, kai hadama dodanni ...BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 37.
Ganin wanan koriyar wuta yasa sarki nawwar saurin miƙewa kafin hannun sadauki salka ya isa kan basadaukiya tini sarki nawwar ya nuna sadauki salka da yatsarsa nan take wata iska mai ƙarfi ta suri sadauki salka ta yi hajijiya dashi sana ta damfara da ƙasa ganin hakane yasa yaran sadauki salka wanda suka shiga cikin "yan kallo suka saje dasu tashi tsaye haɗe da zare makamansu saidai kash basu samu damar ida nufinsu ba suka ja suka tsaya cak sakamakon tsawar da sukaji haɗe da rugugi inda ƙasa ta rinƙa girgiza kamar zata rufta ganakace taba filolin da suka tokare rufin da ya zagaye fadar fara zabtarewa suna danne "yan kallo duk wanan bai isaba bayyanar baƙar inuwar data lulluɓe dukkan filin ita ta ƙara sa "yan kallo durƙushewa inda wasu suka faɗi haɗe da dunƙulewa waje ɗaya cikin firgici da kaɗuwa haɗe da tashin hankali hakance tasa suka ɗaga kawunansu domin ganin masifar da ta haifar da wanan bala'i abinda suka ganine yasa su ƙara gigicewa haɗe da firgicewa wanda dayawa daga cikinsu saida sukayi danasanin ɗaga kawunansu sama da sukayi shikuwa uban gayyar wato sarki nawwar tashi tsaye yayi karon farko da tsabar tsoro da tashin hankali ya bayyana a fuskarsa ganin mawuyacin halin da mutanensa suka shigaba shiri ya tafa hannayensa nan take baƙin labulen da ya nannaɗe kansa tun farkon wanan gasa ya ƙara bayyana yayiwa "yankallo hijabi , sukuwa manyan gayyar ko a jikinsu wai an nyakushi kakkausa ƙara gyara zamama sukayi sadai dakarunsu da suka zo gabansu suka ja daga suna masu raba idanuwa saboda tabbatar da tsaro .... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 38.
Bakomai ne yayi sanadiyyar afkuwar wanan bala'in ba face bayyanar haɗaɗiyar baƙar rundunar da ƙunshi jinsin mutum dana aljan babban abin tashin hankali haɗe da firgici ga wanan baƙar runduna shine baƙin Ƙaton mummunan aljani dake jagorantar wanan baƙar runa domin duk wanda ya kwana ya tashi a duniyar hatsabibanci da jarumta to yasan aljani FARGAM aljani da baya domin baya da shekara sittin da biyu shike riƙe da kambun jarumtar na duniyar baƙaƙen aljannu tabbas dole sunan aljani fargam ya watsu a duniya idan akayi duba da irin gwagwarmayar da ya jima yanayi da hatsabibai, duk da sarki nawwar ya sanya shaki na labulayen tsafi tsakanin "yankallo da aljani fargam amma kallon farko da "yan kallo suka masa saida yasa dayawa dsga cikin sumewa masu ƙaramin ciki kuwa sukayi ɓarinsa, masu ƙarfin haline daga cikinsu ne suks durƙuce haɗe da ƙara dunƙulewa waje ɗaya tabbas kallon aljani fargam ma kanshi babban tashin hankaline ga ƙananun sadaukai cikin murya mai amo wadda take ɗauke da tsantsar amon izza da buwaya irin ta mazajen jiya ya fara magana cikin isa da taƙama "sarki nawwar mai daular ruma sarkin dake burin zama sarkin- sarakan duniya, tabbas ka ɗebo ruwan dafa kanka kaɗebo wa kanka aikin da yafi ƙarfin ka duk da cewa duniya ta shaida kaima sadaukine kuma hamshaƙin matsafi wanda ake damawa dashi a duniyar tsatsuba, amma kasani ba'a zama sarkin sarakai a banza kuma kana zaune a gida ko sarki sahibul kairi bai kai wanan matsayiba saida ya bar karagarsa, ƙasarsa, ya shiga duniya yayi gwa-gwarmaya da hamshaƙan baƙaƙen aljannu da mutane wanda suka amsa sunansu hatsabibai kuma gawurtattu kamar irinsu sarki BARUSA da matar sana ya kai wanan mataki sai kai kake tunani da sa rai cewa zaka taka wanan matsayi kana zaune a gida haƙiƙa kayi kuskure duk da cewa ka taɓuka wani abu saidai kuskurenka ɗaya shine da ka sanya yaudara da ha'inci a cikin lamuranka da bokanka wanan shine babban kuskuren da kuka tafka kai da bokanka... Happy juma'at kareem.BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 39.
Nasan zakayi mamakin ta yadda nasan wanan babban sirri naka duk da cewa kayi amfani da da layarka ta ɓata wajan ɓoye wanan sirri wadda a tunaninka idan har kayi amfani da ita kaf duniya babu wani mahaluki da zai iya wanan sirri naka wananne dalilin da yasa ka tara wanan hamshaƙan sarakunan da matsafa, jarumai daga sassa daban daban na duniya duk da cewa kowannensu saida yayi bincike akan wanan gasar kafin ya taho amma babu wanda ya samu damar ganin wanan sirri naka tabbas wanan sarƙa taka tana ɗaya daga cikin abubuwa biyar mafi daraja a duniya, hm!! amma idan kayi duba da matsayin da na taka a dunuyar tsatsuba wanan ba komai bane kasani shi ilimin tsafi kogine da kowa ke kamfato iyakar iyawarsa ba dole bane abinda na ɗakko yayi daidai da wanda ka ɗauko ba wanan ne dalilin da yasa tun lokacin da aka fara wanan gasa nake bincike akanta daga ƙarshe na gano akwai wani babban sirri dake ƙunshe da ita yayin da na matsa bincike sai na gano babu yadda za'ayi in gano wanan sirri sai na haɗa jinin jinsi huɗu na zubashi a kwatarniyar tsafina sana in haska wanan jinin da madubin tsafina sana inga wanan sirri gani hakane yasa na nazo wanan birni a sirrance na haɗu da aljana zabariyya, daga jinsin dodanni kuwa na nemo su dodo zalƙim, jinsin mutane na nemo sadauki saljam na musu bayani komai inda suka amince kowanne ya zuba jininsa a wanan kwatarniya tawa ta tsafi sana muka kamo wani bijimin zaki muka yankashi mua zuba jinin sa a wanan kwatarniya hakan na faru sai na fiddo maɗubin tsafina na haska wanan jini hakan na faruwa sai ga hotonka da na bokanka yayi da kuke tattunawa akan tsafin ds kake so ka haɗa wanda zaka zama sarkin sarakuna ka gallabi .mutum ɗa aljan daga wanda hakan bazai yiwuba har sai kun mallaki jini, ɓallen ƙashi, da haƙoran manya-manyan sadauksi da hatsabiban jaruman da suka gagari duniya a wanan zamanne kuka samu matsayar cewa zaku aika takardar gayyata zuwa ga sadaukai jarumai da manya-manya hamshaƙan sarakuna... (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 40.
Kai ya isa haka sarki nawwar ya dakawa aljani fargam tsawa cikin wata kakkasar murya mai cike da tsabar ɓacin rai da fusata haɗe da hasala idanuwansa sunyi jawur jikinsa sai tsuma yake karon farko da sarki nawwar ya fara magana cikin murya mai amo" Haƙiƙa ka cika hatsabibi Kuma tantiri da lokaci ɗaya ka tono babban sirrin da na jima ina ɓoyewa, ka cutar dani ka katse mani babban burina na duniya, hakika kayi nasarar tsaida wanan gasa ,saidai baka isa ka hanani cika wanan burin ba duk rintsi duk tsanani koda zatakaimu ga yaƙar juna sai na ida cika burina a yanzu na mallaki ballen ƙashin sadauki salka lokacin da aka karyashi a ƙafa, inada haƙorin aljana zabariyya yayin aljana zulma ta nausheta haƙorinta guda na gaba ya fita , ina da ɗigon jinin dodo zalƙim da dodo kalkus yanzu abin da ya rage shine in mallaki aɗigon jini shahararrun jarumai na guda ukku wanda suka fito daga dauloli ukku sune daular hindi,daular asiya,daular kisra, A yanzu haka ina da ɗigon jinin sadauki salka wanda kowa yasan hafaffen ɗan daular habasha ne sai kuma jini basaudakiya wanda ita kuma kowa yasan haifaffiyar daular rumawace, waɗanan dauloli sune dauloli mafi girma da ƙarfi, yawa da shahara a duniya idan har na kammala haɗa wanan abubuwane zan haɗa da jini na dana matata sana ina haɗa da farin ƙarfe mai daraja ta farko a duniya wanda ake haƙowa a ƙasar kogin nil wanda tuni na mallakeshi in sana'anta KARAGAR MULKI wanda duk wanda ya hauta sai ya shahara, ya tumbatsa, ya gallabi al'ummar mutane data aljannu kai hadama dodanni sai ya kafa tarihin da har duniya tanaɗe baza'a daina tunashi ba, sai ya kasance sunansa kaɗai aka faɗi sai mutum ya girgiza sai ƙowani sarki da ya shahara a duniya yazo ya durƙusa gabansa, sanan babu wanda ya isa ya hau karagar sai jinina... " kai!!! dakata ya isa haka sarki alkasim ya katse sarki nawwar cikin murya mai cike da ƙarfin izzar mulki da tsabar jarumta ya fara magana....




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment