Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba zamu fara wanan gasa ta gwarzon gwaraza yanzu jaruman gasar da zasu kara sune aljana zarma wadda akafi sani da RUWAN BALA'I tare da aljana zabariyya wadda akafi sani da TAURARUWA MAI WUTSIYA GANINKI BA ALKAIRI... Tsawar da alƙalin yaji ce tasashi dakatawa da ida maganarsa inda ya ɗaga kansa cikin firgici hakace ta faru ga duk mahalukin dake wanan filin nantake kallo ya koma sama domin abinda mutane sukayi tozali dashi ba ƙaramin firgitasu yayiba... BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 22.
Guguwar annobar da tashi sama ce itace tayi sanadiyar rikita filin haɗe da ƙara tada hankalin filin gaba daya abin zai baka mamaki idan nace duk wanan tashin hankalin da ke faruwa a wanan filin bai shafi wanan hamshakan sarakunan ba domin su ko a jikinsu domin kuwa guguwarma ko kusantarsu batayiba kamar tana jin tsoron su tabbas "yan magana sunyi gaskiya da sukace "wani darene jemage bai gani ba" kana kallon fuskokinsu maimakon kaga tashin hankali da razana su murmushi ma suke na isa da taƙama ba komaine ya haifar da wanan baƙar guguwar ba face kaɗawar fukafukan wanan shu'uman, tantiran baƙaƙen aljannun da suka gallabi duniyar aljannu domin kuwa sunansu yayi shura matuƙa kuma labarin hatsabibancin su babu inda bai kutsaba a duniyar aljannu tozalin da ''yan kallo sukayi dasu ne shine ya zame musu baban tashin hankali da firgici wanda hakanne yayi sanadiyar sumewar wasu daga cikin ƙanan yara da tsaffi wanda basu saba arba da aljannuba musamman ma wanda yau suka fara halartar wanan fili ganin abin dake faruwane yasa sarki nawwar yayi saurin nuna filin da yatsarsa nan take wanan ƙawanya ta haske ta ƙara bayyana ta zagaye wanan fili dif kamar ɗaukewar ruwan sama wanan tashin hankalin da baƙar guguwar da ta addabi mutane ta ɗauke lokacinne hankalin kowa ya dawo jikinshi.
A tare su aljana zabariyya suka sulmiyo ƙasa suka dira a tsakiyar wanan fili na gasa dirarsu ce tayi sanadiyyar tashin wata baƙar ƙura haɗe da wata ƙaramar girgizar ƙasa kamar haɗin baki suka juyo a tare suna masu fuskantar juna ganin bayyanar wanan hatsabiban aljannun ne yasa jama'ar aljannu ihu haɗe da tafi kowanne daga cikinsu yana kiran sunan gwanarsa yana koɗata wanda hakan ce tasa filin gasar ƙara rudewa kafin daga bisanni kowa yayi shiru yana mai maida hankalinsa kan wanan hataabibai biyu tabbas wanan haɗuwa itace ake kira da kar tasan kar domin kuwa wanan aljannu kowacce daga cikinsu ba ƙaramar hatsabibiya bace kuma ba ƙanan baƙaƙen azzalumai bane domin kuwa cikin ƙanƙanin lokaci sukan tarwatsa babbar ruduna ko ƙaramin gari na aljannu wananne dalilin da yasa hatsabibancinsu ya karaɗe duniyar aljannu kowa na fatan Allah ya kawo ranar da wani abu zai haɗasu a fafata domin a fidda wadda tafi hatsabibanci, jarumta, da ƙarfin dantse sai yau gashi sun haɗu a filin gasa tabbas aljannu sunfi kowa ɗauki da farincikin wanan haɗuwa wananne dalilin da yasa kowanne daga cikinsu ya murje idanuwansa da tattara hankalinsa da nutsuwarsa domin yaba idonsa abinci... AKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 23.
Kallo daya zakayiwa fuskokin jama'ar aljannu kasan cewa sunfi kowa dauki da zaƙuwar a fara wanan fafatawa domin ko nufashin kirki babu maiyi kowanne daga cikinsu ya zazzaro idanuwa yayi ƙuri ko ƙiftawa bashi so yayi dan kada ayi wani abun bai ganiba kallo ɗaya na musu bansan lokacin da na bushe da dariya ba domin tunawa nayi da "yar ƙuriga hakika ko kai mai karatu kagansu a wanan hali idan baka da tsoro baka sanin lokacin da dariya zata ƙwace maka domin wasunsu saura ƙiris idansu ya faɗo.
Yayin da aljana zarma ruwan bala'i da aljana zabariyya tauraruwa mai wutsiya suka fuskanci juna wananne karo na farko da suka fara haɗuwa gashi har zasu fafata kowacce daga cikinsu shakka ce ta hana ta afakawa "yar uwarta domin duk da basu taɓa haɗuwa ba sun san juna domin labari kowacce daga cikinsu babu inda bai zagayaba kafin su fara zagaya juna kowacce tana mai ji har cikin ranta cewa yau ta haɗu da gamonta ba'a jima ba suka fara zagaya juna suna masu ƙarewa juna kallo sai lokacinne suka lura cewa ai wanan filin gasar bazai ishesu su fafata ba hakance tasa kowacce daga cikinsu tayi girgiza nan take tsayinsu da girmansu ya ragu ya koma madaidaici hakan na faruwa kamar da haɗin baki a tare suka wangame baki suka kwarara wata uwar kururuwa wadda ta haifar da ƙaramar girgiza-gizar ƙasa wani dunƙulallen hayaƙi tare da wata baƙar wuta sukayi fitar burgu daga bakunansu suka tashi sama kafin su fallo da gudu wanda takun sawayensu kashi saida yasa ƙasa ta motsa kafin su haɗune aljana zarma ta zaro wasu tsafaffun baƙaƙen miyagun takubba inda itama aljana zabariyya ta zaro wani makami mai kama da lauje wanda saboda masifa da dafin dake jikinsa har wani tiririn baƙin hayaki ke tashi daga jikinsu a tare sukayi tsalle sama suna haɗuwa su kacame da azababban yake suna masu kaiwa juna miyagun harehare masu barazana fauce rayuka cikin baƙin zafinnama da azabar yaƙi cikin ƙwarewa kowacce take saraffa makaminsa tabbas "yan magana sunyi gaskiya da suka ce "wanda ya iya ya huta'' domin da kaga yadda suke sarrafa makamansu kasan sunjima ana damawa dasu a sama suke wanan faɗa amma saboda shawagin da suke haɗe da kaiwa da komowar da suke ne ya haifar da tashin wata ƙaramar guguwa tabbas waɗanan aljannu sun cika hatsabibai kuma shaiɗanu domin kowacce iyakar ƙarfinta take wanan yaƙi domin sunyi imanin cewa idan har sukayi sakaci to kwaf ɗaya za'a musu ba shiri suka dakata suna masu ja da baya taku takwas sana suka zubawa junansu na mujiya...
Febru BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 24.
Yayinda aljana zarma da aljana zabariyya suka zubawa juna ido kowacce babu abinda takeyi face hucin wani baƙin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinsu saboda tsabar fusata da kowaccensu tayi babu abinda kowacce take tunani wanda ya wuce ta yaya zata samu lagwan abokiyar fafatawar ta kamar an tsikaresu a tare suka ƙara fallowa da gudu suna masu ƙarajin fusata saboda tsabagen ƙarfin gudunsu har wata bakar guguwace ke masu rakiya suna haduwa suka ƙara ruguntsumewa da wani sabon azababen yaki wanda yayi sanadiyyar tashin hankalin filin gaba ɗaya a wanan karon kowacce da dukkan ƙarfinta take wanan yaƙin wanan ce tasa kowacce ta sauya salon yaƙinta suka haɗa da kaiwa juna duka da ƙafafuwansu haɗe da kai mazga da fuka-fukinsu haƙiƙa wanan karon abin ya ƙara muni matuka ana cikin wanan baƙin gumurzune aljana zarma tayi wani rimi sama tana mai kaɗa fuka-fukinta cikin azababban gudu tayi sama ganin hakanne yasa aljana zabariyya binta a baya amma kafin ta cimmata sai gani akayi tayi wani irin juyi a sama ta sulmiyo ƙasa kafin aljana zabariyya tayi wani yunƙuri tuni aljana zarma ta ɗaga wanan tsafaffun baƙaƙe takubbanta ta katawa aljana zabariyya wani wawan bahagon sara tabbas wanan jarumta da aljana zarma tayi ba ƙaramin burge "yan kallo tayiba nan take magoya bayanta suka ɗau ihu da tafi saidai kash abin da ya biyo bayane yasa murnarsu ta koma ciki domin kuwa ko ƙwarzane wanan takubba basuwa aljana zabariyya ba duk da taji saran har cikin ranta domin saida tayi wata ƙaramar ƙara haɗe da sulmiyowa ƙasa itakuwa aljana zarma tsabar mamakine tasa tayi kasaƙe tana mai kallon tsafaffun takubbanta domin a tsawon rayuwarta da yaƙe-yaƙenta da tayi bata taɓa samun saɓani ba irin wanan domin kuwa duk abin da ta sara wanan tsababbun takubba nata nantake take tsargeshi gidabiyu koda kuwa dutsine sai yanzune ta ƙara tabbatarwa da ta haɗu da gamonta idan har bata ƙara aage dantseba to tata tana gab da ƙarewa domin faɗuwarta a wanan gasa sa dai-dai yake da tarwatsewa kundin tarihin jarumatarta da shahararta a duniyar aljannu kuma wanan babban abin kunyane ga jama'arta kafin hankalinta ya dawo jikinta ne batayi aune ba sai ganin aljana zabariyya tayi a gabanta kamar an jefota ta zage iya ƙarfinta tayiwa aljana zarma wani kyakkyawan naushi wanda yayi sanadiyyar zubar mata da haƙoran gaba kamar an janyeta haka tayi ƙasa tim ta faɗo wanda hakan yasa ƙasar wanan filin motsawa. BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 25.
Filin gasar yayi shiru yadda kasan mutuwa ta gitta babu abin da kake ji face fitar lumfashin mutane, aljannu haɗe da dodanni idan kayi duba zuwaga "yan kallo wasu daga cikinsu tsabar damuwace fal cike da fuskarsu yayinda wasu kuma mamakine ya mamaye fuskarsu saidai wasu dagacikin "yan kallon tsabar murnace da farinciki yayi musu katutu a zuƙatansu kowa ya zuba tsakiyar wanan fili idanu yana mai cike da kokwanto.
Hannuwantane suka bara bayyana sana daga bisanni kanta ya fito fili hakan nna faruwa sai gangar cikita ya ida futowa daga cikin wawakeken ramin data samar a sanadiyyar naushi da aljana zabariyya ta mata ta silmiyo ta rikito daga sama ta faɗo kallo daya zakayiwa aljana zarma kasan ta bugu domin hannuta na riƙe da bakinta wanda yake yoyon jini hakan na faruwa filin ya ɗau ihu da tafi, mafiya yawan masu ihun da tafin suna yine domin ganin cewa wanan fafatawar bata ƙare ba domi dukkanasu sun rigama sun sare cewa aljana zarma zata iya miƙe har ta fuskanci aljana zabariyya wanda ƙalilanne daga cikin masu ihunne masoyan aljana zarma.
farkon abinda ta farayi bayan ta miƙe shine shafa bakinta da taji yana mata zogi da raɗaɗi tana duba tafin hannunta taga jini hakance yasa cikinta fara tsuma gashin kanta ya miƙe jajayen idanuwanta suka ƙara rinewa yadda kasan an zuba musu jini sana suka ƙara girma ƙofofin hancinta suka ƙara faɗi fuskarta ta ƙara baƙi yadda kasan an shafa mata shuni jijiyoyin jikita suka fito burɗiga-burɗiga kamar saiwar bishiya wani baƙin hayaƙi ya rinƙa futa daga cikin ƙofofin hancinta ta hangame baki tayi wata uwar kururuwa wadda saida tasa gabaki ɗaya filin gasar yin girgiza kowa dake wanan filin saida ya done kunansa haɗe da durƙushewa ƙasa saboda tsabar tashin hankali da kaɗuwa idan kafidda wasu ƙalilan daga cikin "yan kallo da malaman gasa, hamshaƙan matsafa da sarakuna wanda su ko a jikinsu domin su idan da sabo ma har sun sama domin sun jima suna baƙin artabu da azzaluman aljannu sa hatsabiban dodanni dan haka su wanan ihun ba baƙone ba a wajansu haƙiƙa aljana zarma ta fusata, fusatar da bata taɓayi ba domin a yau an rusa mata ginin tarihin jarumtarta wanda babu wani mahaluki da ya taɓa fitar mata da jini nan take ta fuskanci aljana zabariyya wadda itama tuni taja daga haɗe da dunƙule hannu tabbas a yanzune za'a fara waccan fafatawar kamar sharar fage ce.
Kai masu karatu gaskiya na firgita bazan iya tsaywa kallon wanan turnuƙu faɗan ibilisai sai na samu jaruman mazan da zasu iya kareni sabod KANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 26.
Ganin halin da aljana zarma ruwan bala'i tashiga ne yasa dayawa daga cikin "yan kallo tsurewa musamman jama'ar aljannu domin kuwa sun fi kowa sanin ko wacece ita. Ita kuwa gogar taka wato aljana zabariyya jinin jikita tasha nan take itama ta fuskanci aljana zarma tana mai dunƙule hannayenta biyu.
Aljanna zarma ta ware fuka-fikinta haɗe da kurma wata uwar kururuwa karo na biyu sana ta fallo da gudu tana mai tunkarar aljanna zabariyya ganin haka yasa itama aljanna kurma wani sakaran ihu haɗe da fallowa da gudu tabbas karo da dubu sai dubu ta taru domin kowacce a cikinsu idon ta ya rufe basu ganin komai aface azabar yaƙi saura taku biyar su haɗu kowacce ta daka wawan tsalle haɗe da buɗe hannayenta tun daga sama suka ruƙunƙume juna sukayo ƙasa sun faɗowa suka kacame da azababban yaƙi suka rinƙa jibgar junansu kqmar jikinsu ba na jini da tsoka bane haka suka wanzu tsawon lokaci kowacce aka nausa daga cikinsu sai tayi sama ta faɗo amma saboda baƙin naci da taurin zuciya sai kaga zumbur ta tashi ta rama haka sukayi ta tamola da kawunansu tare da yiwa junansu luguden naushi hannu da ƙafa ba'a jima ba suka haɗawa jinansu jini da maji suka wanzu sunaasu tanƙaɗi yadda kasan susha kwaya ana cikin hakane aljana zarma ta shammaci aljana zabariyya ta gabza mata wani uban naushi kamar an janyeta haka tayi sama sana ta faɗo tana mai bajewa a ƙasa cikin tsanani galabaita ta yunƙura zata miƙene ta ƙara ganin aljana zarma a gabanta kamar a zuƙota ta ƙara sunkutarta tayi hajijiya da ita a sama har sau ukku sana ta fyaɗata da ƙasa hakanne yasa aljana zabariyya tayi wata uwar tsiwa haɗe da dafe ƙugunta tayi yunƙurin miƙewa amma ta kasa nan take wani baƙin hawaye ya gangaro mata daga idannuwanta na takaici da baƙin ciki domin kuwa tasan tunda har ta kasa miƙewa to ta faɗi wanan gasa nan take alƙalan gasa suka kaɗa wata ƙaraurawa wadda take nuni da wanan karawa tazo ƙarshe nan take aljana zarma ta ɗaga hannayenta sama filin ya ɗau ihu haɗe da tafi dai-dai lokacinne kuwa wasu likitoci daga jinsin aljannu suka shigo wana filin suna ɗauke da wani gado na ƙarfe wanda ake ɗaukar marar lafiya suka ɗora aljana zabariyya akai sukayi waje da ita sunzo gittawa ta kusa da aljana zarma ne sai aljana zarma ta kalli aljana zabariyya tana mai mata murmushin raini haɗe da mugunta hakan ce tasa aljana zabariyya ta ɗago kai haɗe da tiwa aljana zarma wani irin kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa wanda aljana zarma ta kasa tantance ko mai wanan kallo yake nuf BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 28.
Yayin da aljana zarma ruwan bala'i ta fita daga filin gasa nan take filin yayi shiru kowa ya zuba ido haɗe da kashe kunne domin sauraren wasu jaruman gasa ne za'a kira, ba tare da ɓata lokaci ba alƙalin gasa ya tashi hannunsa na dama yana riƙe da wata doguwar takarda mai ɗauke da sunan jaruman gasa yayin da hannunsa na hagu yake riƙe da bututun magana nan take ya kafa wanan bututun magana a bakin sa ya fara magana masu gasa na gaba sune sadauki salka baƙin dutsi zai fafata da jaruma nuriyya basadaukiya nan take filin yayi shiru kowa ya ware idanunsa domin ganin wanan jaruman gasa, fitar burtun da wani baƙin mulmulallen ƙatone yayi zuwa tsakiyar wanan fili yasa hankalin kowa dake wanan fili ya koma tsakiyar wanan fili tabbas sadauki salka yaci sunansa baƙin dutse domin kuwa surar jikinsa ce zata tabbatar maka da hakan domin kuwa illahirin jikinsa a murɗe yake yadda kasan an jera masa baƙaƙen duwatsu fatar jikinsa kuwa baƙa ce siɗik gashi da tsawo da kauri mummuna ne mai jajayen idanu da ƙaton hanci sanan da zai buɗe bakinsa zaka iya rantsewa da cewa ƙara masa girma akayi tabbas duk jarumtarka idan kayi arba da sadauki salka dolene gabanka ya faɗi kallo ɗaya zakayi masa kasan ya cika sadauki kuma hatsabibin azzalumi wanda hakan ya jima yana zaluntar bayin Allah.
Tozali da wanan garjejen ƙato da ''yan kallo sukayine yasa dayawa daga cikin "yan kallo dafe ƙirji haɗe da ajiyar zuciya domin duk wani bafatake dake kasuwanci a wanan nahiya ta rumawa to ya jima da sanin ko wanene wanan baƙi ƙato domin idan bai taɓa tareshi a dajiba to yaransa sun taɓa tareshi domin kuwa sadauki salka shine shugaban "yan fashin dake wanan nahiya gaba ɗaya ya gallabi sarakuna matsafa da fataken da kaikawao a wanan nahiya domin shi garƙami ne wandon ƙarfe kuma kiciɓus ake dashi mugun gamo a kowani lokaci zaka iya haɗiwa dashi kuma kowa yayi karo dashi sai yayi asara idan baiyi ta rai ba yayi ta dukiya tabbas mafi yawan mutanen dake wanan fili sunyi mamakin ganin wanan. Y (IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 29.
Tabbas mafi yawancin mutanan dake wanan dake wanan fili sun girgiza da da ganin wanan taƙadirin, hatsabibin ƙasurgumin ɓarwon da ya buwayi wanan nahiya ta rumawa gashi yanzu ya bayyana a matsayin jarumin gasa kuma zai kara da mace kowa ya zuba masa idanu yana mai ƙaremasa kallo domin wanan ne karo na farko da ya ayyana kanshi gashi har za'a haɗashi faɗa da mace idan ka dubi fuskokin dayawa daga cikin ''yan zakaga wasu tsabar tausayin wanan jarumar ce a fuskokinsu duk da bata bayyanaba kuma basusan kowacece ba amma kawar da baƙin azzalumi kuma taƙadiri wanda ya jima yana hallaka dukiyoyi da rayukan al'umma kamar sadauki salka sai dubu ta taru in dubu ta tarun ma sai an kai ruwa rana tabbas wanan jaruma yau zata haɗu bala'i haɗe da masifar yaƙin da bata taɓa ganiba yayin da buskokin wasu suke ɗauke da tantsar, tsantsagoran tsana haɗe da baƙin ciki wanda mafi yawancinsu manyan attajiran "yan kasuwane wanda sadauki salka yayi musu sanadin rasa dukiyarsu, wani sashe na jikinsu, masoyansu, kai hadama lafiyarsu tozali da sadauki salka ne ya fama musu ciwon da ya jima a cikin zuciyoyinsu tabbas sun jima suna addu'ar akan Allah ya kawo sanadi ko haɗarin da zai kawo ƙarshen sadauki salka yayin da kuma wasu tsabar tsoro ne ya mamaye zuƙatansu na tozali da mummunar fuska da surar jikin sadauki salka wanda mafi yawa ƙananan yara ne da tsaffi babban abin tashin hankali ma shine tunda ya shigo wanan fili babu abin da yake sai zare jajayen idanunsa haɗe da huci kamar baƙin kumurci shi ko ɗan ɗagawa "yan kallo hannuma baiyi ba tabbas sadauki salka ya zama guguwar annoba a duk wanan nahiya.
Bayyanar kyakyawar matshiyar jarumar ce tasa hankalin "yan kallo tashi kamar tsuntsu daga kan sadauki salka zuwaga wanan kyakyawar jaruma wadda aka kira da basadaukiya tabe take fuskarta cike take da annuri da murmushi yanayi tafiyar da take kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa cikakkiyar jarumace kuma basadaukiya domin tafiya take irin ta mazan jiya.. BAKANDAMIYAR GUMURXU.
Chapter 30.(Basadaukiya & sadauki salka).
Bayyanar kyakyawar matashiyar jarumar da aka kira da basadaukiya ce tasa filin gaba ɗaya ya kaure da ihu da tafi mafi yawancin masu tafi da ihun mutanen birnin ruma ne tozali da basadaukiya da sukayine yasa zuƙatansu suka samu nutsuwa nan take fuskokinsu suka canza daga tsananin fusata da baƙinciki zuwa tsabar farin ciki da annashuwa tabbas sunsa rai kuma suna kyautata zston yaune burinsu zai cika ga mai share musu hawayensu tazo bakomaine ya kawo wanan baban canji a wanan fili ba face bayyanar basadaukiya dirkar birnin ruma.
Jaruma nuriyya itace ɗiya ƙwara ɗaya a wajan sarkin yaƙin birnin ruma mai suna fargam tabbas matsayin da yyake kai ya cancanta dashi domin tsabar jarumta, bajinta, hatsabibanci, da yake dasu yasha baƙar wahala kafin ya taka wanan matsayi yayi abubuwan al'ajabi da dama lolacinsa sana daɗin daɗawa adaline mai kyawawan halaye wananne babban dalilin da yasa ya shahara gabaki ɗayan mutanen birnin ruma suke matuƙar ƙaunarsa.
''Yan magana sunyi gaskiya da sukace barewa bata gudu ɗanta yayi rarrafe domin kaf halayen sarkin yaƙi da tsantsar jarumtarsa da bajintarsa babu wanda jaruma nuriyya bata gadoba tun tana "yar shekara biyar mahaifinta yake bata horon yaƙiai tsanani lokacin da takai shekara bakwai ya fara fita da ita wajan yaƙi tun lokacin takan iya shiga cikin turmutsutsu na yaƙi ta fita lafiya tabbas dayawa daga alummar birnin ruma sun sallama da cewa tafi mahaifinta komai wanan nema dalilin da yasa ake kiranta da BASADAUKIYA babban abinda jaruma nuriyya ta tsana aduniya shine zalunci da azzalumai wananne dalilin da yasa tun tana ƙarama take bincike akan sadauki salka kuma taci alwashin ganin bayan sadauki salka amma hakan ta gagara sunsha yin baƙin artabu haɗe da gumurxu a dazuzzuka daban-daban amma babu wanda ya samu nasara a tsakaninsu saidai su jigata juna haɗe da yiwa juna mugayen raunuka sai sun ga mutuwa ƙarara sana suke rabuwa kowa yaje yayi jiyar rauninsa wanan ne dalilin da yasa ayau aka haɗasu a wajan wanan gasa kuma dukkan wanan abu shirin basadaukiya ne domin ita taje wajan alƙalan gasa ta nemi alfarmar a haɗata da sadauki salka a wanan gasa dole tasa alƙalan gasa sukayi mata wanan alfarma saboda girmanta da darajarta a wanan birni wananne ma dalilin da yasa aka haɗasu faɗa yau domin ayita ta ƙare a gaban mutane.
Rataye take da wata zabgegiyar takobi jinkinta yana sanye da baƙin sulke ta tubƙe dogon gashi ya zubo har gadon bayanta ..


Wannan littafin yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Domin samun cigaban littafin sai ku cigaba da bibiyar shafinmu

BAKANDAMIYAR GUMURZU
Kashi na hudu 4
Na Umar Abdulhadi Mati
Ebook created by Shuraih Usman
Published at www.hausaebooks.com.ng









(IBNI ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 31.
Tungar da Basadaukiya taja a gaban sadauki salka shine yayi sanadiyyar tashin wata matashiyar ƙura tsayuwa tayi irin ta sadaukai mata hannunta na dama na riƙe da zabgegiyar takobi ta ɗorata akan kafaɗarta yayin da hannunta na hagu ke riƙe da faffadan madaidaicin ƙugunta ta zubawa sadauki salka daradaran fararen idanuwanta tana mai masa wani irin murmushi mai nuna tsantsar yadda dakai, haɗe da raina abokin gaba.
Karon farko da ta buɗe baki ta fara magana cikin wata zazzaƙar murya sadauki salka baƙin dutse ko? To yau ko baƙin ƙarfe kake ni basadaukiya naci alwashin sai na ladabtar dakai ayaune watan jin kunyarka ya kama, ayau sai ka amshi hukunci na zaluntar ba'yin Allah da ƙwace musu dukiyoyi da kakeyi tabbas kai gagarabadau ne a wanan nahiya tunda ka gagari sarkuna, attajirai, matsafa, da sadaukai, ka maida dayawa daga cikinsu marayu wasu kayi sanadiyyar karyewar tattalin arziƙinsu dan haƙa ayau ni Basadaukiya sai na ɗaukar musu fansa saina sa zuƙatansu farin ciki saina sa ka zama abin dariya ga alummatai dake wanan nahiya saina... Tsawar da sadauki salka ya dakawa basadaukiya ce tasa ta dakata da maganar da takeyi, haƙiƙa sadauki salka ya gama fusata domin saboda tsananin fusata har wani baƙin hayaƙine ke fita daga hancinsa kamar ba ɗan adamba cikin wata kakkausar murya marar daɗin ji ya fara magana ke yarinya idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi sadauki salkan da kika sani a da bashiine ba a yanxu a gabanki azatonki bani bibiyar duk wani motsi naki, kina ''yar shekara goma yarana sun haɗu dake a dajin dake iyakar wanan ƙasa taku yayin da kika fita farauta kece mutum ta farko da kika mani ɓarnar da ba zan taɓa mantawa ba domin kin kashe mani ɗan'uwa yayin da kukayi arba har sukayi ƙoƙarin yi maki fashi tare da ƙoƙarin cire maki kyallen da kika rufe fuskarki tun daga nan na fara bibiyar alamuranki, bayan nan mun ƙara haɗuwa dake karo na biyu lokacin kina "yar shekara shabiyar a daji inda muka fafata ƙazamin yaƙi a tsakaninmu amma babu wanda yayi nasara daganan bamu ƙara haduwa ba sai yanzu da muka haɗu a filin wanan gasar kisani kamar yadda kikayi mummunan tanadi a kaina nima haka nai miki mummunan tanadi dan haka idan baki shirya ba ma ki shirya dan ga maza nan bisa kanki nan take sadauki salka ya zare wasu adduna guda biyu haɗe da kawarara wata uwar kururuwa wadda saida tasa "yan kallo suka rufe kunnuwansu batare da ɓata lokaciba ya fallo da zababbben gudu......BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 32.
Saboda tsananin gudun da yakeyi har wata guguwa ke take masa baya, itakuwa basadauki zuba masa ido tayi tana mai masa murmushin mugunta ko zare takobinta batayiba saida ya rage baifi taku ukku ba sadauki salka ya isa inda Basadaukiya ke tsayeba sai ya daka wani wawan tsalle haɗe da ɗaga addunansa guda biyu sama cikin mugunnufin a niyarsa yayiwa Basadaukiya farat ɗaya ya yagalgala namanta, idan kayi duba ga duk wanda ke wanan fili zaga ya zazzaro idanuwansa cikin tashin hankali da kaɗuwadomin tuni sun saɗaƙas cewa ƙarshen Basadaukiya yazo saidai kafin wanan sara ya isa gareta cikin tsabar zafinnama kamar walkiya ta zare takobinta ta kare wanan sara cikin ƙwarewa da tsantsar jarumta ganin abinda ya farune yasa "yan kallo suka ɗau ihu haɗe da jinjina a gareta shi kuwa gogannaka wato sadauki salka ƙara fusatashi wanan ihun na "yan kallo yayi nan take suka ruguntsume da azabbban yaƙi cikin baƙin zafinnama tamkar walƙiya suke kaiwa junansu sara da suka kai hadama magara da kai duka haɗe halbi da kafafuwa nan da nan suka tashi hankalon filin su kuwa "yan kallo wanan faɗa annashuwa yasa su domin kuwa faɗane na mazan jiya wanda aka jima suna baƙin artabu haɗe turmutsutsu da mazaje, ganin an ɗauki lokaci ana wanan gumurxu babu wanda ya samu nasarar koda lakutar jikin ɗan uwansa... I ABDULLAHI ABDULLAHI)
BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 33.
Ganin babu wanda yayi nasarar koda lakutar jikin abokin karawarsa ne

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment