Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan dake hannunki toh ni kuwa zan bayyana maki ako wani lokaci" aljanin na gama fadin hakan ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba
.
Cikin hanzari akisa ta cire wannan zoben daga hannunta ta bude wani jaka ta jefa zoben ciki
Bayan shekaru goma sha bakwai lokacin akisa ta kwanta ciwon ajali , toh alokacinne kuma yarsu zarishatu ta cika cikakkiyar mace sai allah yai mata baiwar kyau da farin jini
Don kuwa a wannan lokaci yayan attajirai da sarakuna nata zuwa neman aurenta wajen mahafinta sirrinaddalib
.
Itako zarishatu taki amincewa da gaba dayansu wannan daliline yasa har ta cika shekaru goma sha bakwai batayi aure ba,
Alokacin da akisa taga cutar dake jiiknta bana tashi bane sai ta kira zarishatu tace da ita yake yata hakika wannan cutar dake jikina bana tashi bane, wannan yasa na kiraki don nai maki nasiha na karke.
Bayan akisa tayiwa zarishatu nasiha mai tsuma zuciya sai ta mika mata wannan zoben sannan ta fadi mata amfaninsa, kuma ta sanar da ita labarin wannan zoben
**
Toh kunji labarin zarishatu yar Attajiri sirrinaddalib matan sarki Ayyub ta uku
*
Koda sauran matan sarki sukaga zarishatu tayi shiru sai babbarsu zulaikha tace "yake zarishatu shin me kike takama da shi da har kika dauki wannan al'amari karamin abu"
Koda zarishatu taji wannan batu sai tayi murmushi sannan ta fiddo da wani zoben azurfa sai kyalli yake, ta ajjiyeta akan teburin dake gabansu, kowannensu yakai dubansa kan wannan zoben sannan shamlika tace "tambayarki ake kin wani fiddo zobe maimakon ki bada amsa
.
Murmushi mugunta zarishatu tayi sannan tace "yaku yan uwana kuyi sani cewa wannan zobe itace amsar tambayanku"
Nan take ta fede masu biri har wutsiya game da al'amarin wannan zoben
.
Koda suka saurari labarin wannan zoben sai dukkansu suka kamu da matukar mamaki nan take zarishatu ta dauki wannan zoben ta sanyashi cikin dan yatsanta
.
Aiko tana sanyawa sai shamlika tace da ita "na rokeki zarishatu kada ki kira mana wannan aljani"
Babbarsu zulakiha kuwa sai ta tashi tsaye ta nufi kofan dakin da nufin fita,
Cikin sauri zarishatu ta shafi gefen zoben
Wani murgujejen aljani mara kyan gani ya bayyana koda bayyanar wannan aljani sai shamlika da zulaikha suka suma alokaci guda saboda raazana da sukayi da ganinsa
.
Aljanin ya russuna da guiwowinsa sannan yace "ya shugabata gani na amsa kiranki, ki umarceni ni kuma na aikata"
Zarishatu ta dan sauke ajiyar zuciya sannan tace "kasani yakai MALJANU hakika labari ya iso mani cewa daya daga cikinmu zata samu haihuwa da sarki shin wacece wannan , abunda nake bukata dakai shine kayi bincike ka gano min ko wacece a cikinmu"
.
Aljani maljanu yace "ya shugabata ki sani wannan aikin da kika bani ba sai naje nayi bincike ba, domin na dade da sanin hakan"
Koda zarishatu taji wannan batu sai ta dka masa tsawa tace "gaggauta sanar dani wacce zata haihu da sarki a cikinmu
"
Cikin kyarma aljani maljanu yace " ya shugabata ki gafarceni hakika wacce bakwason nan toh itace zata haihu da sarki, amma nayi bincike na gano cewa bayan ta haihu toh dan da suka haifa zai bace bat daga wannan nahiyar tamu nayi nayi in gano inda zai tafi amma abun yaci tura"
.
Zarishatu ta sallami aljani maljanu
Tafiyarsa keda wuya sai zulaikha da shamlika suka farfado daga dogon suman da suka yi nan take zarishatu ta zayyane masu duk yadda sukayi ita da Aljani Maljanu
.
Allah mai girma hakika Allah yayi gaskiya dayace "iza qadha amran fa inna ma yakunu lahu kun fa ya kun"
.
Bayan kwana bakwai sai taufidatu ta kamu da cikin sarki Ayyub bayan wata tara ta haifi santalelen yaronta , kyakkyawa na gaban kwatance, alokacin da aka haifeshi ma mutane sun zata aljani ne saboda tsabar kyawunsa, mutane daga wasu garuruwan da kauyukan sassan nahiyar suna ta zuwa ganin wannan yari
.
Farin ciki kuwa agun sarki Ayyub bata faduwa,
Do min kuwa saboda farin ciki yana ta raba dukiyarsa ne yana baiwa jama'a
Mutanen birnin yemen baza su taba mancewa da wannan ranar ba, saboda kuwa wannan rana, talakawa,marasa galihu da attajirai sunga yadda ake barin dukiya
.
Su kuwa sauran kishiyoyin taufidatu wannan rana sai ta kasance tamkar ranar bakin ciki ce a garesu, amma zarishatu ita abun bai dameta ba don kuwa tasan mahaifinta ma yafi sarki ayyub dukiya da wasu abun hakan yasa ta saki ranta a ka runga sha'ani da ita
.
Zulaikha da shamlika kuwa hankulansu ba karamin tashi yayi ba a wannan rana saboda sun san cewa izan sarki ya fadi ya mutu toh babu wani abun kirki da zasu samu daga cikin dukiyarsa
.
Sai da aka kwana arba'in ana shagali a birnin yemen sannan dukkanin gidajen garin saida aka yi musu sabbin fenti, Attajirai, yayan sarakuna da sarakai kuwa suka runga halartar garin yemen,
Har takai cewa babu wani isasshen masauki na saukar bako wannan yasa sauran bakin suka sauka a wajen gari suka kafa tantunansu
.
Facaka akayi tayi da abinci da abunsha tamkar ba a san darajarsu ba, ko wanne mutum na garin yemen ranar yasan anyi walima tunda kuwa har cikin gidanka dakaru zasu shigo ma da katuwar tukunyar abinci wanda ko mutane dari ba zasu iya cinyewa ba su girke ita a wajen sannan su baka dukiya mai dumbin yawa, suyi gaba
.
Al'ummar birnin yemen gaba dayansu sun nuna farin cikinsu da wannan yaro , na sarki Ayyub wanda yaci sunan JURAISH
.
Kwanaki suka rinka zuwa suna wucewa har yarima juraish ya cika shekara biyar da haihuwa, alokacin yarima juraish ya taso da ababen Al'ajabi, da mamaki domin kuwa yana dan shekara biyar dinnan yake fita farauta sannan ya farauto manyan namun daji danginsu damisa zaki da sauransu
.
Wata rana yarima juraish yaji yana sha'awar tafiya farauta sai ya nufi fada domin ya sanar wa Abbansa sarki Ayyub, koda ya kariso fada sai sarki ya ayyub ya rungumeshi ya na mai murmushi, ya dubi yarima juraish yace yakai dana farin ciki na shin meke damun kane naga yau kana cikin walwala,
.
Yayin da juraish yaji haka sai yace ya abbana zuwa nayi ka bani izni don ina son fita farauta yau dinnan , koda jin wannan batu sai ran sarki ayyub ya dugunzuma ainun domin kuwa shi ba a son ransa ne ba juraish yake fita farauta saboda kankantar shekarunsa, cikin sanyin jiki yace yakai dana kayi sani cewa sam sam bana kaunar wannan farauta da kake tafiya amma kuma saboda na faranta maka rai yau zan barka ka tafi amma da sharadi guda daya
.
Yarima juraish ya dubi mahaifinsa yace ya abbana shin mene ne wannan sharadi, sarki ayyub ya yi murmushi yace sharadin itace daga yau baza ka sake fita farauta ba har sai shekarunka sun kai ashirin , shin ka yarda da wannan sharadi nawa,
.
Hankalin yarima juraish ya dugunzuma ainun amma da shike yasan mahaifina nasa yana fadane kawai sai yayi murmushi yace na amince
Sarki ayyub ya dubi sarkin yaki yace mai ya hada dakaru dari biyu suyi ma yarima rakiya
.
Cikin kankanin lokaci har wayannan dakaru sn gama shiryawa, yarima juraish kawai suke jira su dau hanya
.
Shi kuwa yarima koda ya baro fada bai zame ko'ina ba sai turakar mahaifiyarsa, da shigarsa cikin turakar sai yazo gaban taufidatu ya russuna yace ya ummina hakika yau naji ina sha'awan zuwa farauta shine nazo na sanar dake don na riga dana fadawa abba koh
.
Hankalin taufidatu ne ya tashi ta tuna da mugun mafarkin datayi yau amma da shike tayi imani da cewa duk wani abun da zai samu mutum toh daga Allah yake kuma ba'a taba gujewa Kaddara
Tayi murmushi ta dubeshi sannan tace Allah ya dawo dakai lafiya
.
Bayan yarima juraish da dakaru kusan dari sun fita daga birnin yemen basu nausa ko'ina ba sai cikin daji, inda suka runga tafiya amma cikin ikon Allah basu hadu da Dabba ko daya ba sai tsuntsaye kawai , suma tsuntayen ko da sun harbesu da kibau basa samunsu sai de kibau din subi ta gefensu, a haka sukayita kutsa kai cikin daji batare da tunanin cewa gari ya fara duhu ba,
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani sukayi wani abu ya wuce su da gudu, kamar wucewar walkiya,
Su kansu basu da hakikanin sanin ko menene wannan ya gilmasu, nan take yarima juraish ya zaburi dokinsa da gudu , ya nufi wannan abu daya wuce, suma sauran dakarun koda ganin yarima ya zaburi dokinsa dukkansu sai suka rufa masa baya suna masu wani irin azababben gudu,
.
Bayan kaman wani lokaci sai gashi yarima juraish ya kusa cimma wannan abu, koda ya matso kusa da wannan dabba sai yaga ashe ma wata katuwar barewace keta tikar gudu, yarima juraish na ganin haka sai ya zaro kibau din dake bayansa ya zaro kifiya daga cikin kwarinsa sannan ya dameta a cikin bakarsa, sai da ya tabe iyaa karfinsa sannan ya saki, ai kuwa yana saki sai wannan kifiyar yaje ya caku a kafar dama na wannan barewar,
.
Barewar ta yi kara sakamakon zafin data ji Amma duk da haka bata daina falfala gudun datake ba, sai gashi an kasa tsere tsakaninta da yarima juraish, ya kasance ita ta kasa guduwa masa shi kuwa ya kasa cimmata,
Ahaka suka kasance suna wannan tsere har tsawon sa'a daya,
Kwatsam ba Zato ba tsammani sai yarima juraish yaga wannan barewar ta fada cikin wani wawakeken rami dake gabansa, cikin matukar sauri ya kama linzamin dokinsa yaja don ya tsaida shi, Amma yadda kasan ma alokacinne yake karama dokin Gudu, yayi ya tsaida dokin Amma dokin taki tsayuwa,
Har dokin ta iso gaban katon ramin sannan ta fada ciki tare da yarima juraish a bayanta
.
Anan na kawo karshen littafi na daya
SHIN YARIMA JURAISH ZAI RAYU
.
INA LABARIN SARKI AYYUB DA MATANSA
.
Domin jin wayannan amsoshin sai ku tareni a littafin SADAUKI UBAN SADAUKAI na biyu 2
......
Yo anan zan tsaya sai wani jikon
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Hakkin mallak (m) keffians News Teller (K N T)
Tare da hadin guiwan hausaebooks page


SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Na Shuraih Usman 99%
Ebook created by Shuraih Usman
Sold @ www.hausaebooks.com.ng & okadabook
,
(c) Shuraih 99% 2018



SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@ Shuraih 99%
Part 2A
.
Dajine da mutane suke matukar tsoransa, baya ga irin muggan dabbobin dake rayuwa a cikin dajin,
Akwai rade-radin cewa akwai mugayen Aljanu masu zuke jinin bil'adama dake rayuwa a cikin dajin irin wannan dalilai dama wasu su suka saka mutane kauracewa Dajin ma'aboci manyan bishiyoyi
.
Hatta fatake sun daina bi ta cikin wannan dajin ,
Tsohone tukuf da shi yana tafiya cikin dajin, yana sanye da riga wacce aka sana'anta ta da fatan Zaki, ya daura mayafi ya rufe al'aurarsa mayafin ya tsaya daidai guiwowinsa, ya soke zabgegiyar takobi a gadon bayansa
.
gashin gemu da gashin kasumba sune suka rufe fuskar tsohon ta yadda ko bakinsa ba a iya hangowa, tsohon wanda ya kasance Farin fata ne, saide yafi kama da Aljani akan a kirashi da mutum,
yana tafe cikin sanda hannunsa rike da mashi ga dukkan alamu farauta yake, sai da ya kusan karade dajin amma ko tsuntsu bai yi arangama da shi ba
Hakan shine yayi matukar bashi mamaki
A iya saninsa da kuma zaman da yayi cikin dajin na shekara da shekaru bai taba fitowa farauta yakai sa'a daya ba batare da sunyi ARANGAMA da muggan dabba ba, kasancewar dajin a cike yake da miyagun dabbobi
.
Cikin takaici da kunan zuciya tsohon ya juya lokacin da dajin ya fara duhu,
Kamar daga sama sai tsohon yaji wani sauti na kara nesa da shi,
Da gudunsa ya nufi bangaren dayaji karar, abun da ya iske ya bashi mamaki matuka
,
Jibgegen Bakin Dokine a yashe a kas cikin jini
Rabon da tsohon nan yaga doki a rayuwarsa tun zamanin kuruciyarsa,
Da saurinsa ya kariso gaban dokin inda ya iske ashe mataccene, nan da nan ya fara tunanin menene yayi sanadiyar mutuwar Dokin nan, lokaci daya tunaninsa ya kau daya tuna irin mugayen namun jejin dake cunkushe a cikin dajin
.
A karon farko tun zuwansa gaban dokin ya mike a gaggauce lokacin daya tuna babu tayadda doki shi kadai zai iso cikin mugun dajin nan, dole dakwai mahayinsa
Tunaninsa ya katse daidai lokacin da digon ruwa ya diga mai a goshi,
Da sauri ya sanya hannunsa ya goge ruwan, koda ya dubi tafin hannusa sai yaga jini, da sauri ya daga kansa sama
Inda Idanuwansa sukai arba da Yaro dan shekara biyar cikin kyakkyawan shiga, saide yaron baya motsi reshen bishiyan ya soki yaron a ciki jini sai bulbulowa yake
Sai a yanzu ne tsohon ya gane asalin abun da ya afku ga mataccen bakin dokin dake yashe a kusa da shi
.
Duk yadda akayi daga saman tsaunin can ne suka fado.
tsohon ya ayyana haka a ransa, cikin kankanin lokaci ya saukar da kyakyawan yaron daga kan bishiyar ya ajjesa a kasa kusa da dokin,
Har tsohon ya fara kiciniyar haka rami don binne gawarwakinsu kwatsam sai yaron ya yi dogon nishi, cikin sauri tsohon yayi jifa da mashin dake hannunsa ya rugo wajen yaron yana zuwa ya dauki yaron ya nufi wani yanki na dajin yana mai falfala gudu,
.
Tsohon na barin wajen da dakika goma sai ga tarin naman daji suna firfitowa daga sassan dajin suna nufo wajenda mataccen dokin nan yake,
Isarsu keda wuya suka fara yagalgala naman dokin
,
Dama dai dabbobin dajin a labe suke sunyi kwaantan bauna, saboda tsoron tsohonnan da suke ji, akaf fadin dajin babu wani bil'adama sai shi kadai, kuma yana ta kashesu tamkar kiyasai hakan yasa basa yawan fitowa sai da dare
********
Tsohon yaci gaba da falfala azababben gudu mai matukar ban mamaki, wanda baki bazai iya fadaba
Kafin cikan rabin sa'a tsohon ya iso bakin bukkarsa daya sassaka ya shigarda yaron cikin bukkar ya cire masa riga inda yayi arba da babban raunin da reshen iccen nan ya ji masa, cikin gaggawa ya shafawa raunin magani ya yaga gefen mayafin daya daura ya daure daidai wajen da raunin yake,
Bayan ya gama yi wa yaron duk wani taimako sai ya futo bakin bukkarsa ya zauna akan wani kututturin itace yana mai jiran farkawan yaron
Fatansa shine yaron ya samu lafiya,
.
Kaman daga sama sai tsohon yaji wata zazzakar murya wacce ya saba jinta tace "sannu da hutawa baba Na dawo daga farautar"
Tsohon ya juya ya dubi mamallakiyar zazzakar muryarnan
Kyakkyawar Yarinyace yar shekara biyar tana sanye da rigan fatan kura gami da gajeran wando, ta rataya kwari da baka a kafadanta, hannunta na dama na rike da wani farin Zomo
.
Yarinyar ta kariso gaban tsohon ta dubeshi tace "me yake faruwa baba na ga yanayin ka ya canja shin wani abune ya faru"
Duk da cewar yarinyar bata gama Wayo tasan duniya ba amma sai da tsohonnan yaji mamaki ainun bisa ga irin tambayar da ta yi mai
Yayi murmushi ya dubeta yace "to me kika kamo daga farautar taki,"
Ta miko mai farin zomon tace "wannan Zomonne na tadda mahaifiyarsa ta mutu kuma wani Zaki na neman ya hallakasa, shine na taimaka masa na daukosa "
.
Suna cikin maganar ne kwatsam sai suka ji ance "su waye ku sannan nan a ina nake"
Kyakkyawar yarinyar da tsohon mutumin suka juyo don ganin wanda yayi maganar
,
Tsohon bai girgiza kamar yadda kyakkywar yarinyar ta girgiza ba
Cikin zafin nama kyakkyawar yarinyar ta zare takobinta daya ke soke a kuibin cinyarta, ba tare da bata lokaci ba ta afka wa yarima juraish dake tsaye a bakin bukkar,
.
Yarima juraish yayi matukar razana da ganin fuskar kyakkyawar yarinyar, duk da shi yaro ne dan shekara biyar, koda ya rage baifi saura taku biyar ba tsakanin yarima juraish da kyakkyawar yarinyar nan sai ta daka tsalle sama ta turo kafanta gaba da nufin ta daki yarima juraish da shi, kafan nata na kusan towa yarima juraish ya goce mata cikin salon bajinta,
.
Tsohon ya daka ma yarinyar tsawa yace "ke lubaina" kyakkyawar yarinyar mai suna lubaina tana kokarin sake kaiwa yarima juraish wani harin kenan tsohon ya dakatar da ita,
.
Yarima juraish ya tsaya baki bude yana kallon yarinya lubaina,
Tsohon ya kariso ya kama hannun yarima juraish yace "yakai wannan yaro, sunana halixu wannan jikatace lubaina, na fita farauta ne da zu shine na tsinceka a saman bishiya kaji mugun rauni a bayanka, kuma alokacin baka cikin hayyacinka shi yasa na dauko ka na kawo ka sansani na?"
.
Tsoho halizu yai ajiyar zuciya ya tambaya "shin wane ne kai, sannan daga ina kake, "
Koda yarima juraish yaji tambayar da tsoho halixu yai masa sai kwalla suka taru a idanunsa, take Tunanin masarautarsu,garinsa,mahaifinsa da mahaifiyarsa sukai masa dirar mikiya a zuciya,
.
Tsoho halixu ya fahimci halin da yarima juraish yake ciki dun haka sai ya janyo hannun yarinya lubaina suka wuce cikin bukkar yana cewa da ita "ki daina gaggawa wurin yanke hukunci yanzu da an samu kuskure kin kasheshi fa, nine na ceto rayuwarsa dun haka kije yanzu ki bashi hakuri"
.
Cikin nadama lubaina ta gyada kai alamar to sannan ta juya ta koma wurin yarima juraish,
Ta iske yarima juraish a zaune yayi tagumi hawaye na zubowa daga idanunsa,
.
Ta durkusa kasa ta dafa hannunsa
Ya dago kai ya dubeta
Murmushi tai masa tace "kayi hakuri"
Shima cikin murmushin yace "na hakura " cikin shagwaba lubaina ta ce da shi "kaga daga yau ka zama yayana na zama kanwarka ba zamu sake fada ba ko"
"Eh kanwata " yarima juraish ya fadi yana mai mikewa tsaye,
Lubaina ta mike daga durkushen da tayi taja hannun yarima juraish suka nufi bukkar da tsoho halixu ya shiga
.
....
Hallau dai kuna tarene da Shuraih Usman inkiya 99%
Ku biyoni
(c) copyright : 2017 Shuraih 99%
(m) hakkin mallaka : Shuraih 99% 2017
Contact: shuraihusman@gmail.comSADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@Shuraih 99%
Part 2B
.
Tun daga wannan rana sai ya kasance a kullum yarima juraish yana tare ne da lubaina, ko farauta tare suke tafiya kusan komai tare suke yi, sunyi matukar shakuwa da junansu,
Bakaramin dadi tsoho halizu yaji ba a zuciyarsa yayin da yaga irin alakar dake tsakanin juraish da lubaina,
A haka tsoho halizu, yarima juraish da Lubaina suka cigaba da rayuwa cikin dokan dajin.
______
Al'amarin sarki Ayyub kuwa mahaifin yarima juraish koda dakarun daya sanya su kula da yarima suka dawo batare da shi ba, sai hankalinsa ya tashi cikin gaggawa ya ce da shugaban dakarun "yakai Hasib a ina kuka baro yarima naga baya tare da ku, alhalin nasan akullum izan kuka fita farauta tare kuke dawowa kuma yarima wurina yake fara zuwa kafin yaje wani wajen"
.
Koda shugaban dakarun mai suna hasib ibn Kayyib yaji maganganun sarki Ayyub sai ya fashe da kuka sannan ya sunkuyar da kansa kas
Cikin kukan hasib ibn kayyib ya labartawa sarki Ayyub labarin Abun da ya faru da yarima yayin da suka fita farauta,,, "ya shugabana a kan idanuwanmu yarima ya fada cikin wawakeken ramin dake bayan gari
.
Koda sarki Ayyub yaji abunda hasib ya fadi sai ya sulale ya fadi akas, cikin gudu hadimai suka zo gareshi, suka daga shi suka dora saman karagar mulki, gabadayan lakkan jikinsa sun mutu, hawaye ya fara gangarowa yana bin kuncinsa, waziri ya dubi sarki yace da shi "ya shugabana kai mani izni yanzu na nemo manyan jarumai su bazama cikin ramin don nemo yarima na tabbata yana raye"
.
Sarki Ayyub ya juyo ya dubi waziri yayin daya ji abunda ya furta yai murmushin karfin hali yace "yakai wazirina kayi sani cewa a shekarun baya na sanar da ku cewa an yimin albishir akan zan samu haihuwa kuma dan da zan haifa zai shiga Duniya zai shahara a duniya a bisa tafarkin yada Addinin islama,
Na tabbata wannan tafiyar da yayi itace tafiyar da aka sanar dani zaiyi, dun haka tsakaninmu da shi yanzu sedai muyi masa Addu'a ubangijin musulunci ya kareshi daga makiyansa sannan ya dawo dashi gida lafiya."
.
Sarki ayyub na gama fadin hakan ya mike ya shige cikin gidan sarauta,
,
Kai tsaye sarki ayyub ya tari Mahaifiyar yarima juraish wato taufidatu da maganar ya sanar da ita dukkan abun da yafaru,
Wannan shine abun daya faru a birnin yemen yayinda labarin batan yarima juraish ya riski iyayensa
..
Al'amarin tsoho halizu,yarima juraish da lubaina kuwa sun cigaba da rayuwa cikin farin ciki annushwa gami da son juna, yarinya lubaina ta dauki yarima juraish ne a matsayin babban yayanta, haka shima juraish ya dauketa ne a matsayin kanwarsa, ko kadan baya son ganin wani abu ya cutar da ita,,
.
Sukan tafi farauta tare su dawo tare kome a tare suke yi
A haka har suka girma
Wata rana yarima juraish da lubaina sukai shiri suka fita farauta inda suka bar tsoho halizu a sansaninsu kamar yadda suka saba, kasancewar tsufa ta kama tsoho halizu sai suka hutar da shi zuwa ko'ina.
__
Sai da juraish da lubaina sukai tafiyar sa'o'i goma amma ko zomo basuyi arba da shi ba hakan ne ya yi matukar basu mamaki, dun a gaba dayan rayuwarsu a cikin dajin basu taba shafe sama da sa'o'I uku batare da sunyi kicibus da wata dabba ba, amma sai gashi yau ko tsuntsu ba suyi gamo da ita ba,,,
Lubaina ta dubi juraish tace "yakai yayana shin bakai mamakin lamarin daya kasance damu a yau ba"
Yarima juraish yace "nayi mamaki sosai kanwata,kuma gashi rana na gab da faduwa, kinga kuwa dolenmu yanzu mu juya mu koma sansani..."
Bai gama rufe bakinsa ba sukaji Guranin zaki daga gabansu,
Juraish da lubaina suka kallo gabansu inda sukaji gurnanin na futowa, babu komai a wurin face tarin dogayen ciyayi,
Lubaina ta ciro kifiya daga kwarinta ta dame a jikin baka, jira kawai take taga kome ne ne a cikin surkukin ciyayin,
A gefen juraish shima ya zare doguwar takobinsa daga kufenta,ya tsaya cikin shirin kota kwana
Gurnanin zakin ya cigaba da kusantosu,
Dogayen Ciyayin suka fara motsi suna kadawa, koda ganin haka sai lubaina ta harba kibau ya shige cikin surkukin ciyayin,
Nan take gurnanin ya dauke dif ciyayin suka daina motsi
Lubaina da juraish suka dumfari surkukin ciyayin don sun tabbatar kome cece a ciki ta halaka, sai da suka kariso gaban ciyayin kwatsam sai sukaga wata narkekiyar zaki tayi fitar burgu daga cikin ciyayin,
Zakin ya tsaya a bayansu, suka juyo suna karewa zakin kallo , jinjina kai juraish yayi don tunda yake yawon farautarsa bai taba cin karo da shirgegen Zaki kamar wannan ba, zakin yayi gurnani ya karkada gashinsa,
Sannan ya falfalo da gudu ya tinkari su juraish
Tun zakin yana nesa lubaina ke yi masa ruwan kibbau amma abun mamaki koda kibbau din sun yi nasarar dira a jikinsa sai kaga sun karye, sun fadi a gefe,
Koda ya rage baifi saura tazarar taki uku tsakanin zakin da juraish ba sai juraish ya daka tsalle yana mai kaiwa zakin mummunan sara a wuya da nufin ya cisge kan zakin,
Koda takobin juraish ta hadu da jikin zakin sai wata sauti ta bayyana, sautin haduwar karfe da karfe, cikin mamaki juraish ya cigaba da kaiwa zakin sara da suka, amma yadda kasan dutse yake sara, koda aka dau karamin lokaci a na wannan gumurzun sai zakin ya shammaci juraish ya yakushe shi da faratansa a cinya, juraish ya gyatse fuska sannan ya cigaba da kaiwa zakin sara da takobinsa,
Al'amarin budurwa lubaina kuwa tun lokacin da aka fara artabun tsakanin dan uwanta da fusataccen zakin ta na gefe tana wa zakin ruwan kibau, da zarar kibau din sun taba jikin zakin se kaga suna zubewa kasa karyayyu,
Cikin fusata juraish ya yarda takobinsa gefe ya dubi zakin yai masa inkiya da hannu kan cewa yazo
,
Zakin yayi gurnani ya daka tsalle gamida wage bakinsa, juraish na ganin haka shima ya daka tsalle, ya dumfari zakin, koda zakin da juraish suka hadu, sai suka zube akas suna birgima juraish yayi nasarar cafke makwogwaron zakin ya matse makogoron da iyakacin karfinsa, tun zakin yana wutstsila kafafu har ya zama gawa, sannan juraish ya saki makogwaron zakin, ya ture gawar zakin gefe guda ya mike tsaye yana nishi,
Lubaina ta rugo ta zo gareshi koda ta ga cinyansa na hagu na zubar da jini sai ta fiddo da wani kullin magani ta barbada mashi a wurin da yaji raunin,ta yaga gefen rigarta ta daure masa wurin
.
Juraish yayi murmushi ya dubi lubaina yace "nagode kanwata, da irin tarin kulawa da kike bani"
Lubaina najin haka ta dago fuska ta dubeshi tace"ai hakkina ne na baka kulawa, kasantuwar bani da wani dan'uwa ko majibinci daya wuce kai, to in ban kula dakai ba wazan baiwa kulawata"
Sadauki juraish ya kinkimi mataccen zakin ya saba a kafadarsa suka nufi sansaninsu suna tafiya suna hira cikin jin Annushwa
**
Isowar su sansanin keda wuya juraish ya jibge gawar zakin a kofan dan karamin bukkar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment