Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

budurwan tun da yake a rayuwarsa bai taba ganin mace mai tsananin kyawu ba kamar wannan budurwa, hatta lubaina datai arba da budurwar sai da kishi ya kamata na ganin ta dareta kyawu nisa ba kusa ba,
Budurwar ta tsaida dariyar nata lokaci guda ta turbune fuska, in kaganta sai ka rantse ba itace ta gama kyalkyalar dariya ba
.
Budurwar ta nuno su yarima da hannu tace "yaku wayannan mace dana miji ina mai yi maku lale marhabun da zuwa Gabatul maut, Dajin mutuwa, dajin da duk abun da ya shigo baya fita, lallai kusani kun aikata mummunan kuskure arayuwarku na shigowa cikin dajinnan,"
Yarima juraish ya ce da budurwar a fusace "yake wannan kyakkyawar budurwa,kiyi sani cewa mu matafiyane hanyace ta biyo damu ta cikin dajinnan, izan har ya kasance mun aikata wani laifi ne agareki na shigowa dajin to muna mai baki hakuri,batun zaki hallakamu kuwa sam bai taso ba"
.
Koda budurwan taji haka sai ta kara daure fuska tamau tace "nasan baku san koni wacece ba shiyasa, to kusani nice sarauniya Murkisa mai mulkar birnin DUMA, na kasance ne a cikin dajinnan don aiwatar da wani babban sihiri wanda muddin na kammalashi zan zamo gagarabadau ga sauran sarakunan duniya, kasata zata bunkasa a fannin tattalin arziki, shekarata hamsin cikin dajinnan ina kokarin hada sihirin, ta hanyar zubda jinin duk wani bil'adama ko aljanin daya ratso ta cikin dajinnan, na hallaka bil'adama da aljan dubu casa'in da takwas, saura mutum biyu ya rage na kammala sana'anta sihirin inda zan zamto gagarabaudau din sarauniya, ina mai umartarku da ku kashe kawunanku da kanku tun kafin kaifin takobina ya ratsa girazanku"
Sarauniya murkisa ta idda maganarta cikin tsawa da gargadi
.
Azucciye yarima juraish da lubaina suka zare takubbansu juraish yace "yake sarauniya murkisa zan baki wata garabasa muddin kin yadda da kanki to ki tunkareni muyi bata kashi izan har kika samu nasarar taba jikina ko takobinki ya yankeni to da kaina zan hallaka kaina kana na hallaka yar uwata lubaina, don haka ga fili ga mai doki me yarage"
.
Koda sarauniya murkisa taji haka sai ta bushe da dariya tace "kasani yakai jarumi juraish kafin ka kagai ga fafatawa dani dole sai ka wuce wasu matakai, " tana gama fadin hakan tafa hannunta tana fadin wasu dalasiman tsafi, nan take dakin ya kama girgiza tamkar zai kife abubuwan dake dakin suka fara tangal tangal kwatsam sai wasu irin dodanni masu munin halitta suka fara fitowa ta karkashin kasa, wayannan dodanni sun kasance jibgaga domin kuwa dodo daya daga cikinsu zai iya cafke mutane uku a hannunsa, dodannin na dauke da kwayar idanu guda daya a akan fuskarsu sai wagegen baki mai dauke da bakaken hakora, babu makami a hannun dodannin, nan fa dodannin sukai kururuwa suka afkawa su yarima juraish da budurwa lubaina
.
Koda su yarima juraish sukaga haka sai suka falfala da azababben gudu suka tari dodannin koda suka hadu sai suka kacame da bakin gumurzu,yarima juraish da lubaina suka wanzu suna ragargazar dodannin babu kakkautawa,hoho izan da ace mutum na wurin yana kallon wannan gumurzu to da sai yayi zaton yarima juraish da lubaina ba mutane bane, sarauniya murkisa dake zaune akan karaga sai bata rai take na ganin irin yadda yarima juraish ke ragargazar dodanninta,
.
Sai da aka dau tsawon lokaci yarima juraish da lubaina suna ragargazar dodannin tamkar suna sassabe a gona, duk inda suka sa gaba sai de kaga sassan jikin dodanni na yawo a iska, kafin su samu nasarar hallaka dodannin gaba daya,
Yarima juraish ya sanya hannu yana share bakin jinin dake jikin takobinsa ya ce da sarauniya murkisa "ina bai baki shawara da ki gaggauta neman inda dare yai maki kafin kaifin takobina ya iso gareki"
Sarauniya murkisa na jin haka ta sake bushewa da dariya a karo na biyu, ta ce "adadin dodonninnan sun kai dubu biyu amma cikin kankanin lokaci kuka gama da su, najin jina ma sadaukantakarku, muje mataki na biyu" sarauniya murkisa na gama fadin hakan ta tafa hannayenta ta na fadar dalasiman tsafi,
.
Koda ta fara furta dalasiman nan sai yarima juraish da lubaina suka tsinci kansu a tsakiyan daji, cikin mamaki suka dubi junansu daga sama sukaji muryan sarauniya murkisa tana cewa dasu "wannan shine Duniyar gwaggon birrai, babu mutum ko aljan dake rayuwa anan, muddin kuka samu nasarar ficewa daga duniyar nan a raye to zaku cimmini a fadata ta birnin DUMA" muryan na zuwa nan ya dauke dif tamkar bai taba wanzuwa ba,
Yarima juraish ya ciro salkar ruwansa yayi alwala itama lubaina tayi alwala yarima yajasu Salla, bayan sun idar da sallar ne sukai Addu'a suka mike suka cigaba da tafiya suna dumfarar gabas,
Suna cikin tafiyar ne yarima juraish ya taka kututturin itace a rashin sani take wata kara ta bayyana, kafin kace kwabo sai wata jibgegiyar itace ta fito daga gabas tayo kan yarima juraish da lubaina, cikin zafin nama lubaina tayi tsalle gefe guda ta finciko yarima juraish itace ya wuce ta gefensa, ba zato ba tsammani sai raga tai fitar burgu daga karkashin kasa ta dauresu tamau,a saman bishiyar dake gefensu tayadda ko hannunsu baza su iya motsawa ba,nan fa su yarima suka fara kokarin balle ragar amma suka gagara sakamakon irin daurin da taimasu
Faruwan hakan keda wuya kunnuwansu yarima ya fara dauko masu wani irin sauti dake kusantosu , nan suka dena kokarin balle ragar suka kasa kunne suna sauraron sautin dake dumfaro su,
.
Koda sautin ta kusantosu sai bishiyu suka fara karairayewa suna zubewa akas, kasa tafara girgiza tana tambal tambal tamkar ana girgiza ruwa a cikin kofi,
Yarima juraish da lubaina suka maida hankalinsu ga inda suka ga bishiyu suna zubewa nan fa sukai arba da abubuwan da sukai sanadiyar karairayewan bishiyun
Ba komai bane illa jibgajibgan gwaggwon biri masu tsananin girman jiki, da munin fuska sudai gwaggwon birinnan sun kasance jajayene zur,adadin su yakai dubu biyar suna tafiya kasa na girgiza suna dukan girazansu
Rundunar Gwaggon birin na karisowa wani gwaggo ya fin ciki ragar da su yarima juraish suke ciki, suka koma inda suka fito yarima juraish da lubaina na hannun wani gwaggon biri
Anan na kawo karshen littafi na biyu
____
SHIN YARIMA JURAISH DA LUBAINA ZASU TSIRA DAGA HANNUN RUNDUNAN GWAGGON BIRINNAN KUWA
.
WANI IRIN KAZAMIN YAKI ZA'A FAFATA TSAKANIN RUNDUNAR GWAGGON BIRI DA SU YARIMA JURAISH
.
SHIN SARAUNIYA MURKISA ZATA SAMU NASARAR ZAMA GAGARABADAU
.
INA LABARIN SARKI AYYUB MAHAIFIN YARIMA JURAISH
.
INA LABARIN WAZIRI IBBAHU DA KASAR MAHARSABAR
.
Domin jin wayannan amsoshi sai ku tareni a littafi na Uku3 SADAUKI UBAN SADAUKAI littafina uku 3 na Shuraih Usman
____
Littafi na uku 3 dana hudu 4 dana biyar 5 na nan zuwa maku akan kari

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment