Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su, ya dubi lubaina yace da ita shiga daga ciki ki duba ko Abba yana nan, kinsansa da son yawatawa
.
Lubaina ta shige cikin bukkar tana shigane tai arba da tsoho halixu a kwance magashiyyan jini na futa daga bakinsa, gaba dayan jikinsa ya dena motsi
Lubaina na ganin haka ta kwarara ihu ta nufi wurin da tsohon ke kwance..
.
To tsohon nafa ya kawo gangara
Amma kafinnan its Shuraih Usman inkiya 99%SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@shuraih 99%
Part 2C
.
Cikin gudu yarima juraish ya shigo cikin bukkar inda ya iske tsoho halixu kwance magashiyyan jini na zuba ta bakinsa, a gefensa ga lubaina ta tallafo kansa tana mai zubda hawaye,
.
Tsoho halixu ya dago kai cikin mawuyacin hali ya dubi yarima juraish, yai masa inkiya da hannu kan ya matso kusa,
Lokaci guda kwalla suka taru a idanun juraish ya karisa gaban tsohon ya durkusa yace "me ya faru dakai Abba,"
.
Tsohon ya kama hannun juraish yace "yaku yayana kuyi sani cewa bana tunanin zan kara wasu kwanaki a cikin duniyar nan, domin kuwa naji ajikina Ajalina ya kusanto ni, wannan yasa zan sanar daku labarina," tsoho halixu ya tsaida maganar tasa yayin da tari mai karfi taci karfinsa,
Lubaina ta dauko battar ruwanta ta kafa wa tsohon a bakinsa,
.
Tsohon yayi nishi sa'ilin da ya gama kwankwadar ruwan ya dubi lubaina yace "yake yata lubaina ayau ne zan sanar dake tarihin rayuwarki, kin dade kina tambayata ko su waye iyayenki,amma ban taba sanar dake su ba, mahaifinki Sarkine a kasar maharbassadar
Kasar MAHARBASSADAR kasace dake dauke da mutane mabanbanta Addini da Al'adu, a kasar kowa yana da daman yai Addinin daya ga dama,
.
Mahaifinki sarki Marhus ya kasance kasurgumin matsafine kuma Adalin sarki wanda baya taba nuna banbanci tsakanin Talaka da Attajiri sarki marhus na da matar Aure guda daya mai suna Nuzaira, sai da suka shekara ashirin kafin nuzaira ta samu ciki,
.
Murna a wajen sarki marhuz baya faduwa, ya kasance a kullum da kowanne lokaci yana tare da Nuzaira yana renon cikinta, ya dena fita fada gaba daya, Wazirinsa mai suna Ibbahu ne ke tafi da Al'amuran fada,
.
Waziri ibbahu babban makiyin sarki marhus ne a boye amma a zahiri yana nuna shi babban masoyinsa ne, bashi da buri daya wuci yaga karshen sarki marhus don ya gaje karagar mulkinsa basau daya ba basau biyu ba ya tura dubunnan dakaru masu dumbin yawa don su hallaka sarki marhus amma sun gagara kasancewar sarki marhus babban sadaukine mai daka wa maza gumba kuma babban matsafi da dukkan bokayen duniya ke shayinsa,
Ba karamin bakin ciki yayi ba yayin da ya samu labarin matar sarki ta samu juna biyu, ya ciji lebe ainun
A da kokarin waziri ibbahu ibn kalzim yake na ganin ya hallaka sarki marhus ne ya samu labarin wani kasurgumin boka mai suna sham'una dake rayuwa a wajen garin
Cikin dare waziri akiyanu yayi shiri irin ta fatake ya fice daga birnin maharsabar ya nufi dajin da kasurgumin boka mai suna Sham'una yake , boka sham'una na zaune a saman wata doguwan tsauni dake wajen birnin maharbassar,
Koda waziri ibbahu yafada wa boka sham'una bukatarsa nason kawar da sarki marhus sai boka sham'una ya bushe da mahaukaciyar dariya, gaba dayan kogon dutsen ya amsa da sautin dariyan bokan mara dadin sauraro, sai da yayi mai isarsa sannan yai shiru ya dubi waziri ibbahu yace "yakai wazirin birnin maharbassar kayi sani cewa bazaka taba samun nasara akan sarki marhus ba, saboda ba karamin kasurgumin matsafi bane, manyan bokaye da matsafan duniya na shayinsa saboda karfin sihirinsa,"
Yayin da waziri ibbahu yaji haka sai ya tausasa murya yace "yakai bokan Duniya kasani cewa an sanar dani cewa kai babban matsafi ne kuma kaine kadai kasan sirri da lagon sarki marhus, wannan tasa nazo gareka, muddin ka taimaka mani nai nasara akan sarki marhus to zan raba kasar mahassabar biyu na baka rabi,"
.
Boka sham'una yaja doguwar numfashi yace "eh to akwai hanya daya amma tana da matukar hadari domin muddin ka aka samu kuskure to dukkanmu zamu hallaka"
Cikin zumudi waziri akiyanu yace "wacce hanya kenan ya babban boka,"
Boka sham'una dake tsugune ya harde kafafu ya dubi waziri akiyanu wanda yai zuru da idanu kuma yai kasake da kunnuwansa yana sauraronsa
Yace "sarki marhus gagarumin matsafine, gagarabadau a fagen matsa, manyan matsafa da dama suna shakkarsa kuma har yau ba'a samu wani matsafi ko sarki daya gano lagonsa ba saini,
Asalin tsafin sarki marhus gadanta yayi a wurin mahaifinsa sarki , shima mahaifinsa ya gaji tsafin ne a wurin kakan sarki marhuz,
Dan gane da binciken danayi a halwar tsafina na gane cewa agaba dayan fadin duniya babu wata tsafi mai karfi kamar ta sarki marhus, muddin kana son ka ci galaba akan sarki marhus to sai ka rabashi da Zoben azurfan dake sanye a hannun hagunsa, domin kuwa wannan zobe ita ce matattarar tsafinta in har babu zoben a tare da shi to babu wani abun da zai iya tabukawa daya danganci tsafi"
Koda boka sham'una ya gama fadin haka sai ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba,
.
Waziri ibbahu ya mike ya fice daga kogon boka sham'una yana futa ya dare kan dokinsa fuskarsa cike da farun ciki na ganin cewa burinsa na shekara da shekaru ya kusan cika,
.
Washe gari waziri ibbahu ya tara mukarrabansa wayanda da yawancinsu yan majalisan sarki marhus ne da ba sa kaunan mulkinsa ganin irin kauna gamida taimako da yake yiwa talakawa, da durkusar da attajirai da yake,
Bayan waziri ibbahu ya fada masu aniyarsa na son kawar da mulkin sarki marhus, dukkansu suka bashi goyon baya, da shawarwarin yadda za'abi a raba sarki marhus da zoben dake hannunsa
.
Alokacin da sarki marhus ya dena fitowa fada ya kasance a kullum yana gida tare da matarsa nuzaira suna renon cikinta, a wannan lokacinne waziri ibbahu ya samu daman aiwatar da duk wani shirinsa na yadda zai raba sarki marhus da zoben sihirinsa
.
Koda dare ya raba kafa ta dauke bakajin motsin komai a birnin maharsabar sai kukan kananun kwari da haushin karnuka, ayayin ne waziri ibbahu ya yi shiga irin ta rikakkun barayi ya sanya bakaken kaya, ya kuma rufe fuskarsa da rawani ta yadda ba'a ganin fuskarsa sai idanunsa,
Kai tsaye waziri ibbahu ya nufi gidan sarki marhus yana isowa ya haura katangar gidan cikin kwarewa,
Dakarune rututu a cikin gidan suna kai da komowa, koda waziri ibbahu ya dirga a cikin gidan sarki marhus sai ya bi wani lungu da ta inda yake tsammanin babu dakarun sarki
.
Yai tafiya mai dan karen nisa kafin ya isa babban falon gidan sarautar, waziri ibbahu ya tsaya a bakin kofan dazai sada shi da babban falon ya fidda da wani guru daga aljihunsa ya rataya a wuyansa,
Ratayarwarsa keda wuya sai ya danna kai cikin falon inda ya iske daruruwan dakaru da hadimai suna zarya, babu abun da zai baiwa mutum mamaki face ganin rashin damuwa da kulawan da dakarun suka yi yayin da waziri ibbahu ibn kalzim ya shigo falon saide abun da mai karatu baka sani ba shine wannan gurun da waziri ya daura a hannunsa itace ta makantar da daruruwan dakarun daga ganinsa,
Haka waziri ibbahu yai ta ratsawa ta cikin dakarun amma basa iya ganinsa, har ya iso bakin turakar sarki marhus,
Cikin takama da isa waziri ibbahu ya kutsa kai cikin turakar inda ya iske sarki marhus da matarsa nuzaira suna kwance a kan faffadan katifa suna sharar barci, nuzaira tana gefen sarki marhus hannunsa na dama ya na kan cikinta,
.
Waziri ibbahu ya matsa kusa da katifan da suke kai zuciyarsa na dakan uku-uku domin kuwa ganin sarki marhus dayayi yai matukar razanashi, cikin tsoro ya fidda kullin garin banju daga aljifun wandonsa ya shaka wa sarki marhus a hancinsa,
Koda sarki marhus ya shaki garin banjun sai baccin nasa ya dadu,
Waziri ibbahu na ganin haka ya kyallara ido a hannun sarki marhus wanda ke dauke da zoben azurfa, zoben sai kyalkyali yake tamkar wata, cikin zumudi waziri ya kama hannun sarki ya fara kokarin zare zoben daga hannun amma zoben yaki futa, duk wata dabara da fasaha sai da ya jarraba don cire zoben daga hannun sarki marhus amma abu ya gagara,
Ganin wankin hula na neman ya kaisa dare ya sanya ya yanke shawaran guntule yatsa mai sanye da zoben,
Har ya zare takobi da nufin ya sare hannun kwatsam sai boka sham'una ya bayyana a dakin yana mai daka masa tsawa, a matukar razane waziri ibbahu ya yi baya don shi a zatonsa sarki marhus ne ya farka koda yaga boka sham'una sai ya cika da mamaki
Nan take boka sham'una yafara ambatan dalasiman tsafi wayanda suka haddasa duhu ya mamaye dakin sai da duhun ya dau tsawon lokaci, har waziri ya fara fargaban kada a garin neman kiba a samo rama, hakan tasa yace da boka sham'una "yakai bokayen duniya kada fa garin tsatsube tsatsubennan naka ka janyo hatsabibin nan ya farka, domin izan ya farka babu shakka sai ya hallakamu ni da kai" boka sham'una ya cigaba da ambatan dalasiman sa wanda shi kadai yasan ma'anarsu sai gashi da kadan da kadan duhun ya yaye,
Sai gashi zoben azurfan dake hannun sarki tana yawo a saman iska, waziri yayi wuf ya sure zoben, cikin farinciki ya sanya zoben a dan yatsansa na hagu
.
Koda waziri ya sanya zoben a hannunsa sai wani bakon karfi ya ziyarci jikinsa, nan take gabobin jikinsa suka fara mummurdewa, dantsensa da suka kasance kananu kamar na yara kana suka cika fam sukai burdum burdum,kayan dake sanye a jikinsa suka fara yayyagewa saboda cikar da jikinsa keyi
Cikin kankanin lokaci kamannin waziri ibbahu suka sauya izuwa na SADAUKI UBAN SADAUKAI,gwarzo uban gwaraza, jarumi uban jarumai, duk yadda mutum ya cika da jarumtaka da sadaukantaka muddin yayi arba da waziri ibbahu cikin wannan sura to sai ya razana,
.
Cikin matukar mamaki waziri ibbahu ya dubi jikinsa sannan ya dubi boka sham'una yana mai kyalkyalewa da dariya, boka sham'una yayui murmushin samun nasara yace "lale marhabun da samun wannan nasara yakai waziri ibbahu ina mai tabbatar maka da cewa a yanzu kaf fadin duniya babu wani sadauki daya kai ka karfin dantse, sarrafa makami,juriya da naci kasani yanzu ka zama SADAUKI UBAN SADAUKAI dodn jarumai, mala'ikan gwaraza, a yanzu kamallaki sirrikan tsafi guda dubu dari biyar wanda babu wani matsafi daya mallaka a duniya, fatana de ka zamo me cika alkawari akan maganarmu"
,
Koda boka sham'una ya gama fadin haka sai waziri yayi murmushi yace "da sannu zaka sameni mai cika alkawari a gareka, amma kafinnan bazan fara kashe la'anannen sarkinnan" rufe bakin waziri keda wuya ya daga takobinsa ya sare kan sarki marhus kan yai sama kamar an cillashi daga gwafa, dungulmin kan ya cigaba da bulbulo da jini tamkar kogi ya balle...
Har waziri ya juya da niyyan ficewa daga dakin sai boka sham'una yace "yakai sarkin sarakai gwarzon gwaraza ya kana shara kuma kana barin baya da kura,"
Cikin rashin fahimta waziri yace "ban gane zancenka nnan ba fahimtar dani da yaran da zan gane"
.
Boka sham'una yace "ka kashe sarki marhus amma kuma kabar matarsa alhalin kana da masaniyar tana dauke da juna biyu shin baka tunanin abun da zata haifa nan gaba zai iya zamowa alakakai gareka kuma barazana ga mulkinka "
Koda waziri yaji haka sai ya juyo da nufin ya hallaka nuzaira yayin daya daga takobinsa sama da nufin ya fille mata kai sai dakaru gidan suka shigo dakin, koda shigowan dakarun suka ga abun da waziri ibbahu yake kokarin aikatawa sai suka yi kukan kura suka dumfareshi suna masu kwarma ihu,
Sautin ihunsu ne ya farkadda gimbiya nuzaira daga daddadan baccin da take, farkawanta keda wuya tai arba da gangarjikin mijinta sarki marhus babu kai, jini na bulbulowa daga dungulmin kan,
Tana ganin haka ta tsandara ihu tana mai rungume gangarjikin sarki marhus, lokacin da dakarun sarki suka afkawa waziri ibbahu da sai ya daga hannunsa ya nuna su nan take suka kama da wuta kafin kace kwabo sun kone kurmus,
.
Gimbiya nuzaira na ganin haka ta mike a guje ta fice daga turakar, waziri yayi ya bushe dariya wacce ta haddasa karamin girgizan kasa, sannan ya bi bayan gimbiya nuzaira , lokaci guda dakarun gidan sarki suka yo kan waziri hannuwansu rike da muggan takobi, saide duk wani badakare daya samu nasarar saran jikin waziri ko ya soka masa takobi maimakon makamin ya illata waziri ibbahu sai de kaga wuta ta kama badakaren ta maida shi toka
.

SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@ Shuraih 99%
Part 2D
Tsoho halixu yayi tari a karo na biyu sannan yacigaba da baiwa su yarima juraish da lubaina labarin sa,
Gimbiya nuzaira kuwa koda ta samu nasarar ficewa daga gidan sai tai ta tikar gudu babu kakkautawa har ta kawo babban kasuwar birnin, a wannan lokaci na futo daga gidana domin na gyara magudanar ruwa dake jikin gidana, kwatsam kamar daga sama sai ganin gimbiya nuzaira nayi ta rugo wurina a guje tana neman taimako,
.
Kallo daya nai mata na ganeta, cikin biyayya na durkusa na kwashi gaisuwa sannan na shigar da ita cikin gidan, inda na hadata da matata, cikin ikon Allah sai naguda ta kama nuzaira matata ta shiga taimaka mata, ni kuma na fito kofan gidana ina mai Addu'ar ubangijin musulunci ya sauketa lafiya,
Ina cikin addu'ar ne naga wani bakin hayaki ya bayyana a gabana a hankali bakin hayakin ya juye izuwa siffar waziri ibbahu, ya dubeni ya kyalkyale da dariyar mugunta kana ya daure fuska tamau kai kace ba shi bane ya gama cin dariya dazu ba,
.
"Yakai wannan tsoho mai karar kwana lallai ka salwantar da rayuwanka da kanka, ta hanyar temakon gimbiya nuzaira, " waziri ibbahu ya fadi yana dubana
Na ce "shin kai wane ne da har kake ikirarin zaka hallakani"
Koda waziri yaji haka sai yace "nine waziri ibbahu bin kalzim sarkin gobe, domin ayanzu haka na kashe sarki marhus, matarsa Nuzaira kadai ta ragemin dana kasheta burikana....."
Sautin kukan jaririn da mukaji yana fitowa daga cikin gidana shine ya katse wa waziri maganarsa, batare daya kara koda furta kalma daya ba ya nufi cikin gidan kai tsaye,
Ina ganin haka na yunkura da zummar na hanashi shiga gidan amma sai naji na kasa motsa dukkan wani gaba dake jikina, hatta kwayar idunawa na ma kasa motsa su nayi,
Shigan waziri cikin gidan keda wuya naji gimbiya Nuzaira ta kwarara ihu, daga karshe naji muryan matata tana mai yin kabbara, koda naji haka sai hawaye ya fara gangarowa daga idanuwana kasantuwar nasan cewa matata da gimbiya nuzaira sun rigamu gidan gaskiya,
Nan take na fara kiran sunayen Allah a cikin zuciyata, ina mai addu'a , nadau kankanin lokaci ina addu'a cikin zuciyata kafin gabobina su saki, ji nayi tamkar an sakoni daga saman bene, a guje na shiga gidan na nufi cikin dakin matata,
Shigata dakin keda wuya nai arba da gawar matata humaira a gefe daya, jini na bulbulowa daga cikinta, gefe guda kuwa gawar gimbiya nuzaira ce jini na bulbulowa ta wuyanta, a gabana kuwa waziri ibbahu ne yana rike da jaririyar da nuzaira ta haifa kafin ya kasheta, koda waziri yai arba dani sai ya nuna ni da dan yatsa nan take wuta tayi futar burgu daga hannunsa ta tunkaro ni, kafin wutar ta kariso gareni ne na fara karanta ayar Alqur'ani mai girma a fili, koda wutar ta iso gareni sai wani shingen gilashi ya bayyana ya kareni daga wutar,
.
A matukar hasale waziri ya ambaci wani kalma sai ga tarin takubbai sun bayyana akan iska suna tunkaroni da nufin su cakeni, takubban na karisowa kusa dani suka zube kasa
Sai da waziri ya aika mani da masifu iri daban-daban amma basu cutar dani ba, koda yaga ya kasa samun nasara akaina da karfin tsafi sai ya ajjiye jaririyar dake hannunsa a gefe daya sannan ya zare takobinsa yace dani "in ka iya ruwa to baka iya tabo ba, hakan in ka iya tabo to baka iya rairayi ba" yana gama fadin hakan ya rugo gareni ,
Koda naga haka nima sai na zare takobina na tareshi koda ya rage baifi saura taku biyar mu hade ba sai waziri ya daka tsalle sama ya kawo min sara akai da nufin ya raba kai na da wuyana, cikin matukar zafin nama na goce ma harinsa amma sai da kaifin takobinsa ta yanki gashin kai na,anan muka kaure da azababben gumurzu inda waziri ibbahu ya wanzu yana kawo min sara da suka ta ko'ina nikuma na wanzu ina mai kare saransa, duk da karfin saransa ta ninka nawa,
.
Sai da muka shafe kusan sa'a daya muna fafata kazamin gumurzu amma dayanmu ya kasa samun nasara akan abokin gwaminsa, har sai da takai ga takubbanmu sun dusashe, waziri ibbahu ya yarda takobinsa amatukar fusace ya kwarara ihu wacce ta haddasa karamar girgizar kasa sannan ya nufoni a guje, yana karisowa dab dani ya daka tsalle sama yana mai kawo min naushi a fuska, koda naushin nasa ya sameni sai nayi baya tamkar an janye ni da majaujawa, cikin zafin nama waziri ibbahu ya daka tsalle daga inda yake ya dirga a gabana yana mai kawo min naushi a karo na biyu, cikin zafin nama na gocewa naushin nasa, nan muka cigaba da kaiwa junanmu naushi da mangari, koda muka aka fara wannan fafatawa sai nagane kurata, domin kuwa karfin naushin waziri ibbahu ya ninka nawa sau biyar, tsananin naci da juriyane yasanya ko ya nausheni nake kokarin ramawa,
Kafin kankanin lokaci har waziri ya hadamini jini da majina, takai ga cewa kare kaina kawai nake bana iya mai da martani, muna cikin hakanne waziri ya cakumeni ya daga sama
SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@ Shuraih 99%
Part 2E
Kafin kankanin lokaci har waziri ya hadamini jini da majina, takai ga cewa kare kaina kawai nake bana iya mai da martani, muna cikin fafatawarne waziri ya cakumeni ya daga sama ya damfara da kasa tsananin zafin danaji ne ya sanya na kurma ihu,
.
Waziri na ganin haka ya bushe da dariya sautin dariyar tasa tai ansakuwa a cikin daren, sai da ya dau lokaci mai tsayi yana tikar dariyar tamkar zautacce lokaci guda ya yanke dariyar tasa yana mai turbune fuska yace "yakai wannan tsoho mai tsananin taurin kai, shin yanzu ina amfanin taurin kan naka,ka ki bari na kashe ka cikin sauki to zan yi maka mummunan kisa wacce babu wanda aka taba yiwa irinta, nine Sarki Ibbahu ibn kalzim ibn kusumu ibn gurzum, jarumin jarumai dodon sadaukai, kuma SADAUKI UBAN SADAUKAI," waziri na zuwa nan a zancensa ya daga takobinsa da nufin ya caketa a cikina, a wannan lokaci ina kwance akas ina haki, hannuna na rike da wata yar karamar wuka dana soketa a karkashin takalmina, cikin zafin nama na mike cikin wani irin salo na shammaci waziri ibbahu na soka mai wukar a kwayar idonsa na hagu, waziri ya kwarara ihu data haddasa ginin gidan ya fara rushewa, cikin zafinnama na suri jaririyar da nuzaira ta haifa na falfala a guje ina mai ficewa daga gidan, koda na fito daga gidan sai nai ta tikar gudu babu kakkautawa,
.
Ina cikin gudun ne na dunga jin takun sahu a bayana alamar ana biye dani,koda na juya sai nai arba da waziri ibbahu yana falfala azababben gudu wukar dana caketa a kwayar idonsa tana ciki har yanzu, ina ganin haka na fara neman taimakon ubangijin musulunci, daya tseratar dani daga sharrin wannan azzalumi, sai da ya kasance baifi saura taki guda ba waziri ya cimmini sai wani guguwa ya bayyana koda bayyanar guguwar sai ta sureni tai sama dani,
Ban san iyakacin tafiyar da guguwar tayi dani ba illa tsintar kaina danayi a cikin wannan kungurmin daji, tun daga wannan rana na fara sabon rayuwa ni da jaririyar gimbiya nuzaira a cikin wannan daji, bana da abincin daya wuci 'ya'yan itatuwa da naman dabbobi,
.
A haka har jaririyar gimbiya nuzaira ta fara girma da taimakon nonon dabbobi dana ke bata, koda naga ta fara girma sai na sanya mata suna Lubaina,"
Tsoho halixu na zuwa nan a labarinsa sai ya dakata, idanuwan lubaina sai kwararar da hawaye suke,yarima juraish dake gefe ya dafa kafadar lubaina cikin salon tausayawa
Tsohon ya dubi lubaina yace "yata wannan shine tarihinki da tarihin kasarki, na sanar dake wannan labarine domin naji ajikina lokacina yayi da wuya na kara koda sa'a dayace a duniya, "
Tsohon ya maida dubansa kan juraish yace "yakai juraish miko hannunka" babu musu yarima juraish ya mika masa hannunsa, tsoho halixu ya kama hannun juraish dana lubaina ya hada guri daya yace "kuyi mini alkawari cewa bazaku taba rabuwa ba, zaku kasance a tare har mutuwanku sannan zaku bar wannan daji ku koma birnin maharsabar ku yaki waziri ibbahu domin nasan mulkin zalunci yake shimfidawa," tsoho halizu na gama fadin hakan ya furta kalman shahada kafin Rai yayi halinsa
.
Bayan kwana biyar da rasuwan tsoho halizu yarima juraish da budurwa lubaina sukai shiri suka fice daga cikin dajin da suke rayuwa suka tunkari gabashin dajin duk da basu san inda suka nufa ba,
.
Sai da suka shafe sama da kwanaki hamsin suna tafiya akas amma ko alamar karamin gari basu gani ba, illa kutsa kai da suke cikin dazuzzuka, tun da suka fara tafiyar suke cin karo da muggan dabbobin amma zuwa daya suke yi musu su hallakasu, basa da abincin daya wuce namun dabbobin da suke hallakawa da 'ya'yan itatuwa, babu abun da ke tsaida su a tafiyar face tsaida Salla gamida bacci
,
A kwana na sittin ne suka iso cikin wani yalwataccen daji mai dogayen bishiyu kalan ganyayen bishiyun sun kasance jajayene, hatta ciyawar dataiwa kasar dajin dabe jace, dajin a yalwace yake da manya manyan koramu, koda yarima juraish da lubaina suka tsinci kansu a cikin wannan daji sai suka cika da tu'ajjibi domin tun da suke a rayuwarsu basu taba gani ko jin labarin wani daji daya kai wannan kawatuwa ba,
,
Take suka fara kalle kalle a cikin dajin, babu abun da ya kara basu mamaki face gani da sukai fulawowin dajin suna dauke da idanuwa,baki da hanci kuma ma har magana fulawowin suke wa junansu,
Yayin da fulawowin sukai arba da su yarima juraish sai suka fara rera wata waka mai dan karar dadi, wacce dadinta ya isa ya mantar da mutum dukkan wani jin dadin duniya,
.
Koda yarima juraish da yarinya lubaina suka kara gaba sai suka hango wani dan karamin gida agabansu gidan sai kyalkyali yake har yana kashe masu idanuwa, ita de wannan gida an sana'anta ne da zallan dutsen lu'u lu'u, suna isowa kofan bakin kofan gidan yarima juraish yakai hannu da nufin ya bude kofar, kafin hannunsa takai ga mabudin kofan sai kofar ta bude da kanta, cikin mamaki yarima juraish ya dubi lubaina sannan suka kutsa kai cikin gidan atare
.
Suna shiga kofan gidan ya kulle kanshi, yarima juraish da lubaina suka fara tafiya a hankali suna masu karewa gidan kallo, ga wanda yaga gidan ta waje zai dauka karamin gidane amma ta ciki ba haka yake ba, domin kuwa tamkar babbar fadar wani mashahurin sarki ne, wasu irin kwaya kwayen sihiri ne dake yawo akan iska suka haskake dakin tarwai,
Nan su yarima suka cigaba da kutsa kai cikin lungu da sakunan gidan suna ganin abubuwan Al'ajabin da basu taba gani ba, a dakin karshe ne sukai arba da kwarangwal da kasusuwan bil adama bila adadin, suka futo daga cikin dakin suka nufi kofan ficewa daga gidan, koda suka iso bakin kofar sai yarima juraish ya kama kofar da yaja da nufin ya bude, amma kofar taki buduwa, babu irin yadda basuyi ba don su bude kofan amma kofan taki buduwa
.
Suna kokarin bude kofan kenan kwatsam sai wata zazzakar murya ta bayyana tana mai kyalkyalewa da dariya, dukkansu suka juyo don ganin me muryar,anan sukai arba da wata kyakkyawar budurwa tana kyalkyale dariya
SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@ Shuraih 99%
Part 2F
Suna kokarin bude kofan kenan kwatsam sai wata zazzakar murya ta bayyana tana mai kyalkyalewa da dariya, dukkansu suka juyo don ganin me muryar,anan sukai arba da wata kyakkyawar budurwa tana kyalkyale dariya
.
Ita dai wannan budurwa tana zaune ne akan wani kasaitaccen karagar mulki da'aka sana'anta da zallan yakutu, budurwar na sanye da doguwar rigan alhariri an yiwa rigar cinbaki da lu'u lu'u ya rigar dame jikinta ta yadda ya bayyana dukkan wasu surorin jikinta,
.
Yarima juraish ya saki baki yana kallon

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment