Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasika
ta kunsa sai tai umarni da a fille kan wannan manzo
da ya kawo wannan wasika , . Koda manzon nan yaga
Abin dake shirin faruwa sai yazare takobinsa sannan
yadan ja baya kamar taku biyar haka sannan yai wata
irin wasa da takobinsa , Nan take wani murgujejen
kato daga cikin fadawan mahaifiyata yataso da niyyar
yai ma wannan manzo kwaf daya koda bakin bawan
ya kaimai sara sai ya tsuguna saran tawuce , . cikin
zafin nama manzonnan ya shammaci wannan bakin
bawan Aljanin ya fille mai kai. . Haba aikoda sauran
fadawa da askarawa sukaga abin daya faru ga dan
uwansu sai gabadayansu sukayi kan wannan manzo
kowannensu rike da mugun makami . . Karasowarsu
kedawuya wannan manzo Ya taresu da sara suka
,woho ho idan da mutum zai ga yadda bil'adama daya
kadai ya gagari dubun Aljanu, . Baka ganin komai
face jikkunan Aljanu dake yawo a sararin samaniya,
Idan bala'I tai bala'I masifa tai masifa toh yan kallo
kanshiga tasku mai tsanani, Ai koda sarauniya
dubyalu wato mahaifiyata ta fuskanci idan akaje
ahaka wannan manzo zai iya karar mata da mayaka, .
Cikin kunan rai da zafin murya tace ma dakarunta su
tsaya bayan sun tsaya Sai tai dubi izuwa ga wannan
manzo ma'abocin rufe fuska,sannan tace yakai
wannan manzo kasani kayi mani babbar barna kuma
sai ka fanshe wannan barnar dakayi mani , Sannan
kuma ka gaya wa sarkinku cewa mu baza mu bar
bautar wannan gunkiya ta maciji ba, . ba zamubar
tafarkin iyaye da kakanni ba, Kuma kafada masa
muma mun shirya mayakin ya tare mu izan yana
ganin zai yi nasara . ****** **********
**************** Kasar nurul ansar kasace na
musulmai zalla wadda sarki abul abbas yake mulka .
Sarki abul abbas Adaline kuma mai jinkan
talakawansa . Talakawa na alfahari da shi sannan
kuma suna jin dadin mulkinsa don yana kwatar musu
yancinsu daga hannun azzaluman attajirai . Babu
abinda ya tsana kamar zalunci da azzalumai Burinsa
shine kaf duniya su kasance musulmai baki daya .
Jarimin gaskene don acikin tarihinsa ba asamu
wanda yayi galaba akansa ba Har iwannan zamani .
Yana da 'da guda daya wanda ake kira da yarima hilal
. Kyakkyawa ne wanda ma a ranar da'aka haifesa sai
da mutane suka ringa tururuwan zuwa ganinsa daga
kauyuka da sauran kasashen nahiyar baki daya . Mata
kuwa binsa suke suna kokarin cusa kansu gareshi
amma shi basu bane a gabansa ba . *********
*********** ********* Koda wannan manzo da
sarki ya aika kasar sarauniya dubyalu. Yadawo ya
zaiyane ma sarki abin daya wakana . Nan take sarki
ya harzuka yace ma sarkin yakinsa maisuna lamiru .
"Ya kai lamiru ina son gobe inga tawagar da zamuje
mu rusa birnin kafirannan . Lamiru yace' angama
ranka shi dade . Washe gari runduna ta hadu iya
haduwa aka buga kugen yaki Sannan aka tasamma
garin iblisha garin da sarauniya dubyalu ke mulki
....... Sarauniya dubyalu ta dade da samun labarin
tashin su sarki abul abbas . Nan itama ta hada nata
rundunar suka nufi filin daga •••••••••••••••
/TAKobin jini . Book 2 . Part 2 Marubucin Littafin
Shuraih Usman . Isowar su sarki abul abbas filin daga
keda wuya sai suka tarar da mahaifiyata wato
sarauniya dubyalu da dakarunta na aljanu . . Su dai
rundunar su sarki abul abbas dakarunsu sun kai
milyan biyu . Abul abbas ne agaba sai sarkin yaki
agefen hagunsa yayin da yarima hilal yake gefen
damansa . Yarima hilal shima zartone kuma jarumi
don shi kadai yana iya fada da mutane sama da dari
sannan ya karsu . . Mu kuma rundunar mu wato
rundunar mahaifiyata sarauniya dubyalu Yawan
adadinmu ya ninka na su abul abbas sau uku amma
wannan bai tsorata su ba . . A lokacin da'aka kacame
da masifaffen yaki duk ina kallon abin dake faruwa ta
hanyar wani madubin tsafi . Yayin danaga yarima
hilal yana yi mana mummunar barna sai na shiga
tura masa da wasu guma gumai na wuta Koda
wayannen guma gumai suka zo daf da shi sai naga ya
fadi wata kalma nan take wannan guma gumai suka
juyo izuwa kan dakarunmu suka ringa kashesu . Koda
nai duba izuwa ban garen sarki abul abbs sai naga
yana tai mana barna domin duk inda ya dosa sai de
kaga gabobin aljanu na yawo a sararin samniya .
Yayinda mahaifiyata dubyalu keta barna cikin
dakarun su abul abbas sai aka samu wani barde mai
zafin nama ya sari dokinta nan take ta fado daga kan
dokin hade dayin wata wuntsilawa wanda kafin takai
kasane ta rarumi mutane biyar sannan tai kasa da su
nan ko shurawa ba suyi ba .$ Yarima hilal ya lura da
irin barnar da dubyalu ke musu $ Wannan tasa ya
dumfareta koda ya rage baifi saura taku isshirin ya
kariso wajen da take ba sai ya falfala da wata
azababben gudu sai da ya kusa zuwa inda take ne sai
yayi wata tsalle yai sama yayin dayake dawowa izuwa
kasane yasa kafa ya doki kirjin dubyalu . Nan take ta
furzar da wani gudan jini daga bakinta sannan itama
ta falfala da gudu ta nufe shi da takobinta wanda ya
rine da jinin bil adama $ . Haduwarsu keda wuya ta
kaimai wani sara da nufin ta fille masa kai amma
cikin zafin nama ya tsuguna wannan sara ta wuce ta
saman kansa . Ko juyowa bai gama yiba dubyalu
takara kai mai wani saran ta gefen cikinsa nan ya kare
saran da takobinsa nan tartsatsin wuta ya fallatsa .
Shima hilal sai ya kaimata wani naushi da nufin ya
zubar mata da hakori baki dayansu amma koda ya
naushetan sai yaji tamkar ya naushi dutse Yayin da
dubyalu taga haka sai ta kyalkyale da wata
mahaukaciyar dariya sannan tace$ . Kasani yakai
wannan jarumi kayi babbar kuskure wadda sai kayi
dana sanin yinta yayin da danasin bazai amfaneka da
komai ba . Kasani yau zan dandana maka dacin
mutuwa wanda ban taba yiwa wani bil adama ba$ .
Koda jin haka sai hilal yace yake wacennan sarauniya
wadda take cikin bata , ina yimaki kashedi na karshe
da ki bar wannan Addini na shirka da kike ki dawo ga
tafarkin gaskiya tafarkin Annabi Ibrahim AS Izan
kuma ki ka bijire wato kikaki toh lallai zan hallakaki
halaka mai muni . Dubyalu najin haka sai ta fusata
ainun sannan ta daka wani tsalle tai sama yayin
datake saukowa ne ta kai ma hilal sara cikin zafin
nama da gwaninta ya goce na saran sannan shima ya
kai mata nashi . Sai da suka shafe kimanin sa'a biyu
suna dauki badadi sannan hankalin dubyalu ya tashi
ta tuna cewa ita fa basadaukiyace acikin aljanu ta
gagari sarakunan aljanu da dama amma wannan
karamin bil'adaman naso ya bata mata lokaci Aikoda
tagama ayyana hakan aranta sai tayi wani tsalle
sannan ta kaima hilal sara acinya da nufin ta fille
cinyra gaba daya cikin zafin nama yatare wannan
saran amma sabida karfin saran saida ta yankkesa a
gefen cinya nan ya kwala ihu Koda dubyalu taga haka
sai tayi dariyar mugunta sannan tayi kansa da nufin
ta hallakashi wani wawan sara ta kaimai takai cikin
zafin nama taga anyi sama da shi sannan wannan
saran data kau an tare sa da wani irin takobi nan take
wata tartsatsin wiyta ta bayyana . Sarki abul abbas ne
ya baiyana yana mai rike da wata takobi da kuma
garkuwa . Nan take sarki abul abbas ya fiddo wata yar
batta sannan ya karanta wasu addu'oi sannan ya
bude battar aiko yana bude battar sai mahaifiyata
dubyalu ta ji tamkar ana fizgota da wani irin kuqiya
nan take ta ringa rikedewa izuwa hayaki tana shiga
cikin wannan battar$$ . Tana gama shiga sarki ya like
bakin battar sannan ya bada umarnin akai yarima can
tanti amai maganin wannan rauni da sarauniya
dubyalu ta mai . Ta wannan hanyarne aka cimu yaki
sannan aka kama mahaifiyata aka kulleta acikin wani
kurkukun kasan kasa cikin wani akwati . . . Nan take
suraila ta rude ta rasa yadda zatayi amma haka dai
tai dauriya ta kara tambayasa " To ni kuma mai na
maka da har kakeson ka hukun tani. . Yayin da aljani
sham'una yaji wannan kalami nata sai ya bata rai
yaringa huci wani bakin hayaki na fita daga bakinsa .
Yace da'ita" ki sani cewa na kai tsawon watanni goma
ina jiran zuwanki . Don tsafina ya tabbatar min kece
kawai zaki iya taimakamin na samu abin da nake
nima . Ki sani cewa yayin da sarki abul abbas ya kama
mahaifiyata na shiga tsananin kunci da bakin ciki. .
Nayi ta neman hanyar da zan ci galaba akan sarki
abul abbas amma bansamu ba sai da na shiga halwar
tsafina nayi bincike na tswon wata biyar sannan na
gano wata hanya . . "Bazan taba cin galaba akan sarki
abul abbas ba sai na mallaki TAKOBIN JINI Wanda
ayanzu haka yana can cikin kogon sha jini. . . Binciken
tsafina ya nuna min in harde mna mallaki takobin jini
toh duk duniya Babu wanda zai ci galaba akaina ki
sani zan mulki duniya gaba dayanta kowani mtum a
duniyar nan zai dawo karkashina . " . . Sannan yakara
da cewa" banason wani tambya dga bakinki" yana
gama fadin haka sai ya sureta suka luluka sama . . .
Wannan shine al'amarin daya afku ga suraila matan
marigayi sarki ashbir . ¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤.
¤¤¤¤¤¤ . . Al'amarin gulmanu kuwa ya wakilta
wazirinsa dariku akan yaje kasar dimashka don ya
nemo mai auren sarauniya lasmin. . Duk da waziri
dariku yasan masifar dake cikin wannan tafiya haka
ya daure yabi umarnin sarki don ya zauna lafya. .
Washe gari da safiya ya hada dakaru mutum dari
sannan ya fice daga birinin ashdamir . . Yayi tafiya
mai tsawon gaske tafiya ta kwana ashirin ba yada
zango , Sannan suka iso binin dimashka isowarsu
keda wuya suka yada zango abayan birnin sakamakon
lokacin darene Baccin sun yada zango kenan sun
huta sannan suka kafa tanti kowa yafara shirin bacci .
. Wayanda aka barsu suyi gadi suna cikin gadi sai
suka ga gari yai duhu sosai hasken farin watan dake
haskaka wajen ya dushe . Can sai suka ga wasu
dakaru manya manya in ka gansu ka rantse
samudawa ne. . Koda isowar wayannan dakaru sai
shugaban su yai wata irin kara wadda tasa su waziri
dake barci suka farka a gigice. . . Waziri ya fito daga
cikin tantinsa Koda yayi arba da wayannan dakaru sai
wata matsananciyar tsoro ta baiyana a fuskarsa
karara . . Shugaban wayannan dakaru masu kama da
samudawa yace ma waziri " Ya kai wannan bawa
makaskanci mai ya rudi zuciyanka har kazo yankinmu
. Toh kasani kayi babban kuskure a rayuwarka wadda
sai kayi dana sanin yinta yayin da dana sanin bazai
amfanekaba . . Shin meya kawoka wannan yanki
Badakaren ya tambayi waziri cikin daka masa tsawa .
Waziri baki na rawa yace "Sar-kin-n kas-ar ashda-
a.mir ne ya" Kai kayi magana man katsaya sai in ina
kake min .badakaren yasake daka matsa tsawa akaro
nabiyu . . Sannan yace koma waye ya aiko ka in kaje
gaban sarauniya ai kayi bayani , Nan wayannan jibga
jibgan dakarun suka kame gabadaya dakarun waziri
dashi kansa . Suka tasa keyarsu izuwa cikin birnin
TAKOBIN JINI . Book 2 Part 3 Marubucin Littafin
Shuraih Usman . . Yayin da suka isa dasu cikin birini
dimashka basu wuce ko ina dasu ba sai wani katon
gida da alama dAi Duk mai waNnan gidan to dan
shan iska ya ginashi$ . . Gidan baya da fasali da ga
waje amma in kashigo ciki to anan ne zaka ganema
idanuwanka ababen al'ajabi . Bakaramin gida bane
Acikin wani daki ne aka sauke waziri sauran dakarun
kuwa suma wani dakinne akayi dasu . Wannan
shugaban dakarun yace ma waziri gobe zamu
gurfanar daku agaban sarauniya duk hukuncin data
yanke gareku deade yake . . Hantar waziri taa kada
yayin daya yi dana sanin zuwansa . Da gaei ya waye
aka fiffito fada Wannan shugaban dakarun yazo daf
da kunnen sarauniya lasmin ya fada mata wani
magana . . Sarauniya lasmin itace ke mulkar birnin
dimashka Ta gaji mulkine a wajen kawunta sarki
hutmus . Ta kasance tana lullube fusakarta da wani
mayafi duk lokacin da zata fito fada hakan yasa
bakowani mutum bane yasan fuskarta . . Koda taji
wannan magana sai tace " Yakai hibru maza jeka kazo
min dasu wayannan bakin . . Wannan garjejen katon
shugaban rundunar wadda sarauniya ta kirashi da
hibru ya tashi ya fice daga fadar . Can bayan wasu
dakikoki sai hibru tafe da waziri dariku Sai muzurai
yake . Koda suka iso fadar sarauniya lasmin anan
zuciyarsa ta kusan tsayawa domin kuwa ko ba'afada
ba ruwa ba sa'an kwando bane . Tun da waziri dariku
yake a duniya bai taba ganin wata fada wadda takai
na birinin haduwa ba Domin ita wannan fada dabenta
anyi sane da zubarjade . Yayin da akayi wata karaga
ta zinari wadda aka mata ado da yakutu ajikin karagar
wasu zane ne na takubba wanda adadinsu yakai
asihirin . Azaune akan karagar ba kowa bace face
sarauniya lasmin . Da wannan lullubi a fuskarta .
Sannan tace ma waziri "Yakai wannan bako mene ne
dalilin dayasa kashigo nahiyata batere da iznina . Nan
waziri yai sauri ya zaro wata wasika Ya mika ma wani
bafaje . Koda bafajen ya karba sai ya mikata izuwa
hannun magatakarda Magatakarda yasoma
karantawa " Sako daga sarkin sarakai sarkin duniya
Wato sarki gulmanu mai mulkin kasar ashdamir.
Izuwa ga kyakyawa kuma sarauniyar kyawawa kisani
tunda na naga wannan fuskar taki dakike rowanta
naji duk duniya babu wacce nake muradin ta xama
mata in bake ba . Ga waziri na nan shizai. Wakilce ni
adaura sannan sai ku taho kasata tare dashi . Sako
daga mai duniya . . Koda maga takarda yakawo
karshen wasikar sai sarauniya lasmin tai wuf cikin
zafin nama ta zare wani takobi sannan ta kaima waziri
dariku sara Sai da yarage bai wuce taki daya ba ta
guntule kan waziri sai tsayar da takobin dedai
wuyansa. . Waziri kuwa ya riga daya sallama jira
kawai yake yaji saukar takobin amma sai yaji shiru . .
Koda ya bude idonsa sai yaga abin daya firgitashi .
Kyakyawar fuskar Sarauniya lasmince yai maraba ma
idaunawansa . Dukda tana cikin bacin raine amma ya
tabbata kafin asamu kyakyawa kamar ta sai antona . .
Farace siririya wadda fuskarta shima yake madaidaici
takasance ita ba doguwa ba kuma ba gajeruwba .
Fararen idanuwanta masu sheki wayanda on mutun
bai lura ba sai yace bata da bakin ido . . "Kayisani
yakai wannan dan sako ni nafi karfin sarkin ka
Sannan kaje kafada mai cewa nace in yaki yake ji toh
TAKOBIN JINi . Book 2 Part 4 ¤¤¤¤¤ Marubuci Littafin
Shuraih Usman . Sannan kafada mai kar yaga ya
kashe sarki ashbir ya zata cewa nima irinsa ce Ni
dabance acikin sarauniya . . Nice mai mulkar
dimashka gabaki dayanta shine zaice in auresa .
Wannan ma ai zancen banza ne . Nan take sarauniya
lasmin tasa aka kame gabadaya dakarun waziri
dariku su darin . Ta antaya su cikin kurkuku sannan
tacema waziri dariku . Kayisani cewa wannan jan
kunnene agareka da kima sarkinka . . . ¤¤¤¤¤¤¤¤¤.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤¤¤ . Gulmanu yana zaune akan
karagarsa ta mulki . Ana ta fadanci, ya harde sai
annushwa yake , . Sai gani akai waziri ya dumfaro
aguje kan doki sai sukuwa yake Yana isowa gaban
sarki gulmanu ya tsai da dokin sannan ya sauko yai
gaisuwa . Farin cikin dake fuskar gulmanu ta canja
izuwa ba cin rai sakamakon ganin wazirinsa yadawo
babu dakarun daya deba sannan babu sarauniya
lasmin . Yadaka ma waziri tsawa cikin hasala "Yakai
wazirina shin meya faru gareka naga duk ka fita daga
hayyacinka " Nan waziri ya bayyanawa sarki gulmanu
duk abinda yafaru . . Ai ko karisawa baiyiba sarki
gulmanu ya karfi takobi ya saremai yan yatsu guda
biyu . Sannan yai jifa da takobin yaringa dukan
fadawansa naushi yarin ga yi musu harsanda wasu
daga cikinsu suka mace . Sannan wani wuta yafara
bullowa ta gaban waziri wanda tunda aka yanke mai
yantsu yake sume haryanzu bai warke ba . Koda
wannan wuta tafara fitowa tanata yaduwa har ta taba
waziri dariku Nan take yatsunsa da sarki gulmanu ya
guntule suka dawo . Sai gani akayi boka balbalin
bala'I ya bayyana hannunsa rike da wata al'amudi na
zinari . Koda gulmanu yai arba da boka balbalin bala'I
nan take yadawo cikin hankalinsa sannan yazo ya
zauna akan karagarsa . . Boka balbalin bala'I na ganin
haka sai ya. Dubi sarki gulmanu sannan yace mai ka
sani yakai gulmanu baza kataba yin nasara akan
sarauniya lasmin ba haka itama baza ta taba yin
nasara akanka ba . In har kanason kayi nasara akanta
to ya zame ma dole kanemi TAKOBIN JINI Inhar ka
mallaki takobin jini to tabbas zaka mulki duniya
gabaki dayanta . Kowa a duniya zai dawo karkashin
mulkinka , " Aina zan samu takobin jinin" Gulmanu ya
tambaya cikin fushi Nan boka balbalin bala'I ya barke
da wata dariya wadda shikansa gulmanu sai da
razana . "Yanzu haka takobin jini yana can a kogon
shajini" Boka balbalin bala'I yafda sannan yakara da
cewa gobe zan baka labarin TAKOBIN JINI da yadda
za'ai ka mallaketa . ¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤¤¤
Al'amarin sarauniya lasmin kuwa da dare ya raba sai
ta sudade ta fita daga gidan sarauta sannan ta yanki
daji taita gudu akan doki . Sannan takai bakin wani
dutse sai ta fadi wasu kalamai wadda ita kadai tasan
ma'anarsu . Rufe bakinta keda wuya sai wannan
dutsen dake gabanta ya tsage sannan ya rabu bari
biyu bari daya yai gefen dama dayan barin kuma yai
gefen hagu . Wani tsohone tukuf dashi gashin kansa
yai tuntu Sannan kasumbarsa ta rufe mai baki
gabadaya fuskarsa ba kyan gani . Yana sanye da riga
falmara na fatan bauna . Sai wani wando data tsaya
mai dedai kauri Wannan tsoho ya bude idanuwansa
Sannan yace maraba da zuwa yake sarauniyar duniya
. Nasan abinda ke tafe dake .
TAKOBIN JINi . Book 2 . Marubucin Littafin Shuraih
Usman Part 5⃣ . Marubucin littafin Shuraih Usman
Wannan tsohon yaci gaba dacewa "ina son kisan wani
abu yake sarauniyar duniya kada ki tari yaki da sarki
gulmanu . Don bazaki yi nasara akansa ba . Haka
shima bazai yi nasara akanki ba sannan kisani shima
yana da dakaru kimanin yadda kike dasu ga shi
babban gwarzone wanda yake dakama maza
gumb........ . "Nima ai basadaukiyace kuma jaruma
don haka babu abin da zai hanani in yakeshi .ta katse
shi dafadin hakan "Kayisani yakai boka kamsusul
lajani babu wani mahalukin dayake duniyarnan
wanda bai da lago . Shima haka zata kasance
agareshi kuma sai kasheshi da wannan hannun nawa
. . Boka kamsusul lajani yace tabbas zaki iya kashe sa
. Kisani yanzu aduk duniyarnan babu wata makami
daza kiyi amfani da ita wajen ganin bayan sarki
gulmanu face TAKOBIN JINI . "Menene kuma takobin
jini" Sarauniya lasmin ta tambaya cikin matukar
mamaki . Tabbas zan sanar dake labarin takobin jini .
Da kuma wajen da zakije ki daukoshi Sannan da irin
hadarurrukan daza ki shiga kafin kikai ga mallakar
wannan takobi . Kisani anyi jarumai,bokaye ,da aljanu
mutane ,wayanda suke son mallakar takobin jini
amma duk sun rasa rayukansu garin fafutukar
mallakarsa . Ayanxu dai takobin jini ya can wani kogo
wanda ake kira da kogon shajini . Izan tauraruwa
zahlu ta yarje maki gobe sai kizo in sanar dake
labarin takobin jini da kuma hanyar daza kibi ki
mallakeshi . . ¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Sarki
abul abbas kuwa tunda suka yaki birnin aljanun
sarauniya dubyalu suka ci galaba akansu . Suka dawo
cikin birnin nurul ansar hade da ganima mai tarin
yawa . Bayan wasu yan kwanaki yarima hilal yana
cikin barci sai yayi mafarki " Yana cikin tafiya acikin
wata daji mai sarkakiya Sai yaringa jin ihun mace
tana neman taimako koda ya kariso wajen Nan take
yai arba da kyakyawan fuskarta masu matar da
dukkan gabban jikin dan adam . . Tana ganinsa sai ta
yi wuf ta rungemeshi tana cewa ka taimakeni
kataimakeni yatsanta nanuni da wani waje daban .
Koda yarima hilal ya lura da kyau sai yaga ashe wata
babbar macijiyace wadda tsabar girmanta zata iya
hade mutani dari alokaci daya . Wannan macijiyar
takasance kanta na wani mummunar aljani ne yayin
da gabban jikinta na macijiyace . Nan take yarima
hilal ya fiddo takobinsa sannan yafara addu'a yana
neman tsari . Aiko nan take wannan macijiyar ta bace
kamar bata taba wanzuwa a wajen ba . . Firgigit ya
farka daga barcin sannan yai addu'a . Abin ya tsaya
mai arai ya ringa tuno fuskar ta wanda bazai taba
goguwa a cikin kwakkwalwarsa ba . Ya kishingida
akan lallausar katifar dayake kwance akai . Ya runtse
idanuwansa. Amma ina daya runtse idanun baya
ganin komai sai fuskarta mai alamar tsorata karara . .
Shin wacece ita To be con
TAKOBIN JINI . Book 2 Part 6⃣ Marubucin littafin:-
Shuraih Usman . Nan fa nan fa hankalin yarima hilal
tai matukar tashi ya . . Har asubah bai samu ya
runtsa ba Haka yaje masallaci yabi jam'i Bayan
yadawo daga masallacinne wata nannauyan bacci tai
awon gaba dashi . Sarki abul abbas bisa kan karagar
mulkinsa ya harde sai annashwa yake halama dai yau
yana cikin farin ciki . Koda sauran fadawa da hakimai
suka haka suma sai wannan farin cikin ta bayyana a
fuskarsu . Ba komai bane yasanya su farin ciki ba illa
tunda ga ranar da matan sarki abul abbas ta rasu
Duk wata walwala da annashwa suka kaura ga fuskar
sarki abul abbas Amma abin al'ajabi sai gashi yau
sarkine yake cikin walwala wanda takasa boyuwa ,
Koda ganin haka sai sarki abul abbas yace ma waziri
"Yakai waziri kayi sani yau ina cikin wani yanayi na
farin ciki wanda ban taba tsintar kaina aciki ba, " .
Waziri yace "Ranka shidadea nima kaina na fahimci
wannan yanayi dake fuskarka ayau dinnan da alama
wani babban al'amarine ke shirin faruwa . Sarki
yace"Tabbas maganarka haka take wani Al'amarine
ke shirin faruwa kuma wannan Al'amari ina murna da
farin ciki da zuwansa domin shine Abin dana ke fata
kafin Allah (SWT) yadauki raina na ganshi da Idona .
Koda waziri yaji wannan zance daga bakin sarki abul
abbas sai fuskarsa ta fadada da murmushi sannan
yace"nima ina farin ciki da faruwan wannan
Al'amari" . Yayin da yarima hilal ya farka daga barci
sai ya tsinci kansa yana mai begen wannan
kyakkyawar fuskar daya ganta cikin mafarki . Lokacin
daya iso fadar sai ya zauna akan tasa karagar sannan
ya dubi mahaifinsa yace mai "ya Abbana ina son nayi
magana dakai" . Koda jin hakan sai sarki ya mike
yashiga cikin gidan sarauta yayin da yarima hilal ke
biye dashi " Wani hadadden lambu mai furanni tako
ina yayin da dabbobi keta yawa tawansu aciki . "Yakai
dana shin menene ke tafe da kai" Sarki abul abbas
yafada yayin dayake duban yarima hilal . "Abbana
kasani jiya nayi wani mafarki acikin mafarkin nawane
naga wata kyakkyawar sura tana neman taimako na ,
Abba kasani na kamu dason wannan sura " Hilal
yafada yayin dakansa ke asunkuye . Nan take sarki
abul abbas yafashe dawata mahaukaciyar dariya
sannan yadafa kafadan hilal yacemai" yakai dana ni
na yarje maka akan wannan yarinya kaje ka nemota
duk inda take Sannan kuma zan taimaka adaren yau
zanyi istihara ingani ko wannan yarinya matarka ce
Da kuma inda take . Nan take yarima hilal ya
rungume mahaifinsa yana mai murmushin farin ciki
*********** *********** ********* Koda safiya
tayi aka taru afada sarki gulmanu sai huci yake kamar
mayunwacin zakin daya fito farauta . Ayayin da
fadawa da sauran hadimai ko wa yashiga taitayinsa
domin sun san ayadda gulmanu yakennan zai iya
kashe daya daga cikinsu batare da sun aikata wani
laifi ba . Gaba dayan fadan ta ringa girgiza wani sauti
na fita ,sautin irin karar rugujewar duwatsu nan
danan hadimai da fadawa suka hankalinsu ya tashi .
Kamar walkiya sai ganin boka balbalin bala'I akayi ya
bayyana Kamar kowani lokaci ya na sanye da
jememmen rigar fatar damisa sai wani warki tare da
kashin kan bil adama a rataye a wuyarsa . Koda
ganinsa take sarki gulmanu ya gabato gabansa
sannan yace masa "Sannu da karisowa yakai bokan
duniya gaba daya kayisani kai nake tsumaye tuntuni
,ka labarta min labarin TAKOBIN JINI . Boka balbalin
bala'I yadubi gulmanu sannan ya bushe da dariya
mai amon gaske sai da yayi mai isarsa sannan yace
mai "Zahlu tabaka nasara kayisani yanzu zan labarta
maka labarin TAKOBIN JINI . . . KASANCE TARE DANI
Takobin jini . Book 2 . Marubucin Littafin Shuraih
usman Part 7⃣ . . Boka balbalin bala'I yaci gaba da
cewa Kayisani yakai gulmanu TARIHIN TAKOBIN JINI
Anyi wani hatsabibi kuma jarimin gaske shekaru
dubu shida da suka wuce shi wannan hatsabibin
jarumin ya kasance bokane sunansa MURAISU
Muraisu ya gagari duk wasu jarumai da bokayen
nahiyarsu Muraisu na iya yaki da dakaru dubu
sannan kuma ya kashe su dukkaninsu batare da ya
nuna alamun gajiya ba . Muraisu yana da wata kanwa
tasa dayake matukar sonta wadda itakuma ko kadan
bata son halayensa hakan nema tasa ta tafi ta barshi
taje can nisa dashi tayi aure . Duk da cewa muraisu
ya binciko inda take acikin madubin tsafinsa hakan
baisa yaje gareta ba . Sabida kafin ta tafi ta
gargadeshi da kada ya tafi nemanta . To ayayin da
muraisu yaga tsufa tazo masa sannan wannan tarin
kundin ilimin tsafinsa izan har ya bari wani ya
mallakeshi bayansa toh yana iya zama gagara badau
a bayan kasa baki daya wannan tasa ya sana'anta
wani takobi wanda har takaishi tsawon shekaru biyu
sannan ya kammala ta , Wannan takobin takasance
marikinta na jauharine yayin da jikinta gabadaya
anyisane da lu'u lu'u sannan aka gauraya da Jini
wannan shiyasa jikin takobin gaba dayanta launin jaa
ce . Yayin da muraisu ya sana'anta wannan takobi sai
yasa wasu dakaru Dubu dari na Aljanu su tsareta
sannan ya dauki takobin yakaita Kokogon sha jini Ita
wacannan takobi na muraisu yayin da mutun ya
mallaketa toh baza ka taba cin nasara akansaba
sannan kuma wannan ma mallakintan zai mulki
duniya gaba dayanta sabida karfin sihirin dake tattare
da takobin sannan kuma manyan sarakunan Aljanu
har su biyar na ma wannan takobin bauta duk ma
mallakin wannan takobin to zasu kasance masu
biyayya agareshi . Kasani yakai gulmanu babu wani
mahaluki a duniya daya taba shiga kogon shajini
sannan ya fito araye Domin ita wannan kogo ta
kasance matattara ce ta masifu dubu ' Kai kodama
kayi nasarar shiga cikin kogon to baza ka iya daukar
wannan takobi ba Koda duk mutanen duniyarnan
zasu taru bazasu iya daukar taba domin tana cike da
wasu manyan sihiri . Muddin kanason ka mallaki
Takobin jini

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment