Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai da tafito daga cikin keken dokin
.Koda suka daga kawunansu sama sai sukaga
wata tartsatsin wuta nata nata fantsama a
sararin samaniya .Nan take sai wata
jibgegiyar tsuntsuwa mai matukar girma irin
wayannan tsuntsaye ana kiransu da rukki
ne.Bisa saman wannan rukki din wani
sadaukin jarumine yana sanye da sulken yaki
da kuma kaftareren takobi a gefen kugunsa
wannan sadauki ya rufe fuskarsa da wata
hular karfe ..Wannan tsuntsuwa tai kasa cikin
kankanin lokaci ta sauko izuwa doron kasa
,tana sauka wannan jarumin mai kirar
sadaukai ya diro daga samansa ..Sannan
yafara tattaki yana nufan wajen da su
sarauniya lasmin suke ita da hilal .Yana
karisowa yace dasu" yaku wayannan jarumai
shin kuna mamakin ganina ne awannan
lokaci .Shin kuna tunanin ku biyu kadai ne
zakui wannan tafiya izuwa neman TAKOBIN
JINI.Toh kusani nima ina daya daga
cikinku.Lasmin ta dubeshi sannan tace dashi
yakai wannan jarumi ma'aboci lullube fuska
shin wanene kai kuma daga ina kake ..Koda
jin haka sai wannan bakon jarumin ya cire
hular dake kansa .Aiko yana cirewa sai
dakarun dake tare da sarauniya lasmin .Suka
zube bisa gwuiwowinsu suna gaisuwa
gareshi baccin sun idar sai sarkin yaki kumru
ya kariso izuwa gabansa yana mai cewa" ya
shugabana ka gafarceni bisa dadewa danayi
ban iso gareka ba"..Nan take wannan jarumi
yadaga masa hannu sa'annan yadubi su hilal
yace dasu " nine sarki gulmanu mai mulkar
birnin ashdamir"..Sarauniya lasmin ta
dubeshi sannan tace dashi "amma mai yasa
baka jiramu mun iso izuwa birnin ka
ba"Gulmanu ya sauke ajiyar zuciya sannan
yace da ita " tabbas bokana ya nuna min duk
abin dayake faruwa daku tun daga lokacin da
kika fito daga gida har iyanzu da kike dab da
shiga birnina ,koda naga kun hadu da
jarumin da zamu fita nema sai nayi shirin fita
sa'annan na fito don tarbeku .Sannan kusani
yanzu bazamu mu shiga birnina ba zamu
tafine izuwa cikin wancan tanti daga nan sai
muyi shawarar daga inda zamu fara neman
wannan takobiYafada yana mai kallon
hilal.Hilal yai murmushi sannan yace dasu
daza ku yarda ku karbi Addinin musulunci da
nikuma sai na dauko maku takobin jini da
hannuna kuma batare da zoben wuta
ba..Koda gulmanu yaji haka sai ya bushe da
dariya sannan yace mai kasani yakai wannan
jarumi ba zamu taba yarda mu amshi
wannan Addini naka ba .Kasani ba za mu
taba watsi da Addinin iyaye da kakanni
ba.Sannan da kake maganar mu amshi
Addinikan toh izan mun amsa menene
Amfanin takobin jinin.Addininka ya haramta
tsafi mukuma baza mu taba watsi da tsafi ba
..Lasmin ta dubeshi tace yanzu mene abun
daya kamata muyi.Anan gulmanu yai nuni da
hannunsa izuwa wani gefe take sai tanti ta
bayyana .Dukkansu suka nufi wannan tanti
amma banda sauran dakaru .Juyowar da
gulmanu zaiyi sai yai arba da shaddadu yana
mai murtuke fuska yana binsu izuwa cikin
wannan tanti.Nan yadaka masa tsawa
yace"kai daedai matsayinka wajen tantin nan
badae cikinsa ba .Shaddadu ko sauraransa
baiyiba in banda sakai dayayi da nufin ya
kutsa cikin tantin aiko yana kutso
kangulmanu yai tsalle ya kaftara masa dundu
abaya sannan yai nuni da hannunsa gareshi
take ya fara daskare wa tundaga kan yatsun
hannunsa koda shaddadu yaga yana
daskarewa sai ya kurma wata irin ihu ..A
yayin dayake ihunne gaba dayan jikinsa ya
daskare yakoma tamkar wani mutum
mutumi
.
..Zanci gaba.TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina Uku (3)
Littafin Shuraih Usman
Part 6
.
Nan sarki gulmanu ya bushe da dariya
wanda ta haddasa karamar girgizar kasa sai
da yayi mai isarsa sannan yai shiru ya dubi
sarauniya lasmin yace " haka kike da bawa
mara jin magana, toh ga abinda rashin jin
maganarsa ta janyo masa"
.
Yana gama fadin hakan sai yasa kai cikin
wannan tantin suma suka bishi abaya
,
Wani kyamushashshen tsohone sanye da
warkin fatan zaki ,
Zaune yake ya nannade kafa , kai kace wani
mashahurin malamine ,
,
Gaba daya idanuwansa a rufe suke bakinsa
ne kawai ke motsi,
,
Koda su sarauniya lasmin sukayi arba da
wannan tsohon sai suka kura masa idanu
suna kallonsa
Sarki gulmanu yace dasu" wannan shine
dirkar birnina boka bal balin bala'I,sannan
kuma da taimakawarsa ne har zamu iya isa
inda aljani sham'una yake"
.
Boka balbalin bala'I ya dubesu daya bayan
daya sannan yafara da cewa"
Yaku wayannan zaratan jarumai kuyi sani
cewa gaba dayanku kun dauko wakanku
babban buri wadda muddin ku ka cika
wannan buri toh tabbas duniya zata shiga
halin kunci da takaici,
,dayanku ne kawai zai mallaki takobin jini,
biyun ku kam sai dai su hallaka,
,
Koda sarki gulmanu yaji haka sai ya dubi
boka balbalin bala'I yace dashi" amma mai
yasa. Baka sanar dani hakan ba tun da wuri"
.
"Nima kaina yaune aka sanar dani "
.
Sarauniya lasmin ta dubeshi tace " waya
sanar dakai"
.
Wani aljani ne daga cikin Hadimaina mai
suna Lumzaru ya sanar dani hakan"
.
Hilal ya dubesu gaba dayansu yace "
innalillahi wa'inna ilai hirra ji'un, da zaku
tuba ga Allah ku bar shirka ,da tsafi toh da ni
zan dauko muku wannan takobi batare da
kunsha wata wahala ba"
.
Gulmanu ya dubeshi yana mai murnushi
yace" kai yarone shi yasa kake fadin wannan
maganar da kasan bazai taba yiwuwa ba,"
.
"Kubar wannan takaddamar yanzu ba
lokacinsa bane , kamata yayi mu nemi mafita
game da wannan tafiya da zamuyi"
Sarauniya lasmince tai wannan furuci a yayin
datake duban hilal da gulmanu
.
Nan boka bal balin bala'I ya tashi daga zaune
ya dubesu yace" wannan tafiya da zakuyi zan
hada ku da Aljani lumzaru amintaccen
hadimina ne shine kadai zai iya kaiku dajin
da aljani sham'una yake , ku sani kafin ku isa
wannan daji sai kun fada cikin masifu da
bala'I kala kala ,
Muddin kuka tsallake wayannan masifun to
tabbas zaku isa ga wannan jeji da aljani
sham'una yake , sai dai nayi nayi in gano
inda ya boye suraila , amma nakasa.
.
Koda gama fadin hakan sai boka bal'balin
bala'I ya bace bat,
,
Bace warsa keda wuya sai wani katon aljani
ya baiyana , shi wannan aljani jikinsa gaba
daya irin na mutane ne, sai dai girma da
Allah ya bashi gashi da wasu fuka fukai a
gadon bayansa ,yana dauke da wata
narkeken kai wacce in mutum yai arba da
wannan kan nasa to yana iya zaucewa ko ya
hallaka, ma
.
Koda bayyanar wannan aljani sai ya dubi su
sarki gulmanu yace " Sunana aljani lumzaru,
sannan kuma nine zanyi muku jagora izuwa
jejin da sham'una yake
.
Bayan dukkansu sun hau bisa kan aljani
lumzaru nan ya tayar da fuka fukansa sannan
ya tashi sama ya luluka cikin gajimare
.
Wani dokar dajine wanda rairayinsa na
hamada ne wasu kananun ciyayi sun yi dajin
lema, a gaban wannan dajin wani tafkeken
korama ce,
Ruwan dake gudana a cikin koramar kyalkyal
da shi gwanin sha'awa,
,
Wani bakin abu na hango a sararin samaniya
yana yiwo kasa, sai da wannan abun ya
kariso izuwa kasa sannan na lura ashe, aljani
lumzaru ne dauke da sarauniya lasmin da
sarki gulmanu sannan yarima hilal,
,
Saukarsu a wannan jeji keda wuya, sai
yarima hilal ya nufi bakin wannan kogi yai
alwala, koda ya idar sai ya tada kabbarar
sallah , nan ya shiga ramakon dukkan sallolin
da bai samu damar yinsu ba,
A gefe kuwa sarki gulmanu ne da sarauniya
lasmin tsaye kusa da juna suna kallonsa,
yayin dayake gudanar da ibadarsa,
"Ni ban taba ganin irin wannan bautar ba,"
sarauniya lasmin ta fadi yayin da take duban
hilal,
"Ta yaya zanriga bautawa abin dana ganinsa,
"ta sake fadi akaro na biyu
Gulmanu ya dubeta sannan yayi murmushi
yace" Na tsani wannan Bakon Addinin , dan
hasalima dabara na hada ma hilal, tarko ce
kuma ya shigeta, "
Sarauniya lasmin ta dubeshi fuskanta dauke
da alamun rashin fahimta tace " ban fahimci
abin da kake nufi daya fada tarkonka ba"
Dariya kawai gulmanu yayi yace"tabbas yake
wannan sarauniya zaki fahimta nan bada
dadewa ba, " yana gama fadin hakan, sai
aljani lumzaru yazo gabansa yace" ya
shugabana hakika ina son na fada maku
wasu abubuwa masu muhimmanci a game
da wannan tafiyar tamu"
Toh a dai dai wannan lokacine yarima hikal
ya idar da ibadarsa salla, sannan ya kariso
wajen da su gulmanu suke,
Aljani lumzaru yai gyaran murya yace"
Ya shugabana lallai kayisani cewa kafin
mukai ga
.
.
Tobe continue
Hakkin mallaka (c) Shuraih Usman
Marubuci:- Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina Uku (3)
Littafin Shuraih Usman
Part 7
.
"Ya shugabana lallai kayisani cewa kafin mu
isa jejin da aljani sham'una ya ke sai mun bi
ta cikin wasu dazuzzuka Hudu, kowani daji
yana dauke da muggun masifa wacce da
zarar mun ketare wannan masifa shine zamu
isa jejin da aljani da sham'una yake,
Dajin farko da zamu fara isa itace GABATUL
HAYYAT,
.
Babu komai a cikin wannan daji face wata
Tafkekiyar macijiya mai kawuna biyar,
Ita wacannan maciya tafi fiye da shekaru
Dubu arba'in a cikin wannan jeji
,
Maciyar nan tana da kawuna biyar a jikinta
kowani kai da irin masifar da yake fesowa,
Abu mai mahimmanci da ya kamata kusani
game da wannan maciyar shine, KAIFI DA
TSINI basa tasiri a jikinta , ruhin wannan
maciya, yana cikin daya daga cikin
kawunanta, inda ruhin kuwa yake shine
tsakiyar kanta ,
Nayi bincike ainun domin na gano daga cikin
kawunanta biyar din nan wanne ne ruhin
yake , amma na kasa,
.
A tarihin wannan daji na Gabatul hayyat
babu wani mahaluki daya taba shiga cikinta
koya ketare ta cikinta batare da ya zama
gawa ba, face aljani sham'una shima kuwa
sabida hatsabiban cinsa ne
.
Daji na gaba kuwa ana kiransa da JEJIN
FATALWI, shi wannan jeji babu komai a
cikinsa sai wasu irin fatalwi, masu maka
makan kawuna , jikinsu kuwa siriri, yayin da
kafafuwansu ke barazanar karyewa a ko wani
lokaci,
Su wannan fatalwi babu wanda yasan iya
zamanin da suka deba a cikin wannan jeji ,
.
Muddin kuka shiga cikin wannan jeji na
fatalwi, toh baza ku taba tsira da rayukanku
ba, yawan adadin wayannan fatalwi yafi
metan, kuma wayannan fatalwi ba a ganinsu
sakamakon wani mayanin tsafi da suke
lullube jikinsu da shi,
Amma idan babu wannan mayani, toh zaku
gansu ",
,
Aljani lumzaru ya sauke numfashi
"Toh ta yaya kenan zamu bi cikin wannan jeji
batare da dayanmu ya hallaka ba" sarauniya
lasmin ce ta jefa wa lumzaru wannan
tambayar.
Lumzaru ya gyara murya sannan yace" ya
shugabata su wayannan fatalwi, tsafi da sihiri
baya tasiri akansu, sannan kuma da zarar
kun shiga wannan jeji to duk wani sihirinku
bazai taba aiki ba har sai kun fice da ga cikin
dajin.
.
Dole duk yadda za'ayi ku sami ku kashe daya
daga cikinsu, izan kun kashe shi toh sai ku
cire wannan mayani da ke lullube a jikinsa,
daya daga cikinku sai ya saka ajikinsa, toh
anan take zai bace ,
Toh ta haka ne kawai zaku iya cin galaba
akansu ,
,
Daji na gaba kuwa ana kiransa da BAHRAIN ,
Dajin bahrain , dajine da aka tsaface shi , fiye
da shekaru da suka shude sunan wannan
daji zuhru ,
A lokacin da aljani sham'una ya tare a cikin
wannan nahiya sai ya sana'anta wani babbar
mutum mutumi ya kafe acikin wannan daji ,
Koda kafe wannan mutum mutumi, sai
wannan daji gabadayanta ta koma izuwa
babbar kogi, ruwan wannan kogin kuwa,
rabinsa, launin fatsi fatsi ne rabin kuwa
launin baki gareshi,
.
A kwai miyagun sihirtattun namun jeji bila
adadin a cikin wannan babbar koramar ,
Abu mai muhimmanci daya kamata kusani
game da wannan daji kuwa shine,
,
Da zarar kun tunkaro dajin zaku gansa a
siffar daji , da kun shigeshi kuwa da taku
arba'in zai rikide izuwa babban kogi, nan take
zaku lume a cikin wannan ruwa,
,
Muddin kuka yi nasarar hallaka halittun
dakae cikin wannan korama , toh wani siririn
hanya zai hudo ta cikin kasa, sai kubi wannan
siririn ramin ,
,
Ayayin da kuka isa karken wannan rami zaku
ga wata kofa, a hannun damarku, sai ku bude
ku shiga, anan ne zaku tarar da wannan
mutum mutumi a kafe cikin kasa, sai kuzo
gaban wannan mutum mutumi din zaku ga
wata akwati a gefen kafufuwansa,
,
Da zarar kun bude wannan akwatin zaku ga
wani Kubba, na bakin karfe sai ku dauki
wannan bakin kubban ,
Ku zurashi a bakin wannan mutum mutumi,
toh nan take zaku ji wata kara,
Mai amo, da zarar wannan kara ta dauke
wannan mutum mutumi zai tarwatse,
.
To a sannan ne wannan jeji zai koma yadda
yake , duk wani sihiri da tsafi zai karye,
.
Daji na gaba kuwa ba jeji bane, yumbun
hamada ne , shi wannan yumbun yana da da
zafi mai matukar radadi, don zai iya narkar
da bakin karfe,
.
A kasar wannan yumbun kuwa, ramuka ne
wayanda yawansu yafi milyan daya,
Kowani rami daya tsayinsa, yafi kamu
arba'in, fadinsa kuwa zai iya cin mutane
dubu ajere, bisa layi,
.
Yumbun kuwa ya rurrufe wayannan ramuka
ta yadda baza ka taba zata akwai wani abu
wai shi rami a wajen ba,"
.
Koda aljani lumzaru ya kawo nan a zancensa
sai ya dubi sarki gulmanu, sa'annan yace" ya
shugabana a yayin da kuka isa bakin wannan
yumbun hamada toh sai ku tsaya, a bakin
wannan yumbu har sai rana ta kusa faduwa,
to a sannan ne zaku ga wata duhuwa ta
mamaye gaba daya ilahirin wannan yumbun
na hamada,
.
Da zarar wannan duhuwa ta baiyana to
dukkan wani zafi da ke cikin wannan yumbu
zai kau,
Sannan wayannan ramukan zasu toshe
,
A sannan ne ku kuma zaku shiga cikin
wannan yumbu,
Ya zama wajibi a gareku ku hanzarta ku
ketare wannan yumbu, kafin cikar sa'a daya,"
,
"Me zai faru izan har muka debi fiye da sa'a
daya acikin wannan yumbu" gulmanu ne ya
katse shi da fadin hakan
,
Aljani lumxaru yace"wannan duhuwa itace ta
kare ku daga masifar wannan yumbu, toh da
zarar sa'a daya ta cika, wannan duhuwa zata
yaye, muddin kuwa kuka bari wannan
duhuwa ta yaye kuna cikin wannan yumbun
toh take zaku narke ku koma tamkar ruwa a
sabida zafin wannan yumbun na hamada,
,
Muddin kuka fice daga cikin wannan daji da
rayukanku,
Toh a sannan ne zaku isa sansanin aljani
Sham'una,
.
,
Am tired men
.
Tobe continue
Hakkin mallaka (c) Shuraih Usman
Marubuci:- Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
TAKOBIN JINI
.
Book 3
.
Littafin Shuraih Usman
Part 8
.
Aljani lumxaru ya cigaba da cewa shikuwa sansanin
aljani sham'una ko ince dajin dayake da zama ,
Maganar gaskiya itace bansan komai game da
wannan daji ba , sai kun isa tukun zakuga irin masifar
dake cikin wannan jeji,
.
Koda gama wannan zance nashi sai sarki gulmanu ya
duvesu yace , gobe da safe zamu isa wancan daji na
farko wato dajin gabatul hayyat, daga nan ne izan
muka tsira da rayuwarmu sai mu cimma daji na
gaba,
,
Amma kafin wannan ina so na gayamaka," ya maida
kallonsa ga yarima hilal kada ka kara yunkurin,
kwadaita mana Addininka kayi Addininka muyi
Addininmu,
Bukata ce ta hada mu da kowa isar da bukatarsa, shi
kenan munyi hannun riga
.
Yarima hilal yayi murmushi sannan yace" naji na
amince bazan kara kiranku izuwa Addinina ba Amma
ina da sharadi guda daya da zan gin daya maku"
.
Sarauniya lasmin tayi sauri ta ce" shin kai kuwa hilal
wani sharadi kenan da harkake cewa zaka gin daya
mana"
"Wannan sharadi kuwa itace duk wani masifan da
daya daga cikinku ya tsinci kansa, zan barsa ya
dogara da ababen bautarsa, da kuma dabararsa a
yayin da ababen bautar tasa da dabarartasa suka ki
aiki, toh a sannan ne zannuna maku Girman
ubangijina, "
. Yarima hilal ya fada yana mai murmushi akaro na
biyu
.
Sarki Gulmanu ya takarkare da wata mahaukaciyar
dariya wadda ta hassada karamar girgizan kasa,
Saida yayi mai isarsa sannan ya tsuke baki yai shiru
ya dubi hilal yace " yo ai wannan ba wani abu bane ,
dukkanmu sadaukaine , kuma matsafa kasani rintsi
ko tsanani wuya ko wahala baza su taba sanyani na
nemi taimakonka ba"
Yana gama fadin hakan ya tashi ya nufi tantinsa ,
***** ********* *******
Washe gari da safe, kowa ya fito ya hallara, toh a
sannan ne aljani lumzaru ya fara magana kamar
haka" kusani cewa wannan tafiya iya kune zakuyi shi
ni zan jira ku anan wajen duk lokacin da kuka samu
nasarar karbo gimbiya suraila daga hannun aljani
lumzaru toh a sannan ne izan kun tsira da rukanku
zaku dawo wannan waje ku iskeni' na rantse da
tauraruwa zahlu bazan taba muskutawa daga wannan
jeji ba harsai naga dawowarku,"
.
Toh dama tun da suka shigo cikin wannan jeji suka
samu itatuwa suka sassaka karamar kwalekwale
wanda zasu tsallaka wannan Ruwa da shi,
Yanzu kuwa da su ka gama jin wannan zance daga
bakin aljani lumzaru sai suka , nufi wajenda
kwalekwalemsu take a gabar wannan korama, suna
isowa suka shiga cikin wannan kwalekwale sannan
suka tuka , basu sha wata wahalaba suka tsallako
izuwa dayan barin wannan jeji, toh a sannan ne suka
kutsa kai ciki batare da wata shakka ba
,
Ayya rashin sani yafi dare duhu lallai da su sarki
gulmanu sun masifar da zasu tarar a wannan daji na
gabatul hayyat toh da sun hakura da wannan bukata
tasu sun koma da baya,
.
Dajine mayalwacin dogayen bishiyu, wayanda
ganyayyakinsu . Ya lullube sararin samaniya,
sakamakon hakannema dajin yazama tamkar wani
stadium din buga wasa,
Ga iska mai dadi dake ratsa sassan jikin biladama,
Suna cikin tafiyane sai sarauniya lasmin taji kamar
kukan wani karamin dabba ta cikin wani sarkakiya,
nan da nan batare da fargaba ba ta nufi wannan
sarkakiyar ta na isowa bakin sarkakiyar sai tasa kai
ciki, toh a sannan ne, taji motsin wucewar wani abu
nan da nan tabi wannan abu da kallo koda ta lura da
kyau, sai taga ba wani abu bane face irin saiwan
bishiyarnan masu lilo tamkar igiya,
Nan take hankalinta ya kwanta,
.
Sarki gulmanu ya dubi hilal yace " nifa na kagu nayi
arba da wannan maciya don naimata kisan wulakanci
sannan kaima na nuna maka karfin sihirin tsafina,"
Hilal yace mai "kada kadamu menene na hanzari,
komai da kake gani lokacine zai nuna, inma cika baki
kake toh duk lokaci zai nuna,"
Suna kan wannan zance nasu ne sai gabadaya
wannan inuwa dake cikin wannan jeji tafara yayewa,
take gaba daya bishiyoyin wannan jeji suka fara
bushewa, ganyayyakin jikinsu kuwa suka zube kasa,
nan take hilal ya bude baki yana ganin ikon Allah, take
gaba daya bishiyoyin wannan daji suka bushe tamkar
basu taba rayuwa ba,
,
Wani gurnani ya biyo baya wannan gurnani kuwa
yana da amo don harsaida su gulmanu suka toshe
kunnuwansu.
.
Nan take sarauniya lasmin takariso wajenda su
gulmanu da hilal suke cikin al'ajabin wannan gurnani
da basu san daga inda yake fitowa ba
.
Wannan gurnani ya sake matsowa toh anan ne sukai
arba da abunda ya kusan haukata tunaninsu,
.
Ba komai bane face wata narkekiyan macijiya mai
kawuna biyar , girman wannan macijiyar kuwa zai kai
na babban tsauni, tsayinta kuwa yafi kamu dubu,
kowane kai dake jikin wannan maciyar yana feso
masifane, kai nafarko wani bakin ruwa yake fesowa a
duk inda wannan ruwan ya zuba kuwa toh nan take
wajen zaiyi rami, mai dan karen zurfi,
Kai na biyu kuwa wani mummunan dafi yake fesowa
shi wannan dafin iz*n ya zuba ajiki bishiya toh nan
take bishiya take , yankwanewa ta kone kurmus
.
Kai na uku kuwa wuta yake fesowa duk inda wannan
wuta ta lasa take abun yake konewa kurmus
.
Kai na hudu kuwa wani miyau tako dalalar wa a yayin
da wannan miyaun ya zuba akasa take zakaga kasa
tana soyewa tamkar an saka kullun kosai a cikin
tafashashshen mangyada,
,
Kai na biyar kuwa baya feso koma saidai kuma
wannan gurnanin to shine yake yinta,
.
Koda gulmanu da lasmin sukai arba da wannan
maciya sai suka dake su kaki nuna alamun tsorata a
tattare dasu shiko hilal Addo'I kawai yake karantowa
a cikin zuciyarsa,
.
Kai na biyar dake jikin wannan maciyar mai gurnani
,yai shiru da gurnanin dayake sannan yafara magana
da wata sauti maradadin sauraro kamar haka
"Yaku wayannan biladama masu karar kwana, shin
baku samu labarin wannan jejin bane da har kukai
gangancin shigowa ciki, toh lallai ina sanar daku na
rantse da wannan kawuna nawa dayanku bazai fita
daga cikin wannan jeji arayeba"
.
Gulmanu yace" kisani yake wannan bakar macijiya ,
lallai munji labarinki, asabida hakannema muka
shigo wannan jeji don muga bayanki lallai yau bazaki
taba tsira ba, "
.
"Kai gafalalle yi mani shiru kafin na gididdibaka da
ranka, lallai kayi sani cewa jarumai masu takama da
jarumta, manyan bokaye masu takama da sihirin
tsafi,manyan dakarun aljanu masu takama da
sadaukantaka sun gagara hallakani daga karshe nine
na hallakasu, toh bare kai kuma wani karamin
cinnaka wanda nake mai ganin abin kalacina,"
wannan macijiya ta fadi
.
Gulmanu yasake dubanta cikin fushi yace" ai dama
karamin cinnaka shike sa giwa tika rawa, sannan
kuma karaminm sani kukumine"
.
Duk wannan abin dake wakana hilal da sarauniya
lasmin na gefe suna kallo , hannun sarauniya lasmin
yana bisa kufen takobinta,
.
Take wannan macijiyar tayi kara sannan takaiwa
gulmanu daya daga cikin kawunanta take wannan kai
ya feso wani irin bakin ruwa, cikin zafin nama
gulmanu ya goce , sauran kawunan kuwa suka
dumfari lasmin ai nan take ta fidda takobinta , ta
tunkari wannan kawuna guda hudu yayinda
wayannan kawuna sukaita fesomata masifa tana
gocewa, abinda yadaure mata kai game da macijiyar
shine batajin sara bare suka, wannan maciyar ta
shammaci, lasmin ta doketa da jelarta a kirji nan take
sarauniya lasmin tai baya yadda kasan anjanyeta ne
da kuge,
Koda gullmanu yaga haka sai ya kara zage damtse
yana saran wannan macijiyar tako ina ajikinta amma
yadda kasan yana sarar dutse, toh a sannan ne shima
ta sure shi da jelarta ta fyda shi da kasa , gulmanu
yaji zafin wannan duka sosai don ji yake ma tamkar,
kashin bayansa ne ya karye, cikin zafin nama, ya daka
tsalle ya sari wannan mciyar a wuya amma saiyaga
nanma baiyi tasiri ba ,
Kawai sai ya yar da takobinsa sannan ya dunkule
hannu ya naushi wannan , macijiya , amma saiyaji
tamkar hannunsa zai fita, nan yata gwada karfin
sihirinsa da karfin tsafinsa akan wannan macijiya
amnma yaki tasiri, itako sarauniya lasmin wacce take
akwance a sume yayin data fada bayan wani
karyayyen bishiya tsininsa ya soke ta a hannu wanda
dalilin zafin data jine har ta some,
.
Nan da nan wannan macijiya ta hada wa gulmanu ji
da majina, sannan ta nanna deshi da kanta, ta zuko
dayan kanta da nufin ta gutsire masa kai ta hade
ganganjikin,
Kwatsam ba zato ba tsammani sai yarima hilal yayi
kabbara sannan yadaga takobinsa yasari wannan
macijiya take wannan macijiyar tai kara sakamakon
wani radadi daya ratsata wanda a dalilin hakannema
ta jefar da gulmanu akas,
.
Nan da nan fa hilal ya cigaba da saran wannan
maciya baji ba gani , ita kuma tana kawomai hari da
kawunanta cikin ikon Allah yana gwocewa,
.
Azuciyar wannan macijiyar kuwa cewa take lallai yau
na hadu da gamona toh waishinma wane irin
biladamane tamkar shaidani,
.
Hilal kuwa babu abin dake damunsa illa rashin
samun lagon wannan maciya nan dananfa wannan
maciya tafara gajiyar dashi gajiya tafara kamashi , ya
tuna inhar ya debi tsawon lokaci yana wannan
gwagwarmayar toh lallai zai iya gajiya , kuma idan ya
gaji toh wannan macijiya zata samu nasara akansa
kenan
.
Cikin zafin nama yafara karanto ayoyin alkur'ani a fili,
bai dade dafara karan towa ba sai ya tuna da bayanin
Aljani lumzaru dayake fadamusu ruhin wannan
macjiya a saman kanta yake ,
.
Ai yana tunawa sai wani gagarumin karfi ya zo
masa,nan ya daka tsalle ya soke tsakiyar kan wannan
macijiyar ta farko nan take yaji tamkar ya soki dutse ,
ya sake daka tsalle ya soki tsakiyar kan wannan
majiyar na biyu nanma tamkar ya soki dutse cikin
zafin nama ya dunga soke tsakiyar kawunan macijiyar
har yaci sa'a ya soke kanta na biyar, take wannan
macijiya tai kara wanda ya haddasa babbar girigizar
kasa nan take ta fadi rikica yadda kasan wani babban
jirgine ya fado.
.
.
KARSHEN TAKOBIN JINI LITTAFI NA UKU
Shekarar:- rubutawa-: 2017
Marubuci:- Shuraih Usman
SHIN YARIMA HILAL, SARKI GULMANU SARAUNIYA
LASMIN ,ZASU SAMU NASARAR KETARE SAURAN
DAZUKAN SU ISA SANSANI ALJANI SHAM'UNA
.
WANI IRIN GWAGWAR MAYA ZASU SHA
.
YA LABARIN ALJANI LUMZARU
.
SHIN WANE NE ZAI MALLAKI TAKOBIN JINI
Don jin wannan amsoshi mu hadu a littafi na hudu
wanda shine karshe
Zai dauki lokaci kafin ya fito.
Hakkin mallaka (c) Shuraih Usman
Marubuci:- Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment