Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zamo wajibi agareka sai ka sanya wata
zoben wuta a yatsan hannunka na hagu .ita zoben
wuta jarumi kuma boka muraisu ne ya sana'an tata
kasani batare da zoben wuta ba Bazaka mallaki
takobin jini ba har abada Zoben wuta tana can dajin
Hajrul ma'ut a saman wata bishiya kasani babu wani
mahaluki daya isa ya shiga dajin hajrul maut sannan
yafito araye domin wannan dajin masana sunyi
ittifaqin cewa gaba daya dajin dunya babu wata dajin
da ta kai ta hatsari . Sannan ko kayi nasarar shiga
dajin hajrul ma'ut kasani bazaka taba ganin wannan
zoben ba ballan tana ma ka daukota . Ita wannan
zoben muraisu ya sana'anta tane da jininsa kasani
izan ba wani wanda yakasance jininsa bane Toh lallai
babu wanda ya isa ya ma iya ganin wannan zoben
barema har ya daukota . Sannan ire iren muraisu
wato danginsa sun dade da shafewa daga doron kasa
A cikinsu mutun dayace tayi saura kuma ba kowa ba
ce illa GIMBIYA SURAILA matar sarki ashbir . Kasani
nayi bincike a cikin halwar tsafina na gano tana nan
araye amma saide tana tare da wani hatsabibin aljani
mai suna sham'una wanda shima burinsa knan ya
mallaki wannan takobi na muraisu . . Ku sance tare
dani
TAKObin jini . Book 2 . Marubucin Littafin Shuraih
usman Part 8 . Kasani nayi bincike a cikin halwar
tsafina na gano tana nan araye amma saide tana tare
da wani hatsabibin aljani mai suna sham'una wanda
shima burinsa knan ya mallaki wannan takobi na
muraisu . Sannan muddin bamu gaggauta karbar
suraila a hannunsa ba to tabbas zai iya ratsawa har
cikin dajin hajrul ma'ut ya dauko zoben wuta sannan
ya nufi kogin shajini ya daoko takobin jini . Izan har
Aljani sham'una ya mallaki takobin jini to tabbas
duniya zata kasance a karkashinsa sannan burinka na
zama sarkin sarakai na duniya bazai tabbata ba. ,nan
take gulmanu ya harzuka matuka gaya sannan yadubi
boka balbalin bala'I yace mai "Toh yanzu me ne ne
mafita Koda jin haka sai boka yai wata guntuwar
murmushi sannan yace ma gulmanu . Kasani duk
fadin duniyar nan babu wani mahaluki daya isa ya
hallaka sham'una har ya karbo gimbiya suraila a
hannunsa . Wani sadauki ma'abocin wata bakuwar
Addini wanda yanxu haka wannan bakuwar Addinin
ta fara bazuwa a sassan duniya baki daya . Shi
wannan sadauki ba kowa bane face Yarima hilal da ga
sarki Abul abbas mai mulkin birnin nurul ansar .
Kasani yarima hilal yafada soyayya da gimbiya suraila
ta dalilin hakan ne zai fita nemarta Awannan fitar
dayayine zaku hadu dashi sannan ku labar tamasa
inda gimbiya suraila take . Yayin daya ceto gimbiya
daga hannun Aljani sham'una sai ku san yadda zakuyi
ku shammace shi ku kashe shi sannan ku tafi da
gimbiya zuwa dajin hajrul mau't inda zata dauko
maku zoben wuta . Kasani wannan aiki bazai taba yi
wuwa ba face kun hada karfi da karfe kai da saruniya
lasmin mai mulkar birnin dimashka . Sannan kafin ku
isa dajin hajrul mau't akwai wasu masifu guda uku
wa yanda da zarar kun sallakesu araye toh tabbas
zaku isa wannan dajin . Rufe bakin boka bal balin
bala'I keda wuya Gulmanu yabama sarkin yakinsa
umarni daya debi dakaru dubu sannan yasa
magatakarda ya rubuta wasika . Gama rubuta wasikar
keda wuya sarki gulmanu ya buga hatiminsa sannan
ya mika ma sarkin yakinsa mai suna kumar Yace mai
"Ku tafi izuwa birnin dimashka sannan ku mikawa
sarauniya lasmin wasikar " . . Sarkin yaki kumar ya
dukad da kansa kasa sannan yace angama ya mai
duniya" . Koda kumar ya mike sai ya haye saman
dokinsa ya falfala da gudu sannan wasu dakaru suka
bishi abaya " Wannnan shine abin daya faru a fadan
sarki gulmanu ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤
Sarauniya lasmin ce kan wata bakar doki yayin da
dakru wajen dari ke biye da ita Nan suka ja tunga
daidae wajen wani katon dutse sannan sarauniya
lasmin ta sauko daga saman dokin ta nufi wannan
dutsen tana zuwa bakin dutsen sai ta furta wasu
dalasimai na tsafi nan take ta bace bat . Bata bayyan
ako'inaba sai acikin kogon da boka kamsusul lajani
yake . Nan kuwa tai arba dashi zaune akan wata
mashimfidi na fatar giwa. . Ta budi baki zatai magana
keanan sai boka kamsusul lajani yai mata ishara da
tai shiru . Sannan yace mata barka da zuwa yake
sarauniyar duniya baki dayanta . Lallai zan sanar dake
labarin Takobin jini . Yafara bata labrin muraisu da
yadda akai ya sana'anta takobin da kuma inda ya
ajjeta sannan yakra da cewa shi wannan takobi bazai
daukuba sai da zoben wuta , Nan ya labarta mata
wajen da zoben wuta yake ajiye sannan hade da fada
mata sirrin wannan zoben babu wanda ya isa ya
dauko shi face wani tsatso na muraisu sannan kuma
wannan jini nasa yanxu dayace kacal ta rage a duniya
. Nan ya labarta mata labarin gimbiya suraila Koda
sarauniya lasmin ta saurari wannan labari sai ta nisa
sannan tace toh yanxu me nene mafita . Babu wani
mahaluki. Daya zai iya hallaka Aljani sham'una
sannan ya ceto suraila face yarima hilal . Sannan
baza ki damar ganin yarima hilal ba face kin hada kai
da sarki gulmanu , Wannan bukata taki baza ta taba
samuwa ba face kun hada karfi da karfe , Sannan
boka kamsusul lajani Yakara dacewa yanxu haka
gulmanu ya turo da sarkin yakinsa tare da wasika a
gareki yana fadin hakan sai ya shafi wata dutse
Shafar wannan dutsen keda wuya sai ga sarkin yaki
kumru tare da dakarunsa sun bayyana ajikin wannan
dutsen sai tsala gudu suke cikin jeji . . ¤¤ END OF
BOOK 2 ¤ SHIN SARAUNIYA LASMIN ZATA YARDA TA
HADA KAI DA GULMANU . SHIN MEKE KUNSHE CIKIN
WASIKAR DA GULMANU YA AIKA . YAYA LABARIN
ALJANI SHAM'UNA TARE DA SURAILA . WACECE
WANNAN DA YARIMA HILAL YaYI MAFARKINTA .
SHIN A CIKINSU WAYE ZAI MALLAKI TAKOBIN JINI . .
DOMIN JIN WAYANNAN AMSOSHIN MU hADU A
TAKOBIN JINI lITTAFI NA UKU . . MARUBUCI:- Shuraih Usman . . SHEKARAR RUBUTAWA:- 2017

TAKOBIN JINI 3
COMPLET
TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina uku (3)
Littafin Shuraih Usman
Part 1
.
.
Sarkin yaki Kumru suka iso birnin dimashka
,masu tsaron kofar garin na hangosu suka
bude musu kofa
.
Abin daya ba ma su sarkin yaki kumru
mamaki kenan har sun fara shirin yaki
,
Koda suka isa cikin birnin dimashka sai wani
bafaje yazo garesu
Sannan yace musu"
Sannunku da zuwa yaku jama'ar birini
ashdamir kusani sarauniya lasmin ce ta
aikoni izuwa shugabanku
"
Kumru najin haka
Sai ya budi baki yace" yakai wannan dan aike
kasani mu ba da yaki muka nufo birnin ku ba
sako ne zamu isar zuwa ga sarauniyarku.
Nan wannan dan aike yajasu yakaisu
masauki
.
Babban gidane ainun sannan gidan ya
kawatu
Dagani kasan irin wannan gidajen dama
anyisune musamman dan karban baki.
Yayin da su kumru suka shiga gidan sai suka
bude bako galala suna ta kalle kalle kamar
wasu yan kauye,
Gidan ya tsaru matuka gaya domin gidan
kusurwa kusurwa ne sannan ga wani
faffadan kilishi wanda yake barazanar hadiye
kafafuwansu
.
Bayan kowa ya samu waje ya huta sai aka
shigo masu da abinci
Bakomai bane illa Gurasa da farfesun dawisu
sai kuma wasu tambulan kayan shaye shaye
wanda wasu ke kunshe da ruwa wasu kam
barasa da dai sauransu.
.
Nan sukaci suka sha sannan sukayi hani'an
Wannan bafajen ya iso gaban kumru sannan
yace dashi ku kwanta ku huta zuwa gobe
sarauniya zata yi magana da kai
,
Sannan ya fice
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤
.
Sadauki yarima hilal tunda sassafe yazo fada
sannan ya haye kan karagar mahaifinsa ya
harde sai wani annashwa yake
.
Yayin da kowa idan yazo fadar sai ya kwashi
gaisuwa
Sannan ya nemi waje ya zauna
.
Tunda ga nisa Abul abbas ya hangi dansa
akan karagar mulkinsa sai shima wata farin
ciki ta cikashi wai yau ga dansa kan karagar
mulkinsa
,
Koda ya Iso wajen sai kowa ya tashi ya
kwashi gaisuwa
,
Yarima hilal ya mike tsaye sannan ya durkusa
har kasa ya gayar da abbansa
, sarki abul abbas ya dafa kafadar hilal
sannan ya tasheshi zaune
,
Yai mai murmushi yace "hakika yau naji dadi
dana ganka kan karagar mulkina ina farin ciki
da haka
,sannan zan sanar dakai labarin wannan
yarinya dakai arba da ita acikin mafarkinka
,
Koda jin haka sai fuskar hilal ta fadada da
wata murmushi alamun farin ciki suka
bayyana akan fuskarsa yace yakai abbana
gaggauta sanar dani labarin wannan
sarauniya ta kyawawa
.
"Yaku yan majalisata kuma wannan al'amari
ya shafeku bama kuba gaba dayan mutanin
duniyar nan wannan al'amari ya shafesu
.sarki abul abbas yafada cikin daqa murya
,
Yayin da yan majalisan suka ji haka
Sai waziri yace "ya mai girma shin tayaya
wannan al'amari yashafemu
"
Koda jin haka sai sarki abul abbas
Yadubi yarima hilal sannan yace
"
Jiya nayi istihara kan matar da dana zai aura
Allah sWt ya nuna min acikin baccina
Ita wannan kyakkyawar yarinya diyace ga
sarki MULKEsH sarkin birnin Askandariya
yayin da wannan yarinya takai munzalin aure
sai mahaifinta wato mulkesh ya aurar da ita
ga wani sarki mai suna ashbir yana mulkar
garin ashdamir
Shi wannan sarki adaline
Amma yanzu wani hatsabibin boka hade da
wani jarumi sun hallaka shi har suka nemi
hallaka wannan yarinya wato matar sarki
ashbir sai Allah ya tseratar da ita
,
Yanxu haka tana hannun wani shu'umin
al'jani wanda shikuma wannan aljani dane ga
Dubyalu sarauniyar aljanun dana kama na
daureta cikin kurkukun karkashin kasa
,
,
Zan cigaba
TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina uku(3)
Littafin Shuraih Usman
Part 2
.
.
.
Yayin da mahaifinta labari yazo masa cewa
wani azzalumi ya hallaka sarki ashbir tare da
yarsa
Sai wani bakin ciki ya turnukeshi
Nan take ya hadiyi zuciya ya mutu
.
Ita wannan yarinya sunanta SURAILA
Yayin da ta tsira daga masifar azzaluminnan
sai ta nufi wannan kasa tawa bisa rashin sa'a
tayi arba da wannan shu'umin aljani
.
Wannan aljani sunansa SHAM'UNA burinsa
kuwa itace ya mulki duniya baki dayanta ,
Yayin dazai mallaki wata takobi ta sihiri
wanda muddin bayana tare da suraila ba to
tabbas bazai mallaki wannan takobi ba
shiyasa ya dauketa
.
Yanxu haka wasu manyan sarakuna na
wancan nahiyar sunyi shiri zasu fita neman
shi wannan aljani sham'una su karbe suraila
a hannunsa daga bisani su tasamma inda
wannan takobi yake
.
Su wayannan sarakuna sunyi bincike sun
gano baza su taba iya yakar aljani sham'una
ba.
Sun gano duk duniya babu mai iya yakar shi
wannan aljani face dana yarima hilal
,
Koda jin haka sai yarima hilal yadago
dakansa wanda tun da sarki abul abbas
yafara bada labarin kansa na sunkuye
.
Abul abbas yaci gaba "
Yanxu haka suna shirin zuwa ga dana hilal
domin su. Yaudareshi ya hallaka aljani
sham'una daga bisani shima su hallakashi
.
Amma abin da basu sani ba shine sune zasu
hallaka $
.$
Yaku jama'ar birnin nurul ansar kusani
wannan wata damace da zamu yayata
Addinin musulunci a duniya baki dayanta $
,$$
Ayayin da zamu nuna ma kafirai cewa
Addinin musulunci shine addinin gaskiya
shine tafarkin Annabi ibrahim AS $$
,$
Sannan yakara da cewa yakai dana ka je ka yi
shiri gobe domin wannan aiki ba wani ne zai
yiba face kai kadanka $
Kasani cewa na yarda da jarumtarka $
$.
Koda gama fadin haka sai hilal wanda kansa
ke a sunkuye ya dago kai sannan ya dubi
dandazon jama'ar dake fadan yai kabbara da
iya karfin muryarsa aiko nan take jama'a
suka amsa ALLAHU AKBAR
.
Washe gari yarima hilal yai gagarumar shiga
sannan yafito fada ya sanya wata bakar riga
ce falmara sannan yasanya wata sulken karfe
wadda take dabai baye da wasu irin kaNa
nan duwatsu
Masu daukar ido
Sannan yasaka wata bakar wando agefen
maransa kuwa ya rataraya takobinsa $
.
Kai duk wanda yagansa a irin wannan shiga
lallai zaice wannan wane mutum
.
Nan sarki yafito fada hilal ya je ya kwashi
gaisuwa sannan yai sallama da mahaifinsa
sarki abul abbas
Ya haukan dokinsa sannan ya fita daga cikin
birnin Nurul ansar yayin da jama'an gari keta
binsa abaya $$
.$
Wannan shine abun daya wakana a birnin
nurul ansar yayin da yarima hilal ya fita
nemar wannan kyakkyawa wato gimbiya
suraila
¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤
.
Kumru kuwa bayan sun huta sai yanemi da
amai iso zuwa fada aiko wannan dan sakon
ya rakashi harfada
.
Sarauniya lasmin na zaune bisa karagar
mulki ana tafiyar da harkokin yadda suka
dace
.
Kawai sai aka hango sarkin yaki kumru tare
da wannan dan aike koda sarkin yaki kumru
ya gabata a fadan sai ya kwashi gaisuwa ga
sarauniya sannan ya ciro wata fata wadda
duk tabi ta jeme saboda danshi dayake
rabarta
.
Yamika wannan jemammiyar fatar ga maga
takarda shikuma ya mika wa sarauniya
Amma sai tai mai umarni daya karanta abin
da abin wannan fatar ta kunsa na take ya
bude wannan fatar$
Yasoma karantawa kamar haka
Sako daga sarki Gulmanu mai mulkin birnin
ashdamir zuwa ga sarauniyar kyawawa ta
duk duniya
Kisani cewa yanxu ba maganar aure ce ta sa
na aiko da wannan wasikar ba
,dalilin wannan wasika itace ina son muhada
karfi da karfe don ganin mun mallaki wannan
takobin duk dana san kina da labarin takobin
$
.$
Kisani amintaccen bokana ya tabbatarmin da
cewa bazan taba mallakar wannan takobi ba
face mun nahada hannu dake
$kamar yadda kema amin taccen bokanki ya
tabbatar miki bazaki taba mallakar wannan
takobi ba face mun hada karfi da karfe
.
Sannan kuma in kin amince sai ki rubuta
wata wasikar sannan kibawa wannan dan
aiken nawa ya kawomin ni kuma sai inyi shiri
inzo in sameki a birnin ki $
Sannan kuma ki sako min mutanena da kika
kulle a gidan kurkuku $
Koda maga takarda ya rufe bakinsa sai waziri
mai suna hammadu yace ya
Ranki shidade anya zamu iya yadda da sarki
gulmanu kuwa kinsan shi dan adam baya da
tabbas kada kizo ki amincemai
Daga baya kuma bayan bukata ta biya ya
nemi ya yaudareki$
.
Koda sarauniya kasmin taji haka sai ta
kyalkale da dariya sannan tace kada damu
yakai hammadu babu abin da zai faru dani
awannan tafiya da zamuyi kuma aishi baisan
wacece sarauniya lasmin mai mulkin
dimaskha bane shiyasa har yake kokarin
yaudarata amma bai san kansa yake
yaudaraba
Takar juyawa izuwa gefen sarkin yakinta
sannan tacemai yakai musabbih inason gobe
a hadamin dakuru mutum doma wayanda
kayarda da jarumtarsu lallai gobe zan isa
zuwa birnin asdamir sannan inaso dakarun
nan afiddasu daga kurkuku a hadasu da
kumru gobe zamu wuce
¤¤¤¤¤$
Zanci gaba
TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina uku (3)
Littafin Shuraih Usman
Part 3
.
.
Washe gari sarauniya lasmin ita da sarkin
yaki kumru suka dauki hanyar birnin
Ashdamir
.
Sunyi tafiya mai nisa sosai sannan
$arauniya tabada umarnin a yada zango
bako ina bane suka yada zango illa acikin
wani daji mai sarkakiya wanda bakajin motsi
ko kukan tsuntsaye
.
Nan take suka kama aikin kafa tantuna
Bayan sun gama kafa tantunan
Sai suka fiddo da guzurinsu domin su cika
cikinsu dashi
.
Ayayin hakanne sai sukaga wata kura ta
turnike gabadaya ilahirin gabashin dajin ba
zato ba tsammani sai wasu jibgagan mutane
suka fara bayyana wayanda adadinsu sunkai
dubu
.
Gabadayansu suna rike da makamai kala kala
.
Su wayannan jibgajibgan mutane. Sun
kasance narka narka wanda girmansu ya
ninka na dakarun sarauniya lasmin sau uku
.$
Wayannan gabza gabzan masu kama da
samudawan farko
Suka fara darewa suna bada wata siririyar
hanya a tsakaninsu
Gama darewarsu keda wuya sai ga wani
narkeken kato ya bayyana yana mai cusguna
fuska
Hannunsa na dama yana rike da wata
sharbebiyar gatari wadda idan karti goma
zasu taru baza su iya rabata da kasa ba a
yayin da dayan hannunasa yana mai rike da
kugunsa
.
Wannan kato dai da halama shine shugaban
wayannan samudawan$
.$
Nan take dakarun sarauniya lasmin suka
firgice da ganin wayannan samudawa kai
hatta sarkin yaki kumru shi kansa daya ke
takama da cewa shi gwarzon mayakine
sannan ya fita yaki kala kala akalla sun kai
talatin
.
Bai taba ganin irin wayannan mutanen ba
kuma ko a labari bai taba jin irin nasu ba
.
Dayai duba izuwa ga sarauniya lasmin sai ya
cika da mamaki
Domin yaga ita ma ko kula da samudawqan
batayiba in banda cin abincinta da take
.
Shugaban samudawan ya kariso gaban su
kumru sannan yace yaku wayannan matafiya
shin meya rudeku da har kuka baro kasarku
gidajenku yan uwanku matanku ku ka kawo
kanku izuwa mahallakarku
.
Lallai da halama baku taba jin labarina ba
,sai budhe da dariya mai kama da karan
aradu koda yai dariyar mai isarsa sai ya
tsyuke baki kace bai taba yin dariya ba tunda
yake a duniya
Sannan yakara da cewa Nine shaddadu
rikakken dan fashin daya gagari dukkan
sarakunan wannan nahiya
.
Ban san yafiyaba balle hakuri lallai yai sai na
dandana maku azababbiyar mutuwa wadda
ban taba dandana ma bil adama ba
$
Yana rufe bakinsa sai ya lura da sarauniya
lasmin wadda ko tasan ma yana wajen in
banda cin abancinta babu abinda take$
.
Koda ganinta haka sai ya harzuka sannan ya
daka mata tsawa yace ke fingalalliyar
sarauniya lallai kisani tunda nake aduniya
babu wanda yataba arba dani batare daya
tsorata ba
.
Kece mutun ta farko wacce tai arba dani
naga ta shagalta sabida bata san ko waye
niba amma da sannu zaki sani
.
Ko rufe baki baiyiba sarauniya lasmin ta mike
tsaye sannan ta kyalkyale da wata irin dariya
koda ta idar da wannan dariya sai ta dubi
shaddadu ta daka mai tsawa 'kai la'ananne
kuma matsoracin dan fashi tuni labarinka ya
zomini cewa kana kwace ga marasa karfi
lallai yau dubunka ta cika tana rufe baki ta
zare takobinta ta afka cikin wayannan
samudawan koda samudawan suka ga haka
suma sai suka yi shirin tarbarta
$.
Ayayin data iso dafdasu sai ta daka tsalle
sannan ta shafka ma guda daga cikinsu sara
akai aiko sai takobin ta tsarge shi gida biyu
.
Koda sauran samudawan suka ga haka ai sai
suka mata ruf dugu ita kuma sai ta cigaba da
saransu tana sukansu nan fa suka cigabada
da faduwa kaasa matattu
,
Koda shugaban samudawan shaddadu yaga
muddin akaci gaba a haka toh lallai za ta iya
karar da yaransa
Itako lasmin sai ta zama kamar wata
shaidaniya a tsakaninsu sai saransu take. $$
Tana wani kalar tsalle tsalle
A duk lokacin da tayi tsalle sama sai dai kaga
kan basamude ya fadi kasa
Cikin lokaci kan kani ta karar da wayannan
samudawan dukkaninsu
Yarage saura shaddadu
¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤m
Al amarin suraila kuwa a yayin da aljani
sham'una ya luluka da ita cikin sararin
samaniya sai suka yi ta kutsawa cikin sama
har suraila ta suma
.
.
Zanci gaba
TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina Uku (3)
Littafin Shuraih Usman
Part 4
.
Farkawanta keda wuya saita tsinci kanta
kwance kan wani katifa mai tsananin laushi ,
cikin wata daki wadda babu komai cikin
wannan dakin face wasu tarkace da kuma
kayan tsafi
.
Sannan kuma dakin gabadayansa an
ginashine da zallar dutse wani abin
mamakinma shine babu wani alama da har
zaisa mutun yagane wannan dakin da dutse
aka ginashi
.
Koda suraila ta gama duba izuwa dakin da
kayan dake cikinsa saita fara tuna abubuwan
da suka faru tun fitowarta daga birnin
ashdamir har haduwarta da aljani sham'una
da kuma abubuwan daya faru tsakaninsu
.
Koda tagama wannan tunani sai ta fashe da
kuka tana mai danasanin kasancewarta a
wannan duniyar
.
Tana cikin kukanne sai taji kamar motsi a
bayanta
Tana waigawa saita ga wani gefe daga cikin
dakin yana janyewa izuwa yayin da wata kofa
tafara samuwa koda kofarnan tasamu sai ga
Aljani sham'una ya baiyana fuskarsa tana
mai cike da farin ciki
.
Ya dubeta sannan ya kyakyace dawata
mahaukaciyar dariya kai kace rufin dakinne
ke barazanar fadowa
Alokaci guda kuma ya tsuke bakinsa.
Sannan ya murtuke fuska tamkar wanda aka
aikomasa da sakon mutuwa
.
Yace yake wacannan budurwa kiyi sani cewa
na dade ina jiran zuwarki domin na mallaki
wata makami wadda muddin na mallaki
wannan makami toh gaba dayan duniya zata
dawo karkashina
Amma kuma wannan makami a zan iya
mallkarta ba batare da taimakawarki ba$
Kisani yanzu haka wannan makami yana can
wata kogo a ajiye
.
.
Ke kin kasance kinada nasaba da jarumin
duniya muraisu kuma ke ce kadai gudan
jininsa data rage a duniya
.
Aikoda suraila taji wannan zance saita kara
fashewa da kuka sannan tace yakai wannan
azzalumi kuma macucin aljani lallai kasani
nagani acikin barcina wani jarumi mai shigar
kamala ya shigo har cikin wannan gida taka
sannan ya yakeka ya kuma kubutar dani$
.
Lallai kasani nan da wani lokaci na tabbata
wannan mafarkin nawa sai ya zama gaskiya
'
Domin ni na kasance duk abin dana gani
cikin mafarki toh sai ya faru dani a zahiri
.
Tana rufe baki sham'uma ya sake bushewa
da wata dariyar wadda amonta ya dauka a
gabadaya cikin dakin
.
Lallai baki san wanene sham'una ba kisani
yanzu haka wannan gida da kike ciki yana
karkashin wata kasace wadda ita wannan
kasar samanta kankara ce kasarta kuma
ruwane zalla
.
Babu ta inda wani aljani ko bil'adama zaiyi
har ya gano wannan gida .
Ke koma ya gano wannan gida toh bazata
shigu mai ba
.
Shin ta hakanne kike ganin shi wannan
jarumin zaiyi iya shigowa cikin wannan gida
.
Babu wani mahaluki aduniyarnan walau
mutum ko aljan wanda har ya isa ya
tunkareni face nayi gutsu gutsu da naman
jikinsa$
.$
Yana gama fadin haka saiya turbune fuska
sannan yai nuni da hannunsa izuwa ga
bangon jikin dakin
.
Yana nuna bangon dakin da hannunsa sai
wani siririn haske mai kamae walkiya ya fita
daga hannun nasa ya dire akan bangon dakin
.
Yana sauka akan bangon dakin sai wata
duhuwa tafara lullube bangon can sai
wannan duhuwar ta yaye wani haske ya
bayyana acikin haskenne yarima hilal ya
bayyana yana mai tsala gudu akan dokinsa
.
Suraila ta kura ma hilal ido tana mai wani
irin kallo wadda ke tabbatar da ta taba
ganinsa
.
Sham'una yace" gashi shi wannan jarumi
tuni na sami labarin fitarsa daga masarautar
su wadda itace karshen rayuwarsa ,
Domin Neman wannan gida nawa tamkar
neman jaki mai kahone
.
Yana gama fadin hakan ya janye hannunsa
ga nunin dayayi , aiko yana janyewa wannan
hasken daya bayyana surar hilal take ya bace
bat tamkar bai taba wanzuwa ba.
.
Yajuya da nufin ya fice daga wannan daki
Yana fita wannan kofa ta kulle kanta
Yadda kasan babu kofa a wajen domin wajen
ashafe yake da bakin dutse
.¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤
Shaddadu yadubi sarauniya lasmin cikin
bacin rai sannan ya zaro takobinsa daga cikin
kubenta yai kukan kura ya dumfari sarauniya
lasmin da gudu ,
Babu abin da zaiba mutum mamaki face
ganin ita sarauniya lasmin ma ko wani
yunkurin kare kanta batayiba face murmushi
da take ,
Aikoda shaddadu ya kariso gabanta sai ya
kaimata sara ta fuska cikin zafin nama da
bajinta irin na manyan sadaukai lasmin ta
tsuguna saran ya wuce ta saman kanta
,
Ai shaddadu bai bari ta waigo ba yakara kai
mata wata saran shima tai nasaran goce
masa ,
Ai shaddadu sai ya haukace mata sara da
suka yashiga kaimata da zabgegiyar
takobinsa.
Sarauniya lasmin kuwa sai zullewa da
gocewa saransa take cikin bajinta
Koda shaddadu yaga wankin hula nason ta
kaisa dare sai yashiga hadawa da karfin sihiri
nanma baiyi tasiri ba
.
Domin kuwa duk wani masifan daya
wurgomata saidai yaga ta je kamar zata
tabata amma tana zuwa kusa da ita sai ta
juwa ta koma kansa
,
Nan danan shaddadu yafara gajiya amma
abin mamaki sai yaga lasminj ko alamun
gajiya babu ajikinta
.
Sai ma murmushi da take mai
Nan ya hasala yai wurgi da takobi sannan ya
bare rigar da take jikinsa
Woho hoho da mutum yana wajen da
shaddadu ya yage rigar jikinsa yai wurgi da
ita toh lallai da mutum ya gane ma
idanuwansa abin tsoro
.
Wani murdaddiyar jikice garshi sannan ga
wannan tozon naman gefen wuya sun yi
burda burda
.
Daga kan kafadarsa izuwa kirjinsa abude
suke amma cikinsa zuwa mararsa sirarane
Gabadaya ilahirin jikinsa duk kwanduwane
duk sun burbudo
.
Ita kanta sarauniya lasmin da taga wannan
sura nashi sai da ta ayyana aranta cewa lallai
yau tagamu da gamonta
.
Koda lasmin tagama ayyana haka aranta sai
tayi jifa da takobinta tana sauraran isowar
shaddadu
.
Shaddadu na ganin hakan sai yayi kukan kura
ya falfalo da gudu izuwa kan lasmin saida
yarage baifi taku biyu ba su hade ba sai ya
kaima ta wani wawan naushi
Lasmin ta tsuguna ta goce ma naushin
Yakara kaimata wani naushin ta gefen ciki ita
ko lasmin saita tare wannan naushin da
hannunta sabida karfin naushin sai da tayi
baya baya tamkar zata fadi amma sai ta tirje
.
Anan ta murtuke fuska itama ta kaimai wani
naushi ta gefen hakar kari dukda shaddadu
yayi kokarin ya kauce wa naushin amma ina
sai da naushin ta sameshi a hakarkari take ya
kurma wani uban ihu wanda tasa dakarun
dake tare da sarauniya lasmin wayanda
tunda akafara wannan gumurzu tsakanin
lasmin da shaddadu suke kallo sannan suna
matukar mamakin jarumtakar sarauniya
lasmin.
suka toshe kunnuwansu don ji sukai tamkar
dodon kunnensu ne zai fashe
.
Lasmin tai wani tsalle asama ta kaimai bugu
da kafa
.
Koda wannan bugu ya sameshi sai yai sama
yana katantanwa sannan ya fado ji kake
jagab faduwar kato
.
Yana faduwa lasmin ta dauki takobinta tai
kanshi aikoda shaddadu yaga haka sai yayi
sauri yazo gaban sarauniya ya zube akasa
yana magiya yana ce mata
" Yake wannan sarauniya ki mani rai nayi
alkawarin daga yau zan zama daya daga cikin
fadawanki kar ki kasheni na tuba na biki
.
Koda lasmin taji haka sai ta kyalkyale da
dariya sannan tace mai "ya kai wannan dan
fashi kasani kaine mutun na farko aduniya da
ya tsere wa kaifin takobina daga yau kazama
shugaban dakaruna "
Taba gama fadin haka ta nufi dokinta sannan
ta hau shima shaddadu nan aka bashi doki
ya hau suka nufi birnin ashdamir
.
Akwana a tashi har suka isa birnin ashdamir
batare da sun haduu da wani abin cutarwa
ba
¤¤¤
Wannan shine abin daya afku ga su
sarauniya lasmin akan hanyarsu ta zuwa
birnin ashdamir
.
.
Koya zata kasance
.
Muje zuwa part 5
TAKOBIN JIN 3!!!
Littafina Uku (3)
Littafin Shuraih Usman
Part 5
¤¤¤Al amarin yarima hilal kuwa tunda ya fice
daga birnin nurul ansar sai ya yanki daji yaita
tsala gudu batare da ya tsaya yada zango ba
sai daya Sai dayayi kwana da kwana ki yana
tsala gudu kan dokinsa Sallah ce kadai ke
tsaida shi sannan yadan ci wani abun .Wata
rana yana cikin tafiya sai ya hango wasu
dandazon mayaka tare da wani keken doki
Agefen keken dokin wani shirbeben
sadaukine yana zaune kan doki .Koda hilal yai
arba da wayannan dakaru sai ya kariso
garesu cikin tsananin mamaki sai yaga
dukkansu sun tsaya sannan kofar wannan
keken doki ta bude .Wata kyakkyawar mace
ta fito Duba daya yaimata yagane wannan
macen tana da wata matsayi a
masarautarsu.Wannan matar tai mai
murmushi sannan tace da shi" Marhaban
bika yakai wannan jarumi kuma sadauki mai
daka ma maza gumba yarima hilal dan Abul
Abbas mai mulkar birnin nurul ansar.Nan
alamun mamaki suka bayyana a fuskar hilal
ya dubi wannan kyakywar matar ya
tambayeta "Shin wacece ke sannan kuma ya
akayi kika sanni ".Koda taji haka sai ta
kyalkyale da dariya sannan tace" hatta abin
daya baroka dAga birnin ku nasani sannan
kuma ina mai tabbatar maka da cewa baza ka
taba samun galaba akan Aljani sham'una ba
face ka hada kai damu "Kisani niga
ubangijina na dogara kuma shine zai bani
nasara akan dukkan abin dana sa agaba "Ya
tari numfashinta cikin hasalaYasake cewa da
ita "wannan furuci da kikayi ya tabbatar min
kece sarauniya lasmin mai mulkar birnin
dimashka to kisani zan hada kai dake amma
bawai don bazan iya tunkarar shm'una bane
A'a saidai don inason na kafa tutar
musulunci awannan na hiya taku kuma shi
kansa takobin da kuke ta zumudin ku mallaka
.Ni zan iya dauko maku shi batare da zoben
wuta ba amma ina son naga shin dabarar ku
da karfin sihirin ku zasu iya taimakon ku ku
mallaki wannan takobi .Koda sarauniya
lasmin taji haka sai tayi murmushi sannan ta
dube hilal tace mai ka yi tafiya mai nisa don
haka kana bukatar hutu ,,Tana gama fadin
haka ta juya ta shige cikin wannan keken doki
shikuma hilal sai yabita da kallo ...Bazato ba
tsammani sai sukaji wata irin kara daga
sama tamkar aradun ce zata fado ita kanta
lasmin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment