Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan dajin wata
kila ko zamu iya cimma gari idan yaso sai mu kira
bakanike yazo ya duba." Inji nabilat.
" Wannan tunani ne mai kyau. Inaga sai ku jiramu nan. Ni
da namil sai muje." Inji aswad.
" Aa, bazaku tafi ku barmu a cikin wannan daji mai ban
tsoro ba. To amma me zai hana muje tare.?" Inji saudat.
" To yayi ba matsala muje din." Inji aswad.
Anan suka raba titi suka shiga cikin dajin mai cike da
dogayen itatuwa sai furanni koina. Aswad da saudat su
kadaine keda torch-light. Daji ne iya daji mai ban tsoro.
Koina ka duba sai itace. A kasa kuwa ciyayi ne masu
sarkako. Aswad shine jagoran tafiyar sai namil a gefensa.
Su kuwa yan matan sai binsu suke kowace jiki na
karkarwa kamar ace kyat su ruga.
PAGE 24
" Wai kuna ganin zamu iya cimma gari anan kuwa? Naga
tafiya muke amma ko alamar gona babu. Koina sai itace
da ramukka." Inji aswad.
" Gaskiya nima fa abunda nake gani kenan. Ai yanxu inaga
kamar munyi minti talatin muna tafiya ko." Cewar
saudat.
" Miye minti talatin? Ai munfi. Mun dade fa a wurinnan."
Nabilat ta bata amsa.
" Ke dubi gabanki." Humairat ta tsawatar.
Ita kuwa saudat bata jiba sai firarta take. Ai kuwa kafin
kaceme sai tayi tuntube da wani kututturen icce. Sai da
tayi yar karamar kara kafin ta juya da nufin faduwa. Shi
kuwa namil da jin ihunta sai yayi sauri ya juyo. To kafin ta
fadin ne yayi saurin rikota.Anan ya tallabota har saida ta
mike tsaye. " Wai,na kuru. Nafa gode dan uwa." Cewar
saudat.
" Kada ki damu saudat ba kome." Inji namil.
Anan saudat ta kalli humairat da nabilat. " Ku kuma da
kuke tumaki kuna ganin zan fadi amma a cikinku ba
wadda zata iya taimaka min." Injita.
" To miye ruwanmu a ciki. Ai naso ace kin fadi kin
karkarye muga yadda zakiyi." Cewar humairat.
" Iyeee. Ni ko?" Saudat ta tambaya.
" To idan akace kedin me zakiyi?" Nabilat ta fadi cikin
wasa.
" Yanxu dai ya isa ko kuwa sai naci uban mutum ne?"
Saudat ta hasko musu fitila.
" Ahayye. Rassss." Tare suka fadi nabilat da humairat.
Daga nan sai suka taba hannu suna dariya.
" Shegiya ke har wani karfi ne dake. Dubarta. Yar
ramamma ba jiki sai tsangwama." Cewar humairat bayan
ta kulle idonta saboda hasken fitilar da aka hasko mata.
" Ji yadda take tafiya burtum burtum sai kace agwagwa.
Wai damu zatayi fada." Inji nabilat.
Anan dai sukayita tsangwamar saudat tun tana iya
ramawa har saida tayi shiru saboda abun yayi yawa. Su
kuwa su aswad saurare kawai suke suna dariya.
PAGE 25
Saboda wannan fira da suke sai da sukayi tafiya mai nisa
ba tare da sun sani ba. Duk da kasancewar dajin mai
tsananin duhu ne amma haka suke tafiya sai kace ba
mutane ba. To suna cikin tafiyar ne sai fitillun su suka
fara billin bilin. Wato su kawo su dauke. A wannan lokaci
kuma suka fara jiyo ihun wasu daga can nesa. Ai kuwa
daga jin haka sai hankalinsu ya tashi. Anan suka fara gudu
domin ganin ko su waye. Sai da sukayi gudu mai dan nisa
kafin su kawo inda abun yake. To anan suka labe bayan
itatuwa suna ganin abunda ke wakana.
Wasu mutane ne masu kirar samudawa sanye da
bakaken kaya. Ba a ganin fuskarsu domin sun rufeta da
bakin kyalle. Kowanensu ya rike kwari da baka tare da
sauran makamai masu ban tsoro na dangin takubba.
Wasu mutane ne suka kamo su biyu mace da namiji sai
ihu suke. A gaban idonsu wadannan samudawan suka
kashe macen da namijin. Daga nan kuma sai suka ja
gangar jikinsu suka wuce da ita wani wuri. Bayan
wucewar su keda wuya sai su aswad suka fito daga
maboyarsu a tsorace.
" Bako shakka dole mu bar wannan dajin. Domin
wadannan mutane da muka gani na taba jin labarinsu da
dadewa. Sai gashi kuma kaddara tasa munxo wurinsu.
Kamar yadda naji ance suna...."
To kafin nabilat ta iyar sai sukaji ihu a bayansu. To anan
sukayi cirko cirko suna tunanin abunyi. Ai kuwa sai ga
wata mata a guje tazo wurinsu. " Don Allah ku taimakeni.
Kasheni zasuyi. Gasunan tafe." Haka matar ke fadi tana
kuka. To anan sukazo wurinta suna lallashinta tare da
tambayarta abunda ke faruwa. Amma saboda tsoron
daya dabaibayeta sai ta kasa bayani iyaka dai abunda take
fadi shine su taimaketa. Wannan abu ya mutukar tayarwa
su aswad hankali domin sai suka rasa abunyi.
" Gaskiya baxan iya zama a wannan wuri ba. Ni inaga
kawai mu koma bakin titi inda motarmu yafi mana
sauki." Humairat ta fadi cikin tsoro. Ai kuwa take ta nufi
hanyar da suka fito wai ta tafiyarta. Cikin sauri aswad ya
jawo hannunta.
PAGE 26
" Wai kinada hankali kuwa? Hanyar da muka fito itace
wannan matar ta fito kuma tace sun biyota ne don su
kasheta. To idan kikaje kika tarar dasu fa. Ni inaga kawai
mu manta da komi muyita gudu har mu kure dajin mu
gani ko zamu samu taimako." Inji aswad.
" To ai ko yanzu bamu tsira ba. Domin hanyar da kakeso
mubi itace mukaga sun shiga tare da gawawwakin mace
da namijin da suka kashe." Inji Humairat.
To anan suka rude suka rasa abunyi. Gaba kura baya
hayaki. Wato idan sukaje gaba basu tsira domin zasu iya
haduwa dasu haka ma idan suka juya baya inda suka fito
shima basu tsira ba.
" Ni inaga kawai mubi shawarar humairat cewa mu koma
inda muka fito wurin motarmu. Inaga zamu iya bacci a
can kafin gobe da safe sai musan abunyi." Inji namil.
" Wannan gaskiya ne ina bayanka." Inji nabilat.
" Nima haka." Saudat ta fada
Daga nan sai suka amince cewa xasu koma ta hanyar da
suka fito saboda gudun kada su hadu da wadannn
miyagu masu kashe mutane. To anan suka juya tare suna
tafiya da sauri cikin tsoro ba mai yarda a barshi baya. Ita
kuwa wannan matar da suka gani sai tayi shiru ta cigaba
da binsu. Ai kuwa basuyi wani nisa ba suka farajin
hargowa. Wasu kibiyoyi ne aka fara sako musu cikin
rashin tsammani. Ai kuwa sai kibiya ta shiga wannan
matar bakuwa. Anan tayi kara ta fadi. Su kuwa saura suka
runtuma baya a guje. Aswad kawaine ya tsaya taimakonta
shima da yaga abun yafi karfinsa dole yayi ta kansa. Gudu
yake suna binsa sai halbi kakeji ta koina. Yana cikin gudun
ne yaji karar matar. Anan yasa a ransa cewa sun kasheta.
A haka aswad yayi gudu iya karfinsa. Sai dakyar ya cimma
abokansa. To daga nan ne suka tsaya suna haki bayan
sunji cewa kamar an daina binsu.
" Wai yanzu meye abunyi kenan. Ku a ganinku haka zamu
cigaba da gudu da mun gansu kenan? Gaskiya inaga ya
kamat muyi fito na fito domin musan abunda suke nema
a gunmu." Cewar saudat.
" Bama shiba. Ya kamata musan ko su waye, kuma me
yasa suke kashe mutane, kuma idan sun kashe to me
sukeyi da sauran gangan jiki." Cewar namil.
PAGE 27
" Duk kunada gaskiya, amma maganar fito na fito dasu
bata tasoba domin sun fimu kome, da farko dai sun fimu
yawa, ga kuma makamai, to ya za ayi mu yaki wadannan.
Ni a ganina kawai mu cigaba da gudu har zuwa karshen
wannan daji wata kila ma samu taimako." Inji aswad.
" Da gaskiyarka aswad, wannan itace kawai mafita."
Cewar humairat.
" To amma yanzu me zai hana mu samu wuri a nan muyi
bacci zuwa gobe sai musan tayi." Cewar nabilat.
" Hmm, to ke in banda abunki ai yanzu ba wanda zai iya
bacci a cikinmu saboda wannan tashin hankali da muke
ciki." Inji aswad. " Inaga dai mu daure mu cigaba da
gudun kafin su iso nan." Ya kara fada.
Duk da kasancewarsu sun gaji, amma haka suka daure
suna tafiya da sauri don gudun wadannan mugaye masu
farautar mutane. Cikin wannan tafiya ne wani dan reshen
bushiya ya fado duum. Ai kuwa nan saudat ta ci taya sai
da suka tarota domin ita a zatonta sune suka kawo musu
harin ba zata.
" Wayyo kafata, ni gaskiya na fara gajiya." Cewar nabilat
bayan ta zauna.
" Wai me kike nufi ne, ki tashi mana mu cigaba." Inji
aswad.
" Kai mu hutu zamuyi, idan kana iyawa to ka tafi kai dai."
Inji humairta bayan itama ta zauna.
Ai kuwa nan suka yi zamansu suna nishi dakyar. Suna
cikin hutun ne bacci ya sacesu amma banda aswad
domin yana nesa dasu. Saidai duk abunda ke faruwa yana
kallo. Kai da ganin fuskarsa kasan yana cikin rashin jin
dadi. To anan ya tashi da nufin tayar dasu sai dai abunda
ke damunsa shine kishin dake busar da makwogoronsa.
To anan ya fara shawara ko ya tayar dasu ko kuwa ya fara
samo ruwan da zaisha. Can sai yaji kishin ya damesa.
Saboda haka baiyi wata wata ba sai ya fara bincike ko zai
samu tafki a wurin. Sai da yayi tafiya mai dan nisa kafin
ya cimma magudanar ruwa masu tafiya. Anan ya duka ya
kwankwada har saida yayi hamdala. Mikewarsa keda
wuya sai ya fara jiyo ihun wasu. Ai kuwa a guje ya juya
domin ganin ko su waye.
PAGE 28
Cikin kankanin lokaci ya isa wurin daya bar su namil na
bacci. A mamakinsa baiga kowa ba. Anan ya tsorata, to
kada dai ace wadannan miyagun sun zo sun wuce dasu.
Anan ya fara kiran sunayensu daya bayan daya amma ba
wanda ya amsa. Can kuma sai ya cigaba da jin ihun. Daga
nan ya runtuma a guje a inda yakejin sautin na fitowa.
Yana cikin gudun ne sai ya tarar da wasu gungun miyagu
sun farauto wasu mutane sai jansu suke da kasa. Anan ya
fara tafiya sannu sannu domin ganarma idonsa. Kicibis
sai yayi arba dasu namil. Wai ashe wannan ihu da yakeji
sune bayan da aka rutsa dasu suna bacci. To anan aswad
ya rasa abunda ke masa dadi. A buge dai wadannan
miyagu basu buguwa balantana shi ko makami bayada.
Cikin bakin ciki da rashin jin dadi ya cigaba da tafiyar
sanda yana binsu a hankali domin ganin inda zasu kaisu.
Su kuwa su namil sai faman kururuwa suke suna neman
taimako. Haka wadannn miyagu suka cigaba da jansu a
kasa har saida suka riski wani makeken gidan sama mai
ban tsoro. Anan aswad ya labe bayan itace har saida suka
gama shiga gidan. Daga nan sai ya lababo domin bude
kofar amma gam ya kasa. Ba yadda bai yi ba amma daya
tura sai yaji kamar kara rufeta ake. A haka ya hakura ya
fara zagayen gidan ko zai samu hanyar shiga. Ai kuwa
cikin sa a ya dace domin wata katanyar makwarara ce ya
hango manne a kasan gina. Ba abunda ke fitowa ciki in
banda wani abu jawur. A haka ya kurawa makwararar
idanu yana tunanin ko menene ke fitowa ciki jawur. Daga
karshe dai sai ya fara tunanin cewa jini ne domin jan yayi
yawa.
Cikin makwararar ya shiga bayan ya durkusa. A haka ya
cigaba da tafiya a durkushe yana tsallake sassan jikin
mutane. Wasu har sun fara wari saboda dadewa. Ai kuwa
sai banko jini akeyi a ciki. Kafin kaceme kayansa sun
koma jawur. Haka dai aswad ya daure ya cigaba da tafiya
har saida ya dau lokaci kafin ya kawo karshen
makwararar.
PAGE 29
Daga nan sai ya diro a cikin wani wangamemen daki. Ba
kome a ciki dakin in banda gawawwaki. Anan ya fara
dube dube. Wasu gawawwakin sun bushe. Wasu kuma
danyu ne da gani kasan ba a dade da kawasu ba. Wasu
kuma a can gefe zigidir ba mai ko kyalle a jiki. An hade
maza da mata a wuri daya ba kyaun gani. A haka dai
aswad ya cigaba da kallon dakin yana kallon abubuwan
ban mamaki. Sai kuma sassan jikin mutane dake sarkafe
a gina. Irin su kai, hannaye, kafafuwa kai harda cinyoyi.
Sai kuma wani katon gatari a kusa ga makwararar. Kai da
gani kasan dashi ake ma mutane kisan gilla. Haka aswad
ya karema dakin kallo tsaf daga nan kuma sai ya nufi kofa
da nufin fita. Murda ganbun yayi a hankali da nufin
budewa amma sai yaga ko alamar girgizawa bai yi ba.
Daga nan sai yasa karfinsa amma duk a banza. Da dai
yaga ganbun na shirin bata masa lokaci sai ya dauko
gatarin dake rataye saman gina.
Cikin karfi ya fara dibar ganbun ba sassauci. Ai kuwa yana
cikin hakane sai yaji tahowar wasu. Anan yayi jifa da
gatarin. Daga nan ya tube kayansa ya koma zindir. Cikin
sauri ya shafama kansa jini sannan yayi kwance cikin
gawawwaki sai kace matacce. Yana nan kwance ne sai
yaga wasu mutum biyu sun shigo mace dana namiji sun
ajiye wasu gawawwaki. Daga nan sai suka fara wata
magana. To a mamakinsa ba hausa ce sukeba. Wani
yarene suke wanda bayaji. Anan ya kurawa namijin idanu
kamar ya sansa. Da karfi yayi magana. " Hamir!" Ai kuwa
sai namijin ya juyo inda yake kwance. To anan hankalin
aswad ya tashi don kada asirinsa ya tonu. Ita kuwa
maccen sai ta hanashi domin a ganinta ba kowa a wurin.
Saboda haka yaji dai kamar an kirasa ne. Daga nan sai
namijin ya fasa zuwa wurin gawawwakin. Iyaka ya bincika
makwarara daga nan suka tafiyarsu.
Shi kuwa aswad cikin sauri ya fito, anan yasa kayansa ya
fita dakin cike da mamaki wannan abu. Bako shakka
yasan wannan namijin. Abokinsa ne kuma dan
makarantarsu. To amma kuma ya akayi ya shigo wannan
kungiya? Wannan itace amsar da aswad ya kasa ba kansa.
PAGE 30
Tafiya yakeyi cikin tsoro da fargaba. Sai juye juye yakeyi
domin a ganinsa ana iya kawo masa hari ta ko ina. Gidan
ya kasance da lunguna masu ban tsoro. Haka dai ya
cigaba da tafiya sako sako kwana kwana amma baiga
abokansa ba. Wannan abu ya mutukar tayar masa da
hankali wanda daga karshe sai ya fara tunanin ko an
kashesu. Yana cikin tafiyar ne sai yaji ana magana cikin
wani daki. To anan ya labe yana lekon ko su waye a ciki.
Idansa ya kafa a huduwar dake ganbun. Anan ya ga
abokinsa hamir da wannan matar da suka shigo dakin
gawawwaki tare. Wasu bokitayya ne cike da jini. Su kuwa
su hamir din sun tube kayansu sai wanka suke da jinin.
Yana cikin lekensu ne sai matar ta juyo. Anan sukayi ido
hudu da aswad. Ai kuwa bai yi wata wata ba ya watsa a
guje.
Yana cikin gudun ne yaci karo da wata mata, a nan ya fadi
saida kansa ya bugi gina. Da sauri ya mike domin ganin
ko wacece. Ai kuwa yana ganinta sai ya ganeta domin
itama yar makarantarsu ce tare sukayi jami a. " Laaaa.
Zee me kikeyi anan? Kema sun kamoki ne?" Anan ya fadi
saboda rashin karfin jiki. " Ki taimake ni zee. Zasu
kasheni."
Anan ita kuwa zee din ta tallaboshi. " Haba aswad ya kana
wannan magana. Kayi shiru kaji ba wanda zai taba min
kai."
Anan ta rikoshi suka fara tafiya har saida suka iso wani
daki. Daga nan ta taimaka masa ta azashi saman wata
kujera. A wannan lokaci jikin aswad ba karfi ko kadan
saboda wahalar daya sha. Jikinsa duk tambo ne na
jimuwar da yayi. Anan zee ta zauna kusa dashi tana tabin
fuskarsa. Daga nan kuma saita rungumeshi cikin
murmushi. Kasancewar aswad cikin rauni ko kallonta
baya iya yi. Hannu tasa da nufin kwance masa bell. Sai
dakyar ya samu ya tsayar da ita.
" Haba aswad ya kana haka. Nasan kafi kowa son wannan
abu da zamuyi." Inji zee.
" E amma banda yanzu." Cewar aswad.
Daga nan saita mike tsaye. Rigarta ta debe ta koma daga
ita sai wata yar shame wadda ta matseta sosai kana ganin
kome nata. Anan tayi tafiya ta rangwada domin ya gani. "
Ina fatan dai zakaso abunda ka gani. Kome na nan yadda
ka barshi ba abunda ya canza." Zee ta fada tana
murmushi.
PAGE 31
Can sai ga hamir ya shigo dakin shi kadai. Ai kuwa aswad
na ganinsa sai ya mike yana tangadi. " Me ya kawoka nan.
Macuci azzalumi. Ashe dama kai dan kungiya ne." Haka
aswad ke fadi a lokacin daya tunkari hamir cikin fushi.
" Haba aswad ya kana fadar haka, ka kwantar da
hankalinka ba abunda zai faru." Anan ta jawo aswad
saman kujerarsa.
Daga nan saita yiwa hamir wani signal da idanu. Ai kuwa
yana ganin haka sai ya fita. " Waike in tambayeki, hala me
kikeyi a cikin wannan gida na marassa imani? Aswad ya
tambaya.
" Na marassa imani fa kace?" Cewar zee.
" E mana, ai naga abunda na gani. Kuma nasan cewa
kema a cikinsu ki...." To kafin ya iyar ne zee ta masa wani
mugun bugu fuska. A nan ya zube kasa sumamme. Daga
nan saita jawoshi ta kaishi wani karamin daki ta kulle.
Bayan kamar minti ashirin, sai ga zee ta dawo tare da
hamir. Anan suka bude dakin da aka kulle aswad amma a
mamakinsu ba kowa ciki. A nan suka fara dube dube
amma ko alamunsa basu gani ba. Juyowa sukayi da nufin
su tafi. Ai kuwa juyowarsu keda wuya sukuyi arba dashi a
tsaye. Anan ya jawo kawunansu ya buga da juna. Ai kuwa
nan suka fadi sumammu jini na fita ta hancinsu. Daga
nan sai ya fita dakin a guje. A nan ya nufi wani lungu mai
tsananin duhu. Gashi bayada fitila domin ya dade da jifa
da ita tun a lokacin da aka biyosu. Saboda haka sai ya fara
tafiya a hankali don gudun kada yaci karo da wani abu.
Fitillun dake gidan basaci sosai. Wasu kuma sun lalace sai
dai su kawo su dauke. Haka dai aswad ya ci gaba da tafiya
cikin duhu yana lalube. Can sai ya farajin nishin wani. A
nan ya nufi inda yakejin sautin na fitowa. Ai kuwa yana
cikin tafiyar ne sai yaji gudun wasu samudawa sun nufo
wurin da yake. Cikin sauri ya boye kusa ga ganbun wani
daki. To bayan sun wucene sai ya shiga dakin dama a
cikine yakejin nishin na fitowa.
PAGE 32
Ai kuwa shigarsa keda wuya ya like hancinsa da hannuwa
saboda tsananin doyin da yakeji. Anan ya fara dube dube
amma baiga kowaba. Kuma baisan ko menene ke wari
ba. Can sai ya hango wani daki. To anan ya nufi ciki. Ai
kuwa shigarsa keda wuya sai ya tarar da kwarangwal na
mutane ( skeleton) tare da wasu gawawwaki duk sun
rube. Dakyar ya samu ya shiga har kuryar dakin. Ai kuwa
shigarsa keda wuya sai ya tarar da nabilat kwance tana
nishi. Sun tube mata kaya ta koma zigidir. Sai kuma
bayanta duk an zaneshi da yuka. Anan aswad yazo kusa
da ita cikin tausayawa. Tallabota yayi yana tambayarta
inda akaje su namil amma bata iya magana. Goyata yayi
ya fito da ita dakin. Daga nan sai ya cigaba da gudu yana
bincikar inda aka aje sauran abokansa. To yana cikin
gudu ne sai ya hango wasu samudawa a gabansa.
Kowanensu sanye da bakaken kaya. Bako shakka kai da
ganin wadannan mutane dole ka girgiza domin tafiyarsu
ma ta daban ce. Anan ya juya baya da nufin tserewa
kuma sai yaga wasu irinsu.
Sun rike kwari da baka kai da gani kasan basada imani.
Aswad a tsorace yake domin yasan dasun iso gunsa to
sunansa gawa. Kawai sai ya hango wani daki a kusa dashi.
Ai kuwa a guje ya kutsa kai ciki. To kafin ya shiga ne wani
daga cikin miyagun ya halbo kibiya. Ai kuwa kai tsaye ta
shiga bayan nabilat. Sai da ta danyi wata kara daganan
bata kara cewa komi ba. To bayan ya shiga dakin ne sai
yaga ashe hanya ce doguwa irin wadda ya baro. Cikin
sauri ya kutsa kai ciki sai faman gudu yake. To bayan yayi
tafiya mai nisa sai ya tsaya domin yaga halin da nabilat
take ciki. Anan yaga ta sandare ko motsi batayi. Girgizata
ya farayi amma ina rai yayi halinsa. Anan ya rungumeta
yana kuka cikin bakin ciki ya rasa babbar abokiya tun
suna yara. Ya dade zaune kusa gareta yana jimami. Bayan
wani lokaci kuma sai ya tashi ya nufi hanyarsa yana tafiya
dakyar. Haka ya cigaba da tafiya yana tangadi sai kace
wanda yasha giya. A wannan lokaci kome nasa ciwo yake.
Yana cikin tafiyar ne ya fadi galabaice ba tare da sanin
inda yake ba.
PAGE 33
A haka aswad ya kasance cikin wannan hali na suma ba
tare da sanin inda yakeba. Sai da aka dau lokaci mai
tsawo kafin surutun wasu miyagu ya tadashi. Cikin sauri
ya tashi firgigit. Labewa yayi cikin wata kwana mai duhu.
Bayan sun wuce ne sai ya fito yana bin bayansu domin
yaga inda zasu. A haka ya cigaba da tafiya yana binsu.
Idan yaga zasu jiyo sai ya boye don kada su ganshi. Sai da
sukayi tafiya mai nisa duk a cikin gidan kafin su shigo
wani irin makeken daki. Duk mutanen dake cikin dakin a
tsaye suke suna sanye da kaya jajjaye masu ban tsoro.
Wani mutum ne yayi tsaye a tsakiyarsu sai wata magana
yake da wani yare. Kasancewar aswad baya jin abunda
suke fadi sai ya boye a cikin labule. Dakin gaba daya an
zagayeshi da jan labule ta ko ina. A haka aswad ya natsu
yana kallonsu domin yaga abunda ke gudana.
Yana cikin kallon ne sai yaga mutumin ya daina magana.
Daganan sai wasu mutum biyu suka shigo da wani namiji
a daure. Saman wani benchi aka daureshi tamau. Daga
nan sai mutumin ya dauko wata yuka. A gaban idonsa aka
yanke wannan mutumi. Yukace aka darara masa a wuya
kamar yadda ake yankan rago. Cikin kankanin lokaci jini
ya kama kwarara kamar fanfo. Anan mutumin wanda da
gani kasan shine shugaba ya dauko wata tasa ya tara
yadda jinin zai zuba a ciki. Shi kuwa mutumin da aka
yanke sai ya kama fizge fizge sai da wasu suka rikeshi. To
bayan jinin ya gama zuba ciki sai shugaban ya dauki tasar
ya kafa kai. Sai da yasha sannan yaba na kusa gareshi. A
haka aka fara zagaye da wannan tasar. Idan wannan
yasha yaba wannan har saida kowa yasha. Shi kuwa na
karshe dasha sai ya ajiye tasar a kusa ga shugaban.
Anan aswad ya lura cewa mutanen maxa da mata ne. Shi
kuwa shugaban sai ya nuni tasar da yatsansa. A nan ya
fara fadin wasu dalassammai na tsafi. Ba a wani jimawa
ba sai yaga innuwar mutumin da aka kashe ta fito cikin
tasar. Anan shugaban ya kama innuwar ya turata cikin
wata kwalba. Daga nan sai ya rufe ya ajiye ta wani wuri
cikin dakin. Can kuma sai aka shigo da wata yarinya
zigidir. Anan aka azata saman benchin da aka kashe
wannan mutumin na farko.
PAGE 34
Bayan an daureta tamau sai shugaban ya tube kayansa ya
koma zigidir. Anan ya fuskanceta da nufin keta mata
haddi. Shi kuwa aswad da karfi ya dago kansa domin
ganin ko wacece wannan yarinyar. Ai kuwa yana dubawa
sai yaga ba kowa ceba in banda humairat. Jikinta duk jini
ne kai da gani kasan ta galabaita. Anan ya fara tunanin
meye abunyi kafin wannan mugun mutumi ya iyar da
nufinsa akanta. Wasu samudawa ne sanye da bakaken
kaya ko fuskarsu ba a gani saboda sun rufeta da bakkin
kyalle. Rike suke da muggan makamai sai kaida komo
kawai suke a cikin dakin domin tabbatar da tsaro.
Hankalin aswad ya mutukar tashi domin yasan idan suka
ganshi to karyarsa ta kare. Haka ya cigaba da wasi wasi sai
daga baya dubara ta fado masa.
Cikin sauri ya fito daga maboyarsa ya kalli shugaban. " Ni
zanyi duk abunda kukeso indai kunyi alkawari bazaku
taba wannan yarinyar ba."
Anan mutanen dake cikin dakin suka tsura masa ido ko
kyaftawa basayi. Daga nan sai shugaban ya fara magana
da wani yare yana kallonsa. Haka ya cigaba da maganar
har saida aswad yayi zaton cewa kamar bayajin hausa.
Mutum biyu daga cikin samudawan ne suka rikoshi. Anan
suka gurfanar dashi gaban shugaban. Daga nan sai suka
dauko wani benci suka axa shi sama. Basu daureshi ba
iyaka dai sunyi tsaye gabansa sai maxurai suke. Bako
shakka aswad yayi wautar bayyana kansa ga wadannan
miyagu. Sai daga bayane wannan tunani ya shiga
kwakwalwsarsa.
Shi kuwa shugaban kai tsaye ya nufi wurin humairta da
nufin biyan bukatarsa. Aswad yayi kokarin tashi domin ya
hanashi amma sai suka rikeshi. Daya ya dafe kafafunsa
dayan kuma hannaye. A gaban idonsa wannan mutumi
ya taka bencin a inda humairat take. Take ya jawota a
jikinsa. Ba yadda aswad bai yiba domin ya hana wannan
abu amma ina sunfi karfinsa domin sun rikeshi gam.
Yana kallo ana warwasawa amma ba yadda ya iya. A haka
ya fara zub da hawaye na bakin ciki domin humairat itace
yarinyarsa tun kafin suyi wannan tafiyar. Sai kuma nabilat
wadda itace babbar kawarsa tun suna yara.
PAGE 35
Saida aka dau lokaci ana warwasawa da humairtat ba
kakkautawa. Su kuwa sauran yan kungiya sai kallo suke
domin abun gwanin ban shawa ne a wurinsu. Ita kuwa
humairat tanaji sai dai bazata iya komeba domin a daure
take tamau. Bayan an gama ne sai shugaban ya dauko
wata karamar yuka. Anan yasa aka juya masa ita. A
saman bayanta ya fara wasu zane zane. Saboda radadin
da takeji dole ta fara ihun wuya. Anan aswad ya gane
cewa irin wannan zanen da aka yiwa humairat bako
shakka shine ya gani ga bayan nabilat kafin ta mutu. To
kenan indai hakane itama sai da shugaban yayi amfani da
ita kafin ayi mata wadannan zanukkan. Bayan an gama
zane bayan humairat da yuka sai aka dauketa aka wuce
da ita wani wuri. Shi kuwa aswad sai suka daureshi tamau
da kaca aka barshi a nan. Yana kallo kowa ya fita dakin ya
barshi a nan.
Ba a wani jimawa ba saiga zee ta shigo dakin. Cikin
rangwada ta shigo cike da murmushi sai taku take dai dai.
" Kai a ganinka ka samu nasara ne ko?" Daga nan saita
fara kewayensa tana masa kallon keta.
" Kai kyakkyawa ne" Ta fada a lokacin data karo bakinta
domin ta sumbaceshi. Ai kuwa da karfi ya tofa mata
yawu. A nan taja da baya tare dayin dariya. Halshenta ta
janyo tana lashe yawun daya tofa mata. Bata damu ba ko
kadan da kazantar dake tattare dasu ba. Wata karamar
yuka ta dauko tana lasawa a halshenta. Anan aswad ya
kura mata idanu domin yaga ko meye take shirin yi. Kusa
ga kafafuwansa ta tsaya. Anan ta fara soka masa yukar a
hankali ga ciki. Datasa sai ta fitar, a duk lokacin data fito
da yukar sai yayi kara saboda tsananin zogin da yakeji.
Kafin kaceme jini ya fara kwararowa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment