Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan sun diro ne sai suka
tabbatar da cewa yanxu sun fito daga gidan. Anan suka
fara gudu baji ba gani kai kace mahaukata. Haka suma
masu bakaken kaya suna dirowa sai suka bisu a guje.
Sai da gudu yayi gudu sannan suka fara hango dishi
dishin titi tare da jin jiniyar motar yan sanda. Anan su
dije suka kara kaimin gudu domin su cimma motar yan
sandan ko xasu samu taimako. Gudu suke suna ihu ko
yan sandan zasuji. Suna cikin gudun ne sai sukaga wasu
mutane sun diro saman itace a gabansu. Mace da namiji
ne idanuwansu sunyi wani baki bakyan gani. Kuma a
wannna lokaci ne masu bakaken kaya suka cimmusu.
Anan nana ta gane namijin. Shine saurayinta hamir
wanda yayi sanadiyar kawota wannan gida itada
abokanta.
" Ke a tsammaninki kinsha ko? To yanxu zakibi yan uwaki
dama suna can suna jiranki."
Anan ya bude hakoransa marar kyan gani yayi cikin su
dije. To kafin ya karasa ne sai sukaga ya fadi. Suna
dubawa sai sukaga yan sanda biyu mace da namiji ashe
sune suka halbeshi. Dije na kallon macen yar sandan saita
ganeta. Itace anisa wadda mairo ta bata labarinta. Kuma
har ta karbe ID card dinta daga hannun mairo. Anan
anisa ta juya zuwa ga macen wato abokiyar hamir.
" Sannunki zee, sai gashi yau mun kara hadewa. Kuma sai
gashi na kamaki a lokacin da nakeso." Inji anisa.
" To daga nan fa?" Zee ta tambaya.
" Sai zuwa lafira." Anan anisa ta bindige zee kasa.
PAGE 60
Su kuwa masu bakaken kaya na ganin haka sai suka
rantama a guje. Anan anisa da abokin aikinta suka rufa
musu baya a guje. Sai da su masu bakaken kayan
gudunsu daban yake. Suna gudu sai kace iska. Kafin
kaceme sun ba su anisa tazara mai yawa. Suna kaiwa ga
gidan. Taba kofar kawai sukayi sai suka bace bat ba a
ganinsu. Haka shima gidan sai ya bace bat wurin ya koma
fili. Anan anisa ta fara cizon hannu domin wannan shine
abunda ya faru a lokacin da yan sanda suka taimaketa
bayan ta fito daga gidan. Yan sandan suna zuwa gidan sai
sukaga ya bace ba a ganinsa. Haka anisa ta dawo tare da
abokin aikinta wurin su dije. Anan dije ta bata ID card
dinta tare da fada mata yadda akayi ta sameshi da kuma
labarinta.
" Kada ki damu dije. Xan taimakeku keda iyayenki. Daga
yanzu bazaku kara zama cikin wannan hali na talauci ba.
Zan mayar dake birni inda zaki samu ilimi na zamani
wato boko keda kanenki. Shi kuwa abbanki zansa a nema
masa aiki mai tsoka." Anan anisa tayi gyaran murya kafin
ta cigaba. " Wannan namiji da kike gani sunansa aswad.
Abokin aikina ne. Kuma shima ya taba shiga irin halin da
kiki tsinci kanki. Ba shi kadai ba har ni nan na taba fadawa
ciki."
Haka suka cigaba da tafita suna hira har suka kawo bakin
motar. To kafin su shiga ne dije da nana suka kalli juna
cikin farin ciki. Daga nan sai suka shiga motar su anisa. A
wannan lokaci hasken safiya ya fara fitowa amma ba
sosai ba. Aswad ne ke tuka motar sai anisa kusa dashi.
Dije da nana a baya. Anan aswad ya mika ya nufi hanyar
fita dajin.
Daga karshe dai anisa ta taimaki dije sosai itada iyayenta.
Ta basu gida a cikin birni. Shi kuma abba an samar mashi
aikin gwamnati. Dama yanada qualification na N C E
aikine bai samu ba. Dije da kanenta sun zama yan birni
gadan gadan domin a gidan anisa suka tare ita ke daukar
dawainiyarsu. Iyaka dai idan ta samu dama takan kaiwa
abokanta na kauye ziyara. Haka ta riki zumunci batayi
watsi da su mairo ba. Da su nana.
PAGE 61
Ni anisa, a kullum idan nayi tunani nakan yi mamakin
wannan duniyar da muke ciki, yadda al amurra suka
tabarbare ba mai tausayi balantana hakuri. Na gano
hakan ne sanadiyar wannan lamari dana gani ya faru
akan idona. Wato hakuri shine maganin zaman duniya.
Saboda haka duk wanda bai yi hakuri ba, to bazai ga
hakuri ba. Talauci masifa ce, fitina ce kuma bala i ne,
wannan dalili shine yasa akace kowa ya tashi ya nemi
nasa ba don komi ba sai don kariya daga wannan masifa
ta talauci.
Wato da ace dije tayi hakurin talaucin data tsinci kanta a
ciki. To da bata shiga wannan masifa ba. Haka shima
karuwanci fitina ne. Domin da ace nana batabin maxa to
bazata hadu da hamir ba har ya kawota wannan gida na
maita ba. Maita gaskiya ce. Kuma koina akan samu
mayyu. Sai dai har yanxu ba a san mafarinta ba, da kuma
yadda ake gane masu fama da ita ba. Da gaske akwai
wannan gida. Kuma ba abunda akeyi a ciki in banda
yankan mutane. Sai dai har yanxu ba wanda ke iya cewa
ga inda gidan yake saboda an asirceshi.
Zee da hamir sun mutu. Amma kuma shugabansu bai
mutu ba. Haka ma macijin da suke bautama yana raye.
Kai in takaice maka labari da yawa daga cikin mayyun
suna raye. Kaga kenan labari bai kare ba. Domin zasu
cigaba da gudanar da miyagun ayyukansu har abada.
Wannan labari ba shirme bane gaskiya ce. Kuma yakan
iya faruwa gareka, gareki, ko kuma garemu.
Ka tsaya kayi tunani, ka hanga, kuma ka auna sai ka
rubuta abunda ka gani a cikin wannan labari idan ba
kamshin gaskiya a cikinsa. Sanina ne cewa duniya ta
canza daga yadda muka santa zuwa akasin haka. Duk
abunda baka tsammamin ya faru shi yake faruwa, kuma
duk abunda kake ganin zai faru shine baya faruwa. Addu
a itace takobin mumini kuma duk wanda ya riketa to
bazai tabe ba har abada. ALLAH ka tsaremu, ka karemu
daga sharrin duk wani mugu na boye dana zahiri. Ameen.
THE END
Based on the novel by abdul king article.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment