Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga kasa. Ita kuwa sai
murmushin keta takeyi. Tana cikin yi masa wannan lahani
sai wani ya shigo dakin. Tana ganinsa saita tsaya.
Daga nan sai suka fara wata magana da wani yare. Aswad
naji amma bai san abunda suke fada ba. Daga nan kuma
sai tayi jifa da yukar tabi mutumin. Aswad na kallo suka
fita dakin. To anan ne ya fara tunanin abunyi kafin ta
dawo. Domin yasan idan ta dawo to lahanin da zata yi
masa sai ya ninka na daxun.
PAGE 36
Yukar data jefar a kusa gareshi take. Sai dai matsalar itace
ko motsin kirki baya iya yi balantana ya tabuka wani abu.
A haka dai ya daure yana mike hannayensa ko zai iya
daukar yukar. Dama an ce mai nema na tare da samu ai
kuwa cikin sa a ya dauko yukar. Dakyar ya lankwasa ya
yanke kacar dake hannunsa na hagu. To kafin ya yanke na
daman ne saiga zee ta dawo. Shi kuma yana ganinta cikin
sauri ya boye yukar a jikinsa. Daga shigowarta ta kura
masa idanu ko kyaftawa batayi. Ai kuwa batayi wata wata
ba ta afka masa sai sumbatarsa take. Shi kuwa aswad
dama yasan abunda ya tanadar mata saboda haka bai
damu ba sai ya bata hadin kai. Saida suka dade suna
sumbatar juna amma bata gano cewa ya yanke kacar da
aka daureshi da ita ba. A haka abu yayi kamari zee sai
nishi take, shi kuwa ya dada kankaneta a jikinsa kamar da
gaske. Suna cikin yini ya fito da yukar ya soka mata a kirji.
Anan ta fadi tana kururuwa shi kuwa jini ya fallatso. Da
sauri ya yanke dayar kacar ta hannunsa na dama. Daga
nan ya kara soka mata yukar a dayan kirjin. Sannan ya
tallabota ya daura saman bencin da aka daureshi. Anan
ya daureta tamau sannan yayi tafiyarsa ya barta tana ihu.
A guje ya fita dakin don gudun kada wasu su shigo. Yana
cikin gudun ne sai ya lura cewa inda yake takawa akwai
digon jini. Saboda haka sai ya yanke shawarar bin sawun
jinin domin yaga mai shi. Ai kuwa haka ya cigaba da
tafiya guda guda har saida yakai wani daki. Shigarsa dakin
keda wuya sai yayi arba da humairat tana nishi daya
bayan daya. Cikin sauri yazo wurinta duk jikinta ya rine
da jini.
Sunkuyawa yayi kusa gareta yana zub da hawayen
tausayawa. Tana ganinsa sai tayi murmushi duk da cewa
cikin ciwo take. A nan ta jawo kansa har saida jikinsa ya
hade da nata. " Ka kulamin da kanka. " Haka ta fadi cikin
kunnensa daga nan bata kara cewa kome ba. Iyaka dai
yaji kalmar shahada wadda itace kalmarta ta karshe.
Aswad yayi kuka sosai domin a cikin ransa ba yarinyar da
yakeda muradin aure irin humairat. Sai kuma gashi ta tafi
ta barshi. A haka ya rungumeta a jikinsa yana kuka cike
da tausayawa. Saida ya dau lokaci a hakan kafin ya saketa
ya fita dakin.
PAGE 37
A haka aswad ya fito dakin cikin jimamin rasa humairat.
Tafiya yake dakyar kai da gani kasan ya gaji sosai. To anan
ne ya fara bidar hanyar fita daga gidan domin a ganinsa
namil da saudat sun mutu. Gidan ya kasance katon gaske
sai kace gari. A haka aswad yayi ta kalwade amma ya kasa
gane hanyar fita. Duk inda ka duba lungu ne cike da
dakuna birjik. Sai dan neman duhun daya mamaye gidan
gaba daya. Ga fitilllu amma basaci sosai saboda haka
mutum ba ko ina yake gani ba. Kuma kasancewar lokacin
a cikin darene. To sai duhun ya karama gidan ban tsoro.
Shi kuwa aswad sai tafiyarsa yake yana tuntube da
gawawwakin mutane. To yana cikin tafiyarne sai yaji
gudun wani kamar an biyo shi. Anan ya labe domin yaga
ko su waye. Ai kuwa suna wucewa ta wurinsa sai yaga
wadannan samudawan ne masu bakaken kaya suka biyo
wani da nufin kasheshi.
A guje ya bisu da nufin yin taimako. Koda ya cimmusu sai
ya tarar sun kama mutumin zasu sareshi. To kafin su
aiwatar da nufinsu ne ya taresu da fada. Gawawwakin
mutane ya rinka dauka yana dukansu dashi. Shi ma
mutumin na ganin haka sai ya samu damar kubcewa. To
anan aka fara bata kashi tsakanin wadannan miyagu dasu
aswad. Saida suka dau lokaci suna fadan kafin su samu
damar kai mutum biyu kasa cikin su goma. To da sukaga
fadan ba mai karewa bane balantana gashi sun fara
gajiya. Cikin wayo suka runtuma a guje su kuwa miyagun
suka bisu. Ba inda wadannan miyagu basu duba ba lungu
lungu sako sako amma basu gansu ba. Saboda haka suka
juyo da nufin komawa.
Su kuwa su aswad sai suka fito daga maboyarsu. To anan
aswad ya gane cewa namil ne ashe dama bai mutu ba.
Cikin jin dadi suka yiwa juna barka tare da cigaba da
binciken gidan ko xasuga saudat.
" Amma fa naji dadin ganinka abokina, ina fatan dai ka
gano inda su nabilat suke?" Namil ya tambaya.
Anan aswad yayi shiru bai tanka ba.
" Lafiya kuwa ya naga kayi shiru?" Ya kara tambaya.
" Yanzu dai muje mu nemi saudat, domin nabilat da
humairat sai dai muyi musu addua." Cewar aswad.
PAGE 38
Anan namil ya done kansa cikin jimamin wannan
magana. Daga nan sai suka mike hanya suna tafiya suna
juyawa don tsoron kada a kawo musu harin ba zata. Sai
da sukayi tafiya mai dan nisa kafin su fara jiyo ihu a cikin
wani daki. A hankali suka bude dakin. Ai kuwa shigarsu
keda wuya suka tarar da saudat a daure saman kujera.
Wani mutum ne fuskarsa a cabe sai kace dodo. Da wasu
dogayen hakora da yake fama dasu marar kyan gani.
Yankan sassan jikinta kawai yake da yuka tana ihu.
Mutumin na juyowa sai yayi arba dasu. Cikin sauri sai ya
dauko gatarinsa yayi cikinsu. Namil ne ya tare shi suka
kaceme da azababben fada. Shi kuwa aswad sai ya nufi
wurin saudat da nufin kwanceta.
Bako shakka mutumin yafi namil karfi nesa ba kusa ba
amma duk da hakan bai yarda an kaishi kasa ba. Wani
takobi ne ya dauko dake rataye a bangon dakin. Dashi
yake kare harin wannan mutumi mai siffar dodanni. Shi
kuwa aswad yana kwance saudat sai ya turata waje
domin ta jirasu. Yana dawowa sai yaga mutumin ya kai
namil kasa yana neman hallaka shi. Da sauri da dauko
wata kwalba ya makama mutumin da kai. Ai kuwa dole ya
saki namil. Anan aswad ya tallabo namil suka fita dakin.
Fitarsu keda wuya sukaci karo da miyagun sai nemansu
suke. Shi kuwa namil baya iya gudu domin akwai rauni a
kafarsa. Haka dai aswad ya rika shi suka cigaba da gudun
su uku. Su kuwa miyagun sai halbo musu kibiya suke.
Suna cikin gudun ne sai sukaji namil yayi wata kara. Anan
suka duba sai sukaga ashe yuka ce ya taka har ta huda
kafarsa ta fito. Ba yadda basu yiba su fitar da yukar
amma suka kasa. Gashi kuma yukar a kasa take idan ba a
fito da itaba to bazai iya tafiya ba.
" Ku tafiyarku wata kila ku tsira da ranku. Ku barni nan
domin nasan lokacina yazo." Haka namil ke fada yana zub
da hawaye. A wannan lokaci kuma miyagun sun kusa
cimmusu. Duk da hakan aswad bai saurari maganarsa ba.
A haka yayita kokarin fitar da yukar amma abu ya
faskara. To anan ne suka kyaleshi domin miyagun na gab
da cimmusu.
PAGE 39
A guje suka shiga kwana sai kace motar da ba burki.
Bayan sunyi nisa kadan sai suka jiyo karar namil. Anan
suka fara zubar da hawaye domin sun san cewa an kashe
shi. A haka aswad da saudat suka cigaba da mugun gudu
sai kace ransu zai fita. Cikin gudun ne suka samu kansu
cikin wani daki. Sai wata katanyar makwarara lake a
kasan dakin. Aswad yayi mamakin ganin wannan
makwarara domin tayi kamada wadda ya shigo cikin
gidan. Amma kuma yasan ba ita bace domin shi wannan
dakin ko alamar jini babu. Kamar an dade ba a yi amfani
dashi ba. Cikin makwararar aswad ya shige ita kuwa
saudat ta bishi a baya. A haka suka cigaba da tafiya har
suka samu damar fitowa daga gidan. To bayan sun diro
ne sai suka kalli juna cikin jin dadi suna mamaki har
yanxu cikin darene duk dadewar da sukayi a gidan.
Tsayuwa sukayi na dan lokaci suna ma gidan kallon tsaf.
Wato makeken gidan sama ne mai ban tsoro. Haka shima
dajin cike yake da dogayen itace sai furanni ko ina. To
suna cikin wannan dube duben ne sai sukaji motsi a
bayansu. Dubawarsu keda wuya sukaci karo da
wadannan miyagun suna fitowa ta makwararar da suka
fito. Ai kuwa cikin karfi su aswad suka ranta a guje ba
sassauci. Gudu suke suna tsallake ramukka sai kace doki.
Saida suka dau lokaci suna gudun sannan suka fara
hango dishi dishin titi. To anan suka kara kaimin gudunsu
domin su cimma titi su gani ko xasu samu mota. Su kuwa
wadannan miyagu sun rufa musu baya sai halbinsu suke
da kibiya.
Cikin gudun ne saudat ta fada wani kwazazzaben rame
mai shegen zurfi. Anan aswad ya tsaya yana tunanin
yadda xai daukota ta. Ita kuwa sai ihu take domin tasan
da sun zo wurin to karyarta ta kare. Da sauri aswad ya
katso bishiya mai dan kwari. Anan ya tura mata, cikin sa a
kuwa ta rike. A hankali ya cigaba da jawota har saida ya
fito da ita. To anan ya juya da gudu da nufin ta biyoshi.
Sai da ya dan yi nisa sai yaji tsit kamar bata biyoshi ba. Ai
kuwa yana juyowa sai yaga ashe miyagun ne suka halbo
mata kibiya har ta nutse a cikinta. Yayi nufin ya taimaka
mata amma dole ya fasa domin suna gab da karasowa. A
haka ya kyaketa suka isar da ita shi kuwa yayi ta kansa.
PAGE 40
A wannan lokaci hasken alfijir ya fara fitowa. Haka aswad
ya cigaba da gudun har saida ya kawo bakin titi. Anan ya
hango wata yar karamar mota ta yan sanda. Hannunsa ya
fara dagawa yana nuni cewa su tsaya. To bayan motar ta
tsaya ne sai yaga ashe mace ce yar sanda ita kadai a ciki.
Anan ta kalleshi taganshi jina jina.
" Malam lafiya kuwa?" Ta tambaya.
" Ba lafiya ba. Don ALLAH ki tamikeni. Kasheni zasuyi."
" Su waye?" Ta tambaya.
Bai tsaya amsa mata ba iyaka ya bude motar ya shigo. "
Muje kawai zan miki bayani." Ya fada.
Anan ta tayar da motar tana dubansa cike da mamaki. "
Hala meye sunanka?"
" Aswad."
" Ni yar sanda ce kuma zan taimakeka idan har mun isa
cikin gari." Haka ta fada tana juya sitarin. " Kada ka damu
sunana anisa." Ta fada bayan ta kama hanyar fita daga
cikin dajin.
A haka aswad ya samu damar tsira daga sharrin
wadannan miyagun mutane bayan ya hadu da anisa.
Maita gaskiya ce. Kuma koina akan samu mayyu. Sai dai
har yanxu ba a san mafarinta ba, da kuma yadda ake
gane masu fama da ita ba. Aswad ya tafi da zimmar cewa
kul a jima kul a dade sai ya fanshi kisan gillar da aka yiwa
abokansa. Haka itama a anisa, wannan dalili shine yasa ta
yanke shawarar zama yar sanda domin ta fadada bincike
domin ganin bayan wadannan mayyu. A duk lokacin daka
tsinci kanka cikin daji, kada kayi tsammanin cewa irin
hakan bazai iya faruwa ba. Ka dauka cewa fiye da hakan
kan iya faruwa.
Wannan ba labari kawai neba. Gaskiyace, da gaske akwai
mayyu masu irin wannan dabi a can a wani gida. Gidan
yana a cikin daji. Sai dai har yanzu ba a san inda dajin
yake ba balantana a gano gidan. Aswad da anisa zasu
hada kansu domin ganin sun cika burinsu na ganin cewa
wadannan mayyu sun kare, to abun tambaya anan shine
ta yaya zasu cika wannan buri tare da daukar fansar kisan
da aka yiwa abokansu?
The story continues on the third version of the last
episode........TAFIYAR DARE 2
MAYYUN JINI
AUTHOR : ABDUL KING ARTICLE
EPISODE 3
PAGE 41
Ni anisa, a kullum idan nayi tunani nakan yi mamakin
wannan duniyar da muke ciki, yadda al amurra suka
tabarbare ba mai tausayi balantana hakuri. Na gano
hakan ne sanadiyar wani lamari dana gani ya faru akan
idona. Wato hakuri shine maganin zaman duniya. Saboda
haka duk wanda bai yi hakuri ba, to bazai ga hakuri ba.
Talauci masifa ce, fitina ce kuma bala i ne, wannan dalili
shine yasa akace kowa ya tashi ya nemi nasa ba don komi
ba sai don kariya daga wannan masifa ta talauci. Bari in
fada maka wani labari na wata yarinya wadda wanna
masifa ta rashi ta faru akanta. Sanadiyar hakan yasa al
amurran rayuwarta suka lalace sabida kin yin hakurin da
tayi.
Sunanta khadija, akan lakanceta da dije, haka ta kasance
cikin wannan sababi na talauci ita da iyayenta. Abbanta
Dan shago ne dashi sai kuma noma da yakeyi duk
shekara. Wataran sukan yini basusa hatsi a baka ba
saboda masifar rashin da suka tsinci kansu a ciki.
Wannan rayuwa da khadija samu kanta a ciki ya jefata
halin kaka ni kayi. Wanda daga karshe ta kasa jurewa da
jarabawar da aka yi mata. Anan kuma ta fara dana sanin
abunda ta aikata.
Kafin dai muje ga labarin bari mu waiwayi abunda ya
faru a baya. Bako shakka na gama binciken da nake
gudanarwa. Kuma a yanzu hakan ina kan bakana na
daukar fansar kisan gillar da aka yiwa abokaina. Sai dai
har yanxu akwai abunda nakeso na tabbatar kafin na fara
aikin. Zee da hamir sune manyan makiyana. Amma da
sannu zasu gane kuskurensu. Kuma da sannu zasuyi dana
sanin abunda suka aikata.
Yanzu bari muje ga labarin khadija da da kuma
makasudin faruwarsa. Tare da jin yadda muka kare da
wadannan miyagun makiya nawa masu farauntar
mutane. A duk lokacin dana tuno abunda ya faru nakan
yi bakin ciki sosai. Amma duk lokacin dana tuno abunda
na shirya sai nayi dariya mai yawa. Nasan cewa kul a jima
kul a dade assiri zai tonu. Kuma karshen alewa kasa. Haka
kome nesan jifa kasa xata dawo.
Wata rana a cikin wani kauye...........
PAGE 42
" Wallahi ni umma yunwa nakeji."
" Haba dije, yanzu kiyi hakuri kije rafi sai ki debo mana
ruwa. Idan malam ya dawo maga abunda ya samo mana
ko."
" To ni kullum sai na yini ba abunda naci, kuma abincin
ko dadi babu."
" Yanzu dai kiyi hakuri diyata ta kaina. Sheka maxa ki
debo mana ruwan."
Haka dije ta karbi tulun badon tasoba. Tafiya take tana
gunguni cikin takaici. " wani shegen tuwo kamar kanacin
dussa. Da wata banzar miya ko gishiri babu. Mtsss." Haka
ta fada cikin gunguni bayan ta kai kofar gida.
" Laaaa dije, dama yanzu nake cewa in biya miki sai gashi
kin fito, yanzu dai taka muje nasan rafin nan ya cika." Inji
kawar dije wato mairo.
A haka dai dije ta daure ta sakar mata dan guntun
murmushi. Daga nan sai suka kama hanyar zuwa rafi. Ita
kuwa mairo ta kasance mai surutu sosai. Tafiya suke sai
zuba take ba sauki. Tun dije tana iya amsawa har takai sai
dai tace to. Sai da suka kai bayan gari sannan suka iso
rafin. Mutane maza da mata kowa sai sha anin gabansa
yake. Masu dibar ruwa nayi masu wanki nayi. Wannan
lokaci marecene sanya sanya domin magrib ta gabato.
Dije ta kasance kyakkyawa abun kallo, saboda haka daga
isowarsu duk samarin dake wurin suka tsura mata ido
kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake. Ita kuwa dije bata
damu ba domin ta saba da irin wannan kallon da ake
mata. Kai da ganin tafiyarta kasan ba lafiya. Domin yinin
yau komi bata ciba tun da safe.
A cikin shagon nasu kome babu domin duk sun cinye
abunda ke ciki. Tun da safe abba ya fita nemo abunda
zasuci amma gashi har marece bai dawo ba. Dije ta
kasance mai tarbiya, ladabi ga kuma kunya. Sai kuma
tarin ilimin addinin da take dauke dashi.
Dakyar ta sunkuya tulunta a cikin ruwan. Ai kuwa tana
janyowa sai santsi ya kwasheta cikin ruwan. Ita kuwa
mairo dama a kusa gareta take. Cikin sauri ta ajiye
tulunta ta shiga cikin ruwan domin ceto dije. Anan ta
tallabota tare da tulunta.
PAGE 43
" Sannu dije." Wasu yan mata da suka kewayeta suna
mata jaje. Can kuma sai ga gungun samari sun iso wurin.
" To ita ya jikin nata." Babba daga cikin samarin yayi
magana.
" E to da sauki." Mairo ta amsa.
" To ALLAH tsare gaba." Ya kara fada.
A haka aka yita zuwa ana ma dije jaje. Ita kuwa kwance
take sai nishi take dai dai sabida ruwan da tasha. Bayan
wani dan lokaci ne mutane suka fara watsewa aka bar
mairo da dije. Ita kuwa mairo sai fita take mata dai dai
domin ta farfado. Duhu ya farayi a wurin sai kuma iskan
dake hurawa mai shiga jiki. Ita kuwa mairo sai karkarwa
take tare da dube dube cikin tsoro. Suna cikin wannan
hali ne sai taga an hasko musu wani haske. Anan mairo ta
juya a mamakinta sai taga mota na xuwa wurinsu. Tayi
mamaki sosai da ganin motar domin a kauyen nasu ko
mai mashin babu. Ita kanta rabonta da taga mota an fi
shekara.
Anan ta kurawa motar idanu har ta iso wurinsu. Ita kuwa
dije sai ta fara farfadowa. To bayan motar ta iso gab dasu
sai sukaga wani mutumi ya fito daga ciki. Shigarsa ba irin
ta mutane bace domin kayan nasa dai abun tsoro ne.
Haka siffar jikinsa domin kirar samudawa ce dashi. Dije
na ganinsa sai ta tashi da karfi. Hannunsa ta kalla daga
nan sai ta ja da baya. Anan ta juya da nufin barin wurin.
" Ke baki dauki tulunki ba." Mairo ta fada amma ina dije
bata amsa ba sai tafiyarta kawai take. Anan ta dauko
tulunan ta ba dije nata daga nan suka fara sauri domin su
bar wurin. Shi kuwa mutumin sai ya bisu da kallo har
suka bace masa da gani.
" Dije yau naga abun mamaki." Mairo ta fada tana waige
waige ta gani in bai biyosu ba. " Wai ko kinga hannunsa?"
Ta tambaya.
" Hmm, ni ban taba ganin wanda aka yiwa zanen maciji
ba a hannu." Mairo ta fada cike da mamaki.
" Maciji fa kikace?" Dije ta tambaya.
" E mana, wai kina nufin bakiga hannunsa ba. Ai zanen
maciji ne aka yi masa a hannu kuma irin wannan zanen
da baxai goge ba har abada." Cewar mairo.
PAGE 44
" To kuwa indai hakane abunda na gani ya zama gaskiya."
Inji dije.
" Hala me kika gani?" Mairo ta tambaya.
Anan dije tayi shiru bata amsa ba. " Abunda nakeso dake
shine idan munje gida kada ki fadawa kowa abunda ya
faru." Inji dije.
" Kada ki damu kawata an gama." Mairo ta fada.
Haka suka cigaba da tafiya har suka iso cikin gari. Daga
nan suka yi sallama kowa ya kama hanyar gida. Ai kuwa
da shigar dije a gida sai ta tarar dasu umma sunyi zaune
zugum sai kace wadanda aka yiwa mutuwa. Dan kanenta
ne a kusa ga umma ya gincira sai cizon baki yake sabida
yunwa. Shi kuwa abba ya debe hular sai zufa ke kwarara a
jikinsa.
" Umma kada dai kicemin yauma ba a samo ba." Dije ta
fada bayan ta ajiye tulun.
Anan suka jiyo suna kallonta amma ba wanda ya tanka
mata. " Innalillahi wainna ilaihir raji un. Gaskiya ni na fara
gajiya wannan abu dame yayi kama. " Anan dije ta shiga
dakinta sai rusa kuka take. Tana cikin kukan ne abba ya
shigo yana lallashinta.
" Haba dije kiyi hakuri mana, shi rashi na Allah ne kuma
samu na Allah ne, kuma nasan Allan nan daya jarrabemu
da wannan rashi bai manta damu ba. Iyaka dai...."
" Iyake me?" Dije ta katseshi. " Kana zama da mutum
kullum babu. Ni nayi dana sanin kasancewa a cikin
wannan gida. Da ace mutum yana zabar inda yakeso da
bazan yarda na fito ta wannan zuri a ba." Haka dije ta
fada cikin kuka.
Shi kuwa abba sai ya matso kusa gareta yana shafa gashin
kanta. " Haba diyata ya kina wannan magana. Sai kace
wadda bataje arabiya ba. Ni a ganina kome nufin Allah
ne. Kuma Allah yasan abunda yasa ya jarrabemu da
wannan rashi. Tana iya yiwuwa ya gwada mu ne ya gani
ko zamu iya hakuri da masifar da muke ciki. To kinga
kuwa idan bamuyi hakuri ba bazai taba yaye mana
wannan masifa da muke ciki ba.
" Jarabawa? Ai wannan jarabawa tayi yawa kome
hakurinka dole ka gaji." Cewar dije.
" Haba dije kada kiyi sabo fa."
" To idan nayi sabo sai me?"
PAGE 45
Anan dije ta tashi da karfi. " Ni tafiyata zanyi bazan iya
zama cikin wannan talauci ba."
Shi kuwa abba sai yabita yana lallashinta. To anan ne
umma ta shigo da taji hayaniyar tayi yawa. " Haba dije
yanzu idan kika fita to ina zaki. Mu fane iyayenki kuma
bakida wasu wadanda suka fimu." Umma tace bayan ta
riko hannunta.
" Ni bazan zauna bakin talaucin ku ya kasheni ba. Baci ba
sha Kullum haka."
" Kibar daga murya kada makwabta suji." Umma ta
tsawatar.
" To idan sunji sai me? Ai abunda na fadi gaskiya ne ba
karya ba."
Anan dan kanenta ya sheko ya rungumeta. " Yaya kada ki
tafi ki barmu mu kadai a nan."
Anan dije tayi shiru tana duban kanenta daga nan kuma
sai ta koma dakinta tayi kwance ruf da ciki. A haka sukayi
bacci basuci kome ba cikin rashin jin dadi.
Tunda kulu kulun safiya umma ta farawa bugawa dije
kofa domin ta tashi. Cikin magagin bacci ta bude kofar sai
hamma takeyi. " Yaufa ki tashi akwai aiki a gidan nan.
Yanzu nan koje ya kawowa abbanki sadakar dawa tiya
uku. "
" Laaa, dawa. Hehehehe." Anan dije ta fada jikin umma ta
kankaneta cikin murna. Tun bata wanke baki ba ta nufi
dakin umma a guje. Dawar ta dauko tiya uku ta fara
durawa cikin bakinta sai da umma ta jinye bokitin.
" Wai dije lafiyanki kuwa. Kinacin dawa danya idan ta
halakaki fa. Yanxu yi maza ki shirya akwai inda zan aikeki.
"
Bayan dije ta kimtsa ne sai ta shiga dakin umma domin
taji sakon da zata bata. Bayan an mata bayanin abunda
akeso tayi sai ta fito daga gidan. Tafiya takeyi tana taku
dai dai. Yau dai fuskarta cike take da annuri ba kamar jiya
ba. Wani lungu ne ta shiga inda gidaje dai dai kune. Haka
dije ta cigaba da shiga lunguna lunguna tana dan wakenta
na yan mata. Bayan tayi tafiya mai nisa ne sai ta kawo
gonar abba. Anan ta gyara daurin kallabinta kada ya fadi.
PAGE 46
Ai kuwa tana kutsa kai ciki sai ta farajin nishi na fitowa a
bayan wata bukka. A hankali ta fara tafiya domin taga ko
waye. Tana kaiwa wurin sai ta tarar da mairo na fesa wani
irin zawo. Da karfi mairo ta mike tsaye saboda tsoro.
Batasan lokacin fa fitsari ya fara fita daga tsaye ba. "
Shegiya dubi gabanki." Dije ta tsawatar.
" Wai na manta." Cewar mairo bayan ta dauko zanenta.
" Ashe dama kece ke mana xawo tun da safe ko?" Dije ta
tambaya.
" Haba kawata yau fa dai ne. Kuma yau din ma matsiyata
yayi." Inji mairo cikin kunya.
" To meye kika zoyi nan?" Dije ta tambaya.
" Au, har kin manta cewa muna fitowa tsintar kara?
Yanxu haka fa girki ne za ayi shine aka tadani naxo tsintar
karan." Mairo ta fada. " Hmm, yar kawata kenan." Mairo
ta fada bayan ta matso kusa ga dije da nufin rike
hannunta. Ai kuwa da karfi dije taja da baya tana like
hanci.
" Gaskiya wari kikeyi sosai, yanxu dai muje ga gulbi can ki
wanke wannan kazantar dake jikinki." Inji dije.
" Ni din ke wari?" Mairo ta tambaya.
" E mana, koda yake ance gwalo bayajin warin jikinsa."
Dije ta fadi cikin yanga.
" To yayi zan rama ai, yanxu dai muje gulbin ko bazaki
rakani ba?" Mairo ta fada cikin murmushi.
" Allah zance baxan jeba." Inji dije
" To yanzu dai kiyi hakuri muje." Mairo ta fada cikin wasa.
Haka suka cigaba da tafiya suna fira har suka kai bakin
gulbin. Da zuwa mairo ta nufi wurin da nufin shiga. Kafin
ta kai sai taji an katsa mata tsawa.
" Kai, uban waye ke lekena?"
Anan sukaga nana ta fito daga cikin gulbin wai ashe
wanka takeyi a ciki. Nana ba karamar shakiyiya ce a garin
ba domin har maza suna shayinta. Ta kasance katanya
kakkarfa mai siffar karfi. Anan ta fito daga cikin gulbin
zigidir tana duban su dije. " Wallahi ni zanci uban yaro. In
banda iskanci me ya kawoku nan ne?"
" Kiyi hakuri nana bamusan kina ciki ba." Mairo ta fada
bayan ta done kanta.
PAGE 47
Anan nana ta matso kusa dasu. Su kuwa kowane jikinsu
sai dar dar yake kada suji mazga. Sun san da cewa nana
bata buguwa a garesu. A wannan lokaci sun mata kallon
tsaf. Bako shakka nana ba karamar katanya bace.
Damatstsan nan cike suke kai kace yar dambe. Zanenta ta
dauko ta yafa. " Wallahi kun kuru yau banajin fada da sai
naci ubanku. Shegu masu kan goriba." Anan nana ta
bangajesu ta wuce.
" Hmm, shegiyar ji tafiyarta. Kato kenan." Mairo ta fada
cikin karamar murya.
" Ke me kikace?" Nana ta juyo.
" Haba nana ai badake takeba. Wannna magana fa
tsakaninmu ne." Dije ta bata amsa.
" Au, kin kuru." Nana ta fada bayan ta cigaba da tafiyarta.
Bayan nana ta wucene sai mairo ta shiga gulbin. Anan ta
tsaftace kanta daga nan suka nufi wurin tsintar karan.
Suna gamawa suka nufi hanyar gida. To akan hanyarsu ne
suka gamu da ummar dije.
" Wai me ya tsayar dakene tun daxu?" Umma ta fada.
" Ba kome umma." Dije ta bata amsa.
" Tun daxu nakejin tsoro,akan hakan yasa nace dole naxo
na duba ko lafiya." Umma ta fada bayan sun fara tafiya
tare.
A haka suka cigaba da tafiya suna fira su uku, sai da suka
kawo wata mararraba sannan suka rabu. Dije da
mamarta suka nufi hanyarsu daban itama mairo haka. A
haka mairo ta cigaba da tafiya ita kadai, kasancewar tun
da safene ba kowa kake gani a hanya ba. To anan hanya
tabi da ita ta wannan rafin da dije ta fada jiya. Ai kuwa
tana kaiwa wurin sai ta tarar da wata mota. Bayan ta kusa
cimma motar ne sai taga wata mata ta fito daga cikin
motar ita kadai. Anan aka fara kallon kallo. Can sai matar
tayi magana ta kirata. Bayan mairo tazo wurin sai matar
ta fara

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment