Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kai mu, ai Ahmad yayi dacen mata ba
kamar ni ba. A da Umma bana tunanin sake aure,
amma yanzun ina ganin dole sai nayi mata biyu".
Umma ta ce, "To ba dai yanzun ba duk nawa ka
ke kuma yaushe kayi wancan?" Ya ce, "Umma ke
dai ki min addu'a, ban samu irin macen data dace
da ni ba". Ta ce, "Ina maka addu'a, Allah ya
shirya maka matarka." Abba ya ce, "Ko ta shiryu
sai nayi aure insha Allahu". Ta ce, "Abba ni ko
gani nake ba ka san wadda za ka aure din ba
itama da nata kalar halin zata zo, sai su taru su
ruda ka". Ya kalli Ummi wadda ya lura da kallon
da ta tsare shi da shi kamar tana son jin abin da
yake fada ne. Ya maida idanunshi kan Umma.
"Na yarda da tarbiyar wannan yarinyar da nake
son aure yanzun, duk da yarinyar bata sona tana
girmamani". Umma ta ce, "Har ka samu kenan,
'yar gidan waye? Ummi kuwa tuni makoshinta ya
bushe, ta zaro idanu tana son ji wa kuma Abba
ke so? 7:....Ya kalli Ummi ganin yadda ta zaro
ido ya ce "Ke ni ke fadama wa ki ka zaro ido ki
ka tsare ni da su?" A hankali ta lumshe idanu
sannan ta maida kanta kan hannun kujera, ya
fuskanci Umma "Ba 'yar unguwar nan ba ce",
matsalar da yarinyar bata sona". Umma ta ce,
"To ka bar ta mana ka samu mai sonka? Yo in
haka ne ma ka ce gara matar taka ta gida, don
ita tana sonka". Yayi shiru zuwa can ya ce
"Umma in dai zan sameta zan aureta a haka".
Umma ta ce, "Kayi addu'a, ina ko mamakin mene
ne ta gani na 'ki a tare dakai Abba?" Ya ce cikin
'yar dariya "Umma ai ba dole ba ne sai ka birgke
kowa". Ummi ta mike jiri na dan dibanta ta shige
ciki. Zance ya dada watsewa, ta furta bayan ta
fada kan gado, ni ina son shi shi kuma ashe yana
can ya zarme da son wata. Ranar ta raba dare
tana kuka daga karshe ta soma ba kanta
shawarar ta samu Abba ta ce a fili dama
shisshigi ne irin na zuciyata Ya Abba ba irina
yake so ba. Shi kuwa zuciyarshi ta soma zargin
wani abu a kan Ummi, irin yanda ya ga tayi
kamar hankalinta ya tashi da batunsa. In ko haka
ne zai fi kowa murna, wata zuciyar ta ce ka sani
ko tsabar jin gulma ne yasa ta kafa maka ido duk
da haka yasha alwashin bibiyarta. Sun taso daga
sallar Juma'a shi da su Ahmad gidan budurwar
Tukur suka dosa, wayar Salis ta katse shi. Wani
aiki ne ya taso dole ya koma gurin aiki. Ya sauke
su a unguwar shi kuma ya nufi gurin aikinshi.
Karfe biyar ya baro gurin aikin da nufin yada
zango gidan Ummanshi. 8.... Yasan yau juma'a
duk yanda aka yi zai samu abinci na musamman,
don al'adarta ce girkinta na juma'a daban ne,
tana girmama ranar da abincin da ta san mijinta
zai yi farin ciki da shi. Haka nan ta kan yi
kwaliyyar musamman, shi yasa yake kara
kwadayin aura Ummi, ya san zata dauki wannan
tarbiyyar. Matasa guda uku a tsaye gefen titi cikin
fara'a da murna suka tsaida shi, ya saba kusan
kullum sai irin haka ta faru. Matasa kan tsaida
shi suna ma su nuna jin dadi da ganinshi, a gaisa
su wuce. Wasu kuma su amshi lambarshi har da
ma su son adireshinsa, yanzun ma sai ya tsaya
zai fito, tsum! Yaga sun bude motar sun shigo.
Biyu baya daya gaba, ya ba su hannu suka gaisa
su duka. Na gaban ya ce. "Mai matasa ai muna
jin dadin taimakon da ka ke mana. Ya kamata a
baka Sardaunan Matasa". Daya daga baya ya ce
"Sarkin Matasa gaba daya zamu ba shi, don yana
kokarin gurin binciko matsalolin matasa". Abba
ya yi murmushi tare da cewa, "Na Gode". Dayan
da bai yi magana ba sai ya ce "Amma mai
Matasa ka san da wannan matsalar?" Abba ya
waiwaya da nufin jin karin bayani, sai ko ya fesa
mishi wata farar hoda a fuska. Take nan atishawa
da tari suka tirnike shi. Ya soma mutsuka
idanunshi bakinshi na furta "Inna lillahi wa'inna
ilaihir raji'un". Kafin 'yar sakwanni kanshi yayi
din, kuma ya fita daga hayyacinsa. Suka tuka
motar suka tashi dashi. * Farkawa ya yi tamkar
wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude ido
tangaran a kan silin, irin na masu hali. Kwan
lantarki irin na kasaitattun gidaje ya daki
hancinshi. Nan take ya shiga tunanin me ya kawo
shi nan? ba 6ata lokaci ya tuna duk abinda ya
faru, da sauri ya tashi zaune yana fadin "Inna
lillahi wa'inna ilaihir raji'un". Ya ci gaba da kallon
dakin, cikin tangameme ne yana dauke da
tafkeken gado da sauran saitin shi. Sai kafet din
tsakar daki da kayan kallo, ga kuma kofofi guda
biyu. Ya tambayi kanshi da cewa me ya kawo ni
nan? me matasan suke nema a gurina?" Take
muryar Hajiya Nina ta fado masa, inda take cewa
"Za ka zo yau din ne ko sai an dauko ka?" ya
girgiza kai tare da cewa, Lallai wannan makirar
matar ce tasa aka mi shi haka". 9... Nan take ya
soma karanta addu'ar neman tsari. Daya daga
cikin kofofin ta bude, ya kure idonsa gurin da
kallo, matar ta shigo sanye cikin doguwar riga
baka mai ma6allai a gaba. Fara ce kyakkyawa,
shekarunta suna tsakanin Talatin da takwas zuwa
arba'in da biyar, domin kyawun nata sun 6oye
shekarunta, ta baza gashi a kafada. Tsura mata
ido yayi yana son tuna inda ya ta6a ganinta,
domin tabbas yasan fuskar. Muryarta ce ta katse
shi,"Dama nasan zuwa yanzun ka farko, kuma ka
gama nazarin yanda aka yi kazo nan. Kila ma
tunda kana da kamannin ma su basira ka hararo
wadda tasa a ka dauko ka". Ya ce, "Kwarai
kuwa". Lokacin ne ya tuno inda ya santa, wato
Hajiya Zabba'u ce matar shaharraran Attajirin nan
Alhaji Uzairu wadda a ke nuno ta a TV da Jaridu
tana taimakon talakawa da Marayu. Wadda ake
labarin tsoron Allahnta da gudun duniyarta,
wadda ta gina Masallatai da Makarantun Addini
ma su dama. Ya girgiza kai cikin matukar
mamaki, ta ce "Ka gane ni kenan?" Ya ce (Cikin
karfin hali) "Lallai mutum mugun ice. Wannan shi
ne Allah a baki shaidan a zuci". Ta ce "Kai ne na
biyu da ka furta wannan kalmar, sai dai bana fata
ka zama na biyu da ya bakunci inda na farkon ya
tafi. 10.... Ta tako a hankali ta dunfaro shi, ya
matsa baya cikin zuciyarshi yana korar shaidan,
'yar dariya tayi. "Nutsu Idris ko ince Abba. Ba
fyade zan maka ba". Ya dubeta da sauri, "Eh haka
nace, in na son hakan zan maka, amma ba
hakanne burina ba". Ta zauna bakin gadon, "Ka
zo mu daidaita, in kana tsoron ciwo zan baka
makari, sai dai ina so ka sani bana dauke da
wata cuta". Ya ce, "Karya ki ke, kina dauke da
mummunar cuta". Ta ce "In ka tashi daga dan
jarida ne, ka koma Likita zan baka dama ka
gwada ni". "Ya ce ba ki bukatar gwaji don ga
ciwonki nan a fili ciwon zuciya". Ta ce, "Sam ba
ni da ciwon a zuciyata, to in ma ina da shi me zai
dameka tunda ba dauka za ka yi ba". Ya sake ja
da baya ya ce, "Zuciyarki ta kamu da ciwon zina.
Ta yi duhu dumdum! har bata iya ganin
gaskiya...". "Ta daga mishi hannu, "Dakata min,
ban tambayeka labarin wa'azi ba, domin in shi
nake son ji ina da kaset-kaset kala-kala zan saka
na ji". Ta mike zuwa wata durowa ta bude, dauri
uku ta dauko ta aje gaban madubi na 'yan dari
biyar-biyar sababbi dal! Ta ce, "Wannan za ka
sha mai ne sannan kasa kati, kuma in ka kwantar
da hankalinka zan canja maka mota, zaka je
Makka. 11.... Sannan idan naga kana bin
umarnina zaka yi suna a aikin jarida fiye da duk
wani dan jarida da ka sani a kasar nan. Kai zaka
taka duk wani matsayi da dan jarida ke takawa".
ta sake nufoshi da tausasa murya. "In kabi yanda
nace ba kai ba sake kwana a talauci..." Ya
katseta da fadin, "In naki fa?" Ta hade rai tare da
zuba mishi ido, "Shima kallonta yake, sai a
lokacin ya ga tsufanta ya bayyana. Ta juya mishi
baya tana 'yar tafiya, sannan ta ce "Am sorry to
say". Ta juya ta dube shi "Za ka mutu". Gabanshi
ya fadi, amma sai ya yi karfin hali ya ce "In na
mutu sai me? Dama can mutuwa zan yi ko ba ki
kashe ni ba. Kuma ni na san ba zan wuce iyakar
ajalina ba, murnata daya zaki sauke min nauyin
zunubaina". Ta matso kusa da shi "Ka san
matasa nawa ke shiga malamai kawai don su yi
hulda da ni? In ka dade muna hulda shi ne muyi
wata biyar, sau daya na rike saurayi har tsawon
shekara daya don yana da hankali". A zuciyar
Abba ya ce "In fa na daka ta matar nan zan mutu
ban auri Ummi ba. Sannan ba Allah a ranta bare
taji nasiha, yanzu bari yabi ta hikima". Ya ce,
"Saboda me suke shiga malamai don suyi hulda
da ke? Sannan daman duniya tasan ki kina
haka?" Ta ce, "Ko kusa, sun sanni a Hajiya Nina
sai in mutum ya zo ya ganni, in ya sanni to in bai
sanni ba duk daya. Sudai burinsu kudin". 12......
Abba ya ce, "Nikam ba zan iya wannan huldar
ba". Ta ce, "Kada ka bari taurin kai yaja ka
nadama irin wadda waninka ya ta6a yi. In kana
da sha'awa in baka labarinsa don ya zamar maka
Ishara". Shirun da Abba ya yi shi yasa ta ci gaba,
domin alamar yana son ji kenan. Da a ce zan fadi
sunanshi zaka sanshi, wani malami daga cikin
Malaman garin nan, haka nan yanda na ganka a
TV kana labarai na kwadaita da kai, shima haka
na ganshi a TV yana wa'azi kuma zuciyata ta
yaba. Na neme shi ya zo kuma shi na fada masa
ni ce Zabba'u ban 6oye masa ba. Sai dai nuna
masa nai aikin rabon zakka zan ba shi, ma'ana
kudi ne masu yawa ban san yadda zan fidda
musu zakka ba. Da jin haka sai ya taho, nan
dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da
maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa
masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke
so ba. Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba,
shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi
guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure
ne ya ce zai gudu. Don gidan nan duk masu tsaro
ne har da ma layin gaba daya. Da sauri za a
kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi
kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka
kwana ciki. Domin duk a hannunmu suke, amma
Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya
min shame-shame zai mutu don yunwa. Ba arziki
na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan
karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa
shi a daki. Nasa Malamina ya karasa min shi,
sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan
cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya
kare a nan. To dama iyalanshi suna ta nemanshi
an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu
ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu
a cikin garin nan da ma wajen shi". CIKI book 3 part 3
ZURFIN CIKI book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24
Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare,
Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi
ne ya fara baki abinci a baki. 20..... Watanki
hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu,
Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana.
Lah, goyo? In ji Ummi. Umma ta ce, "Goyo sosai
kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in
naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku
yanzun sai in ta mamaki. Don tun ba ki fita a
tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata
hudu ba, ki ka tantance muryarshi. Haka nan
sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya. Abba
yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da
tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki
Ummi. In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to
sai da wayo da dabara. Ke har an kai lokacin da
kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in
ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki
wakar da yake miki. Ummin Abba da Alhaji,
Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki
dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break
dinsa zai debo miki tsaraba. Umma na bada tarihi
Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin
yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa
lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi
tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka
yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare
kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in
baki nono". Wata sabuwar kauna da so Ummi taji
ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido,
ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya
ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki
ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin
daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce
"Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne,
kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji". Ummi
ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba?
Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama,
suka amsa. Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya
faru da kai? Nan ya warware musu komai, suka
yi ta al'jabi. Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka
mata suka maida aure ba a bakin komai ba?"
Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z
aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka,
don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba
to can gabanta hadu da mai tona ta. Su Alhaji
suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da
jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga
dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda". Abba ya
ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin
aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda
dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai
ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba".
Suka ce Amin. 21... Ranar su Alhaji a tsakar gida
suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take
yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin
da aka bata. Ashe har yanzu Ya Abba na sonta,
Allah ya sa haka har yanzun. Sai kusan sha daya
Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida. Abba ya ji
dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi
suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta
ce, "Ka gaida 'yan gidan". Ya ce "Za su ji, har ya
kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a
kara sace shi fa, duk suka sa dariya". Abba ya
dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur
kuwa? Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba
shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar
galan na fita". Alhaji ya ce, "Na shigo da mai
dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake
cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi
'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a
Allah zai kare ni. Yau kam Ummi ta dade bata ga
daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau.
Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta
fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai
sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin
karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli
matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce,
"Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk
lokacin da na ganka sai gabana ya fadi,
musamman in kazo min da jarida". Yayi 'yar
dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah
Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in
da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan
sako ne. Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da
ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama,
hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan
jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi? Ta
soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har
ta gama. Kafa kurum take karkadawa tana
tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma
duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba. Amma duk
da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga
manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta
kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta
danna kira. 22.... Jim kadan aka daga ta ce,
"Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da
Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba
lau ba, kana ji? Ina yaron da nake baka labari
dan jarida? Ya ce, Naji. Ta ci gaba, Yaron nan
kaga yanda ya yayata ni a duniya? Sai na koya
mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma
ki ka ce sunanshi? Ta ce Idris, ya ce To zan kira
ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai
na gama bincikena duka. Ta ce an gama. Sintiri
tayi ta yi tsakanin dargajejen falonta zuwa
barandar shakatawarta, lokacin da taji rurin
wayarta tayi tsammanin Malamin ne, sai data
duba taga Aminiyarta ce Haiya Attine. Ta daga da
cewa, "Hello Attinen bishasha ya aka yi ne? Ta
ce, Zabba haka kwallon dan iskan yaron nan zai
miki? Ta ce, Hum! Ke dai bari Aminiyata, yanzun
nan na gama karantawa a jarida ban ma san
hukuncin da zan yanke ma yaron nan ba. Attine
ta ce, sa su Adda su tura shi Jami'ar mi'kakku
mana. Hajiya Zabba'u ta ce, "Ai kuma na riga na
kira Teacher ya ce in saurare shi". Attine ta ce,
"Eh to kin yi dabara ma, kya iya sa Teacher din
ma ya tura ba tare da an zargi kowa ba". Hajiya
Zabba ta ce, "Kin san jami'an tsaro suna cikin
maganar tsundum! Don haka dole in yi taka tsan-
tsan, guri daya yaron ya yi min kyan kai, da bai
fada ma duniya Zabba'u ita ce Nina ba." Attine ta
ce "Eh yayi wannan adalcin, yanzun bari muji ta
bakin Teacher". 23.... Shikam Malamin duk
lamura sun kasa masa daidai, sai kusan karfe uku
saura, sannan ya kira ta da rawar jiki ta dauka.
Ya ce, Hajiya? Ta ce, Na'am ya ce ki tattara ta
batun yaron nan ki watsar domin yanda naga
al'amuran to fa in mun matsa ba zamu kai labari
ba. Haka nan allura zata tono garma game da
damuwar malamin nan, sannan asirinki zai tonu a
gurin maigidanki. Tsaki taja don maigidana
Malam nasha fada maka ban 'ki ya ji ba, tunda
shi ne sanadin komai, tafiya kullum daga waccan
kasa zuwa waccan, kullum cikin bakin yawon
neman kudi. Sam baya biya mini bukatata ba
dole in nema ba? Yarana biyu cal a duniya duk
sun yi aure su ne kawai zan ji kunyar su sani,
don haka in zai yiwu ka sa Aljanu su tsotse min
jinin matsiyaci. Malam ya ce, "Ba zai yiwu ba, ina
ce tun lokacin da ki ka zo min da batunshi kafin
ma ki sa a dauko miki shi sai d ana fada miki
yaron yana da kariyar da take kare shi daga
Ubangiji. Yaron ma'abocin kyautata Sallah ne,
tare da yin Azkar, yana da makarin da Aljanu ba
za su iya tunkararshi ba... Dakata Malam, ta
katse si duk addu'arshi ya kai Malam ne, kuma
muka ci nasara a kanshi? Ya ce kila shi Malamin
kwananshi ya kare dama ke ce sila shi ko
wannan da sauran shan ruwansa. Ta ce, "Kai ne
sila dai daina jingina min mutuwarsa, ya ce ko
kin ki dole ki dauki nauyin zunubin mutuwar
Malam". Yanzun kuma ta wannan sai ki wamu
wani don ni ba zan matsa lamba a kan al'amarin
da Aljanu suka nuna tsoronsu ba, tsaki taja
sannan ta kashe wayar. Har gari ya waye ba ta
daina tunani ba, haka nan bata yanke matsaya
ba. Gidan Aminiyarta Attine bishsha ta nufa, sun
tattauna sosai sannan suka bukaci sukai koken
ga wasu Malaman. Sai dai guri uku zancan iri
daya ne, wato ta bar shi kawai, yayin da guri
biyu suma zancan su iri daya ne, sun ce zata ci
sa'ar kashe shi amma asirinta zai tonu zata rasa
ran 'yarta daya kuma zai yiwu tayi zaman Jarun.
Ta ce, "Wannan akwai shegen yaro, shi yasa da
na ce zan sa Aljanu su dauko shi ya ce min yana
da makaminsu? Daga karshe ta ce na bar shi
mara rabo". Attine ta ce da dai yafi shi yasa tun
farko in naga wanda zai ja min aji ni ke watsi da
shi in nemi wani. Kai jama'a sai kace aikin Allah
menene amfanin zinar ma da har ake shiga
Bokaye dominta? Allah ka tsare mana Imaninmu,
amin. 12 24.... Ummi tana zaune zata wanke 'yan
kayanta na ciki, ta zubo omon cikin ruwa tana
faman karkadawa, tana 'yar wakar da ke sata
nishadi. Sam ba ta ji sallamar Abba ba, yana
jingine yana kallonta, tana fadin, Akwai wanda na
ke so, amma kunya naso, ya wanke ni da soso
dan Yayana. Ta tsoma sikyat dinta da fant da
'yan bireziyoyinta farare ne ta soma cudawa tana
maimaita wannan baitin wakar, shi kadai ta iya.
A jikinta taji cewa ana kallonta, ta waiwaya da
sauri, idanunta tsaf cikin na Abba, sai ta samu
kanta da sunne fuskarta cikin cinyoyi. Ya ce,
"Kunyata ki ke ji ne Ummi?" Ta dago da dan
murmushi, "Sannu da zuwa Yaya Abba". Ya ce,
"Yauwa dama kin iya waka?" Tsohuwa daga daki
ta cafke, tun da ta samu wannan wakar sai ka ce
me hadda, kullum Abba ya isa kofar Tsohuwa
suka gaisa. Ya dawo kofar Umma yana tabayarta.
Ummi ta ce, "Taje Hotoro sunan kanwar Umman
Bashir da ta haihu, ya manta fa matarshi ma ta
na can, Tsohuwa ta fito tana cewa, ai Ummanku
ta juri wulakanci. Waccan haihuwar da Zilai
kanwar Sahura tayi tas a ka zageta a gidan
sunan, amma yau ta koma. Abba ya ce, "Ummata
tayi nisa a zumunci, Allah zai bata lada" Tsohuwa
ta ce, "Ai sai tayi ta yi, in dai shisshigi ne ba
kwarjini". Ta dubi Ummi, wai wankin me ki ke yi
ne har yanzun ina nan ina jira ki yanke min
farce". Ta hango kayan Ummi na daura ta ce,
"Kai ni wannan zamani naku yana bani mamaki,
ace 'yammata suna saka rigar mama? Kunya ta
cika Ummi saboda Abba da ke gurin. 25.... Abba
ya ce, "Kin ji tsohuwa, lokacinku da namu daya
ne? Ku lokacinku kai bai waye ba, ta aje 'yar
kujerarta ta zauna. Tir da wannan wayewar taku
ta zamani, yarinya ta fadi a gaban iyayenta har
ta shiga sa tara mama bata kama dakin kanta
ba? Mu kuwa da wata ma ba sai tayi haihuwa
goma ba ma ta sa ran mama ba. Abba dariya ta
ishe shi yayin da Ummi kunya ta hanata shanya
kayan ta matse ta aje. Abba ya ce, "Yanzun
Ummi har wani girma tayi, shekara sha takwas
kurum ce fa, bata ma cika ba. Ta ce "Mu lokacin
sha biyu sha daya yarinya ta kama dakinta.
Ummi ta zanua ta soma yanke ma Tsohuwa
'kumba, tana cewa To dai nima na kusan tafiya in
huta gorinki. Abba ya matso, "Ummi don Allah in
tambaye ki mana? Ta tsaya da yanke 'kunbar
tana kallonshi, ya maimaita tambayar da gira ta
bashi amsa ya ce kina ko son wannan Sahabin?
Ta maida kanta ga yankan 'kunbar duk jikinta da
hannunta suna dan rawa, a zuciyarta ta ce, "Kai
ne kadai zuciyata ke so, amma a fili sai ta ce,
Um, ya ce Yaya hausar um?" Tayi kokarin
saisaita hawayenta, sannan ta ce Eh, jikinshi yayi
lakwas, Tsohuwa ta ce, "Zancan banza, in bata
sonshi zaka daga batun auren ne?" Ai ko tana so
ko bata so tunda ta kawo shi zance ya kare, ka ji
mai sunan Malam da zancen wofi. Ya ce,
"Tsohuwa ni fa ba wani abu na ce ba, kin ga ma
dai bari in tafi abina. Ummi ina Azimi yau, zan zo
in yi buda baki anjima. Ta ce, "To." Tsohuwa ta
ce, "Wai kai ba ka da gidan mata ne kullum kana
la'ke a nan? Tsoron ta ka ke ji ne da zaka kasa
lankwasata ta yi maka girki?" Ya ce, "Na nan
nake son ci Ummi kam tana can duniyar tunani
tana tambayar kanta shi kenan ta rasa Abbanta?
Son da da yayi mata da ca dama ba na aure ba
ne, na 'yan uwantaka ne? Kai ko dai ta fito ta ce
Abba take so, gaskiya ita fa Sahabi ba sonsa
take ba. Kusan wata daya kenan rabon da ya
samu biyan bukata daga matarsa, don gaskiya
baya iya zuwa dakinta saboda kazanta da kuma
datti da wari da zarni da 'karni ba za su bar shi
ya samu cikakkiyar biyan bukata ba. In ta zo
dakinshi ma jikinta tashi yake, a haka yake
maneji, amma in iskancinta ya motsa har yanga
take mishi (Mtsw! Allah rabamu da kazaman
Mata). Shi kuma yana da wani hali, duk yanda ya
matsu in har ya nuna mata bukatarshi ta 'ki sai
ya hakura ya roki Allah ya shiryeta, shi kuma ya
kare shi da fadawa sharrin zina. 26.... Bai zaginta
ko ya ce zai nuna mata karfin shi, ko ya ce zai
tsaya rokonta, shi yasa yake yawan yin Azumi.
Ummi ta ce, "Umma ki kawo kudi in siyo kwai in
soya ma Yaya Abba doya, ya ce zai zo shan
ruwa. Ta ce, "To je ki kasan filo ki dauko, amma
fa sai kin yi azama don an kusa kiran sallah. Ta
ce, "Ai na dafa ruwan shayi, sannan na masa
kunun tsamiya, doyar ce kawai, ta ce "To sai da
ta gama komai sannan tayi wanka tayi sallah.
Riga da siket na leshi tasa fari tas, bata damu da
yin fenti da dare ba amma yau tayi ta feshe
jikinta da turare wanda shi ne ya sai mata.
Sallamarshi ta jiyo suna

Please Login or Register in order to submit comment