Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai iske Kabir ya isar mishi da sakon uwarshi..................
[5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 29*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




......... Aguje fulani ta sheko akan titin tamkar zata tashi sama inda ta wuce wata hamshakiyar mota wadda ta rasa gano inda ta santa. Atake ta gano motar gayen Nan ce da yayi Mata Rashin mutunci

Ai kuwa da sauri tayo rubos ta dawo inda taga ya faka motar shi zai siyi tuffa da inubi
Ta fito tana sanye katon gilashin ido Wanda ya mamaye fiye da Rabin fuskar ta tana sanye da doguwar Riga ta yadin material lemon green anyi mishi adon fulawowi ja da Baki tayi kyau sosai ta yafa mayafi Dan karami Wanda Bai rufe Mata dogon goshinta ba Wanda iska ke kadawa tamkar kwallo

Kai tsaye ta tunkar me kayan fruit din tana takawa tamkar me tafiya akan kwai.
"Malam bani aybar Nan ta dari biyar ta fada tana Mika mishi gudar naira dubu
Ya karba Yana saka Mata aleda ta Ciro guda biyu tana barewa inda Anwar ke kallonta Yana mamakin yadda take mishi kallon da wa ka shigo garin Abuja? In har ya fahimta dai dai ma sai da yaga bakinta na motsi duk da baiji abinda take fada ba Amma yayi sa ar jiyo tsakin da tayi

Me fruit din ya Miko Mata cikon dari biyar dinta ta dubeshi ba tare da ta karba ba.
Ta Nuno Anwar dake zaune cikin mota Yana kallon ta
"Ka bawa wancan matsiyacin sadaka don nasan irinmu irinmu ya ke jira yayi maula ta fada dai dai da ta jefa mishi bawon ayabar afuskar shi

Daya daga cikin masu biye dashi don bashi kulawa wato body guard dinshi da ya kula da abinda tayiwa uban gidan su ya daga hannu zai sharara Mata Mari Amma da sauri Anwar ya dakatar dashi.

"Da dai ka barshi ya mareni ya Maro ajalin shi jaki da shi Yana biye da jaki Dan uwanshi,

Ta bude motar ta tashige ta figeta aguje ta hau titi inda wani hamshaki da abin ya faru akan idon shi yaji ya mutu da son fulani don shi Allah yayi shi da son mace me tsiwa tana burgeshi don haka da sauri ya shiga tashi motar ya rufa Mata baya inda suka bar Anwar Yana mamakin wannan yarinya daga karshe dai yayi murmushi ya siyi abinda ya kawoshi ya wuce gida

Sister mero tayi sallama gidan izzatu tana murmushi inda izzatu ta fito tana nunata da yatsa , "Ina fatan kinyo wankan gawa kin Kuma taho da likkafanin ki don Ina me tabbatar Miki dab kike da kushewa..........

"Wai Ni na mutu yanzu izzatu? Kai bana zaton Koda kuwa zanyi ido hudu da mutuwar to Zan roki tayi min alfarma in gama dake tukuna ta dauke Ni , ai Ni in kin ganni lahira kaini akai don haka SHIGA ki fito kudi nazo karba.........

"Saboda gyatumin ki ya bani ajiya? "Ko daya gyatumi na Bai Baki ajiya ba Ni dai na Baki ajiya..........
"A gidan ubanwa Kika bani ajiyar? Ke mero ki fita idona wallahi na rantse miki in Kika kaini karshe Zan iya murde Miki wuya ki mutu murus !

"To Bismillah ai ke da kanki kinsan Ina da kaddara a wurinki itace humaira inda kikayi kuskure da tun farko kikace Lada Zaki biyani da cewa kikayi siyar Miki da humairar zanyi da ban bibiye ki don haka ladar aikina har in mutu ba Zan Daina karbarta daga gareki ba don haka dauko min kudi in Kama gabana idan Kuma Zaki iya siyenta ayanzu to muyi ciniki ki bani milyon dari in bar Miki ita har abada idan Kuma ba Zaki iya ba to Zan Rika zuwa ina karbar Yar milyon biyu ko uku idan bukatar hakan ta taso..........

Tasss! Ta dauke meron da mari....
Mero ta dubeta cikin mamaki na karfin halin marinta
"Kika mare Ni izzatu?......
"So ma nake kice Zaki Rama Marin kiga yadda ake hawa hanyar lahira

"Uhum bama Zan Rama ba saboda ke din jakata ce ko ince asusuna don haka dauko min in wuce milyon biyu da dubu dari biyar nake so yau don Ina Jin tausayin ki da uku zance ki bani......

Karar motar fulani da izzatu ta jiyo Wanda ya alamta Mata dawowar ta yasa taga Bari kawai ta sallami izzatu don Bata son ta fahimci komai don haka ta rubuta wa sister mero cek ta Bata Wanda yayi daidai da shigowar fulanin wadda ko kallon mero batayi ba inda meron ke Mata kallon tayi saurin girma

"Momy na dawo cewar fulani dake Hawa Kan bene saboda taga momy tayi bakuwa . "To sannu da dawowa.

"Sai ki tashi ki tafi Allah Ubangiji yasa tsautsayi ko kaddara su sake dawo dake Nan gidan inda Zaki Gane kinyi kuskuren shigowa duniya arashin dace

Mero ta Mike tana murmushi
"To na gode uwar dakina a huta lafiya ta fice daga gidan inda izzatu ta rakota da wata matsiyaciyar harara
A kofar fitowa gidan sister mero taga hamshakiyar motar me daukar hankali tabita da kallo inda shi Kuma na cikin motar ya fito Yana tsaida sister mero ta tsaya suka gaisa inda yake sanar da ita wata yarinya ya biyo wadda ta shiga gidan yanzu .
Atake mero ta Gane humaira yake magana

"Allah sarki ai ya ta ce ince dai ba wani Abu tayi maka ba? "A no Babu abinda tayi min kawai na biyota ne don Allah ya jarabeni da kaunar ta ya fada Yana rusunawa don yaji tace itace uwarta

"Karka damu Alh sai dai ka Kara hakuri don Bata tsayawa da samari Kuma ma ubanta ya ce ba yanzu zaiyi Mata aure ba Amma tunda Allah Ubangiji ya kawoka bani lambar ka sai muyi magana don Nan din ba gidan mu bane munzo wata hidima ne da an Kare zamu koma gida in yaso sai muyi magana

"Ok to mama Babu matsala ya bude motar ya dauko Mata compliment card din shi ya Bata inda mero ta ga suna shi honorable bello Rimaye Bata tsinke da lamarin ba Sai da taga kyautar gieman da yayi Mata suka Rabu akan zasuyi waya ya tafi Yana Jin lallai yayi sa a

Mero tayi murmushi
"Kai lallai abar Allah da lamarin sa wannan yarinya uwarta ta iya haihuwa Ni Kuma na karbi haihuwar ta a sa a yanzune wasan mu da izzatu zai dauko sabon salon da zai kayatar da me kallo da saurare................
[5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 30*
*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*





..........Tunda Kabir yayi kwangilar Nan har yau ba a Kuma kiranshi an bashi wata kwangilar ba inda akayi ta cin burin kwangilar hako Sola da akace za ayi a kauyuka biyar da yake zaton zaiyi har Yana cin buri hatta izzatu ma ta ci nata burin inda Yar lele humaira fulani ma ta shigar da tata bukatar ta son asauya Mata mota wadda ta gani a tashar MBC fitowar shekarar 2019 inda Kuma akayi Mata alkawarin da anyi kwangilar an gama za a yi Mata oder ta sai dai me? Shiru ta bashi Labari inda ya Gane lallai an maida shi aljihun baya koma angama dashi

A fusace ya zaro wayar shi zai Kira eng AK inda izzatu ta dakatar dashi
'zuwa ya kamata kayi ba Kiran waya ba na lura wannan mutumin so yake yaga bayan mu Kabir idan ba sako gambo mafiyas atafiyar nayi ba ba zai saurara Mana ba.

Da sauri ya tashi mota ya nufi gidan eng AK don suyita ta Kare

Eng ya kwashi iyalanshi suka fice country Moll inda suke ta jidar abinda ya kawo su duk da silar zuwan ummita ce wadda tacewa abbanta tana son zuwa don siyo biscuits da kayan makulashe inda shi Kuma ya kwaso su duka suka wuce don gaskiyar magana yanzu duniyar nayi dashi

Ummita da Mubarak da Ahmed da Fatima suka nufi wurin kayan kwalam suna ta jidar abinda suke so cikin sa a ya shigo don siyen makilin da wayar iPhone kawai sai idon shi ya fada kanta wani Abu ya daki zuciyar shi ya zuba Mata ido Yana kallon ta har Bai San lokacin da kafar shi ta taka ta Isa inda suke ba ya Kai hannu Kan abin takai hannu suka dire hannu alokaci daya inda tayi saurin duban shi shima ya dubeta sukayi kallon kuda atare inda yayi saurin Miko Mata abida ta Kai hannu tayi saurin Jan hannun kannenta suka bar shi rike da biscuits din Yana musu rakiya da ido inda ya saki baki Yana kallon su har suka fice inda yake tambayar kanshi Anya kuwa yayiwa kanshi adalci ace Yana amsa sunan kirista yace musulma yake so? Gambo mafiyas da yaji shirun shi tayi yawa ya kwado mishi Kira inda ya dauko abinda ya kawo shi ya fito Yana waiwayen ummita har dai gambo mafiyas ya kula da kallon da yakewa ummita ya faske keyar shi

"Lover boy kayo kamu ko kake zuba Mata ido?
Wilson yayi murmushi Bai tanka ba suka bar wurin

Lokacin da suka iso gida eng ya hango motar Kabir mashi afake inda ya Gane wurin shi yazo
Don haka ya cewa iyalan shi su shigs ciki zaiga bakon shi ya budewa Kabir falon da yake karbar Baki ya karrama shi da ruwa da lemu Yana mishi sannu da zuwa

"Ba ruwa ya kawoni Sha ba AK Jan kunnen ka nazoyi don na Gane Kaine ka ke kokarin gurgun Tani tun kafin ka Fara kwangila nake yi ba Kuma Zan yarda zuwan ka yasa ka kassara niba don haka ka janye jikinka in ko kaki ji to ba zaka ki gani ba

AK ya dubeshi Yana karanto hasbunallahu wa Ni imal wakil don yasan wannan mutum yadda ya fito Yana fada mishi hska to Babu abinda ba zai iya yi ba
"Kayi hakuri me gida Wallahi bani da laifi akan duk abinda kake zaton Ni nayi maka Wallahi ban da hannu Abu daya na sani ana fada Akan aikinka to Zan baka shawara ka gyara don ana fadin kana bada rata shiyasa aikin Babu nagarta wannan shi na sani Kuma me gida nifa kanenka ne komai ya samu bawa da sanin Allah Ni da Kai Babu Wanda yasan gobe sai Allah Ni ban Isa na tare Rabon ka ba duk inda ka shiga sai ka samoshi.........

"Bance kayi min wa azi ba so nake kawai kace ka Daina aikin kwangila har abada ba Wai wani makararren wa azinka Wanda na Saba ji ba.

"Gaskiya me gida ba zanyi maka karya ba don Bata cikin tsarins maganar gaskiya ba Zan iya barin kwangila ba tunda bani na tsara yinta Arayuwa ta ba Allah ne ya zano min ita don haka Ni ALHERIN Allah kawai nake roko ko da gwamnati ta daina yi Dani to zanyi ta mutanen dake can waje komai da lokacin da sa...........

"To shikenan tunda haka kace Amma kar kayi kuka Dani akan abinda zai sameka ba Wai don na rasa yadda zanyi bane yasa nake ta binka a a don in fita hakkin ka Amma tunda ka kawo taurin Kai sai ince zakaga abinda zai faru......

"Me gida ai Babu abinda zai faru sai ALHERI.................

"To shikenan tunda haka kace Ni na wuce
Ya Mike Bai ko yi mishi sallama ba ya fice inda AK ya soma karanto addu oin nema tsari ya koma cikin gida Yana fadawa lubabatu yadda sukayi da Kabir mashi kashe arna inda itama ta bashi shawarar suyi ADDU A itace kadai mafita Amma mutum a yau Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro.
"To Ubangiji yayi min katangar karfe da duk wani me sharri da abin cutarwa ta amsa da Allahumma ameen.

Afusace Kabir ya koma gida izzatu ta tarbeshi tana tambayar yadda sukayi da AK din ya Kuma zayyane Mata yadda sukayi inda tace

"Kaji ko ? Kaji irinta ko har ya dubeka ya fada maka Wai aikinka Babu nagarta? Duk yadda kake kallon lamarin da sauki bashi da sauki Kuma idan ba gambo mafiyas aka sako cikin tafiyar ba to sunanka ma ya kusa Daina motsawa..........

"Abinda ba zanyarda dashi ba kenan don haka maza ki Kira min gambon Nan yazo yayi min maganin wancan marar kunyar wato eng AK

Izzatu tayi murmushi ta jawo wayar ta ta dokawa gambo mafiyas Kira Kara biyu ya dauka...................
[5/22, 6:19 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 31*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




......... Izzatu ta jawo wayar ta ta dokawa gambo mafiyas Kira Kara biyu ya dauka
"Allah ya taimaki hajjyata in karaso ne?

"Kwarai kuwa gambo mafiyas maza kazo kayi min maganin wani tarnaki dake shirin konani taho da sauri don Allah.........
"Angama hajiya gani Nan zuwa...........
Minti talatin gambo mafiyas ya karaso inda Kabir ya dubeshi ya tabbatar da zai iya aikata kowane irin ta addancin
Yayi gaisuwa wurin Kabir inda izzatu take Kora mishi bayani

"Me Kaka so ayi mishi Kabir? Ga gambo Nan zai cika maka kowane irin aiki kake so don aikin shi Babu sabani bara kuskure fada mishi duk yadda kake so ayi mishi inma batar dashi kake so ayi nasan gambo mafiyas ba zai taba baka kunya ba.

Kabir ya dubi gambo mafiyas
"Gambo Ina so ayiwa eng AK abinda sunan shi zai Daina zagawa duniya inaso abatar min dashi ta yadda Zan dawo da duniya ta sabuwa tunda bayyanar shi ce take neman kaini kasa warwas

"Angama me gida bamu address din gidan shi yau din Nan zamu kaddamar mishi
Atake Kabir ya Basu address din gidan har da hoton shi sukayi sallama ya fito Yana cewa su saurare shi zasuji yadda abin zai kasance

Sai dai wani akasi da aka samu Aranar shine gambo mafiyas ya samu Kiran wani abokin shi dake Lagos Kan wata harkallar wadda za a yo wata SATA ta manyan kudi don haka ya bar aikin su izzatu ya shilla Lagos inda ya wakilta ya ranshi su Wilson da zarto wadanda suka horu da aiki suka Kuma kware Amma Wilson din ya fi su kwarewa shiyasa gambo mafiyas yafi ji dashi duk da kasancewar shi mabiyin addinin almasihu Amma sauran duk hausawa ne su hudu sai Wilson na cikon biyar duk suna aiki da gambo mafiyas inda ake bin dare afasa shaguna ko su haura gidaje suyo sata atakaice dai Yan fashi

Wilson ya yi shiri shida su zarto suka nufi gidan eng AK da son aikawa dashi kiyama don umarnin da aka Basu kenan

Suka kumayi sa a suka samu haurawa gidan eng a wani dare suka Kuma tadoshi shi da iyalan shi suna bukatar kudi ya Kuma dauko ya Basu inda cikin sa a idon Wilson ya fada Kan ummita dake sharar kuka akan atak da zarto yayi Mata agoshi

Sun rufe fuskokin su da face mask idon su kurum ake kallo inda ummita ta kula da kallon da yake mata shi Kuma atake ya tuno da ganin da yayi Mata a country mall da irin daukar da tayi mishi da mafarkan ta da yayi tayi har ya Rika zuwa country mall din Wai ko zai sake ganinta Amma ko me kama da ita Bai gani ba sai gashi Wai yau yazo har cikin gidan su da umarnin kashe mahaifin ta atake yaji zuciyar shi tashiga rawa ko babu komai ba zaiso abinda zai sakata zubar hawaye ba don haka ya yanke shawarar sama Mata farin ciki akasin cika umarnin da zai barta Cikin damuwa

Tsini Wanda ya yiwa eng AK atek da bindigar yake fadawa Wilson shifa zai cika aiki ne ko suyi su wuce

Da sauri Wilson din ya dakatar dashi inda yake fadin wrong address
Suka dubi juna inda Wilson din ke fadin su fice kawai da sauri sukayi gaba inda Wilson ya dauko jakar kudin da gwalagwalan su lubabatu da ummita da aka karbe ya zube musu agaban su Yana Basu hakuri ya dubi ummita ya huro Mata kiss ya wuce da sauri suka bar gidan ida zarto ya dauko wata jaka me dauke da kudi wadda yace Wai ba a shiga arziki afita haka Nan

Gambo mafiyas ya Kira Wilson da son yaji yadda aikin ya Kaya Amma Wilson ya sharara mishi karyar Wai wrong address ne aka bada
Kudin da zarto ya dauko su suka rage musu zafi inda gambon ke fadawa izzatu wrong address ne aka sami inda izzatu taketa yiwa gambo sababi Wai ya fara saka wasa a aikinshi in ko hakane gaskiya ba zasu daidaita ba inda yace ta Bari zai dawo Nan da sati guda shi zaiyi Mata aikin da kanshi don ta San Yana Nan da hatsabibancin shi da haka sukayi sallama tace tana sauraren shi Nan da sati dayan ...................
[5/22, 7:10 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 32*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




........Hajiya Mama tazo Jin abinda ya faru ga abdulkarim jikinta har Bari yake don Ubangiji ya hasko Mata lamarin amafarki inda gari na wayewa ta Kira abdulkarim take tambayar shi suna lafiya dai ko? Ya fada Mata suna lafiya sai dai abinda ya faru don haka hajiya Mama ko Karin kumallo batayi ba ta tashi direba ya kawo ta gidan AK

Dukan su suka zube gaban hajiyar tana tambayar su
"Basu dai taba kowa ba ko?
"Basu taba kowa ba hajiya hatta kudi da gwalagwalan da suka karba sun maido sai Yan Wanda ba za a rasa ba...................
"Alhamdulillah tunda dai Basu taba kowa ba sai mu dage da addua Ubangiji yakiyayeka dukkan sharri ya Dora ka Kan makiya suka amsa da ameen da haka hajiyar ta koma gida tana ADDUAR Allah ya Kare Mata danta.

Hon bello Rimaye ya soma budewa sister mero bakin aljihunshi akan son auren humaira fulani inda meron ke shirya yadda zata tunkari izzatu Amma acewar ta sai ta tatsi hon yadda Koda izzatu zata nemi kawo Mata wargi

Wilson kuwa ya kasa samun nutsuwa don muddin zai runtse idon shi to Babu shakka zai hango ummita bare kuma yace bacci zaiyi kaf burinshi da tanajin shi zai Kare ga mafarkin ummita abinda ya tabbatar sonta Bai Kama shi don ya sake shi ba yayi zaton abin nawasa ne amma ya Gane yafi karfin wasa

Gaba daya ya fice hayyacin shi har ya Daina fita ko Ina ya kwanta jinyar ciwon so
Zuciyoyin shi sukayi ta kawo mishi shawara bi da bi har dai ya yarda ya dauki shawarar karshe ta yaje kofar gidan su ummita ko da ganinta ne yayi ya rage radadin sonta
Ai kuwa ya Mike ya fice sai gashi kofar gidan su ya faka motar can gefe ya dawo nesa kadan da gidan ya zauna Yana zubawa kofar gidan ido

Zaman shi ko minti talatin ba ayi ba ta fito cikin motar ta tafice inda ya bi motar da kallo ko ba komai yaji sanyi tunda akalla dai ya hangota inda wata zuciyar ke fada mishi yabi bayan ta zuwa inda zataje ko ba komai zai Kuma ganin ta ai kuwa ya dauki motar yabi bayanta inda suka hadu a traffic wadda ta tsaida su ya juyo Yana kallon ta inda yaga tsantsar kwarjini da haiba inda ya tabbatar ita din me kyau ce

Jikinta ya Bata lallai ana kallon ta sai ta waigo inda idon su ya hadu yaji wani Abu me kama da Jan shock ya fizgeshi ita Kuma tana kallon shi ta tabbatar shine me kallon ta sai ta dauke kanta danjar ta Basu hannu suka wuce inda bisa Dole ya koma gida inda yakejin ya samu hanyar rage kewa

Da yamma ya fito da zummar siyo kayan shayi ya wuce ta kuki cafee inda ya hango ta tafito daga kukin rungume da takardu ta bude motar ta SHIGA ta ja ta nufi gida
Atake ya Gane kuki ta fito zuwa dazun me yuwa computer take karanta
Ya wuce abin shi itama ta wuce batare da tasan yanayi ba

Satin da gambo mafiyas ya dawo daga Lagos ya Kuma samo abin duniya Wanda suke karewa ga Matan banza da kayan maye don basa tsinana abin arziki don haka ya Isa gidan izzatu Yana zukar tabar iblis wiwi

Da sauri ta toshe hanci tana tofar da yawu
"Haba gambo meye haka zaka shigo min da wannan shegiyar tabar me warin Kashin jaki? Don Allah koma waje ka zuke abinka ko dadin me kukeji acikin zukar hayaki hayakinma irin wannan da ko dadin Shaka Babu?..........."yi hakuri hajiya kan ne in Babu hayaki fanko ne Rayuwa ta in Babu mandular Nan akwai damuwa har Rashin lafiya nake kwantawa idan ban busa ta ba

Ya murtsuke sauran ya saka aljihunshi
"Yauwa to haka dai yafi don har kaina ya soma juyawa Nima ka sakani kwalewar Dole

"Yauwa hajiya Ashe akasi aka samu wurin aiki?
"Ai shiyasa nafi yarda da aikin ka yanzu Yaya za ayi kenan?

Ki bar komai a hannu na hajjya Ina me tabbatar Miki Nan da Rana irin ta yau wancan mutumin ya SHIGA UKU ke dai ku tanadi kudi don kin San Ni bana tare da tsautsayi ko kuskure bare wani Abu Wai shi sabani.......

"Karka damu gambo idan aiki yayi kyau ma za a biyaka kudi lunki uku Kai dai baje basirar ka kayi aiki me shegen zafi don ka samu sallama me kyau....

"Angama hajiya bani sati guda Daya kacal zakiji mugun albishir da haka sukayi sallama ya fito ya Kama gabanshi inda izzatu ta Kira Kabir take sanar dashi yadda sukayi da gambo mafiyas yace yayi daidai Kuma zai biya gambon lunki hudu ma ko biyar matukar dai aikin shi yayi sanadin fakuwar eng AK

Cikar satin da gambo mafiyas ya diba yayi daidai da kammaluwar aikin shi inda ya Kira Kabir yace yaje wurin hukuma ya sanar da akwai wani da yake kisan yaran mutane yau ya kashe wata yarinya ya sako a motar shi don haka su tashi Jami ansu da binciken motocin mutane ta haka ne tarkon zai Kama eng AK.

Aikuwa atake Kabir mashi kashe arna ya Kira wayar D P O ya sanar dashi abinda gambo mafiyas ya sanar dashi inda Kuma suka tashi Jami ansu aka soma checking point Wanda duk motar da zataje ko tazo sai me ita ya fito ya bude but sun caje komai kafin su bashi izinin tafiya

Bawan Allah eng abdukarim ya taho batare da sanin mugun qullin da aka hada mishi ba ya taho inda ya iske dogon layin na checking point Wanda ake ta bincike motoci shima ya bi layi batare da sanin shi ake son ganin baya ba ba Kuma Wai idan yajuya zaiyi tafiya ba. A a ganin baya na har abada inda ake son kasa ta rufe idanun shi................

Ubangiji kayi Mana sutura kar ka Bari makiya suga bayanmu 🤔
[5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 33*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




........Sannu ahankali akazo Kan eng AK Wanda ke kallon yadda ake binciken motocin mutane har akazo gareshi

"Ranka ya Dade muna son duba cikin motarka idan Babu damuwa.......

"A a Babu komai yallabai Bismillah ya fito Yana daga musu cikin motar suka bincike ba su samu komai ba sukace ya bude musu but

Ya kewayo ya soma kokarin bude but din Amma wani abun mamaki tamkar an sakawa

Please Login or Register in order to submit comment