Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motar ya fito har ta shige
Ya kasa tsaye da zaune zuciyar shi na kawo mishi shawarwari akan kawai ya jira ta fito in yaso ko mayar da its gidane sai yayi Aiko ya dasa zaman jira har uku na maraice ta fito ta soma tafiya inda ya kula tamkar Bata da lafiya

Ta gota shi kadan ya ga ta dafe bishiya ta rike kanta Wanda alamu suka nuna ciwo yake Mata inda dabara ta fado mishi ya tashi motar ya karaso gareta Yana fitowa

Ya tunkaro ta ta zuba mishi ido kallo daya ta Gane shine Wanda ya tsura Mata idon Nan a country mall

Yayi Mata sallama cikin hausar shi da Bata fita Bata amsa ba ta dai dubeshi
"Sannu fa Naga kamar kina neman taimako na?......
Tayi saurin Kada mishi kanta
"No nagode zaka iya tafiya.
"Kiyi hakuri nasan inda zakije akwai nisa kizo na kaiki Naga kamar kina headache ne ......

"Nagode sosai Zan iya komawa ba damuwa...........
"Kiyi min alfarma ko ta kaiki gida ne tunda har Baki da lafiya..........
"Idan aka ganni a motarka nace me? "Ka ganka kuwa ? "Taimako wani abune da addinin mu ya koyar damu ga mabiyan sa shin kana daga mabiyan ne da zaka taimakeni?

"To duhu da haske basa tarayya a wuri Daya Dole daya ke bawa Daya wuri idan haske ya bayyana to duhu yayewa yake don haka na gode da taimakon ka gareni

"Na sani amma haka Nan naji Ina son taimakon ki tunda muma namu addinin ya koyar damu taimakon Kuma Bai saka kiyayya ga sauran addinan ba indai ba naku adfinin ya saka muku kiyayyar sauran addinan ba. Kiyi hakuri ki shigo na saukeki nayi Miki alkawarin Babu cuta tsakanin mu haka kawai nake son taimakon ki

Azahiri ita kanta tana bukatar taimakon don Jin kanta take tamkar zai tarwatse Dole ma ta nemi abinda zai kaita gida don Bata sababa ga kuma yunwa da takeji wadda idan akasa tace zata tafi to ko shakka Babu sai dai akwashe ta amika gidan don haka ta sallama ta shiga motar yaja suka iso gida ya sauketa ya Miko Mata fakitin maganin ciwon Kai me tsadar gaske ta karba tana godiya

Tun daga wannan Rana Bai Kara shiga cikin lamarin ta ba sai dai zai labe ya kalleta ya more ya koma gida inda kusan kullum sai yazo kuki internet cafee ya ganta batare da ya Bari ta ganshi ba

Hajiya sabuwa first lady matar Mr President take sanar da Mr President din maganar da ta taba fada mishi ta samowa Anwar auren diyar kawarta matar soja wato kudusiyya ta taso don haka atura mutane su nema mishi auren

Ya dubeta Yana murmushi
"Kice auren gata za ayiwa Anwar ba na fada Miki Yar gidan Kabir mashi Nima na nema mishi ba? Ta kwabe Baki da zaka yarda sai ince ka bar maganar Yar gidan Kabir mashi kudusiyya macece daya tamkar da goma.........
"Ba zanyi magana biyu ba tunda dai kema kin samo mishi wata sai ahada mishi biyu don haka itama Yar gidan Kabir mashi din sai muyi magana kawai

Wannan abin ya Bata ran haj sabuwa don tasan idan matar soja taji haka ba zata yarda ba Amma kome kenan zasu San yadda sukayi suka lalata Shirin Yar gidan Kabir din don kudusiyya kawai suke son tayi Rayuwa a gidan Anwar din baza ta tabs Zama da kishiya ba bare har ta Zama Bora

Sai dai da Anwar din ya shigo hajiya sabuwa ke mishi maganar kudusiyya da zaba mishi ita da tayi a matsayyin matar aure yayi saurin tareta.....

"Bana son ta hajiya ku barni na zabo matar da Nike so da kaina tunda Kuma zabar kanku kukayi ke da dady ba hada ku akayi ba.......

"Kayi karya ka bani kunya Wallahi Anwar Dole ne ka auri kudusiyya.....

'to shikenan haj duk abinda ya samu Yar mutane kar kiyi kuka da kowa......
Ya fice ya barta sake da Baki...............
[5/24, 7:50 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 38*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




........Anwar ya fito sukayi kicibus da mahaifin shi ya zube Yana rattaba mishi abinda hajiya sabuwa ta fada mishi akan Wai ta yi mishi Mata da kudusiyya wadda shi atsarin shi kudusiyya batayi mishi ba. Mr President yayi murmushi

"In Banda abinka Anwar meye na damuwa don ta zabo maka matar girma ? Nima fa nayi nufin Yi maka gata kanaji?
"Eh inaji dady.
Yauwa ai kasan gidan Alh Kabir mashi ko? Eh gaskiya kamar na sani Amma dai akwatanta min . Yayi mishi kwatance ya Kuma Gane inda ya bashi rafar dubu hamsin hamsin guda biyu ta dubu dari yace idan sun gama magana ya bada amatsayin kyauta
Ya dubi uban cikin Rashin Gane abinda yake nufi har dai ya tambaya

"Dady wa za a ba wannan kudin shi alh Kabir mashi din?

"A a kaje Zan kirashi zamuyi magana bashi zaka bawa ba ita wadda zaku yi maganar da ita zaka bawa amatsayin kyautar ka.
Ba don ya Gane ba ya taho don har ga Allah shi Bai kawo komai aranshi ba yayi nasarar Gane gidan ya Kuma tura me gadin yayi mishi sallama da alh Kabir
Atare suka iso inda Kabir kewa Anwar sannu da zuwa ya sauke shi a wurin da yake karbar Baki suka gaisa inda Anwar din yake sanar dashi dady ne ya turo shi

"Eh ai ya kirani bayan ka taho Bari in turo maka ita. Ya Mike ya bar Anwar sake da Baki Yana maimaita kalmar Bari in turo maka ita, to itawa za a turo mishi? Sai ya zuba ido kowacece itan

Fulani na zaune cikin ado da kwalliya tamkar me shiri fita party ta zubawa TV ido tana kallon India Wanda take son sanar da dadyn ta tana izuwa India don garin na burgeta sai Kuma gashi ya shigo Yana kiranta

Ta dago da sauri "gani dady
Yauwa dama bakone gareki Yana can masaukin Baki kije ku gaisa..........
"Bako Kuma dady? Ni yace maka yake nema?
Gaskiya dady bani yake nema ba sai dai in wrong address ya samu don Ni ban ba kowa address Dina ba.......

"Eh shi wannan din ma ba cewa ke Kika bashi ba Ni nace mishi yazo ku daidaita ke dai jeki idan kin dawo zamuyi magana.
Ta motse fuska don Sam acewar ta Bata ga mijin Aure a yanzu ba sai gashi Kuma ana son shigs Rayuwar ta

Tasa me aikin su talatu ta biyota da ruwa da lemu inda ta yi gaba don zuwa duba wannan marar kunyar da aka jajubo Mata

Ta taho tamkar tana Jin tausayin kasar fuskar ta murtuk Wai don kar yaga hakoranta ta shigo Babu ko sallama inda idanun su suka hadu su duka tamkar wuta taja su suka ji bugun zuciya Atare inda ta zauna tana auno mishi harara tamkar idanunta zasu fado inda talatun ta shigo dauke da tire Wanda ta jero ruwa da lemu tana Shirin ajewa humaira ta doko Mata tsawa.....

"Koma da ruwan Nan talatu wannan ba bako bane abokin Adawa ne.....

Talatu tayi dabar dabar don Bata fahimta ba inda kuma humaira ta Kuma daka Mata tsawar
"Nace ki koma dashi ko bakiji ba?
Da sauri talatu ta dauki tiren ta koma ciki inda ta fusknce shi shima Yana mamaki abinda suke nufi da turoshi inda atake ya gano gatan da dadyn yace yayi nufin yi mishi har yayi murmushi don yasan ba zasu taba daidaita wa da wannan marar mutuncin ba

Murmushin shi ya Bata haushi. "Au harma na Zama abin dariya agareka ?
"Uban me kazo yi agidan mu? Ko Nan ma kazo ne don ka sake bawa Yan sanda damar su kulle Ni ? Ta fada tana Kada kafa alamar masifa na Shirin tashi

Ya Kuma yin murmushi Wanda ke kuleta da haushi da takaici
"Kiyi hakuri Ranki ya dade............
"Kai bari fa in gaya maka dama inajiran Allah yasake hadamu don in Rama abinda kayi min
To Ni nan da kake gani wallahi uban kuturu ma ya Yi kadan bare na makaho da ba gani yake ba duk uban da ya daure maka.....

Ya gaji da Jin zagin da take mishi don Babu abinda ya tsana a Rayuwar shi irin zagi don haka ya cire hannu ya tsinke ta da Mari Marin da sai da taga giccin koriyar wuta

"Nafi karfin zagi agareki ko Zan zagu ba dai ga irin ki ba jahila marar tsinkaye wallahi ba Irina Mata ke zagi ba nafi zagi ga irinki dabba dake Kuma in har kece ake Shirin abinda aka shirya zanyi maraba da hakan ko don in koya Miki tarbiyar da uwarki Bata koya Miki ba
Ya Mike afusace ya watso Mata kudin da dadyn ya bashi ya Bata
"Gasu Nan ki kaiwa Kabir mashi don saboda su yayi tallar ki inda ya San zai samesu Ashe ke da uban naki duk nema kuke akarkashi na to ku biyo Ni Zan baku na cin abinci

Tana dafe da inda ya zabga Mata Mari har ya fice ta kasa cewa komai Akan cin fuskar da yayi mata
Me yake sanar da ita? Da gaskene tallarta dadyn yayi? Eh ai in Bata manta ba dadyn ya fada Mata shi ya turo shi don haka ta tabbata sai dai tanajin ba abune me yuwa ba matukar Kuma akace hakan sai ya yuwu to za ahaife da marar ido

Ta kwashe kudin ta nufi cikin gidan inda take ganin karfin halin shi na zuwa har cikin gidan su ya zabga Mata Mari

Kabir ya tareta
"Yaya Yar dady Yaya Kika ganshi ? Yayi Miki?
"Wai dady baka San shine yayi min wulakanci har sau uku ba?
"To dady bana son shi don fansa ma Zan dauka akanshi ba Kuma Zan kyale ba don bashi da mutunci to nima Zan gwada mishi bani da mutunci.....

"A a karkiyi haka Anwar Yana da kirki Baki fahimce shi bane don haka dama fada Miki ne bamuyi Anwar shine mijin da aka tsayar Miki Nan da lokaci kadan za ayi biki.....................
[5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 39*


*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




........."A a dady wallahi bana son sa don ya gama saka min kiyayyar sa idan kuma kace Dole sai na aure shi to wallahi Zan bar gida ne kawai in SHIGA duniya........

"A a ba za ayi hakan ba cewar izzatu tunda dai Baki so an Bari.
"To hakan dai yafi momy....
Ta fada tana hayewa saman bene
inda Kuma Kabir yace
"Ba fa Zan janye hadata aure da Anwar ba don auren su shine tabbata ta Akan aikina don auren ta zai zamo min tsani..........

"Nima ba zanso fasuwar auren ba Kabir na dai fada ne don kar ta gudu Amma ai gata can gidan Anwar din da haka suke rufe zancen

Koda Anwar ya koma gida Mr President ya tambayeshi "ya ka ganta ne Anwar? Ya shafa sumar kanshi
'dady batayi min ba wallahi Bata da tarbiya.........

"In Dan tarbiya ai me sauki ne Anwar sai ka dorata Kan irin taka tarbiyar munyi magana ne tuni da ubanta Kai ai Dan gata ne Mata biyu lokaci Daya? Tashi kaje zamuyi magana dashi Kabir din Kai dai ka zamo me adalci agare su Allah yayi jagora

Ya tashi ya fito yanajin shi Kam baiyi sa ar aure ba don kaf Matan da ake Shirin bashi Babu wacce yake so Amma yanajin zaiyi biyayya tunda duka iyayen shi ALHERI suke nufin shi dashi don haka ya zari key din mota ya fice wurin abokin shi badamasi Wanda ya zamo Dan gidan Alh uba Dan yaro don ya sanar dashi irin auren da ake Shirin yi mishi
Yana tafe kamar Wanda akacewa kalli can sai kawai idon shi ya hango mishi ummita wadda ke tafiya akasa zuwa kuki

Gabanshi ya amsa inda ya kusa buga motar Amma Allah ya tsare ya dawo Kan doka da oda inda Kuma ya nemeta sama ko kasa ya rasa

Haka ya Isa gidan su badamasi ya sameshi suka kashe inda badamasin ke fada mishi yanzu yake Shirin zuwa ya Kai mishi albishir din ya samo mata..........

"Kai Amma nayi maka murna don gara kayi aure da dai barikin da kake Kai ba mutumin banza ba Amma ka biyewa Matan banza nima dama nazo ne in fada maka yadda ake Shirin aura min Mata biyu Kuma duk cikin su Babu wadda nace inaso daya daga haj daya daga dady Amma yanzu tahowar Nan da nayi Allah da ikon shi nayi tsuntuwar soyayya Amma Wai kafin na kyafta ido har ta bace wa ganina Amma nayi alkawarin duk duniyar da tashiga sai na nemota nayi ta uku da ita.........

Badamasi ya kyalkyale da dariya
"Kai Amma wallahi su Dad sunyi min daidai Mata biyu lokaci Daya in ba irinku Yan gata ba

Ya Mike da Shirin tafiya
"Na lura ban baka tausayi ba badamasi Bari kawai in wuce tun baka sa zuciya ta bugawa ba..........

"A a malam Bari nazo na nuna maka yarinyar da nake fada maka na samu don ka ganta sai dai fa ban taba yi Mata magana ba saboda kwarjini da tayi min na dai binciko ance min Yar gidan eng AK ce na Kuma San baba ya sanshi shine kawai na fada mishi ina sonta yace in Bari zaiyi mishi magana Amma har yanzu na kasa yi Mata magana sai dai kawai na Zo inda Zan hango ta na kalleta na more.......


"Amma dai ka kusa bada maza badamasi duk barikin ka ace tsoron mace kake?
Ko dayake wata Kil kamila ce shiyasa kake shayinta kaga banbancin matar kwarai da ta banza inda abariki ne Babu wani kwarjinin da Matan bariki kewa Yan bariki tara ce ke dukan goma...........

'ban Yi maka gardama ba abokina muje in nuna maka ita...
Haka suka fito har zuwa kuki cafee inda Kuma cikin sa a ta fito ta soma takawa domin komawa gida inda Kuma agefe guda Wilson shima yake lafe yana Kare Mata kallo inda Kuma gaban Anwar ya buga da karfi yarinyar da ta saci zuciyar shi itace masoyiyar badamasi?
Lallai akwai hayaniya a gaba duk surutun da badamasi keyi domin Koda ummita Anwar baya cikin hayyacin shi da haka sukayi sallama ya taho Kai tsaye ya tunkari Mr President cewar yanzu ne ya samu matar aure idan zasu yarda ya auri Mata uku to ahada mishi da ita idan kuwa ba zasu yarda ba to abar auren duka

Mr President yayi murmushi
"Yar gidan waye ita wannan din ?
Yar gidan eng AK ce ya bashi amsa
"To kaje zanyi mishi magana ko ta hudu ka Kara hangowa kayi magana Zan cike maka su hudu dai dai ai Kai din Dan gata ne,

Anwar ya tashi Yana murmushi yayiwa Mr President sallama ya wuce abinshi..................
[5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_



*Page 40*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




.........Alh uba Dan yaro yazo har gida ya samu eng AK Akan Dan wurin shi badamasi yaga yarshi Yana so har ma suna rokon iri don hada ZURIA

Eng yayi shiru don har ga Allah baya son yiwa ummita auren da ba itace ta kawo Wanda take so ba Kuma hasalima Yana da tarihin Rayuwar badamasi da yadda yake son sheke Aya da Matan bariki shi da kanshi ba zai yarda da auren badamasi ba don haka Bai boyewa Alh uba Dan yaro ba.

"To alh na gode da kauna don me son hada ZURIA da Kai ya gama maka Dukkan kauna sai dai gaskiya alh bana son matsa Mata akan aure don yaran yanzu kana so ina so ma ya aka Kare bare anyi basa so?
"Zan sanar da ita zancen badamasi ka Kuma turoshi yau ko gobe don su gana idan yayi Mata shikenan idan kuwa baiyi Mata alh sai yaro yayi hakuri......

"Kar ka damu abdulkarim koni ba zanso kayiwa yarka Dole a aure ba don wannan zamanin ba irin Wanda ake Dole a zauna lafiya bane Ina fatan alkhairi agaresu idan Kuma baiyi Mata ba sai ya nema agaba da haka sukayi sallama inda ya dire mishi kudi masu kauri akan Wai ya bawa Yar shi ta siyi kayan kwalliya sukayi sallama ya tafi

Bai boyewa lubabatu ba dake ta Shan sharafinta da daukewa ak Kai ya zayyane Mata yadda sukayi da alh uba Dan yaro Amma ke da ke can in kin tanka ta tanka mishi don tana ganin awannan halin za ayiwa ummita aure cikin halin Babu?
Bai bi ta kanta ba ya kira ummita dakin shi ya sanar da ita abinda ke faruwa na game da badamasi da ubanshi ya Zo neman aurenta ya Kuma nemi Jin Ra ayin ta

Ta sunkuyar da kanta kasa tanajin kunya tana Kuma nazari...............
"Kar ki kwari kanki ummita ba Zan taba yi Miki AUREN Dole ba Wanda kike so shi Zan Baki don haka idan kinji ranki Bai dauka ba Babu kunya tsakanina dake Zan Baki damar ki.

"Abba na baka zabi wallahi zanyi maka biyayya muddin ka hango cancanta da dacewa akan shi zanyi maraba in Kuma roki Allah ya zaba min abinda yafi ALHERI

Ya sauke ajiyar zuciya Yana godewa Allah da ya bashi ya me biyayya
"Allah yayi Miki albarka ummita na gode da karrama Ni da kikayi Amma ki Bari zuwa yau ko gobe badamasi zaizo ku gana yadda Kika ganshi ko kikaji shi aranki kar ki boye min ta haka ne Zan yanke hukunci na adalci amatsayina na mahaifin ki
Ta amsa ta fito

Washe gari kuwa sai ga badamasi ya iso cikin shiga ta Alfarma da son ya siyo zuciyar ummita Amma Rashin sa ar da yayi kallo daya tayi mishi taji yayi Mata Kama da Yan duniya ita Kam Bata muradin auren irin su don wayewar su tayi yawa
Sukayi fira ta Yan Mintoci duk yadda yaso ya yaudari zuciyar ta hakan Bata yuwu ba haka sukayi sallama Yana Bata kudi Amma Taki karba tayi godiya inda yake Jin lallai irinta yake so wace macece ke kin kudi a wannan duniyar? Sai yaji ta Kara burgeshi da haka ya taho Yana santin aurenta

"Yaya Kika ga badamasi ummita? Shin yayi miki Koko akwai matsala? Tayi shiru kafin ta dubi abban nata
"Kayi hakuri Abba ka gafarce Ni gaskiya Bai yi min ba wayewar shi tayi min yawa............

"Nima da kin zabi badamasi ummita to da Zan fada Miki aibin auren shi don Nima tarbiyar shi batayi min ba Amma tunda Ra ayin mu yazo Daya shikenan sai abashi hakuri dama ban rufeshi ba ke Kuma Ubangiji ya Baki miji na gari ta amsa ta fito
Haka kuwa akayi ya iske alh uba Dan yaro ya sanar dashi yadda sukayi da yarinya ya Basu hakuri ya dawo gida

Kwana biyu Wilson na kwance Babu lafiya abinda ya tabbatar ciwon son ummita ne ya kayar dashi inda ya hadiyi magani da allurai Amma duk abanza Babu wani sauki sai radadin zuciya
Tamkar Wanda ya amsa umarni ya zaro key din mota ya fice zuwa kuki inda yayi nasarar ganin shigarta ya zauna zaman jiran fitowar ta

Sai yamma ta fito inda ya shigo mota ya karaso inda take tafe akasa ya danno Mata horn
Ta juyo Inda idonta ya hasko Mata shi sai tayi maza ta daure fuska yayin da shi Kuma yajefota da wani murmushi ya fito Yana fadin

"Kice yau da kafar dama Kika fito gashi mun hade don hanyar gidan naku zanbi
Ta sassauta fuskar ta
"Ayya yau Kuma inajin Kaine baka fito da kafar damar ba don yau ba inda kasani zani ba.........
"Sa ar takice take da yawa har nayi nufin kaiki duk inda zakije
Ta dubeshi
"Na taba fada maka duhu da haske basa tarayya a wuri Daya me kake nufi da SHIGA cikin Rayuwata?

Ya shafi sumar kanshi Yana murmushi
"Nagode da wannan damar da Kika bani manufata itace muyi musayar zuciya.......
"A hakan zamuyi musayar zuciya kana a duhu?

"Kasancewar mu mutane jinsi Daya shine kawai alakar mu ta kasanwa mutane Amma akwai banbanci me yawa tamkar nisan sama da kasa don haka kar ka Kuma bibiyata don abinda kazo dashi Kai da kanka kasan ba Mai yuwa bane na gode da taimakon da kataba yi min sai anjima

Ta wuce ta barshi inda yake biye da ita Yana nacin ta shigo motar shi ya kaita gida Amma Bata saurare shi ba haka shima Bai fasa binta ba har ta karaso gida shi Kuma yayi zaman awa kusan biyar Yana son ganin fitowar ta Amma shiru har dai ya gaji ya dawo gida sai dai me?

Yayiwa ummita tsaye arai bacci ma da ta kwanta mafarkin shi tayi tayi da ta farka ma Babu abinda take bege face ta saka idonta cikin nashi inda Kuma kwana biyu shi Kuma baije kuki ba ta damu matuka gaya har ta soma zubar hawaye ta dafe gurbin zuciyar ta

"Kar ki yaudare Ni Mana zuciya? Ta Yaya Zaki sakani son abinda Bai dace Dani ba? Ko kusa haka Kuma ko alama ita kanta lamarin Bai burgeta ba to bare Kuma iyayenta suji Dole ta watsar da wannan gurbatacciyar dake nuna Mata mafarkin ido biyu ......................
[5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*


*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*


_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 41*


*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




............Ta taho tana fatan ayau ta ganshi ko daga nesa ne Amma ko burbushin motar shi Bata hango ba har tsayin sati biyu inda ta bawa zuciyar ta magana Amma lamarin yaki yuwa

Ta fito don komawa gida kamar ance Mata juyo sai ta hango shi ya zuba Mata ido itama ta zuba mishi nata idon inda take hango tsari da kyan halittar shi

Farine tas har ya soma jajaja sumar kanshi baka manyan idanu masu cike da gashin girare baka wuluk sai Dan karamin bakin shi me siraran labba sai sajen dake fuskarshi Wanda Bai Kai kasumba ba a idonta Kam ta Dade Bata ga namiji irin shi ba me yuwa shiyasa ya kasa barin zuciyar ta ganin irin kallon da take mishi yasa ya tako ya karaso gareta

"Amma nayi farin cikin ganinki don kwana biyu da ban ganki ba wallahi na rasa natsuwata Allah yasa ban shiga hakkin ki ba idan nace ki shigo mota ta na maida ke gida

Bata San lokacin da murmushi ya kubce Mata ba ta dauke kanta
"Kar ka yaudare Ni ka Kuma yaudari kanka. Babu hadin tutu da fura Kai da kanka kasan hanyar mu tana da banbanci so ka Daina kusanta kanka Dani don Babu Hadi.........

"Ni kuwa a yanzu kusancin nake nema gareki don bana ko shakka munyi musayar zuciya don ko baki fada ba nagani a idonki so karki damu Ni dake zamu zamo Abu guda.......

Bata jira ya Kare maganar shi ba ta soma tafiya Yana biye da ita da yaga bazata tsaya ba sai ya fito suka jeru suna tafiya Wai zaiyi Mata rakiya ai kuwa sai gashi ya kawota har gida ta shiga shi kuwa ya dawo tun daga wannan Rana yake biyota su taho tare ya kawota har gida shi Kuma ya juya

Ta dawo inda ta samu eng AK yayi Baki Wanda Mubarak ke fada Mata Wai Mr President ne yazo wurin abban su

Eng ya karbi bakuncin Mr President Wanda suka gaisa yake tambayar shi Ina ya shige aka Daina Jin duriyar shi ya bashi amsa da ya na Nan yanayin Rayuwa ne

"To madallah Zan neme ka Amma kafin Nan wata Alfarma nazo nema idan har Allah yayi lamarin
Dama yaron wuri na ne Anwar yaga Yar wurinka yake so shine yace nazo na Yi maka magana idan bakayi Mata miji ba ya shigo cikin masu nema Amma don

Please Login or Register in order to submit comment