Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
®
✏📖
*FIKRA WRITER'S ASSOCIATION*

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪


©Khadija Sidi.....✍🏼


0⃣1⃣

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI✍🏼

SHIMFID'A 🌍

NIAMEY

Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne birni mafi girma a kasar, dake da girman murabba'in kilo mita (239.30) Tun a karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba'a dauke shi da wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarun (1890). A shekarar (1926) ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu a hankali yawan jama'ar yankin ya yi ta karuwa daga (3,000) a shekarar (1930) zuwa kimanin (30,000) a shekarar (1960). Yawan jama'ar Niamey ya kai (250,000) a (1980), a shekara ta (2000) kuma (800,000). Babban musabbabin karuwar jama'a a Niamey shi ne na yawan kaurar jama'a a lokutan fari.

A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma cibiyoyin nuna al'adun gargajiya na Amurka da Faransa da Nijar. Hakanan kuma akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin. Kashi (90)cikin dari na jama'ar Niamey Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika.




SA'AYRASA

MASARAUTAR SA'AYRASA yana bangaren kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba'in kilo mita (156,906). Masarautar Sa'ayrasa na iyaka da Masarautar Fabarusa, ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi. Masarautar Sa'ayrasa ta kasance d'aya daga cikin masarautar da ba su da yawan jama'a, wanda kidayar shekara ta (2001), ta nuna yawan mutanen masarautar ya kusa dubu dari hudu. Jama'ar Masarautar Sa'ayrasa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa. Tattalin arzikin masarautar ya ta'allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina. Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono. Sai dai kuma duk da noman da ake yi a masarautar, masarautar ta kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda fari.

FABARUSA

MASARAUTAR FABARUSA shi ne ya fi kowanne yanki girma a masarautar Nijar, wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita (634,209), watau kwatankwacin kashi hamsin da biyu cikin dari na girman Nijar baki daya. Masarautar Fabarusa ta had'a da Hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar Masarautar buzaye ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana'ar jamaar masarautar ta asali itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun (1990), harkar bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi (20)cikin dari na kudin shigar da take samu.



NIAMEY 1/01/2000

Tafe su ke cikin mota,tin da suka baro masarautar su wato Sa'ayara ta tsunduma cikin kogin tunani, ba ta gushe ba har su ka shigo Niamey, in da makarantar su wato SOVEREING GIRLS SECONDRY SCHOOL ta ke. Wato ‘ya’yan manya da sarakuna na sassa,masarauta da yankunan jamhuriyyar Nijar waannan makarantar su ke. Ajiyar zuci ta saki ganin sun doshi kofar makarantar, yayin da motoci biyu da ke gaban ta su su faka, ta su wacce ta ke ta uku ita ma ta faka. Waigawa ta yi dan ganin ko d'ayar da ke tafe bayan ta su ta sami isowa,ile kuwa sai gasu sun karaso a hankali su ka faka bayan ta su. Hankalin ta ta mayar kan kofar makarantar ta su. Motoci huɗu ne jere reres su ka taho kawo Gimbya Binta yar sarkin Sa'ayrasa makaranta. Ta fari ɗauke da dogarawa guda biyu da direba, ta biyu bayi ne mata su huɗu, sai kuma wacce Gimbiyar 'yar sarki mai dole ke zaune gidan baya, ta yi ɗai-ɗai ta na shan kamshi, tare da ita baiwar ta ce Bintu zaune gaban mota da kuma direba,sai cikon na hud’un dogarawa ne su huɗu zaune, biyu gaba biyu baya.

Tsawar da ta ji an daka mata ya sa ta yi firgit ta dawo cikin hayyacin ta, jin an furta,
‘’idan kin gama rubuta wasikar jakin da ki ka saba sai ki fita’’.
Faɗin _(driver)_ matu'kin mota ya na mai muzurai. Hakan ya sa ta saurin fitowa daga motar dan kuwa har sun shigo farfajiyar makarantar ba ta sani ba. Tini sauran bayi yan uwanta sun yi sahu suna jiran fitowar Gimbiya Binta. Cikin su Bintu ta shige ta tsaya kan na ta sahun, yayin da dogarai su ka karaso cikin azama, su ka yi na su sahun ta ɗayan ɓangaran. Daga bayin har dogarawa kalar yadin da ke sanye jikin su ɗaya, ruwan toka ne da shuɗi. Rigar ruwan toka sai zanin shuɗi.

Kan su sunkuye babu mai motsi kai kace gumaka aka aje, matu'kin ya buɗewa Gimbiya Binta kofa. K’afafun ta fara fiddowa waje, sanye cikin takalmi fata mai dankaran tsada, sai bayan wasu yan dik’ik’a sannan ta k’arasa fitowa. Tuni suka fara ma ta kirari da faɗin,
‘’taka a hankali Gimbiya yar sarki mai dole, takawan ki lafiya sarauniyar mata’’.

Sanye ta ke cikin kayan makaranta, riga da _skert_ buje sai kuma hijabi wanda ke tsayawa iyaka kafaɗa. Alkyabba ce ta alfarma ɗaure bisa kayan makarantar. Cikin sarauta da tak’ama ta ke takawa ɗaya bayan ɗaya ta wuce, su ka rufa mata baya. Haka su ka wuce ciki zuciyar Bintu cike da tunanin halin da akwatin karfen ta zai shiga matukar ba ta dawo da wuri ba dan Ado matu'ki ba mutunci gare shi ba, dan ya koma da kayan Kuka Sheka ba k’aramin aikin sa ba ne. Hantar cikin ta tuni ta kaɗa

Motoci sai shiga da fice su ke kasancewar yau rana ce ta dawowar ɗalibai daga hutun zango na uku. Kai tsaye sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka nufa, wanda a k’a'ida kowanne ɗaki dan d’alibai biyu aka yi. A dai-dai katangar da ta raba harabar makaranta da sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka tsaya, dan kuwa babu damar dogarai su shiga ɗakin kwanan kasacencewar dokar makaranta ta hana maza shiga. Nan su ke jiran dogarawa masu ɗauke da akwatina su k’araso su karb’i akwatunan dan karasawa da su ciki. Ita kuwa Gimbiya Binta kai tsaye ta shige,biyu daga cikin bayim biye da ita, ya rage daga Bintu sai bayi guda biyu. Dan sauri jikin ta har ɓari yake, Allah-Allah ta ke su samu su shigar da kayan Gimbiya Binta dan ta samu damar kwaso na ta. Sai da su ka ɗauki kusan minti goma kafin su k’araso ɗauke da kaya niki-niki, wanda kuwa faɗar adadadin su aiki ne ja, wai kuma a hakan ma akwai saura cikin mota. Haka suka shiga jidar kayan su na hawa da su sama,bhar bene na uku tukanna ka isa ɗakin Gimbiya. Ta nan kishingiɗe kan gado, ɗakin yayi fes-fes dama tin ana sauran kwana uku a dawo makaranta a ke gyarawa.

Su na hawa su na sauka har sai da su ka yi sahu uku. Bintu na Murna da sun sake komawa za su kwashe sauran kayan. Budan bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi,
'’akwati nawa ne su ka rage?’’.
’Daya daga cikin bayin ta amsa mata da,
"huɗu ne su ka yi saura ranki shi daɗe'’.
Gimbiya ta ce,
"to! Za ku iya tafiya kubarwa ɗiyar bayi sauran ta k’arasa hawa da kayan’’.
Tuni idanun Bintu ya raina fata, ba wai wuyar hawa da kayan ba ne damuwan ta ba, a'a ita ta dan akwaitin k’arfe ta ta ke. Cikin girmamawa su ka durkusa su na mai faɗin,
"an gama ran ki shi daɗe'’,
hannu kawai ta ɗan ɗaga musu alamar sa iya tafiya. Cikin hanzari su ka daɗa rusunawa kafin su tashi su ka fice. Ai fa Bintu ba ta san san da ta arta a na kare ba, ta na ji sauran bayin suna dariya suna cewa:-
‘’Ba ke mai yiwa Gimbiya hidima a boko ba, Allah shi k’ara’’,
ɗaya ta k’ara da "ai tin da aka zab’e ta wani girman kai ya game jikin ta, ɗiyar bayi a makarantar girma’’.
Yi ta yi kamar ba ta ji su ba, ta k’arasa ta ɗauro akwati ɗaya a ka d’aya kuma ta jawo shi a hannu. Ba ta kai ga hawa bene ba ta yi kaciɓus da su, haka su ka wuce ta suna mata dariyar kyeta. Cikin himma ta haye abun ta sama, sai da ta kai ga kofar ɗakin ta tsaya dan ta ɗan sami nutsuwa dan kuwa idan Gimbiya ta gano ta lalle kashin ta ya bushe. A hankali ta tura kofar tare da sallama. Gimbiya ko ta nuna ta san ta shigo bare ma ta amsa sallamar. Cike da nutsuwa ta aje akwatinan sannan ta fito, nan ta sake zurawa a guje, ta kwaso sauran akwatinan kamar dai yanda ta yiwa biyun farko. Aje akwatinan ke da wuya ta juya da niyyar sake fita, Gimbiya ta daka mata tsawa,
"ina zaki? Nufin ki ni zan jera mi ki kayan yau kuma ɗiyar bayi?’’.
Jiki na rawa Bintu ta zube k’asa ta na mai faɗin,
"tuba na ke ranki ya daɗe ni ce zan jera dama sauri na ke dan kwaso nawa kayan kar Ado ya manta ya juya da su’’.
Shiru idan Gimbiya Binta ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka. Da shirun yayi yawa Bintu ta ɗaga kai ta kai kallon ta gare ta, sai gani ma ta yi ta runtse ido kamar mai bacci. Dole jiki ba laka Bintu ta tashi ta shiga jera akwatunan, sai da ta gama tsaf sannan ta durk’usa ta ce,
‘’ran Gimbiya ya daɗe na idda’’.

Sai da wasu dak’ikai su ka shuɗe, har Bintu ta na tunanin ko dai bacci ta ke sannan ta ji ta ce,
‘’kya iya kwaso tsummokaran na ki’’.
A wulakance ta yi furucin cike da 'kas'kanci. Russunawa ta yi cike da girmamawa ta ce,
‘’godiya na ke ran ki shi daɗe", ta tashi ta fice. Nan fa duk nutsuwar ta ya gushe, ta ranta a na kare, ba ta ji ba ta ba ta gani. Dalibai ma su shiga da fice cikin farfajiyar wajan faɗi su ke,
"ta fara, in dai wannan ce dama duk dawowa hutu haka ta ke".
A guje ta fito daga harabar ɗakin kwana ta shigo sashen ajijjuwa. Ba ta ga tahowar shi ba sai ji ta yi karo da shi. Ta yi saurin yin baya saura k’iris ta faɗi ya yi saurin sa hannu biyu ya rik’o ta. Sakin baki ta yi ta na kallan sa,ta ma manta da gudun da ta ke.

Sanye ya ke cikin bakar _suite_, wankan tarwaɗa be mai dan faffaɗar kafaɗa. Ya na da dogon hanci, yayin da gashin bakin sa da ya zagaye bakin na sa ya k’ara masa kyau da k’warjini. Idanun sa rufe cikin bakin gilashi hakan ya sa ba ta sami damar ganin kwayen idanun na sa ba. Kamar daga sama muryar sa ya dakin dodon kunnan ta,jin ya ce
‘’hankali mana gudun me ki ke haka ke kuwa?’’.
Ta yi saurin ja da baya,hakan ya sa shi sakin ta.
’’Yi hakuri dan Allah Ado direba zai tafi da kaya na’’.
Bintu ta furta idanun ta na shirin kawo ruwa. Sai a sannan ya dubi kayan jikin ta ya na mai faɗin,
‘’Tabbas wannan shigar ta ki ta bayin Masarautar Sa'ayrasa ne, ina shigowa na ga motocin na su na fita, sun manta da ke ne...?’’,
ba ta bari ya karasa maganar ba bare ta bashi amsa ta sa gudu ta na mai faɗin,
"shikenan ni Bintu sun tafi da akwati na,shikenan na banu na shiga uku na lalace’’

Cikin rashin fahimta ya bita da kallo har sai da ta kure masa sannan ya d’aga kafad’a ya sauke sannan ya yi ciki abun sa.Isar ta wajan yawan motoci masu kai kawo ya k’aru,sai dai babu motocin Sa'ayrasa babu alamar su. Kwallar da ke idanun ta tuni su ka fara gangarowa bisa kuncin ta.
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪


©Khadija Sidi.....✍🏼


Wannan labari sadaukarwa ne kuma tukwici ne ga FIRDAUSI SODANGI,wacce ta amince da wannan batu na "garin masoya ba ya nisa" har ta kawo ziyarar ta gare ni. Allah ya bar zumunci ya bar kauna Amen.

0⃣2⃣

Bintu na shirin juyawa ta hangi akwatin ta jefe tsakiyar filin, da gudun ta ta k’arasa ta rungumo abin ta ta na maida numfashi. Wani mai mota ne ya ba a mata k’ura sa’annan ya lek’o ya na fa in

"shashasha sai kin jawo wani ya taka ki’’

ko aga kai bata yi ba bare ma ta san ya na yi. Ita dai burin ta ya cika ta sami akwatin ta.

Offishin shugaban makarantar katan ofishine wande aka kawata shi kai ka ce ofishin shugaban wani yankin ne. Ganin wanda ke zaune gaban sa da kuma abun da ke tafe da shi ya sa shi zufa na ba gaira ba dalili rufe shugaban makarantar. Kana ya nisa tare da fa in
"(your excenllency) Ya mai girma....’’
"Aisar,ko ka kira ni Aisar Gaddafi Nur,(his excenllely) ya na gida yallabai’’
ya katse shi hankali kwance. Zufa shugaban makarantar wanda dalibai ke kira Malam Hamisu ya goge,ya na mai gyara murya ya ce

"toh Yallbai,yanzu dai nufin za ka yi bad da kama kamar malami cikin wannan makaranta ta mu har tsawan zango aya.....’’

Yana mai murmushi ya ce
‘’ba bad da kama ba Yallabai,gyaran lafazin shi ne ina neman alfarmar koyarwa a makaranta na tsawan zango aya’’

cikin nazari Mallam Hamisu ya ke duban sa "me zai sa dan Shugaban kasa so ya koyar a makarantar nan?na zango aya? Ko shakka babu ya na daga cikin motanen oye wanda ke yiwa kasa bincike da aiki cikin surru, dama ba tun yau ya ke jin maganar ba,kaddai wani sharrin aka kullawa makarantar sa.....’’
Zancen zucin da ya ke yi cikin ran sa kenan dan kuwa ruwa ba ya tsami banza. Can dai ya gyara murya sannan ya ce

‘’Yallabai....’’

‘’Aisar’’

Saurayin ne ya k’ara katse shi ya k’ara da

"tunda zan zauna k’ark’ashin ka ya kamata ka saba da kira na da sunana.’’

Cikin jinjina kai Malam Hamisu ya amsa da

"Haka ne Aisar,muna maraba da kai,kuma ina mai tabbatar ma ka mu yan kasa ne masu kishin kasan mu,na gari ma su san ci gaban kasar mu.’’

Ya na mai murmushin nuna gamsuwa Aisar ya tashi tsaye gami da mik’a ma Malam Hamisu hannu ya ce

"madallah da kai,kuma na gode kwarai,gobe InshaAllahu zan fara koyarwa sai a bani aji a kuma zaga da ni makarantar sauran Malamai su sanni ko koyar da ni sharad’an makaranta idan akwai, duk abun da ka ke buk’ata in koyar shi zan koyar’’

Mallam Hamisu shi ma in tashi yayi,ya na murmushin yake ya amshi hannun Aisar,fa i ya ke

"Madallah Allah ya nuna mana’’
amma a zahirin gaskiya a tsorace ya ke da Aisar.

Sai da ya raka shi har kofa ya tabbatar ya tafi sannan ya dawo ofishin sa da sauri dan ha a taron zaman Malamai na gaggawa dan kuwa shi gani ya ke akwai matsala shi ya sa aka mu su shunan Aisar. Shi kuwa Aisar ya na fita shugaban su ya kira ya na mai sheda ma sa yanda su ka yi da Malam Hamisu,Shugaban na su yayi murna kwarai dan kuwa kamfanin da su ke bincike akai kusa da makarantar ne. Ko da ya aje wayar sai ya tsinci kan sa ya na mai waige waige ko zai sake ganin wannan baiwar,amma yawan daliban da ke kai kawo,da wanda su ka sa masa ido ya sa shi kasa gane wacece wace

"ba mamaki ma ta sami motar garin na su"

abun da ya fa a kenan kafin ya shige motar shi da ya saba basaja da ita ya bar harabar makarantar.

Wacece Bintu

Bintu Bala Mahuta sunan ta,amma Bintu iyar bayi ake kiranta a masarautar su kasancewa suna aya ta ci da da Gimbiya Binta, wato sunan maihaifiyar ta wacce Allah yayiwa rasuwa wajan haihuwar Gimbiya Binta. Mahaifiyar Bintu wacce ta ke babbar baiwar matar sarki wacce ake kira da uwar bayi,ta haifi Bintu yau,washegari aka haifi Gimbiya Binta kuma mahaifiyar Binta ta ce ga garin ku. Kun ga kenan sunan su aya,banbancin ranar haihuwar su kwana aya,dan haka shekarun su ma aya.

Shekarar Bintu goma sha biyar da haihu,mahaifin ta babban bawan wazirin Sa’ayrasa ne,kasancewar haka tare da alfarmar mahaifiyar ta da take babbar baiwar matar sarki mai rasuwa ya sa da za a kai Gimbiya Binta makarantar kwana aka zab’e ta cikin bayi domin kula da ita,dan ko a cikin ‘ya’yan bayi babu wanda ya san fada da al’adun ciki kamar Bintu. Ta wannan hanya aka rab’uka ta cikin makarantar su Gimbiya Binta musammam dan hidimar ta. Amma fa a wahalce ta ke samin ilimi,kai ba ma ilimi ba komai na Bintu cike ya ke da wahala. Wanka ne kawai ba ta yiwa Gimbiya Binta,amma komai na ta ita ce. Wanki da guga da a k’aidar makarantar akwai mai yi musu amma ita Gimbiya Binta sam ba ta yarda sai dai Bintu ta mata,hatta jakar makarantar ta ma Bintu ke gyarawa ta aukar mata. Idan jinga aka ba su sai dai ta yi na ta ta kuma yi na Gimbiya Binta, sai dai idan malamin da ya san rubutun su ne shi ne sai ta jira idan Bintu ta gama ta kwafa. Rubutu kuwa idan an mu su a allo sai dai ta kwafi na Gimbiya Binta,idan sun dawo aki ta kwafi na ta.

Batun wajan kwana kuwa aki aya su ke,duk da gadaje biyu ne a akin ba ta isa ta kwanta a gado Gimbiya Binta na gado ba, ah ah sai dai ta sami yar tabarma ta rab’ike daga can gefe a k’asa. Tun masu kula da akin kwanan na magana har sun hakura sun yi shiru dan sun ga tsakanin baiwa da uwar gijiyar ta sai Allah. Bintu ba ta isa ta riga ta bacci ba,kuma dole ta riga ta tashi ta ha a mata ruwan wanka. Wajan cin abunci ba ta isa ta zauna cikin yan uwan ta alibai ta ci abunci ba,sai dai ta jira Gimbiya ta gama,ta raka ta aki ko aji sannan ta dawo ta ci na ta. Kuma a duk in da su ke sai ta tabbatar kowa ya san Bintu iyar bayi ce, shi ya sa ma ta hana ta sa kaya in dai ba shigar bayin Sa’ayyarasa ba idan ranar sa kayan su na gida yayi.

Allah ya yiwa Bintu wani abu wai shi tsayi da diri,dan kuwa jikin ta ya girmi shekarun ta. A shekarun ta tana da zubin cikakkiyar budurwa idan ba fuskar ta aka kalla ba ba wanda ba ya b'oye shekarun na ta.

Bintu baka ce,irn bakin nan na wayayyun matan nan da ba sa shafa man da zai sake mu su kala. Doguwar fuska gare ta,amma ba mai tsayi sosai ba,ta na da manyan idanu ga hanci har baka,sai wushirya da ke mata kyau duk sanda ta dara ko ta bu e hakora. Ta na da suma matuka,ko ta aure kan ta da kallabi yawan sumar be b’oyuwa.

Daga ita har Gimbiya Binta aji uku suke. Ba ta da buri da ya wuce su kai aji shi da su gama makarantar ko ta huta da jarabar Gimbiya,dan kuwa ko k’awaye Bintu ba da shi a makarantar.

Aisar Gaddafi Nur

Aisar saurayi ne mai kimanin shekara talatin a duniya. Aisar ya da e cikin aikin sa da ya ke matuk’ar so tun kan mahaifin sa ya zama shugaban kasan jamhuriyyar Nijar. Aiki ne wanda ake mu su lakani da mutan b’oye,wato masu bincike da kula da kasa amma ta k’ark’ashin k’asa. Tin hawan mahaifin sa kujerar shugaban k’asa ya na ji ya na gani dole aka dakatar shi saboda yanayin aikin na su na sirri ne hatta sunan da ya ke amfani da shi cikin aikin da ban ya ke da sunan sa na yanka,ba zai yiyu a ha a da siyasa ba dan ba mamaki ma wata rana aiki ya bi ta kan gidan na su. Amma shi ba haka ya so ba. Hakan ya sa sam Aisar ba ya san shiga sabgar gidan gwamnati ko abun da ya shafi harkar siyasar baban shi. Ko zama gidan shugaban k’asan ma be cika yi ba,in ka gan shi ciki toh wajan iyayen sa ya je gaidawa ya tafi,in da Allah ya taimaka ba shi ka ai ba ne ya na da yayye ba laifi, dan ba kowa ba ne ma ya san shi a matsayin an shugaban kasa. Hakan be sa kungiyar Aisar janye dakatar da shi da su ka yi ba,har ma ya fidda rai ya hakura har sai baban shi ya sauka kwatsam ya ji kiran aiki na wani bincike da ya bi ta kan wani kamfani da ke kusa da makarantar su Bintu. Yayi murna kwarai duk da kuwa aikin ba nasa ba ne,shi kawai taimako zai yi shi ya sa sai dai ya rab’uke daga gefe har sai lokacin taimakon yayi. Kungiyar ta su ce ta ba shi izinin neman koyarwa a nan makarantar ta sovereign girls secondry school,su ka kuma ce ya je da sunan sa na ainihi tun da hawan baban sa mulki an fara ya awa cewa

1 Comments On BINTU DIYAR BAYI CE 1
avatar
aminu-1-2

10 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment