Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Compiled by Umar Dalha.







*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*




1

*Dukan yabo da godiya ya tabata ga ubangijin talikai , Wanda bai haifa ba kuma ba'a haifeshi ba , na godewa Allah da ya nuna min karshen novel DINA Duk karyar kada , ina rokonsa da ya bani ikon fara wanan cikin sa'a ya kauceni fadawa halaka dalilinsa, duk wani abin karuwa ya dorani saman sa abin ki ya kauce ni daga shi , wanan novel na kirkiri abina ne ina rokon Allah ya tayani isar da sakon dake cikinsa, masu karatu ina kara Mika sokon gaisuwata da kuma godiyata Allah ya barmu tare, Daukacin jama'ar gidan mu Exclusive Allah ya kara daukaka, marubuta baki daya ina jinjina na gode*








Labari

Kakarin amai take tana jan nunfashinta , ita kuwa ta daneta ta matse mata baki ala Dole sai ta dura mata danyen misan da ta tsinto a cikin bola , MAhaukaciya ce na hango ta dane wata yar budurwa tana kokarin dura mata mushe a bakinta ita kuwa ta gumtse bakin taki budewa , tana tsaka da kokowa da ita sai naga ta dakata , ta ja da baya kuma sai naga ta saka ihu ta shiga shure shure tana dafa cikinta da alama nakuda ce ta taso mata , yarinyar nan naga ta taso da gudu tana ta bibiyar wanan mahaukaciyar tana fadin , sanu haihuwar ce ?

Ita dai Mahaukaciya ba bakin magana banda juya kai ba abinda take hakan yasa yarinyarnan fita da gudu daga cikin tsumakoran da suka saka suka dadaure sukayi dan dakinsu inda zapi , sanyi , damana ke riskarsu , tana FIta tayi ta gudu tana haki da kyar ta samu ta fito cikin layin domin a can cikin bola ne suke can karshen anguwa , tana fitowa ta tsaya tana waige waige ta rasa ina zata dosa domin neman taimako , wani gida ta hango tamkar kango ta nufa domin wani lokacin sunkan sakata kai shara gidansu wato bola , su bata dan kanzo da ruwan daurayarsu na kayan wankin su wani lokacin har barinta suke ta debi na rijiya taje su sha dadinsu ita da Mahaukaciya ,

Tana shiga ta rafka salama ta ja gefe ta rakube , wasu yara naga sun fito su kansu daudar jikinsu ta ishe su suna ta wasa suna ganin wanan yar budurwar saï naji sun fara wake suna fadin *Ke mai suna Yar Mahaukaciya yaya haukan ki Yar Mahaukaciya , shin ina babarki Mahaukaciya tana ta zuba haukan? Yar mahaukaciya* ita kuwa sai murmushi take aika musu bata ce komai ba , har suka gama daukar maganar su suka tafi abinsu , ta kusan rabin awa a tsaye sai ga uwar gidan ta fito ta sha damara da niyar yin surfe tana ganin Yar mahaukaciya tayi hamdallah ta yafitota

Yar mahaukaciya ta matsa da Sauri ta zuguna a gabanta ,
Larai ta ce " idan abinci kike so zan baki da ruwan rijiya ke harma da zanin daurawata aman sai kin surfe min wanan dawar gaba dayanta

Yar mahaukaciya ta juya inda aka nuna mata dawa ta hadiyi wani yawu mai daci ta ce " To uwar gida ran gida zan surfa yanzu kuwa

Larai ta washe hakora ta kama mata buhun dawar suka tsayar da tirmin da tabaryar ta gyara yagegen zanin dake daure a jikinta ta shiga daka ba kakautawa , tun da rana ba ita ta gama ba sai yama lilis , Larai ta aiketa tayo mata cefane taje har cikin kasuwa a kafarta ita dai fama take ta gama ta koma wajen Mahaukaciya tasan yanzu ta dena iface ifacen domin takanyi hakan ,
Ba ita ta gama bautar gidan yawa ba sai da wajen shigar magariba ,
Larai ta harhado mata abinci harda na shekaran jiya ya gama yin tsami ta turo mata harda kanzo ta sauye mata shi a cikin wani bokici da ya gama yin tsatsa sanan ta ce ta jawo guga biyu ta isa gudun kar ruwan rijiyar ya kare ta je ta jawo guga biyun ta sauye a tsohuwar jarkarta ta dauka gaba daya tana tafe tana Sauri yara kuwa sai binta suke suna fadin yar Mahaukaciya ita kuwa bata kulasu famarta ta isa bola


Tana zuwa ta hango dan karton da ta kara ta rufe an janye shi ta kara Sauri ta shige cikin kewayen nasu , jini jini ta fara gani a dashe a ko'ina ta yaye rufar da tayi da ledodi tana yayewa gabanta na faduwa don abinda idanuwanta suka gani bata san sanda ta saki bokicin abincin da ta wuni tana aiki dalilinsa ya zube a nan ba ta dauki hanunta ta dora saman kanta saman bakar ledar da tayi dan kwali da ita ta kurma ihu domin jariri ta gani konce cikin jini yashe a nan gashi ba Mahaukaciya ba alamarta da gudu ta karasa ta shiga dage dage da alama neman Mahaukaciyar take









Shin ina mahaukaciya? Yaron nan wa ya haife shi? Su waye Mahaukaciya da Yar Mahaukaciya? Taku har kulun Sajida
[9/9 19:54] Sajida: *'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*








2

Dadaga tarin tarikicen su take tana ihun kuka tana Kiran Mahaukaciyata ina kike ? Da kyar ta dena dage dagen ta matso kusa da jaririn nan ta tsura masa ido yaron sai kuka yake tun karfinsa wani tausayinsa ya kama ta ta Mika hanu a nitse ta dauko shi ta jawo ruwan nan ta wanke masa fuskarsa ta dorashi a bayanta ta dauki zanin nan da Larai ta bata ta goya shi ta fito ta fantsama neman Mahaukaciya ,




Wai shin wacece Yar mahaukaciya?


Yar mahaukaciya ita kanta bata san sunanta ba bata san na mahaifiyarta ba , ita dai ta fara wayo ta ganta a gidansu bola kuma taji yara na kiranta da *Yar Mahaukaciya* ana kiran mahaifiyarta da *Mahaukaciya* duk da irin tarin daudar da suke ciki da cin abinci marar kyau da kwana a waje marar kyau idan ka kalesu zaka gane cewar fararen mutane ne rayuwa ce kawai ta mayar da su masu duhu , Yar Mahaukaciya ba arabi bale boko , bata da kowa sai Mahaukaciya , tarbiyarta tarbiyar Allah ce domin tanada nutsuwa tana masifar son Mahaifiyarta Mahaukaciya , bata son komai ya rabeta kulun cikin shan dukanta take domin idan ta kawo mata abu mushe taki ci sai kawai ta daneta wataran ta dura mata wataran kuwa ta samu ta gudu ,
Abincinsu gida gida take bi tayi aikace aikacen ragwayen mata ta samu abinda ta samu ta kai musu su ci abinsu kuma ruwa na kwata ne kadai basa sha domin tana yin iya kokarinta don ganin mahaukaciya ta kwana da ruwa a dakin , tun tana karama suke cikin bolar nan wataran ta wayi gari taga Mahaukaciya na dauke da ciki bata san KO na waye ba hasalima sai da taji yara na fada ta gane inda suka dosa tayi mamakin inda mahaukaciya ta samu cikin nan harma tayi tunanin KO hakan kawai ake wayar gari da shi , ita dai bata da mai bata amsa hakan yasa ta yi shiru abinta take lalaba mahaifiyarta cikin tsananin so da kauna iya labarin tarihin mahaukaciya Kenan


Tafe take da dan yaro a bayanta tana girgizashi tana fadin kayi shiru dan Mahaukaciya muje mû nemo Mahaukaciyarmu mu kawota gidan mu ta goya sabon dan mu , kayi shiru Dan mahaukaciyana tana ta yawo gaba daya ta jigata sai jiri take na tsananin yunwa ga Dan mahaukaciya sai dai ta bashi ruwa yara kuwa banda tsokanarta ba abinda suke duk inda ta zaga sai an biyota ana fadin lah Yar mahaukaciya ta sato beby har ta ISO wajen wani police zata huce taji yace " ke yar mahaukaciya dan wa kika sato haka?

Tayi narai narai gabanta na mugun faduwa ta ce " Mahaukaciya ta haife shi kuma ta gudu

Ya zabga mata mari har sai da ta dan fara sakin fitsari ya damketa sai police station , suna zuwa ya Nuna cewar ta sato yaro ne suka shiga tambayarta amsar dai data ce Dan Mahaukaciya ne hakan yasa suka kunce yaron suka shiga nadarta Dole sai ta fadi inda ta sato yaro banda kuka ba abinda take suna tsaka da dukanta sai ga tsohon daraja shima police din ne aman ya fisu mukami , yana zuwa ya tambayi mai tayi


Ilyasu yayi masa bayanin ai ga abinda aka kamata da shi

Tsohon daraja ya ce " tabas kwanakin baya naga Mahaukaciya da ciki a jikinta kuma yau na ganta wajen kasuwa ba cikin sanan saninta duk jini ne tabas wanan yaro *Dan Mahaukaciya ne* dan haka ku saki baiwar Allahn nan tayi tafiyarta


Haka suka saketa ba dan ransu ya so ba domin sun so ta kwana a nan suyi anfani da ita ,sai dai kash tsoho ya kawo cikas

Da kyar take takawa domin ta daku ta dauko dan Mahaukaciyar tayi wajen kasuwar don neman Mahaukaciya tana tafe tana kuka yaron na kuka tayi kasuwa neman duniyarnan ba Wanda bata yi ba ta juyo ta nufi wani layi tana tafe 'tana kugin sunan Mahaukaciya har ta isa wata makaranta ta zauna tayi tagumi almajirai sai shigi da fici suke suna ta sha'aninsu har akayi sallar isha'i bayan an gama sallah Malan ya fito daga masalaci ya hangi yatinyar nan zaune tana ta jijiga yaro a hanunta kawai sai wani tausayinta ya kama shi ya matso yayi mata salama

Ta dago jajayan idanuwanta masy shige da na misa ta sauke su saman fuskar wanan Malan mai cike da Haiba ta amsa salamarsa

Ya ce " Baiwar Allah lafiya kike zaune a nan? Ga yaronki da alama yunwa yake ji to ki bashi ya sha mana

Yar Mahaulaciya ta kale shi tace " Malan ai ruwan ya kare babu kuma abincinsa

Malan sai yaji tausayinta ya ce tashi mû shiga gidana a tatsa miki nonon akuya tayi sabuwar haihuwa sai ki bashi ya sha , ta mike har tana harde kafafuwanta ta bi bayansa suka shiga gidansa

Matansa biyu dayar mai kirkin gaske DAyar kuwa tadi dafi zafi hakan yasa ya nufi dakin saratu ya fada mata ta fito ta taimaki yarinyar nan da danta ,

Saratu ta fito suka gaisa da yar Mahaukaciya tace miko yaron a bashi nonon akuya kema kije ga ruwan dumi kiyi wanka domin da alama sabuwar haihuwace

Yar Mahaukaciya ta ce " nayi wanka? Da gaske?

Saratu ta ce " eh man ga bokici ki dauka ki zuba ruwan sai ki dan sirka da na rijiyar ki je kiyi wanka shima bara nayi masa sai a bashi nonon

Sai washe hakora take domin itadai da wayonta har ta manta rabonta da tayi wanka ta jawo isashen ruwa ta kai bayi ta aje saratu ta bata soda ta dauko mata jacen kayanta ta mika mata har tana fadin ki wanka ruwan zafin da kyau fa saboda jego ita dai har lumshe ido take tana zuba ruwa a jikinta kafin ta fito Saratu ta wanke dan mahaukaciya ta bashi nonon akuya ya sha sosai har ya samu wani ni'imtacen baci mai dadi

Wanka take tun karfinta wani bakin ruwa na zuba daga jikinta yana bin magudadar ruwan nan da nan sai gâta ta fara haske tamtar mai , ta cire ledar dake rufe a kanta ta dauki sodar nan ta ringa kwabata a cikin gashin kanta nan da nan naga wata irin dauda mai yauki tana zuba daga kanta ta kama kwarara ruwa gaba dayanta ta darwaye jikinta dagowar da zata yi na zaro ido domin gashin kanta ba baki bane kalar 🙍🏼 masara ne yelow gaba dayansa aman yalow mai haske ga shegen tsayi da gareshi na tambayi kaina wai Yar Mahaukaciya yar hausawa ce kuwa? Ta dauko ledarta ta daure kanta ta saka kayan da Saratu ta bata sai ajiyar zuciya take domin ta rabu da kashi 80 na daudar dake jikinta tana fitowa gaban Saratu ya fadi , duk irin kirkin saratu matsalarta daya ce kishi Allah yayi mata kishin mijinta tamkar mai , hakan yasa da Sauri ta daukowa Yar Mahaukaciya yan tsumakoron da ta dadauko mata ta bata ta hada mata da tuwon lamshi mai yawa ta ce " to yar uwa rufe gidan zamu yi kinsan Malan ba a nan yake kwana ba hakan yasa Mike rufe gida da wuri

Yar Mahaukaciya ta kama godiya harda tsugunawa saratu ta ce ba komai ta dora mata dan Mahaukaciya ta goya ta dauki sauran kayan tayi gaba tana yiwa Allah godiya taci GABA da Neman Mahaukaciya









😌
[9/9 19:54] Sajida: *'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*









3
Tafiya take har karfe biyu na dare yayi mata ta gaji tamkar ta kife idanuwanta sai zugi suke yi mata na baci dan mahaukaciya kuwa sai bacinsa yake shekawa hankalinsa konce domin ya sha nonon akuyar nan ya koshi , wata bishiya ta hango a hankali ta isa ta samu ta rakube ta shinfide dan Mahaukaciya tayi konce a gefensa ta shiga tunanin duniya tana tunani tana share hawayenta ta mike da ruwan na yar jarkar ta zauna ta daura wata kalar alwalah gaba daya ba daidai bace ta juya Gabas tayi sallah Wace bata karanta komai sai dai tayi ta musmus da baki shima wajen Larai ta jiyo idan tana sallah tamkar koton kurciya nan da nan ta gama tana salamcewa ta konta kusa da dan kaninta tana adu'ar Allah ya jikanta ya ya fito mata da Mahaukaciya ,

Haka rayuwa tayi ta tafiyarwa yar mahaukaciya tun bata iya raino ba har ta kware ta iya goya yaron da zuwa wanki , shara a bata nera ashirin nera goma ta je ta siyowa Dan Mahaukaciya koko ta zo ta bashi ya sha , idan ya koshi itama ta samu ta sha , a tanzu yara sun koma tsokanar Yar Mahaukaciya da Dan shege ita dai ta kanta take tana nema musu dan abunda zasu saka a bakarsu har yanzu tana zuba ido ne taga ta inda Mahaukaciya zata bilo duk fitar da zata yi kuwa sai ta nemi Mahaukaciya har yanzu bata fida rai da ita ba ,



Konce take ta samu da kyar barci ya dauke Dan Mahaukaciya ita kuwa sai hama take ga wani uban sauro na damunta inuwa inuwar mutun ta fara gani ta mike zumbur ta fara kalon kofar wani katon mutun ne bakikirin mai murdaden jiki ya shigo kafin ta ankara tayi wani abu har ya watsa mata wata hoda a fuskarta ya kwasheta ya sakata cikin wata bakar mota ya dauko jaririn shima ya saka shi cikin motar wa'inda suke cikin motar suka figi motar ,

Tafiya suke tun karfinsu sai da sukayi tafiyar awa hudu sai gasu a garin jos suka karkata suka nufi wani tankamemen gida mai shegen kyau suna isa aka wangale musu porte din suka dana kai ciki , wata hanya naga sun dauka a cikin gidan sun nufi wani gate din aka kuma bude musu , suna isa ya diro ya bude ya dauko Yar Mahaukaciya a kafadarsa ya nufi wani daki da ita ya dauko yaron shima ya Mika shi wajen wata tsohuwa naga ta nufi ciki da shi ,

Dishi dishi ta fara gani sanan a gankali ta buda idanuwanta , wajen da ta ganta konce saman wani makeken gado Wanda tunda uwarta ta haifeta bata taba sanin akoyshi a nan cikin duniya ba ta Mike tsaye da Sauri ta fara dubedube can ta koma ta zauna ta tare fuskarta da hanayenta ta shiga tinani , watarana taji kishiyoyin Larai suna fadin idan aka mutu akoy wuta akoy aljana , ance a aljanar akoy manyan gadaje da manyan TV da komai da komai a wutar kuwa wutace kawai sunce ai idan Larai ta mutu tace ita aljanar zata zaba su kuwa a kaisu wuta dan sun aure mata miji ( to kaji Larai shawara Kenan za'ayi miki?) , ta kuma daga kanta ta hango babar TV din ta kali gadon da take zaune saman kansa a fili ta furta " Au Kenan mutuwa nayi aka kawoni aljana? To ina dan Mahaukaciya da Mahaukaciya ? Ku zo ku ga aljana ku zo muyi zaman mû a nan aljanar tafi duniyar dadi , tana tsaka da maganarta aka bude dakin wata mata ce ta shigo rusheshiyarta ta ja ta tsaya da Sauri yar Mahaukaciya ta mike tana soshe soshe tana kalonta

Matar nan ta ce " ke yarinya ki tashi nayi miki wanka na shirya ki na kaiki wajen hajiya

Yar Mahaukaciya ta ce" baiwar Allah nan ina ne? Duniya ce KO lahira?

Matar nan ta ce " ke karki kawo min maganar banza ta kama Yar Mahaukaciya kiiii sai cikin bayi tana ji tana gani matar nan ta tube ta tamkar wata beby ta zirata cikin bahon wanka ta kama dirzarta da wani soso mai shegen zafi , tun tana nonokewa har ta hakura matar nan dan rashin imani ta dauko wani tirare da detol ta zuba a ruwan har kanta ta kuma darje jikin Yar Mahaukaciya jikin har wani sulbi yake na wahala ruwan ya kuwa shigar mata ido ta rufe ruf tayi ta murzawa aman matar nan bata damu ba , tana gamawa ta jawo tawul ta nade jikin yar Mahaukaciya ta jawota tsakar dakin nan Yar mahaukaciya ji take tamkar sabuwa har wata iska ke daukan ta tayi fayau da ita farinta yayi mugun fitowa ,

Matar nan mai suna Mesi wato ba musulma bace ta dauko kayan bushe gashi da wani mahaukacin kaya doguwar riga mai daukan hankali ta jawo hanun Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita ta shiga bushe mata gashin kanta ta dauko man shafawa ta shafa mata nan da nan kan nan mai kalar blonde ya fara sheki ta saka ribom ta daure aman har gadon bayanta ya zubo , ta mika mata sabon pant da breziya ta saka gaba daya aikin nan da take yi mata bata yi mata magana itama tayi shiru tana kikifta manyan idanuwanta ta rasa wanan wani irin Abu ne? Wanan wata irin masifa ce? Meye za'ayi mata ne? Ina za'a kaita? Ina Dan Mahaukaciya? Nan din ina ne?















Ni ma ban sani ba yar mahaukaciya sai dai mu bisu mu gani
[9/9 19:56] Sajida: *'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*








4

Tana tsaka da sakar zuci taji Mesi cikin wata uwar muryarta tamkar namiji tace " ke tashi mu tapi

Cikin Sauri Yar Mahaukaciya ta mike ta bi bayan Mesi suka ratsa wani falo baba , suna ratsa na biyu ta hango wata tsohuwa tana ta jijiga yaro a hanunta ,

Tsohuwar ta matso ta mika mata yaron ta ce " bashi ya sha

Yar Mahaukaciya tayi shiru ta amshi Dan Mahaukaciya ta rungume shi yana ta bacinsa kawai sai taki cewa komai

Mesi ta ce " yaronta ne kuma mahaulaciyar ce dan Haka kawai mû kaisu wajen Hajiya


Tsohuwa ta washe hakoranta jajaye ta ce " kai aman hauka shi kadai yake wanan yarinyar mai kyau haka ya kamata? ( tsohuwa shin haukan ba kadarar Allah bane? Akoy Wanda ya isa ya kaucewa kadara ne? )


Messi ta ce " baki ma ga gashin kanta ba wani mai shegen kyau sai tambayar masifa ke malama mu je KO na ci ubanki a nan

Yar Mahaukaciya tayi gaba da gudugudu suna biye a bayanta sunyi tafiya mai nisa sai gasu sun bilo dakin wata mata tana zaune bakin gadonta ta hakimce Matar zatayi shekara arba'in da biyar a duniya ,

Suna shigowa su duka suka tsuguna suna gaishe da ita banda yar Mahaukaciya


Hajiya Falmata ta ce " ya zaku kwaso min yarinya karama haka nayi yaya da ita?

Mesi ta ce " ai hajiya wanan ta dade cikin hauka yanzu haka da kokowa da komai muka samu muka fito da ita kinga sai da na sharara mata mari hudu sanan ta dena buge buge kuma kinga yaron nan danta ne ita ta haife shi bashida uba shege ne kuma ita din ma shegiyar


Hajiya Falmata tayi shiru ta ce to ku zaunar da ita

Suka zaunar da Yar Mahaukaciya ita dai binsu take da kalo bata ce komai ba , sai da suka zaunar da ita suka fice

Hajiya falmata ta taso ta zauna nesa da yar Mahaukaciya ta kura mata ido ta ce " ba laifi kina da kyanki , kuma kinfi wancen Wanda nayi da ita kuma na kasheta da alama ke zaki fita iyawa kuma aikina zai fi ci sosai

Gaban yar Mahaukaciya banda faduwa ba abinda yake tayi shiru tana ta kifta ido , ita dai
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment