Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irrin mutanen nan i'yan tsubbu ne Aminullahi dukiyar kawai suki buƙata matsayin ta yo har ne za'a gayawa RUHI BIYU ai fatalwa sai a film ko novel Aminullahi kar kayarda da irrin mutanen nan mahaukata " cewar kaka yana magana ransa a 'bacce , INEEE ce ta d'aura da cewa " ahtooooo ko a cikin tatsuniya ba , kawai anga mu fa'da gatuwar gida ko govenar bai mallaki irrin sa ba , anmman hassada da 'bakin ciki wai fatalwa" dariya suka fashe dashi suka mayarda abun wasa , nan Aminullahi ya kuma gidan su da wane sirrin da ya ɓoye a zuchiyar sa yana fitta ya tuntsire da dariya juyawa yayi yace "mahaukata da sannu sannu zaku fahimchi abinda ke gudana " juyawa yayi don ganin ko akaiw wanda ke ganinsa ganin bakowa ya gyrah court nashi ya wucce gidan sa....










Tofah babban magana Aminullahi how far.








Samira ce kwance akan gadon ta tana juyawa tana kuka mai chin zuchiya tunda suka dawo asibiti batawa kowa magana ba itta dai tasan meke damunta kwatsam taga an kashe wutar d"akin razana tayi tace "waye ne Please kudaina wahalar dani ba san me na muku ba" dawo da hasken akayi taga ba kowa tashi tayi ta fara tafiya a hankali tana d'an ganin_ganin ko ana binta hankali take tafiya a tunanin ta wai ta b'oya ne karu da mutum tayi tayi saurin ganin waye ne , daga 'kasa take ganin tufafin da yatsu irrin ta bil'adama lokacin da ta sauke idon ta chass akan wannan hallitar, wazata gani a gabanta kuwa idan ba.














ohhhhh A'kalamina ya tsaya chakk tsaban tsananin tsoro firgichi don haka my lovely sister zoki 'karasa musu wanan....






Al'kalamin ƙanwar soja ✍️✍️✍️






share fissabillilah 🥰*☠️💀 RUHI BIYU☠️💀*




*Littafin had'aka*💪



MALLAKIN




*©Fateemah Rabi'u (ZAHRA ROYAL STAR)*
&
*K'ANWAR SOJA*


























*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






PAGE 9️⃣➡️1️⃣0️⃣




Wa zata gani a gabanta kuwa idan ba wannan matar data gani da d'iyarta a asibiti matar sanye take da farar kaya tsawon matar harya wuce misali ga fuskar ta tayi fari fat ga wani jini na d'iga daga idanuwanta wadda inya d'igo k'asa har wani tafar-fasa yake yanzu kuwa matar harda ciki a jikinta cikinne ya fara juyi, Samira dake tsaye cike da tsananin tsoro numfashinta na barazanar d'aukewa jitayi wani abu ya fashe runtse idanuwanta tayi kukan jariri taji wani iri maisa mutum ya saki fitsari da sauri ta bud'e idanuwanta bakinta ne ya fara motsi ga idanuwa data zaro saka makon tozali da tayi da cikin matar nan ne ya fashe jaririn dake ciki ya fito ya nufo wajanta kansa a lauye tafe yake duk jini jikinsa yana kuka,




Matar ce ta mik'o mata hannu wadda yayi zank'alele cikin wata amon murya marar dad'i ta kama cewa "ki cecemu nida jaririna ki cecemu nida jaririnahhhhh numfashinta ne ya fara d'aukewa tana so tayi ihu amma ta kasa gashi tana so ma ta tuno da wata addu'a ma amma ina kamar an datse mata baki,




Jitai an kama hannuta cike da firgici ta waiga zuciyar tace ta kama bugawa da sauri da sauri yarinyar ta gani tana cewa itama ta taimakawa mamanta cike da gargad'i yarinyar tace "bana ce kubar gidan nan ba ku hanzarta barin gidan nan nacehhh"


Wani irin ihu ta buga saka makon gani da tayi jarire sun cika d'akin suna nufo ta sun cika mata kunne da kuka,


Dai-dai time d'in Innee na tahowa ai da sauri jin ihon jikanyarta da hanzari ta fada d'akin,


Wani irin jan birki tayi ganin wannan jariren sun juyo wajanta sallalami ta kama cikin rud'ewa tunkan takai iya ga addu'ar tana d'akko komai ya bace bat ai nan take itama ta zube a sume,




Da sauri Mommy da Daddy da suka juyo ihun Innee suka nufo d'akin salati suka kamayi ganin Samira a sume Innee ma haka cikin k'osa da wannan al'amari Mommy tace "tabbas akwai abin ke shirin faruwa nidai please Daddynsu ka nemo mutunan nan wadda Aminullah ya kawo kamar yasan wani abu dan gane da wannan murd'and'an gidan" ta idasa maganar cike da damuwa da sauri ta yayyafa masu ruwa farkawa sukai a firgice da sauri Samira ta rungume Mommy, Mommy tace "mi yake faruwa ne? Uhum na ganku cikin wannan yanayin?"


Zata bud'e baki tayi magana saita ji komai ya goge mata, Mommy ta k'ara tabbayarta ba amsa Innee ma dai duk wani abunda ta gani duk ta manta sai cewa tayi wai tana shigowa taji bacci ya d'auketa


Sai Samira tace "Mommy please nidai mubar gidan nan kawai" Daddy ne ya kalli d'iyar tashi yace "yanzu banda inda zamu zaunawa banda inda ya wuce nan amma zansan abinyi"






Aminullah ne zaune da Bilkisu tana kan ciyarsa sai shagwaba take mai d'an tattab'a ta yayi yace "matar Aminullah anya banyi ajiya a nan ba kuwa" yana tab'a cikinta da sauri ta tashi zunbur tana tunani lallai kuwa yaushe rabonda taga al'adarta wani abun tsalle ta buga tana k'ank'ameshi cike da tsananin murna tace "Habibi ya akai ka gane inada juna biyu?" Murmushi yayi mata sana yace "hmm lallai matar nan kin manta ni Likita ne" murmushi tayi tana k'ara rungume meshi shima cike yake da tsananin farin ciki dan sun dad'e ba haihuwa suna cikin wannan murna wayar Aminullah tayi k'ara da sauri ya zarota ya d'auka ganin Daddyn Samira ne ke kira,




Bayan sun gaisa Daddy yace "Aminullah ina so wannan mutanan ya dawo ina so in mai wasu tabbayoyi ne" cike da gamsuwa yace "inshallah zan kawoshi zuwa gobe" "to shikenan ngd sosai yaron kirki" cewar Daddy sallama sukai cike da mutumtawa,




Washe gari gari kuwa kamar yadda yayi al'k'awari suna zaune a falo saiga shi sun shigo da wannan mutanan yanzu shiga ce yayi irin ta kamala daka zaunawa sukai Kaka zaiyi magana Daddy ya tsayar dashi yace "please Kaka daga ganin mutunan bazai cetar damu ba kabarsa muga wane irin taimako zai bamu"




Shuru falon ya d'auka sana mutunan ya fara magana cike da kamala yace "kamar yadda na fara baku labari cewa akwai abunda ya faru a gidan nan to tabbas hakane sai dai ni kaina bazan ce ga taka mai-mai ga abinda ya faru ba nidai sani na akwai matar da zata iya bada tarihin gidan nan da abinda ya faru saboda itace tayi makwaftaka dasu wadda suka zauna wannan gida ita wancan lokacin tana zauna ne da iyayanta waccan gidan wadda yake mallakin su wannan yaro Aminullah, to shekaru da yawa dole sai mun nemo matar duk inda take dan yanzu ta tsofa gaskiya Sana abu na gaba" yad'an tsagaita sana yace "Ni gaskiya ba mutum bane kamar ku ni rauhani nine wadda bama citarwa kuma musulmai ne"


Cike da rud'ewa da kuma tsoro suke binsa da kallo bare Innee sai zare ido take Aminullah kanga abin ya rud'e sa dajin cewa ba mutum bane,


Daddy ne yayi k'arfin halin cewa "to bawan Allah bazamu iya tashi daga gidan bane mu rabo da matsalar?"


Wannan bawan Allah yace "gaskiya ai tunda kuka riga kuka shugo sa to koda kun fita shi wannan mai gidan shima RUHIN sa zai dawo ne domin cikar borin sa wadda bai cikasa ba zamanin daya wuce kuma zai dawo jikin d'an Adam ne wadda zai iya shigar kowa a cikin ku amma dole sai ma'au rata, sana itah Samira ya nunata yace ana yawan miki inkiya cewa kubar wannan gida to ba wasu bane sai RUHIN uwa da kuma d'iyarta wadda suma ranar da akai wani dare mai suna DARE BIYU komai ya faro har suka bar duniya wadda Allah bai bani sani ga miye ya faru ba sai ita wannan mata itace zata fiddamu cikin DUHU har mu zamu masalaha dan duk inda kukaje wannan RUHIN mijin yana tare daku dan shine BAK'IN RUHI kuma bazai taba rabuwa daku ba harsai ya cika muradinsa, Sana za'a k'ara DARE BIYU a wannan daren zai bayyana zai k'ara dawowa domin cika burinsa amma da taimako Allah indai munji abinda ya faro a gidan inshallah zamu san abinyi"




Ya idasa maganar cike da tabbatarwa cike da gamsuwa su duka suka bishi da Allah yasa a dace inda Aminullah yayi al'k'awarin nemo matar duk inda take inyaso in akasan inda take sai aje aji labarin musabbabin miye ya faru a cikin wannan gida....








****************** Sa'adha ce zaune sai lallashinta Sameer yake ya rasa mike damunta kuma tana so tasanar dashi damuwar ta amma data bud'e baki domin magana sai taga kamar ana gargad'inta ne




Cike da damuwa shima yake shafa kanta yana kwantar mata da hankali fita yayi yace "bari naje nad'an dawo" da to kawai ta bishi


Kamar jira ake ya fita wutar d'akin ta d'auke wani irin duhu ne ya mamaye d'akin Sa'adha kuwa dake zaune kan kuje da sauri ta tashi cike da tsananin tsoro hadari ne yayi gaggami sai walk'iya ake ga iska windows sai k'ara suke saki wadda da anyi walk'iya falau saita haske koh ina kamar safiya cikin haka aka sake wata walk'iyar inda nan Sa'adha ta hango wata mace mai dai kama da ita zaune tana kallon idanuwanta na fitar da wani bakin hayak'i ga gashin ta duk ya bud'e fuskarta kuwa duk an karceta duk ta b'aci da jini zuciyar tace ta bara bugawa saboda tsananin tsoro wata irin tsawa aka yi sai aka kece da wani irin ruwa mai k'arfin gaske cikin sauri Sa'adha ta k'ak'k'ame jikinta dariya ce aka kece da ata mai amsa kuwwa, runtse idanuwanta tayi ta tusa kanta a tsakanin cinyoyinta


Jitai an tab'a ta cike da wani irin firgici ta d'ago Sameer ta gani tsaye kanta ga haske ya dawo babu k'arar saukar ruwa babu walk'iyar nan da komai ya dawo normal cike da mamaki da tsoro ta tashi ta k'ak'k'ame shi cikin sauri ya zaune da ita a jikinsa,






A waje kuwa y'an mata duk da abinda ya faro amma sha'anin gabansu kawai suke canna hangi wata ta nufi gidan k'asa shiga kawai take ko tsoro babu a ranta dan itafa ta tab'a ganin wasu kayan mata a gidan k'asan nan kuma tasha alwashin saita sasu koda ta shiga ciki wajan duk yayi yana duk ta dabaibaye wajan ga kura kota ina amma haka ta kutsa kai har takai saitin wani akwati bud'e sa tayi ta fara zab'ar kaya dan kayane masu kyan gaske saida ta zab'a tana wani rangwad'a tana gwadawa da sauri ta d'auki wasu tana cewa "kai wannan zasuyi min kyau bari na sasu yau da dare rufewa tayi ta fito daga wajan




Da dare kuwa kowa na harkar gabansa wasu najin kid'a wasu zuk'e-zuk'e wasu cance suke ba abinda ya shamasu gaba fitowa tayi sanye da kayan da sauri wata ta tashi tace "Wow Maryam wannan kyau haka kin ganki kuwa" sai zuzzuta take ita kuwa Maryam dama ga iyaye dasan girma jitai wayar ta tayi k'ara matsawa tayi can nesa inda ba mutane ta juya baya gani tayi number da aka kirata ba suna ba number d'an tsaki tayi waigowar da zai ta fasa wata uwar k'ara wadda ba wadda ya jiyota bare ya kawo mata d'auki illa kuwa abinda ta gani ya girgiza wata mace ta gani rik'e da wata sharb'eb'iyar wuk'a matar ita ba sama ba ita ba k'asa ba tana wata mahaukaciyar dariya mai firgita RUHIN d'an Adam ta nunata da wuk'ar tace "lallai dole ki mutu rawar kai taja miki nayi al'k'awarin duk wadda yasa kayan nan sunansa gawa ke gaki isassa kohhhh ta k'are maganar cike da b'acin rai cike da tsananin tsoro Maryam zata bud'e baki domin magana matar ko ince aljanar ta d'aga wannan sharb'eb'iyar wukar sai akan Maryam kagaba d'aya ta d'auke mata kai........✍️😳












*Fateemah Rabi'u ce (ZAHRA ROYAL STAR)*✍️✍️✍️






Share and comment Fisabilillahi🥰🙏


☠️💀 RUHI BIYU☠️💀*




*Littafin had'aka*💪



MALLAKIN




*©Fateemah Rabi'u (ZAHRA ROYAL STAR)*
&
*K'ANWAR SOJA*




























*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






page 1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣






"Yanzu don Allah tafiya zakayi dear ina kasan mutanen nan ne, wai dole sai ka taimaka musu, ina kasan zaga same wanan tsuhuwar matar bayan abu ya d'au lokacin mai tsawo gaskiya abun nan da ban mamaki wallahi".






Janyo ta jikinsa yayi yafara romance nata yana mata rad'a a kunne ," ke kwantar da hankali ke sweety na inshallah za'adace duk wanda ya taimaka wa wane a rayuwar sa shima Allah zai taimake shi ta inda bai sane ba kawai ke aminchi mun zan shiga cikin garin Kano nafi sa rai cewa yanzu achan take duk da cewa Kano tumbin Giwa ce babban gari ne anmman nasha alwashin nemo ta a duk inda ke kinje masoyiyar Aminullahi adu'ah da fatan nasara zaki min , a wanan tafiyar da zanyi,"














'kan'kame sa tayi da kyau "to hubby na Allah sa a dace , anmman kamin alƙawarin cewa zaka dawo mu chigaba da rainon unborn namu,"




" kar kidamu a koyaushe ina tare dake ameen wanan ittace mace ta gari ," sanin logon matarshi yayi nan ya cire mata tunani da waswasin dake damunta, safiya nayi ya shirya mata kayanta da nashi ya fito tsaff dashi shiga motar shi yayi ya iso gidan ma'kobtan su






"Assallamu Alaikum" cewar Aminullahi yana shigowa samunsu yayi akan dining suna breakfast " ah ga d'an Albarka nan 'karaso mana ciki " cewar Daddy ganin da matarshi Samira ce ta mi'ke aunty Balki a d'akina zaki sau'ka ko ," murmurshi tayi don dai kar ta gwalle ta ba da'di yasa ta amsa mi'ka mata trolley Aminullahi yayi ta amsa ta hau samar bini dashi , da ido ya bita har saida INEEE ta lura da haka murmurshi manya tayi tace " gun tsaya kamar wasu gumaka" "ko iso dining table ayi breakfast daku Mana " cewar Mommy tana musu nuni .












Abunka da mai ciki tamkar bata chi abinchin gidan taba zama tayi ta gabza har Aminullahi yaji kunya, sallama da mutanin gidan yayi suka mai Rakiya har mota da adu'ah Allah bada nasarar nemo matar nan,








To fa sai dai muce all the best Mrs Aminullahi .






*****************************************




"waiyoo Allah mun shiga ukku mun kawo kanmu gidan mutuwar mu kullum da mutuwa ake tashi Mai Maryam tayi da ta chanchanchi muguwar kissa irrin wanan waiyoo Mommy na da man kin hannani zuwa gun nan anmman na mike 'karyar zani gidan bukin 'kawata a chan niger yau ga amfanin jin maganar iyayye gabaɗaya Ashe Mommy tasan mutuwa ta anan take yasa ta hanani zuwa duk zugin kune kawaye mussanm ma ke Sofie," Ummi ce tayi magamar tana kallon Sofie da ta zuba uban tagumi hararra ta dalla mata kana tace






" Kuma don ubanki sai naja 'kafarki nace sai kinzo ko , dukkan ku nafi ku shoga tashin hankali a ranar birthday na aka kashe babbar 'kawata ga Maryam ma da ado harda sar'kar gwal ammman aka cire mata kai akabar ganganr jiki a yashe kamar a wane film da na saba gani a gida, " fashewa da kuka na saman drower side tayi " wallahi duk bawan Nan bane. gaba na daga d'akin zuby sai na Maryam sai Sofie sai nawa a jire muki yakzu nema na kusan mutuwa idan aka kashe Sofie kina,"










daga saman gadon Sofie ta sau'ko "kan burau uban chan, ke moffy nece zan mutu ko kunya bakiji kina gayyamun to wallahi ƙarya ne banga uban da zai kashe ne in tsaya ba itta ma Maryam nin ai ganganchin sune ya zanga tokobi na tsaya bazan gudu ba,"










Moffy ce ta mi'ke tsaye "aikin banza anwa uwar kwarto fyd'e, ni kunga tafiya kowacce kawai tayi ta kanta anmman wanan abun sai mun lura sosai idan munason tsiratar da rayuwar mu, "






" ne kam an dai cuchi rayuwata wallahi Sofie Allah ya isa tsakanin na dake duk kice sillar jifane cikin wanan masifar da nabi maganar uwata ai da yamzu Ina Shan icecream hankali kwance , itta dai ta 'kifin shurun ta burinta kasai su bar Mata d'akin ta tashiga d'akin Maryam dun ta d'auko kayanta masu kyau tasha ado, don kayan Maryam na keana biyu Nan na musamman ne , bugun 'kofar d'akin akayi hakan yasa duk hankali su yayi kan 'kofar , bugawa aka Kuma yayi a karo ba biyu har rigi_rigin kumawa baya sukiye , Sofie ce tace " waye!!!? " cikin rawar muryarta.












Shiru sukaji chan akace idan bazaku bu'di ba zan shigo ta gini habawa ai gudu akafara moffy ce ta hanka'd'a Ummi har ta zube a'kasa tayi toilet, Sofie ce ta biyota garam zata rufe toilet non ta buge goshin Sofie da take cewa " don Allah bud'i na shiga ciki,." "wallahi ban bud'iwa ce Miki akayi Banda hankali kawai neme gun 'boya ,










Mime ce ta shiga cikin warldrop inda Sofie tayi 'kasan gado , ihu Ummi takiye kun ƙarya mun kafata ku taimaka ko 'boye ne Ina duk sun tafe sun barta ko tashi takasaye wasa da fittalar d'akin aka fara nan hankalin su ya tashi matukar gaske shikkinan yau ranar mutuwata ta zo Mommy, ke yafe mun , ban'kaja 'kofar akayi yarinya tagani i'yar 'karama Fara fatr kamar an shafamata farin 'kasa a jinkinta idon nan nata 'bola 'bola matsowa taye kusa da Ummi ta d'aga hanunta sama ta zare kanta , ta cire tayi baya , tafiya kan yakiye asama saitin kan Ummi yaye dake ihu adu'an ma takasa yi , razanani ihu ta buga wanda ya hargitsa i'yan matan,.










Kan ne yafara magana , haba Ummi tashi ke mayar min da kaina kinji ko bansan wa yacire mun shiva tashi ke gyrah min kaina",




" innahu min Sulaimaana wa innahu da sunan Allah, kukuki ganin mu bama ganin ku mu tsiratar da numfashin mu, " kiye mun Autar aljjanu" tun tsirawa sa dariya kainin yaye ganganr jikin ne ya matso hannu tasa ta mayar da kanta ta d'ago gadon da Sofie take ta wullar a 'kife sake tin tsirawa da dariyar tayi , sanan ta 'bacce ɓatt suma dukka biyun sukayi a gun ,












Security ne guda biyu da gudu sukaji sautin fa'duwar abu saurin zuwa gun sukayi suka zaro bindigar hannu tira 'kofar sukayi nan sukaga komai net kamar ko sauro bai zauna agunba balle d'an Adam da Ummi da Sofie kwamce agado kamar masu barchi qjiyar zuchiya suka sauke a tare suka rufe musu 'kofar,








Bayan wane lokachin kowacce ta fotoo a ma'boyarta tana son magana akan abunda tagani amman ya faskara Ummi da Sofie kuma kwanchiyar hankali ya 'kare musu gani sukiyi ko mafarki ne ko gaske ne oho nan kuwacce ta tatfi zuwa d'akin ta,




Da missalin 'karfe sha biyu na dare Mimee ce tafitoo d'akin ta cikin sand'a ta shiga wane d'akin mai kyau da yakasance ba makule kasamcewar tunda aka kashe Maryam ana binchiki a ciki shoga tayi ta kunna fittilla d'akin ta hango Waldrop bud'iwa taye cikin sand'a ta ga wasu kaya masu matikar kyau "oh ne Mimee ko ina Maryam ta saya kaya nan maau shigin kyau oho" d'aukar su tayi yayi guda goma ,ta ajiye su , tareda sa wane zazzafan riga tamkar sleeping drees tq w "hooo zanyi chiliing na gobe da su ta ajiyi a
saura 'kasan kayanta ta hau yin barchi hankali kwance ,










"Shegiya 'barauniyar kaya na kinyi kuskure d'aukan man ajiyata a wanan d'akin nan ko bil'adama Nan an xuba muku taurin kai , kayan na ne ba wacce ta isa ta d'auka min ," a razane Mimee ta farka ta fara kunna boom na side bed , daga 'kafa ta kafe Ido infa ta hango zara _zaratan farce masu muni da girma har takai saman kqnta wane uban ihu ta buga ta sake fitsari a shimfiɗ'ar ta , dariyar ta buga mata "keeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeee" zubewa Mimee tayi tafara kakarwa da yatsa ta nuna ta sama ta d'aga ta tafara shillo da ita a d'akin itta kuwa sai ihu takiye bud'i bakinta tayi tamkar zata had'iyi ta ganin cikin bqkin Mimee tayi nan ta hango jini kwaramye a cikin sa kamar yana mallala ya wanke godam sha'katawar nasu sanya farchin ta taye ta cikin chibyar ta ta zaro wasu kayan cikinta wahe tini ta zube a 'kasa ta zama matachiyyar gawa ,










Gaba-d'aya iyan gidan nan suka taro lallai lallai a musu hanyar cikin wanan gidan sha'katawar an fiddasu waje domin bazasu jure mutuwar mutum d'auki d'aya d'aya da ake musu ba nan wane ganin yau ma antashi da mummunar mutuwar Mimee, nan wane tsohon security ya gyrah murya yace " ba wanda zai bar gidan nan sai dai dukka mu mutu a cikin sa tunda naga mai kama da wata baiwar Allah da aka zallunta a chan shikaru baya a gidan nan nasan lokachin dawowar ta d'aukar fansa ya gabato , nakanji sautin muryar ta tana cewa zan dawo !!! zan dawo!!! d'aukar fansata duk daren dad'iwa,.....




Daga al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️💞💞💞💞💞💞








Share & comment fissabillilah 🥰



Barka da ranar juma'a , don't forget to read Suratul kahfi 🥰🥰*☠️💀 RUHI BIYU☠️💀*




*Littafin had'aka*💪



MALLAKIN




*©Fateemah Rabi'u (ZAHRA ROYAL STAR)*
&
*K'ANWAR SOJA*
























*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*








PAGE 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣




Tafiyar Aminullah da kwana biyu dare ne sosai wadda duhun sa yayi yawa wadda ko tafin hannunka baka iya gani




Ga wani hadari da yayi gaggami sai walk'iya ake wadda daga gani kasan koda yaushe ruwa na iya sakkowa,




Samira tayi d'ai-d'ai akan gado sai bacci take Iliham na kusa da ita wani ihu tayi ga mamakin ta ba wadda yajita gashi so take ta tashi amma ta kasa kamar in d'aure mata jiki so take ta tab'a Iliham dake kusa da ita tana kiran sunanta da k'arfi amma ina kwata-kwata muryar bata fita, wasu irin hawaye ne ke zuba daga fuskar ta daga kanta tayi sama wani zaro ido tayi duk da d'akin duhu ne walk'iyar da akai shiya taimaka mata ta hango abin saman silin d'in d'akin wannan yarinyar ce sama kamar fanka sai juyi take tana wage wargajejan bakin wadda yake d'auke da wasu irin hakura barasa kyan gani tana aiko ma da Samira wani kallo irin na gargad'in cewar basuji maganar ta ba,




Samira ku saboda da tsananin tsoro jitai jikinta ya kulle mararta ta juya wani irin ciwon ciki ne ya tasu mata lokacin jitayi al'adarta na bimata kama tasan ba lokacin take ba amma ta kusa amma wannan tsoro ya haifar mata da zowanta,




Juyi take so tayi saboda azabar da take ji na ciwon cikin su take tayi magana amma kamar an d'aure mata bakine gashi jikinta har wani rawa yake saboda azaba




Jitayi bakinta kamar an fizgo addu'a ta zata da k'arfi jitayi lokaci guda komai ya dawo dai-dai tashi tayi da sauri ta sauka tana tafiya a duduk'e har takai band'aki ta gyara jikinta sai murk'ususu take ta kwanta gan gado jitai kamar ina ja mata gashi hana mata dariya a saitin kunnanta haka ta kwana batai bacci ba har gari ya waye sai gaba nin asuba sana komai ya lafa mata wani baccin wahala ya sureta.




A wajan Aminullah kuwa koda ya isa hotal ya kama ya Kira wani abokinsa mai suna Jamilu koda yazo hotal bayan sun gaisa Aminullah ke mai bayanin cewa yazo neman wata matane cike da d'an mamaki Jamilu yace "to amma Allah yasa dai kana da picture d'inta da sauri Aminullah yace "ehh saboda na samu picture d'in a gina data zauna gashi ma ka gani" yana mik'a mai picture d'in




Kalla yayi lokaci guda ya zaro ido da sauri Aminullah yace "koka santa ne?" Cike da d'an mamaki yace "kware kuwa na santa a wata unguwa amma yanzu dai tashi muje da sauri anguwar Allah yasa mu dace"


Da sauri Aminullah ya tashi ya shirya suka d'au hanyar anguwar koda suka isa saida suka aika yaro yayi sallama da wadda yake cikin gida

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment