Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata yarinyar ce ta lek'o da sauri Aminullah yayi mata sallama amsawa tayi tana masu kallon rashin sani da sauri Aminullah da lura da haka yace "baiwar Allah munzo neman wata baiwar Allah ne a nan wadda muka ji labarin nan gidan take", ya idasa maganar yana nuna mata picture d'in matar d'an kallon tayi sosai tace Allah sarki Hafsat kenan amma kunyi rashin sa'a dan kuwa sun kwana biyu da tashi daga nan unguwar Gaskiya amma yayana kamar yasan inda suka koma amma yanzu yana Abuja wajan aiki sai dai inya dawo amma inaga sai nan da sati biyu ko uku in zaku iya jira to" ta idasa maganar tana kallon su,




Aminullah kuwa sauke ajiyar zuciya ya kasa cewa komai shidai mafatanshi Allah yasa yayan nata yasan inda Hafsat d'in take sai Jamilu ne yayi saurin cewa "ba matsala ki bamu number ki kota yayan naki mana zamu iya jira ai" da sauri tace "gaskiya yayana baya d'aukar number kokun kira ba lallai ma ku samai ba amma ga number ta indai ya iso zan sanar daku" "to shikenan mun gode fah" cewar Aminullah tafiya sukai cike da jimamin abun da fatan samunta nan kusa koya koma gida a warware wannan cekwakiya......






******************Da sauri mutanan wajan suka kalle sa ganin yayi katob'ara da sauri yace "ina nufin saifa kunyi taka tsantsan a gidan nan duk zaku iya wucewa duk wuce sukai jikinsu a sanyaye da nadamar zuwa wannan waje gashi suna su su koma gida amma ba hali sudai wannan tafiya ta zamar masu (BAK'AR TAFIYA Nah Meenat A Yandoma),






Shi kuwa security d'in zufa ya sharce yace dole mai gida yana doro a k'asar nan zan sanar dashi abin yake faruwa gashi ma kwata-kwata yaje yayi zamansa a wata k'asa yak'i dawowa yabar mutane da masifa,




Sa'adha kuwa yau kwata-kwata zazzabe ne ya rufe ta zaune Sameer yake yana lallaminta akan ta ci abinci wadda kallonsa take bai dad'e da fita ba dan samo mata abinci amma da fitar sa ya dawo tashi yayi ya shiga band'aki shuru-shuru bai fito ba jitai an bud'e k'ofar shigowa da sauri ta tashi zaune cike da gigicewa kanta ta faraji ya fara juyawa kallon k'ofar take Sameer ne ke shigowa da abinci hannunsa da alama yanzu ya sayo shi ya dawo kallonsa take tana kallon k'ofar band'aki kallon abincin da waccan a ajiye gani tayi ba komai wajan da sauri ta tashi tsaye ta dafe kanta da sauri Sameer ya kamata yana kiran sunanta "Sa'adha!!! Sa'adha!!! Lafiya kike kuwa? Tashi kisha magani ga abinci" gani yayi bata motsi cike da tashin hankali ya fara girgiza ta gani yayi suma tayi da sauri ya d'akko ruwa ya yayyafa mata wani numfashi taja k'ak'k'ame sa tayi cike da tsoro tace "Sameer kalar kafa na gani irinka ya zo da abinci wai inci kuma yana band'aki kaje ga duba" maganar take cike da fitar hayyaci gani yayi bata cikin hayyacinta d'an kwantar da ita yayi ya bud'e band'akin ba komai ciki da sauri ta zaro ido shin koda ta haukace ne wasu irin hawaye ne ya shiga bin k'uncinta da sauri Sameer ya dawo kusa da ita yace "please Sa'adha ki daina damuwa amma ba komai a d'akin nan ki daina tunani da yawa duk shi ke jawo miki haka" saida yaga hankalinta yad'an kwanta yace "bari inje ind'an watsa ruwa" ai da sauri ta tashi zunbur ta k'ak'k'ame shi tana kuka wai ba inda zashi ya barta ta k'ara ganin wani abun cike da tausayinta ya zauna yana k'ara lallab'ata cewar ba abinda zai sameta yanzu zai dawo sai ya da gaske da gyar ya fita ai kuwa kamar jira ake ya fita taji an bud'e band'aki za'a fito cike da tsananin tsoro take kallon k'ofar zuciyar ta sab'o da bugawar da take kamar ta faso girjinta ta fito..........✍️














*Fateemah Rabi'u ce (ZAHRA ROYAL STAR)*✍️✍️✍️






Share And Comment Fisabilillahi🙏🥰


























*☠️💀 RUHI BIYU☠️💀*
*Littafin had'aka
MALLAKIN




*©Fateemah Rabi'u (ZAHRA ROYAL STAR)*
&
*K'ANWAR SOJA*






















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*






15 AND 16




Bayan sati biyu yau Aminullahi ya kuma domin samun cikkin bayani akan yayyan yarinyar wayar sace ta dauki 'kara ya ajiye turare dayaki fisawa " sallama yayi nan naji yace " okay ya dawo ma kinan Alhamdullah ai daman yau ina shirin dawowa gidan naku , " murmurshi yayyi ya kashe wayan key kawai ya d'auka yayi gaba da abokin nasa .










Koda suka isa gidan sun sami yayyan nata cikin mutuntawa suka gaisa da girma ma juna nan ya gayyamai abunda ke tafi dashi da uzurin sa ," to babban magana Aminullahi tabbas nasan inda ta kuma anmman matsalar d'ayace ku bare gobe mu kama hanya Allah sa Kuma mu dace " ameen suka amsa , cikin alamu samun nasara , Aminullahi ya Kuma domin shiryawa.
























*****************************************








Cike da tsananin tsoro take kallon k'ofar zuciyar ta sab'o da bugawar da take kamar ta faso girjinta ta fito, jan bargon jikinta akayi da isa ma ratsa cikin 'gashi Jan 'kafafun ta ta nad'i shi da cikinta ta takure gu d'aya tana mai runtse da ido saboda kar ta bud'i idon taga ba dai_dai ba,




"Sa'adha ke tashi ga abinchin ke bazaki ce nawa ba wai ,?" jin an ambachi sunan ta da muryar Sameer yasa ta kanne ido d'aya ta Lego ihu ta buga ganin abinchin duk kan majizai da kunnamai cikin plate nin , dariya ya buga da yasa d'akin girgiza cikin sautin amo yace " fansa ta!!! fansa ta kice !!! kicee sillar komai ki fitooo sararri ko na hallaka illahirn gidan sha'katawar nan. " wanan sautin ya sa doddon kunnen Sa'adha da'ukewa gaba d'aya, bszstp ba tsammani ya nuna ta da yatsa ta bud'i kwalla_kwallan idanun ta tana lelo a sama , gogguwace mai tsanani 'karfi ta taso daga gidan sha'kawatar nepa ya d'auki , sai tsawa da walƙiya da ya razana illahirin mutanen dake rayuwa a wanan gidan labulle kowane d'aki na rawa da motsawa da 'karfinsa .










"Innalillahi wa ina iallhin raji'oun, annoba ta iso garimu shikkinan yau ma za'ayi kissan kai ko gawar wa zai bayyana a safiyar gobe Allah ka ceccemu ne fa tunda naga mai kama da wancan matar nasan cewa za'a tafka babban kuskure da yawaitan zubar jini a gidan nan , gashi Alhaji baya nan ko waya ta ma bai d'auka ba, ha'kika ya barmu cikin tashin hankali da masifu watarana zamu waye gari kowa sai ya mutu kai harta tsuntsaye idan sunbi wanan gidan ina sa ran zasu zama gawa"










Tsawar da aka buga ne ya sa tsoho dawo wa daga duniyar tunanin sa yana bargo yana buga dukan adu'a da yazo daga bakinsa haɗawa kawai yakiye




(may be harda adu'a shiga toilet 🤣).








Dai dai lokacin da na hango 'kiftawa inuwar dogon abu tamkar bishiyar kuka da ya ri'ga a cikin daji walƙiya ce ta haska chan naga fuskar Sa'adha tamkar wata zakanya sai hucce taki ta na zolo da duguwar harshinta dake waje wanda zaratan ha'kuran bakinta suka sauya kammani gaba-daya ido d'aya ya ma'kale a saman goshinta ,gashin kanta a barbaji ,sai zare ido take ,












Chan na hango wane security na bugun wata yarinya kyakyawar gaske da bazata wucce shikaru goma sha tara ba " ohh kun iya baiwa wasu masu kud'i gangan jikin ku muna ganin ku ,ko yau na ganki kina wanka da wane guy nan masu hannu da shuni, anmman dake mu gadin ku muke cewa akayi mike duwatsu ne mu bamajin sha'awar mace ,








D'ayan ya matso yana chan wandon jikinsa zuwa 'kasa wallahi oga kana 'bata mana time, mu ra'kashi kawai ai ansaba bani gu Ni nafara kamar kai kam da sauran ka dubi fa yanda, " bai gama maganar ba aka buga tsawa da ya basu mamaki " tunda uwata ta haifini yau naji sautin tsawar aradu kamar a ƙwaƙwalwa ta aka sauki ",












Tuni sun lafta ta da 'kasa duk sun biyu sun afka mata cikin mummunar yanayin rayuwar su , " oga duba kamar bata numfashi kai duk shigiyar yan'kanta nan ta kasa 'daukar maza biyu akan ta ashe ma sabuwa ce ," dariya yaye " kai ta mutu fa" le'kata yayi yayyafa mata ruwa " tabbas ta mutu oga to ya zamuyi " yauwa oga tunda ana kissa a gidan nan ai bamu da matsala mata náwa muka musu fyad'i kuma sirrin mu bai tunu ba",










Iskace tayi gaba dasu duk biyun suka fara shillo a sama juyawan da zasuyi suka hango gaba_daya ruwan dake sau'kowa ya zama jini mai muguwar wari da 'karni ,ihun oga ya buga , ( ihunka banza sunan wane gari kinan)




wujijjiga dasu akiye a sararin samaniya sai rusa ihu sukiye kansu ta had'a ta gura filli guda, ta zura hannu daga 'kasar chibiyar su ta 'balla musu gabansa daga hanji da jijjiyar da ya haɗa musu ihu mai razanarwa suka buga nan suka zube a 'kasa suna matattu,, dariya ta buga ta 'bacce 'batt ,










Ranar Monday da misalin karfe goma na safiya , jirgi mai 'kirar jeeb fara ce ta sau'ko daga kasar Dubai, security ne kusan goma cikin shigar suit da bakar shoe, su ka jira mota guda goma sha biyu , saukowa yakiye daga saman step na jirgin sanyaye yaki cikin white suit da white cover shoe ya sa sirrin glass a idon sa, Black beuty be Wanda girma yafa kamashi, dake mai kudi ne kamar d'an shikkara tallatin a duniya,










Tamau ya d'aure fuska security ya bude mai mota '"ya'laɓai barka da zuwa" karaf ya wankan ma manager gidan mari " wani irrin rashin hankali kukiyi a gidan sha'katawar tawa ace ssi kisssan kai akiyi a ciki mahaukata bazaku kashi makashin ba," ya'laɓai kayi haƙuri abun yafe 'karfin mu ne Bama sanin kissar sai nufa gawa kamar fatalwa ko aljannu ne" dariya ya fashe dashi " a duniya wayagaya muku akai fatalwa da aljjanu mahaukata kawai ne zabga fatalwa kuma sai na shige kowa yi ne,








Buɗi gate nin akayi dai dai da fitowar Sa'adha sa'kale da hannun Sameer ssi murmurshi yakiye nan ya fara bautawa da bodyguard suna taki Mai baya d'ago idon sa yayi dai dai da da:ga idon Sa'adha, ruɗiwa yayi lokacin guda ya nuna ta yatssa bakin sa na rawa ya zabura yace "....................✍️✍️✍️✍️






Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞








Comments and share please 🥰🙏














*☠️💀 RUHI BIYU☠️💀*




*Littafin had'aka*💪



MALLAKIN




*©Fateemah Rabi'u (ZAHRA ROYAL STAR)*
&
*K'ANWAR SOJA*


























*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*




PAGE 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣




Koda Aminullah ya shiryo daga shi sai wadda zai rakashi wato Salim kenan dan Jamilu yayi tafiya,




Kama hanya sukai a cikin mota suna d'an tattauna abin da Salim wadda shima abun ya girgiza sa kuma yayi niyar bada taimako dan yace harda shi za'a koma dan magance matsalar,


Salim ya kasan kyakkyawan gaske ne matashi ne wadda bai wuce shekara 29 ba zuwa 30 Yana da barkwanci sosai da san mutane yana tausayi kamar mace d'abi'arsa ce wannan.




Koda suka isa gidan shiga kawai sukai dan Salim ya santa sosai da jikokin da take rik'e dasu sun san Salim sosai shi yasa suka shiga kai tsaye cike da mamaki jikanyarta mai suna Ikilima tace "Ya Salim kaine yau da kanka?" "Bari kedai k'anwata mune tafe Allah yasa dai Innah Hafsat tana nan?" Ya fad'a dai-dai sun zauna kan kojera,


D'akko ruwa tayi da lemo tana ajiye masu tace "ai kuwa kunyi sa'a tana nan kasan bata lafiya sosai so tana nan bari nasa Nahna ta taimaka mu d'an kamota saboda da k'afarta bata iya takawa sosai" ta idasa tana kiran Nahna!!! Nahna!!!" "Na'am" ta amsa tana k'araso wa cike da girmamawa ta gaidasu amsawa sukai cike da mutumtawa Ikilima tace "muje ciki suna so suga Innah ne" to ta amsa shiga sukai ba'a wani dad'e ba suka fiddo ta zaunar da ita sukai kan kujera,


Aminullah dake kallonta cike da tausayawa dan Gsky ta tsofa sosai a ziciyarsa kuwa cewa gaskiya da alama abinda ya faro a gidan nan da dad'ewa katse tunanin yayi da gaida ta amsawa tayi cike da dattako tana jan Salim kan cewa ya yada su.


Bayan nan Salim ya fara koro mata bayani abinda ya kawosu ai Innah Hafsat najin wannan magana tari ya sark'eta cike da tsoron abin a ranta na shekarun da suka shud'e, da sauri Ikilima ta bata ruwa tana cewa "wannan abun zai yiwu kuwa bafa asu ana takura mata bakwa ganin jikin nata sai a hankali dan Allah ko rabo da ita da wannan labarin pls" ta idasa maganar cike da tausayin Kakar tasu,


Da sauri Innah Hafsat tace "a'a barsu zan gaya masu komai dan gane da abinda ya faro a cikin wannan gida duk da na tsofa hakan baisa na manta da komai ba saboda da tsananin rud'anin dake cikin labarin"


Ta idasa maganar tana kallon su gyara zama sukai sosai suna fuskantarta inda su Ikilima suka basu waje, ta fara da cewa


*WAIWAYE*


A wancan lokacin na kasan nida iyaye na muna makwaftaka da wannan gidan wadda wasu mutane ke zaune mai gidan sunansa Abubakar da matarsa mai suna Badeeyya suna da d'iya mace mai suna Hanan sai cikin dake jikin Badeeyya wadda haihuwa yau ko gobe Badeeyya tana kirki Gaskiya da d'iyarta kyakkyawa wadda bata wuce shekara biyar 5 ba suna da wata bishiya a wajan gidan wadda take fidda wasu irin firanni masu k'amshi na kasan ina sun wannan fulawowiyin Ina yawan zuwa dumin d'iba idan naje mijinta Abubakar ya kasance bayada sakin fuska ko kad'an baya dariya yana bak'ar zuciya a lokacin yana wani buri a ransa na cewa kota halin yayane saifa an haifar mai namiji wadda akan yasa shi ya shiga aikata Asiri shirka wadda ya kasance ya zama bukan kansa da kansa wadda wannan buri indai zai cika sa saiya salwantar da d'iya mace wadda bata wuce shekara biyar 5 ba dan nima lokacin bana wuce shekara biyar d'in,


A kullum innazo yana zaremin ido dasan kamani danya cika wannan bak'in k'od'irin a kaina saida Allah baya basa sa'a a kaina gashi a lokacin saura kwana d'aya ayi DARE BIYU kuma a wannan daren zai cika burinsa,


Kamar kullum garin saiyayi lullufe daka gani kasan cewa dare biyun za'ai wadda anata sanarwa a redeo da talabishan cewa kuwa karya fita a wannan rana sai dai ni ganin cewa kusane na fita domin d'ebo fulawowiyi koda na fita yana zaune wajan takowa yayi kusa dani ban sani ba naji an kamani wutsil-wutsil na farayi ina kuka dan ina ba'ain tsoron sa kamar daga sama mukaji muryar Badeeyya tana cewa "haba ka saketa mana zo maza ki d'iba mi kake hakane Wai" ta idasa tana jawoni ko d'iba banyi ba na fizge na nufi wani waje na lab'e ta wajan gidan dan lokacin kamar ance kar in tafi,


Kallon matarsa yake cike da b'acin rai tana so ta ruguza mai harka duk yadda za'ai zaifa ya ciki burinsa ko akan d'iyarsa ne kuwa wani murmushi yayi jin ya samu mafita da sauri ya koma gida Badeeyya kuwa ta d'an tsaya tana kallon yanayin garin dake had'ewa rana na shiga cikin duhu,


A cikin gida kuwa Hanan ce zaune sai wasanta take tana ganin Babanta ta tashi cike da murna ta nufe shi kama hannunta yayi yace "kina so muyi wasa?" Cike da yarinyata ta amsa tana tsalle ya k'ara cewa "to ki runtse idonki saina ce ki bud'e sana" Allah sarki ita kuwa yarinya ganin Babanta ne bata san mizai faru ba ta runtse, kama hannunta yayi suna tayi har yakai sai tin wani d'akinsa na tsafi ba wadda ke shiga d'ikin saishi ko matarsa bata isa ta shiga d'akin ba sunsha fad'a da ita akan d'akin,




Suna shiga ya zaunar da ita akan wani abu ina k'ara mata wasa akan karta bud'e idanuwanta fa wata sharb'eb'iyar wuk'a ya d'akko saitin yarinyar ya tsaya wasu irin surutai ya fara a hankali wani irin yare yana karanto abubuwan tsafinsa dai-dai dare ya gama mamaye garin dai-dai lokacin ya daga wannan wuk'ar ya d'aukewa yarinyar sa kai gaba d'aya jani ne ya fara tartsatso masa har fuskarsa dai-dai lokacin Badeeyya taji gabanta ya yanke ya fad'i nufu cikin gidan tayi da sauri kamar ana ingizata ta nufi d'akin da bata tab'a shiga ba tana shiga dai-dai lokacin da yake salwantar da rayuwar d'iyarsa wani irin aban ihu ta buga ta tana zaro ido cike da tsananin tsoro da mamaki take takawa a hankali har taje gaban da gawar d'iyarta shi cike da rashin tsoro da bushewar zuciya yake kallonta ba alamar nadama a idanuwansa cike da tsawa Badeeyya ta nunasa da yatsa tace "mi kayi haka mi kaiwa d'iyarkahhhh " cike da tsawa da fitar hayyaci kuka take sosai har tana shid'ewa cike da rashin tsoro ya fara bata amsa da kuma burin da zai cika cike da mamaki da jahilci take kallon sa d'aukar wuk'ar daya kashe mata d'iya tayi tana nunasa da ita tace "ashe kae dabbane ban sani ba ashe ina tare da k'asurgumin jahili ban sani ba a yau nayi danasanin kasancewa tare dakai ba burinka ka haifi da namiji ba to bari in kashe kaina da abinda yake ciki na sai muga ta inda burin naka zai cika" da gama maganar ta ta d'aga wuk'ar ta chakama cikinta ta lume chan ciki har saida ta b'ollo bayanta fad'uwa tayi wajan ko shurawa bataiba wani abun ihu ya buga yana k'arasuwa wajanta amma ina ta riga ta aiwatar wani ihu ya sake yi wadda har gidan da dajin na girgiza fitowa yayi shi kuma ya nufi wata rijiya mai zurfin gaske wadda ke nesa da gidan saida ya waiga baiga kuwa sana yace "nima zan mutu kamar yadda kuka mutu amma wllhy saina dawo saina cika burina ko RUHI na zai sa salama" yana gama fad'ar haka ya fad'a rijiyar,


Ni kuwa da komai ya faru a idona tsoro ne ya hanani motsi dan har fitsari na saki koda na koma gida a gigice na matsama iyayena kan cewa mubar wajan da gidan kwata-kwata mu koma cikin gari dama ninasa mu zauna wajan iyayena suna sona sosai shi yasa ko kwana d'aya bamu k'araba muka bar wajan ba shiri.




Back to story


Ta idasa labarin cike da jimami da alhili har wata zufa take, Aminullah kuwa da Salim baki ya k'ara mutuwa sai gumi suke wannan labari ya girgiza su matuk'a gaya basu tab'a tunanin haka abin yake ba,


Godiya sukai mata sosai sana sukai sallama koda suka fito Aminullah yace "to Abokina banga ta zama ba yanzu hanyar gida zan kama domin sanar dasu komai" da sauri Salim yace "tare zamu dai inshallah"


Ai kuwa kamar yadda sukace Salim saida ya koma gida ya shirya sana saka d'au hanyar gida basu wani dad'e ba suka isa kai tsaye gidan su Samira suka nufa daf da zasu shiga gidan sukaga wannan Rauhanin tsaye cike da d'an mamaki Aminullah yake kallonsa sai kuma ya tuna bafa mutum bane , Rauhanin yace "ai nima yanzu nasan labarin dan tare dani mukaje dan dai nasa bazaku iya gani naba" cike da kawar da mamakin dake ransu dan har Salim yasan labarin Rauhanin su duka suka rank'aya cikin gidan,




Koda suka isa sunyi sa'a kuwa duk suna falon Samira da duk ta d'an rame ai kuwa suna shigowa ba inda idonta ya sauka sai akan Salim gabanta ne taji ya fad'i shima a wajansa hakane tunda ya d'ora idonsa a kanta yaji wani irin tausayinta har cikin ransa zaunawa sukai suna gaisawa inda Innee tana ganin mutunan nan ta tsuke bakinta tayi shuru da tana shirin yin magana bayan sun zauna Daddy da Mommy suka fara tanbayar Aminullah ya hanya bayan ya amsa ya gyra zama yace " to anyi nasara dai Alhmdllhi an samo tarihin gidan nan kuma yanzu zan sanar da ku" gyara zama sukai gaba d'aya suna bada hankalin su Aminullah ya fara zayyano masu komai abinda Inna Hafsat ta sanar dasu game da abinda ya faru gidan da gama bada labarin kowa na falon saida ya girgiza da jin wannan murd'and'an abu Samira kuwa dake tsaye saboda labarin ya gigita ta har takai da mik'ewa tsaye jirine ta fara gani dishi-dishi fad'uwa tayi a sume da sauri Salim dake kusa da ita da saurin dabai san ya iyaba ya tare ta hannunsa.........








****************** Alhaji Adam kuwa daya zabura yana nuna Sa'adha zaro wata bindiga yayi yana nunata da ita yana cewa "baki mutu ba ashe to bari na kashe ki kona k'ara kashe ki" ya idasa yana zazzare ido da sauri Sameer ya shiga tsakiya yana cewa "ya hakan Alhaji mi kake cewa ne? wannan fa ba wadda kake nufi bace" dai-dai ya idasa maganar wani malami mai kamala yana isowa security d'in nan yaje ya kirasa dan wannan abun dole sai da malami Sa'adha kuwa dake b'oye bayan Sameer jikinta sai rawa yake,


Koda malamin ya karanci abin yace "Alhaji Adam dole fa saika bamu had'i kai zan kira ita mai wannan aikin dan wannan yarinya ba ita bace kamace kawai cike da gamsuwa,


Malamin ya fara karanto addu'oi da ayoyin al'k'ur ani wata irin guguwace ta turnik'e ila hirin wajan da wata k'ara mai firgitar wa Cike da wata amon murya wadda saita sa mutum fitsari naji ta fara magan a a mamakina a jikin Sameer ta bayyana da sauri Sa'adha dake kusa dashi ta matsa har tana shirin fad'uwa saboda gigicewa tace "miye na wani kirana mlm mi kake so da har ka kirani?" Mlm kuwa cike da malinta yace "shin miye dalilinki na bayya na jikin bawan Allah? Sana miye dalilinki na kashe mutane eyee?" Ya idasa ransa a d'an bace wata irin dariya mai amsa kuwwa ta shek'e da ita cike da wata irin murya wadda ta gauraye gaba d'aya gidan tace "d'aukar fansahhhh d'aukar fansahhhh mn amma yanzu zan sanar dakai mafarin labarin daya sa ni wannan d'aukar fansar" mlm yace "muna sauraranki cike da raunin abunda ya faru da ita ta fara bada labari duk a cikin Sameer take magana.


*WAIWAYE*


Ni dai sunana Nurulhuda Alhaji Adam mijina nane tun asali auran Soyayya mukai dashi ya na sona sosai muna rayuwarmu a wannan gida cike da farin-ciki sai dai mi lokaci guda Adam ya fara chanza halaye ina ganin sauyi tattare dashi baya bani hakkina na aure kullum innayi korafi sai yace na cika jaraba da yawa yayi tsaki ya juyamin baya ya kwana ashe ban sani ba mijina ya fara bin matan banza ne ni banda labari kamar kullum yauma saida ga mamakina ina nemansa cikin Soyayya ya biya min buk'atata yana lallab'a ni kan cewa gobe za'a kaine sayayya domin yana so ya faranta min naji dad'i haka sosai sai dae ban sani ba ashe wata karuwarsa zai kawo a gidan baiso na sani ne a wannan daren ne ni kuma na samu ciki wadda ni kaina bansan dashi ba,




Washe gari kuwa kamar yadda yace bayan na shirya yana zaune nace "ya gana baka shirya bane?" Wani kallo yayi min yace "No ai bada ni za'aba kije kawai driver ya kaiki" banji dad'i ba amma haka na hakura muka wuce bayan tafiya kuwa karuwar tasa ta zu suka shige d'akina na sunna suna aikata masha'arsu akan gado na na sannu baiyi zaton dawowa ta da wuriba dan in na tafi sayayya ina dad'ewa sai dae wannan Karan banyi ba,




Koda na dawo da farin-ciki na na fad'a d'akin wani irin salati naja ina runtse idanuwana zuciya ta na bugawa da sauri shi kuwa cike da borin kunya ya tashi yasa kayansa karuwar ma da gudu tabar gidan kuka nake sosai zuciya ta na wani irin zafi nace "ashe ma'ana ta kake ci shin mina rageka dashi Adam ka fad'amin?" Tana kama kwalar rigarsa tana kuka iya k'arfinta shi kuwa wata

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment