Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyar da aure maryam tafara laulayin ciki,murna gurin farouk da hajiya se wanda yagani,dan daga gidansu gidanta suka nufa,anan farouk yay mata albishir.

Ayko zagaye maryam suka shigayi hajiya na bada baiti farouk na amshi,maryam wacce yanzu itama ta saba da abun dariyar farouk da hajiya dan haka tana daga zaune tana musu tafi sukuma suna wakarsu.

Kowa a dangin maryam yana tayata murna da samun soyayyar miji data suruka ahade wanda bakasafai aka fiye samuba.

Cikin maryam me laulayine,hakanne yasa ta koma gidan hajiya da zama,farouk shima komawa yayi,acewarshi shima baze zaunaba.

Yau maryam ce zaune tana cin goribarta datake jinta kamar nama dan dadi,farouk yashigo inda take.

kallon gabanta yayi yaga taci kwallon goribar sunkai biyar ga na shida a hannunta ,

da sauri ya karasa inda take,ya kwace goribar sannan yace.

"wlh ya isheki haka baby taya zaki zauna kita durawa cikinki tukar katako me siga,wlh baze yiwuba,kibari in kin haifemin dana sekici gaba da ci "

maryam wacce ke shirin yin kuka da kyar tace.

"baby kayiwa girman Allah kabani,nima bayin kaina bane kataimaka"

"wlh bazan baki ba sede kici wani abun ba wannan ba"

Yunkurawa tayi dakyar,tamike tafara binshi tana rokonshi ayko ficewa yayi da gudu da ledar goribar,zeje yakaiwa hajiya.

Binshi tayi itama tana kuka,yabata amman yaki.

A kitchen suka samu hajiya tana soyawa maryam manjan da zataci danwake.

"yauwa hajiya,don Allah kalli haukar da maryam takeyi,tasaka goruba agaba se ci takeyi,sekace bata da hankali"

"hajiya don Allah kice yabani"cewar maryam tana kuka

"zaka bata ko sena bata maka,lokacin cikinka mahaifinka buhu guda ya ajiyemin na gorubar,tundaga wata uku har na haifeka ban dena ciba"cewar hajiya.

"dankari kice goruba na nada shiyasa lokuta da dama se inji ina warinta ashe itace ta ginani,ni Allah ma yataimakeni bata yimin tsuroba,to ni bazaa ci a ba dana ba Allah hajiya"yafadi sanda yaruga waje abinsa riƙe da ledar.

Kuka maryam zatayi hajiya ta jawota ta zaunar daita ta miƙo mata ɗan wakenta.

tuni ta mance,da zancan goruba,tashiga zabgawa danwakenta yaji tana ci.

********

Ranar da maryam zata haihu ba hajiyaba ba farouk ba dukansu kuka suke,yan uwan maryam ne ke karfafa musu guiwa.

Ayko cikin kankanin lokaci,ta haifo yaranta duka mata masu tsananin kyau.

fadin murnar da sukayi yazama kauyanci.


hajiya rasa inda zatasa jikokin nata tayi,wayyo rayuwa,taimusu dadi.

Ranar suna anyi bidiri,inda yara suka ci sunan kakanninsu mata,amman suna kiransu,da,khairat,da kausar.
Uku the readers_p.m.l and

A duniya in kanason ganin bacin ran farouk kataɓa wainnan yaya,son da yake musu har tsoro yakeba maryam,dan har ita data haifesu inta tabasu rufe ido yake yaci mutuncinta.

Bayan shekaru huɗu da haihuwar su twins,Maryam tasake samun wani cikin inda har ya isa haihuwama.

*********

Yau maryam ta tashi da nakuda,da sauri suka nufi asibiti,

Ta jima tana nakudar,duk abinda yadace amata anyi amman ta gaza haihuwa da kanta,hakanne yasa,aka yanke shawarar yimata cs.

farouk yagaza shiga cs din se wani likitanne yashiga,inda akayi cs ɗin a saa aka ciro mata yarinyar ta kyakkyawa me kama da ita.

Bayan ankaita dakin hutune,dayake ana mata karinjinibayan ta farka ta nemi ganin farouk.

Yana zuwa tasamishi kuka shima kukan yakeyi,dan likitan ya shaida mishi,tasamu matsala sede atayata da addua.

Cikin kuka maryam tace akawo mata su khairat,ba musu aka shigo dasu.

kama hannun farouk tayi dayake ta kuka,tace cikin kuka.

"Farouk gasunan,nasan kana sonsu,nafi kowa sanin hakan,amman duk da haka zan barmaka amanarsu,don Allah farouk ko bayan raina karka baesu sui kukan rashina don Allah,ga kuma wannan jaririya farouk kazamo musu uwa da uba don Allah,duk randa kabarsu sukayi kukan mutuwata,farouk kaida Allah
*AMANA NA BARMAKA*"

Tarine yafara sarketa,da sauri farouk ya tallafota yana kuka yake fadin

"ciwo ba mutuwa bace maryam zaki tashi,bazaki mutu kibar ni ba don Allah kidawo cikin hayyacinki,amanarki kuma na amsa ko da ranki,pls kidena fatan mutuwa"

Jin da yayi tayi nauyi a hannunsane yasa yayi gaggawar dago fuskarsa yana kallonta.

Cikarshi likitane yasa duba daya yamata ya fahimci ta amsa kiran Allah.

wata kara yasaki,shima ya yanke jiki ya fadi agurin.

maaikatan gurinne suka rufu akansa suna ceto rayuwarshi.

Hajiya ma jin mutuwar maryam seda ta suma.


Haka aka tafi da gawar maryam gida akamata wanka aka sallaceta,aka kaita gidanta na gaskiya,inda mahaifinta da kanshi yasakata akabarinta.

Farouk ko yana Asibiti rai a hannun Allah dan ko numfashi ta oxygen yakeyinsa.

����������������
*AMANA TA BARMIN*
����������������


Zahra Surbajo


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.

❄❄❄❄❄❄❄❄
*idan kaji gangami da labari,rigiji gabji babbar gayya,inkaji ki gudu s gudu ne be zoba,me akwai shiyake rabo.*
*Natayaki murnar kammala littafin KYAUTAR ALLAH,HALIMATU KANGIWA(AUNTY HALILOSS)Allah ya kara basira da daukaka,gskiya kinyi namijin kokari,wajen nishadantarwa da kum fadakarwa,kin bata hankalin dare gurin tsara labarin,Allah yasa kifi haka Surbajonki ce iya wuya ana tare*


*13-14*


Ba wanda mutuwar maryam bata girgizashi ba.


Seda farouk ya kwashe watanni biyu a Asibiti besan inda kanshi yakeba,seda hajiya ta haɗa da rokon Allah sannan Ya dawo cikin natsuwarshi.

kuka farouk ba irin wanda bayayi na rashin maryam,tuni kamanninshi suka canja,ya rame yayi baki beda aykin yi sena kuka,jaririyar sunan maryam aka maidar mata suna kiranta little.

kowa ya kalli farouk da yayanshi se ya tausaya musu,suma yaran ullum cikin kiran mamansu suke.


Hajiya kullum itace ke ɗawainiya da yaran,dan ko little bata ba dangin maryam ba.


**********

*Bayan shekara biyu.*


yanzu ba laifi farouk ya warware yana cigaba da harkokinsa,yaransa ko ko ransa beso kamarsu.

Hajiya na tayashi rike amanar maryam,koda wasa basa son bacin ran yaran.

little ko tuni take tafiyarta tayi wayonta.

Dan har ansata play class,yayinda su khairat suke primary one.

Hajiya tasha tuntubar farouk akan yayi aure,amman sede yasamata kuka yabar gurin,yana fita yayanshi ze kwasa da darduma,su tafi gurin maryam a makabarta,ranar can zasu wuni,sel laasar zasu dawo.

Daga haka se yamaida abun ibada,duk ranar jumaa,dasu zeje masallacin jummaa,da an sakko,se suwuce makabarta ziyarar maryam.


Duk sanda zakaga faraa a fuskar farouk yana gaban kabarin maryam ne,zamansa agurinne kawai yake kwantar da hankalinshi.


Hajiya abun takaisu ga tasa farouk agaba tana kuka tana rokonshi yayi aure,sabida tana tsoron ta mutu farouk beda me rike masa yaransa.


Ganin kullum hajiya,cikin yin kukane aykinta,yasa farouk fara tunanin wacce ze aura.

inda ya kwantarwa hajiya hankali da cewa zeyi auran.

***********


Yau yana zaune a office,segashi anshigo da wata mara lafiya emmergency.

Bayan ya dubatane yasamu,ashe ciwon zuciyane yakamata one time.

Koda ya tambayi wainda suka kawota abunda ya janyo mata ciwon cewa sukayi cikin kuka.

"yau auranta saura sati biyu shine dangin mijin dayake masu kudine sukace basu amince ya auri yar talakaba,to shine da taji labarin ta yanke jiki ta faɗi".

Sosai yatausayawa yarinyar.

mahaifinta yaja gefe yace masa.

"Baba in na nemi auran yarka zaka bani,nanda sati biyun inyaso se a aura dani kenan.?"

Kuka uban yasa yana faɗin.

"Yaro na gode maka,wlh bansan da bakin da zanyima godiyaba,kataimakeni kuma kafitar dani kunya"


Ayko hakan akayi,dan sanda farouk yakaiwa hajiya zancan,sosai tayi murna,bincike sukayi suka tabbatar da nagartar yarinyar,dan haka cikin sati biyu aka daura auran,farouk da amaryarsa,Aisha.


Dayake har lokacin tana Asibiti,bata warkeba,koda aka fada mata farouk ya aureta sosai taji daɗin baiwar da Allah yamata,narasa wani kuma tasamu wani.

Sati uku da daura aure aka kawo amarya gidanta.


Ranar hajiya tafi kowa jin daɗi,da hakan,shiko yana ɗaka ya kulle kanshi se kuka yake,dan gani yake yaci amanar maryam.

Be fitoba seda yaji gidan yayi shuru alamar kowa ya watse.

Dakin Aisha yashiga inda yasameta zaune tana kuka.

kan gadon yahau ya zauna yafara rarrashinta,da kyar tayi shuru.

Sallah sukayi,sannan suka kwanta.


Jin mace kusa dashi ne kuma mallakinsa yasa shaawarsa motsawa,duk yadda yaso ya daure ya kasa,seda ya kusanci Aisha A ranar.

sosai yaji daɗin samunta budurwa,haka yayta riritata har garin Allah ya waye.

Suko su khairat ranar basubar hajiya tayi bacciba dan dukansu kuka suke mata dan tunda maryam ta rasu tare suke kwana dashi a gado ɗaya,shiyasa suka kasa bacci.

Ayko da sassafe,ko wanka sunki yarda tayi musu sude daddyn su,hakan yasa da zaa kaiwa su farouk abincin safe ta tarkata dasu aka tafi.

Sanda suka shigo falon yayi daidai da fitowar farouk da Aisha daga ɗakin cikin kwalliya,Aisha ce agaba yana binta abaya,ita kuma se tafiyar daukar hankali take.


Su khairat suna hango daddynsu,suka hada baki gurin fadin

"daddy daddy daddy"suka kwasa da gudu zuwa gurinshi,suna kuka.

Ay farouk yana hangosu,jikinshi har rawa yake dan ya kosa yaji ɗuminsu ajikinshi,yaji kuma abinda yasasu kukan,ga kuma Aisha a gabanshi suna sakkowa daga kan stairs se wani yauki takeyi,dayake hankalin farouk yagama tashi besan sanda ya angaje Aisha ba ya isa gurin, yayanshi,itako Aisha gangarowa tafarayi tundaga gurin har zuwa kasa,jikake.
tuuum��ta daku da tiles.

farouk bedamu da waigowa yaga meya fado ba,gurin yayansi yaje yarungumesu yana shafa kansu,tunkan yaji me aka musu shima yafara hawayen.

cikin kuka kausar tace.

"daddy shine jiya bakazo munyi bacciba,ina katafi kabarmu?"

wasu hawayene suka sake zubo masa,yace.

"kuyi hakuri,bacci ne ya ɗaukeni anan banxoba,amman bazan sakeba insha Allahu"

Rungumeshi sukayi suna fadin.

"we love you so much dad"

tausayinsune yakamashi na ganin tun baa je ko ina ba auran dayayi yanaso ya shiga tsakaninshi da yayanshi,dan haka dole ze san abinda yakeyi dan baze yarda da abinda zesa masa yaya kuka ba.

itako Aisha,targade tayi kafa,asakamako. faɗuwar,ita ta dauka wani abune yasamu yaran dayasa ya gigice haka kawai se taji ashema zancan banzane,bakin cikine yasa tamike tana ɗingisa kafa ta koma saman tana kukan takaici.


Shiko farouk yama manta da ita,bare yasan ya yar da ita,har tayo rauni.

hankalinshi nakan [10:40, 14/09/2017] ‪+234 803 698 6494‬: ����������������
*AMANA TA BARMIN*
����������������


Zahra Surbajo


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*15-16*


Farouk hankalinshi be kwantaba,seda yaga yayiwa yaranshi wanka ya shirya su sunci abinci sannan ya kunna musu cartoon,ya haura sama dan ya shirya shima.

Se alokacin ya tuno da Aisha,dan haka ɗakinta ya nufa,da sallamarsa yashiga dakin,kwance ya hangota,tana kuka ta riƙe ƙafarta.

Da sauri yanufeta,ya ɗagota yana tambayarta abunda ya sameta,cikin kuka ta nuna mishi kafarta wacce har ta fara kumbura.

"garin yaya kikaji ciwo Aisha?"

"kaine katureni na faɗi"ta bashi amsa tana kuka.

Se alokacin yatuno da yaji karar faɗuwar abu dazu ashe itace.

Cike dajin kunya yafara rarrashinta.


Dayake ya iya gyaran targaɗan gyara mata yayi tana ta zuba ihu.

Duk tayi gumi hakanne yasa,ya dauketa zuwa toilet yafara yimata wanka,suna cikin wankan ya saba mata sabulu a fuska,ya jiyo karar,little a falo,a 360 yafice yabar Aisha da sabulu a fuska.

Koda yaje se yasamu,khairat ce wai ta canja musu channel shiyasa take kukan.

Ze saka Mata wanda takeso,suma su khairat sukasa kuka hakanne yasa ya ɗauketa yakaita ɗakinshi yasaka mata wanda takeson.

itako Aisha bakin cikin daya rufeta baze misaltuba,wai kwananta daya gidan miji tafara fuskantar matsala,sabida waincan shegun yaran,to wlh baze yiwuba dole in ɗauki mataki.

karasa wankan tayi tafito da kanta ta shirya,ba abinda yake bata haushi,se lura da tayi farouk ɗan soyayya ne amman wainnan yayan nashi zasu hanata cin gajiyar soyayyar.

Falo ta fito inda tasamu su kausar suna kallo koda tafito cikinsu ba wacce ta kalleta bare tasa ran zasu gaisheta.

cike da mamakinsu ta wuce dinning taci abinci,sannan ta dawo falon,tana zama suka mike da gudu suka nufi dakin babansu.

lokacin wanka,yafito ya shirya,sannan ya dauko little,a kafada ya rike hannun khausar,khairat nabinsu a baya suka dawo falon.

Nanfa suka shiga wasa da yaran nashi hankalinshi kwance beda damuwar komai tunda yayanshi nacikin farinciki.


*********

Bayan wata uku,Aisha sam bata da kwanciyar hankali,halin ko in kulan farouk yafara isarta,dan yanzu takai,sede ya sato jiki yazo gurinta cikin dare,kuma ko yana tsaka da saduwa da ita yajiyo kukan daya cikinsu ze zare jikinshi ya maida kayanshi,ya bar dakin.

Irin su kafi shayinnnan da akeyi da safe duk Aisha bata sansuba,ga shi su kausar tamkar yaran turawa gurin barna da rashin jin magana,dan in tadaga murya sukayi kuka yanzu farouk zezo yafara balai wuyan shi yana tsawo kamar zakara.


Duk irin barnar da sukayi agurinshi,ba barna bace,kuma bata isa ta kai kararsu gurinshiba,hakanne yasa Aisha fara hukuntasu in baya gidan inda bayan tamusu shegen duka sannan ta zayyano musu rules kamar haka.

"In bada rana ba inna kuma ganinku kunzo gurin daddynku,ko kun kirashi sekunci ubanku,kuma duk wacce ta faɗamishi abunda nai muku sena yankata"ta karasa batun tana jan kunnuwansu.

Suko se gyaɗa kai sukeyi,suna bata hakuri.


Tundaga lokacin Aisha tasamu yencin zama da mijinta,dan maganin bacci ta siyo,tana ganin yakusa dawowa,dukansu zata bisu ta basu susha,suita bacci,dan haka koya leka yaga suna bacci baya damuwa,se suje susha soyayyarsu da Aishan shi.

Katan guda ta siya na maganin baccin ta boye.

Yau farouk a hanyarshi ta zuwa office motarshi ta tsaya,ganin beyi nisa bane,yasa yahau napep ya dawo dashi gida dan yaɗauki wata motar.

Bayan fitarshi,Aisha ta taso su kausar,dagasu se pant pant,tasasu nilldown,harda little,tana tambayarsu wanda yayi fitsarin kwance acikinsu.

Kuka sukeyi sun kasa bata amsa hakanne ya tunzura,Aisha tafara zabga musu bulalar hannunta,nanfa suka shiga ihu,

Ana haka,farouk yashigo falon da gudunshi sabida juyo kukan yaran nashi da yayi.

Wani uban tsalle ya yi ya dira gaban Aisha,tana ganinshi ta yar da bulalar tafara bashi hakuri,barin makauniya yashiga yi da ita,yana kuka yake faɗin.

"kin cuceni Aisha,maryam fa Amana ta barmin na wainnan yaran amman dan zalinci irin naki kika sasu agaba kina duka wlh banyafe miki ba yanzu base anjimaba ki je gidanku nasakeki saki daya,na sakeki saki biyu na sakeki saki uku,kificemin daga gida"

Koda yay sakin bedana dukan taba seda ya farfasa mata jiki itama.

Aisha tayi danasanin taɓa masa yara,ba kadanba,wannan wanne irin abun kunyane aure wata hudu har an saketa saki irin wanda babu kome acikinsa.

Gurinsu kausar yanufa dasuke zaune sunata kuka,dubansa yakai jikinsu,duk ta fashe musu shi da bulala,hawayene zafafa suke biyo kumatunsa,gurin little yakai dubansa,agigice yayi kanta,kwance take numfashinta na fita da kyar.

Agigice ya haura ɗakinshi ya dauko kayan ayki yashiga ceto rayuwarta.

Da kyar yasamu numfashinta ya daidaita.

Haka Aisha ta haɗa yanata yanata tafice agidan tana kukn danasani,ta nufi gidan iyayenta.


Muje zuwa


surbajo for life.
[17:54, 14/09/2017] ‪+234 803 698 6494‬: ����������������
*AMANA TA BARMIN*
����������������


Zahra Surbajo


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*17-18*


Koda farouk yaje yafadawa hajiya abunda yafaru,sosai ta rufeshi da faɗa,shiko ko ajikinshi,dan yana ganin hakan da yayi shine daidai.

Rayuwa taci gaba da tafiya,su kausar har sunkai shekara tara a duniya,litte kuma shida.

Har yanzu in ba tare da babansu ba bazasuyi bacciba,komai shi yake musu,basuda damuwar komai.

Agefe daya kuma hajiya ce ke hura masa wuta akan yayi aure,duk yadda yaso ya kaucewa batun amman yakasa shawo kan hajiya,dole tasa yafara,tunanin inda ze nemo matar aure.

Kwatsa Allah ya hadashi,da khadeeja,yarinyar makotansu.

Soyayya suke da khadeeja bata wasa ba,shiyasa baa dauki lokaci ba,gurin daura auransu.

Ranar da amarya ta tare,da ango ze shiga daki,sosai yaci ado,.

Sun raya daren sosai cike daso da kaunar juna,.


Seda khadeeja tayi sati biyu sannan aka kawo su kausar.

Da farkon zuwansu ta nunamusu soyayya,to sede su kausar irin yaran nanne masu wuyar shaani,kwata kwata basu da yadda bare har takai ga ansaba dasu.

Wannan hali nasu yasa khadeeja fara ja baya dasu,kwata kwata tadena jansu ajiki.

Yanzu da sauki suna yarda su kwana su kadai,ammafa da sassafe zasu koma gurin babansu.

wannan sammako da suke musu shima yana bata ran khadeeja.

gashi ko hutu akayi shegun yaran basa zuwa gidan hajiya suna makale da ubansu.

Sannu a hankali khadeeja tafara fito da makaman yakinta na yakar su khairat.

Da farkode horo da yunwa tafara,daga bisani ta kara da sasu shara da mopping,in basuyi da kyauba su wuni kamun kunne.

Yaran gaba daya sun fita hayyacinsu,sabida wahala ga babansu bayanan yayi tafiya.

seda farouk yayi wata guda a inda yaje sannan ya dawo batare daya shaidawa khadeeja yana hanyaba.

yana shiga get,ya hangesu gurin shanya,khairat tayi wa kausar maka wuya,suna shanya kayan da khadeeja tasasu su wanke mata,bece komaiba.

se ya lallaba yashige,falon,tana kwance tana bacci,dakinshi yashige yazauna.

Ayko be jima da shigaba yajiyo kukan yaran .
.fitowa yayi yatsaya yana jin abinda take faɗi

"shegu yan iska,ba ance kune kuka kori matar babanku ba toni dan kar uwarku sede ni na koreku,matsiyata masu bakin hali,wannan munafuncin naku da gani gurin uwarku kuka koyo shi,tonice maganinku,har zan saku wanki kuyi be fitaba,sannan kwana biyu sharar ku bata fita bare mopping yayi kyau,dan haka tunda ubanku bayanan watan cin uwarku ya tsaya"

Ganin farouk agabanta yana hucine yasa tayi shuru jikinta yafara bari.

kyawawan mari yadunga fesa mata seda yamata kwarara guda shida,sannan yace.

"Kije na sakeki saki biyu,kuma cutarmin da yara da kikayi na barki da Allah"

Ihu khadeeja takeyi tana bashi hakuri ko takanta beyiba yanufi yayanshi,dake tsaye sunyi zuruzuru alamun yunwa.

Kitchen yanufa dasu yasamu tayi girki dan haka ajiye musu yayi yaga suna cin abincin kamar sun shekara basu ci ba.

Tausayinsu ne yakamashi besan sanda shima ya fashe da kuka ba.


*********


Hajiya kamar ta aro baki a makwabta sabida fada

Seda ya fada mata abinda yafarune ta sassauta masa.

iyayen khadeeja sunji haushin sakin yarsu ba kadanba,

Shiko farouk ci gaba yayi da rayuwarshi cikin kwanciyar,hankali.

hajiya bata takura masa akan yasake aureba.ta dukufa gurin yimasa adduar samun mata ta gari.

Inta ce masa.

"Farouku aure har yanzu shuru,ba zaka yi bane?"

amsarshi kullum dayace.

"hajiya nifa matanne sam basuda imani,kuma ko dan wasa da yaranafa basayi,basa jansu ajiki,bare watarana asaba dasu,kuma hajiya kinde san halin yaran nan sunada wuyar shaani"

"to Allah yabaka me maida kanta daidai da yaran sabida tsabar yin wasa dasu din,amman wlh kasan abinda kakeyi inba hakaba wlh auran dole zan maka kabar ganin banason damuwarka"

Duk sanda hajiya taimasa irin wannan adduar har sanyi yakeji aranshi,sabida shi aganinshi inde ze samu macen da zata dunga yiwa yaransa wasa ba abinda baze mataba.

Wasa wasa bayan khadeeja seda farouk yasake auran wata farida itama yargidan jiya,yasaketa sabida zalintar yaranshi da takeyi.


Tundaga wannan lokacin ko farouk ya nemi aure baa bashi,sede ace auri sakine shi,har cewa akeyi inde akaga ya auri mace ta zauna lfy ta sede in yaranshinw suka mutu.


Tun abun be damunsa har yazo yana damunsa,sabida shi mutum ne mabukaci kuma be iya neman mata ba.

Hajiyama abun yafara damunta,musamman in taga farouku acikin damuwa,

Wannan dalilinne yasa hajiya tunanin zuwa garinsu ta nemo masa aure,dan ita ba yarinya bace tasan damuwar danta dan haka zata nemamasa maganinta.


*******


*KANO STATE,KURA L,G,A*


Garin kura garine na manoma musamman fannin shinkafa,alumar kura sun iya nomanta.


Alhaji Hussaini kura,kanine ne ga hajiya mahaifiyar farouk,shine kadai dan uwanta daya rage mata kuma take ji dashi,tayi tati yadawo birni gurinta yaki,shima mazaunin garinne,yanada rufin asiri dedai gwargwado.

matarshi,yar wani garine acan gaban kuran me suna karfi,.

Yarsu guda daya,me suna Bilkisu,amman suna kiranta da megado.

Megado yarinyace yar kimanin shekara goma sha hudu a duniya,kyakkyawace ajin farko,sede matsalar megado shine.

Gabuwace ta ajin farko,wawta da sakarci,masifa,da tsiya,ba wanda ta kyale, kaf garin ansanta shiyasa yan garin suke mata kirari ,da

"me gadon tsiya da masifa"

kowaye ya kirata da hakan take zata waiga ta na dariya tabashi amsa da cewa.

"hakane ba karya,akwai tsiya da masifa,amman bana wasa da sallah"

duk girman mutum megado zata iya zageshi tas batare da yamata komaiba,inko yasake yadoketa,duk inda taganshi seta jefeshi,

tun ana kawo kararta gurin mahaifinta har andena kawowa.

Yadoketa ba irin horon da beyiwa megado amman kamar ba ita yakewa ba,sema kara gaba abun yake,har a mari ansaka megado gudun kar ta fita ta ɗauko magana.

har cikin gidan mutane take shiga ta daki da agaban iyayenshi inyayi mata rashin kunya.


bashi ko cikin megado ana cewa hanjine ita shine jinin jikinta.

in taga me tallah seta tsayar taci kuma bazata biyaba,in akayi magana tasa duka.

hakanne yasa akadena bata,to in baa bataba setaja anyi asara dan kifarwa zatayi.

sharia a fadar me gari kullum se an saurari ta megado,tun megari yana sauraron karar ta har yazamana in ankai sede yace mutum yaje yayi Allah ya isa kawai.

kullum addu'ar mahaifinta Allah yakawo sanadin shiryiwarta.mahaifiyarta ma haka.

muje zuwa.


surbajo for life.
[10:30, 15/09/2017] ‪+234 803 698 6494‬: ����������������
*AMANA TA BARMIN*
����������������


Zahra Surbajo


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.


*WORLD OF HAUSA NOVELS������*��

*A gaskiya naji daɗin kasancewa tare daku jiya sosai kun saka ni nishadi,soyayyar da kuka nunamin jiya ta tabbatarmin kullum da surbajo kuke kwana kuke tashi,amman naji dadi sosai wlh,musamman adduar da Meenarh luv kikamin��,gaskiya iliminki ya nunamin duk yadda akayi a gida aka koyar dake wannan addua,gado sedan gado,dagani ba tambaya daga gidan malamai kika fito,nagode sosai Allah yabar zumunci,fans atayani godiya gurin masoyiyata wato meenarh luv��ana mugun tare��*


*19-20*



Hajiya ce zaune ita da farouk suna tattauna yadda zasu shawo matsalar rashin auran farouk.

"Hajiya wlh ina cikin damuwa,kece mahaifiyata aminiyata abokiyar shawarata,banida wanda zan fadawa damuwata sama dake don Allah hajiya kisamomin mafita"farouk ya fada fuskarshi dauke da damuwa.

Gwauron numfashi hajiya taja sannan tace.

"idan ka amince zanje kura nasamomaka matar da zaka aura amman bisa sharadi"

Da sauri farouk yace.

"wlh hajiya kowanne sharadine na amince dashi,inde matukar zaki samomin matar auran"


"sharadina shine,duk wuya duk runtsi kasaki matar,ban yafemaka nonona dakasha ba,ka amince?"


shuru yayi yana tunani seda hajiya ta sake maimaita tambayar sannan yace a sanyaye.

"Na amince hajiya"

"da kyau,seka tashi kaje ka fara shiri,dannasan agarin bazan rasa yar da zaa aura maka ba koda ranar dana isane"


Godiya farouk yayiwa hajiya sosai,yatashi yafice,yanufi makarantar su kausar domin daukosu an tashi.

***********

yau hajiya ta dira garin kura.

Alhaji hussaini farincikin dayayi na ganinta baya misaltuwa.

nan aka dunga shigowa ana gaisheta,kowa yayi murna da zuwanta.

megado ko,gamsam gamsam ta shigo ta tsaya akanta kere re tace.

"Hajiyar birni ce yau agidannamu to hannu da zuwa"ta fadi tana sosa kwarkwatar data cije ta akai.

Dariya hajiya tayi sannan tace.

"megado ikon Allah,ana nan de da wannan tsiyar"

Dariya megado tayi sannan tace.

"fadi ki kara,akwai tsiya da masifa,sallah ce de kawai bana wasa da ita"

Dariya hajiya tayi sosai dan abun dariya yabata,megado ce tace.

"hajiya banga tsarabata bane,ko nufinki haka kija wanko kafa kika taho garin namu?"

jawota hajiya tayi tana dariya tace.

"ni na isa megado inzo banyo miki tsarababa,kinganta nan nayo miki"ta faɗi tana janyo akwatin data yimata tsarabar.

rawa da murna ba irin wacce me gado bata yiba agaban hajiya.

mahaifanta ko tagumi sukayi suna kallon sarautar Allah.

idon megado ne yasauka kan iyayan nata taga ita kawai suke kallo,ayko take ta hada rai tace.

"haba baba da inna,yazaayi kuzuba min na jiyamu,in nakuma faɗi ba gaskiya kurage sa ido,ba doe mutanan gari su samin idoba tunda wainda suka kyenkyaheni ma na jiyamun suke samun"

korata hajiya tayi bayan tabar gurinne,hajiya ta dubi ɗan uwannata taga damuwa karara a fuskarshi,cikin tausayawa tace.

"Hussaini meyasa baka sanar dani halin megado karuwa yayi ba?"

"yaya bashi da amfani indunga ɗaga miki hankali,tunda iya kokari kinayimin shiyas kawai bansanar dakeba"cewar mahaifin megado.

shuru hajiya tayi tana nazari sannan tace.

"to tunda megado taki makaranta meyas bazaka aurar da ita ba,sabida yawancin irin su megado aurene kawai yake kimtsasu"

"yaya garin nanfa mutum daidaine wanda megado bata yimasa rashin kunyaba,wanne ubane ze amince dansa ya aureta,gatanan ko kare be taba zuwa kofar gidannan yayi haushi domin ta ba bare kuma saurayi"

"Tunda abun hakane,su sinkita mu da muka haifeta bazamu kita ba,zamu ci gaba da yimata addua insha Allahu nan gaba zata bada mamaki,dan haka na yanke shawarar haɗata aure da farouku dan gurina,dan mutaru mu rufawa juna asiri"cewar hajiya.

a tsorace mahaifin megado yace.

"yaya farouku fa kikace,in banda abunki me farouku zeyi da megado,don Allah kibar batunnan karki shigar da farouku cikin damuwa da kanki"

"kade san halina bana magana biyu dan haka katashi kafara sanar da jamaarka,gobe daurin auran yarka,shine kawai"

Sanin da yayi inyayi magana ranta ze bacine yasa yayi shuru yamike yafice a gidan yaje yafara sanarwa,cikin kan kanin lokaci gari ya ɗauka,gobe auren megadon tsiya da masifa.


Hajiya kawun farouk takira tasanar dashi,dan haka ya shaida mata,za suyo sammako gobe su taho ɗaurin auran.


Farouk ma sanda ta faɗa masa yayi murna sosai inda shima yace zezo goben.

megado ko batasan wainar da ake toyawa ba,shaaninta kawai takeyi

**********

washe gari a babban masallacin garin dubvan jamaa suka shaida auran megado da farouk.

kowa seson yaga wanda ya aureta yakeyi,sanda farouk ya bayyana a matsayin angon megado bawanda be firgita ba.

kyau,kudi,ilimi,haiba,kwarjini,da cikar zati,ba abinda farouk bedashi,amman ya buge da auren megadon tsiya da masifa,wannan shine cecekucen da jamaa sukeyi,gameda auran.


gimbiya megado,nacan tana rambaɗa kwalliya,sabida yau jummaa,zata fita yawon daukar maganarta.


mata ne suka shigo inda take suna mata guɗa aka,ana fadin.

"su megado lokaci yayi bana muwaba,to ade sauya hali dan can birnine,wlh kika musu,dibar albarka magarkama zasu jefa ki"

ko ajikinta,tabisu da kallo da cewa.

"meye hadina da birni kuma,?"


"Ay yau an daura miki aure,wlh megado kinyi saar miji,kyakkyawa kamae balarabe,wlh wanke hannu ki taɓa,"


ido ta ware sannan tace

"ku don Allah da gaske kukemin anyimin aure yau kuma da balarabe?"


"da gaske mana inbaki yarda ba kije ki tambayi hajiyar birni"

da gudu ta fice a ɗakin tanufi gurin hajiyan birni ko sallama batayiba tace.

"Hajiyan birni wai an yi.in aure da balarabe,kuma wai birni zaa kaini?"

dariya tambayar taba hajiya dan haka kai kawai ta daga mata,gami da cewa.

"kina de son auran ko,?"

wata shewa megado tayi sannan tace.

"jar uba!!akwai tsiya abirni kenan,wlh insonshi sosai,billahillazi,najima ina kaunar inganni a birni,ahe lokacine beyiba,to hajiya yauhe zaa kaini gidan mijin? kinga kar dare yayi kuma baa kaini ba"

dariya hajiya kawai takesha kamar cikinta zeyi ciwo tace mata.

"kije ki shirya gobe da safe zamu tafi"


ayko da murnarta tafice adakin tana ta tsalle tsalle.

shiko farouk be bukaci ganin amaeyaba tunda yasan gobe zaa kawota,dan haka,daga gurin ɗaurin aure suka wuce kaduna shida su kawun shi.

megaso ranar bata yi bacciba tun cikin dare ta hada duk abinda take bukata.

iyayanta sosai suka mata

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment