Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace zan gani....... kamar daga sama

Sarkin fada yace nine shedar akwai ta acikin wannan aiki.

Kusan ma itace shugabarmu domin ita tasamu yin

wannan aiki, kuma ni inada shedar dazata nunama kowa

abinda ma bakusani ba, dama na ajeta sbd irin wannan

rana. Ai Gimbiya Zakiyyah batasan lokacin data sauko

kasa daga kan kujerar datake ba.

Anan Sarkin Fada yatashi yace tabbas ni nasan ayau

asirina yagama tonuwa, dan haka banga dalilin bata

maku lokaci ba, nasan Allah ya dade yana aramun rana,

sede inaso kuyi hakuri da duk abinda zakuji, bakomai

bane yasani aikata haka se SON ZUCIYA.

Wadda azamanin nayanzu shine abinda yake dawainiya

da mutane da dama, wanda kuma bakowa bane yake

saka mana son zuciya se shedan, da kuma mu kammu

idan muka kasa tsarkake zuciyarmu.

Ban kasance mutum nagari ba a masarautar nan, na

dade ina aikata abubuwa da dama, sede babu wanda

yasani, harzuwa yanzu. Alokacin da aka haifi Yarima

Areef, babban dalilin dayasa najawoshi jikina shine dan insalwantar da rayuwarshi, yazamana beda amfani

arayuwa gaba daya.

Ada nayi niyar kasheshi sede shakuwar damukayi tahana

ni, duk da Jakadiya Karima taso akasheshi, nine na hana.

Babu irin maganin da ban bashi ba dan kawai inga

yazamo dolo agidan nan amma hakan beyuwu ba, abu

daya nasan yayi tasiri ajikinshi shine yanda bedamu da

sarauta ba.

Alokacin daya girma se abun yadawo kaina, tunda

yadawo daga karatu na lura bayason ganina, hakan yasa

naja baya dashi. Amma sanin naci ribar cire mashi

sarauta aranshi hankali na ya kwanta.

Wannan kenan.

Bayan Jakadiya Karima tazo tasameni akan Gimbiya

Zakiyyah tana nemana, bayan naje ita da Medaki suna

zaune tafadamun abinda takeso inyi, sunaso insan yanda

zanyi inhallaka Fulani da abinda ke cikinta. Aranar da

dare itace agurin Sarki, hakan yabamu damar shiga

dakin Fulani mu biyu, nina fesa mata abinda yake sa

mutum bacci, sede ban fesa mata ba sebayan

muntasheta, alokacin taganni seta fara kokarin yimana ihu, hartaji mani ciwo afuska, ganin za,a jimu ne yasani fesa mata maganin, nan take tayi bacci.

Kamata mukayi muka fita da ita, muka sata mota, dama

munhada baki da masu gadin gate su 2, wato Lado da

Mati, hakan yasa suka bude mana kofa muka fita. Munyi

tafiya menisa dan seda mukaje wani daji dayake bayan

garin Darazo kusa da wata Mabarta, anan muka wurgata

cikin wani rami.

Sede wanda muka aikata laifin dashi banganshi anan ba,

amma inaso ashigomun da amintaccen bawan Sarki

Hasheem me kula da komai nashi nacikin gida, shine

wanda yatemaka mun mukayi wannan abun.

Sarki Hasheem runtse idonshi kawai yayi yana karanto

addu,a dan zuciyarshi zafi takeyi, jiyake kamar zata fito.

Ganin haka Malam yasa aka miko mashi ruwa yayi

addu,a aciki yabama Sarki Qaseem wanda shima kukan

yakeyi, yace yabashi.

Dakin yayi shiru sautin kukan mutane kawai akeji,

jisukeyi kamar almara ce ake fada masu. Bayan anshigo

da bawan, anan yaxube yana kuka, yace dan Allah

kumun rai wlh Son Zuciya ne da kwadayin abun duniya

suka kaini da aikata wannan abu. Waziri yace haka kowa

yake fada Son Zuciya, Ai kowa yasan son Zuciya bacinta.

Sarkin fada yafiddo wata karamar waya daga aljihunshi

yamika ma Waziri yace wannan shine shedar dazata

nuna maku akwai sa hannun Zakiyyah acikin duk wani

munafunci da akayi, bazan kirata Gimbiya ba sbd tazama

tamkar mata agurina. Saurin dafe kai Sarki Hasheem yayi dajin abinda Sarkin fada yafada.

Wata waya waxiri yaciro yajona ajikin wayar yahada da

T. V ya kunna kowa yamaida hankalinshi akan t,v. Tun

daga lokacin dasuke zaune afalon Gimbiya Zakiyyah tana

fada masu yanda za,a kawar da Fulani, da duk wani

munafunci dasukayi, harzuwa lokacin daya fara neman

Medaki, tunda Sarki yaga sunfara aikata masha,a yarufe

idonshi, aranshi yana fadin wato dama karya medaki

tamashi babu wani fyaden da akayi mata, dama can yar

iska ce. Areef kuwa yahana beauty ma ta kalli abinda

akeyi, ya kwantar da ita akan cinyarshi yana shafa mata kai, daga haka tayi bacci.

Babban abinda ya dagama kowa hankali lokacin da aka

nuno sanda suka fara aikata masha,a da Gimbiyyah

Zakiyyah. Salati kowa yafarayi, hakan yasa Sarki yabude idonshi, sede yayi dana sanin ganin abinda matarshi da

bafadenshi suke aikatawa. Waziri yasa hannu yakashe

wayar.

Shiru kowa yayi se kukan Gimbiya Zakiyyah dana medaki

kawai akeji. Jakadiya Karima ta tashi tace wlh shima

akwai abinda befada maku ba, idan bazaku manta ba,

alokacin da za,a nada Sarkin fada bashi bane aka zaba

ko? Waziri yadaga kai. Nan Jakadiya tashiga basu labarin

da Sarkin fada yabata.

Mamaki yakama kowa jin irin abinda sarkin fada ya

aikata. Hayanice tacika falon. Bayan kowa yanutsu,

Waziri yace lallai babu abinda zamuce sede muyi godiya

ga Allah wanda shine yake tsaremu aduk inda muke.

Tabbas akace dazama da makiyi gara zama da barawo,

kuma dama ance makusan cinka shine makashinka.

Tabbas kunso kashe abinda Allah yaso yafito duniya,

sede babu wanda ya isa ya aikata wani abu seda izinin

Allah. Matar da kukaso kashewa da diyarta gasunan

araye. Kallon Areef yayi yace daga matar taka kowa

yaganta.

Murmushi yayi dan seyanzu yafara fita daga duhun

dayake ciki, tashin beauty zeyi Malam yace abarta, zata tashi da kanta. Kowa mamakin ganin beauty yakeyi wai

itace diyar Fulani, Sarki kam wani irin sanyi yaji yana ratsashi duk da damuwar datake ranshi.

Waziri yace akwai bayanin da Malam zeyi mana kafin

afadi irin hukuncin daza,ayi ma kowa. Amma zamuje

hutu daga nan zuwa bayan azahar dan sallah tagabato,

wasu fadawa yasa suka tasa keyar su Gimbiya Zakiyyah,

Medaki dasu Jakadiya yace atsaresu. Kuma yasa suhada

da mati da Lado.

Kuka kawai sukeyi. Sarkin fada kuwa murmushi kawai

yakeyi.

Matsawa yayi kusa da Gimbiya Zakiyyah yace kinsan

akullum tunanin yan sarauta akullum iya karshi harshe,

dan basa amfani da tunaninsu sede na bayinsu. Kinga

koyanzu ya isa kigane banbanci tsakanin Bawa da me

mulki. Kuka tasaka, aka turasu zuwa kurkutu.

Nima yakamata inhuta haka kafin sudawo.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady).

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..πŸ›€πŸ›€πŸ•πŸ•πŸ•πŸ›€πŸ›€πŸ›€

AMAKABARTA AKA HAIFENI

πŸ›€πŸ›€πŸ•πŸ•πŸ•πŸ›€πŸ›€πŸ›€

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

[email protected]

Season 105⚜110

Zaune suke gaba daya harda masu laifi, zuwa wannan

lokacin idanunsu haryagaji da zubar hawaye. Sarki

Hasheem ya kalli Gimbiya Zakiyya, duk tafita hayyacinta, har seda tabashi tausayi dan yasan halin mahaifiyarta

idan hartaji abinda tayi tabbas zata saba mata.

Kawar da kanshi yayi ya kalli beauty wadda take haryanzu ajikin Areef, tunda Fulani ta tureta haryanzu

taki kara kallonta kuma koda aka dawo sallah agurin

Areef ta tsaya, shikam dama haka yakeso, yariketa kamar ance za,a kwaceta. Dan bemanta da halin data shiga ba

lokacin da Momynshi tayi mashi fada.

Malam yayi gyaran murya yace Alhamdulillahi Allah

yakawomu abinda na dade ina fatar Allah yakawomana

karshen shi, tabbas masarautar nan tashiga tashin

hankali da rudani, wanda zance bacewar Fulani agidan

nan tamkar saukowar wani haske ne wanda yazo ya

haske duk wani duhu dayake gidan nan. Kuma ya haska

duk wasu munafukai dasuke tare da mutanen gidan.

Abin mamaki wai ace wanda kayarda dashi yanzu

aduniya shine yake cutarka. Gaskiya nayi matukar girgiza dajin wadanda suka aikata wannan ta,asa wai

makusantan Sarki ne, acikinsu kaf babu wani bare.

Dama haka duniya take, duk wanda zakayima hassada

tamkar kana kara kusan tashi da ubangiji ne, domin

tunda annabi yasamu makiya to babu wani dan adam

din daze iya kubuta daga sharrinsu.

Sede abinda nakeso inkara tunatar daku, shine addu,a

domin itace makamin mumini, duk da ake cewa bawa

baya iya kaucema kaddararshi, amma idan muka rike

addu,a babu abinda bazata yimana ba.

Addu,a takan canza sharri yazama khairi, kuma tanasa

tsanani yazama sauki, dan haka koda Allah ya kaddaro

maka wata kaddara marar kyau, idan har karike addu,a

abun ze iya zo maka dasauki. Arayuwa baka taba gane

makiyinka, harse ranar da asirinshi yatonu.

Agskiya Sarkin Fada kabamu mamaki sosai, da irin

abubuwan damukaji ka aikata, ba kowane me imani

bane ze iya aikata abinda ka aikata. Kaci amanar kanka, addininka, iyayenka, matarka, da kuma Ubangidanka.

Duk irin halaccin dayayi maka arayuwa, seda ka

ha'inceshi, kashiga gonarshi har 2, duk da haka bata

isheka ba seda kayi sanadiyar rugujewar farin cikinshi, tahanyar kauda abinda yake matukar so, kaso ka halakar

dasu amma Allah be baka iko ba.

Ko kasan ta dalilinka irin ukubar da Fulani da diyarta

suka shiga? Mezaka cema Allah aranar gobe kiyama idan

yatambayeka akan amana? Ko kasan kalar abincin

dasukaci atsawon shekaru 18 acikin MAKABARTA?

Ta dalilinka matar da babu ruwanta, bata yima kowa

komai ba, amma saboda SON ZUCIYA irin taku kaida

mabiyanka kunsa baiwar Allah tahaihu a MAKABARTA.

Yarinya ta tashi a MAKABARTA. Bata san kowa ba se

Mamanta da kaburbura, da bishiyoyi.

Wancen bawan Allah da kuke ganinshi agidan nan badan

kowa yake zaune ba sedan farin cikin yarinyar da kukaso ku hanata zuwa duniya. Shine mutum na 2 daya

temakeso, wanda badanshi ba haka Yarinya zata girma

har shekaru 18 amma batasan komai ba, kuma ita ba hauka ba, barashin lafiya ba.

Kawai saboda tsabar SON ZUCIYA irin taku, bara infada

maku abinda bakusani ba, kuma zakusan cewar duk

zakaran da Allah yanufa da tsara to ko ana muzuru ana

shaho se yayi.

Idan bakusani ba aranar da kuka wurgar da Fulani acikin dare kuka wurgata cikin rami, to aranar ta haihu, kunsan suwa Allah yaturo mata kawai dan yanason yanuna

maku baya bacci? Wasu bayinsa ne, kuma yan uwa

musulmai, wadan da suka fito daga jinsin aljanu.

Akusa da fadarsu kuka wurgata, kuma cikin ikon Allah

alokacin suka temaka mata harta haifi diyarta acikin

koshin lafiya. Zakusha mamaki idan nabaku labarin da

daya daga cikin aljanun, wanda yakasance shugaba

agurinsu, shine yabani labarin abinda yafaru. Bara kuji....

Kaf duk abinda Malam yasani seda yafada masu, gaba

daya falon babu wanda beyi kuka ba saboda tausayin

Fulani da beauty, kowa ya tausaya masu yanda sukayi

rayuwarsu acikin MAKABARTA. Fulani da Beauty sunfi

kowa kuka, dan ita beauty tade taso taganta a

MAKABARTA.

Atunaninta nanne muhallinsu, kuma Fulani ita kadaice

wadda tasani, mace, se kuma Baba wanda shima

shikadai tasani namiji. Kuka takeyi sosai ayau dataji

labarinta, ashe inda take tunanin muhallinsu ne, take

cewa acan aka haifeta, ashe muhallin matattune, segashi yanzu ana fadin AMAKABARTA AKA HAIFETA.

Malam yace ga Baba nan, shine megadin MAKABARTAR

da suke zaune, kuma shine mutumin daya zauna dasu

bisa gaskiya da amana, kuma ko matarshi betaba fada

mawa ba, harseda yaga lokaci yayi daya kamata yafada

mawani, alokacinne yazo yasameni yafadamun.........

Duk abinda Baba yafada mashi seda yafada masu, da irin

dawainiyar da yayi dasu. Hakanne yasa alokacin da

yagama bani labari, mukaje muka daukosu duk da seda

wannan aljanu suka rokemu akan mukula dasu idan har

wani yakara yunkurin cutar dasu bazasu kyaleshi ba.

Tundaga ranar damuka daukosu, nafara tunanin tabbas

abinda nagani acikin istaharata yana shige da wadannan

bayin Allah, idan baku manta ba Waziri, azuwan da

kukayi nafada maku naga Fulani akusa dani, kuma tana

raye, sede bansan awane waje take ba.

Hakan yasa nafara zargin wannan mata da diyarta zasu

iya kasancewa matar Sarki da diyarshi. Amma gudun

kada inyi saurin fadar abinda zuciyata take fada mun

hakan yasa lokacin da Safeeya tazo mani da alfarmar

abata wannan yarinya ta taho da ita nan gidan yasa nayi tunanin barinsu suzo, sena cemata dole sutaho su duka.

Hakan yasa naroki alfarma gurin Baba nayabar aikinshi

yataho tare dasu. Adaren dazasu tafi nakira Safeeya daki nake cemata ina zargin wani abu akan mutanen nan,

itama tace mun zuciyarta tafara saka mata irin abinda nake zargi, dan ita tasan Fulani sosai, amma tacemun

bazata iya cewa ita bace dan alokacin ko Sarki yaganta

baze iya ganeta ba, tsawon shekaru 18, gashi bacikin

hankalinta take ba, kuma bagurin jin dadi ba, babu

wankan kirki, babu sallah, ba lallai bane a iya ganeta.

Shiyasa nace ma Safeeya sutafi tare, ta ajesu agurinta

kuma kada tabari kowa yasan dazamansu idan har

tasamu nutsuwa da tsafta zata dawo cikin kamanninta,

idan kuma ba ita bace shikenan nace munyi temako.

Alokacin nakira Waziri mukayi maganar, dan aduk fadin

masarautar nan mutum 3 nafi yarda dasu, kuma yana

daya daga cikinsu, Sarki Qaseem, da Sarki Hasheem.

Babban dalilin dayasa banyi maganar da Sarki Qaseem

ba, nasan yanda halinshi yake, baze taba iya hakura abi abun asannu ba, kamar yanda nashirya, shiyasa ban fada

mashi ba.

Bayan Safeeya takirani tafadamun tagano wannan

mahaukaciyar bakowa bace se Fulani da diyarta,

alokacinma nace mata taboye abun harse angano

wadanda suka aikata mata haka. Nakira Waziri nafada

mashi, kuma alokacin yake fadamun yafara zargin Sarkin

Fada.

Ni nace mashi yacigaba da bibiyarshi harse ansamu

cikakkiyar shedar dazata bada damar kamashi sannan,

kuma nafada mashi bashi kadai bane dole akwai wata ko

wani makusancin Sarki. Alokacin seyake cemun shifa

yana zargin Jakadiya Karima.

Nima nayarda da abinda yafada, hakan yasa nace mashi

ya zuba masu ido su duka biyun. To Alhamdulillahi yau

gashi damukayi hakuri Allah yanuna mana makiyanmu

afili.

Sede kuma akwai abu daya danakeso intambaya Waziri.

Ina wannan bafaden da Sarkin fada yajama sharrin kisa,

ina fatan ba,a yanke mashi hukuncin kisa alokacin ba?

Gyara zama Waziri yayi yace, alokacin kam Sarki ya

yanke mashi hukuncin kisa.

Sede ni ajikina bansan meyasa banyarda da hukuncin da

Sarki ya yanke ba, kuma zuciyata takasa yarda da cewar

shine yayi kisan, amma alokacin kuma zuciyata bata

zargin Sarkin fada, sede kawai taki yarda da wanda akace yayi kisan.

Hakan yasa naja Sarki falo tafada mashi da kada ya

yanke hukuncin dazezo yadameshi daga baya, nine

nabashi shawarar daya yanke mashi hukuncin daurin rai

da rai. Kuma haka akayi, haryanzu yana nan akurkutun

gidan nan.

Sede tun lokacin dana fara zargin Sarkin fada da rashin gaskiya acikin gidan nan, tun daga ranar nafara kaimashi ziyara, mukan zauna muyi fira,acikin zaman damukayi

ne, nakara yarda dabashine yayi kisan ba, kuma

akwanakin baya ne nasa aka canza mashi gurin aiki,

harda gurin zama.

Kuma tunjiya nasa aka fiddoshi yanzu haka yana

masauki. Malam yace kasa akirashi yazo nan. Waziri ya

aiki daya daga cikin fadawan gurin. Malam yace wannan

shine iyakar abinda nasani agame da rayuwar Fulani da

diyarta. Wadda haryanzu babu wanda yasan sunanta.

Abinda Baba yake kiranta dashi shine Yar Baba, wanda

yacemun ada yaji Fulani tana kiranta da Baby, jin sunan zeyi mashi wahala ne, yake kiranta da diyarshi. Amma

ayanzu tunda gashi sundawo gida, za,a iya saka mata sun kuma Waziri se muji daga gareku wane irin hukunci

zaku yankema wadannan maciya amanar.

Sallamar bafaden da aka aika ne tasasu kallon kofa, tare suke da wanda aka likama kisan da Sarkin Fada yayi,

zama yayi yana kwasar gaisuwa, daka ganshi kasan

yajigata, atsawon zaman dayayi akurkutu shekaru

dayawa.

Kallon Sarki Qaseem da Sarki Hasheem Waziri yayi,

domin jin abinda zasu fada. Sarki Qaseem yayi gyaran

murya yace, ni babu abinda zance, sede kawai inma

Allah godiya daya kawomu karshen wannan matsala

damuke ciki. Tabbas wadan nan mutane, kunsamu cikin

tashin hankali, babu abinda zance maku se Allah ya isa.

Sede abu daya nakeso kusani, hakan da kukayi bashine

ze samurika tsoron mutane ba,ko kuma mudena jawo

su zuwa jikinmu ba, ai ba,a taba taruwa azama daya,

idan wani yazo daniyar cutarka, Allah ze aiko maka dana gari, wanda ze zauna da kai badan komai naka ba, sedan

son dayake maka domin Allah.

Idan kuka kalli Jakadiya Safeeya da Malam,da Matata da

kuma matar Yaya wato Fulani, daga baya muka kara

samun Baban Darazo da abokin Yarima wato Haisam.

Duka wadan nan dana lissafo babu wanda muka hada

jini dashi, kuma babu wanda muka tashi dashi acikin

gidan nan.

Asalima bamu taba tunanin zasu shigo cikin rayuwarmu

ba, sedaga baya muka sansu, kuma duk da basu kasance

yan uwa agare mu ba, sun zauna damu tsakani da Allah,

babu wanda yakeda niyar cutar damu.

Idan muka kalli Malam da kanwarshi, bawai dan sun rasa

abinda zasuci bane yasa suka shigo jikinmu. Jakadiya

Safeeya tazo gidan nan badan kowa ba sedan bin

umarnin yayanta, kuma duk da haka tarika kaskantar da

kanta agaremu, wanda inda dan kudine zatazo, ninasan

babu abinda ze kawota, dan aduk fadin garin Bauchi,

darazo, Gombe, harma da makotanmu mutane dayawa

sunsan Malam, kuma kowa yasan babban mutum ne.

Idan har kudine, bayada damuwa dasu, asalima yakan

dauko wasu suci akarkashin shi. Amma duk da haka suke

zama tare damu abisa gaskiya da amana. Wannan kadai

ya isa yanuna ma kowa cewa wanda baku hada komai

dashi ba, ze iya yimaka abinda makusancinka baze maka

ba.

Yanzu ku kalli irin cin amanar da akayima Yaya, Gimbiya Zakiyya kinci amanar sarauta, kuma kinci amanar

iyayenki, amatsayinki na Uwar gidan yaya amma aka

hada baki dake, aka cuceshi, koba komai, mahaifinki da

Abbanmu abokan junane sosai, kuma dama sune suka

hada aurenku, alokacin Yaya bayasonki amma nayi

imani da Allah haryanzu betaba fada maki keba

ra,ayinshi bace.

Haka yakarbi zabin iyayenmu kuma yazauna dake da

gaskiya da amana, segashi daga karshe kinzama butulu,

bayan butulci ma harseda kika hada da cin amanar

aurenku. Wa iyazubillah, kina matar aure amma kika

aikata wannan babban zunubi agidanki. Amma kanki

kikai mawa, kuma wlh. Kowace irin alaka ketsakinmu

bazata hana ayanke maki hukunci dede da laifinki ba.

Kuka tasaka tana fadin natuba, dan Allah kumun rai, wlh duk abinda kuka fada gaskiya ne, amma niban aikata

abinda kukagani da son rai na ba. Nide nasan babu

abinda na tsana kamar zama guri daya da talaka, kuma

ni tunda nake wlh wannan aikin da Sarkin fada yamun

shikadai ne, yataba hadani dashi harmukayi magana.

Akwai sanda jakadiya Karima tazo tacemun wai Sarkin

Fada yana gaisheni.

Wlh ku tambayeta idan har zata fadi gaskiya zata fada

maku irin cin mutuncin dana mata akan abinda tazo

mun dashi, wlh babu wata alaka datake tsakanina dashi,

ko aranar danasan munfara aikata sabo dashi, yana

shigowa da masifa narufeshi, amma bansan ya akayi

daga baya harna bashi hadin kai ba.

Dan Allah Sarkin fada kafada masu ba laifina bane. Wani malalacin murmushi Sarkin Fada yayi yadauke idonshi

daga kallonta. Sarki Qaseem yace wannan kuma yarage

naki, kinsan masarautar nan bata yanke hukunci seta

tabbatar da sheda tazahiri, kuma ba mutum daya ba,

kowa gurin nan yaga abinda kuka aikata, dan haka ki

adana kalamanki.

Kallon Medaki yayi, yace kenarasa ma mezance maki,

kinfi kowa zama cikakkiyar butulu, kinfi kowa sanin

dayanda aka aureki da irin halaccin da Yaya yayi maki,

duk da nibanyarda da labarin da mamanki tabada ba,

amma sbd sanin girman alkawarin da yaya yadaukar

mata, haka mukayi hakuri ya aureki.

Amma kirasa da abinda zaki saka mashi se irin wannan

cin amanar, kema zakiga sakamakonki. Kuma abinda

nakeso dake inaso kifada mana wacece ke? Da kuma

asalin garinku.

Cikin sheshshekar kuka Medaki tace wlh nima bansan

inane asalin garinmu ba, nadesan ayawon damukeyi

daga wannan kauyen zuwa wani iyayena suka haifeni.

Kuma sanin dana yima iyayena basu bani tarbiya tagari

ba, babu ilimin addini bare na boko, to sukansu ma basu

damu danasu addininba.

Nikaina nafara sanin Sallah ne alokacin dana ke bin wata kawata islamiyarsu, anan nafara sanin addini na, harna

fara fahimta sosai, sekawai innata tafara doramun talla, domin ita macece meson kudi.

Aduk lokacin dana saida tana siyamun duk abinda

nakeso, nima tundaga ranar son kudi,yashiga raina.

alokacin kuma na hadu da wani saurayi shine yakara

huremun kunne, haryayi nasarar ciremun budurcina,

seda muka zubar da ciki har 2, kuma Innata bata

tabamun fada ba, wannan shine sanadiyar lalacewar

mahaifata.

Mahaifina dan caca ne, bedamu da ya rayuwata takeba,

shiyasa nakasance tamkar dabbar daji, banida wani

takunkumin daze hanani aikata abinda naga dama.

Sanadiyar Caca mahaifina yarasa ranshi, mutanen gari

suka koremu harmuka hadu daku, Innata tafada maku

karya har kuka yarda damu.

Tabbas nasan naci amanar mijina, wanda yarufamun

asiri, duk da yagane banje da budurcina ba, amma be

tsaneni ba, asalima cikin laluma ya tambayani, shima

nafada mashi fyade akamun wanda karyane, amma haka

ya yarda dani, kuma yacemun beyarda infadama

kowaba.

Dan Allah kayafe mani, nasan bankasance mace tagari

ba, naci amanarka dan Allah kuyafemun. Kuka tasaka

wanda seda wasu daga cikin mutanen falon sukaji

tausayinta,,,,, hayaniya sukaji awaje, Wazirine da fadawa suka leka.

Wani kodaddan mutumi suka gani wanda beda kyan

gani, sunata rigima da masu gadi. Waziri yace ku kyaleshi yakaraso, haka yataho yanata zare ido. Yana zuwa yace

wani nake nema agidan nan nayi mashi aiki be bani

kudina ba. Kuma nafada mashi idan har bebani kudina

ba zanzo intona mashi asiri.

Murmushi Waziri yayi yace kashigo semuji wa kake

nema. Kowa mamakin ganin mutumin daya shigo

yakeyi, banda Sarkin Fada wanda yaketa muzurai. Waziri

yace munajinka wakake nema?.

Yace sunanshi Sarkin Fada, kuma ya kasance daya daga

cikin mutanen danake yima aiki, duk wani aikinshi nine

nakeyi mashi, anan yarika fadin duk irin asirin dayasashi yayi, harda wanda yayima Areef, dana Jakadiya Karima

wanda tazubarma Gimbiya Suhailat ciki kuma aka daure

mahaifarta, har yakawo asirin karshe dayayi mashi.

Yace aranar yazomun akan yanason inbashi maganin

mallakar zuciyar Matar Sarki, Zakiyyah, yacemun yadade

yana sha,awarta amma yasan bazata taba bashi kanta ba,

hakan yasa yazo inbashi magani, alokacin yacemun beda

kudi amma yasan idan yasamu sa,ar kusantarta

yamallake zuciyarta zesamu kudi.

Tun ranar dana bashi bankara ganinshi ba, shine yanzu

nazo inkarbi hakkina. Salati kowa yakeyi, sbd wani abin al,ajabin dasuka karaji yabullo. Murmushi Waziri yayi

yace kaima seka samu guri kazauna kajira naka

hukuncin tunda Allah yakawoka. Zaro ido boka yayi yana

fadin aishikenan kuma wlh nayafe mashi kubarni intafi.

Seda yabama kowa dariya, nan fadawa suka zaunar

dashi. Se alokacin Sarki Hasheem yayi magana, jikinshi

asanyaye yace Malam, kafadi irin hukuncin daya kamata

ayima kowa abisa koyarwa ta addinin musulunci, kamar

yanda yazo a Qur'ani. Dan nagaji da kallon fuskokin

wadannan mutanen.

Dan duk acikinsu nafijin haushin mutum daya, bakowa

bace se Jakadiya Karima. Allah ya isa tsakanina dake, kin cuceni, wlh zan iya yafema kowa agurin nan amma

banda ke, bazan taba iya yafe maki ba. Mundaukeki Uwa

asheke makiyarmuce nida dan uwana..... kuka yasaka

tamkar karamin yaro.

Alokacin hatta da Malam seda yazubar mashi da kwalla

sbd yanda yakeyin kuka kowa yasan abun yana cimashi

rai sosai. Sarki Qaseem yana kuka yace Malam dan Allah

ayanke masu hukunci kada ciwon Yaya yadawo.

Malam yace Alhamdulillahi, kamar yanda kuka sani duk

wani laifi na duniya babu hukuncin da Alku'ani da hadisi basu kawo ba, dan haka zamu duba muga irin hukuncin

da Allah yace ayima masu irin laifinku. Zanfara daga kasa zuwa sama, wato daga masu karamin laifi zuwa babba.

Zan fara da masu gadi, mati da Lado, tabbas kun aikata

babban kuskure, domin da farko kunci amanar

masarauta, sannan kunbada gudummuwa gurin aikata

fasadi, dan haka hukuncinku anan shine zakuyi zaman

kurkutu natsawon shekaru 2, domin aladabtar daku,

sannan baku bakara aiki awata masarauta.

Se amintaccen bawan Sarki Hasheem, kaima kaci

amanar Uban gidanka, sannan kazamo daya daga cikin

wanda yatemaka ma Sarkin fada kuka sace Fulani. Dalili

daya ne bazesa ayanke maka hukuncin kisa ba, saboda

Fulani bata mutu ba, kuma Qur,ani cewa yayi wanda

yakashe akashe shi, sbd haka kaima za,a daureka

akurkutu na tsawon shekaru 5, tare da aiki metsanani.

Gimbiya Zakiyya, kinkasance matar aure, wadda aka

kamaki da laifuka biyu. Nafarko kina da sa hannu abatan Fulani, wanda dakunsami dama kasheta zakuyi. Nabiyu

kuma laifin aikata zina. To hukuncin zina anan yakasu

kashi 2, akwai na wadda bata tabayin aure ba, wato

budurwa, akwai kuma na wadda ta tabayin aure.

Idan budurwa tayi zina, kuma aka tabbatar dashedu, za,a yanke mata hukunci bulala 100, idan abokin yinnata

shima saurayine, hukuncinsu daya.

Matar aure. Duk matar datayi zina kuma tanada aure, ko

ta taba yin aure. Hukuncinta kisane, tahanyar jefewa da duwatsu, wanda yara ne zasu jefeta harta mutu, za,a

rufe duka jikinta cikin rami abar kanta shine za,ayita jifa

harta mutu.

Idan abokin zinarta yataba aure, hukuncinsu daya, idan

kuma shi beda aure, to nata daban nashi daban. Abisa

shedar da muka samu daga gurin wanda yayi maki asirin

da kika fada wannan alfasha.

Kamar yanda yazo a arba'una hadith, mazon Allah yace

INNALLAHA TAJAWAZILI AN UMMATI➑➑ Lallai Allah

yagafarta ma al'ummata, AL,,KADAHA... abinda sukayi

da KUSKURE. WANNISIYANA... abinda sukayi da

MANTUWA. WAMASTUKURUHU ALAIHI... da abinda AKA

TURSASASU AKANSHI. Rawahul bukhari wa muslim.

Abisa duba da wannan hadisi, sarkin Fada yayi amfani da karfin asiri ta hanayar mallakeki har kika biye mashi

kuka aikata alfasha. Abisa wannan hadisi, anan bakida

laifi agurin aikata wannan zina. Dan haka bazaki dauki

hukuncin zina ba anan.

Sede hukuncin dazaki dauka na aikata laifin cin amana

gurin niyar salwantar da rayuwar Fulani, dan haka zakiyi zaman kurkutu shekara 5. Saura hukunci kuma yarage

ga mijinki.

Tunkafin yacigaba Sarki Hasheem yace Malam da ita da

Medaki duk nayanke igiyara aurena akansu, dan haka

kacigaba da yanke hukuncinka. Hannu Zakiyyah ta dora

akai tana kuka.

Malam yace Medaki, kema hukuncinki biyu ne. Amma

tunda nakarshen megaba daya ne, to hukunci daya

zamu yanke maki, naki hukuncin kisa ne, tahanyar

jefewa, tunda ke kin amsa kece kika bama sarkin Fada

hadin kai da kanki. Dan haka hukuncin kisa zaki dauka.

Jakadiya Karima kema hukuncin kisa ne akanki, sbd

kin aikata kisan kai domin kinsa anzubar da cikin

Gimbiya Suhailat. Anyanke maki hukuncin kisa daurin rai da rai akurkutu, tare da horo metsanani.

Boka, kaima hukuncin kisa ne, ta hanyar rataya, tunda ka amsa laifinka, kuma Allah kadai yasan iyakar ta,asar

dakayi.

Hukuncinmu na karshe akan Sarkin fada, kai kam da ana

mutuwa adawo to da seka karbi duka hukuncinka.

Amma hukuncinka anan shine kisa ta hanyar rataya.

Anan muka kawo karshen wannan hukunci na

MASARAUTAR BUBAYERO. Inafatan hukunci yayi maku,

idan kuma akwai wani abu kuna iya fada, yajuya yana

kallon Sarki. Sarki Qaseem yakalli Yayanshi. Kai yadaga alamun hukunci yayi, sannan yace kuma agobe za,a

aiwatar da wannan hukunci.

Ihu Gimbiya Zakiyyah tasaka kamar meshirin shiga

hauka, Medaki da Jakadiya ma kuka kawai sukeyi kamar

ransu zefita. Haka aka kara tasasu zuwa kurkutu kafin

gobe.

Nima nace Allah yakaimu goben da rai da lafiya.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..πŸ›€πŸ›€πŸ•πŸ•πŸ•πŸ›€πŸ›€πŸ›€

AMAKABARTA AKA HAIFENI

πŸ›€πŸ›€πŸ•πŸ•πŸ•πŸ›€πŸ›€πŸ›€

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

[email protected]

Season 110⚜115

Kusa da Baban Darazo Fulani ta matsa, idanunta

haryanzu basu dena zubar da kwalla ba, dukawa tayi har

kasa tace, Baba hakika banida bakin dazanyi maka

godiya, kayimun abinda bakowa ne dan Adam bane ze

iya yimani shi.

Tabbas kazamo daya daga cikin mutane masu

muhimmanci arayuwata, kuma daga yau inaso

kadaukeni tamkar diyarka ta cikinka, inaso kadauko

duka iyalanka kudawo nan dazama dan suma sunzama

yan uwana.

Baba yace babu komai Fulani, duk abinda nayi maki nayi

shine dan Allah, banyi dan wani abu naku ba, asalima

bansan wane irin matsayi gareki ba. Hakika naji dadin

yanda kika dauke ni, kuma nagode Allah yasaka da

alkhairi.

Haka kowa yatashi yanufi bangarenshi kafin gobe da

safe. Haisam ya kalli Areef yace abokina nizan tafi gida, amma dole gobe indawo in kalli wasan daza,ayi agidan

nan. Tabbas nakara daukar darasi agidanku.

Allah yakara mana karfin imani kuma yacire mana SON

ZUCIYA. Areef yace amin, nima kaina abubuwan gidan

nan sun gama daga mun hankali, naji tausayin beauty na

sosai, ta dalilin masu SON ZUCIYA tarasa ingantatacciyar rayuwa da kowane dan Adam masu galihu

1 Comments On A MAKABARTA AKA HAIFE NI
avatar
najjwa

1 year ago

Reply

gaskiya littafin yanada dadi

Please Login or Register in order to submit comment