Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

saman

cinyarta tana murmushi.

Haisam yace tashi muje masallaci kada Abba yace

beganmu ba, Jakadiya tafita tace sekun dawo, akwai

abinci akitchen idan kundawo, suka ce to. Areef yaduka

kusa da beauty yace wato yau kinga yar uwa shine ko ki

kalleni ko? Kai tagirgiza ta tashi ta kalleshi. Dariya Haisam yayi yace beauty bakida matsala, kome akace kiyi sekiyi, gaskiya nan gaba zankoya maki bakomai zaki rika yiba.

Duka Areef yakaimashi yana fadin todan bukulu, ai seka

hanata, Allah yakashe yabani idan munyi aure base

narika magiya ba shine zakace wani tadena. Haisam yace

sosai ma, har wannan son jikin duk sena hanata. Dariya Areef yayi yanufi hanayar fita yace tunda kaine mijin ai se ingani, aini naji dadin wannan abu, sonjiki. Ai shine abinso, fita sukayi suna dariya.

Ayman tace sister da kikayi wanka kinyi alwala ko? Kai

tadaga mata, tace yauwa tashi muje kiyi sallah nima inyi alwala inyi, hannunta takama suka nufin daki.

Sarkin fada ne tsaye abakin kofar Gimbiya Zakiyyah se

waige waige yakeyi kamar marar gaskiya, wani abu

yadauko aleda yasa a idonshi, kafin yashiga gidan,

alokacin tagama sallah tafito falo, da sallama yashiga, cike da mamaki tace kai? Waya baka ikon shigowa part

dina? Ko kuma wani yace maka ina nemanka? Kai

yadago suka hada ido, wani irin abu taji ya tsikareta,

saurin rufe ido tayi, ganin halin data shiga yasa yayi

murmushi aranshi yace anzo gurin. Kallonta yayi yace

nadauka ai kinason ganina shiyasa nazo amma bari

inkoma.

Saurin bude ido tayi tasaki murmushi tace ni na isa nace ka koma? Shigo sannu da zuwa, zama yayi abisa kujera,

tace a,a muje daga ciki kada wasu suganka. Murmushi

yayi yatashi yana lashe baki aranshi yana fadin wayyo ni.

Daki suka shiga tace meza,a kawo maka? Murmushi yayi

yace bakomai zoki zauna kawai fira nazo muyi, wani irin yanayi taji tashiga, tahowa tayi kusa dashi tana wani

girgiza, kusa dashi tazauna tace togani, kallonta yayi

yakamo hannunta yace babu wanda zeshigo ko? Lumshe

idanu tayi alokacin taji wani bakon yanayi yashigeta, tace ina zuwa bari inbada sako akulle mun gidan kuma kada

abar kowa yashigo, yace akulle gida nida ba nan zan

kwana ba, wani irin kallo tayi mashi tace, kama isa, ai tunda kashigo sede da asuba kafita. Dariya yayi yace duk abinda kika fada dede ne rankiyadade, murmushi tayi

tafita. Wani irin tsalle yayi na farin ciki, hannunshi yasa a aljihu yaciro wani abu aranshi yana fadin saboda tsaro.

Bayan sundawo daga sallah part din Jakadiya Safeeya

suka wuce, anan suka samesu afalo beauty tana kwance

kan cinyar Ayman ita kuma tana ta wasa da gashinta

tana bata labari, da sallama suka shiga, Haisam yace to wlh baze yuwu ba, wannan matar taka zata sama Angel

dina taurin cinya, Areef yace wlh kai dan iska ne, agaban beauty kake wannan maganar sokake ka kangararmun

da ita, bacin kasan yarinya ce. Ai dasauri beauty ta tashi jin abinda Areef yafada, kafafuwa tafara durzawa akasa

tana turo baki tana kunkunai.

Dariya Ayman da Haisam sukayi, Ayman tajawota tace yi

hakuri, shine yace maki yarinya ko? Kai tadaga tana kara turo baki, kamar zatayi kuka, ai ganin haka yasa Areef ya matso yaduka kasa kusa da ita yana fadin yihakuri

beauty na wasa nakeyi kinji? Kai ta daga tana murmushi, Areef yace yauwa beauty na, tashi muci abinci in baki

tsara barki. Tashi tayi tanufi kitchen.

Haisam yace gsky kaci sa,ar mata wannan saurin sauka haka, to wlh kaji tsoron Allah, Areef yace da tsoronka

nakeji? Sarkin sa ido kawai, kuma badakai zanci abinci

ba, nida beauty zanci. Haisam yace Allah nagode maka

nima daka hadani da abin sona ayau, nadana shiga 3

agurinka, Angel muma tare zamuci ko? Kai tadaga tana

murmushi, lokacin da beauty tafito tasan alokacin ake

bama mamanta abinci, harta nufi dakinta se kuma ta

tuna da maganar Jakadiya Safeeya,,,,,,,, kada kisake

kishiga dakin can idan akwai mutane agidan nan, idan ba haka ba, kamata zasuyi bazaki kara ganinta ba. Maganar

Areef ce tadawo da ita, beauty mezakiyi awannan dakin

kuma?

Juyowa tayi tana murmushi ta girgiza kai, tanufo

gurinsu, ansar abincin yayi ta koma tadauko sauran,

atare yazuba masu yamika ma Haisam yace ganaku nan,

dariya yayi yajawo yazuba masu, Areef yace taho beauty

na muci, zama tayi kusa dashi, sede bega ta jingina dashi ba, murmushi yayi aranshi yace su beauty anfara girma

kenan, abaki yafara bata tanaci, shima yace nima bani

zakiyi ko? Kai tadaga tana murmushi, haka sukarika cin

abincinsu sun manta dawasu Su Haisam.

Dariya Jakadiya Safeeya tayi jin abinda Gimbiya Suhailat tafada, tace ai sundawo tundazu suna gidana, acan

nabarsu suna cin abinci ma. Wani murmushin jin dadi

Gimbiya tayi tace ai nasan Yarima zeso Ayman, gashi

lokaci guda har sun saba, wato kunyata sukeji shiyasa

suka tafi can. Jakadiya tace emana agida na za,ayi firar ai, kinsan Yarima. Naguri nane, ai, gimbiya tace aise suyita ta tafiya nima haka nakeso, Allah yabama Yaya lafiya

musha biki. Kallon agogo Jakadiya tayi tace bari inje gida seda safe Gimbiya.

Kallonta tayi tace haba de tunyanzu sallar isha,i ma

yanzu za,ayi, wai meyasa yanzu bakison zama anan sosai, musammamma da dare? Gaban Jakadiya yafadi, aranta

tace nasan Fulani tana can takusa tashi ai dole inkoma

kada su Yarima suganota. Dasauri tayi murmushi tace ai dole intafi inje inji inda aka tsaya amaganarsu,

murmushin jindadi Gimbiya tayi tace hakane fa,

Jakadiya tace nikam yanzu ai nasamu yan fira tunda de

kunya tahanasu zama anan, dan yarima ma cewa yayi

bayaso kusani harse Sarki yasamu lafiya yasan dayayi

maku magana za,a sa rana. Gimbiya tayi dariyar jin dadi tace kibarni dasu, zamu gwada masu bamusan komai ba

dakanshi zezo mana da maganar, bari hubby yadawo

infada mashi, sosai Jakadiya taji dadin maganar Gimbiya, sallama tayi mata tafita.

Koda taje kowa yana zaune tare da masoyiyarshi, Areef

yanata koyama beauty rubutu da karatu, kitchen ta

wuce ta dauko abinci tace sannuku da aiki, Yarima yace

Aunty har kindawo? Tace bari inshiga ciki inci abinci inyi wanka sukace to afito lafiya.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya babu wanda yasan abinda yake tafiya atsakanin masoyan. Abangarensu

kuwa soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, akoda yaushe

suna part din Jakadiya Safeeya, Areef yadage sosai yana koyama beauty karatu da rubutu, suna dawowa office

beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira

beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira

kome yakoyamata take daukeshi, ayanzu har rubutu ta

iya, dan tana hada kalmomi.

Ganin haka yasa hankalin Jakadiya yafara tashi, samunta tayi tafada mata kome Yarima ya tambayeta kada

tabashi amsa, idan ba haka ba, duk ranar da yasan

labarinta bazata kara ganinshi ba kuma zesa akoresu,

kada kisake kice mashi A MAKABARTA AKA HAIFEKI,

kawai kifada mashi abinda nafada mai, kinji ko? Ta daga kai, da wannan hankalin Jakadiya Safeeya yadan kwanta,

kuma akaci sa,a shima be cika yimata tambayoyi ba.

Abangaren Gimbiya Zakiyya kuwa ta kwace ma Medaki

Sarkin fada, dan duk dare agurinta yake kwana, wani irin sonshi takeyi, har bataso yayi nisa, sosai Medaki tashiga damuwa sede tunda Jakadiya Karima tayi mata bayanin

komai, shima Sarkin Fada yace mata yayi hakane dan

kawai yarama irin cin mutuncin datayi masu ne, kuma

kudinta yakeci sosai, kuma yana kawoma su Medaki,

hakan yasa hankalinta ya kwanta idan yasamu lokaci

kuma yana zuwa gurinta.

Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya Waziri akullum

yana kara sakama Sarkin fada ido, dan sunyi waya da

malam yace mashi yayi kokari yagama hada duk wata

sheda daza,a fara tuhumar Sarkin fada yana nan zuwa

tunda jikin Sarki yafara sauki, yanaso akawo karshen

matsalar gidan.

Gimbiya Suhailat ce tafito tana neman Ayman, ganin

bata ganta ba, wata baiwa tace sunfita bagaren Jakadiya Safeeya. Murmushi tayi tace yaude bari inje da kaina

inga wata wainar ake toyawa, kuma in nuna masu nasan

abinda suke boyemun, ai gara azo ayi bikin nan kowama

yahuta. Allah nagode maka da zaka cikamana burinmu,

bari indawo in bama Yaya albishir medadi, itama nasan

zataji dadi ace Ayman dinta zatayi aure. Fita tayi wasu bayi suna take mata baya, suka nufi bangaren Jakadiya

Safeeya.

Zaune suke afalo, Areef da beauty suna zaune bisa

doguwar kujera, sungama karatu, yana bata biscuit

abaki, suna ta firar su gwanin ban sha,awa, Haisam da

Ayman suma suna zaune kasa yana bata ice cream tana

ta zuba mashi shagwaba.

Jakadiya kam tana dakin Fulani tagama yimata wanka

tana sa mata kaya, tayi kyau sosai, hutun datake samu

kyanta yafito har kiba tayi. Jakadiya tace insha Allhu

komai zezo karshe da malam yazo kema kije gurin

mijinki koze samu sauki.

Wazirine da Sarki Qaseem suka fito zasuje bangaren sarki Hasheem, dede gurin part din. gimbiya Zakiyya

zasu wuce, sega Jakadiya da Sarkin Fada sunfito daga

gidan, Sarkin Fada se gyara wando yakeyi, suna fitowa

suka kwashe da dariya, hannu yamika mata suka kashe,

yace kai wlh yau nasha roman Gimbiya, sosai, kinsan

tundazu naso infito ta hanani, ashede haka Sarki yakejin dadinshi. Jakadiya tace ba dole sunemeka ba, tunda kana dauke masu nauyin abinda musakin mijinsu yakasa ba,

ai wlh..........

Maganar ce ta makale sakamakon idanu data hada dasu

Waziri. Hannu tasa ta tabo sarkin fada dayake shirin yin magana. Wata irin zabura yayi alokacin da idanunshi

sukaga abinda take nuna mashi, wani irin kallo Sarki da Waziri suke binsu dashi,,,, kuttt suka hadiyi wani miyau me daci, ga wata irin zufa datake fito masu.

Shinko su waziri sunji firarsu? Kubiyoni anext page

danjin abinda yafaru.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

AMAKABARTA AKA HAIFENI

🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

Season 85 ⚜90

Idan ran Sarki Qaseem yayi dubu to yabaci dajin irin

kalaman Sarkin fada da Jakadiya Karima, Waziri ne,

yajuya ya kalli Sarki Qaseem, shi kanshi ya tsorata da

ganin yanayinshi. Cikin sauri yataboshi, yana kallonshi yayi mashi alamu da ido.

Juyawa yayi murmushi dauke afuskarshi yakalli su Sarkin fada yace dama gurin memartaba zamuje kuma segashi

munhadu, ko kuma daga can kuke? Dasauri Sarkin fada

yace wlh kuwa shinema mukashiga gurin Gimbiya muyi

mata albishir naganin halin da Sarki yake ciki.

Gaskiya munji dadi sosai, jikinshi yayi kyau, yanzun nan nashiga ko kinti 2 banyi ba, shine ma muka fito da

Jakadiya. Amma ai kuma yanzu kukazo nan, ko kun dade

tsaye anan? Waziri yayi murmushi yace ai ko second 2

bamuyi anan ba, kuka ganmu, bari mukarasa. Wata irin

ajiyar zuciya suka saki, har suna hada baki gurin fadin to adubashi, Jakadiya Karima tajuya tanama Sarki Qaseem

kirari, hannu yadaga mata tare da kakalo murmushi

sannan suka wuce.

Sarkin Fada yace wai! Allah yasomu damun kama kanmu

ashema basujimu ba, Jakadiya tace kaide bari, nidama

nasan dakyar idan sunjimu, dan Sarki Qaseem mutum

ne wanda beson jin abinda bedameshi ba. Sarkin Fada

yace haka ne, shima ai Wazirin na Allah ne, babu

ruwanshi dajin gulma, akwai addini, muje gurin Medaki

itama inkwashi rabona. Jakadiya tace to amma gaskiya

yau nima inaso muje dakina.

Wani kallo yayi mata, sannan yace haba Jakadiya da

girmanki kike fadin haka, ai kibarma Gimbiyoyin Sarki,

ke kam yanzu ai kinwuce wannan matsayin. Hade rai tayi

tace amma ai duk tsufa na ban kaika ba ko? Dariya yayi

yace haka ne, amma kinmanta namiji baya tsufa? Kawai

kibar wannan maganar muje inyi abinda zefishsheni.

Wani guri kafin akai part din Sarki Hasheem suka samu

suka zauna, idanuwan Sarki Qaseem har rufewa sukeyi

sbd bacin rai, da kyar ya iya daga baki yace, dan Allah Waziri kace abinda naji ba gsky bane, nabama mutanen

gidan nan amana musamman wadannan 2, acikinsu

Yaya yafison Jakadiya Karima, nima haka, dan Allah

Waziri. Wani irin tausayinsu ne yakama Waziri, ganin

idanun Sarki Qaseem sunyi ja yasashi matsawa kusa

dashi tare da dafashi yace.

Memartaba wane irin matsayi kabani azuciyar ka?

Kallonshi Sarki yayi yace aduk gidan nan kaine mutumi

nafarko damuka fara aminta da kai, kawuce kowane irin

matasayi agurinmu har ka kai matsayin dan uwa

agurinmu. Bari kaji aduk fadin duniyar nan kai kadai

muke iya fadama sirrinmu, shiyasa bama jayayya da duk

wata shawara dazaka kawo mana.

Kawai kafadi abinda ke ranka namaka alkawarin

komenene zankarbe shi, nasan bazaka taba fada mana

abinda ze cutar damu ba. Gyaran murya Waziri yayi,

fuskarshi cike da annurin kalaman dayaji daga bakin

Sarki Qaseem, ahankali yafara fada mashi duk irin

abubuwan daya fara gani agurin Sarkin fada, har firar

dasukayi seda yafada mashi, daga karshe yace zakayi

mamakin idan nafada maka Gimbiya Fulani tana cikin

gidan nan tsawon watanni 3?.

Seda Sarki yakusa kwarewa saboda firgita, kai waziri

yadaga alamun da gaske yake, sannan yacigaba, akwai

abubuwa da yawa wanda bakusansu ba, daga ni se

Malam, se Jakadiya Safeeya kadai muka sansu, amma

inaso abari se gobe idan Malam yazo zeyi maku bayanin

komai, sede abinda nakeso kasani bawai munboye

Fulani da wata manufa tamu bane, a,a wannan umarnin

Malam ne.

Kuma alokacin da muka kawota gidan nan, babu wanda

yasan itace, dan tun lokacin data bace tsawon shekaru

18, har zuwa yanzu tana cikin yanayi na hauka, kuma

wahala data sha ne yasa muka kasa ganeta, acikin yan

kwana kin nan dayake tana samun kulawa agurin Jakadiya Safeeya, dan agurinta take zaune, tofa alokacin ne, tafara dawowa kamanninta, sbd tana samun tsafta,

shine Jakadiya ta ganeta.

Bayan tafada ma Malam, yace kada tafada ma kowa,

kuma yakirani yafada mun, nima yace kada infada ma

kowa, dan wadan da suka aikata mata wannan laifin

suna cikin masarautar mu, dole semunbi asannu zamu

iya ganosu.

Ajiya mukayi waya dashi yace mun zezo gobe domin

yanaso yakawo karshen halin da masarautar mu take

ciki. Babban abin farin ciki tahaifi cikin dake jikinta, Allah ya azurta ta dasamun diya mace, aranar data bar gidan

nan kamar yanda su Malam suka sami labari daga gurin

wadan da suka tsinceta, to aranar ta haihu, kaga yanzu

Yarinyar tana da shekara 18 da watanni.

Babban abinda yasa nataboka alokacin damu kaji abinda

su Sarkin fada suke fada shine, kasan idan baka iya kama barawo ba, to shine zekama ka. Nadade dasanin halin da

Sarkin fada yake ciki shida matar Sarki Medaki, suna

aikata kazamar harka, kusan kullum agurinta yake

kwana, nasamu wannan bayanin ne daga gurin daya

daga cikin bayin dana sa ya kular mun da duk wani

motsi na waziri.

Dan haka ayanzu base gobe ba, inaso kabani dama nasa

akama Sarkin Fada da Jakadiya akullesu har zuwa gobe,

idan Malam yazo se afito dasu, nasan idan aka maimaita

masu laifin dasukayi, zasu tona duk abinda sukayi.

Hawayen dake idanun Sarki Qaseem yagoge, saboda

bakaramin kaduwa yayi dajin labarin Waziri ba.

Da ace beji abinda suka fada dazu ba, kuma ace ba

waziri bane yafada mashi dabaze taba yarda da abinda

aka fada ba, kallon Waziri yayi yace ayanzu bani da

sauran bakin magana, da kai da Malam nabaku damar

ku aiwatar da duk wani abu da yayi dede da hukuncin

masarautar nan, sede abu daya nakeso, inaso akawo ma

Yaya Fulaninshi yagani, kila ta silar haka yasamu sauki, banaso afadi wani abu harse yasamu sauki, dan yaji duk

irin abinda mahintan makusantanmu suka aikata. Waziri

yace godiya nake, bara inje insa akama su, kafin wani

tunanin yashige su sugudu. Sarki Qaseem yace shikenan

bara inshiga gurin Yaya kada yaji shiru.

Da sallama su Gimbiya Suhailat suka shiga falon Jakadiya Safeeya, adede lokacin da Beauty tana karbar biscuit

ahannun Areef shi kuma yana ta mata wasa da hankali,

se dariya sukeyi, hannu tasa zata karba, cikin rashi sa,a tafada jikinshi. Kwanciya tayi saman cinyarshi tana ta

dariya shima haka.

Cak Gimbiya ta tsaya da sauran Sallamar data fara,

tsayawa tayi tana kallonsu cike da mamaki, da takaici,

sam bata kula dasu Ayman ba, sede kawai taji dariya

agefenta, saurin kallon gurin tayi, ai jitayi kamar tazube

dan takaici, Haisam ne, yake kokarin saka ma, Ayman sweet abaki, sunata dariya abinsu.

Kamar daga sama sukaji wata irin tsawa, wadda tasa

beauty saurin kankame Areef, tayi,wani Uban ashar

Gimbiya tasaki, wanda ita kanta batasan ta iyashi ba.

Gaba dayansu hankalinsu atashe suka juyo suna

kallonta, cike da kaduwa Haisam da Ayman suka sauko

kasa, shikam Areef sam abun be daga mashi hankali ba,

kara rungume Beauty yayi saboda kukan datasa mashi,

sam bata taba jin wata aba wai ita tsawa ba, tunda take, hakan yasa tayi mugun tsorata.

Gimbiya cike da bacin rai tace kai dan Ubanka bazaka

saketa ba, kabani hankalinka? Jakadiya ce tayi saurin

fitowa daga dakin fulani, dan dama tayi bacci ta tsaya

gyara mata dakinne kafin tafita, tana cikin gyara taji

wannan hayaniya.

Alokacin data fito saura kadan tazube saboda kaduwa,

cak ta tsaya bakin kofa tana zaro ido tare da kallon

Gimbiya. Areef yakama beauty suka sauka kasa, dan

shima alokacin da Gimbiya tamashi wannan zagin

bakaramin kaduwa yayi ba, dan tunda yake betaba jin

irin zagin abakin momynshi ba, ko fada bata taba

yimashi ba.

Wani irin murmushin takaici Gimbiya tayi, ta kalli

Jakadiya, rai abace tace sannu munafukar Allah,

mayaudariya, maha inciya, ashe dama abinda kike

kullawa kenan? Kinaso ki batama yarona tarbiyya tunda

ke baki dashi? Wato duk ginin da nakeyi kece kike rushe shi? Kinje kinsamo wata matalauciyar yarinya kin hadata da Yarima, ita kuma diyata kin hadata da abokinshi.

Ashe dama duk zaman damukeyi zaman munafurci ne ?

Wai meyasa duk wanda be fito daga gidan sarauta ba,

zaka sameshi maci amana ne? Lallai zamanki yazo karshe

agidan nan, bazan kara amincewa da banzan halinki ba.

Kai kuma Haisam kake kowa? Inaso kasani Ayman

Yarima zata aura, garama ka tattara soyayyarka kayi

waje da ita, ko kuma kaima kaje kasamu diyar dan siyasa ka aura, danmu bama auratayya da yan siyasa, domin

Sarauta gado ce, kuma ajininmu take, kufa?.

Mulki ne, da lokacinku yacika ko kunaso ko bakwa so,

dole kusauka kubama wanda yaci, dan haka kada inkara

ganinka agidan nan, bare kuma tare da Yarima ko

Ayman. Ke kuma kisaurari hukuncinki, matsawa tayi ta

ture beauty wadda tundazu take kuka.

Hannu Areef yasa yariketa sosai shima hawayene suke

zuba a idonshi, da kyar yace Momy dan Allah kiyi hakuri wlh beauty itace rayuwata, idan kika rabani da ita

mutuwa zanyi, ture ta tayi takama hannunshi dana

Ayman wadda itama kukan takeyi, Haisam ne kawai

medauriya acikinsu, amma har jakadiya kuka takeyi.

Jansu tarikayi kamar yara har suka fita daga falon,

dasauri Jakadiya ta matsa takamo beauty ta dagata zasu

shiga daki, kuka kawai, takeyi harda sheshsheka, tana tashi takoma tazube kasa sumemmiya.

Abakin kofar falon Areef ya toge, duk yanda Gimbiya

taso tajashi kasawa tayi, hannunshi ya fisge alokacin

dayaji Jakadiya tasa wani irin kuka tana fadin munshiga 3 Yar Baba dan Allah kitashi, dasauri yakoma falon,

Gimbiya tabishi tana fadin kadawo nace maka ko. Yana

zuwa yaga beautynshi kwance akasa babu alamun rai

atare da ita, wata irin kara shima yasaki tare da dafe

kanshi yazube kasa asume.

Urs.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

AMAKABARTA AKA HAIFENI

🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

Season 90⚜95

Da gudu Gimbiya da Haisam sukayi kansu, tana zuwa

takama Areef hankali tashe tafara jijjigashi tana kuka, Jakadiya Safeeya ma beauty tarika jijjigawa tana kuka.

Haisam ne yayi kokarin fita waje yakira wasu bayi maza, suka dawo tare.

Su suka dauki Areef shi kuma yadauki beauty suka fita,

Jakadiya, Gimbiya da Ayman suna binsu abaya, cikin

mota yasakasu, Jakadiya tashiga tare da Ayman ya kulle

kofar ko kallon Gimbiya beyi ba yaja motar suka barta

nan tsaye dan babu halin tabisu, tunda Sarki Qaseem

besani ba.

Komawa tayi part dinta tana kuka, kara tunano kalaman

Areef tayi,,,, Momy wlh kika rabani da beauty nima

mutuwa zanyi. Hannutasa tarufe duka kunnuwanta tana

fadin bazaka mutu ba Yarima, kaine farin cikina, dan

Allah kar kamun haka. Saman kujera tafada tana kuka

bayinta se hakuri suke bata.

Waziri ne, tare da wasu manyan bayi maza suna binshi

abaya, hanyar lambu suka nufa dan yafi zaton suna can,

koda sukaje basu same su ba, tunawa yayi da Medaki,

hakan yasa suka nufi can.

Alokacin Sarkin Fada da Medaki suna cikin daki, ita ko

Jakadiya Karima tana zaune falo tana kallo ta tasa

farfesun kaji tanaci. Wata baiwa ce tashigo falon, ai

dasauri Jakadiya tace Uban wa yabaki izinin shigowa?

Bana hanaku idan muna gidan nan kushigo ba?.

Dukawa tayi tace Allah yabaki hakuri, dama Waziri ne, ya tambayeni ko keda Sarkin fada kuna ciki, shine nace

masa kuna nan, shine yace amaku magana. Cikin

Jakadiya ne yayi wani kara, nan take zufa tafara keto

mata, batasan lokacin data saki cinyar kazar datake

hannunta ba.

Cike da tashin hankali tace ubanwa yace kifada masa

muna ciki? Innalillahi wainnailaihirraji,un. Munshiga 3

kada de ace asirinmu ne yake shirin tonuwa? Tashi kiba

mutane guri munafuka. Hanyar dakin Medaki tanufa, har

tuntube takeyi, tana zuwa tafara bubbuga masu,alokacin

sunyi nisa cikin harka, dade sukaji bugun yayi yawa,

shine Sarkin Fada yayi saurin zira babbar rigarshi, ko wando besa ba, haka yaje yabude.

Ai yana fitowa Jakadiya tajawoshi tana fadin munshi 3

gasu Waziri can abakin kofa suna jiranmu. Zaro ido yayi yana fadin waya fada masu muna nan? Tace kaide

kawuce muje, bawannan bane agabanmu, yanda zamu

kare kanmu bakamar ma kai, danni wlh tawa mesauki

ce, tunda ni macece kuma kowa yasan inada hakkin

shiga duk inda nakeso amasarautar nan.

Sarkin fada yace kiwa Allah kije kice ke kadai ce, bakisan inda nayi ba, nasan zasu kyaleki. Zaro ido tayi tare da dafe kirji tana fadin Jar Uban nan, ai wlh baka isa ba, ai gara ma kai, kome akayi maka kasha dadi, nifa?

Menasha, kun hadani da naman kaza da kallo kunshige

daki, ai wlh inde nafita kaima seka fita.

Bugun kofar falo ne, ya sasu saurin kallon gurin alokacin Medaki tayi saurin fitowa da daurin gaba ajikinta, kanta ko dan kwali babu, tana fadin wai meke faruwa haka?

Shigowar Waziri ce tasata yinshiru, idanu 2 suka hada

dashi, hakan yasa yayi saurin kauda kanshi, ai dasauri

takoma daki, kallon Sarkin Fada yayi wanda ko rawani

babu akanshi, dagashi se babbar riga,, jikinshi kam ko

wando babu.

Hannu Sarkin Fada yadora akanshi yana fadin shikenan

yau kuma ahaka tazo mani. Waziri cike da bacin rai yasa fadawa sukamashi, Jakadiya Karima tace ai dama kullum

ina fada maku kune bakwaji, yau ga irin ta nan, nikam

baruwana, Allah yakara, hanyar waje tanufa tana shirin

fita. Wani kallo da Waziri yayi mata yasa dole taja burki tana raba idanu.

Wazirin yace ku kamosu dukan su akaisu kurkutu zuwa

gobe, kuma inaso kusaka kwakkwaran tsaro agidan nan,

yanzu zan fadama sauran masu tsaro, kada abari kowa

yafita daga gidan nan koda kuwa matar Sarki ce, koma

waye dole akirani kafin yashigo ko yafita. Haka aka tasa keyarsu zuwa kurkutu. Medaki kuwa tana daki tarasa

inda zata sa ranta.

Suna zuwa asibiti aka karbesu akayi emergency dasu,

kowa aka fara bashi temakon gaggawa, cikin lokaci

kankani Areef ya farfado, sede beauty ko alamun motsi

batayi, hakan yasa likita yace akai Yarima dakin hutu, nan suka cigaba da duba Beauty.

Tunda Areef ya farfado yafara kiran beauty, kuka

yasakama Haisam da Jakadiya Safeeya, se lallashin shi

sukeyi, Areef yace wlh idan wani abu yasami beauty na,

nima Momy zata rasani. Haisam yace kadena fadin haka

Areef insha Allahu zata warke. Karar wayar Haisam ce ta katsesu, Areef yace idan Momy ce kace mata ban farfado

ba dan Allah.

Yana dagawa tace Haisam yaya jikin Yariman? Wani irin

haushi yaji, wato ita ta danta ma kawai takeyi. Ahankali yace Momy Areef yana cikin wani yanayi, addu,a kawai

zakitayashi. Cike da tashin hankali tace ina likitan banishi, yace suna can akanshi suna bashi temako.

Dan Allah Haisam kace ma likita yayi duk yanda zeyi kada dana yarasa ranshi, ko wani abun yasameshi dan Allah.

To kawai yace mata, yakashe wayar. Runtse ido Haisam

yayi yana karajin haushin kalaman Momy, Areef yace

hankalinta yatashi ko?.

Kai kawai yadaga mashi, yace ina ganin matsalar mu

zatazo cikin sauki, sbd Momy tana sonka sosai, dan haka dole muhada mata plan. Murmushi Areef yayi yace haka

ne, abokina nagode, yanzu muje inga jikin beauty na.

Jakadiya Safeeya tace a,a Yarima ka kwanta jikinka babu kwari, likitoci suna kanta suna nema mata sauki.

Komawa yayi yakwanta zuciyarshi tana zafi.

Sarki Qaseem ne, afalonshi hankalinshi tashe da abinda

Waziri yafada mashi sungani apart din Medaki, haka

yazauna yadafe kanshi da hannu 2, jin haryanzu shiru

bega Gimbiya Suhailat tafito ba, yasa yatashi yanufi

dakinta, kwance yasameta tana ta kuka, cikin sauri

yakarasa gurinta tare da kamota ya rungume.

Kara rungumeshi tayi tasaki wani sabon kuka, shafa

bayanta yafarayi yana fadin meyafaru kike kuka haka?

Kanta tadago, tana share hawaye tace shikenan

munshiga 3 Hubby, zamu rasa danmu guda 1 da Allah

yabamu. Cike da tashin hankali Sarki yace bangane

mikike nufi ba, meyasamu Areef din ? Ko hadari yayi? Kai tashiga girgiza mashi, tace yana can asibiti likitoci ma sunkasa samo kanshi. Sarki yace dan Allah kitashi

kifadamun abinda yafaru, wlh zuciyata gab take da

bugawa, bakisan irin tashin hankalin daya sameni ba,

kifadamun abinda yafaru tunkafin nima kirasani.

Ai dasauri Gimbiya ta tashi tana kallonshi, se alokacin ta kula da yanayinshi, idanunshi sunyi ja sosai,cike da

kaduwa tace hubby dan Allah meyafaru, kallonta yayi

dan yafara kulewa da ita, tureta yayi cike da bacin rai, yace ya ina tambayarki kina tambayata dan kin rai nani, kawai kifadamun abinda yafaru idan bahaka zanbar

maki gidan. Matsowa tayi ta rungumeshi tana kuka, dan

tunda suke betaba yimata irin wannan ba, asalima bata

taba ganinshi cikin irin wannan yanayin ba.

Dagowa tayi tajawoshi suka zauna bisa gado, kanshi tajawo tadora saman cinyarta tana ta shafa kanshi,

lumshe ido yayi, yana sauke ajiyar zuciya. shiru sukayi nawani lokaci, jinyayi shiru yasa tadagshi ta tashi takawo mashi ruwa mesanyi, dakanta tabashi, kofi guda ya

shanye, sannan takara jawoshi yakwanta akan cinyarta.

Ahankali tana shafa kanshi tace hubby karika fadin

Innalillahi Wainnailaihirraji,un, kayi haka harso 5,

sannan infada maka abinda yafaru, amma ina fatan

bazakamun fada ba idan kaji abinda nayi?

Cike da fargaba Medaki tashiga falon Gimbiya Zakiyyah,

alokacin tana zaune tana hutawa, kallonta tayi tace

kekuma lafiyarki zaki shigo mani gida ahaka, ko Sarki ne ya mutu? Medaki tazauna tace ai da mutuwa yayi zefi

sauki da halin dazamu shiga nida ke, da su Jakadiya,

cinkin lokaci kadan.

Tashi tayi daga kishingiden datake tana yamutsa fuska

tace bangane abinda kike nufi ba? Anan tafada mata duk

abinda yafaru, har halin datake ciki ita da Sarkin Fada seda tafada mata, dan ita tariga da tagama yarda da ita, tunda taga halinsu daya ne. Wani irin miskilin murmushi Gimbiya Zakiyyah tayi, tayi mata wani irin kallo, tace.

Lallai bansan ke Jahila bace se
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On A MAKABARTA AKA HAIFE NI
avatar
najjwa

3 months ago

Reply

gaskiya littafin yanada dadi

Please Login or Register in order to submit comment