You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kuwa tun faduwar dayayi haryanzu
akwance yake tun maganar dayayi da farko bekara cewa
komai ba. Gimbiya Suhailat da Safeeya se kuka sukeyi,
Baban Rayhana kuwa zaune kawai yake, idonshi harsun
kumbura sbd kuka, yakasa cewa komai.
Abu kamar wasa har dare yayi babu Fulani, yan sanda
harsungaji da nema, hankalin kowa atashe yake, banda
munafukai, sede Jakadaiya tana zaune kusa da Sarki,
idonta itama ya kumbura dan kuka, mutane se hakuri
suke bata. Waziri yakira malam yayi mashi bayanin halin da,akeciki, shima ya jajanta masu. Yace sujirashi zuwa
washe gari.
Washe gari tunda asuba. Malam yakira waziri yace mashi
agaskiya Fulani tana cikin mawuyacin hali, sede besan
inda take ba, amma kuma tana raye, za,a cigaba da
addu,a. Anan yafada mashi halin da Sarki yake ciki, anan malam yace bakomai nan da kwana 2 zezo se asan
abinda za,ayi.
Jikin sarki babu sauki, ko abinci bayaci se dakyar suke matsa mashi yaci kadan, Ranar da Malam yazo ne, suka
shiga suka tattauna da mayan fada, kuma suka yanke
hukuncin nada Qaseem amatsayin Sarkin masarautar
Bubayero. Lokacin da Qaseem yaji kin amincewa yayi.
Da kyar suka shawo kanshi, washe gari aka nadashi Sarki.
Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba, se fada take tana fadin wannan ai shine kai kai koma kan
mashekiya, wato munyi abu kuma yadawo kaina, kai
bazeyuwu ba yanzu shikenan natashi daga matar Sarki?
Wlh dasake. Jakadiya tace haba Gimbiya najifa ance
rikon kwarya ne aka bashi, da sarki yasamu lfy zemaida
mashi mulkinshi.
Haka sukayita bata baki, da kyar ta hakura, abu daya ne yasata kara yarda mulki zedawo hannunsu dataji ance
Qaseem yace baze dawo gidan Sarki ba.
Bayan anyi nadi malam yakoma Darazo, haka akacigaba
da nema ma Sarki magani da adduo'i, ankaishi asibitoci
dayawa amma jikinshi babu sauki, matsalar shanyewar
barin jiki ne tasameshi, hakan yasa aka fara yimashi
gashin kashi, sede babu yanda basuyi ba akan afitar dashi waje, amma sarki yaki yarda koda suka fadama
malam, seyace su kyaleshi, babban abinda zesa yadawo
dede to ganin Fulani ne, hakan yasa suka kyaleshi aka
cigaba da yimashi maganin gida.
Medaki kuwa cin duniyarsu sukeyi da tsinke, ita da
Sarkin fada. Duk wani munafunci yadawo daga Jakadiya
se Sarkin Fada. Gimbiya suhailat da Safeeya haryanzu
sunajin kadaicin rashin Fulani, Babanta kuwa tundaga
ranar yadena zuwa ko ina kullum yana kofar gida, sede
masu aiki suzo suyi mashi aiki sutafi.
Wannan shine asalin labarin Masarautar Bubayero.
Zamucigaba da cigaban labarin anext page. Nagode
Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 65 ⚜70
Tafiya sukeyi amota, Jakadiya Safeeya, kallon Wannan
mahaukaciyar kawai takeyi, tana kara tuno maganganun
da malam yafada mata ana gobe zasu taho, waigawa tayi
takara kallon Yar Baba wadda tayi lamo ajikin Baba tana ta bacci.
Aranta tace tabbas suna kama sosai ma, sede kawai
wahalar duniya zatasa baza,a iya gane kamar suba. Dole
nayi yanda malam yace idan har muna son musami
abinda muke so. Tunawa tayi da abinda malam yafada
mata akan Waziri, aranta tace tabbas da ace kowane
Sarki zesamu mutum me amana kamar Waziri dayaji
dadi, addu,a tayi akan Allah yate makesu akan mutanen
masarautarsu.
Alokacin dasuka isa Masarautar Bubayero Jakadiya
Safeeya tayima Waziri waya akan sun iso, alokacin gurin karfe 12 , Waziri yace togani nan zuwa. Yana zuwa
yabada umarnin abude masu gate, direct gurin part din
Sarki Qaseem suka nufa, dayake ranar asabara ce, kuma
azahar batayi ba, babu kowa awaje se bayin dasuke kai
da kawowa.
Suna fitowa Jakadiya Safeeya takama matar, shi kuma
Baba yakama Yar Baba Waziri yayi masu jagora zuwa
bangaren Jakadiya Safeeya, dayake, dakuna ne, guda 2 se
falo da kitchen, kuma kowane daki akwai bandaki aciki, idan kaga yanda Gimbiya Suhailat tasa aka gyara ma
Jakadiya Safeeya part dinta zaka dauka nawata
mekudice, babu abinda ba,a zuba ba na kyale kyale
afalon, dakunan ma haka, gidan yayi kyau sosai. Duk da
abangaren Gimbiya takecin abinci amma a kitchen dinta
ma akwai kayan girki da kayan abinci.
Bayan sun shiga Waziri yakalli Baba yace sannunku da
hanya, Baba yace yauwa munsameku lafiya? Yace lafiya
lau, Waziri yace Alhamdulillahi Baba gashi kazo
masarautar mu, kuma insha Allahu zakaji dadin zama
damu, sede akwai abubuwan danakeso ka kiyaye kuma
ka kula dasu, na farko de nasan malam yafada maka
yanayin yanda gidan sarauta yake, dan haka abu daya
zan fada maka shine akwai Wani mutum Sarkin Fada,
inaso duk yanda zeso yashiga jikinka kada kabari wata
magana wadda tashafeka tahadaku, zan kaika gurin Sarki
amatsayin wanda malam yaturo domin kazauna tare
damu, ka kula dashi sosai dasauran mutane, idan muka
fita zan kaika gurin Baban Gimbiya Fulani, mutum ne,
nagari kuma shima dattijo ne, nasan zakaji dadin zama
dashi, koba komai daka zauna kana fira da mutanen
gidan nan gara karika zuwa gurinshi kuna fira.
Baba yace nagode sosai, kuma insha Allah zaka sameni
merike alkawari, fatanmu de Allah yabama wannan
baiwa tashi lafiya, suka ce amin. Waziri yace muje
ingwada maka masaukinka kafin Sarki yafito, kallon
Jakadiya Safeeya yayi yace nasan akwai abubuwa da
dama dasuke bukata, anjima kamar da yamma zankawo
maki kudi, sekije kasuwa kisiyo masu kayan amfani,
game da sutura ma, duk kisiyo masu, idan yaso seki
hado da dogayen riguna surika sawa kafin tela ya gama
dinkawa. Kallon Yar Baba yayi yace daga cikin gidan nan kada kifita ko ina kinji? Ta daga mashi kai, yace yauwa, dakin fita akwai mutanen dazasu kamaki, saurin boyewa
tayi bayan Jakadiya safeeya jin abinda Waziri yafada.
Murmushi yayi yace tsoro kamar farar kura.
Tashi sukayi shida Baba, yace Sena dawo anjiman, tace
to mungode, nima abinci zan dafa masu kafin inshiga
gurin Gimbiya. Yar Baba tashi tayi ta matsa kusa da
mamanta wadda take zaune akasa tayi shiru tana ta wasa
da kafet din falon, kwanciya tayi bisa cinyarta, tana mata murmushi, dankwalin kanta mamar tacire, tafara yimata
wasa da gashin kanta, ita kuma se lumshe ido takeyi.
Jakadiya Safeeya tana kallonsu tace ikon Allah, Uwa da
Diya se Allah, gaba daya sungama burgeta, murmushi
tayi tace Allah yasaka maki, akan duk wanda yayi maki
wannan abun. Tashi tayi tanufi kitchen.
Waziri ne, zaune afadar Sarki, bayan sungama gaisawa
yafada mashi Jakadiya Safeeya ta dawo, tare da wani
tsoho, malam yace sutaho tare, yazauna anan, amma
nabashi masauki abangarena, shine nace bari infada
maka. Murmushi Sarki Qaseem yayi yace, Waziri ai duk abinda kayi dede ne, babu laifi, kazaba mashi duk aikin daze iya mesauki kasan abinda zaka rika biyanshi ai?
Yace hakane, godiya muke.
Sarki Qaseem yace Waziri akwai maganar danakeso
muyi akan Yarima, kasan yagama karatunshi kuma
yacemun shi aikin gwamnati yakeson yayi, to munyi
magana da abokina harma an daukeshi , ranar litinin
zefara zuwa, anan gidan gamnati, sun bashi assistant
director. Kuma nasan saboda abokinshi ne yanace
yanason yayi aiki acan, dan shima acan yake aiki.
Kasan wani magana dayazo mani da ita? Munyi mashi
maganar aure, Momynshi tanaso tayi mashi maganar
diyar yayarta datake can kasarsu, amma seta fara
tambayarshi koyana da wadda yakeso, budar bakinshi se
cewa yayi yafison yasamu wadda bata fito daga gidan
sarauta ba. Haba Waziri yama zece haka, ko Yaya daya
auri mata 2 ba yan sarauta ba, ai matarshi tafarko daga gidan sarauta tafito, shine mukace bamu yarda ba,
amma zaka iya kiranshi ka karaji daga bakinshi, kasan
banason bacin ranshi, inaso kanuna mashi nayarda
yafara auren yar sarauta daga baya se ya auri zabinshi.
Waziri yace wannan ba wata matsala bace daza'a bata
rai, kabarni dashi zanji tabakinshi tunda beriga yasamu wadda yakeso ba, ai dasauki, kuma zanga abokinshi
Haisam nasan shima zeyimashi magana. Murmushin jin
dadi Sarki Qaseem yayi yace. Hakan yayi kyau, muje
muga jikin Yaya.
Jakadiya Safeeya ce zaune afalon Gimbiya Suhailat,
Gimbiya tace bakiji yanda naji ba, yan kwanakin nan
dabaki nan, idan Sarki yafita sede inta zama nikadai,
dariya Jakadiya Safeeya tayi tace nima duk banji dadi ba, ya Sarki da jikin? Gimbiya tace jiki kam dasauki, da ranar dasu Waziri suka kawo mashi magani, dakuma maganar
da malam yayi akan Fulani ranar har murmushi seda
yayi, kuma nantake yashanye maganin, inasha Allahu
zesamu lafiya. Jakadiya tace Allah yabashi lafiya, ina dana Yarima?.
Hmmm Yarima rigima, kinsan abinda yazo mana dashi
kuwa? Tace a,a. Nan tafada mata yanda sukayi dashi,
tace kuma nibazan amince mashi ya auri kowa ba, se
jinin sarauta, Jakadiya tace kiyi hakuri, ita harka ta aure ba,aso ana tsanantawa acikinta, addu,a yakamata kiyi
mashi amatsayinki na mahaifiyarshi se Allah yayi mashi
zabi nagari.
Gimbiya tace hakane, amma nafison yabi zabin dana
yimashi, diyar yayata nakeso ya aura,duk da ban fada
masuba, banaso infada masu Yarinyar tasa abun aranta,
nasan bayanzu zatayi aure ba,shiyasa nayi shiru harseya amince, sannan nayi masu magana. Jakadiya tace
bakomai Allah yashige mana gaba, nima zanyi mashi
magana tunda de besamu wadda yakeso seya auri
zabinku, idan yaso daga baya seya auri zabinshi. Gimbiya tayi murmushi jin dadi tace shiyasa nake sonki. Allah
yayi mana zabi nagari.
Da yamma kamar yanda Waziri yace, haka yasa driver
yadauki Jakadiya Safeeya yanufi kasuwa da ita, acan
tasiya masu kayan amfani dayawa, sede yawan siyayyar
duk ta Yar Baba tafi yawa, kananan kaya ma duk nata
sunfi yawa, dasauran kayan amfani na yan mata. Data
gama suka wuce gurin tela, anan tayi mashi bayanin
yanayinsu tabiya kudin dinki yabata ranar karba.
Jakadiya Karima ce zaune afalon Gimbiyar Babbar Gida
tare da Medaki, Gimbiya tace waini Jakadiya kina kula da Suhailat kuwa? Kada fa ta shammacemu kamar yanda
Rayhana tayi mana. Jakadiya tace haba Ranki yadade ai
ita da haihuwa sede alahira, kada kidamu bazan baki
kunya ba. Murmushi tayi tace, haka nakesonji.
Medaki tace bari intashi inje nasan yanzu angama shirya Sarki inje induba jikinshi, yamutsa fuska Gimbiya tayi ta kauda kai, Jakadiya tace afito lafiya Gimbiya. Tana fita Gimbiya taja tsaki tace aikin banza kamar wata tsiya zata iya yimashi, ni wannan mata tsau tsayi ne kawai yasa
Sarki ya aureta, shide talaka duk yanda akayi dashi baya iya sakewa. Shiru de Jakadiya tayi bata ce komai ba, tashi tayi tace bari inje gurin Sarkin Fada.
Koda Jakadiya Safeeya takoma part dinta har lokacin
maman Yar Baba bata tashi daga baccin datakeyi ba,
saboda acikin maganin da likita yabata akwai mesa
bacci, dan yace idan tana yawan bacci kwakwalwarta
zatafi samun hutu, YarBaba kuwa tana zaune tana kallo.
Jakadiya tace Yar baba zokiga wani abu, tashi tayi
tamatsa kusa da ita tazauna tare da jingina da jikinta, jakadiya Tayi murmushi tace, hmmm ke kam mage ma
nan taganki tabarki inde gurin sonjiki ne. Dariya Yar
Baba tayi takara kwantawa jikinta.
Kayan tafiddo tafara nuna mata, hada inner wears duk
tarika gwada mata yanda ake saka su, se murna Yar Baba
takeyi, Jakadiya tace zankoya maki yanda ake amfani
dasu duka, kuma kinsande nafada maki banason kazanta
ko? Kai ta daga mata, tace yauwa, yanzu tashi muje ciki kiyi wanka semu fara.
Ranar litinin Areef yafara zuwa office, aranar duk macen data ganshi se miyanta ya tsinke, sbd kyawun da yayi,
tare suke da Haisam, Areef yace nifa nafara tsarguwa,
naga se kallona akeyi. Dariya Haisam yayi yace kada
kadamu sunga dan saurayi me kyau ne. Duka ya
kaimashi yana fadin kai dan iska ne, yace emana kasani
ko anan kasamu zabinka tunda babu yar gidan sarauta
acikinsu.
Areef yace Allah ya kyauta, anfada maka ni matata zatayi aiki ne, lallai ma, kai bakasan irin macen danake so na aura ba. Kawaide katayani da addu,a. Haisam yace ato
idan kuma nizan rigaka aishikenan,Areef yace nima zanfi
son haka, da haka suka isa Office dinsu.
Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai sbd yanzu
yanashan magani tunda yaji maganar da Malam yayi,
kuma yana cin abinci sosai, hakan yasa Sarki Qaseem
yace afara fita dashi fada hakan zerika rage mashi zaman kadaicin dayakeyi.
Haka suka cigaba da rayuwa agidan Sarki, babu wanda
yasan dazamansu, aduk lokacin da Baba yaso ganin Yar
Baba yakanje yaganta susha fira, har mamakin ganin
yanda tacanza cikin lokaci kadan yakeyi, gashi tsafta
agurinta kamar da ita aka halicceta, akullum setayi
wanka so 3 kuma ko sallah tayi setayi kwalliya, Jakadiya safeeya kam har mamakin saurin fahimtar datake da ita
take, kome takoya mata ba wuya tadaukeshi.
Akullum da dare kafin su kwanta se sunyi karatun
littattafai, dan zaman datayi takara sanin abubuwa
dayawa agurin Jakadiya safeeya, harta da girki tafara
koya mata, sbd tace idan bata nan setarika dafa masu.
Duk da ankawo dinkunansu amma bata son saka atamfa
ko less, tafison tasa kananan kaya, Mamanta kuwa tunda
takeshan magani, yanzu haukanta da sauki, batayin
komai, sede tazauna tayi shiru idan kuma kaga tana
dariya to ita da yarta ce, duk da baccinta yafi yawa akan idonta biyu.
Zaune Areef da Haisam suke acikin lambu suna hutawa,
babu kowa agurin, danshi Areef becika son fadawa suna
binshi ba, yafison daga shi se Abokinshi Haisam wadda
yakasance da ga dupty gvernor na gombe, kuma tare
sukayi karatu dashi.
Yar Baba tana gama kwalliya tafito dasauri dan ta nuna
ma Jakadiya dan tasan bata fita ba, tana zuwa falo taga bata nan, kitchen tashiga nan ma bata ganta ba, turo
baki tayi dantagane tafita, hanyar dataga tana bi tashigo ko tafita tabi, tana zuwa ta tura kofar cikin sa,a tajita abude, murmushi tayi tafita.
Cike da tsoro tafara takawa tana bin cikin lambun,
swimming pool tagani kallonshi tayi. Taci gaba da
tafiyarta, can taji dawisu yafara kuka, ai batasan lokacin data juya dagudu zata koma inda tafito ba, cikin rashin sa,a tayi tuntube da dutse kawai tafada cikin ruwan.
Su Areef dasuke zaune nesa da ruwan sukaji karar wani
abu acikin ruwa, koda Areef yakai kallonshi ga ruwan
kawai yaga mutum yana ta daga hannu da kafa acikin
ruwa. Cikin sauri yatabo Haisam yana nuna mashi, duk
da basu san kowaye ba, Dasauri suka nufi bakin ruwan.
Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
(The story of hard kingdom)
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@House of Novella Association
(H,O,N,A)
www.NabilaLady5@gmail.com
Season 70 ⚜75
Babu bata lokaci Yarima Areef ya fada cikin ruwan, yana zuwa kusa da ita yadaukota, alokacin tasha ruwa harta
suma, fitowa yayi daga ruwan tana rungume ajikinshi,
abisa kafet din dasuke zaune yakwantar da ita yadora
kanta saman cinyarshi, Haisam yana biye dashi duk sun
rude.
Kallon tsoro, mamaki suka farayi mata, addu.a duk
wadda tazo bakin Areef yinta yakeyi danshi gani yake
kamar ba mutum bace. Haisam yace Areef bakada
hankali kana ganin kamar ba mutum ba amma zaka
dorata akan cinyarka? Tunda de kacirota tashi mutafi,
fara jan hannun Areef yayi.
Areef da jikinshi yagama mutuwa sbd tsabar firgici bema san yanayi ba. Da karfi yajashi sannan yadawo
hankalinshi, katashi mubar gurin nan, nidama can
nafara zargin gurin, gashi yanzu munfara gani. Areef
yafara girgiza kai, yamaida kallonshi kan kyakkyawar
fuskarta, sannan yace ba aljana bace, duk da bantaba
ganinta amasarautar nan ba, amma kalli kafarta babu
alamun tako ajiki. Haisam yace anfada maka aljanu basa
fitowa asiffar mutane? Hmmm kaga malam wannan
yarinya kyanta yayi yawa, wlh zantafi inkira mutane ko
katashi mutafi.
Idanun Areef suka cika da kwalla yakalli Haisam yace dan Allah, katsaya ni nayarda mute maketa ta farfado, kaga
zamu fidda kanmu daga zargin da muke mata. Haisam
yace naji, idan ma Mutum ce daga ina tafito? Areef be
tsaya bashi amsa ba, kawai yaduka tare da saka bakinshi cikin nata yafara hura mata iska, shiru yaji, yamike yana kara kallonta.
Kamshin jikinta duk yagama cika mashi hanci, Haisam
yace kadanna cikinta, hannu yasa, jikinshi se rawa yakeyi yafara danna cikinta, can sega ruwa yafara fitowa ta
bakinta, haka yayi tayi, harseda tagama fitar da ruwan
datasha.
Tari tafarayi hakan ya tabbatar masu data farfado, cike da firgici ta tashi ta shige jikin Areef, duk ta kanan
nadeshi, tafara kuka. Areef kasa magana yayi, dan duk
tasakan mashi kasala ajiki, dukawa Haisam yayi yace ya
isa haka, tashi muji daga ina kike.
Kintashi tayi, sede tadena kukan datakeyi , tayi lamo
ajikin Areef kamar wata yar baby, Areef kuwa kallonta
kawai yakeyi, bemasan abinda Haisam yake fada ba,
ganin haka yasa Haisam ya bugi kafadar shi, dasauri yamaida kallonshi gurinshi, gira yadaga mashi yana fadin kallon fa nameye?.
Kabari mutambayi yarinya daga ina tashigo amma
kawani rungumeta kamar kana shirin bata mama.
Murmushi Areef yayi yana sosa kai. Dagota yayi, ahankali ta tashi tana kallonshi, sede taki barin jikinshi, se rawar sanyi takeyi.
Areef yace daga ina kike, meyakawoki nan har kika fada
ruwa? Hannu ta daga tana mashi nuni da hanyar part din
Jakadiya Safeeya. Haisam yace baki iya magana ne, kinaji ana maki magana zaki tsaya kina mana maganar
kurame, kuma gashi alamu yanuna kinji me yace.
Komawa tayi jikin Areef zata kwanta, dan gaba daya wani zazzabi takeji, sanyi sekara shigarta yakeyi.
Dasauri Haisam yajawota yana fadin yau ko sunanki
mage senaga karshen son jiki. Areef yace haba bros
kabita ahankali mana, kama hannun Areef tayi tarike
sosai tafara kuka. Tsaki Haisam yaja yace toni zantafi.
Areef kamar zeyi kuka yace plsss kabari muji daga
bakinta. Kallonta yayi, yace Beauty tashi kifadamun daga ina kike kinji, kinga kada yatafi yabarni kuma nasan
mutane zekira kuma kamaki zasuyi, ai dasauri ta tashi
tarike hannunshi, shima tashi yayi yana murmushi.
Haisam yace daganinta batada gaskiya gashi daga yin
maganar kamawa tamike. Hannu tasa tana kara nuna
mashi hanyar data fito, Areef yace baki iya magana ne?
Kai tadaga mashi, tare da fara janshi zuwa hanyar.
Atunaninshi ko sanyi ne yahanata magana, hakan yasa
yafara binta. Da har Haisam ya kyaleshi se kuma yayi
tunanin kada ta cutar dashi seyabisu.
Sunkusa zuwa gurin sukaci karo da Jakadiya tafito daga
cikin gida hankalinta atashe. Cak ta tsaya tana masu
kallon mamaki, kara kallon Yar Baba tayi, nan hankalinta yafara tashi ganin kayanta ajike, sede ganin wanda suke tare, yasa taboye tashin hankalinta. Da gudu taruga ta
rungume Jakadiya Safeeya, janta tayi zuwa cikin gida,
suma suka bi bayansu.
Seda tashiga da ita daki tasata tacire kayan tace tasaka wasu kafin tafito, juyawa tayi takoma falo. Bayan
sungama gaisawa, Areef yace Aunty ashe beauty agidanki
take? Kawai muna zaune nida Haisam agurin lambu
semukaji karar wani abu acikin ruwa, muna dubawa
ashe ita ce tafada, koda nacirota, ta suma, da kyar ta
farfado. Shine tabamu tsoro, dan bamutaba ganinta
agidan nan ba, gashi kuma kyanta ya kai akirata da
aljana.
Koda muka fara tambayarta bata bamu amsa ba, sede
kuma tanajin abinda muke fada, shine daga karshe
tajawo ni muka taho nan. Ajiyar zuciya Jakadiya tayi jin bayanin da Areef yayi mata. Murmushi tayi tace Allah
sarki sannunku nagode sosai, inbadanku ba kila data
halaka, mantawa nayi ban kulle kofar ba, kuma nasan nitafito nema dan banyi mata sallama ba dazantafi.
Shirun dakaji tayi ai bata iya magana, tunda aka haifeta ahaka take, sede tanajin duk abinda aka fada. Tausayinta ne yakamasu, jikinsu duk yayi sanyi bakamar Haisam.
Areef yadaga baki zeyi magana kenan tafito, baki yasaki yana kallonta, gani yake kamar ba ita bace, tasaka riga doguwa me siririn hannu tayi mata kyau sosai, kalarta Ja ce, gashi bata daura dankwali ba, fuskarta tasha kwalliya kamar meshirin zuwa gasar kyau, hannunta rike da
comb, tana zuwa tafada jikin jakadiya ta mika mata
comb din.
Murmushi tayi tace Uhm Yar Baba sarkin kwalliya yanzu
seda kika kara wata kwalliyar? Kwantawa tayi jikinta
takamo hannunta tadorashi akan wuyanta, jakadiya tace
kai naji jikinki dazafi, ko ruwan dakika shiga ne, ze sakar maki Zazzabi?.
Kai tadaga mata, tana lumshe ido, Haisam yace Aunty ai
dama yakamata abata magani tasha, kada yarufeta. Jawo
hannunta takarayi tana mata nuni data sharce mata
gashinta, fara Sharce mata tayi tana fadin kuma gashi
babu magani agidan nan, sede inje gurin Gimbiya kozan
samu.
Haisam yace a,a bari kawai idan muka fita semu siyo
mata, kallon Areef yayi yace kai kuma mr. Watching seka tashi mutafi musiyo magani, shiru yayi mashi yana
kallon yanda tarufe ido tana bacci, ga gashinta daya
gama tafiya dashi. Dan bakinta yasha red janbaki, tayi
mashi kyau sosai. Dukan dayaji akafadarshi ne yamaido
dashi tunanin dayakeyi.
Hararar Haisam yayi, gwalo yayi mashi yana murmushi.
Areef yace Aunty amma bansanki da diya ba ina kika
samota? Tace tare muka dawo da ita daga Darazo, acan
gidan Malam take, diyar Dan uwanmu ce. Zekara
magana Haisam yace katashi muje musamo mata
magani bata lafiya, idan mundawo seka idasa tambayar
taka. Tashi yayi yana sosa kai yana murmushi yace Aunty semun dawo.
Kallonshi tayi tace dan Allah banason inji wannan
maganar agurin kowa, koda kuwa Gimbiya ce, ko Sarki,
kuje kudawo zakuji dalilina nafadar haka. Suka ce to, fita sukayi Areef yanayi yana waige, bugewar dayayi da kofa
ce tasashi saurin dafe goshin shi. Dariya Haisam yasa
hada rike ciki, suna fita Areef yakai mashi duka yana kara dafe goshin shi. Haisam ya tsagaita dariyarshi yana fadin sannu abokina ai bansan kaji zafi ba. Areef yace kacigaba lokacinka ne dariya ma yanzu kafara yimani inde akan
beauty ne. Haisam yazaro ido yace akwai wata a kasa
kenan? Areef yayi murmushi yace a,a sede asama dan
iska. Dariya suka saka kafin suka nufi hanyar parking
space.
Cak sarkin fada yatsaya ganin abinda beyi tsammani ba,
adede lokacin dayake fitowa daga part din Medaki, daka ganshi kasan baya cikin nutsuwarshi. Wani irin kallo
Waziri yake binshi dashi, cikin tsarguwa Sarkin fada ya matso yana washe baki yace rankaidade barka da fitowa,
nima yanzu nafito zani fada shine Jakadiya Karima take
shedamun Gimbiya Medaki tana nemana. Toyanzu
nashiga ko minti 3 ma banyi ba, tambayta tayi shine
kaga nafito. Muje fadar ai can kayi ko? .
Da ido Waziri ya kafeshi, bece mashi komai ba, kifce
kifce yafarayi yana fadin ai semu wuce ko? Murmushi
Waziri yayi ya girgiza kai yace muje, haka suka nufi fada cikin Sarkin fada duk ya duru ruwa, se addu,a yake Allah yasa Waziri be harbo jirginshi ba.
Baban Fulani ne zaune akofar gidanshi tare da Baba suna ta fira, dan zaman dayayi bakaramin sabo sukayi ba,
Baba yace gaskiya ina tausaya maka halin daka shiga,
tabbas ka hadu da jarabawa, sede kuma hakurin dakayi
gashi nan Allah yabarka da lafiyarka, kuma dama anason
me hkr aduk lokacin da wata jarabawa tasameshi. Baban
Fulani yace hakane, nima ada nayi niyar komawa kasata,
sede ganin irin karamcin da mutanen nan sukayi mani
da kuma rashin sanin Rayhana tana raye ko mace,
wannan dalilin shine babban abinda yahanani tafiya,
amma insha Allahu nasan za,a ganta tunda de anfada
mana tana raye. Baba yace ai Allah baya bacci, koma a
ina take wata rana zata dawo.
Koda su Areef suka koma jikin Yar Baba yarikice, Zazzabi ya saukar mata sosai, dan bata tabayin zazzabi
mezafinshi ba, se kuka takeyi dama kuma gata raguwa,
kwance take ajikin Jakadiya Safeeya suka shigo bakinsu
dauke da sallama, dasauri Areef yazauna kusa da
Jakadiya yana fadin Aunty bade jikin bane?.
Tace wlh kuwa, tunda kuka fita ta kwanta shikenan
zazzabi yarufeta, Haisam yace Aunty kawai kutashi
mutafi asibiti, zaro ido tayi tace A,a kawai ku kawo
maganin inbata nasan zata samu sauki, kaga abincinma
taki ci. Zata kara magana kenan taji motsi adakin Maman Yar Baba, saurin tashi tayi ta kwantar da ita bisa kujera tace inazuwa bari inshiga bandaki, Yarima kabata abinci kila taci seku bata maganin nasan zata samu bacci, bari infito.
Abakin kofa tasameta, dama tasan lokacin cin abincinta
yayi jira take Yar Baba ta kyaleta taje ta tadata tabata abinci tasha maganinta, saurin kama hannunta tayi
tasama kofar key suka koma ciki, bandaki tajata seda ta wanke mata baki tayi fitsari, sannan suka dawo tazauna
dan tabata abinci.
Abincin yadauka ya matsa kusa da ita, hannu yasa
yadagota, tana tashi ta lafe ajikinshi, zama yayi akan
kujerar, hakan yasa takara shigewa jikinshi. Dariya
Haisam yayi yazauna yana fadin wlh Beautyn Areef keda
mage bansan wanda yafi wani son jiki ba, Areef yace
kaga malam kabarta taci abinci tunda ba,a jikinka ta kwanta ba. Haisam yace ato adebi ahankali dan wlh
kosannu bazan cemaka ba idan kacemun,,,,,,, gira
yadaga mashi yana murmushi yace ai kagane?.
Areef yace kaide kasani dan iska kawai, kamata yayi ya
rungumeta ahankali yace kinajina ko beauty? Kai tadaga mashi tana turo baki, murmushi yayi yace yauwa idan
bakiso inkira mutane sukamaki to kici abinci inbaki
magani zaki warke, ai dajin haka tabude baki. Dariya
Haisam yayi yace anya beauty bata tsoron mutane
kuwa? Wannan shine karo na biyu danaga tana tsoro
idan ance mutane. Areef yace haka ne, nima nalura da
haka, kuma inaso Aunty tafito tadan bani labarinta, dan ban gamsu da bayaninta nadazu ba, yarinyar nan tafi
kama da diyan larabawa.
Haisam yace shiyasa naga kuna dan kama , harararshi
yayi yace ta ina? Haisam yace wlh ba batun wasa ba,
dazu data kulle idonta na kalleta naga kundanyi kama,
musamman tagurin idanunku da bakinku. Areef yace
kaji dashi, nibanga wata kama ba, kyaleshi yayi yadauki cokali yafara bata abinci.
Hankalinshi gaba daya yana gurin kallon yanda take cin
abincinta, shikanshi abun burgewa ne, tana jikinshi
ahaka tagama cin abincin, shiko Haisam kallonsu kawai
yakeyi, yafiddo waya yana daukarsu vedio, sun bala,in
burgeshi, gani yake kamar atare aka halicce su. Magani
ya ballo sede da kyar tasha, shima seda yayi mata wayo, tana gamasha ta koma jikinshi ta kwanta, kallonta yayi
yace bacci zakiyi? Kai tadaga mashi, tare da lumshe ido, ko minti 5 ba,ayi ba. Bacci yadauketa. Areef yace beauty bakida matsala, yarinya cekace jaririya acikin minti 5
harkinyi bacci.
Bayan tagama bata abinci tabata magungunanta, sannan
tajata zuwa bandaki, wanka tayi mata, bayan sunfito
tagoge mata jiki, ta dauko wata doguwar riga tasa mata, kwantar da ita tayi bisa gado. Idanu ta kura mata ganin yanda dan kwanakin dasukayi tasake sosai, kara kallonta tayi, gabanta taji yana bugawa dasauri, matsawa tayi
kusa da ita dan takara tabbatar da abinda tagani. Tabbas wannan matar zargin malam yazama gaskiya, wasu
hawayen farin ciki ne, suka rika fito mata, zama tayi
takama hannunta tana fadin ita ce, wlh itace, dama
nasan malam baze taba fadin abu yazama ba haka ba,
aiko ayau Sarki zeji labari medadi.
Waya tadauko takira Malam, bayan sungaisa, yace
Safeeya yanajiki cikin farin ciki haka? Wlh malam
tunaninka yazama gsky, dama kace kana tunanin
wannan matar kamar Gimbiya Fulani, wlh, itace, nadade
dafara tunanin haka tun akan diyarta, kamarsu da ita
nake gani afuskarta, sede bakowane ze gane hakan ba,
amma nide wlh yanda nasan Fulani kamarta bazata iya
bacemun ba.
Hamdala Malam yayi yace nadade da tunnin haka, sede kinsan irin wannan al,amarin ba,a saurin yanke mashi
hukunci, dole muyi ma Allah godiya, kuma zansa ayi
sadaka, sede akwai abu daya danakeso daga gareki,
wannan