Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar daga ni seke se Waziri mukasanta,

shima yanzu zankirashi infada mashi zarginmu yazama

gaskiya, ammafa dole muyi shiru da bakinmu, kinsan

idan har baka iya kama barawo ba, toshi seya kamaka,

acikin gidan sarautar nan, akwai munafukai dayawa,

idan bamubi asannu ba, bazamu iya kamasu ba.

Dan haka nasan haryanzu babu wanda yasan dazamansu

agurinki, inaso kicigaba da rike sirrinmu, har ranar da Allah zebama Gimbiya lfy, bincikenmu zefi tafiya dede.

Shiru tayi can kuma tace amma malam akwai mutum 2

dasuka san Yar Baba tana gurina, Yarima da abokinshi,

yanzu haka suna gidan nan,,,,,,,,, kwashe duk abinda

yafaru tayi tafada mashi, malam yace babu damuwa

inaso kibarshi ayanda kika fada masu, sede kada kibari

suga Gimbiya tunda dama kince bata fitowa falo,sallama

yayi mata yace zekira Waziri.

Falo tafita ta iske su zaune, murmushi tayi tace kuyi

hakuri nabarku dajira. Areef yace bakomai, hartayi bacci ma, Jakadiya tace kwantar da ita muje nima fita zanyi

nasan gimbiya tana jirana, Areef yace a,a muje inkaita

daki ahaka ai seta fado. Daukarta yayi kamar baby ya

nufi dakin jakadiya, saman gado yadorata, juyi tayi

takara rungumoshi, harseda yafada mata. Wani yarrr

yaji ajikinshi, murmushi yayi yacire hannunta yajawo

pillow yasa mata, nan take tarungumeshi, tsayawa yayi

yana kallonta, dukawa yayi ya sumbaci goshinta, tare da fadin Allah kasa Momy da Abba sukarbi zabina. Juyawa

yayi yafita.

Bayan malam yakira Waziri sundade suna magana,

bakaramin dadi Waziri yajiba dayaji bayanin malam,

haka suka dade suna tattaunawa, daga karshe Waziri

yace akwai wani sirri dana fara ganowa agidan nan

amma inaso inkara tabbatar dashi kafin infada maka.

Malam yace Allah yayi mana jagora, insha Allah komai

yakusa zuwa karshe, zan aiko da maganin me martaba.

Godiya Waziri yayi mashi sukayi sallama.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert lady)

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

AMAKABARTA AKA HAIFENI

🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

Season 75⚜80

Waziri ne zaune tare da Sarkin Fada, Waziri ya kalli

Sarkin fada yace, kasan nifa nafara gajiya da masarautar nan, bamu samun komai se wahala, shi wancan Yana

zaune, jaririma yafishi dadin sha,ani, shikuma Sarki

Qaseem bawani aiki yake ba, kullum da anyi magana

yace Yayanshi, kawai idan bazasu iya ba, yakamata

sumika ma nawajenka.

Amma kuma zamusha shiririta, dan nasan Yarima kwata

kwata sarauta bata dameshi ba, shiyasa kozaman fada

bayaso. Wata irin dariya Sarkin fada yayi, da alama

antabo mashi inda yake mashi kai kai, baki ya karkace

yafara zuba, ashede kaima kana layina, yoni idan tanine ai dayanzu an dade dashafe babin wadannan sarakunan





2.


Aduniya babu abinda natsana kamar inga wadannan

mutane 2 suna farin ciki, shiyasa bakaramin dadi najiba alokacin da akace Sarki ya samu matsalar shanyewar

barin jiki. Naso ace Sarki Qaseem be anshi sarautar ba, nasan kila da kai za abama.

Amma kana maganar wani Yarima ai har abada bazeyi

sarauta ba, sede idan ubanshi ya mutu, ai akwai dalilin dayasa bayason sarauta, anfada maka son danake mashi

nabanza ne? Nifa banason wani daga zuri'arsu yaci gaba

da mulkin nan. Waziri yace amma nasan duk ranar da

akace angano inda Fulani take nasan daga ranar Sarki

zewarke.

Dasauri Sarkin fada yace ina, ai har abada kuwa baze

warke ba, dan bana tunanin Fulani tana raye, saurin

kallonshi Waziri yayi yace kamar ya kenan? Rufe baki

yayi yafara in ina, yace a,a kagane bawai ina nufin

tamutu ba, gani nayi yau shekaru nawa da batan ta, inda tana raye ai da anganta. Wani murmushi Waziri yayi

yace dama musami labarin mutuwarta ai dayafi, Sarkin

fada dasauri yace wlh kuwa da kowa ya huta. Tashi yayi

yace bari inje gurin mutuniyata, waziri yace wakenan?.

Jakadiya Karima mana ai kasan duk gidan nan banida

aminiya kamarta, wato matar nan tasan takan duniya,

sallama yayi mashi yayi gaba. Wata irin zufa ce tafara

fitoma Waziri, ahankali yace Jakadiya Karima? Tasan

takan duniya? Aminiyarshi?. Murmushi yayi yace

nasamu daya, saura na biyu. Waya yaciro yakira malam,

sun dade suna magana kafin yakashe yanufi fada.

Areef ne kwance akafar Momynshi Jakadiya Safeeya tana

gefe suna fira, ahankali Gimbiya tashafi kanshi tace

Yarima haryanzu naji shiru tunda mukayi maganar aure

baka kara cewa komai ba, kasanfa kabar Abbanka cikin

damuwa. Wani murmushi yasaki tare da lumshe ido, ita

yakara gani aidonshi alokacin dayake bata abinci,

ahankali yace beauty.

Momy tace wacece kuma Beauty? Saurin bude ido yayi

yace kawai Momy inason mace me kyau, shiyasa kikaji

nace beauty, murmushi tayi tace to kasamu kenan? Kai

ya girgiza mata yace nade kusa samu kitayani addu,a.

Momy tace Allah yasa irin zabin muce? Bata fuska yayi

yamike tsaye yace Momy wai haryanzu baku cire

wannan ra,ayin daga ranku ba? Nifa agskiya bazan auri

yarinyar data taso gidan sarauta ba, duk wata al,ada tata da dabi'unta duk na sarauta, nidan sarauta itama yar

sarauta towazeyi mulkin kenan?. Shiru Momy tayi tana

kallonshi, tashi Jakadiya Safeeya tayi takama hannunshi tace haba dan autan Gimbiya, tomeye na bata ran?

Zomuje gida kafadamun abinda kakeso, amma nima

zanfada maka wanda nakeso, kayarda ? Kai yadaga mata

taja hannunshi suka fita, da murmushi Gimbiya tabisu,

aranta tana fatan Allah yasa ya amince.

Gimbiya Zakiyyah ce take tafaman masifa akan jakadiya

Karima, wai ke wace irin mata ce, harni zakizo kirika fada ma, wai Sarkin fada yana gaishe ni. Toshi wanene

dazemun wannan aiken, ko anfada maki ni baiwace

dazakizomun da wannan maganar. Amma balaifinku

bane, dan kunsami sakin fuska daga gurina ne, shiyasa

kuke fadamun abinda kukaga dama, inda narike mulkina

wlh ko kusa dani akace kizauna baza kizoba.

Kuma inaso kifadamun akan wane dalili Sarkin fada yace

kigaisheni? Kasa tayi da kai tace Allah yahuci zuciyarki, wlh bada wata manufa yace nagaisheki ba, dama ganina

yayi zanshigo nan shine yace ingaisheki, amma ai be isa yayi maki irin gaisuwar dakike tunani ba, agafarceni

Gimbiya. Zama tayi tana huci tace, wannan shine karo

nakarshe dazaki kara batamun rai, idan bahaka ba, wlh

sekin fuskanci hukunci na. Godiya nake ranki yadade

uwargida agurin Sarki, mace daya tamkar da dubu, fitila me haske zuciyar Sarki, Allah yakaramaki lafiya da

daukaka aduniya, Allah yasa kifi haka. Murmushi tasaki

sannan tadaga mata hannu tace muje kirakani gurin

Medaki inaso indubata. Zaro ido Jakadiya tayi tace Eye, na'am , mekikace? Wata harara tasakar mata tace kina

nufin bakiji menace ba? Nima yau inaso inje bangarenta.

Wani miyau medaci Jakadiya tahadiya, dan ta tuna sanda

zatazo nan sunhadu da Sarkin fada kuma zeje gurin

Medaki. Tashi tayi jiki asanyaye suka nufi bangaren

Medaki, bayi suna take mata baya.

Koda suka shiga azaune suka sami yar baba tana kallon

casset din da Jakadiya ta kunna mata, tana ganin Areef

tashiga sakin murmushi, shima murmushin yasaki, tare

da sakin ajiyar zuciya, kusa da ita yazauna yana fadin

beauty jiki yayi sauki ko? Matsowa tayi kusa dashi tadora kanta saman kafadarshi tare da daga mashi kai. Girgiza

kai jakadiya tayi aranta tace dole in nuna ma Yar Baba

matsayin kowane namiji agurinta, wato ita atunaninta

yanda take hawan Baba kowama zata mashi haka? Dole musake sabon karatu. Tanaso tace mata ta tashi kuma

bataso Areef yadauka dawata manufa, zama tayi akasa

tace zonan yar Baba inji jikinki.

Tashi tayi taje tazauna kasa tare da dora kanta saman

cinyarta, hannu tasa ajikinta tace ai zazzabin ma yatafi ko? Kai ta daga mata tana maida kallonta gurin Areef.

Itama Jakadiya shi ta kalla, aranta tace tabbas kuna kama daga idonku har gurin bakinku, saukowa yayi shima

yazauna akasa,ya kalli Jakadiya yace.

Aunty kina ganin idan nafitoma Momy da Abba wadda

naji zuciyata tanaso, kuma bata kasance yar sarauta ba, kina ganin zasu ansheta? Murmushi Jakadiya tayi tace

kwarai ma kuwa, amma dole sekayi abinda zanfada

maka idan bahaka ba to sede ka auri mata 2, nikam

banaso ka hada macen da kake so da wata, kana ganin

yanda Sarki yakasance alokacin daya samu wadda

yakeso, jiyayi dama beyi aure ba, da babu abinda zesa

yakara aure bayan ya aurin zabinshi. Kuma kasan yanda

sharrin matan sarauta yake, idan har sukaga mijinsu

yana nuna fifiko atsakinsu yanzu zakaga anfara shigo da hassada.

Kuma nibanason kayi wani abu daze zo yaraba zumincin

dake tsakanin iyayenka, duk da bangama gano wacce

kake so ba, amma inaso yanzu kafada mun. Shiru yayi

yana kara kallon beauty, itama shi take kallo, yace Aunty zanfada maki amma banaso beauty taji. Ai tanajin

abinda yafada tafara dirza kafa akasa, tana turo baki tare dayin bayaninta da hannu na kurame. Dariya suka saka,

yace metace wai?.

Jakadiya tace a,a ni baruwana kaine dakayi magana take

wannan borin. Kallonta yayi yace beauty ai wannan

maganar manya ce shiyasa nace banaso kiji, tashi tayi

tadauki pillown kujera takwada mashi tashige daki tana

dira kafa, dariya yayi hada rike ciki. Wayarshi ce tayi kara, yana dauka yace kasameni gidan Aunty.

Jakadiya tace hala Haisam ne ? Yace ai kinsan seshi,

shikadai ne abokina aduniya nayarda dashi kamar yanda

ya yarda dani, shiyasa bana tsoron yasan komai daga

gareni. Sallama sukaji, Areef yace kashigo mana katsaya kamar kazo gidan surukai.

Zama yayi bayan sungaisa da Jakadiya yamika ma Areef

hannu suka gaisa yana fadin ai garani bagidan surukan

nazo nazauna ba. Dariya suka saka, Areef yace yauwa

Aunty inajinki menene abinda kikeso inyi? Zama ta gyara ta kalli Haisam tasake fadin abinda tafada da farko,

sannan takara dacewa abinda nakeso da kai yanzu

kafadamun wace yarinya kakeso kuma a ina take, daga

nan ni kuma zanfada maka mezakayi.

Sarki Qaseem ne zaune afalon gimbiya suna fira tana

mika mashi kankana, kallonshi tayi tace Hubby, kayi

hakuri nayi wani hukunci kuma bansanar da kai ba.

Jawota yayi yasata ajikinshi sannan yace bakida damuwa kome kika yanke nasan zeyi dede da ra,ayi na, kinsan

muna tafiya akan tsari daya. Murmushi tayi tace haka ne, dama bawani abu bane, munyi waya da Yaya nace mata

tashiryo Ayman tadorota jirgi gobe ta taho.

Naga alamar Yarima yakasa samun wadda yakeso, nayi

tunanin baya shiga cikin yan mata ne, shiyasa besamu

wadda yakeso ba, amma idan Ayman tazo zansata tarika

yimashi duk wata hidima, kuma surika fita tare nasan yin hakan zesa su shaku har soyayya tashiga tsakaninsu.

Murmushi Sarki yayi yace, shiyasa nake sonki dayawa,

kinyarda ra,ayinmu yana tafiya dede? Kai tadaga tana

wasa da hannunshi. Yace amma ina fatan baki fadama

Ummin Aymana dalilinki nasan tazo ba ko? Tace kamar

kasani, banaso mushiga tsakaninsu harsesun shirya

kansu sannan.

Yace da kyau, nafison kamar yanda naganki naji inasonki kema haka banaso mushiga hakkin Areef, duk da idan ya

gwada bazebi zabinmu ba, bazanyarda ba, amma ko ita

kada kifada mata dalilin sawa tazo, kawai kibarta, nasan zasu saba. Rungumeshi tayi tana fadin nagode hubby na.

Kiss yayi mata akumatu, yana fadin bari inje gurin yaya yau likitan daze fara yimashi gashi zezo daga,

U.S, Tace Allah yasa adace, amma anan zezauna ko? Yace

e zeyi kamar wata guda, kuma insha Allahu munasa ran

nasara. Tace Allah yasa.

Da sallama suka shiga falon Medaki, sede bata nan, cike da fargaba Jakadiya karima tace rankiyadade kizauna

bari inje indubota, zata shiga kenan tafito tana fadin

ashe yau manyan baki garemu, Gimbiya Yaya da kanki

aida kin aiko nazo. Ya mutsa fuska tayi tace kawai nima sha,awar fitowar nakeyi.

Zama tayi Jakadiya sebinta da idanu takeyi jikinta yana tsima, wata baiwa ce tashigo hannunta rike da katon

faranti medauke da kayan marmari, jakadayi tace barka

da fitowa Gimbiya, tace yauwa sannunki. Jakadiya tace

ina fatan wannan kayan marmarin nadazu da aka kawo

marasa kyau anfitar dasu ko? Medaki ta kalli Jakadiya,

tayi murmushi tace ai basu dade bama. Gimbiya

Zakiyyah tace shiyasa nakeso arika duba kayan daza,a

kawo base ankawo ba ace basuda kyau.

Jakadiya tace kwarai ma kuwa, ai tunda basu cikin gidan nan hankalina ai yakwanta. Gimbiya Zakiyyah tace se

akara kula. Medaki datake dariya aciki takara kallon

Jakadiya wadda jikinta yayi sanyi, aranta tace lallai

Jakadiya yar duniya ce, aifa sekayan marmarin, Sarkin

Fada ai yamafisu komai. Gimbiya Zakiyyah tace yanzu fa

idan Sarki yafadi ya mutu shikenan munzama yan kallo

agidan sarauta ko?

Medaki tace nima nayi wannan tunanin anya babu saka

hannun kaninshi arashin warke warshi kuwa? Ace ciwo

shekara 18 harda watanni amma be warke ba. Kiduba fa

kiga yanda yaki yarda afitar dashi waje, kullum seyarika fadin wai yace baya so, to mutumin da baya magana

taya zece bayaso?

Jakadiya tace nizan fada maku haka, nida ake komai

agabana, aduk lokacin da za,ayima Sarki gashi ko za,a

bashi magani, daga Sarki Qaseem se Waziri kadai suke

shiga dakin, nima nasan akwai abinda suke kullawa, kalli yanda Waziri da Sarki suka hade kansu, kullum yana

manne dashi, Sarkin fada beda wani anfani agurinsu.

Gimbiya Zakiyyah tace, to gaskiya bazan yarda ba, daga

yanzu inaso kirika saka idanu akan duk wani abu

dasukeyi, tunda kowa yasan kece makusanciyar Sarki,

dole subarki kizauna tare dashi. Jakadiya tace angama

Gimbiya, tashi tayi tace nizan koma. Medaki tace nagode, kigaida gida sena shigo.

Inajinka Yarima fadamun kasande babu abinda bazan

iya yimaka ba, dan farin cikinka. Shiru yayi yana sosa kai, Haisam yace Aunty wlh beauty yakeso, tunda nake da

Areef bantaba jin yayi maganar wata ba, amma aranar

dayafara haduwa da beauty beda magana se tata,

kumani tun alokacin nagane yafada soyayyarta, amma

sanin halin iyayenshi yasa yayi shiru.

Jakadiya Safeeya tace, na jima dasanin haka, sede akwai abinda nakeso kasani, idan har kanason yar Baba dole

Kaboye ma Iyayenka harse zuwa wani lokacin daya

kamata, banaso azo ahada tashin hankali, wanda zeyi

sanadiyar rushewar zumunci. Areef yace Aunty akwai

wani zumunci atsakaninki dasu Abba ne? Saurin girgiza

kai tayi tace bahaka nake nufi ba, kaide kawai kayi yanda nace, kawai kanuna masu kana nema nan da dan lokaci

komai zezo karshe.

Areef yace amma Aunty yanaga kamar beauty ba irin ta

yan nigeria bace, gsky kyanta yawuce misali. Rasa

mezata ce mashi tayi, tace kasan dangin mamarta ba yan

nan bane, buzaye ne. Areef yayi murmushi yace haba

shiyasa. Amma haka aka haifeta bataji, tomeyasa ba,a

kaita asibiti ba? Jakadiya tace gsky ba,a kaita asibiti ba, kuma banaso kace zaka kaita ayanzu, idan lokaci yayi

seka kaita, nima inaji ajikina kamar zata warke. Haisam yace mungode Aunty Allah yabiyaki, tace amin, tashi yayi yace bara inje inbada hakuri.

Jakadiya tace, a,a nasan tayi bacci kabarta kawai anjima sekadawo. Haisam yace malam muje akwai inda nakeso

muje, sallama sukayi mata suka fita. Ajiyar zuciya tayi tace Allah katona asirin mutanen dasukayi wannan abu

kowa yahuta, nasan Gimbiya zakifi kowa farin cikin zabin da Yarima yayi, sede ina tsoron zuwan Ayman kada

ahada rigima, nasan duk mun son da kikema Fulani

bekai na yar uwarki ba. Tashi tayi tashiga dakin Fulani.

Zama tayi takura mata ido tana kwance tana bacci, tace

tabbas wahala tana canzama mutum kamanni, nayi

mamakin yanda banganeki ba tun farko, amma ba abun

mamaki bane, sbd irin wuyar da kikasha ashekaru 18 ko Sarki baze iya ganekiba. Fita tayi tanufi dakin beauty.

Jawota tayi tana fadin haba yar leleta, yihakuri, yace

zedawo anjima ai, kobakison yadawo? Kaita girgiza tana

turo baki, dariya Jakadiya tayi tace, shikenan, tashi muyi wata magana me amfani, tashi tayi tazauna tare da dora

kanta bisa kafadar Jakadiya, murmushi tayi tace Sarkin

son jiki, to kinsan menakeso infada maki? Daga yau

banason inkara ganin Yarima yazo kinhau jikinshi, ko

hannunshi banaso kitaba, kinsan nafada maki babu kyau

kataba namijin da ba,a maku aure ba ko? Dan haka

yanzu yace yana sonki, kuma aurenki zeyi.

Tokinga duk macen da akace anaso bazata kara bari

saurayinta yataba taba harse an daura aure, kinji ko? Kai tadaga tana rufe fuska, Jakadiya tace kobaki sonshi,

dasauri tayi mata alamun a,a dariya tayi tace kamar

gaske keda bakisan wani so ba. To inde kinasonshi idan

yazo kirika zama nesa dashi kinji? Ta daga kai. Jakadiya tace yauwa tashi kidauko Fikhu mucigaba da karatunmu.

Shiru Sarkin fada yayi yana jin bayanin Jakadiya

karima, harta gama yayi dariya yace lallai, wato nine ma kayan marmarin? Amma kinhadu, wlh kamar nasani

inazuwa nace mata sauri nakeyi. Ita kuma Gimbiya dan

tasamu ance ana gaisheta zata fadamun haka. To wlh

tunda miyau na yabiya da ita kota halin yaya senasha

romonta. Jakadiya tace wlh bakada dama, wato duk

matan Sarki seka more? Yace kede muje zuwa kawai.

Washe gari tunda safe aka shiga da Sarki Hasheem dakin

gashi, inda sabon likitan yafiddo kayan aiki masu nagarta yafara yimashi gashi dasu, Sarki Qaseem da Waziri se

addu,a sukeyi Allah yasa adace. Jakadiya Karima ce tayi sallama tashigo falon, bayan tamika gaisuwarta da

tambayar me jiki, tace dazu naga wani bature shine nace ko bako mukayi ne?

Waziri yace abokin Sarki ne, tace aiyo, nace memartaba

ko wanka akemashi ne? Waziri yace dan Allah kifita

koma menene idan angama za,a kiraki, tashi tayi tana

cewa to to afito lafiya, da harara yarakata aranshi yana fadin tabbas abinda zuciyata take fadamun akanki yafara zama gaskiya, amma muje zuwa nasan lokacin yataho.

Sarki yace meyasa baka fada mata gaskiya ba, kasan

aduk gidan nan babu wadda Yaya yakeso kamarta, Yanda

muka dauketa kamar Uwa take agaremu dan mundade

da ita. Waziri cike da takaici yace nasani, kawai banason yawan magana ne kasan addu,a mukeyi shiyasa nace

mata haka dan karta katsemu. Kallonshi Sarki yayi badan ya yarda da abinda yafada ba.

Sarkin fada ne zaune adakinshi hannunshi rike da wani

abu yana kallo yana murmushi, yace Gidan sarauta babu

gsky, nasan wata rana dole asirinmu zetonu, akullum

idan bayi suka hada kai da yan sarauta karshe sune

masha wuya, nasan mu munfi bayi matsayi, amma

kuma kaskantattau Gimbiya take daukarmu agidan nan, ranar tonan asiri aranar zakamun rana. Dariya yayi

yamaida abun cikin jakarshi yana fadin wai Sarkin Fada?

Kode Sarkin tsiya? Wata dariya yayi yace koni ina tsoron kaina.

Seda Ayman takwana 1 dazuwa sannan suka hadu da

Areef, yafito da yamma cikin shirin fita afalo yagansu

zaune, Areef yace kai, Momy yaushe Ayman tazo bansani

ba? Murmushi tayi tace kana can gurin Haisam kuma

sanda kadawo tayi bacci, dasafe kuma kafita aiki bata

tashi ba, dama cewa nayi zaka ganta da idonka. Dariya

yayi yazauna yana fadin mutanen misrah tace Yaya Areef

inakwana, yace lfy lau, kinzo lafiya ya yan gidan? Tace lafiya lau suna gaisheka, yace to ina tsarabata? Tace tana nan, yace yauwa bari inje Haisam yana jirana idan

nadawo zan karba.

Momy tace inazakuje? Yace wlh kawai zamufita garine,

tace to ai dakuntafi tare itama taga garin, yace hakanefa taso muje kiga birni, dariya tayi tace wane birnin kuma, fita sukayi suna fadin semun dawo Momy. Da kallon

sha,awa tabisu tana murmushi, tare da fadin Allah kasa

su hada kansu amin.

Tare suka jero har bakin motar da Haisam yake tsaye

yana jiranshi. Idanu Haisam yaware yana kallon Ayman

wadda taketa dariya ita da Areef, gaba daya tagama

tafiya dashi, suna zuwa gaban motar Areef yace yi hakuri kaga wadda ta tsaidani nan, se alokacin itama ta kula

dashi. Idanu itama tazuba mashi tana kallonshi cike da

burgewa, gaba daya yagama tafiya da ita. Areef ya tsaya yana kallon Haisam wandda bemasan abinda yakeyi ba,

juyawa yayi yakalli Ayman, itama mamaki tabashi yanda

ta tsaya tana kallon Haisam, dariya Areef yayi ya harde hannuwa akirji tare da jingina jikin mota yana fadin ikon Allah.

Nima nace Ikon Allan gaske, Areef tayani gani.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

AMAKABARTA AKA HAIFENI

🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

Season 80 ⚜85

Season 80 ⚜85

Da karfi Areef yabugi kafadar Haisam yana dariya, cikin sauri Haisam da Ayman suka dawo cikin

hankalinsu, kunya duk takamata ganin Areef yagane

kallon dasukeyi, cikin dakewa Haisam yace wlh kai dan

iska ne, ni nayima haka lokacin dakaga Beauty?.

Dariyar da yakeyi ya dena yana fadin ai gani nayi

kunmaida ni dan kallo, Haisam yajuya yakara kallon

Ayman wadda ta sadda kanta kasa tana wasa da

yatsunta, murmushi yayi yace yaushe kukayi bakuwa

bansani ba?.

Areef yace kaide kashiga mota muje, kuma kabani key

din, Haisam yace saboda? Areef yace kaima kasan bazan

shiga tukinka yanzu ba, idan ko zaka tuka to wlh sede

acire center mirrior. Dariya Haisam yayi ya cilla mashi key din, yana fadin ai se inzauna baya kaga nahuta da

waige.

Tunda suka fara tafiya Haisam yakasa zama dede, ita ko

duk kunya takamata, da kyar ta iya gaishe shi. Haisam

yace lfy lau kinzo lfy? Tace lafiya lau, Areef yace malam yazaka barni ina tuki karika juyawa gurinta anbarni

sekace driver. Dariya Haisam yayi yace Allah yabaka

hakuri Yaya Babba.

Dariya Areef yayi, yace kaji munafunci, zakayi bayani ne.

Wani gurin shakatawa sukaje, bayan yayi parking suka

sami guri suka zauna, haryanzu Haisam yakasa dauke

idonshi akan Ayman. Jan Areef yayi gefe, anan yace dan

Allah abokina ina kasamo wannan me kyan? Dariya Areef

yayi yace diyar Yayar Momy ce fa, jiya tazo, nima seyau naganta shine Momy tace mufito tare. Ajiyar zuciya yayi yace Allah yasa wani beriga ni ba, kasan Allah? Alokacin dana ganta jinayi numfashina yana neman tafiya.

Bantaba haduwa da macen data tafi dani alokaci guda

ba, se Ayman, kuma yanzu ba se anjima ba, zanshigar da

kaina. Areef yace ai bazaka sha wahala ba, dan naga

itama ta kyasa. Haisam yace muje munbarta ita kadai,

Areef yace kawaide kutashi mutafi gida nima wlh beauty

na nakeson gani. Haisam yace dan Allah kabani 5

minutes ya isa.

Cikin wani shopping complex Areef yashiga, haka yayi ta daukarma Beauty kayan lashe lashe. Zama Haisam yayi

akan kujerar datake fuskantar Ayman, shiru yayi yana

kallonta har nawani lokaci, ahankali cikin murya mecike da so yakira sunanta da Angel. Seda taji wani Yarrr

alokacin dataji sunan, kara dukar da kanta tayi tana

murmushi.

Kara kiran sunan yayi, ganin bazata dagoba yace haba

Angel, ko rowar fuskar ake mani? Wlh bazan boye maki

ba, tun lokacin danayi ido biyu dake, kika tafi da

zuciyata, Allah yasa babu kowa ataki zuciyar kamar

yanda tawa take empty? Wani dadi ne yaziyarci zuciyarta jin abinda yafada.

Angel kode in hakura akwai wani dan uwanki kuma dan

kasarku wanda yarigani. Batasan lokacin datace a,a ba, dariya yayi yace kina nufin nasamu karbuwa kenan? Kai

tadaga, wani sanyi yaji aranshi, hannu yamika mata yace tobani wayarki insa maki number ta.

Yana cikin sawa Areef yadawo hannunshi dauke da

manyan ledoji guda 2, yace kai wlh nagaji zantafi kuma

sede kunemi mota. Haisam yace ai mungama harna

kashe boss. Dariya yayi yace ainasan dama bazaka sha

wahala ba. Ayman cikin hausarta wadda bata goge ba,

tace Yaya tsaraba kasiyomun?.

Dariya yayi yace haba Ayman ai yanzu kinfita daga

hannuna, nima iyalina nasiya mawa. Turo baki tayi tace

kai Yaya yaushe kayi aure? Yace keyanzu aure kikayi dana ganki kina fira? Murmushi tayi tare da saddar da kanta.

Haisam yace Angel tashi muje kizabi abinda kike so,

Areef yace oho de, aide seda nayi sannan kuma kuyi

sauri.

Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai, dan yanzu yafara motsa hannunshi da kafarshi dasuka dena amfani ada,

bakaramin dadi Waziri da Sarki Qaseem sukaji ba, sede

haryanzu befara magana ba, kuma akullum tare suke fita

dashi fada, sede idan yana bacci.

Acikin matanshi babu wadda take zuwa gurinshi da

sunan wani abu, tsakinsu dashi sede su shiga su duba

jikinshi, amma ko abinci Waziri ko Sarki Qaseem suke

bashi.

Gimbiya Suhailat ce, zaune tare da Sarki, kallonshi tayi tace kasan hubby Ayman da Yarima sunfita yawo,

bakaga lokacin daya ganta ba, yanda yake fara,a, itama

haka, wlh bakaji yanda naji dadi ba. Sarki yace lallai

munkusa shan biki agidan nan, sede inaso abari har yaya yakara samun sauki sannan. Tace hakan ma yayi, Allah

yakara mashi lafiya, yace amin.

Suna dawowa, suka nufi gidan jakadiya Safeeya, sede

Areef yace ma Haisam sujirashi yashiga yayi magana da

Aunty, kade gane menake nufi? Haisam yace hakane

gskiya jeka bari muzauna alambu.

Bayan sun gaisa yayi mata bayanin abinda yake tafe

dashi. Wani irin dadi ne, yashiga zuciyarta, sede bata

fada mashi dalilin zuwan Ayman ba,kallonshi tayi tace

gskiya naji dadin wannan maganar kuma Haisam

mutumin kirki ne, nasan ko kanwarka yanuna yana so

zaka bashi, dan kafi kowa sanin halinshi, amma akwai

wani abu guda danakeso infada maku daga kai har

Ayman.

Kada ku kuskura kubari Gimbiya ko Sarki wani yasan

tarayyarsu da Haisam, kasan dalilin dayasa nafada maka

haka? Saboda kasan ra,ayin iyayenka akan sarauta, kubar abin aranku, nan da wani lokaci komai zeyi dede, kaima

alokacin zanyi masu maganar Yar Baba, kaga se ahada

datasu Ayman, kaje kakirawosu, bakomai nasan idan

nace ma Ayman kada tafadama kowa Yar Baba tana gida

bazata fada ba. Areef yace Aunty kamar akwai wani abu dakike boyemun dan Allah kifadamun, kinsan halina

babu wanda zan fada mawa.

Kai tagirgiza tace babu abinda nake boye maka, kaide

inaso kayi biyayya da duk wata magana dazan fada

maka, nafika sanin masarautar nan, dan haka kabi

abinda nafada maka, kasan bazan taba cutar da kai ba.

Kirawosu inyimasu jawabin dana maka, inaso inshiga

cikin gida. Waya yadauka yakira Haisam yace su shigo.

Bayan sun gaisa Jakadiya Safeeya tayi masu irin bayanin datayi ma Areef, kallon Ayman tayi tace inafatan kingane abinda nake nufi? Idan har kunaso burinku yacika to

kubi abinda nafada, bance soyayyarku akwai matsala ba,

sede kuyi hakuri na wani lokaci zaku gane abinda nake

nufi. Ayman tace mungode Aunty kuma bazan fadama

kowa ba. Tace naji dadin haka, bari inshiga cikin gida.

Yar Baba tana shiryawa ne. Kasan mutuniyar ko bacci

zatayi setayi kwalliya.

Areef yace ai haka akeso Aunty, wai niko Aunty Beauty

bata iya rubutu ba, inaganin kamar tunda tanaji ai zamu iya fira ta waya, muna rubutu ko kuma ta takarda. Shiru tayi kafin tace , kasan tunda tagirma aka gane bataji,

shiyasa ba,a sata makaranta ba, amma karatun addini

tasan abubuwa da dama kuma Allah yabata wata baiwa

tasaurin fahimtar abu, kome aka koya mata cikin lokaci

kadan zata daukeshi, har mamakin kokarinta nakeyi, ni

kaina danayi boko da hada rubutu zan rika koya mata.

Haisam yace, abu me sauki kenan, ina ganin Areef kafara koya mata rubutu, ahankali sekurika shiga cikin karatun boko, kuma nan gaba za,a iya daukar mata me lesson.

Areef yace hakane, tunda tana saurin fahimta, insha

Allahu setayi karatu, Allah yayi mana jagora, Aunty

kirata, se mubar mata Ayman muje muyi sallar magrib.

Bayan tafito, tazauna kusa da Ayman, tana ta murmushi,

Ayman ma murmushi tayi tare da jawo hannunta, ai

kamar jira take tadora kanta saman kafadar Ayman,

dariya duka suka saka, jakadiya Safeeya tace naga ranar da zaki dena son jiki kekam, daga ganin mutane, baki

santa ba amma kin hayeta. Daga ta tayi tana murmushi,

Ayman takara jawota tace Aunty kibarta, kinga dama

bani da kanwa yanzu nasamu, kwantawa tayi

1 Comments On A MAKABARTA AKA HAIFE NI
avatar
najjwa

9 months ago

Reply

gaskiya littafin yanada dadi

Please Login or Register in order to submit comment