Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa ya hak'uri ya janyo filet d'in, yana Kai
lomar farko take ya zabura ya Fara lezaya amai tamkar
zai amayar da hanjin shi. Ita ko ta bishi da kallon takaici,
to miye illar wannan abincin, gashi nima naci tawa har
na k'oshi, don ma in k'ara gyra mashi ita har da k'wai na
saka aciki, zancen da take yi azuciyar ta kenan. A fili
kuma ta taso tana yi Mai sannu had'e da tambayar miye?
Nan yakai duban shi gare ta yace yanzu fisabilillah
Lateefa haka ake dafa indomie, kin tashi kin zabgama
Abu tarugu haka, ga k'arnin k'wai na tashi, sannan kin
cika gishiri. Tace duk Kai ka jiyo wa'annan abubuwan ni
dai naci abata lafiya lau. Hakan yaja jiki ya shiga kicin ya
had'a tea yasha, sannan yayi wanka yayi kwanciyar shi.
Jin shiru yasa Lateefa ta biyo bayan shi koda tazo har ya
kwanta. Hakan tazo kusa dashi ta kwanta sai k'amshi take
zabgawa, tace Kimba kayi hak'uri kar ka fara kawo muna
matsala a rayuwar auren mu. Yace Lateefa matsala ta
d'aya dake rashin kulawa ta 6angaren girki, ko so kike yi
afara tsegumin cewa mijin ki na yawon restaurant? Tace
to kabari muyi ma Mum magana ta samo muna y'ar aiki.
Yace au bama ki koyi aikin ba sai dai anemo Mai aiki.
Tace gaskiya sai dai kayi hak'uri ni ban iya zaman shiga
kicin girki. Hakan suka yi ta rigima tsakanin su saida
Shureim yace shikenan za asamo y'ar aiki d'in, nan suka
shirya sai gashi anfara shan soyayya, nan na fito na
janyo k'ofa har Ina cin Karo da k'ofa ```lolx```
****************** *WACE* *CE* *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng*?
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng d'iya ce gun malam salisu da Inna uwani.
Gwaggo lami itace Mace ta farko a wurin malam salisu,
auren zumunci ne akayi dashi da ita. Sun kusa shekara
takwas da aure Gwaggo lami ko 6atan wata bata ta6a yi
ba. Daga baya ne Allah ya had'a malam da uwani wurin
yawon saye da sayarwar shi ya had'u da ita can k'auyen
raha. Lokacin da yazo da maganar Gwaggo lami hauka
ce kawai bata yi ba, duk iya abinda zata yi tayi amma
kash Allah ya k'addari sai uwani ta shigo gidan. Bayan
anyi aure ne uwani ta tare, ta Fara cin karo da uk'uba
hd'e da masifa gurin Gwaggo lami. Amma fa duk abinda
take yi bata yi gaban malam akan tsananin makircin ta.
Cikin hakan Allah yaba uwani ciki Wanda Gwaggo na
hango hakan ta k'ara tsanan ta k'iyayyar ta had'e da
takurawa zuwa ga uwani. Ta yita samo abubuwa masu
zubar da ciki tana bata har tayi nasarar zubar da ciki
uku. Akan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne Allah yayi ikon shi da iyawar shi har
aka haife ta. Zun azab tu kuma sunga takura a hannun
Gwaggo, har uwani ta had'u da ciwon hawan jini Wanda
yayi ajalin ta. Koda ta rasu BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng nada shekara uku da
haihuwa, y'an uwan uwani sun so su kar6e ta malam ya
basu hak'uri ya rik'e abar shi. Tun tana da shekara biyar
ita ke ebo ruwa rafi ta cika duka kayan gidan. Lokacin
har islamiya malam ya saka ta cikin makircinta ta janye
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng daga zuwa makarantar saboda yawon talla. Ta
boko ma malam yaso ya saka ta Gwaggo tace
makarantar y'an iska ce. Hakan ya hak'ura ba don baya
so ba sai don baya da yadda zai yi ne. Akwai lokacin da
yayan uwani yazo duba BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya d'an yi Mata siyayya,
nan Gwaggo ta kar6e kayan ta k'ona su, kuma ya nemi
alfarmar zuwa da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta yi masu kwana biyu Gwaggo
ta hana saboda lokacin malam bai gari. Hakan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng
taga renon azaba hannun Gwaggo har zuwa yanzu da
aka yi Mata aure tana da shekara goma sha hud'u. ©
*SDY* *JEGAL* [10/28, 1:33 PM] +234 803 325 6478: 🍒
*BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *80*- *85*🍒 Kwanaki sun shud'e, watanni ma
haka har gashi shekaru sun shud'e. A cikin hakanne
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng take batun zana jarabawar junior living. An samu
fahimtar juna sosai tsakanin ta da Murtala. Ta waye sosai
ta 6angaren girki da kuma kwalliya, hakan ma tana
tarairayar mijin ta dai-dai yada ta iya. Cikin hakanne
arzik'in Murtala ya bunk'asa kasuwan cin shi sai ci gaba
suke yi. **************** Lateefa ta kowane 6angare
tana bama Shureim kulawa, sai dai matsala guda har
yanzu tak'i mayar da hankali 6angaren girki. Lokacin da
abin yayi yawa har Mum yaje ma da maganar, kuma ta
yi iya yin ta Abu ya gagara, dole haka ta hak'ura ta basu
Bizzy ta rik'a taya su aiki. Sai dai koda tazo itama girkin
sai a slow saboda gurin Mum ba girki ta keyi ba goge-
goge da shafe-shafe ne aikin ta sai kuma shara. Koda
tazo tayi girki ranar farko ta dafa farar shinkafa da miyar
tumatur, hakan Shureim ya daure yaci ba wai don
abincin ya yima shi ba. Shiyasa Mum ke bashi shawa ko
ruwan tea bata bari y'ar aiki ta dafa Mata. Yanzu da ace
Ina da mata biyu ko Lateefa bata iya girki ba ai d'ayar ba
zata rasa iyawa ba. Tuno da furucin ta akan kishiya yasa
gaban shi ya fad'i dammm. Koda ta shigo d'akin yana
shiri gaggauce zai je asibiti, hakan ta yi sauri ta kawo Mai
ruwan tea ta had'a Mai. Nan dai ya jure yasha ba wai
don ya yi mashi dai-dai ba. Tare suka fito ta shiga gidan
mak'wab ciyar ta Mmn zahra, saboda Allah ya had'a jinin
su. Tana shiga suka gaisa nan suka shiga hirar duniya,
har suka fad'o kan wata mak'waf ciyar su da za ayima
abokiyar zama cikin satinnan. Mmn Zahra tace kinji
ranar assabar za akawo ma Mum Zee abokiyar zama ko?
Take ta zabura ta gwalo ido waje tace yaushe Abban Zee
ya dai na son ta? Mmn Zahra tayi dariya sosai tace ke ko
Lateefa waya ce maki in an daina son Kane ake yima
kishiya, ai shi aure nufin Allah ne kuma matar mutum
k'abarin sa. Kuma kin ga ita Mum Zee wallahi tamkar
bata damu ba, saboda matar akwai ta da tawakkali.
Lateefa tace bata dai son mijin ta, in har tana son shi
dole zata yi kishin sa. Eh to shi kishi wani Abu ne da Allah
ke dasawa k'ark'ashin zuciyar Mace, kuma ko wace Mace
Nada kishi duniya amma na wata yafi na wata. Saboda
akwai masu kishin hauka, kuma akwai Mai na tsabta.
Lateefa tace ke nifa in zaki sauke min littafin kishiya ban
ta6a gane wannan bitar, maybe ma koda aka haifeni
6angaren d'aukar wannan bitar ya shafe duka. Mmn
Zahra tayi dariya sosai tace to Allah ya kyauta. Ta amsa
da Amin tace kin dai ji magana. Tace ya Kama ta ranar
auren mu daure mu lek'a Mata. Lateefa tace ke ni fa ko
gidan da keda Mata biyu bana shiga. Mmn Zahra tayi
murmushi tayi tace ki daure muje kinsan Mum zee
akwai k'ok'arin sada zumunci. Tace ya yi Zan duba in har
Zan iya zuwa to Zan Kira ki. *********************
Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ke ta shirye-shirye zata je suna k'auyen
su, sanadiyyar lantana k'awar ta data haihu. Murtala ya
yi Mata siyayyar kayan jarirai da sabulai yace takai ma
lantana, ya had'a Mata da kayan da zata kaima iyayen ta
ciki kuwa har da kayan abinci, hakan ma ya had'a na
iyayen shi. Amma dai ba can zaki kwana ba ko? Tace
naso kabar ni in kwana d'aya, amma tunda kace ba
sokoto zaka kwana ba nima Zan dawo yau. Yace to
shikenan in kin shirya direba zai kaiki don munyi
magana da Mum tun jiya. Tace nima mun yi magana har
ta bada sak'on da za aje dashi. Hakan ya gaggauta shirin
shi har ya fita kuma ya dawo ya gaya Mata magana cikin
kunne, tayi murmushi ta soke Kai, ya sumbaci goshin ta
ya wuce, har ya tada mota tana tsaye tana yi Mai bye-
bye. Ta juya ta shiga part d'in Mum bayan ta gaida ta
take gaya Mata ta shirya, nan tayi ma direba magana ya
fitar da mota yasa kayan ta suka d'auki hanya sai Kimba.
Gidan su Murtala ta fara sauka nan aka yita tarairayar ta,
k'annen Murtala duk sun cika d'aki ana murnar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng
tazo. Bayan ta sallame su ne tace zata lek'a sunan lantana
daga nan ta shiga gidan su, haka yaran gidan suka cika
mota sai k'ofar gidan su. Gidan su lantana ta Fara shiga
nan suka rungume juna suna murna, ta kar6i jaririya ta
ganta. Inna habiba sai murna ake yi BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng tazo, sai ga
yara sun cika gida Ana lek'en ta ana cewa eh wallahi y'ar
Baba ce. Hakan ta cika su da goma ta arzik'i sannan ta
shiga gidan su. Baban ta ta fara cin Karo dashi ta
durk'usa ta gaida shi, ya rik'o ta yace mashaAllah y'ar
Baba, kina jin dad'in ki. Tayi murmushi, ta juya ta gaida
Gwaggo. Ta amsa ba yabo ba fallasa, sai harara take
binta da ita, nan dai suka ta6a hira ta fitar musu da nasu
kayan. Baba nata godiya yana saka Mata albarka, Gwaggo
ko cewa take yi an gode. Hakan tayi sallama da kowa ta
Kama hanyar Jega saboda tana so ta yima Murtala abinci
kamin ya dawo. Tana shigowa part d'in Mum ta Fara
shiga bayan sun gaisa ta tashi tace Mum Zan shiga in
dafama Murtala abinci, munyi waya yace ya kusa
k'arasowa. Mum tace ai na ajiye maku abinci in kika
tashi ki shiga maku dashi, keda kika dawo yanzu ko
hutawa baki yi ba. Tace Mum an gode sosai, nan ta zauna
suka rik'a hirar k'auyen su BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Can taji wayar ta na
ruri cikin jaka, koda ta d'auko taga Murtala ne takai
duban ta ga Mum tayi murmushi tace inaga ya iso. Tana
d'aga wayar take gaban ta ya fad'i jin muryar wani
daban. Tace eh nan ne, kawai Mum taji ta furta
innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, take ta fad'i k'asa
sumammiya. © *SDY* *JEGAL* [10/28, 1:34 PM] +234
803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *85*- *90*🍒 Mum ta yi
saurin tasowa ta gir gizata sai dai bata numfashi, nan
Mum ta jawo wayar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta duba no taga Murtala ne
ya Kira, nan ta Kira taji ko lafiya can taji wani ya d'aga
nan ya yimata bayanin Allah ya yiwa Mai wayar rasuwa
yanzu haka suna asbitin Aleru. Innalillahi wa Inna ilaihi
raji'un, hakan Dad yaji Mum na furtawa da k'arfi. Koda
ya sauko yaga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng zube k'asa bata ko numfashi ga
Mum tsaye kanta duk ta rud'e. Nan yake tambayar meke
faruwa haka? Mum ta gaya Mai saiga Dad zube saman
kujera cikin tashin hankali da rud'u. Mum ta yi sauri ta
d'auko ruwa fridge ta zuba ma BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng nan take taja wani
dogon numfashi, Mum ta rik'a ta ta tashi sai ido take bin
ta dashi. Dad ya Kira Shureim ya gaya Mai meke faruwa,
yace yaje asibitin Aleru yazo da gawar Murtala. Kamin
kace kwabo duk inda y'an Uwa suke labari ya Kai musu.
Mutanen Kimba sun zo cikin tashin hankali, in da akazo
da gawar shi aka yimai sutura sai gidan shi na gaskiya.
Ashe lokacin da zai dawo daga sokoto har ya kawo Aleru
sai wani sa ya gitta Mai wurin ya kauce Ashe akwai tilera
bayan shi, hakan direban yayi k'ok'arin kauce mar
amma abin ya faskara saida yabi ta kan shi shida wasu
mutum biyu saman mashin inda su duka uku basuyi rai
ba. Bayan an Kai shi gidan shi na gaskiya ne aka zo
zaman makoki. Duk Wanda ya kalli BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai ta bashi
tausayi komi rashin imanin shi, dai-dai da Gwaggo yau
an d'an tausaya ma BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Saboda da ita da mutum
mutumi basu da maraba, bata yiwa kowa magana sai dai
tabi mutum da ido. Yau kwanan Murtala biyu da rasuwa
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng duk ta fita hayyacin ta, tun jiya babu mahaluk'in
da ta yiwa magana har yau, sai dai ko gaisuwa ake yi
Mata ta bi mutum da ido kawai. Abin har ya Fara bawa
mutane tsoro, har yau Dad ya shigo da Baban ta har
d'akin da take ciki. Baban ta na kallon ta shima ya rik'a
Shafar hawaye, yace y'ar Baba haka kika koma, kiyi
hakuri ki barwa Allah, Wanda ya bamu Murtala yafi mu
son shi ya kar6i abinshi. Kiyi tawakkali kinji BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, Kai
kawai ta d'aga Mai sai hawaye dake zubowa duk sun
wanke Mata fuska. Lateefa na gefen ta tana sa tissue tana
goge Mata fuska ita ma tana hawaye. Babu abin da ke
damun ta sai rashin maganar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, abinci ma ta kasa
ci sai da k'yar Lateefa ke samu tasha fresh milk. Baban ta
yace in akwai zam-zam kusa abashi. Nan Mum ta tashi ta
d'auko ta bashi ya yi addu'a yaje da kanshi kusa ga
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya bata yace tasha, nan ta kauda kanta. Ya k'ara
bata, ta kalleshi taga ya had'e ran shi, nan Lateefa ta
kar6a ta bata tasha kad'an. Ko ruwa ta sha ji take yi
tamkar zuciyar ta zata k'one. Duk Wanda yazo gaisuwa
yaga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai ya tausaya Mata yanayin da take ciki.
Lokacin sallar la'asar tayi zata tashi tayi sallah kawai
akaga ta zube, nan kuka ya koma sabo. Nan Mum ta Kira
wayar Shureim daga waje tace tayi sauri ya shigo. Hakan
aka Kama BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng aka shiga d'akin Mum da ita. Shureim
na shigowa kallo d'aya ya yi Mata ya kauda fuskar shi
saboda duk ta zabge tamkar wadda tayi sati kwance. Nan
ya fita ya siyo allura da ruwa aka yi Mata k'arin ruwa.
Lateefa ta kasa d'agawa daga wurin ta, ko sallah da k'yar
aka rarrashe ta sannan ta je tayi. Tana k'are addu'a tazo
gurin ta ta zauna, malam ma yana gefen ta yana tofa
Mata addu'a. Sai bayan isha'i sannan ta farka, tabi d'akin
da kallo, koda ta Kai duban ta gefen ta Lateefa ta gani
zaune idon ta sunyi jazir, sai Mum dake saman dadduma
tana lazimi, malam ma na gefen ta. Tamkar a T.V komi ya
dawo Mata take ta tuna meke faruwa, nan ta fashe da
kuka tana cewa Murtala haka zaka yimin, ka tafi baka
cika burin ka akaina ba. Nan Mum ta taso tana rarrashin
ta, malam yace a k'yale ta tayi kukan shima rahama ne
gare ta. Sai da taci kuka ya ishe ta sannan tayi shiru, nan
ta tashi tayi sallolin ta ta fara lazimi duk da hakan sai dai
tabi mutane da ido. Dangin mahaifiyar ta suma sunzo
gaisuwa daga raha Mata uku maza biyu. Dangin malam
ma gwaggon shi kawai ta rage Mai da yaran ta biyu suma
duk sun zo gaisuwa. Yau ne kwana uku da rasuwar
Murtala kuma yau ne za ayi addu'a kowa ya watse. Da
k'arfe biyar aka yi addu'a, nan mutuwar ta koma ma
dangin shi sabuwa su da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Kowa ya Kama gaban
shi sai dangi na kusa, irin su Hindatu k'anwar margyayi
da Lateefa, sai kuma Gwaggo da tace zata zauna sai an
kwana biyu, Gwaggo Allah yasa zaman arzik'i ne zaki yi.
( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﻟﺠﻤﻴﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﺎﺕ) © *SDY*
*JEGAL* [10/28, 1:35 PM] +234 803 325 6478: 🍒
*BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *90*- *95*🍒 Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta gama takaba.
Duk Mai imani ya gan ta zai San cewa mutuwa ta ta6a ta,
duk ta kod'e ta fita hayyacin ta. Bayan sati d'aya da gama
takaba d'in ta an raba abinda yake hakk'in ta an bata.
Malam yazo saboda zuwa da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gida, Dad na wurin
da Baban margyayi da Mum. Nan Mum tace malam
salisu ina neman alfarma da Ku bar min BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng har
salisu ina neman alfarma da Ku bar min BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng har
zuwa lokacin da Zan cika burina akan ta. Kaga yanzu ta
gama makarantar gaba da primary har anfara ciku-cikun
shigar ta health sai ga wannan rasuwar Allah ya kawo.
Nan malam yayi shiru ya kasa magana. Sai da Mum ta
sake magana sannan ya Kai duban shi zuwa gare ta. Yace
yanzu abinda nake dubi kinga can k'auye za a yita maida
magana cewa mijin ta ya rasu amma nabar ta wurin Ku
zaman kwad'ayi. Sai yanzu Baban Murtala yasa baki yace
malam salisu yanzu ba abiyar ta mutane, kuma shi d'a
na kowa ne, kaga ko bada auren margya yiba in har zaka
duba zaman takewa to zaka iya bama Alhj Suleiman
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Kuma in har Kai ga taka zuciya zaka iya bashi ita
har ta gama karatun ta to kar kabi ta surutun mutane.
Malam yace to shikenan, Allah ya saka maku da alkhairi
kuma yabar k'auna. Mum ta amsa da ameen, ta d'ora da
cewa inshaAllah duk juma'a zata sa direba yakai BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng
can gida Kimba ta zaga y'an Uwa in yaso lahadi ya koma
ya d'auko ta. Da hakan suka tashi ya samu ke6ancewa da
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ya k'ara yi Mata nasiha da kuma hak'uri da
k'addarar da ta samu bawa. Tace ba komai Baba, amma
ina jin kewar ka har cikin raina. Yace to kiyi hak'uri kinga
hajiya Safiya tace duk sati zata sa akai ki kiyi muna
kwana biyu, ke dai ki kula da karatun ki kuma ki tsare
mutuncin ki. Tace tau Baba Allah ya Kai Ku gida lafiya, ka
gaida min su Gwaggo. Bayan angama ciku-cikun shiga
makaran tar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, ta Fara karatun ta ba laifi tana
maida hankali, kuma bata cika shiga sabgar mutane ba
dama tun farko bata da tarkacen k'awaye lantana ce
kawai k'awar ta. Yanzu ma ta had'u da k'awa guda wadda
tasu tazo d'aya wato Aisha Yagani. Babu ruwan su da
shiga sabgar mutane karatun su kawai suka sakama
gaba. ****** ********* Can kuma 6angaren Shureim
yana fama da matsalar Lateefa, tana bashi kulawa ko ina
musamman wurin kwanciya, amma fa har yanzu bata
shiga kicin da sunan girki. Tun Bizzy na Jagal-gala musu
abinci har ta fara iyawa ba laifi, Mum da Mamar Lateefa
sun yita fad'a har sun gaji sun saka Mata ido. Wani lokaci
haka k'anwar ta Shema'u zata zo gidan ta yi Mata girki
Mai rai da lafiya, saboda ba kalar girkin da Shema'u bata
iya ba, don ma'abuciyar son girki ce tun tana k'arama.
Tana zaune falo tana waya da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng tana complain kan
cewa bata son tahowa gidan su. Tace kiyi Anty Lateefa
Zan zo satinnan amma fa sai na fasa zuwa Kimba kenan.
Lateefa ta ce gaskiya kam abamu wannan satin. Jin
sallamar Mmn zahra yasa ta tsinke wayar. Nan ta zauna
suka gaisa ta kar6i zahra tana Mata wasa. Maman zahra
tace ki tashi mu shiga gidan Mum zee muyi Mata Allah
sanya alkhairi tunda bamu samu zuwa auren ba
sanadiyyar rasuwar da aka yi maku. Har zata Fara
complain kuma tayi shiru ta figi gyalen ta suka wuce.
Suna shiga gidan sukayi part d'in Mum zee bayan sun
gaisa sun Mata Allah sanya alkhairi, sai suka shiga hirar
duniya duk yawancin hirar tasu akan kishiya ne. Sun
tashi zasu wuce ta raka su part d'in Amarya, nan ta
tarbesu hannu biyu suka gaisa mutunce suka tashi.
Lateefa ta kalli Mum zee tace yanzu wannan kishiya ce
kenan, kun raba miji kenan. Tayi murmushi tace ba laifi
muna zaman fahimta tsakanin mu, don tana bani girma
na. Hakan suka fito ta dubi Mmn zahra tace in banda
jarabar namiji me wannan amaryar zata nuna ma Mum
zee. Nan Mmn zahra tayi murmushi tace baki ganewa
ne. Tace banko ta6a gane wa in dai akan kishiya ne.
Hakan suka rabu kowa ya shige gidan shi. © *SDY*
*JEGAL* [10/28, 1:37 PM] +234 803 325 6478: 🍒
*BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng* *95*- *100*🍒 Lateefa ta shirya ta dawo falo
tana jiran shi, yana fitowa suka wuce, saboda zai sauke
ta gidan su Muftah shiko zai wuce wurin d'aurin aure. An
d'aura auren *MUFTAH* da matar shi *BILKISU*
*BILYAMIN* sai dai fatar zaman lafiya tsakanin su. Sai
zuwa dare da aka Kai Amarya Shureim ya rako ango
sannan ya wuce da Lateefa. Nan yake yiwa Muftah sharri
kan cewa sai sun zo barka nan da wata tara, saboda naga
zumud'in naka yayi yawa. ******** ********* Yau
tun safe Lateefa ke Kai kawo a gidan, tana ba Bizzy
umurnin abinda zata dafa. Can ta shiga d'akin Shureim
yace wai yau me ya hana ki zama haka? Tace ka manta
na gaya ma Sis zata zo muna yini yau. Yace OK shine kike
ta rawar Kai haka, ni na zata daga wata k'asa za kiyi bak'i,
saboda naga wataran baki tashi daga bacci sai k'arfe
goma, amma yau kece da tashi tun takwas. Tayi
murmushi tace Kimba wallahi Ina ji da Sis BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ne
tamkar k'anwata Shema'u, naga Kai ko tausaya Mata
baka yi. Nan yayi murmushi yace asha aiki lafiya, koda
bak'uwar taki ma sai dai taci girkin y'ar aiki ya bita da
gwalo. Gane cewa tsokana yake ji yasa ta k'yale shi ta
shiga wanka. Koda ta fito ta shirya sai ta dawo falo ta
zauna, bata fi minti goma da zama ba sai ga BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta iso
ita da k'awar ta Yagani. Hakan ta shek'o ta rungume
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sai murna take yi, tace ma Yagani bismillah zauna
mana. Hakan suka zauna tasa Bizzy ta cika masu wuri da
kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe. Suna zaune suna hira
ne sai ga Shureim ya fito cikin shiga ta alfarma, ya saka
k'ananan kaya ga sajen shi ya kwanta luf, ya had'u iya
had'uwa ga kwarjini da ya cika fuskar shi. Nan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta
durk'usa har k'asa tace yaya ina wuni. Ya amsa da k'alau
ya d'ora da cewa ya karatun, ya kuka baro Mum? Tace
k'alau Alhmdulillah. Nan ma Yagani ta gaida shi, ya amsa
yace to akula da karatun. Nan yakai duban shi ga Lateefa
yace to ni zan fita, nan ta rakashi sai da ya tada mota
sannan ta dawo. Bayan su BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng sun ci iya abin da zasu
ci, nan ta jasu har bedroom d'in ta suna ta hira, Lateefa
tace yaushe zaku gama karatun? Tace nan da shekara
guda. Jin kiran azzahar ne yasa suka tashi domin sauke
farali. Bayan sun gama sallah ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta shiga kicin ita
da Yagani ta had'a masu abincin dare, sannan suka
kimtsa zuwa tafiya gida. Lateefa tace kiyi hak'uri Kimba
ya dawo sai ya sauke Ku nima inaso in bishi in gaida
Mum. Da k'yar ta samu suka zauna, sai da Shureim ya
dawo yaci abinci yayi wanka ya canza kaya yayi shigar
manyan kaya. Nan ya kwashe su suka wuce, Yagani ya
fara saukewa Lateefa ta bata ledar kayan Shafa tayi
godiya sannan suka wuce gida. Nan suka zauna gurin
Mum suna ta hira sai daga baya suka wuce. **********
********** ```BAYAN``` ```SHEKARA```
```D'AYA``` Yau ne BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng suka gama exam d'in su ta
k'are health, daka dube su zaka San cewa suna cikin farin
ciki. Bayan fitowar su da kar6ar address d'in juna kowa
ya Kama gaban shi. Hakan kowa yaje gida cikin farin ciki
da murna. _BAYAN_ _KWANA_ _UKU_ Kamar yadda suka
yi alk'awari da Mum kan cewa in ta gama karatu yazo ya
wuce da ita. Hakan yasa yau malam ya zo domin zuwa
da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gida, koda yazo ya taradda Baban margyayi
ma yazo hakan suka zauna aka tattauna rayuwar yau da
kullum. Cikin hakan ne Dad yace malam salisu Zan k'ara
Neman wata alfarma Karo na biyu zuwa gare ka. Malam
yace haba Alhj wace irin alfarma ce wannan, na gaya ma
babu shamaki tsakanin mu. Ya yi murmushi yace d'an ka
Shureim zaka bawa BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng aure. Baban margyayi yace
Alhj ya akayi kasan abinda ke cikin zuciya ta, dama
wannan maganar ce ta kawo ni. Nan dai suka yi maganar
aka aje d'aurin aure sati guda masu zuwa. Malam yace to
zai je da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng gida sai ranar alhamis zata dawo. Hakan
suka d'ungu ma sai Kimba, saida suka sauka malam yake
gayama BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng meke faruwa. Tace Baba don Allah ka
taimakeni Ku janye wannan maganar, bazan iya auren
Yya Shureim ba, innayi hakan na yaudari Anty Lateefa.
Yace kiyi hak'uri y'ar Baba ba yin kaina bane, kuma
kinsan mutanen nan sunfi k'arfin komai a wurin mu.
Gwaggo tace kiyi hak'uri shi aure nufi ne na ubangiji,
nan suka rarrashe ta sannan ta tashi ta koma d'aki. Tana
shiga d'aki ta fasa kuka maicin rai, tace mutuwa Mai
yankan k'auna, yanzu da wane ido Zan kalli Anty Lateefa
naje Mata matsayin kishiya. Tana cikin tunanin ne taji
Gwaggo saman kan ta, tace shegiya mayya kin lashe
musu yaro ya mutu yanzu kin koma ga d'an cikin su. To
wallahi Bari in gaya maki ko Zan tafi tsira ra ba zaki aure
shi ba, makwad'aiciya Mai idon cin nera ta Kai Mata
rank'washi sannan ta fita. Bayan taje ziyara dangin innar
ta, kuma taje gidan su margyari har gidan lantana sai da
taje. Yau Mum ta turo direba ya koma da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng, sannan
tasa aka d'auko Mata Lateefa. Nan ta had'a su tana yi
masu nasiha sannan ta furta ma Lateefa abinda ke
faruwa. Dama an gaya ma Shureim ya amsa ba yabo ba
fallasa sai dai fargabar had'uwar shi da Lateefa. Lateefa
ta bi Mum da ido tace bangane ba. Mum tace saura
kwana biyu auren Shureim da BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng. Idon sun
k'ank'ance ta bud'a baki zata yi magana kome ta tuna,
sai ta zabura ta nufi hanya tamkar zararra. Mum na kiran
ta ko waiwayo ta bata yiba da saurin ta tafita daga gidan.
BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng ta rik'a kuka maicin rai tace Mum kiyi hak'uri ki
janye maganar nan, kin ga Lateefa ba zata ji dad'i ba.
Mum tace mu mukasan dalilin wannan had'in, in kema
zaki bijiremin ne kamar yada Lateefa ta yimin to
bisimillah, ta tashi ta wuce d'akin ta tabar BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng nan.
Yau ne mutane suka shaida auren _SHUREIM_
_SULEIMAN_ *DA* _BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng_ _SALISU_ A garin Kimba,
Allah ya basu zaman lafiya. (Masoyan BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng Ku fito Ku
taya ta zaman kishi da Lateefa, _lolx_) © *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:38 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJAH daga www.hausaebooks.com.ng*
*100*-

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment