Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gashin ta yasha gyara kamar tasan zaizo ga wani sirrin k'amshi da take yi
Ga skin nata yai smooth sosai, Babyn ta ya girma Hajiya cewa tai tanada gafin Nono yanda yaron yai girma sosai kamar anyi 3 months
Sun zaga dangi na kusa har katsina sunje Maiduguri, koina sunje kowa kuma yai murna
Tukwicin Hajiya na gyaramasa mata da tayi kujeran Makka yabata tayi murna duk da tana zuwa amma irin wannan kyauta ta bazata akwai dad'i
Kilishi ma ganin tana so haka ta siya mata sosai, tai farin ciki k'annenta dasu sukaje Libiya tunda sun jima basu jeba
Fadeela tayi murna, sun zaga dangin Maman ta, har gidan Abokin Abban ta da silarsa Abban ta ya had'u da Maman ta taje yai murna shima
Daga nan basu dawo 9ja ba NIGER suka tsaya, lokacin da jirgi ya sauke su tagane wajan
Kallon sa tai, kai ya kad'a mata duk jama'ar wajan Bata lura da kowa ba, rungumeshi tai tana hawaye tace Abban Sultan Nagode sosai Allah ya kiyaye mun kai Allah kuma yabaka abinda kake so duniya da lahira Allah yabamu zuri'a ta gari Allah yabamu tsawan rai mai amfani
Tana k'irjinsa take wannan addu'a, kanta ya Shafa yace Ameen mata ta gari, komai kike so zan miki Iya aljihuna da k'arfina, kina kiyaye komai nawa nimaizaisa bazan yi abinda ranki zaiyi dad'i ba
Hannun Abdallah ya kama yace tawo ga motar ma tazo, abokinsa ya zo ya d'auke shi, gidan Adda Bena taga yayi, nan ma kallonsa tai, of course ina zuwa fa, har Abban Ku ma yazo
Gidan suka shiga angyara kamar ba shiba, k'awayenta ta gani ciki harda Ummul fadeela da Hauwa Jabo data taimaki Aunty Meimi lokacin Haihuwa
Kuka suka saka antuno da, baran da sukaji tana magana nan wata sabuwar murna aka saki
K'awarta Rash tai aure itama tazo wasu kuma basa garin, Lallai mijinta abin alfaharin ta ne, kud'i yaraba musu
Abdallah kowa ya ganshi yaga Abban sa, sun jinjinawa kirki irin na FUTHA da sukaji yana hannun ta, Adda tai kukan rashin aminiyar kwarai dalilin ta, ta sauya hali take kula da mijin ta, ta ajiye sana'a gefe takula da gidan ta dole tayi kuka
Mak'ota sunzo wasu kuma ta shiga, anmusu abin arzik'i abinci ko ina kawo musu ake
Gidan da suka zauna ta shiga tun a soro tasan cewa tafiya tai tafiya, tunda gashi ancanja tsarin komai na gidan
Ikon Allah wannan mutumin ta gani ya ganeta itama, wanda tacinyewa abinci a kasuwar duffa dariya yai yace Ashe baki mutu ba, akace kin mutu Abban ki yazo nan yabata labarin yadda akai
Matarsa mai kirki, shima kud'i tabashi yai godiya sosai
[10/11 10:23 am] @ut@r h@jiy@βœπŸ»πŸ’…πŸ»: A washe gari suka tarkata suka koma k'asar su ta gado wato NIGERIAπŸ‡³πŸ‡¬, Lagos suka sauka gidan su, shima an k'ara gyara shi yai kyau ancanja abubuwa na gidan sosai
Rayuwa wad'an nan ma'auratan sukeshimfid'a wa mai tsafta tafi da ilimin boko dana addini ga Abdallah da sukai masa rik'o na gaskiya da amana yaron kuma ayanzu yak'ara hankali

*5 Years ago*

Gidan na koma naga meke faruwa bayan dogon lokacin dana d'auka ban waiwayi gidan ba
Gidan yana nan yadda nasan shi before, sai gyara da k'awatashi danaga anyi ga wasu flowers da aka k'ara ga kayan wasa daga gefe da lilo dana gani ga paint da aka canja
Badan nasan gidan ba, a yankin Ikeja yake, kuma tsarin gidan shine danace bashi neba saboda gyara daya sha
Parlour nayi, kai ! Yara nagani wajan su hud'u kuma dukkansu kama suke da Abban su Illa mace kwaya d'aya da tayi kama da FUTHA kusan kansu d'aya yaran macen itace dai k'arama Lallai Allah da iko yake
Da fari ya hanaka amma Idan yafara baka, har saika k'osa
Kowanne cikin yaran strow ne a hannun su Almara'i suke sha. Babban shekaran sa 5, sai yan biyun kuma 3 sai k'aramar su batafi one year ba
Ita tana kan Carpet a zaune fuskanta duk madara ta b'ata tak'i kuma a tab'a fuskar mai aikin gidan da yayunta daga sun daukai tissue zata saka kuka shiyasa suka kyaleta
Alamar tafiya naji, FUTUHATUL KHAIR ce tareda mijinta cikin shiga ta alfarma shi kakin sane ajikin sa itakuma Pakistan ne red yamata kyau kamar ajikin ta aka d'inka tana nan yadda take saima kyau data qara yi
Daddy kadawo shine baka tashemu ba, munata jiran ka har mukayi bacci
Sultan ne yake magana, kansa yashafa yace I'm sorry Boy mun tsaya a border ne, daga airport naso nazarto gida kodan saboda Ku amma bansamu sarari ba
Kayi hak'uri kaji, tom Sady, d'aya Bayan d'aya yabi yashafa kansu, twince sunan su Hakeem da Haleem yara kyawawa gashin Maman su suka d'akko
Wajan Babyn yayi ya dagata sama yace yarinyar Momi bakiyi missing Dady ba, ko kallon sa bakiyi ba
[10/11 11:17 am] @ut@r h@jiy@βœπŸ»πŸ’…πŸ»: Yana kallon fuskanta da sauri ya mik'awa Momin ta Ita, yace wannan yarinyar sai ke, kalli fuskan ta hala kema haka kikayi kina yarinya?
Haba dai saidai kai, nima narasa ina ta koyi haka, badamar ace za'a gyara yanxu kaji kuka kamar zata tsaga gidan
Dariya yayi yace, gata da k'iwa kuma koni bata yadda dani, Huum kowa ma haka take masa baran Aheed k'anin ta kenan, tace kaga Idan yazo gidan nan kamar taga dodo
Bata yadda dashi shiyasa shima baya kulata, ga wani hali data koya daga tafara shan nono idantacika bakin ta dashi saita bullutso dashi
Yan yan yan yan, lallai *ZAHRAN MOMI* kazama ce ke yana magana yana tab'a kuma tun ta dariya tafara masa
Kan cinyanta tasakata tafara feeding nata, tafara sha kenan ta tajiyo sallaman Abdallah ai da sauri ta CIKA tafara kiciniyar kwacewa ta sakko wajan sa
Shima ganin haka da saurinsa ya tawo, yace *My ZAHRA* oyoyo, wangale baki tafara,
Huum kaga wanda kawai batawa k'iwa amma kowa saita gwada masa Farouq ne yayi maganar
Dariya Abdallah yasaki yace Abba ina kaga mata nawa miji k'iwa sai dai Idan baso ko Matas?, kamar taji mai yace tasaki dariya
Lallai amma ka d'auko mata da k'azanta, eh Abba inaso a haka wataran sai labari.Sai anzo ana layi, badan nace ina so ba da daga kan president governor sai sunzo
Dariya Abba yayi yace lallai zanso nayi tsahon rai dan zanga wannan lokaci
Abdallah kenan yaro mai hankali da sanin yakamata yanzu haka yanada shekara 15 yayi girma yana SS3 a school
FUTHA dai murmushi take tana godewa Allah daya bata miji da dangin miji masu sonta da son komai nata
Rayuwa tamata dad'i batada matsala karatunta ta k'are cikin sa'a mijinta na kyautatamata yanamata abinda take so Sai in batace tana so ba
Abdallah d'aukan *ZAHRA* yai suka fita, bayan ya goge mata fuska, su kuma yaran d'akin su sukayi
Ganin haka shima Farouq yace office yasha ruwa yau, gara aje ayi aikin lada asamawa *ZAHRA* k"anwa ko kani
Dariya sosai tayi, haka ta mik'e tana rangaji akayi *MASTER BEDROOM*nima danaga haka k'afafuwana naja a hankali na fice ina kwad'ayin nima Allah yaban Family fin haka ma

*Ina Godiya ga Allah mai kowa mai komai daya bani ikon kammala wannan littafi ina rok'on Allah yasa abinda akaji na amfani ayi AIKI dashi, Wanda akasin Hakane a zubar da shi*

*Ina Godiya ga writers 'yan uwana da kuke bawa kowa k'arfin gwiwa wajan kanbaba rubutun sa, jini ne ko Na jikin Auta, Auta tana sonku harba adadi*

*Aunty Sady Jegal, My STYLICH, Didi Aneesa Nafeesat Anker, Princess Hassy, Zahar Bukar, Queen Meemi Jameela Mohd Ali kuna zuciyar Auta ko da yaushe*

*Jabo jabonation Hauwa ta, kina zuciyata Aunty Bilkisu, Faty Axland, STYLICH Anker, Anee Sahaf dukkan Ku kuna raina*
*Wanda ban fad'a ba, kuma kuma raina Allah yasani*
*Jinjinar ban girma Aunty Mamu, tabarya mai baki biyu*
*Yar uwata Rabin raina Yayata Maryam Mohd kina raina, koda yaushe burin ki, ki farantan Nagode miki sosai, Maryam d'in Umma Halima ta ina nan zuwa wajan ki*

*@ut@ ce, ta Hajiyan ta Yar albarkar Baban ta*


*Ku saurareni cikin wani sabon littafina mai zuwa nan gaba mai taken SO BABBAR CUTA*






DOCUMENT


MADE


BY



SALMA SWEET NOVELS GROUP ADMIN.



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment