Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lura magana yake son janta da ita, inason matata amma ita tana k'ina haka dama rayuwa take
Dariya ce ta kamata jin wai waqa yake a haka, Lallai one love bata kyauta ba ana sonta tana k'in mutum kai gaskiya tayi rashin kirki
Haka sukaita zolayar junan su aure da dad'i
Sai wajan yamma akazo mata sallama danginta dasu fido Sodangi, ansha kuka Abdallah dai yak'i binsu har kusan suma yayi akan anshigar dashi motor, bashiri suka direshi anan suka musu fatan alkhairi Sodangi tace Yaro wato Auntyn ka kasani zamu rama ne
Fadeela sun shigo bayan tafiyar su, girki sukai anayi ana shak'iyanci suna yasukaga bata tafiyar tata ta ko suga alamun tasha kuka, kodai ba'ayi abin ba
Uwaku mai za'ayi kinga Fadeela dama haka kike, tashi bazaku lalatamun mata ba
Ku fice, sunabm dariya kowacce cikin kunya yakamasu suna irin nan zancen suka fita, Abdallah binsu yai yasaba da Fadeela dama
Huum kinji yaran nan koh, Allah ya kyauta
Zaman su zamane na gaskiya da amana da mutun ta juna, sun sake da juna shi kuma ya baje yana kwasar gara ta abinci da abin sha
Yau watan su guda kenan ya barta ta sake dashi amma bawai dan wani abu ba, kuma gashi hutunsa ya kusan k'arewa shiyasa yau za'ayi final ba semi final ba
Da confidence nasa yashiga gida, tarbonsa tai kamar yadda take yi, d'aga ta sama yai yace yarinya taqi tayi k'iba kodan ban bata white milk ba, amma I'm sorry yau zaki santa
Huum Baby mene kuma naji ka fad'a yanzu?, Huum zaki sanine yanzu dai wanka abinci shine gaba nayi sallolina
Saving nashi tai, tare suka ci coconut rice ce sai stew, sai lemon pineapple datayi masa
Kai abincin yau yayi dad'i, kamar kada na k'oshi tanajin dad'i Idan yana yaba abincin ta, wataran shima yanayine saboda yana ganin murmushi akan fuskanta burinsa yasaka ta farin ciki
Wanka ya shiga, abinci yafara ci, kodaya fito k'in kallo yabari ayi, yace ta tawo tamasa massages ya gaji
Bata kawo komai ba, tace 5 minutes narage kayan Jikina, haka tafara masa yana lumshe ido yana bud'ewa tana masa hira mai dad'i
Daga massages kuma naga abin yana neman wuce gona iri ba shiri na tarkata kayana da wayata da charger ta nayi gaba

@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: *FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*page 146-150*

Sad'af nayi gaba abina nahau online naga me NWA gidan hira suke nasan ana can ana shafta ina shiga kuwa da Idon Jabo nafara tozali ta bazo shi Aunty Sady kuma ta watsamata barkono dariya aka saka
Anan na shan take daga nan bacci yafara d'iba na ana nayi a parlour amma wani ikon Allah komai cikin gentle banji kwarototo ba ko wani hatsaniya ko kuka
Sai da akayi assalatu na koma nasan dai komai ake angama baza'ayi second round ba
Leqawa nayi lah ikon Allah bacci naga sunayi, itada shi amma bedsheet d'in bana farko bane, har blanket d'in ma saukar numfashi naji a hankali waih ai ina lek'a Idon FUTHA naga ya kumbura daga gani ansha kuka anyi gwagwarmaya afilin daga, gentle ta wasa jini
Bacci dai take suna k'ank'ame da juna, kamar za'a kwaceta a wajan sa
So mai dad'i da tsafta shine yake wakana awanan gida kowa yazo sai sun bashi sha'awa tana girma mashi tana bashi kulawa tana kula da cikin sa da gado kuma
Lallai kayi dace da mace ko miji nagari shine ka more kuma kasan ribar aure
House gal da aka bata, aikinta shara wanke wanke mopping amma ko kwanon da maigidan zaici abinci Bata bari ta tab'a, abinci kullum Idan tayi saita kaiwa Mama wataran gidan su ma tana kaiwa
Iyayen suna alfahari da ita
Fadeela itama ansaka rana, Mama bata tab'a zuwa ba saiyau datazo itada Maman FUTHA
Murna inataka saka ina taka ajiye wa, komai d'akko musu tayi wani abin dariya a freeing tattasaine adafe shima d'akko wa tai sudai murmushi suke ganin yadda 'yarsu tayi kyau
Lokacin daya dawo shima yai murna, tareda Abdallah sukazo FUTHA taso ya zauna amma yak'i shidai Maman Fadeela itace tasa yanzu itama Fadeelan yamata yaji
Iyayen ta maza suma sunzo qawayenta kowa sai tabashi sha'awa
Mijinta yana kula da ita, tare suke aikin gida, ayi ball tare ayi wanka komai tare
Idan akazo 'yar Lido Idan taci kansa take fad'awa tana looser looser daga wannan wasan kuma zai birkitota tashiga faranta ran juna
FUTHA na k'ok'arin akan mijin ta, tana kyauta tamasa sosai
*Bayan 5 months*

Sun koma Lagos dan har addmition ya nemamata LASU, tana karantar Micro biology, tana qoqari akan karatun ta, chat da wani abu duk ta ajiyeshi gefe, burinta kawai tayiwa mijinta abinda zaiyi alfahari da ita
Sai karatun ta data saka a gaba
Farkon dawowar su ta hadu da Mama Nafee a Lagos ba k'aramar murna sukai ba, anan tagayamata tadawo nan da saida abinci tabaro garin su
Kud'i suka bata mai yawa, Abban ta dayaji labari gida ya siyamata maikyau yasa aka kafamata runfa anan take sana'arta
Lallai taimako yajamata riba babba, itama tanawa FUTHA abin k'aruwa irin na garin su, kuma tana kula da ita sosai
Su Musa yaran Mama Nafee da suka taimakawa FUTHA suma sun dawo Lagos
Mijinta yana k'aunar ta super market ya bud'e masu anan cikin Agege
FUTHA Allah baibata ciki ba, har yanzu basu damu ba ada ya fara tunanin ko karatun datake ne yasaka ta yin wani abu, amma daga baya yagane Allah ne bai kawo ba
To Sai muyi fatan Allah ya kawo nagari ba saurin haihuwar ba

@ut@r h@jiy@💅🏻✍
[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: *FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to My Besty Nafeesat Anker Allah yaqara lafiya. Ameen*

*Page 151-155*

Lokaci yana tafiya rayuwa na juyawa komai na Allah yanada iyakarsa, gashi yanzu lokacin bikin Fadeela ne yazo shiri suke zasu koma Sokoto Allah ya taimaketa sun sami hutu a lokacin
Tun safe take yin shirin ta na tafiya tana jiran sa amma shiru, Har wajan 4 pm bai dawo ba sai yanzu dataji k'aran bud'e gate
Assalamu alaikum One love amun afuwa aiki yamun yawa sosai, amma gashi na dawo
Yana magana yana shigowa, tana kan kujera ko kallon sa batayi ba, ta gane sa bayason fita ko'ina shiyasa daga school sai wajan Saloon ko k'unshi bata zuwa saidai mai k'unshin tazo
Wata k'awarta tayimata hanyar Mai kitso da k'unshi Asy Khaleel tana Lagos
Haba yammata keda Idan mukaje two weeks zamuyi natsaya shirya komai fah shiyasa
Ai haka zakace indai fitace yanzu zaka fara cewa wani abu, tana magana bakinta yana turo wa, OK naji amin afuwa ko nasami relief
Dariya tai ganin yana neman kamata tasan kwanan zancen kafin me daga ita harshi sun shan take daga nan kuma sai Oga Master room
Tafiya tasha ruwa dan koda suka kamalla abubuwan su, suna mak'ale da juna bayan sun fito daga wanka
Hira suke akan karatun ta, yanamata tambaya tana bashi answer akan cikin sa take tana d'an wasa da sajen sa
One love yes One love yah?, nace maizahana muje Asibiti kaga har yanzu shiru wajan one year da rabi da auren mu, kaga kuma wasu 9 month ma sun haihu Plx I beg muje ko wata matsalan ne
Birkitito yai, k'ara matseta yai ajikin sa, yace FUTHA Allah shine yakeda ikon komai, kuma Idan yaso ayanzu ma yabamu nasaka kwaina ajikin ki, Idan kuma baiyi nufin haka ba wallahi ko zamuje ko'ina akan Haihuwa Bazamu samu ba, aibamuyi jimawar dazamu fara zarya wajan likita ba
Kuma Idan kinyi tunani Maman ku tayi wajan 3 years kafin ta haifeki, batak'ara Haihuwa ba saibayan 9 years lokacin da kika b'ata
Maman mu saidata jima kafin nima ta haifan data haifan Sai Fadeela daga kanta bata k'ara ba
Kinga kuma yanzu sai labari tunda gashi sun haihun mune yaran na su, so Kada ki k'arasa maganar zuwa wajan Doctor kinji?
Insha Allah haka suka manta zancen suka shiga sabgar su
Washe gari flight suka bi sai Sokoto garin ziyara
Gidan su suka sauka saida suka huta ma sannan suka shiga gidan, waih ina zansakaki Mama nan tai tayi dasu, dangin ta sunzo kowa sai yabon alkhirin FUTHA yake dayake wasu sunje wasu kuma Idan sukazo suna zuwar musu
Da daddare gidan su taje, k'annen ta kamar sa cinye ta saboda murnasu, Abban ta yaji dadin ganin ta cikin kwanciyar hankali batada damuwa
Maman ta ma haka, sai wajan 12 yazo suka tafi, Biki anyi shi cikin kwanciyar hankali da lumana amarya tayi kyau anyi dinner kala kala Ango yasha kyau
Libiya aka kaita inda Ahmad yake tunda acan komai nasa yake, cousin d'in FUTHA ne, so ita ta lulaqa dangin Mama aka kaita
Mutane masu karamci da sanin Yakama ta, da mutunta juna, Fadeela ansha kuka dama akace aure yak'in Mata mai d'auke mace daga cikin gidan su, unguwar su area tasu, garin su watama k'asar su kacokan Allah kaimana mai kyau
One weeks sukayi a Libiya aka juyo, akabar kowa da halinsa Fadeela dai kowa yasan tanada kirki, su Sodangi duk sunzo zumunci sosai suke Abdallah dai ikon Allah Fadeela itama yak'i ta dole dai FUTHA itace ta d'auke shi
Mijin ta yanason Abdallah sosai, baran yaran mai hankali ne, haka suka tarkato suka dawo gida.
Sati d'aya suka k'ara suka koma gida, Maman Fadeela kullum addu'a tata Allah yabawa FUTHA ciki mai albarka itama Maman ta haka
Hajiya kakar ta itama burinta haka, baran Abban ta shi har sawa yayi ataimaka da addu'a Allah dai ba'aimasa tilas sai ran da yaso

*3 years Later*

FUTHA ta k'are karatun ta cikin nasara da sa'a service ma take yi, Allah ya taimaketa a kusa take yi wata ma'aikata ce
Amma duk da haka ma bata zuwa sosai, Farouq yak'ara samun matsayi awajen aikin sa rayuwa tayi musu dad'i
Yazama chief na custom duka, gida aka bashi ga securities da aka bashi motoci ma wajan 3 aka bashi, gidane babba part wajan 3 ne agidan
Anyi walima tagani ta fad'a, FUTHA tak'ara girma tayi kyau rayuwarta ta inganta
Abdallah yazama saurayi, yanzu haka ma yana dangin Abban sa ta kaishi yagan su
Fadeela ta haihu ansamu mace FUTUHATUL KHAIR aka saka mata yarinya tayi goshi ta d'auko farin jinin mai sunan ta
Yau dukkan su suna Sokoto ana taron family, ita tarigashi zuwa shi sai aranar yazo tunda komai ya canja yanzu
Tun tawowarta takejin ba dad'i amma haka ta daure, ga kasala da bacci datake Ji tun suna gida wataran kafin ya dawo ma tayi bacci
Ko hira ake kan kace me bacci ya tafi da ita, shiyasa yake cemata lazy yanzu tayi wajan 2 months ahaka amma kwanan nan tafijin kasala
Maman sa ta lura da ita da yanayin ta, hakan yasa tace bara dai agama taron suje Asibiti ko zaton ta ne yake son tabbata
Lokacin dayazo bacci take, shiyasa basu had'u ba, sai a wajan taron
Jinjina ta kaimasa tana murmushi, shima haka tunda wajan maza daban, sosai taron ya k'ayatar aka d'anyi abubuwa da dama aka k'ara sanin wasu dangin na Abban su Farouq
Anci an sha anyi pictures sosai anyi musayar number ta waya, amma fa FUTHA ita bazata ce ga abinda akayi ba, dan rabi baccin ta tasha har taro ya watse
Basu zarce gida ba, saida Mama tace aje Asibiti aga maiyake damunta, badan taso ba akaje tunda ita bacci yaci k'arfin ta
Alhamdulillah Allah maibawa mutum abinda yake so lokacin da baiyi tsammani ba, gwajin farko saiga ciki wata uku wayyo murna farin ciki
Ko kafin su koma gida labari ya bazu, Abbanta murna zaiyi jika k'annenta ma haka
Badan Mama taso ba tabashi matar sa suka koma amma saidayasha kashedi akan ya kula da ita
Komai take so yamata, akan lokaci shidai to yake cewa shida yafi kowa murna akan cikin amma shi akewa takara
Haka suka koma, suna rainon cikin su babu laulayi sai bacci, shima ya ragu yanzu, Mama Nafee itace kullum take kamata abinci saboda nata take so
Tafi tafi cikinta sai girma yake, duk bayan one to two weeks ake zuwa Asibiti, kuma Mama na waya akan lokaci taji ya jikin nata
Cikinta ya shiga watan haihuwa, shiyasa Mama da kanta tazo ta d'auketa kada ta haihu ita d'aya
Shima haka yaso, saboda aikin sa, gida kuma duk da da mutane amma dai gara tana kusa da gida
Kayan baby kamar Hauka aka siyo, komai dai sai san barka, ba k'arya akwatu set akayi ma baby kafin ma yazo ko tazo duniya

@ut@r h@jiy@

Loading Second to d last episode.........
[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [10/11 7:58 am] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*page 156-160*

Alhamdulillah kulawa dai dai gwargwado tana samu wajan Mama Bata barinta ita d'aya koina ta zauna Mama na wajan
Daga Asibiti kullum Sai an turo wata nurse ta kara duba lafiyar ta
Zaman gidan yamata dad'i, batada matsala Abdallah ya dawo fitina salamu alaikum, Mama tare suke kwana saboda Abba yaje umrah shiyasa Tare a gado d'aya suke bajewa
Daga gidan su kullum sai an kamata abinci, k'annenta kowa rige rigen zuwa dubata yake
Farouq yanamata waya akai akai, kullum burinsa Allah ya sauki Matarsa lafiya
4:30 dai dai na asubah FUTHA ce zaune kan dadduma bayan ta idar da nafeelfun ta carbi take ja, har akayi Assalatu tana kan dadduma Mama itama ta tashi lokacin
Tashin da zatayi danyin raka'atul fijr, habawa gaba d'aya mararta ta rik'e takasa katab'us haka Mama ta fito ta tarar da ita
Yan aikin gidan ta kirawo bayan taiwa driver waya kan ya fito da motor
Allah sarki har suka isa asibitin tanata mirk'ususu, sai yada kai take, tana yarfe hannu hawaye wani yanabin wani
A haka suka k'arasa da gudu aka d'auketa sai labour room, Haihuwa ce amma kuma lokacin baiyi ba, gashi wahala take Idan tayi nan saitayi nan
Har 7:00 ana abu d'aya ita takasa gayawa kowa ma, addu'a takemata sosai itama FUTUHATUL KHAIR bakinta salati da hailala yake yi ba wannan ihun da kwakwazo irin na sauran Mata
Shikuma acan kaida 8 yake mata waya, ya buga shiru har ba adadi jikinsa yabashi wani iri tun asubah daya farka
Jin ba'ayi picking ba gata Mama ya buga hakan yasa bashiri yaje office yai signing wasu takarddu yabiyo flight
10 dai dai awanann lokacin ta wahala ta jigata ita kuma Haihuwa tazo, gashi bata da wani k'arfin Iya komai
Allah cikin ikon sa kafin ma afaramata wasu abubuwan faya ta fashe cikin mintina k'alilan ta haifo Babyn ta Namiji k'ato tareda mabiyya suka fad'o
Adaidai nan ya shigo asibitin shima bayan bayanin daya amsa wajan yaran gidan su lokacin daya je
Yaro tabarkalllah an gyarashi an shafeshi da zaitun angoge sai bayan 4 hours kuma ayi wanka
Reception ya shiga nan yaga Mama a zaune da sauri ya k'arasa Mama yayah?
Bayani tamasa kafin yace komai, ankawo baby cikin farin shawl yaci fararen kayan sanyi ga gashin sa a kwance duk ya cika fuskar sa
K'aidar asibitin sune zasuyi maka komai, har maijegon su zasu bata kaya da pad bill shine dai zaiyi aiki
Masha Allah abinda yafito abakin su lokacin da suka amshi babyn, yana hannun su duka yaro k'ato dashi
Waya suka bugawa gidan su FUTHA, kafin wani lokacin sun cika asibitin yan uwansu duk sunzo
Hajiyan su itama saigata dayake anmata waya
Maman FUTHA tazo da tayi kamar bazata ba saboda kunya, tunani tai abin aina farin ciki ne, kuma futha dai ba ita tayi rainon taba bare ace da kunya mayafi ta yafa, shine fa ta tawo
Yan Asibiti da staffs kowa ma yasha kyauta kud'i kujeran Makkah haka sukabada biyar da wadda taka musu baby da wadda ta amsheta lokacin da aka kata, da wadda tayi jigila da ita tana lobour room haka yabisu da kujeran Makka
Basu suka baro asibitin ba sai wajan 2:00 ta farka taga dangi da yawa ga baby, bata karb'eshi ba ganin da mutane
Tarkatawa sukai akayi gidan Mama anan za'ayi jegon tunda anan aka fara rainon cikin Har kawo Haihuwar sa
Abdallah anyi k'ani yana kusa dashi kamr ya cinye saboda murna
Maman FUTHA daga Asibiti ta zarce gidan ta
Hajiya ce ta biyo su itace zatayi wanka tunda anzama d'aya Mama ta d'auki Hajiya kamar uwar mijinta
Angon k'arni dai yakasa fita daga ya ajiye baby zaizo yak'ara d'auka, abin dariya ma
Ruwa aka d'ora bayan ansiyo kayan cikin garwa, yana zafi baby aka fara yiwa kafin Uwar
Anyi daru wajan wanka dan ita kuka tasaka lokacin da Hajiya tace tashiga ruwa, gani tayi kamar ma tafasa yake cikin sa, ba yadda ta iya tanaji tana gani ta dannata da k'arfi
Da zafi amma ana yan mintuna saitaji dad'i harwani lumshe ido takeyi, bacci yana so yatafi da ita
Kya taso ai da kuka kika saka, yanzu kinfara jin gatan da ake miki shine zakiyi bacci, huum wani gata kindai azabtar dani wallahi gara Haihuwa da wankan Indai hakane, ni ko ihu banyi ba amma wannan ruwan kina zuban shi ihu nasaka
Kyaji dashi haka suke fito ana fad'a dariya yan d'akin suka ringa yi
Fadeela ana mata waya, dama ita a ready take, tunda taji ta koma gida, murna tai tace a turo mata photon babyn kafin suzo dan yau ko gobe zasu ganta
Kafin dare kowa yaji Haihuwar k'awayen ta wasu sunzo ma, na Lagos duk sunji
Kowa murna yake mata, mijinta dai bak'i sun hanashi sakat, daga ya shiga mutane zasu fara sallama
Shi yana so suyi magana me take so, dan da safe yake son komawa
Dole sai hak'uri yai da asubah ya shiga, nan Mama tace yabari Fadeela dasu Basmah suzo ayimasa waya Idan suka lissafa
Ok Mama nabar ayyuka, zan koma sallama yai musu Ji yake kamar ya tafi da Babyn tare da uwar y had'a yaringa d'aukan pics harsaida mama tace ya isa
Nan ma saidayace kullum aringa d'aukan pics na Babyn aturo masa
Tom za'a turo, ba kunya ita Uwar ma hartafika jin nauyin mutane, amma agabana kake wannan maganar
Kansa ya shafa yana murmushi yayi wa FUTHA peck a kumatu yai saurin fita yabarta dajin kunyay
Dariya Hajiya tai tace ga k'arshen kunya ya nuna
Kaya nagani na fad'a kakannin yaro suka masa, da suka dawo daga Saudi, kowa kuma burinsa yai musu abin bajinta jikokin su na farko kaya har kusan rasa inda zata saka tai
Fadeela dasu Sodangi Basmah Sahaf Stylich Munay Mrs Omar Aunty Nafee Aunty Jidda dukkansu sunzo yanzu sunzama kamar yan cikin gida
Tare dasu akayi lissafin komai da abubuwan rabo duka dasu akayi
A account d'in Stylich aka saka kud'in ma, kayan flour dasu lemo Abban FUTHA yace suje Hotel Su karb'a yayi magana
Yaro yazo da goshi, Kayan snacks duk Abban tane ya d'auki nauyin da lemo da ruwa
A gida suka ce za'ayi ba wata fita da za'ai, komai cikin tsari akeyin sa da gwanan cewa
Gobe ne suna, gida yacika ya tunbatsa da mutane yammatan dasu Fadeela gidan FUTHA suka Shiga itama anan ta zauna aka mata k'unshi ja da bak'i
Anan kuma suka ajiye komai da komai nasu, Har kayan sawar su danata
Abdallah yaga yan uwa cikin su yashiga tunda yasan wasu
Ango tun asubah yabiyo jirgi yazo, yace dashi za'ayi sunan
Yaro yaci sunan Muhammad Ahmad, za ana cemasa Sultan haka suka tsara
Taron suna anfara cikin nasara ba kace nace ba hayaniya abinci ne kowa yaci yakuma ya tafi da shi anyi hotuna na tarihi kowa kagani cikin annashuwa yake
Dangin Maman FUTHA gidan ta suka sauka, wasu kuma suna gidan su, Babyn aka kai musu ya jima itama daga k'arshe Farouq d'aukan ta yai yace taje ayi photo da ita tunda danginta suna can
Taji dad'i sosai, suna ya qayatu FUTHA tasha kayan barka sosai writers da basa bada komai sai dai aci a tashi wannan karan sun bada dan ya Hajja turmin Super ta bada Nafee Anker kuma set na overall guda biyu, Queen Meemi ita 5000k ta bada sunyi k'ok'ari sosai dai wannan karan
FUTHA tayi kyau, tasaka kaya masu kyau, daga super sai Swiss sai Sanata da Sharaton tayi kyau sosai
Fadeela matayi kyau, Abdallah shima kaya wajan set goma akayi masa banda wanda Fadeela ta kamasa tunda d'an gidan tane kai kowa a wajan ya fidda tsantsan kyau nasa
Taro ya tashi lafiya sai fatan Allah ya maida kowa gida lafiya
Wanka itada Babyn aka musu, shitafi bukata a yanzu dan ta gaji sosai
Kowa ma baccin sa yai da wuri, Sultan bashida rigima yanada hak'uri baya mata kuka duk jagwalgwalon daya sha na d'auka
Abban CHUCHU ya saitu ya dawo hanya, shima 50k da kayan baby haka ya Ka musu, wasu daga cikin yan gidan sunzo ba a nuna musu komai ba tunda duniya ta koya musu
Kowa dai yazo lafiya ya koma gida lafiya, kama daga na wasu garin Har na wata k'asar daban anbar Maijego da babyn ta da Hajiya mai wanka lafiya
Oga aiki ya tsare shi, sai dai waya, wajan two weeks kenan rabon ta dashi
FUTHA tayi kyau tayiwa k'iba mai ban sha'awa Hajiya Mama Maman ta dukkansu k'ok'arin su su gyara yar su.

*Remain Last page*

@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [10/11 9:39 am] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻:


*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*_THE END, K'ARSHE_*

FUTHA tasha gyara, dan wataran Hajiya Idan tabata wani abu kotace tayi tsuguno dashi zata fara kai wallahi nagaji da wannan kayan haka kawai aringa sawa cikin mutum na ciwo da wannan kayan
Lallai yarinya ai gatan kenan, Idan ba haka ba wazai kalle ki duk d'okinsa akan ki wallahi saiya dena, Sai maigidan tsalle, karya gado duk zan had'a miki
Dariya Mama tai tace wannan drama haka, to ke FUTHA kiyi hak'uri Hajiya gyara take wataran da kanki zaki nemeta ta baki
Kai ta sunkuyar tana d'an murmushi, tana wasa da hannun Sultan dayake shan Mamma
Wannan Satin FUTHA sukayi arba'in, shima asatin yazo, rud'ewa yai ganin yadda One love tai kyau ta fita sosai tayi fresh sai kace milk ko kazar turawa
Ai baiji kunya ba, ko da yake Hajiya tana wajan Mama, laluba matar sa yai, sosai hakan yasashi nishad'i, dan ji yayi kamar sun shekara rabon da jikin su ya had'u waje guda
Kallon ta yake yana yaba kyan da tayi ga

Please Login or Register in order to submit comment