Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya tayi, tace a'a da inda baku duba ba, tunda dakunje inda muke zaku ganmu

D'akin suka shiga, nan ta bada hak'uri, akan kad'eta da sukayi, sannan tafito da kud'i ten thousand tabayar, tareda maganin ta, sosai sukai godiya sannan ta fito


Itafa Hajiya tashiga nazari, da alama matar ta kirki ce, dan babu alamun rashin kamun kai tare dasu

Kuma hak'ik'anin gaskiya FUTHA dataji suna fad'a ba yarta bace
[29/09 8:38 am] @ut@r h@jj@ju✍🏻💅🏻🌹: To idan hakane, a ina ta sameta?, kuma ya akai suke zaune cikin kasuwa?, dan daga gani yarinyar jinin larabawa ce, ko dai wata qasar

Ita kamar gani take tasan fuskar, amma a ina, abinda tun a asibiti takasa tunawa kenan

Batada mai bata amsar wannan tambayoyin, haka harsuka k'arasa gida


Fadeela tagani, kan kujera budurwar 'yarta, hartayi bacci, sosai tasan tayi missing ganinta, tunda daga, Kaduna ta dawo, shiyasa take cewa Malam Idi yad'an k'ara gudu, akan kada suzo basu sameta ba

Tashinta tayi, tace Fadeela tashi, mun dawo, nasan kingaji da jiran mu?
Mik'ewa tayi, tace wallahi Mama harnagaji da kiran wayar ki, fatana dai dakika dawo lafiya

Amma meyafaru, zama tayi tace kedai bari, garin saurin mu dawo, akan hanya muka bige wata budurwa, amma bataji ciwo sosai ba, munkaita gidan su ma

Sosai yabawa fadeela labarin, yanda taga inda suke zaune, hartace wallahi da ace, matar zata bata ita, babu abunda zaisa bazata ru'keta ba, dan yarinyar daga gani, zatayi hankali

Amma zansa, asamon labarin ta, dan gaskiya sosai nakejin yarinyar ajikina

Haka suka gama, hirar su, kowa yanemi makwanci, dan ko abinci bata tsaya ciba, sallah kawai tayi, suka haye sama


~@ut@r h@jiy@~


[11/10, 8:14 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [29/09 6:29 pm] @ut@r h@jj@ju✍🏻💅🏻🌹: *FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussain*

*In dedicated to FUTHA Luv*

_Page 73-74_

Sosai Hajiya Hafsa tafara bincike akan FUTHA, amma a b'oye dan ita gaskiya tana tausayamata ganin a irin gurin da suke kwana

Bayan haka, indai ansan cikin garin take, ya kamata afara neman dangin ta, amma zaman cikin kasuwa bai kamaci yarinya kamila irin wannan ba

Haka kawai take jin, yarinyar cikin ranta, itama kanta Fadeela labarin FUTHA taji, amma taji ta kwanta mata

Shiyasa yau ta dage saitaje cikin kasuwa gurin FUTHA, mama taso hanata, amma ganin yadda ta nace, harda cewa zata gayawa *Yaya Farouq* dariya mama tayi, tace yome *Farouq* zaimun, mutumin dabaya gari, kuma ko yana gari, mutumin daba magana yake ba, ta ina zaki kai k'arata wajan sa?

Nidai dan Allah Mama ki barni, haka dai tace taje, amma kada ta dad'e

Haka ta shirya, Malam Idi ya kaita, Shopwell tashiga, kayan makeup da undies tasiya mata, sai chocolate


Lokacin da sukaje, Mama nakan ciniki, itakuma FUTHA tana ciki, sallama sukayi, Musa ne yace me zaki siya?, babu nazo gurin FUTHA ne, Mama daga can, tace makarantar ku d'aya? A'a ni 'yar matar data kad'eta ne, jikinta nazo dubawa

Ohoo, to shiga tana ciki, sosai d'akin gashi k'arami amma yayi kyau, sallama tayi

"Wa alaika salam"
.mik'ewa zaune tayi, murmushi tayi mata, tayimata alama sannu, duk da bata ganeta ba

Zama tayi Fadeela akan kujerar dake d'akin, itadai bata Santa ba, kuma duk zaman datayi da Mama, bata tab'a ganin wani yazo gunta ba

Indai ba, mutanen da suke kasuwanci ba, ganin FUTHA na dogon nazari, yasaka Fadeela ta koma inda take, hannunta ta kama

Tace, nasan baki ganeni ba, ni 'yar matar data kad'eki ce, labarinki tabani, naji inason kawance dake, kuma na duba jikin ki


Ya ya?, ina fatan ban takuramiki ba, kai ya kad'a, kafin me hira suke tayi, duk fa wani abin Fadeela bata ganewa, amma tana k'ok'arin nunawa ta gane


Haka suka shantake har la'asar, abinci ta kamata, da lemo, fadeela sai kwano aka bari, ta lamushe komai


Waya Ido yamata ta fito, su tafi, kamar kada su rabu, haka ta tafi, lemo roba uku tabata, tunda batada abin bayar wa, idan kud'ine ai daga gani suna dashi

Mama ma, sallama tayi mata

Zumunci sosai, ya k'ullu tsakanin Fadeela da FUTHA, kusan duk Bayan kwana biyu Fadeela ke zuwa wajan FUTHA, itace dai bata tab'a zuwa ba


Labarin yayan ta, kusan kullum dashi ake farawa, custom ne babba, mai aikin tsakani da Allah, yana zaune a Lagos sai bayan sati biyu yake zuwa


Yau FUTHA cikin tashin hankali take, saboda Mama garinsu zata koma, dama kud'i taxo nema, kuma tasamu, ba'a garin take ba, tana zaune a Chadi, yak'in da ake agarin shi ya korosu, itada k'annenta, to su sun koma, itace kad'ai a Nigeria🇳🇬, itama jini zata d'aga

A b'oye taringa had'a komai, dan kada sugani, sosai take tausayawa FUTHA, saboda tasan idan ta tafi da ita, kamar taqara nisa da ita, da iyayen ta ne

Kuma yanzu wazata bawa ita?, hankalinta duk a tashe yake, balantana yanxu da FUTHA tasani, hankalinta yafi tashi

Fadeela ce, tazo ganin idon FUTHA tayi, yayi Ja, da'alama kuka tasha, tambayar ta tayi, bata b'oye wa Fadeela komai ba, haka tabata labarin ta, daga lokacin da Kaber ya tsinceta har kawo zamanta a Niger da mutuwar Aunty Meemi, da accident d'in da sukayi
(Bazata iya tuna komai, na gidan suba, kota tuna, bazata tantance komai ba)

Kuka ta tayata, jin labarin ta, duk da, wani rubuta mata, tayi wani kuma, ishara tayimata da hannu


Fadeela ce tace, share hawayenki, dama muna buk'atarki, zaki koma gidan mu, zamu rik'eki da amana, kamar yadda Aunty Meemi ta rik'eki

Zaki cigaba da karatun ki, kuma a haka, zamu bada cigiyar danginki

Insha Allah zaki kasance abin alfahari wataran, kada kisa damuwa aranki, komai a rubuce yake cikin k'addarar ki, ki godewa Allah, da baki fad'a mugun hannu ba


Shekara wajan shida, baka gida, ai abin da ciwo, amma da Allah, kuma baxaki iya tuna komai, ba?

Kai ta kad'a, ahaka Fadeela ta tauatae shirya kayanta, hawaye ne yake zuba kawai a idonta


Sabo turken wawa, (ko mutuwa ce, sabo akeyiwa kuka, ba itaba), Mama shago shago, take lek'awa sallama, had'a da, Neman yafiya, dan zaman ta awajan shekara 6 kenan, kuma dole akwai wanda zaka b'ata wa, akwai wanda zai b'ata maka

Haka aka yafi, juna, tana kuka mutane da yaranta sunayi, haka mota taja sai tasha, inda zatahau motar Lagos, daga nan ta hau ta Chadi, tareda FUTHA dasu kabeeru, Isah, Musa, Bala Fadeela aka tafi rakata


Suna tsaye mota taja, wani kuka tasaka, tana tuna abin alkhairin Mama wajan ta, matarda ake fad'in halayenta da masifarta, amma bata tab'a yimata ba

Ake fad'ar rowarta, amma ita bataimata ba, komai yimata take, ko yanzu badan tak'i karb'a ba, dubu Ashirin tabata, ganin kamar,
[29/09 6:33 pm] @ut@r h@jj@ju✍🏻💅🏻🌹: ranta ya b'aci, yasaka ta d'ebi dubu goma, itama Kabeeru tabawa wanda yakata gurin, batareda kyashi ba, ko bak'in ciki, shima danyaja jari

Tunda mama tabar musu, komai na kayan abinci, wani kuma siya sukayi, sosai tayi musu abin arzik'i

Haka kowa yajuya, dan shiga mota, wadda suka rako ta tafi, saifatan saduwar alkhairi

Daga nan, Fadeela itada driver'n su, basu zarce ko inaba, sai unguwarsu

@ut@r h@jiy@
[11/10, 8:18 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [09/10 6:18 am] @ut@r h@jiy@💅🏻✍🏻: *FUTUHATUL KHAIR*

*°°°°°°°°°®NWA°°°°°°°°°°°*

*©Zainba Y Hussain*

*Dedicated to Futha Luv, 'yar mutan Bauchi*

*Allah ka d'aukakamu ka kad'aukaka qungiyarmu, kasa mu zama wad'anda za'a amfana da abinda muke rubutawa Ameen, bi jahi habeebe Mohd SAW*

*page 75-76*

Alu quarters itace unguwar da driver'n da dosa, wayyo dama sokoto da manyan gidan haka, lallai gaba d'aya kaina kwancewa yayi ganin yadda aka keta gidaje, gini a qawace ahaka har muka iso wani katafaran gida, kamar a qasar Kuwait ko Qatar


Haka driver yayi hon, da gudu naga wani d'an saurayi yaxo ya bud'e, shi kansa get d'in gidan abin kallone, FUTHA ansaki baki ana kallon gida mai kyau

Tunani tafara itama fa, kamar ada can tasan gida mai irin haka, a ina?, takasa tunawa, haka har yaje parking area ya ajiye motar


Fadeela ce ta tanjo hannunta, tace welvoe to our resident Futha, ba baki murmushi ta saumata kawai, ahaka suka doshi hanyar main parlour d'in

Lokacin da sukaje Mama nakan kujera a zauna remote ne hannunta, tana ganin su ta mik'e oyoyo 'yata sannu, kunsha hanya

Kamata tayi, sunkuyar da kai Futha tayi, tsuguwana bakintane yayi motsi alamar gaisheta take, lahiya lou 'yata sannu koh

Kusa da ita, ta zauna a k'asa amma, tana d'an wasa da hannunta, Fadeela ce tace, Mama bara muyi wanka, yunwa nakeji wallahi dama banyi break ba na fita, tawo Futha muje

Kama hannunta tayi, suka haura sama

K'ayataccen d'aki wanda yaji komai middle na yammata bawai na manya ba, na gani, d'akine komai pink kama daga kusan rabin kayan sawarta har furniture da pent na d'akin komai dai sai sanbarka

Haka suka Shiga, Fadeela gado ta fad'a tace washa bayana, kinji gajiyar danayi, dariya tai kawai, itama ta gaji,amma bata iya hawa mata gado

K'asa ta zauna, ta mik'e k'afa tana d'an matsawa
[09/10 8:39 am] @ut@r h@jiy@💅🏻✍🏻: A hankali, ita Fadeela daga kwanciya sai bacci, itama haka, baccin su, suke hankali kwance, especially Futha da aka dad'e ba ayi irinsa ba, ga sanyin AC na bugarta saima qara sakewa datayi take baccin ta

Jin shirun yayi yawa, yasaka Mama shigowa dariya tayi, tace kwayi bacci yara, tun safe sai yanxu, kuma a haka bakuci komai ba, idanta yakai kan FUTHA datake yashe kan carpet, sosai yarinyar ta qara birgeta, gata kyakyawa ga gashi kamar India ko larabawa, (a zuciya ta nace ai itace)

Tashinta tayi a hankali, ido ta bud'e,murmushi Mama tayi mata, kan gado ta nuna mata, ki koma anan ,zaki gaji, kinji haka ta mik'e ta koma


Bacci sukayia, basu suka farkaba sai wajan magareeb, Allah yasa dukkansu suna fashin sallah

Ruwa Fadeela ta had'a mata, na wanka sai k'amshi yake, ki tashi kiyi wanka, muci abinci cikina k'ugi yake, bara ni nashiga na Mama

Doguwan riga tabata, tace ungo Idan kin fito ki saka, yaya *Farouq* ya siyamun wannan rigar, murmushi tayimata, karb'a tayi ajiye, ta shiga toilet itama Fadeela ta fita


A shurye Fadeela tazo ta tarar da Futha a'a a harkin shirya, nima bara kiga in maxa, Mama na jiranmu, itama shiryawa tayi, Humrah ta bata itama tashafa suka sauka downstairs

Mama suka tarar kan dining tareda Abban su, gaidashi Fadeela tayi, itama Futha haka, hannu ya kad'a yace lale 'yata sannu koh, kai ta kad'a

Abinci ne mai rai da motsi, Tuwan shinkafa da miyar taushe taji manshanu da naman kasuwa manya cikin sa, sai juice na Apple, ganin 'yan gidan kowa nacin nasa, yasaka itama ta zage tana kwasar gara

Haka suka ci, suka gama, kuskure bakinsu sukai, aka dawo parlour kallo, suna kallon suna d'an tab'a hira, ahaka har lokaci yayi Mama tayimusu sallama tayi part d'in Abba

@ut@r h@jiy@💅🏻👗
[11/10, 8:25 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [23/10 3:47 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻💦👗: *FUTUHATUL KHAIR*

°°°°°° *®NAW*°°°°°°

*©Zainab Y Hussein*

*_In dedication to FUTHA LUV_*

_*~page 77-78~*_

*I'm sorry 4 delay Fans, luv u all*

Zaman FUTHA gidan Mama yasa taqara wayewa rayuwanta kuma ta inganta, komai take so ba'ayi mata geji da shi ba
Fadeela ma tana iyakar qoqarinta wajan nuna kulawa da FUTHA, Abba kansa ya d'auke ta like Fadeela
School kanta sai da aka canja mata, duk da bata Iya maida abu da baki, amma kowa yasan tanada qoqari
Bata shigewa qawaye dan tasan ita ba kowa bace, face yarinya mara asali mara gata, mai yawo daga nan qasa zuwa wannan gari
Daga hannun wannan sai hannun wanccen
Shiyasa ko a gidan, Qur'an kusan shine abokin hiran ta, sai in Fadeela tana nan

Yanzu duk wanda yasan FUTHA saiya qara kallon ta, dan taqara wani fari da kyau ga gashinta dayake shan gyara yanzu
Hankalinta kwance, duk da ada d'inma hankalinta a kwance yake, amma nan gidan saitaji tafi sakewa ga AC data ke bugunta any time, ga abinci mai hankali
Islamiyya agida suke, malami guda aka ka musu itada Fadeela, tunda wanda keyiwa Fadeela yayi tafiya

"Mama akullum Idan tana kallon FUTHA, saitaga tana mata kama da wata amma tarasa a ina, shiyasa wani lokacin har pics take d'ebowa ko wai zataga da wadda take mata kama
"Idan kaga FUTHA kaga namanta, kamar su d'aya batad'auki komai na Abbanta ba, kamarta da larabawan Libya sak, har tsahon saidai ita NATA farin baikai nasu ba, anan sainace dangin Abbanta tayi

Fadeela "Mama ke kwala mata kira," na'am Mamasco, gani nan
daga upstairs ta sauko, Mama gani, FUTHA na kamawa gashin ta, kinsan bata iyawa
Ok" kuyi sauri mana, kunsan yau Aunty Zainab zatazo kuma gashi kunce dole sai kunje Kano, nibadan kun naceba aida ba kujeba, ga shi Hajiya Zainab tana zataga 'yata
Kullum inamata maganar ta, Allah mama Idan bamije yau ba, nasan tafiyan ruwa zata sha
Ba komai, kudai fara zuwa Ku amso min alkakin danace
Haka akayi suna dawowa daga karb'owa, ko 10 minute basu qara ba driver yajasu sai Kano ta dabo
[23/10 4:32 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻💦👗: Gidan qanwar Mama sukaje, karb'a tayi musu ta arziqi, dan dama ita ta nace suzo, shiyasa suma suka matsa sai sun tawo, next week su FUTHA zasu fara WAEC, shiyasa ko 4 days sukai is ok
Sahaf sunan 'yarta, ita qanwar Maman, itama budurwa ce mai hankali, tana buk ma, so tunda suka zo tare ake tafiya school da su, daga nan aje can daga can aje nan
Gidajen qawayenta ba'a barshi ba, kullum dai ahanya ake wuni, sun zaga gari sosai
Sunje gidajen tarihi na Kano, sunga Dala da Goran Dutse, alal haqiqa garin yamusu dad'i
Samari kusan 4 to 5 sai sunyi sallama wajan FUTHA, ita abin dariya yake bata, Idan akace wa ake nema?
Wai balarabiyar data zo, to ita Idan ta fita da wani bakin zatayi magana, shiyasa ko taga fita bata yi
Suyi, suyi ta fita amma qi take, ita batasan tana zata fara zance ba koda tanada baki, bare babu
Haka kowa yake tafiya da sagaggiyar gwiwarsa, Fadeela tayi masifa harta gaji, tace ke Allah yabaki kyau shine kike wulaqanci, ba dad'i amma nasan wataran zaki so wani, shima ya rama

Hhhh Sahaf dai dariya take, ganin Fadeela ta d'au zafi, harda dena kula FUTHA
Ko gurin kwanciya qasa ta sakko FUTHA tasa pillow da blanket ta kwanta, tare suke da ita a qasa ana kallo, dataga Fadeela bata kulata ba, saitayi tawowar ta, kwalla tafara sharewa tanada kwance
Me Fadeela take nufi?, daga bata fita ba zatayi fushi da ita?, ita batasan batason kula kowa ba, saboda rashin dangi, Idan akazo tambaya akace ba'asan danginta ba, ya zatayi daga nan duniya zatasan ko wacece ita
Bayan haka, su masu sonta sunada baki, ita bata dashi, ya za'ayi ayi hiran?
Kuka tafara tana takura kanta da tuna wani abu ko yaya na rayuwanta, abaya ko ta tuna garin su da sunan Abbanta amma ta kasa bazata Iya ba
Sahaf ce tace ke ina FUTHA?, banganta ba, naga da ita ake kallon?, waigawa tayi ita, inata yi to?
Fadeela ce tace kyaleta fushi tayi, haka ake mutum yazo gunka amma kaqi ka fita, dan taga tanada kyau ko me?
Naga har lecturer naku saida yazo jiya, amma kememe taqi fita, ita ba'akwamaceta ba, sai itace, wallahi bazan kulata ba, Idan yaso ta tafi gida yanzu ma
Umma ce tace Fadeela Ba haka ake ba, kuma kedakanki kike cemata haka, idan wani yafada fa, kuma da agabanta kika fad'a bazataji dad'i ba
Kya saurari uzurinta, kafin ki yanke hukunci, kuma ke kanki kika kalleta kinsan badaga qaramin gida ta fito ba
Kurunga jin uxurin mutum, kafin ku yanke hukunci, yarinya mai hankali da addini, plx Fadeela adena arin haka
Kuka naje naga tanayi, kuma yanada nasaba da abinda kikayi mata, narashin kulata da kike
Huum, Umma hakane Insha Allah bazan qara ba, bari naje, dayafi kuwa dan bakiyi daidai ba

Haurawa sama tayi, qofan abud'e take, shiga tai, ganinta tai takifa kanta a pillow, qarasa wa tai, d'ago kanta tai
Akan cinyanta tasaka kan FUTHA, fushi koh FUTHA menamiki kike kuka akan nayi miki magana kibar wulaqanci shine zaki dawo qasa ki kwanta
Kai takad'a bahaka ba, huum to yane?, bayani tafara mata akan batason tafita tarasa yazatayi magana, kuma ita suna zuwa wajanta dan basu san ita bata magana ba
Bayani tamata, sannan ta ringa bata haquri akan bazata kuma ba
Kafin me sai dariya, haka suka kasance har ranar dazasu koma

Kuma Ya Farouq shima aranar ko washe gari zai dawo daga Lagos

@ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [23/10 7:38 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻💦👗: *FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA Luv*

*page 79-80*


Tsit kake jin parlour na gidan. Masu hayaniya basu nan, antafi kasuwa siyayya, anbar Umma ita kad'ai agida
FUTHA kinga wani yari wallahi tai kyau, ki d'auka, dariya aka saka saboda yarin wani qatone ga ita kuma batason yari qato
Uhum tace
Haba hajiya ki d'auka mana zan miki ragi, yana magana yana wani kashe ido
Dariya akayi ganin yanda tayi kicin kicin da fuska, jitayi dama tana magana ta zageshi
Babba ne amma sai wani kashe ido yake yana matsowa kusa da ita, hannu ta d'aga alamar ya isheta surutun da yake
Ganin basu gane ba, fita tai ta tsaya har suka gama suka fito

Ko da aka koma gida, labarin aka ringa bayarwa, Umma itama saidata dara tata dariyar
Kayansu duk sungama had'a wa, saijiran driver yazo a tafi,
Hajiya Zainab taso ta had'u da yarinyar da qawarta kebata labari, Allah baiyi ba, lokacin da taje gidan ta kuma tana libiya, shiyasa basu had'u ba

Mama dai tunda Hajya Zainab tazo ta yinarmata taketa kallon ta, takasa sanin ina tasan mai irin fuskanta
Haka ta qaraci tunanin ta ta haqura, Hajiya to bakida pic na yarta ki?, lah inada shi bara kigani awaya, hartafara bud'e gallery, akayi mata waya, shiyasa ita bataga pic d'in ba
Hajiya Zainab matar abokin Abban su Fadeela ce, lokacin da suka dawo Sokoto da zama suka had'u dashi, abota ta qullu ta tsakani da Allah
Matansu ma haka, sosai suke gum inch, su a Sama road suke zaune inda ya tamfatsa gidan sa

Shekaransa 3 da tarewa agarin, abokansa suka matsamasa yafito takara, Allah yabashi sa'a alokacin inda ya kasance yacinye kuriar gaba d'aya, akashi 100 yanada 80

A wannan shekara Sokoto tayi sa'ar governor, mai hankali da kirki, ga aiki, ga taimakon talaka
Matarsa ma tana taimakonsa da shawara ta gari, shekarar sa 4 yana a matsayin, kafin wani ,zaben yazo
Mutane sin so ya qara fitowa amma yaqi, badan komai ba, yanason kasancewa cikin iyalansa amma ba hali, kuma shi baywani son hayaniya sosai, wannan dalilin yasaka shi qin kara fitowa
Ayanzu haka shine Senator ne, Abuja yake da ,zama, amma sannu sannu ya dawo sokoto gaba d'aya, kodan garin ya amfana dashi
Tunda annunamasa hallaci da qauna a garin, bashida matsala a rayuwa, sai d'aya wadda akullum da ita suke tashi daga shi har matarsa da ita
Rashin tilon 'yarsu da sukayi, amma wani ikon Allah saidai suyi tunanin ta, amma ba ikon yiwa wani magana akanta (aikin asirine, wanda baikaryeba)

Tanada kirki sosai Hajuga Zainab, qawartace sosai, sunyi wajan 10 years tare, tanada kirki, bata d'aukan kanta wata
Yaranta 3 duk maza suna business tare, kaya ake kamu su, kafin yanzu kuma da saidai su bayar ana kaiwa Saudi, senigalies da Atamfa Super da shaddoji a d'inke su ake kai musu
Abotarsu sai san barka, kansu a had'e yake kamar ya da qanwa ko wacce tana takatsantsan wajan kiyaye abinda zaika rashin jituwa tsakanin su
[23/10 7:50 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻💦👗: Sahaf bataso zasu tafi su barta ba, tana da biki na qawar tane aminiya miss Hafcy, da babu abinda zaisa bata bisu ba
Har da kuka da zasu rabu, ita kanta FUTHA tayi sabo da su, haka motarsu ta d'aga sai birnin shehu

A mota tunsuna hira har bacci ya kwasesu, dan akwai tafiya tsakanin Kano da sokoto sosai, shiyasa har sukai baccin su suka tashi ba'azo ba
Alhamdulillah sun fita daga gida asa'a sun dawo asa'a, godiya ga wanda yake kare bawansa alokacin da yaso
Mama tayi mutuqar murna da dawowar yaranta, bare FUTHA itama tayi missing mama, wanka ko wacce tai akanbaje ana ta bada labarin Kano
Mama FUTHA tayi miji, takusa kamiki suruki mai hankali kuwa
"Allah sarki 'yata Waye shi a ina suka had'u?
Ita FUTHA sakin baki tayi jin zatayi mata qarya ina ta had'u da saurayin, amma bara dai taji wacce qaryan zatayi
Mama ai yari da sarqa yake saidawa kinga wani kallo na love daya ke mata, ya mato akanta sosai, saurayi dashi bakinsa Maikyau
Dariya ita FUTHA tai jin wannan tsohon akecewa Yaro
Ko mama ma dai dariya tai, dataji gaskiyan labarin
Huum kinga gobe yayanku zai dawo, saboda haka saiku tanadi mai za'a girka masa

Kai Ya Farouq ya kusa, lallai watan fita yawo da cin dad'i, yazo

Nan tafara bawa FUTHA labarin yayanta dama dai tasanshi abaki sauran ganin sa

@ut@r h@jiy@💅🏻✍🏻
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [24/10 8:23 am] @ut@r h@jj@ju✍🏻💅🏻💦👗🌹📚: *FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to Bilkisu(FUTHA Luv)*

*page 81-83*

Mama ikon Allah flight en qarfe nawa zaibiyo?
"Naji dai yace wai sai wajan magbree zai iso gida, amma 4 zai sauka
" hum, dama broth haka yake, mu muna d'okin ganinsa shi kuma saiya gama yawansa cikin gari sannan zai dawo gida
Ke kuma banda abinki ai ko ya sauka ko da gida yafara zuwa dole dai sai yaje o office nasu na nan, kinga kuwa bagara yagama da su ba?
Haka ne to, Allah mam na qagu naga broth 2 month ban ganshi ba
Wanccen zuwan da yai duka bana nan, shi kuma nasan murna yake da bana nan
Kyaji da shi, ai ya huta kuwa, ba fita kullum muna tare
Haka kikace koh?, eh mana
Itadai FUTHA murmushi take, komai nasu yana burgeta, yanda suke yin wasa da dariya
4:24pm agogon Niger da 9ja ya buga, adai dai lokacin ne Custom Farouq Yake sakkowa daga airport na sokoto, danzuwa mahaifarsa bayan wata d'aya da sati 2 daya shafe bai ziyarci gida ba
" Farouq mutum ne, wanda yasan yakamata yanada hankali, daidai yanada biyayya, rayuwansa simple ce, namiji ne har namiji kyakyawa ne ajin farko, yanada kwarjini da Haiba, da farin jini, ga jajircewa wajan aikin sa, shine assistance chief na Nigerian Customs duka, yana zaune a Lagos inda cibiyarsu take, baya d'aukan hauka ko wargi ga masu hannu da shuni akan kayansu Idan aka kama
Baya amsar bravery nd corruption ga kowa, wannan yaqara siyamasa mutunci ya kuma d'auka ka darajar sa
Tsayayyene akan aikin sa, rashin aikata mugun hali wa qasar sa itace tasa duk inda yashiga yake da kwarjini
Duk wata barazana bata sashi firgita akan abinda yasaka agaba, baya shakka yakama kayan kowaye indai ansami akasin abinda qasa takeson shigowa dashi,
Addu'a ta Iyayensa ita take riqe dashi, da tsarin ubangiji amma da tuni saidai wani bashi ba, wannan kyawawan halayyen nasa, sune suka saka yakeda wannan matsayin ayanzu
, bawai dan shekaransa yakai ba, abashi ba wannan matsayin ba, a'a ikon Allah da kuma tsayuwa akan gaskiya ruwa da iska
Yai fice afad'in 9ja duka, a Lagos yake da zama, amma yana zaga all 36 states d'in, dan ganin yanayin aikin kowa
Farouq kenan, d'a tamkar da dubu, iyayensa suna alfahari dashi dama jama'a baki d'aya
Qanwarsa guda Fadeela, komai nasa natane, yana sonta matsalanta d'aya tana takuramasa da broth akaini guri kaza, daga andawo taqara cewa nan, sosai yake qaunar ta, wataran suyi fad'a wataran ashirya
Iyayensa suna son yai aure, shima haka bawai yaqi bane, amma yammatan ne abin tsoro, suba tangaren bane bare a kwankwasa aga ne tagari, kuma ba kwarya ne suba, yanzu zakaga mace har mace amma halin nata sai a hankali
Ansha shine ya warke, ya tab'a yin budurwa Aneesa A Rimi, (Anee), sosai yake sonta itama haka, amma nata Iya bakine, bawai dan Allah take sonsa ba, saidatagama cinye kud'in sa, ya isheta sannan ta fara masa wulaqanci ya sota sosai, bayanda baiyi da ita ba, amma taqi kunsan 'yan katsina da son kud'i
Haka yarinyar tamasa, baifi da wata biyu ba, saijin bikinta yai, dama ankusa shine dai tace bara taci kud'insa tayi wasa da hankalin sa
Wannan yasa yake tsoran mace, amma duk da haka, baiga wadda tamasa ba, daya fara dating nata

*Labari*
* * *

Saukarsa keda wuya, ya hango driver na gidan su, yana washe baki
"Oga barka da zuwa"
"Ansha hanya, wallahi kuwa, sannu to
Briefcase nasa ya amsa, shi kuma gaisawa ya tsaya
gaisawa da mutane wanda yasan

Please Login or Register in order to submit comment