Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan qawarki
Wallahi kuwa aje wataran, Yau ai ranace mai tarihi da farin ciki a wajan mu
Amma FUTHA zaki Iya sanin sunan garinku da Abban ki?
Kai ta d'aga (kunsan dama harda mantau aka saka mata)(amma koda babu Mantau a shekarunta bazata iya fadar wani information Maikyau ba)
Mama nasan dai Baby Maman mu ke cewa, then a Katsina muke amma daga nan bansan komai akai ba
Mama na a Libiya take, muna zuwa, da Abuja wajan Aunty na
Yauwa to a katsina wacce unguwa Abban ki kuma ya sunan sa?Mama ke tambayar ta
Abba kawai ake cewa, haka dai sukaita tambayar ta ita kanta taso ta tuno wani abu amma ta kasa
Haka zamanta yaci gaba, HAJIYA Zainab taiwa Mama waya akan batada lafiya sun tafi garin su
Sosai ta jimantamata akan Allah yabata lafiya, bata fad'a mata cewar ga abinda yasameta ba
Saboda batason tunowa, yawan maganar shine yasamata ciwo, gashi jininta har yakai 200 abinda ba'aso kuma
Ya Farouq acan bashida tunani saina 'yar makaranta, har ya dawo yana tuna ta, wajan kwana 2 yana zuwa qofan school en amma Allah baisa ya ganta ba
Yau yana CBN qrts gidan su Leemcy wanta abokin sane, kamar ance d'aga kanka itace cikin motor suda Fadeela, motar bata Gidan su bace, ita yagani kad'ai ba Fadeela da gudu ya tashi,amma ina kan yaje sun qule
Abin tausayi ayanzu duk wanda yasanshi yasan yanada damuwa ko Mama tayi tambayar shiru
Yau wajan shopping yaje itama haka, lokacin ita tare suke da class mate nata, tunda sauran kwana 2 candy nasu shine aka zo siyayyan gift wanda zasu bawa teachers nasu
A wajan cashier suka had'u, matsawa yai kusa da ita, jikinsa har rawa yake ganinta da wata baqar abaya anyi rolling ga kanta yai tum, ga giranta baqa data qawatamata fuska
Yana qarasa wa har yace yammata........ sai qirr yaji Waya, kamar bazai d'aga ba, saboda yaga har anfara musu lissafi suna biyan bills
OMG ogansaneke kira da sauri ya d'aga dan yayi yayi yagama wayan ya juya
Saidaya qare sannan ya juya wayam, innalillah, dubawa yafara harda fita waje amma shiru ba ita ba labarinta
Hankalinsa ya tashi, sosai yafara tunanin kodai aljana take masa haka?, bashida answer
Mama ce Yau dai tasha alwashin lallai sai anje gidan Hajiya Zainab suyimata sannu da kuma gaisuwa had'e da jaje, Maigidan ta yagayamata komai
Haka kuwa duk suka shirya

@ut@r h@jiy@๐Ÿ‘ฑ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ’…๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [01/11 6:09 am] @ut@r h@jiy@๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’๐Ÿปโœ๐Ÿป๐Ÿ’:

*FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*page 106-110*

Fadeela ta riga FUTHA shiryawa, tana tsaye dai tana kallon ta, ganin madarar kyau da Allah yabawa FUTHA, akan stool take amma sai gani nayi ta miqe da sauri
D'akin Mama tai, Mama!Mama! na tuno wallahi natuno
Me kika tuno Fadeela?, mama wallahi FUTHA 'yar gidan uncle Abdallah ce, Mamanta Hajiya Zainab, kuma kinji tace a katsina suke, before suma a katsina suke, kuma ina yayar sa Aunty Meenah a Abuja take, Libiya garin su Hajiya Zainab itace ga kamarta da ita kamr antsaga kara
Ajiyar zuciya Mama ta sauke, tace Ikon Allah, wato Allah Idan yaso ya jarrabeka abu yana kusa da kai saiya hanaka ganin sa, wallahi tunani na a kullum nasan fuskar FUTHA amma a ina?, shine abinda nake kasa tuno wa
Allahu Akhbar Allah mai girma buwayi gagara misali, mai hikimane shi cikin Hikima Allah Hakeem, wato itace Bilkisu wadda nakejin labarin ta b'ata, bana ita tagayan ba
A family nata na Libiya da sukazo ake maida zance
Wallahi itace ga kama nan, Mama ina zaune kawai na kalleta saina hangi Fuskan Aunty Zainab, aisai muyi sauri mu tashi Allah yasa abinda muke zargi dai dai ne
Ameen Fadeela tace, bakinta yakasa rufuwa FUTHA zataga iyayen ta, kai babu abin godiya bayan Azzawa jallah
Ke Fadeela ki rufe bakin sai dariya d murna kike, Hala Abdulaziz yace yana so, hhhh bansani ba inadai farin ciki ne
Huum ni kuma kinga jikina some how nake jin sa, kamar wani abu zai faru amma na murna banjin baqin ciki ne, tun kwanaki sainayita mafarkin wata mata da yara 3 amma bayansu ajuye sunata laluba ciyayi Idan naje sai naga sunmun nisa
Jiya kuma har wajan su na qarasa na zauna kafin muyi magana akayi kiran Sallah, shine jiki na duk ya mutu
Kafad'arta ta dafa tace komai yazo qarshe insha Allah, wannan matar ba kowa bace illa mahai.......
Fadeela ku fito inajiran ku, maganar dabata qarasa ba kenan suka fito
A'a yammatan Mama haka kukayi kyau, lallai munkusa shan biki, dariya sukai amma ba wadda tai magana
Da adda'u suka shiga motor, baran FUTHA da qirjinta sai fat fat fat yake mata, dannewa take kawai
Hanyar Sama road suka nufa gidan Alhaji Abdallah Mai Nasara, babu wanda yai magana cikin su, ita mama addau take Allah yasa haka ne, itama tasamu real parents
Itama kanta Hajiya Zainab tana zaune akan carpet kallo suke amma ita idontane akai hankalin ta baya wajan, Ahad ne ya tab'ota yace Mama lafiya?
naga tun d'azu kamar ba kallon kike ba.Ahad wani iri jiki na yake, kamar zanga wani abu, ko kuma zan rasa
Insha Allah alkhairi ne, kidena saka damuwa Allah zai bayyana Aunty indai har tana raye, kiyawaita addu'a kuka qin cin abinci, tunani duk bashi zaisaka Allah yaka mafita ba, addu'a itace babbar mafita
Hakane Ahad Allah ya rayamun ku, Ameen uwa ta gari
haka suka ringa keta gidaje masu kyau har Allah ya kasu qofan dazata sadaka da gidan
Horn sukai akazo aka bud'e
Already dama ansan su, ba maganar bincike ko wajan wa aka zo
Da qarfin gaske daga Maman FUTHA har ita sukaji bugun zuciya, kamar ta juya FUTHA amma ba hali, haka suka jera kowa da abinda yake saqawa har suka isa parlour d'in
[01/11 6:20 am] @ut@r h@jiy@๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’๐Ÿปโœ๐Ÿป๐Ÿ’: Assalamu alaikum, ga baqi ba notice
Haba dai wani notice jiya nake cewa yau zanzo fa, saina tashi jikina a mace
Marab....... d'agakan da tayi shine ya hanata qarasa fad'an abinda ta ke so
HAJIYA menake gani a bayan ki, BILKISU ce wallahi 'yata ce aka ce ta mutu ga kama nan sai kuka
Itama lokacin da tayi arba da Mama jitayi a duniya ba abunda take so sama da ita. taga ne Maman ta, ga kama ma nan, da gudu ta qarasa tace Mama ! mama !
Nice Baby Mama kina raye baki je kin duba niba, ina Abba yake Mama nagane ki kece Mama na, Mama ina Abba meyasa baku qwaceni wajan Aunty Chuchu da zata tafi dani ba?
Fadeela mama na kenan, wallahi itace ina mafarkn ta fuskan Mama bai b'acemun Mama ina Babyn mu ko baki haifa ba?
Gaba d'ayan su jikinsu rawa yake, kowa kuka yake ita FUTHA takasa sakin Maman ta, sai wani qara riqunqumeta take yi
Wata irin soyayya da qauna ta d'a da uwa itace take sauka a jiki da zuciya na wad'an nan bayin Allah
Sosai suka ringa koke koke na murna, Mama ce ta tab'a bakin ta tace Baby yana ga kina magana?
Mama ban jima da farawa ba, Ina garanny Mama?
Bata rufe baki ba, tajiyo hayaniya sune Waheed ne ya musu waya akan suzo anga Aunty

@ut@r H@jiy@๐Ÿ‘ฑ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ’…๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [01/11 8:44 pm] @ut@r h@jj@ju๐Ÿ‘ฑ๐Ÿปโ€โ™€โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ“š๐Ÿ“:


*FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*In dedication to My Friend Sadiya Abdallah Shehu(STYLICH BICH), Wllh I dn no ur love to me is highest, u care about me nd ma love once, may almighty Allah protect, assist u n guide u among ur evil, u r indeed d greatest Stylich u support me aloot, love does nt care abt money or beauty, our love is generally 4rom Rabbis samawati I'm out of word Stylich, may Allah SWT bless u wth great personality husband, nd bless u too wth good Children, I love u, I love really appreciate wth ur good prayer to me, Ma STYLICH nd Ur Blood sister Ya Hajja. Ya Allah bless STYLICH wth powerful health Ameen*

*page 111-115*

Hajiya da gudu ta shigo, tana cewa Allah Hakeem da gaske anga Bilkisu?, tana shigowa da ita tafara cin karo
Habawa da gudu taje ta rungume ta, tana kuka BILKISU ki yafeni wallahi bada sanina nayi miki abinda nai miki ba
Bilkisu kina raye, akace kin mutu, munje Har NIGER gidan Alhaji Raheem yace kunyi accident, Baby kece tana magana tana shafa fuskan ta
Gaba d'aya jitayi ko yau Allah ya d'auki ranta tacika burin ta taga iyayen ta, cikin aminci, lallai Allah shi keda IKO
Abbanta ma sai gashi shida Abban su Fadeela, waya akayimusu, ahaf wani sabon kuka da murna su suka qara samun waje acikin gidan
Abban su Fadeela yace Allah qadiran wa maridan wa hayyan rayayyen sarki, wato 'yarka tana gida na amma Allah baibamu ikon gane taba
Nan fa hira ta sarqe FUTHA tana kusa da Abban ta (Dama yana qaunar FUTHA sosai)
Qannen ta dukkansu haka suka ringa zuwa suna mata murna, kafin me saiga 'yan uwa da abokan arziqi, sun cika gida
Mutane basu ragu ba, sai da akayi sallah ta Magreeb, abokan Abban ta nan ma kowa yazo yayimasa murna
Aunty Meenah itama Sai gata, anmata waya flight ta biyo, kai Iyaye rahma FUTHA jitayi kamar da can wani Abu baitab'a faruwa ba
Basu sami damar magana da Mama ba dole sai da safe tace zata zo, Fadeela fuska tai tace itada qafarta qafar FUTHA bazasu rabu ba
Haka Mama ta tafi ita d'aya, tana mai farin ciki da murna
Kwana tayi da Iyayenta anamata sannu, ana bata labarin abubuwa
'Yan uwan Maman ta suma ayanzu haka suna cikin jirgi dan zuwa ganin jikar su, da 'yar su
Haka akayi washe gari da wuri Mama tazo, anan ma tayi breakfast ita da su
Nan Maman FUTHA tace Hajya banda bakin godiya duk abinda zance ban biyaki da shi ba, Illa iyaka nace Allah ya qara had'e kan mu
Ameen tace, Huum nifa bansan da gaske cewa 'yarki bace, ashe haka ne, amma ya akayi bakwa maganarta sannan ta b'ata baku nemeta ba, sai yanzu?
Kuka Maman FUTHA tasaka tace Allah ya isa tsakanina da Chuchu ta cuceni ko da yake kanta tayi wa, dan gashi ni yanzu sai dai labari abinda tayi ya jute mata itada uwar ta da uban ta
Huum, to ai Hajya ya akayi, yarinyar Ku tab'ata kuma kuka mance da ita?
[01/11 9:11 pm] @ut@r h@jj@ju๐Ÿ‘ฑ๐Ÿปโ€โ™€โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ“š๐Ÿ“: Kuka Hajiya Zainab tasaka tace
*TUNA BAYA*

Lokacin da FUTHA ta fita bansani ba, nayi zaton tana garden ko study room, har dare ban ganta ba, ganin lokaci ya ja, gashi Abban ta ya koma gidan jiya ba halin magana, saina yi zaton ko tana gidan Hajiya
Haka dai har dare, muna abu d'aya nida 'yar kina, ganin shirin yai yawa yasaka naja motor sai gidan Hajiya, hankalina atashe na shiga, mugun ji wai bata nan, kuka nasaka
Kafin Safiya naci kuka na qoshi haka na tashi nayita sallah da addu'a akan Allah ya bayyanamun 'ya
Safiya nayi, nafita ba inda banjeba inda nasani banganta ba
Abban ta kuma waya ban izini bare naganshi har na fad'a masa, haka har wajan one week ba labari gidan Hajiya ko naje sai daitace Allah ya bayyana amma ba wani duba ko magana mai dad'i, ko ta nuna damuwar ta
Gidansu Chuchu naje nan ma ba fuska, Illa dariya da shewa da aka mun, gashi lokacin cikina ya girma, ban Iya komai ga cuta ta ciki ga damuwa ta rashin 'ya
Chuchu Murna take, harwani sabon wulaqanci ta qaro, banda halin ganin miji gashi a Asibiti ana son ganin sa, saboda since CS za'a mun
Gashi shiru, nakasa fad'awa gida, 'yan wajan aiki na, sunmun kara dan har garuruwa suke tafiya da pics nata
Amma shiru ba labari, Allah maji roqon bawansa nakama naquda bata nan lokacin, komae ya shigo dashi d'akina oho, haka ya shigo ya ganni a haka
Asibiti muka nifa, Na wahala na galab'aita dole akace yasaka hannu CS za'a mun
Kud'in yatafi d'aukowa dama ya shiga dashi gida jiya, nan ya duba baigani ba haka yasa ya d'aga gadon ta
Waih addu'a ita tazo bakin sa, abinda yagani ya d'aga masa hankali, d'aukowa yai ya qone, itama acan house gal na Chuchu ta d'akko wannan leda ta yar ta yimata filla filla
Shidai yana tsaye sai masu gadi ne suka ga ya fad'i, daidai lokacin Hajya tazo
Asibiti akayi dashi, nan fa akayimasa agajin gaggawa, wata nurse ce tafito take tambayar ina wanda yaka wata mata, Allah Raheem maganara kamar a kunnansa haka ya miqe Hajya na bin bayansa
Yara uku ta Haifa batare da anyi mata komai ba, murna nan Hajiya tafara kuka tana neman gafara ta
Banja da nisa ba, tunda nasan aikin sihiri ne, yafemata nayi daga ita har d'anta

@ut@r h@jiy@๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ’๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [02/11 8:45 am] @ut@r h@jj@ju๐Ÿ‘ฑ๐Ÿปโ€โ™€โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ“š๐Ÿ“:

*FUTUHATUL KHAIR*


*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*Adda Bena Yau ban hawa online, bare nagamu da ke, Jabo ta zugaki nasan balinta, ina off yau hhh*

*page 116-120*

Sosai Abdul yai murna da yaran, haka muka tarkato sai gida, Kowa yana murna amma ni zuciyata a cunkushe take saboda b'atan 'yata
Hajiya da kanta tamun wanka ta gyara yaran, tayimun Tuwo da Miya sai kunun kanwa, ko data kamun ban iya sawa abakina ba inacan tunanin Baby
Kafad'anta Abdul ya tab'a yace Maman Baby kici abinci mana then saikiyi tunanin nasan bana komai bane saina abinda nayi miki nasan badan haqurin ki ba, wallahi bazaki yafeni ba
Nazamto macuci a gareki na danne miki hakk'in ki na yasar da 'yata na cuceta dan Allah kuyi hak'uri Ku gafarcen ba yin kaina bane plx Matar arzik'i?
Kuka na fashe da shi nace na yafemaka duniya da lahira, Amma Baby ta b'ata wajan 6 days kenan ba'a ganta ba
What! kina hauka innalillah wannan wacce irin masifa ce, bashiri ya bazama Sai nema
Danginta suma sunzo da su aka ringa nema amma har tsawan sati biyu ba labari, haka na ta rame na d'ashe bancin abincin kirki addu'a itace abar yina ko wani lokaci
Abban ki saiya zamo nafishi dauriya kullum cikin tashin hankali yake baya Iya cin komi
Rarrashi shine nawa, da ban baki duk da nima ina buqatar mai kwantarmun da hankaki
Chuchu koda tazo gida dayake bata nan, hankalin tashe dataga kowa a dangi ya koma yanda yake mun, gashi Abdul ko sauraronta baiyi ba
A ranar dataje d'akin sa duka ya mata, shi baisan wacce k'addara ce tasaka shi auren Chuchu ba, da da hali daya tsigeta a rayuwan sa
Lokacin da masu gadin gidan suka rink'a bashi labarin abinda yayiwa Zainab kuka ya k'ara saki, lallai Zainab mace ce ta arzik'i
Maman Chuchu dai komai yafara lalacewa dan Abban nasu yafaramata wulaqanci, kafin wani lokaci asirin jikin sa ya karye, nan itama yacimata mutunci yai kuka akan rabashi da tayi da wansa da family nasa
Gashi ta b'ata masa yara, babu na zab'e cikin su, ita ma Chuchu miji babu shi yamanta da ita
Munyi nema munyi nema har ba adadi, Abban Chuchu shine yaji lokacin da suke magana akan itace tasaka aka b'atar da BILKISU
Nan fa yazo yagayamana aranar Chuchu tasha duka koni danakeda d'anyen jego sai dana daketa, kuma yace ta fitomasa da 'ya
Hajiyansa kaf sukace court itace zata rabasu da ita
Dukan da taci shine yasaka taimaza taiwa wanda tabawa Bilkisu ya yar akan yaje yazo mata da ita
Tsit ba labari, gashi lokaci yana qurewa, ganin bazatayi nasara ba yasata Shiga malamai akan tanaso ayimata d'aurin baki adena maganar FUTUHA
Allahu Akhbar wallahi tundaga ranar ban qara magana ba, Har dangin Abban ta gara dangina suna magana
Tsafi gaskiyar maishi dan haka tayi mana, amma wani ikon Allah daga ranar bata k'ara samun dama kan kowa ba
Tayi zaman shekara biyu lokacin yarana sunyi kwari, Abdul ya saketa sakamakon ganin ta da yai da wani, yayi kuka yayi danasanin auren ta
Abban ta shima hak'uri yaita bamu, lokacin shima ya aurar da sauran yaran, itakuma tana zaune amma ba kwarjini
Dawowar mu sokoto dalilin baqin cikin ganinta da yai da wani,
Abokinsa Abban Fadeela sin had'u a Umrah shiyace ya dawo Sokoto
Yanzu gashi munyi zaman mu lafiya, lokaci yanaja nasara da d'aukaka ta zowa Abban ki ya fito takaran governor Allah ya bashi
Kowa yana k'aunar Abban ki, yaranmu suna sonki, duk da bama maganarki amma Su kina ransu, addu'arsu garemu da ke itace tayi sanadiyyar warwarewar komai, har gidan nan tazo kwanaki lokacin da hankali yazo mana
Tafad'i yanda tai, itama yanzu haka tazama bata magana
FUTUHATUL KHAIR ina k'aunarki, inafatan kinga ne ba laifin mu bane nak'in nemanki?
Hajiya Nagode sosai wallahi na yadda ke macece ta gari, bakisan ta ba ki d'auki nauyinta har kike mata komai duk da kinsan bakida tabbas na ganin iyayenta
Kinji abin da ya faru, tana magana tana share hawaye da majina, kowa kuka yake yana tsinewa Chuchu da Maman ta
Allahu Akhbar nan itama FUTHA da ita kanta Maman Fadeela suka bada labarin komai, waih ansha kuka duk da FUTHA batasha wahala ba Amma dai rashin iyaye kusa da ciwo
Bata fad'i rashin arxik'in da dangin Aunty Meimi suka mata ba
Sosai Abban ta yace insha Allah ya d'auki alk'awarin nemosu har ita Mama NAFEE sun taka rawar gani arayuwarta
Idan yai duba da yadda Kabeer da Meimi suka maida ta 'ya komai ita, to ai haka Mama Nafee itama tamaidata 'ya har school tasaka ta
Bata barunta tayi aiki, tana karemata mutuncinta, tana sonta duk da ba ita ta tsince ta ba
Mama kuma aisai godiya da fatan zumunci mai d'orewa, dan sunmata hallaci makaranta wadda ba 'yayan kowa suke ba ita suka sakata IMAN INTERNATIONAL SCHOOL lallai sunyi aiki
Kowa dai yayi k'ok'ari akan FUTUHATUL KHAIR. Murna bata k'arewa Abban ta murnarsa tafita kowa
Dangin Mamanta sunzo suma murna, daga kan Uncles da Aunties nata, sai yammata yaran Yayun Maman ta kamar su d'aya da yaran
Dama tanajin larabci nan fa hira t b'alle sama sukai FUTHA na kusa da Fadeela, komai Fadeela
Rayuwa tayiwa kowa dad'i, yanzu basuda matsala ta komai, sai wadda baza'a rasa ba

*Bayan Sati 3*
Farouq komai ya kwance masa abin tausayi, Fadeela kanta tana tausaya wa Broth nata, gashi anyi nemanta har cikin super market amma abin shiru
Addu'a ita yasaka agaba, Mama taji labari itama addu'a take masa Allah ya bayyanata idan da alkhairi
Yau Lagos suka tafi gidan Aunty Benaxir cousin na Abban tace, yankin Ikeja
Sunje lafiya kai garin Lagos yana kyau, sun sha yawo anje beach anje unguwanni da dama
Yau zasu tafi itada K'annen ta suka zo, sai wasu 'yan uwan su
Dan haka itace a gaban motor anata hira tana kyalkyala dariya kanta ta juyar tana kallon gari, batason hawa flight tace gari zata gani ko a tawowar su saida suka tsaya a Kaduna nan ma tazaga
Shikuma daidai lokacin fitowar sa kenan daga office zaije gida ya d'auko wasu files
Cikin nishad'i yake driver nasa hira yake masa, idonsa a rufe yana hango 'Yar Makaranta da yanayinta da yaga gani lokacin da suka had'u a shopping
Idonsa yake bud'e wa a hankali yana murmushi, gefen da zai kalla waih itace k'ara kalla yai wallahi itace da sauri yace driver yi sauri ka tsaya, ya zata tsayawa zasuyi amma ina saiyaga kamar ma qara speed yai na motor d'in
Da sauri ya shiga da kansa yake driving d'in ya kusa kamosu ๐Ÿ›ฃ traffic ๐Ÿšฆta tsayar dama gashi sun shigo wajan cunkoso duk k'ok'arinsa nayai sauri ya wuce abin yaci tura
Sun wuce gashi shi mai adalci ne bayan haka ko da yazo wucewa motoci sunyi yawa
Kansa ya buga a sitiyari hawaye ya fitar mai zafi, office d'in da baikoma ba kenan yafara had'a kayansa ya tawo Sokoto

@ut@r h@jiy@๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ’๐Ÿป
[11/10, 8:26 PM] โ€ช+234 809 308 3613โ€ฌ: [03/11 10:17 am] @ut@r h@jj@ju๐Ÿ‘ฑ๐Ÿปโ€โ™€โœ๐Ÿป๐Ÿ’…๐Ÿป๐Ÿ“š๐Ÿ“:


*FUTUHATUL KHAIR*

*ยฎNWA*

*ยฉZainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*Page 121-125*

Tafiya tayi kyau anje lafiya andawo lafiya, sai fatan gajiya tabi lafiya
Shima Farouq yazo gida lafiya sumul, koda Mama ta ganshi tasan da matsala tunda ranar aiki ce
D'akin sa ta bari ya shiga, sannan ta bishi, yana kan sopa kansa yana kallon sama ya dafe kansa da hannun sa
Baiji shigowan ta ba sai jin hannun Mama yai akan fuskan sa
Son lafiya kana dawowa daga gaisuwa ko abinci baka ciba kazo ka fara tunani lafiya ko wajan aiki ne ko baka da lafiya?
Mik'ewa yayi yana cije baki saboda kansa daya ke d'an ciwo. Mama ba awajan aiki bane. "wallahi dai inajin Mama 'yar Makaranta aljana ce indai mun had'u to saita sub'ucemun, jiya a logas nagan ta duk k'ok'arin namata magana abin yaci tura"
Nakasa kuma cireta a idona, hmm Omar ba komai kuma insha Allah ba aljana bace, then kadena saka damuwa aranka Idan har matar kace wallahi saika aure ta kaji Omar Farouq d'ina gwarzo na jarumina amma awajan aiki banda wajan 'yar Makaranta
Dariya ce sosai ta kama shi, yauwa katashi kayi wanka sannan kayi sallah kaci abinci sai ayi addu'a kasa nima ko har gida zata zo kaganta
Murmushi yayi, sannan ya mik'e. Yadda Mama tace yayi haka yayi harda d'akko Qur'an yana karantawa
Mama daga nan sai wajan Fadeela jiya namata waya bata d'aga ba, nasan fushi tayi mun tafi, tunda nad'an huce gajiya Bara naje
Ai kuwa dai dan ranar da kuka tafi kamar tayi kuka, dan ma Ahmad yana nan shine fa sukaita hira harta ware
Naji yana magana ma wai yasami mata a 9ja, (Ahmad d'an wan Maman FUTUHATUL KHAIR ne)
Lallai Allah ya tabbatar nasan da batayi fushi ba, tuni tamun waya. Mama natafi dama already ashirye take driver ne ya fito da mota suka tafi
Salamu alaikum Sis Fadeela kaina bisa wuyana nasan nayi laifi, wallahi tafiyan da sauri tazo amma amun afuwa
Fitowa Fadeela tayi tana d'aure fuska tace ni ina ruwana, dama nasan haka zaki ce
Wallahi ba haka ba, to kiyi hak'uri na amsa laifina kinga Mama na kallon mu kada tamana dariya
Namayi dariyar, rungume juna sukai suna dariya,gaishe da Mama FUTHA tayi ta ajiye mata tsaraba. d'aki sukai sai hira, nan aka fara hiran Ahmad da soyayyan da suka fara itadai FUTHA dariya ce tata ita dai batason wata So ba, abinda sai yanzu tamasa mu bakin maganar
Kai namanta broth yana gida kuma baici komai ba, couscous mukayi na zuba masa amma yakasa ci, yanata tunanin 'yar Makaranta
Wace kuma 'yar Makaranta?, wa tace nan ta bata labarin tun farkon had'uwar su kawo jiya
OMG! Allah sarki Allah ya bayyana ta, amma zama bacin abinci da matsala
"Bara kiga namasa faten wake

Please Login or Register in order to submit comment